Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wacce za'ayi. Ta kai ƙarshen zancen dajin daɗi aranta dan b'aro b'aro ta hango tsoranta a idan HASEENAN..
Aiko cikin sauri ta tashi tana rintse idonta wanda yayi jajawur, ga hawaye na fitta kamar ruwa, wani hijabin MEENATU tagani a gefan gadanta, ta d'auka ta saka, kana ta nufo inda HAIRANAN take, kallo d'aya zaka mata kasan a tsorace take.. HAIRANAH tayi mata murmushin mugunta tare da bud'e ƙofar...

Dake HAIRANAN ce tafara fittowa, saita fitto cikin wani yanayi, nan ko gaban MEENATU ya fad'i, dan HAIRANAN ta fitto ne da wata kasala akuma cikin wani hali.
Sai dukkansu hud'in suka zuba mata ido..
Tana qarasa fittowa HASEENAH ta biyo bayanta tana tafiya daqer daqer...
Sai kuma kallansu ya koma kan HASEENAN..

Asiya da MEENATU suka sauke ajiyar zuciya...
Idan AHMAD ya koma kan HAIRANAH, saita sunkuyar da kanta qasa, saiya rintse idansa, Wato tana jinsa dan tsabagen iskanci yana rokwanta taqi dena dukan HASEENAN ko... Ai ba zato ba tsammani saiji tayi Kawai itama ya d'auketa da wani shegen mari irin wanda ta d'auke HASEENAH dashi d'azu...

Marin ya shigeta sosai, hakan yasa tayi saurin fashewa da kuka tare da dafe wajen tana cewa, "Nifa ban san mena aikata ba, ni dai kawai naga na dawo hayyacina da wannan wayar wutar a hannuna, ban san meya faru dani ba...
Ai kan AHMAD yace wani abu, sai Asiya tace "Kaji ko, kaji ko Yallab'ai, ai dama na gaya maka aljanune da ita, tunda naga tayo shashin Hajjiya MEENATU nasan ba lafiya ba, dan gani nayi idanta ya juye yayi jajawur kamar bana bil'adama ba, ban tab'a ganinta a irin wannan yanayi ba, haba ni dama nasan da walakin...
HAIRANAH ta zubama Asiya ido, gaskiya ta qara temakwanta.. Kana ta maida kallanta qasa daci gaba da kukanta

AHMAD yayi shuru da zubama HAIRANAN ido, can yace "Haka ne, saita d'aga mai kai alamar zai iya yuhuwa hakan ne, sai yaci gana da cewa, Toh bani wayar wutan, HAIRANAH ta qara qanqame wayar, tace, "Idan na baka dokana zakayi da ita...
Yace "No.. Zan yar da ita ne, akan me zan dakeki, tunda komai kinyisa ne ba'a cikin hayyacin ki bah..

Jin hakan yasa HAIRANAH bashi, ya ko karb'a yaba Asiya sannan yace ta zauna kusa da MEENATU..

Ba musu ta zauna kusa da ita tana me qarema MEENATUN kallo kamar bata santa ba, sai kuma ta maida kallan nata kan AHMAD d'in wanda yake sallamar Asiya da Bala..
Kana ya sakasu su uku a gaba yace yana san yasan ainiyin abun daya haddasa fad'an tun daga farko, ya kai ƙarshen zancen da kallan MEENATU
Aiko shuru tamai, ganinta ai ta gaya mai gaskiya d'azu, meye kuma na qara mai mai ta mai..

Aiko cikin tsoro muraran HASEENAH na hawaye ta fara gaya mai yanda fad'an nasu ya faro, ta tabbatar mai sune suka fara zuwa shashinta suka jata da fad'an a waccen ranar har hakan yasa sukayi sanadiyar zubar mata da cikin jikin nata, amma wallahi sunyi nadama, dan basu zaci tana da aljanu ba, da koda wasa bazasu tab'a lafiyarta ba..
Dan Allah dan Annabi yayi hakuri ya rufa musu asiri wallahi kuskure ne baza su qara yin hakan ba...

AHMAD yaja numfashi yace "Wannan wane irin bala'i ne, wane irin masifa ne, haka kawai ku tashi kuje har shashinta kuje ku nad'a mata dokan tsiya har da zubar mata da ciki Sannan kuma Ku d'ora mata lefin itace ta fara neman ku da fad'an, yanzu ko hakan bata faru ba kuna ganin kumma kanku adalci kenan.

Cikin kuka sosai MEENATU tace "Wallahi bamu san tana da ciki ba, da munsan tana dashi tun farko bazamu daketa har mu zubar mata dashi bah
HAIRANAH najin hakan ta kalli MEENATUN, sai tayi saurin sunkuyar da kanta..

AHMAD Yace "Gud, ai gashi ta barku da jinya sai kuje kuta fama...
HASEENAH tace "Dan Allah dan Annabi nidai ina rokwanka daka rufa mana asiri kan kar wani yaji batun nan bare Baba Alhaji, wallahi munyi nadama..
Galla mata wata shegiyar harara AHMAD d'in yayi da cewa, "Tashi ki ficce min da gani kafin na qara yi miki dukan da zaki kasa muruwa, Sannan idan na qara ganin qafarki a gidan nan ba abin dazai hanani b'allaki na b'alla banza, shegiya munafuka maƙaryaciyar banza maƙaryaciyar hofi , mutane suna zaman zamansu kinzo kin shiga rayuwarsu.....
Simi simi HASEENAH tatashi tana d'ingishi tabar falan, haka babu tab'a lokaci tayi asibiti dan a duba lafiyarta...


AHMAD ya dawo da kallansa kan MEENATU yaci gaba da cewa, kinci albarkacin cikin dake jikinki bazan hukuntaki ba, dan yanzu haka ma neman jinya kike, daba abin da zai hanani d'aukar mummunan mataki akanki.
Yanzu saiki shiga ciki ki gyara kanki daga wannan qarnin da kike yi, kana ki fitto muje asibiti na duba lafiyarki..

Tashi tayi tayi room d'inta kbatare datace mai komai ba, kallo d'aya zaka mata kasan tana buqatar kulawar gaggawa kamar dai qanwar tata HASEENAH, ita koda wasa ma bata d'auka zai barta haka cikin sauƙi ba..

Bata san har acikin zuciyarsa tausayinta ne ya kamasa ba.

Tashi yayi da kallan HAIRANAH wacce tayi shuru kawai tana kallansu alamar jikinta yayi sanyi irin na masu lalurar aljanu😂.. _RAHEEMAT nace su HAIRANAH an iya basaja_

Ke kuma saiki tashi muje ko..
Tashi tayi dayin nesa dashi sosai jin itama tana ƙarnin kwan datasa MEENATUN zubarwa Lokacin da take zanetan...

Tana gaba yana binta a baya, tare da mamakin aikin nata...
Suna isa falan nata ya galla mata wata shegiyar harara yaci gaba da cewa, Wato Aljanune dake ko, saita sunkuyar da kanta, sune suka shiga jikinki kika dinga dokar Matata da qanwarta ko.
HAIRANAH ta d'aga mai kai alamar eh..
Yayi murmushi daci gaba da cewa, "toh jeki toilet kema ki raba kanki da wannan qarnin saiki zo part d'ina na cire miki su.
Shuru HAIRANAH tayi..
Ganin tayi shurun yaci da fad'in, aa kwantar da hankalinki fah, ba wani abu ake musu ba, Yasin kawai zan ja musu k'afa hamsin, kowace k'afa d'aya sai'a tofa ajikin bulala a shaud'a miki, ina ganin kafinma akai hamsin d'in zasu fitta daga jikinki, dan zana ake musu bana wasa ba, ya ƙarshen zancen da juyawa alamar zashi part d'in nasa....
Aiko cikin Sauri da tsoro HAIRANAH tace, "aa basai anyimin hakan ba, nifa lafiyata qalau, kawai ina san su tabbatar maka da gaskiyar zancen ne da kansu, kuma nima nayi nadama, dan Allah kadda ka kulani. Takai ƙarshen zancen da zubo da hawaye..

Girgiza kai kawai yayi da barin falan batare dayace mata komai ba..
Dan shi ko'a film bai tab'a cin karo da labari irin wannan ba...
Taje tasaka Yaya da qanwar a gaba tata maka, batare da tsoro ko wani tunani ba, hmm koda yake susuka fara nuna mata hanya...


MEENATU bata sakama jininta ruwan zafi sosai ba, tadai raba jinin nata da qarnin ta Saka wasu kayan, a cikin motarsa tagansa, ta shiga d'aqar tana lallab'a jikin nata...

Sosai ya duba lafiyar jikin nata bayan isarsu
Anci sa'a cikin dake jikin nata yana lafiya lau, dan bata bari HAIRANAN ta tab'a mata lafiyarsa ba, amma dole tana buqatar kulawa sosai, dan zata d'auki sati biyu a asibitin ko fiyema da hakan...

Tana qoqarin kiran momyn su danta turo mata da qanwarta wata Jamila, wacce take bin HASEENAH, saiga kiran momyn nasu

MEENATUN na d'auka momyn tafara sauke mata bala'i, kan sai taci uwar HAIRANAH, dan bazata dakesu abanza ba, idan aljanune da ita itama sune da ita, dan haka ba abin dazai hanata zuwa gidan anjima ayi wacce za'ayi, dan Yanzu haka tana tare da HASEENAH ne, taga yanda jikinta ya farfashe..
MEENATU taja numfashi tace da ita, ai itama haka jikin nata yake, amma abin da take so da ita shine yanzu acikin rufun asiri suke, idan tace zatayi magana ko zataje tayima HAIRANAN bori toh kowa zai san abin daya faru, kuma dole abasu rashin gaskiya dan basune da gaskiyar ba, musamman Baba Alhaji idan yaji lamarin abin ba zaizo musu da kyau ba..
Jin hakan yasa momyn nasu yin shuru na d'an wani lokaci, can tace toh yanzu haka zasu bar HAIRANAN ba d'aukar mataki...
cikin damuwa MEENATUN take ce mata, tayi hakuri a yanzu ta lafiyarsu suke, ta bari su samu lafiya, neman yanda zasuyi bazai basu wahala ba...
Haka dai momyn nasu tayi hakuri ta turo mata Jamila qanwar tata badan ranta yaso abin da HAIRANAN tayi ba, kuma wai ace babu d'aukar mataki ayanzun..


Shiko AHMAD dama ya barma MEENATUN wata matemakiyarsa me kula da ita har zuwa ranar dazata samu kanta cikin lafiya, kamar yanda dai HAIRANAH tayi tata jinyar a asibitin..


Da dare ne da misalin qarfe takwas da kwata HAIRANAH taci kwalliyar qananun kaya da wadata kanta da turare tana jiran dawowar mijin nata su jone, dan yau ma itace dashi..
Wayarta ce a hannunta sai ta shiga kiran HEESHAM...

