Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

cin abincin dake gabansa wanda momyn su HEESHAM ta aiko musu shida Dadynsu HEESHAM d'in, kana ya qara nunama Dadynsu HEESHAM d'in Nadamarsa akan abin da suka aikata, aiko Dadynsu HEESHAM d'in ya nuna mishi b'acin ransa, daga baya kuma ya fahimcesa suka fahimci juna..

Ramlat da Hannatu ko da suka dawo suna ganin NUWAIRA tashiga ransu, nan suka rumgumeta bayan momynsu tabasu labarin komai da yanda take agunsu..


HEESHAM ko barinsu asibitin shida Baba Alhaji lallashin Baba Alhajin yahauyi cikin wayo irin nasa, sarai baba Alhajin ya gane yaran so yake ya yafema mamansu HAIRANAN cikin sauqi, dan haka bai kulasa ba..

AHMAD da HAIRANAH ko abin daya faru tsakaninsu shine, bayan kowa ya watse, sam HAIRANAH bata wani damu da cewar wai Baba Alhaji mahaifine ga Maman nasu ba, dama ita kallan farko data masa nan taji hankalinta ya kwanta dashi, dan haka cigaba da kukanta tayi na rashin masoyin nata AUFAN...
AHMAD ya galla mata wata shegiyar harara, yace "kimin shuru anan wajen, wawiya kawai, kirasa wanda zakiso wai sai Arne, wanda Bashi da addinin da zaki d'aga murya kice addininsa ne, kuma yazo a d'an fashi, amma dan tsabagen dabbanci, bayan kinsan hakan kike b'arewa mutane baki kina wani yi musu kuka... Narantse da Allah idan na qara jin kukanki saina fasa bakinki..
HAIRANAH tadalla masa tata hararar da dalla dallan idanta dan ba qaramin haushi ya bata ba tace dashi, "Karka qara kiran AUFAN da Arne, dan kanya mutu sanda ya Muslinta, to wai ma kai ina ruwanka, Ansoshi d'in sai me..😙 taqarashe zancen nata da murgud'a mai baki..
Ran AHMAD ya b'aci, ai HAIRANAH bata ankare ba saiji tayi kawai an dalleta da wani zazzafan mari, Marin da tunda take bata tab'a jin me zafi irinsa ba...
Nan ta fashe da kuka...
AHMAD ya fara cire bell d'in jikinsa yana cewa, "Zaki min shuru ne kosaina farfasa miki jiki...😳

Arayuwar HAIRANAH bata san a tab'a lafiyar jikinta, batu na duka kona zana shiyasa take kiyayewa ko a makaranta ne.. Ko wasa irin na banzan nan ita bata taso da yinsa ba, dan kar'a jimata ciwo, tana san jikinta sosai bata san a tab'a mata lafiyarta, shiyasa take ma mamanta biyayya sosai ita da SABEER, dan sune masu duka agidansu, suna da saurin hannu..

Shiyasa da yanzu taji Marin bazatan da AHMAD yakai mata tagigice, bata qara tsurewa ba Saida taga yana qoqarin cire bell.. Ai ba shiri bayan taji abin dayace, tayi shuru kamar ba itace me kukan nan ba🤣.... Dama shi AHMAD ba zaneta zaiyi da bell d'in ba, duk dai barazana ce, kasancewar yaga bata jin dad'i, amma inda ace lafiyarta lau yanda ya gane itama qanwace agaresa wallahi zaneta zaiyi, kamar yanda yake Zane qannansa idan sunyi lefi..

Ganin hakan yasa ya qara galla mata harara da barin cire bell d'in da yayi niya..
Saiya zauna kan kujera da d'aukar jaridar da Ake ajiyema marasa lafiya yana dubawa
Ita kam HAIRANAH harga Allah ta tsorata dashi...
Sai kallansa take, da ganin rashin imani irin nasa, Yaya zai hanata kukan rashin masoyinta, dan kuma tayi magana ya wani Dalla mata Marin da tunda take bata tab'a jin irinsa ba..
Wannan kallan da take masa shiya bata damar qare masa kallo tsab batare daya sani ba, yana da kyau sosai, irin wannan kyan da kowace mace zataso mallakarsa matsayin mijin auranta..
Can data gaji da kallansa sai tace, "Zanyi fitsari..
Saiya tsaya cak da duba jaridar, ya juyo ya kalleta yaga ta turo baki gaba, bai mata magana ba, ya tashi da niyar cire mata ruwan daya Saka mata, ai yana tab'ata shock yayi ram dasu, tayi saurin janye hannunta a tsorace, suka qurama junansu ido, zuciyarsu na bugawa, can dai AHMAD ya galla mata harara, ba shiri ta miqa masa hannun nata da niyar sakar mai kuka, kamar ya gane dan haka yayi saurin ce mata, "idan kikamin kuka wallahi saina qara baki wani Marin dayafi na d'azu.. Saurin had'iye kukan tayi, ya kama hannun nata, duk da sun kuma jin wani shock d'in hakan bai Sa ya bar cire mata ruwan ba, sanda ya gama cire matan tace, "Nifa bazan iya tashi ba, sanda ya qara hararara kana ya fitta daga d'akin, ya turo mata wata ma'aikaciyar asibitin, tatemaka mata taje tayo alwala tayi sallah, zata kwanta Ramlat yayar HEESHAM ta shigo d'akin, nan suka gaisa, Ramlat tayi mata sannu tace mata momynsu ce taturota, HAIRANAH tace mata amma ita yayar HEESHAM ce ko, da murmushi Ramlat tatabbatar mata, taqara da cewa, "ke kuma yayar NUWAIRA ko😀.. tace mata "aa, ni qanwarta ce.. Ramlat tace, "Amma kin fita giba kad'an haka..
Tace "ai shiyasa Ake cewa ni yayarta ce.
Murmushi Ramlat ta qarayi da fara zuba mata abinci, kad'an HAIRANAN taci ta barshi, AHMAD ya shigo d'akin da niyar mayar mata da ruwan, aiko tana ganinsa ta d'aure fuska da turo baki, sarai AHMAD d'in ya gane ganinsa ne yasata canjawa..
Ramlat ta gaishesa ya amsa kana ya mayarma da HAIRANAN ruwan, still sanda suka kuma jin wani shock d'in a jikin nasu..



HEESHAM yaso komawa asibitin, saiya tsinci kansa da fama da ciwan kai, hakan yasa bayan isha'i yana yin sallah ya kwanta, amma HAIRANAN na ransa...


Mamansu NUWAIRA ma tana yin sallar isha tasa direban momyn HEESHAM ya kaita gidansu...
Mamanta na ganinta ta rungumeta, nan takama qafar mahaifiyar tata tadinga neman yafiyarta, kun san uwa, nan take ta yafe mata..
Bayan sun nutsu Lubabatun ta kwashe komai tagayama mahaifiyar tata...
Nan ko mahaifiyar tata tagaya mata dama tana ganin HAIRANAH tashiga ranta, taqara da cewa Yanzu su tashi suje wajen Babah Alhajin ko Allah zaisa ya saurareta..

Aiko nan taje ta gaida kishiyoyin Maman nata, suka amsa da mamakin ganinta, dansu har sun manta da ita, d'aya ce acikin kishiyoyin maman nata bata gani ba, dama tasan da rasuwarta, kana tadawo sukaje ita da mahaifiyar tata wajen Baba Alhajin.. Hakurin duniya Lubabatu tabashi amma yaqi sauraranta..
Haka tadinga kuka da tara masa kaf y'an gidan suna masu tayata basa hakuri.. Amma Sam yaqi sauraransu, yace shi ya rigada yayafeta daga cikin y'ay'ansa.

Haka dole ta hakura ta koma shashin mahaifiyarta...


