Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za'a ganesa, dan haka Maganin kar ayi tofa kar'a fara..😊
Haka yaga mutane suna ta alwala suna shiga masallacin, nan zuciyarsa ta nutsu dajin karatun da akeyi acikin sallar, sai yaji karatun ya masa dad'i, musamman dake suratul alrahaman akeyi..
Shidai koda zaibi wani addini to addinin musulunci zaibi.. Dan alura irin tasa ya lura addinin kamar zaifi gaskiya..

Yana kallo mutane suka dinga fitowa daga masallacin alamar an idar da sallar..
Bayan ya tabbatar kowa yayi gabansa saiya fitto ya zauna akan motarsa yana tunanin kar Baba Alhajin yace mai yabai gansa a masallacin ba, koda yake mutanan da yawa bai zama lalle ya tambayesa ba..
Yana cikin zancen zucin ne HEESHAM da Baba Alhajin suka fitto, nan yaje garesu cikin murmushi..
Babah Alhaji yace, suje falansa dan zaifi gane me yake cewa..
Nan dad'i ya kama AUFAN dan baya so dama yace su shiga cikin masallacin suyi maganar.
Falan da Baba Alhajin yake fad'a a ƙofar gidansa yake, da alama yana zantawa da mutanansa ne awajen, dan falan yana da girma sosai, gashi yaji kafet tako ta ina, sai tum tum da suke baje awajen abin gwanin ban sha'awa..
Falan sai tashin qamshi yake..
Suna zama Baba Alhaji yace da HEESHAM yaje ya kira HAIRANAH tazo..
Aiko nan HEESHAM ya fitta kiranta..
Ya sameta a falon Hajjiyan nasa tana tayata linke kaya, yace "HAIRANAH kike kowa🤔, tace "haka sunan yake, bashi da dad'i ne😃, yayi murmushi da cewa, aina gaya miki tun ranar farko, Baba Alhaji ne yace na kiraki..
Tashi tayi tanama Hajjiya sallama,
Hajjiya tace "amma zaki dawo ko, HAIRANAH tayi murmushi, tace "insha Allah zan dawo Hajjiya..
Murmushi Hajjiyan tayi da cewa, "toh Allah yasa..
Haka suka jero shida ita yana cewa, "garinku biyu ne, HAIRANAH ta kallesa tace "Me kagani, "yace naganki a kano gaki kuma a Abuja, tace "kano mahaifatace Abuja ko gidan Aure na ne insha Allah😃
Yace "Allah yasa..
Daidai nan suka iso falan da Baba Alhajin yake, sai HEESHAM ya koma cikin gidan d'akinsa da aka ware mai..

Babah Alhaji ya kalli AUFAN yace "ina jinka... AUFAN ya gyara zama yace, "Sunana AUFAN, ita kuma HAIRANAH, mun dad'e muna Soyayya shine muka yanke shawarar muyi Aure, sai iyayenta sukaqi, kasancewar ni maraya ne, dan banda kowa, ban san suwaye iyayena ba, kuma wanda ya tsinceni ya raine ni ya rasu shida matarsa, dama bai tab'a aihuwa ba, toh abakin wani amininsa nake jin ni wanene, shi ne da iyayen HAIRANAH suka buqaci in turo da iyayena sai nayi kuskuran tura wasu iyayen a matsayin nawa ban gaya musu gaskigar koni wanene ba, dake iyayenta masu binkice ne anan suka gane way'annan iyaye ba iyayena bane, shine mahaifinta yayi rantsuwa kan bazai aura mata ni ba, toh mu kuma muna san junanmu, azahirin gaskiya idan har bamu zama ma'aurata zamu iya aikata ba dai dai ba, zamu iya aikata abin kunya, shine muka shirya mu gudu a mana Aure a wani wajen daga baya sai muje wajen iyayen nata ko Allah zaisa su hakura su yafe mana. (Rahama Muh'md Rufa'i Nalele tace gaskiya AUFAN ya iya tsari🤔)