Yana tare da NUWAIRAN sa a falonsa suna kallan wani film na India, tare da bama Soyayya hakk'inta, kanta na kan cinyarsa yana me shafa kan cikin matuƙar santa da ƙaunarta, sai zuba mai shagwaɓa take me tsuma zuciyata, fad'i, take "Dan Allah luv kayi hakuri ka barni nasha ice cream d'incan, yace "Baza kisha bafa my Auntii, dan daga wannan lokacin mata irin ki masu san shan sanyi suke fara yima yaransu illa dasu kansu, dan haka bana san yin jinyar Babyna dake kanki, kiyi hakuri kawai sai Allah ya kaimu gobe, tunda bawai na hanaki sha gabaki d'aya bane, aa bazan bari bane ki dinga sha aduk Lokacin da kikaga dama, irin sau uku ko sama da hakan, sau d'aya ya isa tunda ba yanda zanyi dake..
NUWAIRA ta b'ata rai cikin shagwaɓa tace, "toh daga yanzu shikenan, yace "No, tace "please please please dan Allah..
Bai kulata ba ganin kiran HAIRANAN daya shigo masa..
Ya d'auka da cewa, "Y'ar uwa ya akayi ne
HAIRANAH taja numfashi tare dayin dariya tace, "Hmm kaidai bari, zanso kaga aikin danama MEENATU da HAIRANAH abin ba'a cewa komai.
Yace "Subhanallah, kice nayi missing, tace "Yes, ai in gayama! zane su nayi na farfasa musu jiki, suka d'auka aljanu ne dani, baka ga yanda suka tsorata dani ba, YA AHMAD ne kawai yasan ina cikin hankalina, ammafa nasha mari agunsa.
Yayi murmushi da cewa, "Gaya min yanda komai ya faru da sauri.
HAIRANAH tayi dariya da kwashe komai ta gaya mai batare data manta da komai ba..
HEESHAM yaci dariya, yace "Gud Y'ar hannuna, ina yinki sosai, kinyi min maganinsu, gobe ma idan suka qara wallahi kinji na rantse zan tayaki gyara tunaninsu...
Tace "Nasan banda wata matsala idan ina tare dakai, godiya sosai nakema Allah dayasa ka zamo d'an uwa a gareni, yanzu dai sai da safe ka gaida min da Aunty NUWAIRA dan naji ya AHMAD na kulle gida, qila sun dawo ne..
Yace atashi lafiya sister..
Sai ta kashe wayar

NUWAIRA ta kallesa da tashi ta kafesa da ido tace "Dawa kake waya, yace "Ha'a! da budurwata mana...
Cikin sauri tace "Dame kace..
Yace "Nasan ai kinji..
Qarasa tashi tayi kamar zatayi kuka fuskar nan a shagwaɓe tanemi barin falan..
Ganin hakan yasa ya jawota jikinsa yaci gaba da cewa "Sorry my Auntii, Allah da HAIRANAH nayi wayar, babu ni babu wata budurwa dan kin isheni a komai.
Murmushi tayi, da cewa "Tome kuke tattaunawa, yace "sirrin gidanta ne..
Tace "Wato bazaka gaya min ba, yace "Zata gaya miki da kanta..
Tace "Hmm ku kuka sa'ni..




AHMAD ko yana shiga falan HAIRANAN taje da gudu ta rungumesa tana cewa, "Dan Allah ka dena fushi dani my blood, wallahi nayi nadama bazan qara aikata maka hakan akan matarka da qanwarta ba..
Kiss ya sakar mata da cewa, "Toh nayi hakurin idan har da gaske bazaki qara ba, tace "Bazan qaraba insha Allah..
Yace "Gud, kina free ne, ko har yanzu acikin jinin kike, tace "Ai Allah ya soka, dan yanzu na idar da ibadata. Cikin jin daɗi yace, "Me kika rok'a mana, tace "Umm, da fari dacewa anan gidan duniya dana lahira, bayan kuma nayi maka Addu'a kai da iyayenmu da y'an uwan mu, daga ƙarshe saina qara da Addu'ar mallake ka... Takai ƙarshen zancen da rufe idanta, yayi murmushi da cewa, "Da gaske my Baby kina san mallakeni, sanda tabud'e idan nata tace "Wallahi duk macen duniya my blood tana san mallake mijinta, dan Allah zaka tayani da Addu'a akan hakan..
AHMAD ya waro ido yace "wai kina nufin na tayaki Addu'ar Allah yasa ki mallakeni, tace "Haka nake nufi, yace "Ku biyu ne dani fah, tace "Na sa'ni, yace "Zan dai miki wata Addu'ar, amma banda wannan, danna tsorata da ita, kedai kitayin kayanki is ok, tace "Ba damuwa, dan nasan wannan bani goyan bayan da kayi bazai tashi a banza ba.
Yace "ina sanki sosai my Baby, dan Allah ki kula min da cikina na gaba da zaki sake samu a karo na biyu, tace "Hmm, ina maka fatan alkairi, kuma nayi maka alƙawarin bazan qara bari a zubar maka dashi ba, zan kula da kaina insha Allah..
Yace "Allahn ya yarda, tace "Ameen..