NUWAIRA sun kulle da Hannatu, dama sa'annin juna ne, dan haka hira suka dinyi kamar sunsan juna, Hannatu ta d'auko mata hotunansu wai tagansu.
Ta yarda AHMAD abin san kowace y'a mace ne, amma HEESHAM samunsu da wiyar samu yake, haka tadinga kallan hotunan da gane kowa, ahaka har tasan Yaran Kawu Kabiru da yaran Kawu Jamilu, kallo d'aya tama HASEENAH gabanta ya fad'i da ita, nan taji bata san yarinyar, haka tayabi kowa amma taqi yaban HASEENAN, Hannatu tace, "kin yabi kowa amma banda HASEENAH, sam NUWAIRA bata b'oye mata ba tace, "Wallahi Hannatu haka kawai naji yarinyar bata min ba..
Hannatu taja numfashi tace, "Tana da rawar kai sosai, gashi ba ƙaramin san HEESHAM take ba, yana santa baya Santa kowa ya kasa gane masa, dake haka halinsa yake, baya d'aukar abu da wani mahimmanci, shiyasa kowa yake ganin yana Santa kuma qila ya iya Auranta..
Gaban NUWAIRA ne ya faÉ—i haka kawai dan jin kalaman Hannatun, cikin sanyin jiki tace, "Ko kad'an banga dacewarsu a Soyayya ba..
Dariya Hannatu tayi da cewa, "Naji ajikina kamar da gaske ko kad'an HASEENAH bata miki ba, kuma tana da kirki kad'an haka, itadai barta da rawar kai..
Kallan hotunan Ramlat NUWAIRA tahauyi cikin san basar da hirar HASEENAN tana cewa, "Gaskiya Ramlat tafiki kyau sosai, tana kama da HEESHAM..
Hannatu tace, "Dama kinfi yaban HEESHAM dole kice Ramlat tafina kyau, dan dama ita tana kama dashi, yayin dani nake kama da Ya Sadeeq, Ya AHMAD ne kawai bai samu me kama dashi ba acikinmu..
Haka NUWAIRA dai tadinga kallan hotunan tana yaba kowa acikinsu, har suka gangaro kan hotunan gidansu Baba Alhaji, haka kawai taji tana san tsowan..


Washe gari da misalin qarfe takwas da rabi HEESHAM ya dira a d'akin da HAIRANAH take, tana ganinsa tasakar murmushi, daidai nan AHMAD ya shigo d'akin, saita d'aura fuska, murmushi yayi kawai ya dubata dakyau yaga jikin nata da sauƙi, HEESHAM ya kalli AHMAD d'in yace, "Yau za'a sallameta ko, Yace mai "eh, yanzu bata tare da wata matsala.. Ya faɗi hakan da ficcewa, HEESHAM yaje gefan gadan yace, miye na wani d'aure fuska... Tace "Hmm wannan doctor d'in bashi da mutunci..
HEESHAM ya waro ido yace, "Ke Yayana ne fah, kuma yana da kirki sosai..
Tace "Shine jiya ya mareni bayan yasan ba lafiya bace dani, wallahi mugu ne, koshi waye naka saina fad'a..
Yace "amma abin da mamaki, nasan shi da tausayin me jinya, mezaisa ya mareki...
"Waifa Saidai nadena kukan masoyina AUFAN, har yana kiransa da Sunan dabai dace ba, bayan kafin ya mutuwa sanda ya muslinta, haka dai ya gaya min kalamai marasa dad'i akansa, kasan bazan iya jurewa ba, shine dan nayi magana ya dalleni da mari har yana qoqarin cire bell wai zai dake ni, wallahi banda bandah lafiya kuma ina tsoran duka daya gane kuransa..

HEESHAM da Ramlat sukayi dariya a tare, har suna had'a wajen cewa, "Wah, Ya AHMAD d'in ne zai gane kuskuransa, mundai fahimceki, amma zamu baki shawara kadda kibari kizama abokiyar fad'ansa, wallahi Karki zama abokiyar FaÉ—ansa...
HAIRANAH tatab'e baki tace "Baku sanni bane, amma badai yanzu zaku sanni ba, insha Allah zan baku mamaki...
Shuru suka mata kawai suna dariya..
Can HEESHAM ya bata wani rubutu da Baba Alhaji ya bashi ya bata, rubutun kwantar da damuwa ne, da cire abu arai wanda yake damun mutum nan take, rubutun yana shiga jikin mutum ahankali ne saika dinga jin damuwa taka tana fitta daga ranka..
HAIRANAH batayi musun karb'a ba, nan ta karb'a Ramlat ta juye mata a kofi, tasha da bismillah..
Bayan tasha ne, momynsu HEESHAM ta shigo d'akin da kayan breakfast ahannunta, HEESHAM ya karb'eta bayan ta zauna suka gaisheta dukkansu, Momy tashafa kan HAIRANAH tace, "Sannu HAIRANAH, dafatan jiki yayi kyau..
Cikin jin kunya HAIRANAH tace, "Alhamdulillah, tace "Toh masha Allah tana me maida kallanta ga HEESHAM taciga da cewa "Auta ya gidan Baba Alhajin.. Yace "normal momy, tace "nayi kewarka sosai adawo haka pls.. Yace "toh insha Allah gobe..
Tace "Toh Allah ya kaimu, Ramlat maza kuyi breakfast d'in yayanku ya bada sallama, daga nan gidan Baba Alhaji zamu..
HEESHAM yace "naji Hajjiya kakah tana kiran mitin, da alama kamar akan mamansu HAIRANAN take kiran, "Eh akanta ne, Allah yasa asamu kan Baba Alhajin..
Yace "ameen..

Aiko bayan sun gama direct gidan Baba Alhajin sukaje...
Lokacin dangi sun fara taruwa, dan idan akayi kira irin wannan kowa hanzarta zuwa yake...

NUWAIRA tana kusa da Hajjiya kaka wato kakarsu ita da HAIRANAN, Lokacin qarfe 1 da rabi, nan dangi suka dinga rokwan Babah Alhaji yace shifa yayafe maman su NUWAIRA daga y'ay'ansa, dan haka sudene b'ata bakinsu, NUWAIRA tashi tayi taje garesa dama HEESHAM yana kusa dashi tace, "Dan Allah Baba Alhaji dan albarkacinmu kaji qan mahaifiyarmu ka yafe mata bazata ƙara bijirema umarninka ba, dan Allah..
Muryar tata tama HEESHAM dad'i sosai, dan haka saiya shiga qare mata kallo, tana dakyau sosai, tatara dukkan abubuwan da namiji yakeso agun y'a mace, jikinsu dai d'aya da HAIRANAH.. Saidai HAIRANAH tafita kiba kad'an haka..
Shima kallan Baba Alhajin yayi da cewa, "Dan Allah Baba kayafe mata, dan Allah kaji..

Jan numfashi Baba Alhajin yayi da shafa kan NUWAIRAN dana HEESHAM d'in yace "Na hakura jikokina, na yafema maman naku albarkacinku..
Nan cikin murna NUWAIRA ta kama hannunsa ta sumbata tace, "Ina sanka kakana, Kaine zaka zab'amin mijin daya dace dani a family..
A tare sukayi murmushi shida AHMAD dake shima AHMAD d'in ya amsa kiran mitin d'in.. Kana Baba Alhajin yace mata, Zanko zab'a miki wanda ya dace dake.. Da murmushi akan fuskarta tace, "Allah ya qara maka lafiya.. Yace ameen..
Haka taro ya watse kowa dajin daɗin yanda Baba Alhaji yayafe Lubabatun, amma yawancin familyn matan hankalinsu ya tashi ganin HAIRANAH da NUWAIRA, dan yaran sunzo dakyau matuƙa, masu mazaje nan take suka fara Addu'a akan Allah yasa kar d'aya daga cikinsu tazama kishiya agaresu, dan sun san Baba Alhaji ba ruwansa idan har yamaka had'in farko, idan kaga wata a dangin kuma kana santa kana da damar da zaka Aureta, Sannan ba'a masa buri.. Kana da damar da zaka auri hud'u a dangin, shidai bare ne baya san ya shigo danginsa...
Toh gasu NUWAIRA, haka dai yayi hakuri, dan yaran sun shiga ransa sosai..