Baba Alhaji yayi murmushi, da tsaida kallansa akan HAIRANAH, haka kawai yarinyar ta shiga ransa..
Haka kawai yaji yana santa, ba wacce tafad'o masa arai sai ƴarsa Lubabatu data gudu itama taje can da saurayinta, tana da rai bata da rai oho bai sani ba, yasan yanzu iyayen HAIRANAH suna can cikin tashin hankalin ina take...
Kallan AUFAN yayi da cewa, "Zan d'aura muku Aure sanadin wannan furucin daka min kan indai baku zama ma'aurata ba zaku iya aikata ba dai dai ba, na fahimceku, amma zanso HAIRANAH takira iyayenta tace musu tana lafiya lau a inda take, yanzu haka kuna wajena zan d'aura muku Auran daga baya zakuzo garesu, Saidai Baku kad'ai zakuje garesun ba, dani zakuje, idan kunyarda da hakan zan d'aura muku Aure yanzu, sai kuje gobe kudawo kukaini wajen su iyayen HAIRANAN, dan su tabbatar da auranku, Sannan suyi hakuri da qaddarar da Allah ya rubuto muku..

Cikin jin dad'i AUFAN yace "nidai na yarda.. Ya kai ƙarshen zancen nasa da kallan HAIRANAH wacce itama cikin jin dad'in tace "Nima na yarda..
Baba Alhaji yace "Toh kira iyayen naki.. Ya Faɗi idansa akan HAIRANAN, nan babu b'ata lokaci ta zaro wayarta cikin jakarta da kunnata tafara laluban Num na mamanta..

Lokacin hankalin iyayen nata a tashe yake, dan da asuba da NUWAIRA tatashi bata ganta ba, Sam bata damu ba, tunaninta tana d'akin mamansu ne, sanda gari yayi haske taje gaida iyayen nata suke tambayarta ina HAIRANAH, nan take ce musu ai ita tunda tatashi da asuba bataga HAIRANAH ba..
Habawa nan mamansu tatashi hankalinta tashe ita da Baban nasu suka hau kiran HAIRANAH suna dubata lungu da sak'o na gidan, amma ba HAIRANAH ba alamarta, SABEER ya fitto yana cewa ina HAIRANAN take, nan NUWAIRA taqara gaya mai abun data gayama iyayen nasu..
Shuru yayi yana tunani, can yace shidai daya tashi da asuba zaije masallaci yaga gida a bud'e sai yayi tunanin ko Babansu ne ya bud'e gidan yayin futarsa masallaci..
Cikin damuwa Baban nasu yace shima Ganin ƙofar yayi a bud'e sai shima tunaninsa ya basa ko SABEER d'in ya rigasa fitta zuwa masallacin ne...
Nan dai suka kasance cikin damuwa suka hau kiran number na HAIRANAH amma a kashe, can NUWAIRA tabasu wasiqar data ga HAIRANAN ta rubuta wanda tun tashinta bata lura da ita ba sai a lokacin. Ga abin da HAIRANAN tace..

_Ciwan so Baban ciwo ne, ina sanku iyayena, ina ƙaunarki Y'ar uwata da d'an uwana, amma kuyi hakuri zanbi san zuciyata dan ni nasan yanda nake ji araina, zanbi AUFAN Muje can wani waje ayi mana Aure, Allah ya ƙaddara saduwarmu Ameen_

Suna jin hakan mama tayanke jiki tafad'i, Babansu ko wani zazzafan gumi ne yaketa qaryo masa, daƴar da siɗin goshi suka samu maman tafarfad'o, aiko ba abin data hauyi sai kuka, lallashin duniya NUWAIRA da SABEER sunyi mata amma abun yaci tura, nan dai tayi shurun dan karan kanta da kwashe komai na tahirin rayuwarta kaf tabama NUWAIRA da SABEER d'in labarin, mahaifinsu najinta...

Hankalin NUWAIRA da SABEER ba ƙaramin tashi yayi ba, nan hawaye ya zuboma NUWAIRA tace, "Amma a gaskiya Mama bakiyima iyayenki adalci ba, gujema iyaye babbar masifa ce ga y'ay'ayensu, gashi Allah ya nuna miki iyakarki tunda ransu kafin mutuwarsu..
SABEER yace, "maganar NUWAIRA gaskiya ce mama, idan har kina san kiga dai dai tofa sai kije kin bama iyayenki hakuri kin nemi gafararsu sun yafe miki, idan ba haka ba bayan HAIRANAH ni da NUWAIRA wata qila muma tamu jarabtar da Allah zai nuna miki akammu tana gaba, iyaye abin abisu ne, ba abin aqi binsu bane...

Cikin damuwa Babansu yace, "nine Babban me lefi kudena ganin lefin mahaifiyarku, da'ace tun farko ban kawo shawarar yin hakan ba da mahaifiyarku tayima iyayenta biyayya, dan Allah Y'ay'ana kuyafemin banyima kakanninku adalci ba, dan sun haifi y'arsu cin ciyar da ita sun tufatar da ita sun bata ilimi da kulawa, sun nuna mata ƙauna, amma saboda ni duk tamanta hakan ta guje musu taqi bin umarninsu kan abin da suke so, wallahi nine me lefi ba kowa..
NUWAIRA ta kalli Baban nasu tace, "Baba wannan qaddarace, kuma kowa da irin tasa, da bakuyi hakan ba da ba'a samemu ba, da bakuyi hakan ba qila da atiti zaku samemu, dama Allah ya ƙadarta muku hakan ne dan yazama izzina ga wasu masu ishin haikata irin hakan..

Toh me karatu suna cikin wannan halin ne kiran HAIRANAH ya shigo wayar mamanta, SABEER na gani ya kalli iyayen nasu cikin farin ciki yace "ga HAIRANAH ta kira..
Nan cikin sauri Baban nasu ya karb'i wayar da d'aukar kiran yana me bud'e maganar afili dan kowa yaji me zatace...

Haka anan wajen Baba Alhaji itama HAIRANAN bud'e maganar afili tayi dan AUFAN da shi suji me iyayen nata zasuce mata..

Tace "Hello Mamana..😄 cikin sanyin murya, Babanta yace "HAIRANAH kina ina, cikin jin kunyar Baban nata tace, "Baba ina garin Abuja, dan tun cikin dare muka sauka a garin, Baba ina san AUFAN yanzu gamu wajen Baba Alhaji wani tsowo me fahimta ya yarda zai d'aura mana Aure nida AUFAN, amma yace saina kiraku na gaya muku ina cikin kushin lafiya, kana ya d'aura mana Auran yanzu, Sannan idan Allah ya kaimu gobe muzo tare dashi nan garin kano dan munemi afuwarku kukuma yarda cewa da aure tsakaninmu, dan Allah baba mama aunty NUWAIRA Ya SABEER kuyafemin, ni kad'ai nasan ya nake jin AUFAN araina...
Da damuwa Baban nata yace "na fahimceki HAIRANAH amma kidawo gida a d'aura muku auran kinji...
HAIRANAH tayi murmushi tace "aa Baba, ni nasan halinka, tunda kayimin rantsuwa bazaka auramin shiba nasan yanzu ma bazaka d'auramin shi ba..
Cikin sauri Mamanta ta karb'i wayar a hannun Baban nasu tace, "HAIRANAH Y'ata.. Cikin sauri HAIRANAH tace "Na'am Mamana.. Tace "kidawo gida wallahi za'a d'aura miki Auren dashi.. HAIRANAH tace, "Nifa mama nafi yarda da Baba Alhaji fiye daku, wallahi idan har igiyar Auran AUFAN bata hau kaina ayau ba bazan dawo gareku ba, dan nasan halinki duk abin da baba yace kiyi shi kikeyi, dan haka bazaki min wayo nadawo gida naji kawai kun d'aura min Aure da wani ba AUFAN ba, dan haka sai anjima gobe zamuzo da Baba Alhaji insha Allahu, kimma sanshi mana Mamah, Babban mutumin nanne fa, wanda kike yawan ce mana mutumin arziqi ne, wanda kike kiransa da Alhaji Muhammad me gwala gwalai,😄 hmmm sai gobe bye bye Mamana.. HAIRANAH ta kashe wayarta gabaki d'aya.. Da kallan Baba Alhaji tace "Baba kaji yanda mukayi dasu..
Shuru yayi mata, zuciyarsa na gaya masa kamar yasan me muryar mahaifiyarta, amma ya share yace, "naji komai jikata, yanzu zan tara mutane na d'aura muku Auran, kuma ni zan bada sadaki..
Nan murna ta kamasu, musamman AUFAN dan ba qaramin jin dad'i yayi ba, nan qarin ƙaunar HAIRANAH taqara shiga ransa, yana Santa da gaskiya👌🏻...

Cikin rashin sani Baba Alhaji ya Tara mutane a Lokacin ya d'aura Auran AUFAN wanda yace ainihin sunansa Muhammad😨.. Haka ya d'aura Auran Muhammad AUFAN da FATIMA HAIRANAH Suleiman..😭 akan sadaki duba hamsin..


Bayan an d'aura Auran ne, Baba Alhaji yace HAIRANAH ko zata kwana a gidansa idan AUFAN d'in Bashi da gida.. Nan AUFAN yace mai yana da gida nasa nakansa, zasuje gobe sadawo..
Baba Alhaji yace mai to ba damuwa amma suje da HEESHAM yaga gidan nasu.

Aiko haka akayi, dan da HEESHAM sukaje gidan, Ashe gidan AUFAN d'in ma a bayan layansu su HEESHAM yake, ma'ana gidan iyayen HEESHAM..
Dan suna d'auko hanya HEESHAM yace "Ashe a bayan layinmu gidan naka yake..
Da mamaki AUFAN yace "Kana nufin gidan iyayenka, HEESHAM yace "Yes..

Bayan HEESHAM yaga gidan yayi musu sallama zai tafi, haka kawai AUFAN ya tsinci kansa dasan karb'ar numbar HEESHAM d'in, haka ko HEESHAM ya basa numbarsa shima ya karb'i tasa, har HAIRANAH nacema HEESHAM d'in KAIMA sunanka dadad'i😄, murmushi yayi mata kawai, danshi harga Allah haka kawai yake jin babu dad'i aransa tunda yaji an d'aura auranta da AUFAN d'in, kuma yana jin gabansa na fad'uwa alamar kamar wani abu zai FARU da auran nasu.. Haka dai ya qara yi musu sallama ya koma unguwarsu Baba Alhaji yana gayamai yaga gidan Ashema a bayan layinsu yake, Baba Alhajin yace to madallah..



Abun da AUFAN bai sani ba shine, akan idan ogansu aka d'aura Auran nasa da HAIRANAN.. Dan labari yaje masa kuma yayi rantsuwa ba abin da zai hanasa kashe AUFAN d'in acikin wannan dare.. Dan babu Yaran dayayi mai muguwar yaudara irin AUFAN d'in...





Iyayen HAIRANAH ko suna jin Sunan wanda ta ambata da cewar shine zai d'aura mata Aure da AUFAN, hankalinsu ya qara tashi, shine kan Maman nasu tayima HAIRANAN magana ta kashe wayar, aiko nan imani ya qara shiga zuciyar iyayen nata, cikin zubar hawaye NUWAIRA tace, Baba mama kungani ko, da Allah ya tashi turata saiya turata wajen mutumin da kuka guje masa, wannan kad'ai ya qaramin imani araina.
Mama ku shirya kawai muma mu shirya kayanmu muje abujan yanzu, in yaso komai ya faru acan d'in. SABEER ya tari ƙarshen maganar NUWAIRA da fad'in hakan yana me kallan iyayan nasu.
Mama tace "ba matsala amma mu bari sai gobe, saidai zan kira Babban Yayana Ummar kan ya tsaida Baba Alhaji karya tawo dan musamu mu sameshi karya tawo mu kuma mun bar na..
NUWAIRA tace "Yauwa mama, nan mama ta lalubo number na Babban wanta Ummar wanda tunda ta gudu bata tab'a kiransa ba, amma duk tana d'auke da numbers d'insu.

Lokacin Ummar yana d'akinsa ya dawo daga ma'aikatarsa kenan dan baya jin dad'i ne, matarsa ma bata san ya dawo ba, danta kofar baya ya shiga gidan, shine Mahaifi ga HEESHAM...

Ɗansa na farko shine AHMAD, sai Sadeeq wanda ita Lubabatun ta raina lokacin suna ƙanana kafin ta gudu, bayan ta gudun ne ya qara haihuwar Ramlat itama tana da shekara uku ya qara haihuwar Hannatu, sai HEESHAM d'an autansa. Ya kama shi dai yaransa biyar kenan a duniya, kuma bai qara Aure ba dan har yanzu yana tare da matarsa y'ar uwarsu Aisha.. Wacce yaran nasa suke kiranta da Momy.

A kira na biyu ne ya d'auka yana cewa, "Assalamu'alaikum..
Cikin kuka mamansu NUWAIRAN tace, "Yaya Ummar..
Shuru Ummar yayi dan shidai bazai tab'a mantawa da muryar Lubabatu ba, cikin fad'uwar gaba da tashi daga kwancen dayake yace da ita, "Lubabatu, da Lubabatu nake magana...
Cikin kuka sosai mama ta face majina dan jin wata sabowar ƙaunar d'an uwan nata tace mai, "Wallahi nice Yaya Ummar, dan Allah dan annabi kayafemin, nasan kafi kowa ƙaunata acikinku, shiyasa kai nafara kira ayanzu, abin dana shuka shina girba, nan batare da b'ata lokaci ba ta kwashe komai tagayamai, da yanda suka gudu da yanda itama HAIRANAH tagudun musu.. Da Auran da Baba Alhaji zai d'aura mata, duk sanda ta gaya masa komai, nan ko ƙaunar qanwar tasa taqara kamasa, sai taqara dace masa "dan Allah Yaya Ummar kasan yanda zakayi ka tsayar da Baba Alhaji daga zuwan dazaiyi garemu gobe, dan inasan mu Muje mu samesa ne, wallahi Yayana nayi nadama sosai kan abin danayi masa..
Yace "Karki damu ƙanwata, zanja hankalinsa, amma goben kuzo da wuri Allah ya kawoku lafiya, tace mai "Ameen Nagode..
Haka Dadyn HEESHAM ya ajiye wayarsa da godema Allah dazai dawo musu da qanwar tasu..
Hakama Mamansu NUWAIRAN yau takasance cikin farin ciki gobe zata kasance da iyayenta da kuma danginta...

Tun a Lokacin NUWAIRA tafara had'a kayanta, dan ita Allah yayita dasan taga tana da dangi, Ashe ko tana dasu.
Haka SABEER yakira Sadeeq da Anwar wasu abokanayensa way'anda sukayi skull tare, dake a abuja SABEER yayi karatun nasa su kuma suna zama a Abujan ne yace dasu su shirya karb'arsa gobe yana nan zuwa garesu...





Bayan futan HEESHAM AUFAN rungumar HAIRANAH yayi cikin so da ƙauna, yace "nayi miki alqawari zan rik'eki da amana, dan babu abin dazai kauda tunani akanki tunda kin bani gaskiya da amana..❤
Tace "karka damu dama haka Allah yake ikwansa, sai kaga ya had'a bayinsa cikin Soyayya kuma a lokaci qanqani, karka manta had'uwata dakai da Soyayyarmu da Auran namu duk bai wucce wata biyu ba idamma mun kai..
Nidai fatana ka rike alqawarin nan da fahimmanci, idan kaci amanar Soyayyata zan barka da Allah..
"Har abada bani bacin amanar Soyayyarki..
Zame jikinta tayi tana murmushi jin furucinsa tace, "Ya kamata muyi sallah ko, kaji ana kira..
Sanda ya sosa qeya kana yace ni zanje nayi a masallaci, maza ki hanzalta kafin wuccewarta..
Nan ko ta haura sama inda ta kwana jiya tana cemai kadawo da wuri na fara jin yunwa, Toh yace mata..

Bayan ta idar sai gashi ya shigo room d'in yana ce mata, "tashi Muje muci abinci a waje.. Tace "bazaka kawo na girka ba, "yace "wane ni dasa amarya aiki, idan dai kina jin k'iwar fitta ne yanzu nasa aje a siya mana abin da muke so...
Da murmushi tace "Baka sanni bane dasan yawo, aikona gaji haka zan tashi nace maka muje.
Yace "tofah, gashi ni kuma me kulle ne, dan bana san naga mace ta cika yawo..
Tashi HAIRANAH tayi da d'aukar gyalanta tace "kaga na d'auki gyalena tashi Muje tunkan kace kafasa..
Murmushi yayi, ba shakka zaiji dad'in mu'amalat da yarinyar dan tayi masa💯✔...
Haka sukaje wani Babban wajen cin abinci sukaci abin da ransu ke so, yakaita wani wajen shaqatawa dan da gaske ya gane yarinyar tana san Yawo da yawa, ana gab da kiran sallar isha'i suka dawo gidan nashi..
Nan cikin sauri HAIRANAH ta haura sama yin sallah..
Shi kuma yaje farfajiyar gidan nasa ya tsaya wai anufinsa shima yaje tasa sallar dan karta ganesa.
Sanda ya bata lokaci me tsawo wanda yake da tabbacin ta idar kana ya kulle gidan nasa cikin rashin sani ya kulle da ogansu acikin gidan harda abokan aikinsa bai sani ba..

Yana shiga falan nasa yaji saƙo ya shigo wayarsa, yana dubawa yaga MTN ne, kuma gashi Azeez ya kirasa kusan 29 miss call..
Yace "what 😳 Azeez da kira haka, saiya koma duba sak'o ganin guda 4 ne anan ma yaga bayan MTN duk Azeez d'in ne me sauran.. Nan ya fara karanta sakwan nasa cikin sauri.. Ga abin daya rubuto mai

_AUFAN karka shiga gidanka oga da abokan aikinmu muna cikin gidanka, yaji komai na Auran ka da HAIRANAH, ina qaunarka AUFAN amma magana ta gaskiya banine na gayama oga zakayi Aure ba, bansan ya akayi yaji ba, nidai ya kirani Sanda naje nagane mitin ya kira, Ashe akanka ya kira mitin d'in, ina ta kiran wayarka a Lokacin dan kaji abin da yake tsara mana dan kasan bazan iya kiranka a gabansa ba, amma baka d'auka, yanzu wannan message d'inma da nake maka inayi ne kad'an kad'an a matsayin game nake yi dan hankalinsa yana kaina, pls AUFAN ka duba sak'ona pls ka ankare.._

Tun kan AUFAN Yakai ƙarshe a karanta sak'on gumi ya fara tsatstsafo masa..
Nan cikin tashin hankali ya kalli saman falan nasa inda HAIRANAH take kana ya maida kallansa ga falan nasa ya ƙarema ko ina kallo, ba shakka ogansu yana gidan, dan ga qamshin Maganin da bokan ogan nasa suke bashi,
Ba wacce take ran AUFAN a yanzu kamar HAIRANAH, yasani a rashin adalci irin na ogansu zai iya had'awa harda ita ya kashesu tare, gashi ba bundiga a jikinsa...
Nan hankalinsa ya qara tashi, kan yayi wani cikakken motsi sai ganin HAIRANAH yayi tana gangarowa daga saman lenan falan cikin kyakkyawar shigarta ta atamfa riga da siket, tun daga nesa yaje jiyo qamshinta, nan ya lumshe ido hawaye ya zubo masa, bai tab'a nadama a rayuwar kan fashi da makami ba sai yau..
Ogansa da yake kallansa yayi murmushi dan ya gane AUFAN d'in yasan suna gidan ayanzu, kuma a cikin yaransa ne wani ya gayamai a message ba shakka Azeez ne. Yana gama wannan tunanin ya fitto daga wajen dayake a b'oye, yana tafa hannu, da cewa "sannu AUFAN, Ashe kayi Aure, ya fad'i hakan da zama akan d'aya daga cikin kujerun falan...
Gaban HAIRANAH ya fad'i Ganin ogan nasu, da ganin da tayi mutane suna ta fitowa daga kowane lungu da sak'o na falan, ga bindigogi a hannayensu, haka Suka zagayesu, cikin matuƙar razana HAIRANAH taje ta rungume AUFAN tana cewa Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un me yake faruwa AUFAN, suwaye way'annan, meyasa kake hawaye, me yake faruwa ne, takai qarshen zancen ta zubo da hawaye dan ta tsorata sosai..
Cikin kuka AUFAN ya qara rungumeta kana ya jata zuwa kan d'aya daga cikin kujerun falan.. Ya zaunar da ita, ya durƙusa da kama hannayenta yayi kuka yayi kuka sosai😭 yana me sunbatarsu, hankalin HAIRANAH ya qara tashi sosai, dan yaqi ce mata komai sai aikin kukan da yake mata..
Can dayaga ta qara volume d'in kukanta sai ya tsaida nasa yahau share mata nata, kana yace "HAIRANAH ni ba musulmi bane, ni Arne ne, dan bani da addini, ni ba mutumin arziqi bane dan ni d'an fashi da makami ne, Lokacin da kika shiga cikin rayuwa ta kice mace tafarko dana fara yima wani so wanda yake dai dai da MASIFAR SOH,.. Bana qarya dan ina da gaskiya amma akan ƙaunarki nafara qarya, ki yarda dani na aureki ne kawai dan so da ƙauna..
Nan AUFAN ya kwashe labarinsa na gaskiya bai b'oye ma HAIRANAH komai ba? ya gaya mata, kana ya qara mata da cewa, "HAIRANAH zan musulinta dan ƙaunar da nake miki ina san idan ogana ya tashi kasheni ya kasheni ina cikin addininki, dan Allah ubangijinki ki musulintar dani HAIRANAH..😭

Ai HAIRANAH najin kalaman AUFAN tatashi hankalinta ya bala'in tashi, zuciyarta na bugawa tatashi tana cewa "komai ya faru dani ni HAIRANAH, Dan ba labari Ake bani ba, azahi nake jin komai da ganin komai dan gashi YA FARU AKAN KAI NAH🙆🏻... na shiga uku ni HAIRANAH..😭

AUFAN ya qara matsawa gabanta yace "Lokaci na qurewa HAIRANAH, dan Allanki ki musulintar dani...
HAIRANAH ta kallesa ƙirjinta nayi mata zafi, ta dafe wajen, ta koma ta zauna kan kujerar, tace "karka musulunta danni AUFAN, ka musulinta dan Allah badanni ba, dan shi musulinci ba haka yake ba, idan mutum zai shigesa shiga yake dan Allah da gane cewa addinin musulincin addinin gaskiya ne..
Yace "dama na dad'e da gane hakan HAIRANAH, dan haka musulintar dani dan nasan bazasu barni ba, duk inda zani sai sun bini sun kasheni, basu da imani sam..
Numfashin HAIRANAH nayin sama sama tace, "kace Ashhadu allah'inaha'illallahu, "yace "Ashhadu allah'ilaha'illallahu, tace "Wa ash'hadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu, yace wa ash'hadu anna Muhammadan abduhu warasulullahu.. Tace "kace kasheda babu abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma annabi Muhammadu manzansa ne, yace "na sheda babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma annabi Muhammadu manzansa ne..
Murmushi HAIRANAH tayi, tace "ka shiga musulinci AUFAN, tana faɗin hakan ta rushe da kuka me tab'a ZUCHIYA tana meci gaba da cewa wallahi YA FARU AKAN KAINA BA LABARI AKE BANI BA..

AUFAN Yayi murmushi da kallan ogansa ya kalli Azeez wanda fuskarsa ta jike da hawaye, abin da AUFAN bai sani ba shine duk abin da HAIRANAN take gaya mai shima yana fad'a aransa, haka kawai imani ya shiga ransa lokaci d'aya yaji kuma ya yarda da musulinci lokaci d'aya...

AUFAN ya qara yin murmushi yace, "bazanji komai ba idan zaka kasheni oga, amma karka tab'a HAIRANAH..

Ogan nasu ya bushe da dariya yace, "har ita saina kashe AUFAN...
Ai kan AUFAN yayi magana Azeez yayi saurin hanb'are na hannun damar ogan nasu ya kwace bundigarsa, tare da saurin wurgama AUFAN bundigar, ai cikin sauri AUFAN ya cafke bundigar da saurin tashi yana nuna ogan nasu da ita..
Saiya kasance Azeez tabayan ogan nasu yana nuna sauran abokan aikinsu da bundigarsa, shi kuma AUFAN yana nuna ogan nasu da bundigar da Azeez ya wurgo masa..

Ogan nasu baiyi mamakin hakan ba, dan yasan dama bakinsu d'aya, kuskure dai yayi na barin Azeez bai kashesa da wuri ba, kamar yanda yake daniyar yi bayan ya kashe AUFAN..

Cikin sauri AUFAN yace da abokan aikin nasa kowa ya yar da bundigarsa kafin ya kashe ogan nasu. Cikin sauri ko suka sake bindigogin nasu qasa...

Nan yace su koma can baya su kwanta suka kwanta, ya d'auke bundigar ogan nasu kana yace HAIRANAH tatashi subar gidan haka HAIRANAH tatashi zuciyarta nayi mata zafi ita da Azeez suka ficce daga falan, AUFAN yabi bayansu a hankali cikin ankarewa da abokan aikin nasa, haka ya ficce daga falan yaja kofar..
Aiko yana fitowa yayi waje da gudu danshi kwata kwata ya manta ogansa baya Yawo da bundiga d'aya a jikinsa, sai yanzu ya tuna, dan yana juyawa baya yaji tashin ogan nasu Yana cewa "Kayi kuskure AUFAN,

AUFAN yana fittowa ya d'auki HAIRANAH kamar wata baby suka dinga sheqa gudu shida Azeez, dan idan suka tsaya shiga mota dole ogan nasu zai cimma burinsa akansu..

Dake HAIRANAH tana kallan bayan AUFAN nan taga ogan su AUFAN d'in ya fitto daga gidan da seta wata bundigarsa zai sakarma AUFAN aka🙆🏻, ai ba shiri ta kwalla wani uban ihu wanda duk wanda yake cikin unguwar Sanda yajita...

AHMAD Yayan HEESHAM wanda yake kan hanyarsa ta zuwa gidansu cikin motarsa wanda dawowarsa kenan daga asibitinsa... Kansa ne yaji ya Sara masa jin muryar HAIRANAH? gaskiya yaji muryar tata har cikin ransa hakan ya haifar mai da rintse idansa cikin sauri dajin muguwar fad'uwar gaba, wacce itama tasashi dafe ƙirjinsa da d'ayan hannunsa wanda baya kan matuqin motar tasa..
Har wani gumi ne ya fara tsattsafo masa... Yana bud'e idan nasa. Ya sauke akan HAIRANAH wacce ya ganta d'auke a hannun AUFAN, dai dai nan kuma motarsa ta tsaya cak akan layin dasu AUFAN din suke wanda baifi tafiya kad'an motar zata

Please Login or Register in order to submit comment