Tun anan suka fara b'ata tunanin juna, toh dama da ƙauna, dan haka ya maqiyansu za suyi dasu.💋





Ahaka fa sanda MEENATU tayi wata biyu da sati d'aya a asibiti kafin tama AHMAD yanda zai koma da ita gida, ta warke tsaf tsaf da ita, amma HASEENAH sanda tayi wata uku babu kwana biyu kafin ta warke abinta.

Lokacin Addu'ar AHMAD d'in taci dan dawowa kawai MEENATUN tayi tatarar da HAIRANAH da cikin wata biyu.
Kan uba, shine abin datace lokacin dataga HAIRANAH ta rako AHMAD dan tafiyarsa office, tayi wani kyau sosai amma daga dukkan alama wannan ba irin na farkwan bane, yasata ta rame, sai kuma amai da yake damunta da zaran taci abinci ta koshi, tofa saita zub da shi, wannan yasa tarame sosai sai dai fari da kyau kam ba'a magana, MEENATU ta gane tana da cikin ne dataga AHMAD d'in yakai hannunsa wajen ya sumbata cikin matuƙar so da ƙauna, yayin da taga HAIRANAN ta saki murmushi me qayatarwa...
Ai ba shiri ta sauke labulan windown nata..
Ta lalubi number na HASEENAH tana ce mata, "kin san miye...
HASEENAH dake wajen gyaran fata, ana gyarata saboda tab'an dokan da HAIRANAN tayi mata ana wanketa, taja numfashi tace "aa sai kin fad'a.. Tace "hmm, Y'ar abu kazan uban can ciki ne da ita, yanzu ya zanyi...
HASEENAH tace "Kwantar da hankalin ki mana, dama ba yau mukayi zamuje wajen malami na ba, MEENATU tace haka ne,ni sai yanzu ma na tuna, kinga kina ina ne kawai nazo yanzu na sameki..
Tace "ina wajen Arfat tana wanke min fatata.
Tace "Ok bari gani nan zuwa.. "ok ina jiranki, HASEENAH ta bata amsa da kashe wayarta..




NUWAIRA ko tana ganin aya yanzu agun HEESHAM, kasancewar cikin nata ya fara fittowa, bashi da aiki sai damunta da futana, bani bani hannunsa nakai, bini bini yace baza tayi aiki ba, taje taja masa asara, tunda ba kwari yayi ba.
Ta rasa wane irin so HEESHAM yake mata da cikin nata..
A kullum godiya takema Allah daya bata shi a matsayin mijin Auran ta..
Duk da yana da rawar kai, amma Sam ita bata ganin hakan, dan sanshi da ƙaunarsa ya rigada ya rufe mata ido..

Yanzu haka tana hanyarta ta barowa daga gidan Khadija ne, tazo mata ranar shine tayi mata alk'awarin zataje mata yau, aiko da taje taji dad'i sosai dan daqer ta barta tatafi, Khadija akwaita dasan mutane, bare kuma NUWAIRA da HAIRANAH da suka shiga zuciyarta lokaci d'aya.
Sansu take da zuciya d'aya, macece me gaskiya, ba batun b'oye b'oye, (Duk da Hausawa na cewa me suna Khadija akwaita da ƙarya🙈) amma ita wannan da sauƙi kam.

Toh NUWAIRAN ayanzu gidan HAIRANAH ta kuma nufa, dan bata san me yasa HEESHAM ya tsani tace zata unguwa ba, duk da fittar tata baifi sau huɗu bane, taje gidan Ramlat sau biyu, taje gidan Hannatu sau d'aya, sai yanzu da taje gidan Khadija take san biyawa gidan qanwar tata...
Amma gani yake ta fiya yawo, dan shi har a zuciyarsa ya Saka sai bayan wata bakwai zai kaita duk inda takeso, amma saboda nacinta haka dai yayi hakuri ya barta, amma gidan iyayen nasu yace shi da kansa zai kaita, wallahi idan taje zasu b'ata, toh NUWAIRA dai bata san duk abin dazai jawo mata matsala dashi, dan haka koda taje gidan Ramlat da Hannatu batayi gigin zuwa gidansu da gun Momy ba, ko Yanzu ma da take akan hanya bata kawo tunanin zuwa garesu ba, tabarsa duk lokacin dayaga dama ya barta..


Tana yin parking a harabar gidansu HAIRANAN bayan ta fitto daga motar tata sai kawai taci karo da MEENATU...
Nan suka tsaya kallan kallo
Da murmushi akan fuskar NUWAIRA tace "Sannu ko, barka da rana, da fatan na sameku lafiya.
MEENATU ta had'iye wani shegen yawu, tace "Yauwa sannu, lafiya lau muke, Ashe kin kusa haihuwa, NUWAIRA tace "Kai haba, yaushe ya fara motsi, ta faɗin mata hakan dayin part na HAIRANAH abinta, dan ita har a zuciyarta Sam MEENATU bata kwanta mata ba..

Dake AHMAD ya siyama ko waccensu mota sati d'aya daya wucce, hakan yasa MEENATUN shiga motar tata, Yau dai ba neman rakiyar Bala direba, dan yanzu baya ma gidan, Saidai idan wata acikinsu bazata iya tuqi ba saita kirasa ya kaita duk inda take so.

Tuqi kawai MEENATU takeyi tana mamakin ganin ciki ajikin NUWAIRA, to ina aikin da malamin HASEENAH yayi mata, bata da wannan amsar har sai sunje gabansa taji me zaice musu.
"tab yau Ƴar uwata akwai jin mummunan labari, ta faɗi hakan abayyane tana me qara gudun motar tata...


HAIRANAH na tsaye a kitchen d'inta wajen ajiyar abincinta, ta zubama duk abincikan ido kasancewarsu d'anye, tana duba wanda zata girka taci ne acikinsu, yunwa takeji amma sam bata san me zataci ba..
Saiji tayi NUWAIRA ta rungumesa ta baya, tana cewa, "Me yake damunki Qanwata, me kike san dafawa da kikazo kika zubama sito ido..
HAIRANAH tayi murmushin jin daɗi tare da juyowa cikin matuƙar murna ta rungume yayar tata tana cewa ƙamshin turaranki ne yasani ganeki da kika tab'a fatar jikina
Nayi missing d'inki my Aunty, ta faɗi hakan tana me Jan NUWAIRAN zuwa falanta
Sanda suka zauna taci gaba da cewa, LA LA LA😳.. Tare zaku aihu da MEENATU, Kai Aunty NUWAIRA irin wannan kyau haka, gaskiya ke kam ciki yayi miki kyau.
NUWAIRA tayi murmushi da cewa, "Yanzu wata amsa zan baki, kin dai san futunan HEE-SHAM, shi ya bani man da mace me ciki ya dace ta shafa sa'ilin da take dashi, ga magunguna kala kala da yake bani yasani gaba saina shasu a gaban nasa, ni har nagani Wallahi, Gaskiya Y'ar uwa Nagode ma Allah daya bani HEE-SHAM, amma fa yana da futuna..
HAIRANAH tace "Gaskiya ne, ba wanda zai ganki baki bashi sha'awa ba, na tuna ranar YA AHMAD ya bani wasu mayuka wai na masu ciki ne, dalilin dayasa naqi amfani dasu qamshinsu tadamin da hankali yake, yanzu haka ma naji ƙamshin d'aya daga cikinsu a fatarki..
NUWAIRA tace "sune, da zaki d'aure ki dinga shafawa zasu qara miki kyau, ki haihu da kyan fatarki, ba sai kinje a wannan kwurarran lokacin ahau yi miki gyara dan fittowa a suna Fes dake ba..
Tace "Toh zanyi qoqarin hakan..
NUWAIRA ta zuba mata ido, da cewa "Me yake damunki ne, naga kin rame, ammafa kinyi kyau sosai..
Tace "Cikin ba irin na farko bane Aunty NUWAIRA, wannan yana bani wahala sosai, komai naci sainayi amai, bakiga yanda hankalin YA AHMAD yake tashi ba, amma dake haka tsarin masu ciki yake, dole yake zuba min ido ba yanda zaiyi, sai aikin bani magunguna kamar wata y'ar kwaya, yace min dai idan yakai wata biyar ko shidda komai zai canja min da ikwan Allah..
NUWAIRA tace "Ikwan Allah, ni ban wani fuskanci matsala ba, Saidai kwad'ayi yayi min yawa, daga nace abu kaza nake so sai nace abu kaza nake so...
Am! naji kince cikin ba irin na farko bane, kin samu ciki kinyi b'arinsa ne har kika samu wani ban sani ba.

HAIRANAH ta waro ido cikin mamaki tace "Wai kina nufin har yanzu HEESHAM bai baki labarin komai ba.
NUWAIRA ta gyara zama tace "aa aa, ba abin daya gaya min wallahi.
HAIRANAH tace "Gaskiya ya cika amini nagari, yanzu dai me kike san ci na dafa miki kisha labari.
Tace "Daga dukkan alamu, baki da zab'in abin da kike san girkawa, dan ganinki da nayi a tsaye nasan tunanin me zakici kikeyi, dan haka bari kigani na had'a mana abin kwad'ayi, kwanta kawai kiga abin dazan had'a mana, badai kina da komai ba. HAIRANAH ta d'aga mata kai cikin matuƙar jin daɗi tace "Saidai abin da baza'a rasa ba.

Aiko NUWAIRA tashi tayi ta shiga kitchen d'in ta fara had'e haden kwad'ayinta, ba wani abu tayi ba face Hana kwalla, Hana kwalla wata abace wacce ake jajjagen kayan gwari a Saka kifi aciki da sinadarin d'and'ano, Sannan a duddun k'ula yayi kamar boll Sannan a kad'a kwai ana sakawa acikin kwan ana soyawa..
Sanda ta gama ta yanka kayan lanbu da saka musu sinadarin d'and'ano kana ta soyasu sama sama ta juye a gefan hana kwallan..

Data sakama HAIRANAH a gaba har yawunta tsinkewa yakeyi, nan suka baje suka cinye abinsu, HAIRANAH tace "Gaskiya Aunty NUWAIRA kin samu ladana, dama ace bai qare ba na qaraci.
NUWAIRA tace "da yawa nayi ai, tunani zaki ba MEENATU ko y'ar aikinki wacce momy ta gaya min ta Sama muku ke da MEENATUN, akwai saura aciki indai baki ƙoshi ba kije ki d'auko tunda basu gani ba, gaba idan kinyi kya basu..
HAIRANAH ta sakar ma NUWAIRA kis a hannu tace "tab, ai ajiyewa zanyi naci anjima, MEENATU kona bata baci zatayi ba, Asiya ko idan tana sha'awa tazo ta had'a..
NUWAIRA tace "Me zaisa MEENATUN baza taci ba..
Tace "Kawai tunanina ne ya bani hakan, NUWAIRA tace "Ammako kina da mugun tunani, idan kawai kinyi niyar bata ki bata bana san kawo mugun tunani akan wanda kike tare dashi, hakan yana haifar da tsana, da kuma rashin yarda, idan kuma aka samu hakan babu batun zaman lafiya kenan, duk abin da zakiyi mata kiyi mata kawai da zuciya d'aya...

HAIRANAH tace, "Toh insha Allah a gaba zan gyara, Sannan magana ta zaman lafiya kima bar batunta, dan babu ita tsakanina da ita, gaisuwace kawai tsakaninmu, idan naganta na gaisheta Sam bana jira saita fara min magana, dan nasan nice qarama, amma bayan haka ba wani batun zaman lafiya...

NUWAIRA tace "Toh duk meya jawo hakan, tace "Hmmm..

Nan ba tare da b'ata lokaci ba HAIRANAN ta bata labarin fad'an nasu, da yanda suka mata da kuma yanda itama tayi musu..
Da farko har idan NUWAIRA ya fara kawo ruwa, daga baya kuma taci dariya. Tace "Kai, amma kin musu aiki da yawa, da a'ce ni sukama hakan kin sun daki banza, dan bazan iya yi musu abin da kika musu ba, HAIRANAH tayi dariya tace, "ke kam dama nasan bazaki iya ba, amma baki da matsala dan HEESHAM zai tsaya miki, dan Asiya ranar taji MEENATU na gayama wata ƙawarta wai HEESHAM har gida yaje ya tsittsinkama HASEENAH mari kafin na zanesu...
NUWAIRA tace "Zai aikata, dan nima ranar kamar zai mareni, danya kamani ina shan qanqara, Sam baya san yaga ina mu'a mula da kayan sanyi..
HAIRANAH tace "Wallahi haka YA AHMAD ma, Sam baya sona da kayan sanyin....

Haka dai suka dinga hirarsu abin gwanin ban sha'awa, toh waye zaice baya san d'an uwansa..


MEENATU ikwan Allah ne kawai ya kawota wajen Arfat me gyaran jiki, tana zuwa tace "Ke qaramar y'ar iska, malaminki shegen malami ne, ga kishiyarki can da ciki..
HASEENAH ta gyara zama da cewa, "Bani da wata kishiya face NUWAIRA, Sannan na dad'e da shafe shafinta, ba ita ba ciki da HEESHAM har iya ƙarshen rayuwa, wallahi HEESHAM nawa ni kad'ai Aunty MEENATU.

MEENATU tace "lalle saiki gyara zancenki yanzu, yana can ya gama kwasar amarci, ya kuma barki da mamaki, dan wallahi ko kaffara bazanyi ba naga NUWAIRA yanzu da ciki acikin gidana tazo wajen qanwarta, idan kuma kina tantama muje shegen malamin naki ya duba miki..

Ai ana kan qarasa wanke ma HASEENAN k'afa ta yafa gyalenta tace "Muje na kore tantama..
Arfat na cewawa ta tsaya a gama wanke mata mana, amma ko kallanta batayi ba sukayi gaba abinsu
Tace "Lalle malamai sune suke ci a wannan zamanin.. Ta fad'i hakan a bayyane tana me kama wani aikin nata..


Suna zuwa wajen malamin nasu bayan yayi dubansa yayi murmushi, da cewa "Da gaske tana da ciki, kuma zata haife abinta lafiya....
HASEENAH taji gabanta ya fad'i tace "ban gane ba, kana nufin yaudarata kakeyi kenan, yace "aini babu batun yaudara tsakani na dake, gaskiya

Please Login or Register in order to submit comment