Dadynsu HEESHAM bama babansu NUWAIRA wani qaramin gidansa yayi yace su zauna tunda yaji sunce kwana hud'u zasuyi, shine yace su bari kawai suyi sati d'ayan dan ayi bikin AHMAD da MEENATU da Sadeeq da Khadija dasu..
Nan sukace toh ba damuwa, Momynsu HEESHAM tace amma NUWAIRA da HAIRANAH awajenta zasu zauna har zuwa Lokacin tafiyar tasu.. Nanma ba damuwa sukace mata..

Sun keb'ance su uku, wato Maman su NUWAIRA da Babansu da Dadynsu HEESHAM.. Inda shi Dadynsu HEESHAM d'in yace cewa, "shawara dama nake san baku, me zai hana kudawo Abuja nan da zama, ina ganin hakan zaisa ran Baba Alhaji yayi masa dad'i, tunda dama shi kasuwar danginsa ne bayaso, yana san yaga zuri'arsa tana dungule waje guda..
Jan numfashi Babansu NUWAIRA yayi, yace "Nima na fahimci baya san kasuwar zuri'arsa, zanyi komai dan ganin farin cikinsa a yanzu, ina san ya sake da Lubabatu kamar yanda ya sakewa da kowa cikin yaransa, yanzu me kake ganin yadace ayi..
Dadyn HEESHAM ya gyara tsayuwa, yace akwai wani gida ajikin gidana, me gidan yayi min tallansa kan yana san saidawa, idan kana so sai namasa magana kuyi cinikinsa..
Nan murna takama Babansu NUWAIRAN yace.. Suje yanzu suyima maganar, Lubabatu tayi murmushi har azuciyarta taji dad'in wannan shawara, haka data gayama momyn su HEESHAM da SABEER NUWAIRA sun nuna jin daÉ—insu..

Haka HAIRANAH da NUWAIRA sukabi momynsu HEESHAM gidanta, ai HEESHAM na ganin hakan ya tattara kayansa dayima Baba Alhaji sallah wai ya tafi gidansu😂 ..
Murmushi kawai Baba Alhajin yayi, ya gane kamar HEESHAM nasan HAIRANAH..

Wannan abu ba ƙaramin daɗi yayima AHMAD ba, dan ya gane wallahi san NUWAIRA ne yayi mai mugun kamu daga kallo d'aya, haka itama NUWAIRA taji dadin haka, zata more ganin HEESHAM san ranta ba tare da tasan me san ganin nashi yake nufi ga ziciyarya ba..


Allah sarki HAIRANAH, tayi hakuri ta yarda AUFAN ya barta har abada, tana dai kuka idan tana masa Addu'a kad'an haka amma da sauƙi damuwar dan bata jita kamar yanda take tunani ba, tunda tasha rubutun da baba Alhajin ya bata, sai take jin AUFAN d'in yana fitta daga ranta, tunda har ta iya zama ayi hira da ita acikin wannan dare, anan itama tasan waye HEESHAM da AHMAD da sauran y'an uwan nata, Saidai itama kallo d'aya tama MEENATU gabanta ya fad'i, nan take ba b'ata lokaci taji bata Santa kwata kwata..


A kwana biyu agidan kowa ya gane shak'uwar dake tsakanin HAIRANAH da HEESHAM.. Lokacin ne kuma hankalin NUWAIRA ya tashi, haka kawai taji bata San ganin HAIRANAH da HEESHAM d'in atare, dan haka yanzu zama tayi tana tuhumar kanta dalili, nan tagano wallahi Soyayyar HEESHAM ce tamata mugun mamu, nan NUWAIRA takasa zaune ta kasa tsaye, me kenan, hmm tafaru ta ƙare, Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un,😭 ita dai a tunani irin nata gani take kamar HAIRANAH da HEESHAM d'in san junansu suke, gashi ayanda take jin HEESHAM d'in aranta kamar bazata iya rayuwa babu shi, sanshi take ƙaunarsa take da gaske, b'ata fatan taga tasamu matsala akan Soyayyarsa..
Shiga toilet d'insu Ramlat tayi tadinga zabga kuka san ranta, bata san tayi rayuwar kishi da ƙanwar tata, gashi shi wanda zatayi danji baisan tana yi ba.. Haka tawanke fuskarta tadawo bed d'in nasu, duk ta wani zama wani iri haka, daga gane me ya faru da ita..
Hannatu tashigo bedroom d'in da dafa kafad'ar tace, "Yana ganki haka kamar kinyi kuka, tace "Kwaro ne ya shigar min idon harnama ciresa.. Tace "Toh sannu, dama momy ce tace kizo amiki kallan ke kad'aice ba'ama ba..
Tashi NUWAIRAN tayi da cewa, "Toh muje..
Haka suka fitto farfajiyar gidan, anan suke a baje daga HAIRANAH HASEENAH MEENATU Ramlat harda yaran Kawu jamilu, matan watoh Haulat da Sakinat duk sa'anin juna ne dasu NUWAIRAN..
Duk an gama musu lallan, saura NUWAIRAN ce kawai..
HASEENAH sai kallan NUWAIRA da HAIRANAH take, tana jinjina kyau irin nasu..
Haka NUWAIRA ta zauna me lallan ta yarfe mata hannun nata, tace bata san tayi mata a qafa..

Toh dake qarfe goma na dare suna da wani faty wanda za'a gabatar na Angwaye da amare kasancewar gobe asabar zaka d'aura Auran. Sai hakan yaba kowa damar yin kwalliya ta kece raini kasancewar ma Anko ne, dinki ne kawai da kwalliya ya bambanta kowa.. Amma duk familyn sunyi anko d'in.
Dama momyn su HEESHAM tana jin ance su NUWAIRA zasukai ayi bikin dasu saita nema musu anko d'in duk kayan bikin ta kira telansu Ramlat ya gwadasu kwana biyu tsakani ya kawo musu kayan..
Shiyasa suma suke cikin anko d'in..
Sunyi kyau sosai dan telan gwanine wajen d'inki..

Wajen fatyn ya had'u over HAIRANAH da NUWAIRA basu tab'a ganin wajen bidi'a me kyau irin wajen ba, kowa ma sun lura yaga kyan wajen.. Haka kowa ya zauna wajen dayaga dama, kayan sha ne burjik akan kowane teburin, Angwaye da amare sunyi kyau sosai, Sadeeq da Khadija kalan kayansu lemon green ne me haske, sunyi kyau sosai cikin shigar, haka AHMAD da MEENATU suma shigarsu iri d'ayance, su kuma Jan Kaya suka saka, irin dafaffan Jan nan me kalan kyau baja fatau ba..

NUWAIRA ta kalli inda HEESHAM yake, yana tare da HASEENAH dasu uku ne a teburin nasu da HAIRANAH, sai HAIRANAN dawowa inda take da alama ta fuskanci HAIRANAN tagane HASEENAH bata san ta zauna da HEESHAM d'in ne,
Dan gashi da HAIRANAH tabar wajen tafi sakewa da HEESHAM d'in, sai wani rawar kai da shigemai takeyi, saikace mijinta, nan ran NUWAIRA ya b'aci sosai bata san lokacin dataja tsaki ba.. Duk sai taji ta tsani HASEENAN.
HAIRANAH tace "Aunty lafiya kike tsaki ke kad'ai.. Kallanta NUWAIRAN tayi Dake itama tana jin d'an haushinta aciki tace, "Lafiya, wani abu ne.. HAIRANAH tatab'e baki tace "aa ba komai.
NUWAIRA ta qara Jan tsaki, sai ran HAIRANAN yad'an b'aci daidai Lokacin HEESHAM ya d'aga mata hannu alamar tadawo dan Allah.. Sai tatashi taje garesan, yace "lokaci d'aya kika tashi da barin nan, gayamin meyasa.. tace "babu komaifa, naje gayama Aunty NUWAIRA abu ne..
Yace da alama kuma abun da kikaje gaya matan bai mata dad'i ba, danga b'acin rai can akan fuskarta, gashi kuma ta shafa miki danga naki ramma a b'ace yake, dan Allah gayamin wane abu ne haka wanda yasa ranki da nata b'aci alokaci d'aya.
Kan HAIRANAH tabashi amsa HASEENAH ta amshe cikin b'acin rai da cewa "ina ruwanka toh da b'acin ran Yayarta bare nata..
Atare HEESHAM d'in da HAIRANAH suka maida kallansu kanta..
Sam dama yarinyar batama HAIRANAH ba, dan haka cikin d'an jin zafin furucin nata tace, "Wata irin tambayace wannan, lefine dan ya nuna kulawarsa garemu, ko ke kad'aice y'ar uwa agaresa...
Amsar dabama HASEENAH haushi dan haka tace, "gani nayi zaqewar tasa tana san yin yawa akanki ne, ke ba budurwarsaba ba komai ba face Æ´an'uwantaka yana san baki kulawar data zarce misali, bayan hakan ya dace ne da wacce take da hakkin mallakarsa matsayin mijin Auranta, lefine dan na tambayesa meyasa shi yin hakan, gayamin hakan yazama lefi ne..
Yanzu HAIRANAH tagane duk me yasa HASEENAH cika da batsewa tun farko, dan haka murmushin tura haushi tayi mata da tashi ta d'auki watarta da kallan HEESHAM d'in tace, "Dan Allah tashi kamin photo da Khadija & Ya Sadeeq amma banda wancan mugun Yayan naka.
HASEENAN ma tashin tayi da kallan nasa tace, "Duk inda zaka ina biye dakai.
HEESHAM yaja numfashi da tashin yana meyi mata murmushi da cewa, "Kin zama jelata kenan, tayi murmushi tace, "komai ma zan iya zama indai akanka ne, shuru yayi mata da kallan HAIRANAH itama ya sakar mata murmushin yana cewa, "ba qaramin haskasu zakiyi ba idan nayi muku hotan, dan kinfisu kyau nesa ba kusa ba, HAIRANAH tayi murmushi zatayi magana HASEENAH tace, "Ina wani kyau anan, kaima ka faÉ—in mata hakan ne dan wasa, amma kasan idan da amare a waje dishashe kyan kowa yake..
HAIRANAH najin hakan tayi gaba abinta HEESHAM yabi bayanta haka ko HASEENAH tabi bayansa,..
NUWAIRA dake kallansu tace y'an iska kawai marasa aikin yi..😂

Dama shi HEESHAM yasan HASEENAH da shegen kishin tsiya, gashi fa shi bai tab'a cewa yana Santa ba, amma dan d'orama kai damuwa tabi duk ta ishesa..

AHMAD ko hankalinsa nakan NUWAIRA Sam baya kan amaryar tasa, tun amaryar bata gane ba har tazo ta gane, ranta ko ba qaramin b'aci yayi ba, nan take taji wata masifaffiyar tsanar NUWAIRA ta kamata, dan kallo d'aya zakama AHMAD d'in kagano Santa yake yi...

Shiko Yaji daÉ—in yanda duk wanda yaje gun NUWAIRAN take d'aure fuska duk da baya sanin me take cema abokan nasa dana qanin nasa yasan bazai wucce cewa tana da mijin Aure ba, dan ya lura magana d'aya zuwa biyu take musu suke barinta.. Hakama Yan uwansu na danginsu..
Ya lura Yarinya tana da aji kad'an haka, Sannan ya gane ranta a b'ace yake, da alama akwai abun dayake damunta..

Agefe guda kuma hankalinsa nakan HAIRANAH, akwai wani d'an uwansu abokinsa Yaro ne ga Baba Kabiru, sunansa Hashim, bashi da hali me kyau ko kad'an, ba ƙaramin san mata ne dashi ba, zina kamar gida take awajensa, ya b'ata yaran mutane bila adadin, AHMAD ne kawai yasan shi da wannan halin, dan fuska biyu garesa, kullum AHMAD d'in acikin yimai wa'azi yake, amma Sam baya sauraransa.. daga yanayin kallan da yakema HAIRANAH yasan so yake ya b'ata tunaninta.. Da AHMAD d'in ya ƙarema HAIRANAH kallo daga sama har qasa wani b'acin rai ne yayi ram dashi.. Dan d'inkin nata ya kamata sosai amma da gyale a jikinta kuma Babba ne, amma ai shara shara ne, ta saka wani takalmi me tsini duk da batayi make-up ba amma tayi kyau sosai, wannan yasa ransa b'aci sosai, aganinsa da hijabi tasaka dole zai b'oye mata surarta, nan haushinta ya qara yawa aransa..
Bayan HEESHAM ya d'auketa hoton ita da Khadija da Sadeeq, had'a ido sukayi ita da AHMAD d'in yako galla mata harara, itama ta galla masa har da murgud'a masa baki,
Dake hankalin HEESHAM na kansu nan ya lura dasu, sai suka bashi dariya, amma yayi murmush, ya lura HAIRANAH zatayi rashin ji kamarsa, amma maganar gaskiya bazaiso tafad'a tarkwan Yayan nasa ba, danya sanshi da saurin hannu..
Bayan sun dawo wajen zamansu wani abokin Yayan nasa AHMAD yazo ya d'agasa wai zasuyi wata magana, sunansa Bashir.
Can wajen hanyar waje yayi dashi wai dan Allah ya shawo masa kan NUWAIRA yana santa dan Allah ya temakesa, HEESHAM yayi murmushi yace mai sufa basa Auran bare, Auran gida sukeyi, yace mai yasani, shidai yamai alkawarin zai shawo masa kanta, ya tabbatar addu'arsa bazata fad'i qasa banza ba, qila daga kansa sucanja sufara Auran baren..
Jinshi kawai HEESHAM d'in yayi yace toh bara yaje ya gwada shawo masa kan nata, ammafa shi ba alqawari yayi masa ba, idan ta amince shikenan idan taqi amincewa gaskiya bazai matsa mata ba..
Yace badamu amma Karya mata magana yanzu dan yaga ranta kamar a b'ace yake, yadai bari sai sun koma gida.. Toh kawai HEESHAM yace mai...

Koda ya dawo baiga HASEENAH awajen ba tabar wajen tunda abokin Yayan nasa ya d'agasa.. HAIRANAH ta kallesa tace, "HEESHAM kasan miye, yace "Aa, tace "wallahi bana san waccar y'ar uwar tamu, takai ƙarshen zancen nata da nuna mai MEENATU..
Ya kai kallansa kan MEENATUN dama shi baya shiri da ita, dan wata ranah ya tab'a kamata a gidansu tana yima wani saurayinta kiss, kiss irin na ma'auratan nan, shiko saurayin natan sai shafa komai na jikinta yake, toh tun daga ranar yaji ya tsaneta, Sam baya santa, haka yaji baqin ciki sosai Ganin sun fara Soyayya da Yayan nasa, shidai bai gayama kowa ba, dan tazo har gida ta roƙesa akan dan Allah ya rufa mata asiri kadda ya gayama kowa wallahi tadena, shidai shuru yayi mata alokacin..
Yanzu ko.murmushi yama HAIRANAH yace, Wallahi Nima ba wani shiri nake da ita ba, amma kaddafa ki kulata da leman fad'a makira ce..
HAIRANAH tace "toh ina ruwa da ita, amma gaskiya bana santa, kasuba yanda take wani riqe Ya AHMAD..
HEESHAM yayi shuru da kallansu yana wani tunani daban

Haka fatin ya tashi anci dai ansha komai yayi yanda ake so, kud'i dai yayi aiki dan taran kana gani na waÆ´anda sukaci suka data kai ne..
HEESHAM sune
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment