Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

momyn sai yace da HAIRANAN "Amma ke wawiya, akan me zaki gayama momy hakan, yanzu kowa zai gane cewa kina san Ya AHMAD..
Shuru HAIRANAH tayi da zubama HEESHAM ido, saiya galla mata harara yaci gaba da cewa, kin kwafsa wallahi..
Nan kwakwalwarta tahau caji, can cikin tsoro ta waro ido tace "Wallahi bana sanshi, qaryane ba sanshi nake ba, na shiga uku ni HAIRANAH, me kake nufi ne HEESHAM, shikenan ni Saidai na dinga san mutane ni bazan samu wanda yake sona ba, gaskiya ba haka bane, AUFAN shine wanda naso, amma Ya AHMAD ba sanshi nake ba, dan Allah HEESHAM karka qara faɗin hakan wani taji.. Nidai yazu kaban mafita kawai...

HEESHAM ya ƴalƴale da dariya da duba falan da kyau yaga dai ba kowa da zai jisu, sai yace "Wallahi K'awata san YA AHMAD kike, kinsan dai bazan rantse miki akan ƙarya ba, kuma momy ta gano ki, harshi uban gaiyar, dan yajiki yanzu haka, mafita d'aya ce karki kuskura koda wasa idan akace za'a had'aki Aure dashi ki yarda, ki barshi sai yazo da kansa yace miki yana sanki tukunna, kuma shima saikin ja maza aji, saikin gwara kansa..
Ai nan take gumi ya tsattsafo mata, taji kanta ya sara, tace "Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un, tawa kaddarar kenan ni HAIRANAH, san mutanan da basu fara sona ba, yace "Zan d'oraki akan hanya, karki wani damu kinji, tace "Toh amma yanzu ya za'ayi, Yace "Idan momy ta fitto karki nuna mata wani abu najin kunya, dan ayanzu ta yarda kina san Ya AHMAD d'in, amma ke kanki baki sani ba, toh azauna a haka, karki kuskura ki nuna mata kinsan tasan kina sanshi ta hakan ne shirinmu zaifi tafiya..
Nan takama hannun HEESHAM d'in ta sakar mai kiss tace "Nagode aboki, yace " Karki damu ina dare dake, yanzu zo mu haura sama wajen baranda kisha iska, toh tace mai, nanko suka haura saman tanan cikin falan..


AHMAD ko kallan momy yayi da murmushi yace "Menene momyna..
Tace "Akwai matsala AHMAD, ai kaji yanda mukayi da HAIRANAH, yarinyar sanka take yanzu ya za'ayi.
Yace "Ai momy nima ina santa, danni na fara santa ma kafin ita tasoni... Momy taja numfashi tace, "kuma sam bata gane cewa sanka take ba abin gwanin ban tausayi, ina san yaran Lubabatu dan nunamin qaunar da tayi tunda na Auri mahaifinku, ita ta raineka AHMAD kai da Sadeeq wallahi ina santa sosai.. Amma bani san tashin hankali da fitinar momysu MEENATU...
AHMAD ya qara yin murmushi yace, "Magana ta gaskiya momy ina san HAIRANAH sosai, kuma banqima yanzu mutare da ita agidan nawa ba inda ace za'a d'aura min Aure da ita ayanzun.. Naje na gayama Baba Alhaji cewar ina santa ai, kuma ya bani damar zuwa na samu Soyayyarta, Karki damu kanki da wata momynsu MEENATU momy, dan bazata hana Allah ikwansa, amma Auran HAIRANAH kam idan har ina da rai ba makawa agareni idan Allah yaso..
Momy taqara Jan mufashi tace Allah ya tabbatar da alkairinsa, kaidai ka kulamin da kanka, Sannan kayi hankali da MEENATU, danna lura tana da kishi sosai, karka gaya mata cewa kana san HAIRANAH, kayi mata shuru kawai idan Allah yayi matarka ce ni da kaina zanje na mata magana..
Yace "Angama momy, yanzu bara muje naji muryar mamansu HAIRANAN kamar nan take nufowa, "Eh dama
Tare zakuje can gidan nakan ai, yace "Ayya Toh bari muje, tace "toh Allah ya kaiku lafiya, nan suka fitto a tare, AHMAD ya gaida mamansu HAIRANAN ganin ta shigo falan, aiko ta amsa cikin kulawa sai ya fitta, momy ta kalleta itama suka gaisa kana tace bari suje tunda taga duk sun shirya a kintsansu suke, HAIRANAH ce dai da HEESHAM taga kamar basu da niyar zuwa danta hangosu a baranda zaune, momy tace mata ai basa shiri da MEENATU ne shiyasa sukace basu ba zuwa gidan nata, tace kaji shirme, bayan ba zama zasuyi ba, kawai ganin gida ne, toh Allah ya kyauta musu, momy tace ameen Sannan tafitto..


HAIRANAH na ganin fitowar kowa taja tsaki da bugar kafaɗar HEESHAM tace, "Kalli kowa acikinsu sai murnar zuwa yake amma banda Hannatu, HEESHAM yace "Da kuma mutuniyar taki ba, kalleta da kyau sai cika take tana batsewa ran nan nata a b'ace, HAIRANAH tace "Na lura da ita ai tuntuni, shegiya ni ina ruwana da ita, kalli wani bakinta sharb'eb'e dashi, kwata kwata basu dace da juna ita da Ya AHMAD d'in ba..
HEESHAM yayi dariya sosai yace, "ga gajeran hanci, da wiya zalo zalo.. HAIRANAN ta kwashe da dariya, tace "Wallahi Aboki ba a santa, yace "Na sani k'awa, idan kika Auri mijin nata takawo miki wani iskanci ki kirani mu zane ta..😂 tace "Mu farfasa mata bakin muga na magana ko.. "A mana, HEESHAM yace da ita hakan, dan ya gane kishin nata da yarinta aciki, amma da gaske idan ta kirasa dan su zane MEENATUN wallahi zai amsa kiran, Saidai duk abin da zai faru ya faru...
Yana kallan abar qaunar tasa zata shiga motar Sadeeq wanda yazo shida matarsa Khadija yanzu, kafin ta shiga motar sanda ta d'ago kanta ta kallesa, shiko ya bata sak'o, dan sakar mata murmushinsa yayi wanda ayanzu ya gane yana mata dad'i sosai kana ya bata kiss da hannunsa yana meyi mata nuni da wankanta yayi mai kyau sosai, dan gashi tana gani sai d'aukarta yake a hoto ta wayarsa, sai kawar ta sakar mai murmushi da naga mai hannu alamar bye, kana ta shige motar da bala'in jin daɗin kulawar daya bata, da kuma qarin MASIFAR SONSHI aranta.. Gashi ba wanda ya lura dasu sai HAIRANAH

Haka suka ficce daga gidan ya zamana daga momy saisu su HEESHAM d'in sai masu aikin gidan.. HEESHAM yace da HAIRANAN taje ta shirya ya kaita wajen shaƙatawar.. Aiko cikin jin daɗi ta gangaro daga saman tana cemai toh..





Da gaske MEENATU ranta b'ace yake kamar yanda HEESHAM yace tana cika tana batsewa, ran nata ya b'aci ne saboda ganin da NUWAIRA za'aje gidan nata, tasan dai HAIRANAH da HEESHAM baza suje ba, toh taso NUWAIRAN ma tace bazata ba, wannan yasa ranta b'acin take cika take batsewar.
Hannatu ko tunani tayi ko da ita takeyi, hakan yasa itama ta d'aure fuskarta, kana dai gani kasan bata san zuwa gidan..

Ahaka dai suka iso gidan, wanda yake cikin jerin unguwannin manya, gaskiya gidan ya had'u ainun, dan gashi tunkan su NUWAIRAN su shiga ciki suka fara santin gidan, anan ƙofar gidan sukaga HASEENAH da momynsu da qawarta da kuma wata qawar HASEENAH suna masu jiran zuwansu ran nan babu dad'i haka, AHMAD ya fitto ya gaida momynsu MEENATUN ta amsa ad'an gajarce, dan ranta a b'ace yake dashi, sunzo gidan me gadi yace musu babu kin cikin gidan a hannunsa, bayan kuma MEENATU tace mata shi AHMAD d'in ya bama me gadin key d'in, kuma ta kira number na MEENATUN tun tuni amma bata d'aga ba, dama suna so ne kan kowa yazo suyi binne binnansu da zasuyi na kar wata ta shigo gidan a matsayin matar AHMAD d'in ta biyu, sai kuma gashi basu samu yanda suke so ba, wannan yasa duk ransu yake a b'ace..

Ba da wani mutuntawa can ba mamansu NUWAIRA ta akalli Hauwa'un momynsu MEENATUN ta gaidata tare da mata murnar tarewar AHMAD d'in da MEENATU..
Itama d'in ad'an gajercen ta amsa mata, kana suka shiga ciki..
Masha Allah kowa yake cewa, dan gidan yayi kyau sosai, ya tara komai da ake buƙata acikin gida irin waƴannan...
Sai dai dama kallan farko da dazaka yima tsarin gidan zaka gane na mata biyu ne, amma dake yanzu ita kad'aice sai AHMAD d'in ya ƙawata d'ayan part d'in da cewa nashi ne..
Wannan abu shiyasa MEENATU sakewa, taji daɗi aranta, ta yarda ita kad'ai ce da gida..

NUWAIRA da HASEENAH ko sai kallan kallo suke, ita dai NUWAIRA tasan kallan tsana takema HASEENAH, itako HASEENAN na tsanan takema NUWAIRAN bana tsanan take mata ba duk bazaka gane ba...
Haka dai mamansu NUWAIRAN tayi ma momynsu MEENATUN sallama kan zasu tafi... Aiko cikin jin daɗi ta amsa mata da kulawa..
Ramlat Hannatu NUWAIRA Khadija Sadeeq duk suka tayo suka barsu..
Tun akan hanya Sadeeq yayi hanyar gidansa da matarsa, su kuma sukayo gidan momy...
Nan mamansu HAIRANAH bayan tagama yima momy santin gidan saita koma gidanta..
Ramlat ta tambayi momy ina HAIRANAH, momy tace "Sun tafi wajen shaƙatawa ita da HEESHAM...
NUWAIRA najin hakan tayi room nasu dasan kiransa a waya ta tambayesa me yakeso ta dafa masa...


Lokacin suna wani wajen shaƙatawa wanda ba'a dad'e da bud'esa, wajen yayi kyau sosai, danya tafi da hankalin HAIRANAH sosai, sai zaga wajen suke cikin farin ciki da walwala abin gwanin ban sha'awa, sunsha kayan dad'i na sanyi kala kala, yanzu haka sun zauna ne suna hutawa, kasancewar wajen babban waje ne, zagashi sai anayi ana hutawa....
HAIRANAH ta kalli HEESHAM d'in take, "Wallahi HEESHAM duk kaina ya kulle, har yanzu haushin kaina nake da nake san YA AHMAD, abin ya tab'ani sosai, dan banyi zato ba..
HEESHAM yace "Ni dai na gaya miki sanshi kike, kuma tunda yaji wannan maganar da kika gayama momy nasan bazai barki ba saiya Aure ki, dama fa nima naga kamar yana sanki..
HAIRANAH ta waro ido tace, "Gwara dakace kamar yana sona, dan sai dai kama, amma ba gaskiya bane, kullum acikin hararata yake, kuma da farko naga tsanata sosai a kwayar idansa, HEESHAM yace "Kika sani ko duk kishi ne, tace "Haba HEESHAM, saikace yau na fara Soyayya, nasan kishi na kuma san tsana, bafa akan AUFAN na fara Soyayya ba, kawai tashi tazo min da zafi ne...
HEESHAM zaiyi magana yaga kiran NUWAIRAN ya shigo wayarsa, da murmushi cikin sanyi ya d'auka yana cewa "Allah yasa naji zazzaƙar muryar my Auntii cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, Tace "Kajita HEE-SHAM, na dawo gida banganku ba, momy take cewa kum fita yawan shaƙatawa, yace "Yes, bake na fara yima tayi kikaqi amsawa ba, tace "Toh ayanzu idan ka qara min zan amsa maka Wallahi zan amsa maka, ban san me yasa naji wani iri a yanzu ba, Yace "Toh kisamu nutsuwa pls, akoda yaushe HEESHAM yana tare dake, idan kina so na dawo da HAIRANAH na d'auke ki ayanzu zan dawo da ita na d'aukekin...
Tace "aa, ban shiryama yau ba, amma zan shiryama duk ranar da kaso hakan, dan Allah ka gayamin me kake san ci nayi maka anjima, "Komai kin iya my Auntii, kiyi abin dazaki samu ladansa da yawa kawai, tace "Ka tabbatar idan nayi abin da baya cikin cimarka zakaci, yace "Yes, me zai hana
Hmmm na lura baki san yanda naji daɗin abincinki bane akan harshena, da kisan yanda najishi da komai ma zaki min batare da tunani ko shakka ba..
Tace "idan ko haka ne, zan qirqiro wasu dabarun a girki, waƴanda baka san da zamansu ba, wallahi zanyi maka su dan kawai naga farin cikinka...
HEESHAM ya gyara zama cikin k'asa da murya sosai yace "Toh Nagode sosai amma gayamin... Tace "Mazan gaya maka, yace "Me kike so nayi miki wanda zai faranta ranki, tace "Ina da abin da nake bala'in so agareka HEE-SHAM amma yanzu ba lokacin gaya maka shi bane, Yace "Har sai yaushe zaki gayamin, tace sai lokaci yayi.. Yace "Bana so natakura miki my Auntii, amma ga wata tunatarwa, idan mutum yana san wani abu agun wani, qoqari yake ya mallaki wannan abun cikin sauri, dan zai iya yuhuwa ko waninsa nasan wannan abun, ko wani daban can... Kinga idan baiyi amfani da damarsa tun farko wajen amsar wannan abun ba har wannan waninsan ya rigasa amsa ko wani can ya rigasa amsa ba shakka ran wannan mutumi zai b'aci, ya dawo yana cizan yatsa, yana me furta wannan kalmar ta dama nayi kaza kafin zuwan kaza dama nayi da shikenan.. Toh my Auntii bana san Kalmar dana sani ta wahalar min dake, qila wannan abun da kike so a gareni wani ko wata suna so agareni, yanzu idan suka rigaki amshewa yazakiyi idan baki gaya min yanzu ba kika tsaya tsayuwar jiran lokaci, wanda shi idan yazo baya komawa baya..
NUWAIRA tayi shuru jikinta yayi sanyi, hankalinta kuma ya tashi, tasani idan har batayi qoqari tayi abin dayasa ya fara santa yanzu ba, dole zata samu matsala acan gaba, dan yanzu maza tsad'a suke yayin da mata suke araha, bata san wata ta kwace mata shi, idan har hakan ta faru ta tabbatar itakam tata ta ƙare

Yanzu bata san me zatayi ba, gashi AHMAD baya kusa bare ya gaya mata yanda zatayi, dan haka cikin sanyin jiki tace mai, "HEE-SHAM...
Har cikin kwakwalwarsa sanda yajita, cikin lumshe ido yace "Kin iya faɗin sunana my Auntii.. Murmushi tayi da cewa "kawai kabari idan ka dawo gida na gaya maka..
Ya gane so take ta gayama AHMAD dan ya gaya mata me zatace mai, dan haka shima murmushin yayi dace mata, "bye bye... Suka ajiye waya..
HAIRANAH tace "Ni dai aduniya kaf banga wanda Aunty NUWAIRA tasake dashi take kulawa kamar ka ba HEESHAM, dan bata tab'a tsayawa da wani namiji sunyi hirar minti biyar ba
Hakan yasa muka fara zargin kodai tana da aljanun qin maza ne..
HEESHAM yace "Yayi dai dai.. Tace "Ban gane ba, yace "kawai inaga basa yi mata ne, kinsan akwai mutanan dasu suna maka kallan farko idan bakayi musu ba basa sauraranka, idanko kayi musu sai kiga har jan lokaci suke wajen san hira dakai..
HAIRANAH tace "Tabbas na yarda da zancen ka, Saidai ina san kacireni a duhu ka sani a haske, Soyayya kuke kai da Aunty NUWAIRAN koko kawai kun fara shak'uwa da juna ne, murmushin HEESHAM yayi yace "Dake ban tab'a Soyayya ba, amma ni inaga shakuwa ce kawai muka bara samu, kinsanfa ta iya girki.. HAIRANAH tace "Eh gaskiya kam, ta iya sosai... Yace "Allah yasa kema gwanace kifi MEENATU iyawa a gidan ya AHMAD..
Sanda tayi dariya kana tace "ameen, aiko ban iya ba, sainayi qoqarin iyawa danna fita iyawar, nifako😀 idan nazama kishiyar wannan shegiyar matar gaskiya za'a samu matsala..
Yace "ba wata matsala da za'a samu.... Kan tabashi amsa saijin wani saurayi sukayi akansu yana musu sallama, HEESHAM ne ya amsa tare da kallansa daga sama har qasa, gaskiya saurayin ya had'a sosai.. Yace da HEESHAM dan Allah yad'anzo gefe yana san magana dashi, bayan HEESHAM ya tashi yaje garesan gayamai yayi wai yana san HAIRANAH ne, dan Allah idan ba budurwarsa bace ya temakesa dan Allah, HEESHAM yayi murmushi yace mai yana zuwa, wajen HAIRANAN ya koma yace mata "Ke, wancan gay d'in wai sanki yake, HAIRANAH ta hararesa tace "Baka taya Yayanka kishi ne, yace "No, kiyi tunani mana, ai ta hakan ne zaki yarda da zancena nace miki da nayi YA AHMAD d'in yana sanki, ba mamaki agida ko yana da wacce take saka miki ido acikin Hannatu my Auntii Aunty Ramlat wajan gaya mai kina tsayawa da samari ko baki tsayawa, idan yanzu yaji kina tsayawa dasu hankalinsa zai tashi yasa yayi saurin fitowa ba tare daya shirya ba wajen nuna miki cewa yana sanki..
HAIRANAH tayi murmushi tace "Nifa haka kawai nakasa yarda yana sona, bare yasa d'aya daga cikinsu Hannatun tasamai ido akaina... HEESHAM ya lumshe ido yace "HAIRANAH... Tace "Aboki.. Yace "Kinsan Allah ki yarda kawai Ya AHMAD yana sanki, yana MASIFAR SONKI, dazaran kin fara kula samari nan zaki yarda da hakan.. Tace "Ok, bazanqi tataka ba HEESHAM, amma kasan halin ZUCHIYA kar naje na fara san wani acikin waƴanda zan fara kulawa, kasanfa ban iya so ba, idan zanso abu sanshi nake gabaki d'aya kuma da gaske..
Yace "Nafa sani ƙawa, amma bazai barki kikaiga san wani ba wallahi, ni nasan waye YA AHMAD, Dan haka yanzu duk wanda zaice yana sanki ki kaisa gida kawai, ba wani abin dazai faru dan kinsan mu Auran dangi muke, kuma bari kigani duk da momy tasan hakan saita nuna miki bata san ta dinga ganinki da samari, dan qarara nasan zata nuna kishin d'anta, kinsan iyayannan namu dasan ƴaƴa,
HAIRANAH ta kwashe da dariya tace "Na yarda toh Aboki..
Nan HAIRANAH ta nuna tanayi da saurayin nan, daga nan sukaje wani wajen shaƙatawar nan ma tayi samari kusan uku kai a tak'aice dai HAIRANAH tayi samari a wannan ranah sama da shidda, har sanda tafara yima HEESHAM k'orafi, shiko dad'i ne ya kamasa dan yasan wannan fittar da sukayi ba alkairi bace ga YA AHMAD😂...

Suna dawowa gida HEESHAM d'in ya dinga dube duben neman NUWAIRA, bai ganta ba, can ya jiyota a kitchen ita da Momy suna girki, ita tana nata da shi, momy da Ramlat suna yin na gida, gaskiya ganinta ya saukar mai da nutsuwa sosai, wannan yasa ya gane yafa fara santa da zafi..
Bai yarda sun gansa ba, yayi part d'insa, amma ita NUWAIRAN tasan yazo wajen, dan taji ƙamshin turaransa..


AHMAD ko dama suna zuwa gidan nasa bayan ya nuna masu komai ficcewa yayi zuwa can wajen wani Abokinsa doctor Fatihu.
Fatihu dai wani abokin AHMAD ne wanda yake matuƙar san AHMAD d'in, shima AHMAD d'in yana sanshi sosai adai zaman takewarsu babu wani Hassana ko munafunci ko san ZUCHIYA sundai d'auki juna da mahimmanci da amana, ba abun da suke b'oyema juna, shima doctor ne, yana aiki a kano asibitin malam aminu kano, da kuma nan garin Abujan cikin asibitin AHMAD d'in, Yana da mata guda biyu, Hafsat da Hauwa, duk basu aihu ba, dan atare ya Aure su, kuma AHMAD d'in ne yasashi Auransu a tare, danshi Fatihu maraya ne, agidan marayu ya taso, Hauwa uwar gidansa itace anan Abuja, sai Hafsat dake kano itama a gidan nata, a skull suka had'u da AHMAD har abotarsu tayi qarfi suka kawo har iyanzu, Fatihu yana san Momyn su AHMAD sosai dan ta nuna qauna agaresa, ta d'aukesa kamar d'anta, musamman dataji maraya ne, wannan shine Fatihu Babban Aboki ga AHMAD..

Bayan AHMAD ya zauna Fatihu kallansa yayi yace, "Yanzu dai kasamu lafiya, sai'a dawo aiki ko.
AHMAD yace "Zan dawo amma sainaci amarci, wallahi Fatihu Aure nake so na qara..
Fatihu ya ƴalƴale mai da dariya yace, "Gaskiyarka ɗan-uwana mata biyu dad'i garesu, kai bazaka san waye kai ba sai kana da mata biyu, ammafa suna da wiyar sha'ani, musamman idan kagane kafisan d'aya daga cikinsu, ni dama nasan a futunarka bazaka iya zama da mace d'aya ba, kaifa ko yaushe acikin azumi kake... Shiyasa baka gaba baka baya ajiki, yanzu ko dole kayi jiki, dan nasan kaza d'auke wasu azumin da kakeyi, Abokina Aurefa yayi a rayuwa, ina goyan bayanka kan ka qara zata maka amfani sosai. AHMAD yayi murmushi yace, "MEENATUN tana da kishi sosai, haka itama wannan d'in, duk basu ƙaunar juna, gasu y'an'uwan juna, kaga ai ita MEENATU babanta da Dadynmu uwarsu d'aya ubansu d'aya, haka itama HAIRANAH da mamanta da Dadynmu uwarsu d'aya ubansu d'aya..
Fatihu najin hakan ya tsaida tunaninsa dakyau akan AHMAD d'in yace, "Duk da nasan Auran dangi kukeyi amma fa dole zaka fuskanci matsala da matanka qilama da iyayansu, fatana koda wani abun ya faru kayi aiki da hankali pls.. AHMAD yace "insha Allah Abokina, yace "Nine zan had'a maka kayan lefan amarya, yace "Toh Nagode..
Nan shima Fatihu ya gyara zama yana gaya mai damuwarsa dasan yabasa mafita..



Amarya MEENATU dai taga jama'a dangin nasu sosai sunje ganin gidan nata, kuma kuwa sai yabawa yake, bayan dangi da abokan azziqi dana tsiya kowa ya watse haka momynsu da HASEENAH suka sata yin wanka da wasu kayan tsafi tsafi da asirce a sirce na bokaye ta gyara kanta..
Momyn nata ta kalleta tace, "ga wannan kwaryar kisan inda zaki ajiyeta wajen dabazai gani ba, Sannan kadda ki kuskura yaqi kusantarki yau, idan har hakan tafaru kinyi asara, dan bazaki mallakeshi yanda kike so ba... Tace "Toh momy, zanyi dukkam abin da kika ce, HASEENAH tace, "Kina mallakesa yau kin huta da batun wata uwar miji, dan sai yanda kikayi dashi, uwarsa bata ba juyasa yanda tafaro. MEENATU tayi dariya tace "Kamarko kinsan momyn nan tasa da tsinannan sa ido take, bakiga zamammu acanba zama nayi kamar wata marainiya, kullum zama a d'aki kamar wata mayya..
Momynsu tace "Toh zaki mallakesa idan har ya kunsance yau, amma idan kika bari sai gobe asirin ya karya kuma kimma Kanki asara, dan tunran gini tunran zane, wannan kwaryar ko itace zata miki Katanga da zuwan wata kishiya, idanko kika bari ta fashe dole kiganki da kishiya, sauran binne binnan da bamu samu munyi ba zanje na gaya ma bokan ko babu matsala, tunda lokaci ya qure mana, MEENATU taja numfashi tace "Nifa nagaya miki ya gayamin yabama me gadin key d'in, tace "inda ya basa ai da mungama komai kafin kuzo.. HASEENAH tace "share wannan maganar kawai momy, zomuje gida dare nayi.. Nan sukama MEENATUN sallama suka ficce..


Lokacin ko k'arfe takwas da rabi ne na dare, NUWAIRA na zaune tana jiran HEESHAM ya dawo daga masallaci yaci abincinsa ya yaba mata, sai kawai taji wani saurayin HAIRANAH ya kirata awaya.. Nan tatashi dama da kulliyarta taje ta gayama momy tayi bak'o, toh momy tace mata kawai.

Nan harabar gidan suke zaune kan wasu kujeru wanda dama Dady yayi masu kujerun ne dan yin hira wajen, Hannatu ce can gefe ita da saurayin nata AMAAR, sai itama ta zauna da bakwan nata acan gefe..
NUWAIRA dake ganinsu ta window kiran AHMAD tahauyi, lokacin ya saka kan motarsa kenan cikin gidansa saiya tsaya amsa kiran nata..
"Ya AHMAD ga wani can yazo ga HAIRANAH zai maka b'arna, saurayi ne na karshe daga ganinsa yayi kama da SAMARIN BANAH, Sam babu haɗi kafisa had'ewa takowane fanni, naji maka kishi sosai, dan Allah kazo karya d'auki lokaci yana maka b'arna, duk da nasan abu ne me wiya ta iya Auransa, NUWAIRA ta gaya mai hakan cikin tabbatarwa
Ran AHMAD b'ace yace "Ganinan zuwa sister...


Haka bai qarasa shiga gidan nasa ba yajuya kan motarsa sai gidan momy, HAIRANAH ta sake sai hira take da d'an saurayin nata, kawai daga ita har Hannatu basuyi zato ba, kawai sai sukaga motar AHMAD na dannowa farfajiyar gidan, daidai nan, HEESHAM shima ya shigo daga dawowarsa daga masallaci..
AHMAD ya ƙarema HAIRANAH kallo tsaf daga cikin motar tasa ransa nayi masa zafi haka ya fitto direct nufar inda suke yayi, HAIRANAH kallo d'aya tayi masa taji gabanta ya fad'i, dan bata tab'a ganin fuskar nan tasa a murtuqe haka ba..
Yace da ita "Ke wannan waye, HAIRANAH ta kalli HEESHAM ya d'aga mata gira alamar tace saurayinta ne, tace "Saurayina ne.. Sanda AHMAD ya rintse idonsa danjin zafin amsar tata...
Yace "tashi ki shiga gida, tace "Ya AHMAD ina sanshi fa kuma.. Ai bata qarasa ba taga yana niyar d'auketa da mari ba shiri ta tashi da gudu tayi cikin gidan, ya kalli saurayin nata yace "Kai kuma karna kuskura na qara ganinka a nan gidan, dan ammata miji, dafatan kagane ko...
Cikin damuwa saurayin ya tashi ya ficce daga harabar gidan, HEESHAM zaiyi cikin gidan AHMAD ya tsaidashi wajen cigaba da cewa, ka kiramin ita ina bakin get, yace "Toh Yaya..
Yana shiga falan ko ya ganta kan hannun kujera yace mata, "kinga abin da nake gaya miki ko, tace "Eh wallahi, kasan Allah sai yau nagane meyasa yake min masifa idan ya ganni da wani, ammafa na tsorata sosai da ganinsa, gashi ransa a b'ace yake sosai, ba mamaki ko Hannatu ce tagaya masa, HEESHAM yayi murmushi yace, "ba mamaki kam, yanzu dai wai kije injisa, yana bakin get, duk abin da zaice miki ki nuna ke kina san saurayin kinji, tayi murmushi tace "Toh, kajirani anan, duk yanda mukayi zan fad'a maka yanzu, yace "No nizanje naci abincin my Auntii idan na gama zan kiraki a waya, tace "Ok aci dad'i lafiya, dan naji momy na cewa Aunty NUWAIRAN tasha wahala wajen had'a naku abincin... Yace "Wow, kinga tafiyata... Tana ganin tafiyar tasa tayi wajen AHMAD d'in. Baya ta cikin harabar gidan nasu, dan ya fitta waje, sanda ta fitta wajen taga yana cikin motarsa, dan haka gaban motar tashiga tana cewa, "Gani Yaya.. Bai kalleta ba yace "Yanzu samarinki nawa, tace "shidda,
shuru yayi mata kamar bazaiyi magana ba, sai zuwa can yace "kuma acikinsu wa kikafi so, tace "dukkan su ina sansu, anan ne ya juyo ya kalleta da galla mata wata shegiyar harara, yace "wallahi daga yau na qara ganinki da samari ranki idan yayi dubu saiya b'aci, tace "mezaisa, bayan ni Aure nake so..
Yace "Aure kike so ko, tace "A mana. Yace zanje na
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment