Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kana ya shafa addu'arsa ya koma room d'inta tare da shafeta da addu'ar, dan yasan batayi ba, kana ya janyota jikinsa...

Da asuba a tare suka tashi, suna had'a ido tayi wani saurin rufe idan nata, yayi murmushi da cewa, "Hmm, Antin nan kina san mijinki da yawa, na kasa manta wannan salan naki a kiss, kasa bacci nayi dan murnar kwarewarki, ina fatan dai zaki qara min shi a yau, dan da gaske yak'i barin tunani na...
Shuru tamai cikin matuƙar jin kunyarsa, kamar k'asa ta tsage ta shige ciki, dan haka tashi tayi cikin sauri ta shiga toilet abinta..
Murmushin ya qara yi Kawai dayin room nasa.

Shiyajasu sallah duk da yasan a cikin layin nasu akwai masallaci, dan yana ji ma sunayi..
Suna idarwa ta kwanta akan kafaɗarsa tace "Dan Allah Luv, ka roqa mana Allah karya qara nuna mana irin na jiya, kaga dana shiga toilet normal naganni kamar yanda nake, yace "Bara nagani, tako nuna masa, yace "Luv har yanzu a rufe yake fa.. Tana kalla sai taga da gasken arufen yake, nan hawaye ya zubo mata, cikin kuka tace wallahi yanzu dana shiga toilet ganina nayi kamar yanda nasanni, wai me yake faruwa dani ne, me yake shirin san faruwa ne..
Sai kawai ya rungumeta, ya hau lallashinta, aiko Addu'a sosai sukayi..

Gari nayin haske momy ta kawo musu breakfast, haka sukaci sama sama, kowa da abin da yake tunani aransa, Amma HEESHAM d'in ya lura tafishi shiga damuwa ayanzu, dan haka bayan sun gama sun tashi daga dining d'in, saiya kama hannunta yace "Ba'a san ganin Amarya cikin damuwa, dan haka bana son ganinki a cikinta my Auntii, dan Allah ki kwantar min da hankalinki.
Kallansa tayi cikin damuwa da ƙauna tace "Ko wace amarya tana bama mijinta farin ciki a daran jiya, ni meyasa na kasa baka wannan farin cikin mijina, yace "Allah ne bai bani ba my Auntii, kuma banyi fushi dashi akan hakan ba, tace "Toh yanzu ya matsayin Soyayyata take agunka, yace "Tana nan yanda take, banda abinki mezai sameta daga fara karb'ar ƙaddara jiya..
Tace "Bana san wannan ƙaddarar dan... Saurin rufe mata baki yayi da cewa, "Luv, kar kiyi sab'o mana, badai ni bane, ina tare dake ai, har gaban abada bazan tab'a barinki dan kina tare da wata matsala ba, kawai ki nutsu kiji abin dazan gaya miki ayanzu..
Gyad'a mai kai tayi, sai yaci gaba da cewa,
Kowane mutum yana tare da qaddararsa, haka duk wata masifa batafi qarfin Allah ba, Allahn yana iya jarabtar mutum tako ta ina, mutane sukan iya jefa mutane y'an uwansu cikin wata rayuwa, zai iya yuhuwa wannan ƙaddarar data samemu daga Allah take, ya mana hakan ne dan yaga ya zamu yi, zai kuma iya yuhuwa da'akwai sila, qila wani ne yayi mana hakan dan ya jefa rayuwarmu cikin qunci, toh ki kwantar da hankalinki, duk wata cuta da kika ganta Allah ya saukar da maganinta, dan haka yanzu mu dage da Addu'a kan Allah ya warware mana wannan matsalar koya kawo mana mafuta a cikinta, muyi hakan na kwana bakwai muga yanda Allah zaiyi damu....
Qara gyad'a masa kai tayi da Faɗin, "Amma dai har yanzu kana sona ko, yayi murmushi da rungumarta yace "Auntii nifa ba jikinki nake so ba, ke nake so, zan rayu dake koda babu wannan Soyayyar, sanki gareni kawai yana bani nishaɗi, kedai kici gaba da Sona kawai nutsuwata, qara maqalesa tayi hawaye ya zubo mata tace "Toh, ina sanka mijina, kuma kar kamin kishiya kaji, murmushi me had'e da dariya yayi tare da cewa, "Ke kad'aice Matar HEESHAM har a gidan aljanna, koda zan rasa rayuwata zan dage da Addu'a da kuma bin lungu da sak'o wajen nema mana Mafita..
"Yauwa nagode sosai mijina, kai kad'ai nake sO, tunda nazo duniya ban tab'a Soyayya ba sai a kanka. "Nima ke kad'ai nake sO Matata! Ina san kicire kowace damuwa aranki nasamu farin ciki, dan ganinki a farin cikin shine samun farin cikin ruhina... Tace "Toh zan cire komai insha Allah, takai ƙarshen zancen da d'ago da kanta tana kallansa tare daci gaba da cewa, yanzu fitta zuwa office zakayi kabarni ko, yace "Kai haba, saikace bana tare da Amarya ta, bazanje ko ina ba, dan ina tare dake har nan kwanaki bakwai, cikin murna tace da gaske, bai kula amsar tata ba kawai kiss ya sakar mata da cewa "Muje kiga gidan naki, daga nan muje room nawa na saka mana wani film zakiji daɗinsa sosai lovely nah.. tace "Ina sanka mijina, yace "Nima fa haka nake sanki..





Daidai Lokacin HASEENAH waya take da yayarta MEENATU inda take ce mata... "kinsan Allah Aunty MEENATU, Yau na tashi da matuƙar farin ciki, Gaskiya Qawata Jamila tayi, itace ta had'ani da malamin, ya nuna yana sona, da kuma manufarsa akaina, niko na yarda, dan a lokacin bani da wani buri a rayuwata kamar na baqanta rayuwar NUWAIRAN, kuma har gobe a hakan nake, yanzu muka fara ni da ita, Ya tabbatar min babu makarin wannan asirin danayi musu, idan ko suka samu makarin ba makawa wajensa sukazo...
MEENATU ta kyalkyale da dariya tace "idanko haka ne har abada bazasu samu makarin ba, dan Saidai su dauwama a hakan, ni ai dana san da wannan malamin da wallahi gunsa naje yayima HAIRANAH hakan. Tace "Yanzun ma ai bata b'aci ba, ki tambayesa zaki wajen momyn namu bata da lafiya, kina zuwa kawai saimu had'e dan momyn ma tace zataje wajensa, dan taga kan Dadynmu yana rawa, qila yana san qara Aure ne.. MEENATU tace "Toh jirani zan kiraki yanzu idan ya barni saiku jirani, Toh HASEENAN tace mata da kashe wayar... Kallo d'aya zaka mata kasan duniya tayi mata dad'i...

MEENATU ko da gaske kiran wayar AHMAD tahauyi, lokacin yabar gidan yayi office d'insa, dayaga kiran nata da kamar bazai d'auka ba, dan sauri yake zai shiga wani aikin gaggawa daya samu wata yarinya, yana d'auka tace "My dia dan Allah ina san zuwa gida yanzu duba momyna wai bata da lafiya, yace "Subhanallah, me yake damunta, nan kuma sai tahau kame kame, "Hmm am wai kamar ciwan ciki ko ciwan baya ne, aa zazzafan zazzab'i ne, shuru yayi cikin tunanin amsar da take basa, can yace, "Kibari idan na dawo maje dukkanmu mu dubata, cikin sauri tace "No, ina san ganinta ne yanzu, hankalina ne yake a tashe dan Allah kar kace bazani ba, takai ƙarshen zancen da fashewa da kukan munafunci, yace "Ya salam, Is owkie, kije amma karki kai yamma, yana gama gaya mata hakan ya kashe wayar tasa..
Itako cikin farin ciki takira direban nasu na gidan wanda AHMAD d'in ya ajiye musu ta gaya mai maza ya fitto da mota zai kaita gida, kana tahau shiryawa...

Lokacin data fitto harabar gidan yayi dai dai da fittowar HAIRANAH itama dan zuwa wajen shaƙatawar gidan dan hutawa, kasancewar yanzu tagama komai, gwaiba ce a hannunta da Apple tanaci gwanin ban sha'awa, nan suka had'u sukama juna kallan kallo, MEENATU ta galla mata harara tace, "Yauwa dama ina san gaya miki, wallahi zuciyata cike take da tsanarki, duk wannan kalaman dana fad'ana ranar cewar zamu zauna lafiya ba gaskiya bane, dan bazan tab'a zama da kishiya ba, bare har in zauna da ita lafiya, kamar yanda nagaya miki a baya kad da kiyi kuskuran fara san mijina naja miki kunne amma kikaqi ji, to kisani wallahi ko ana ha maza ha mata saina fiddake daga gidan nan, zan tabbatar miki shiga gidan wata ba abu bane me sauƙi, abu ne me matuƙar wahala, Sannan bayan na b'ata miki rayuwa haka zan kad'aki gidanku, danni nayi alƙawarin dani kad'ai mijina zaiyi rayuwa...

HAIRANAH ta kalleta sheqeqe, tace "Alƙawarinki alƙawarin banza, ke inda ke mai hankali ce kyayi wannan maganar, ga ishara Allah ya nuna miki bakece da Kanki ba shine dake amma dan toshewar basira kin kasa ganewa, ya kamata ki gane HAIRANAH bata d'aya daga cikin matan da suke jin tsoran kishiya, Sannan bata d'aya daga cikin matan da kishiya zata saka mata ciwan kai, mijinki ne dai na Aura kuma wallahi ina sanshi Sannan cika bakinki da mugun udirinki ba zaisa na janye na bar miki shi..
Lalle ma MEENATUN nan kin kica y'ar rainin hankali, har kina wani ko ana ha maza ha mata sai kin fiddani daga gidan, toh naga isarki, ki fitar dani idan kin cika ke y'ar halak ce, banza wawiya dabbar banza dabbar daji abin qi har a zuciyar masu imani, an Auri mijin naki idan kin fasa aiwatar da udirinki akaina kin raina Allahn daya halicceki, kuma...
Ai HAIRANAH bata kai ƙarshen zancen nata da sauke numfashi ba sai jin wani mari tayi wanda bata tab'a jin irinsa agun kowa ba, dan ko yayanta SABEER da mamansu basa mata irin wannan duk lefin da zatayi ko, tayi saurin dafe kumatunta tana ƙarema MEENATU kallo, wacce ta sharara mata marin, sai cika take tana batsewa ran nan nata a matuƙar mugun b'ace, dan ba'a tab'a gaya mata maganganu masu zafi kamar yanda HAIRANAN ta gaya mata yanzu ba, Faɗi take, "ke har kin isa kisani a gaba kina gaya min maganganu masu zafi haka, wacece ke, dan kin Auri mijina hakan shi zai baki damar cin mutunci na, zaki gani ne, Wallahi saina fittar dake daga cikin gidan nan, kuma a wulaƙance a tagayyare, bakisan ni wacece ba shiyasa kike fad'an zancena zancen cika baki ne, zaki san wacece MEENATU. Tana kaiwa nan a zancen nata ta juya dan shigewa cikin mota, ai ba zato ba tsammani saiji tayi HAIRANAH ta fincikota ta baya ta juyo da ita, babu b'ata lokaci ta d'aga hannu ta tsinka mata mari, taqara d'agawa taƙara tsinketa da wani, tare da hankad'eta tana me cewa, "Waike a tunaninki kinkai matsayin da qazamin hannunki zai tab'a fatar jikina kuma na barki haka batare dana hukuntaki ba, toh bari kiji, wannan ya zama na farko da kuma ƙarshe, karki qara kuskuran Kai hannunki jikina, danni ba haka nake ba, dan na tub'e mu casu muyi raga raga da komai ba komai bane a gareni, dan mu jininmu ba'a halicceshi da tsoro...

Habawa, ai HAIRANAH nakaiwa nan MEENATU takamata da kokuwa, HAIRANAH dai har a zuciyarta bataso suyi kokuwa ba, dan da gaske ta yarda yin hakan yana jawowa Maigida tsiya, kuma a aji irin nata bata so su cakame haka ba, amma dataga MEENATUN ba baya bace shine ta cika mata baki dan tashiga taitayinta, amma Sam tabayi tsammanin zata cakameta da kokuwa ba, dan haka itama biye mata tayi, suka dinga kokuwa, ko wacce a cikinsu taqi bama Y'ar uwarta damar kaita qasa, Bala direba yaga bala'i, dan akan idansa komai yake faruwa, ayanzu cewa yake, "Hajjiya kuyi hakuri ko akira me gidan ne ya rabaku, MEENATU na fad'an tace "idan ka kirasa abakin aikinka, nan HAIRANAH tayi amfani da maganar da MEENATUN ta tsaya yi dashi ta saci qafarta saiji kake ti ti tim😨 ta sauketa a qasa, qoqarin san hawa ruwan cikinta take yi amma MEENATUN taqi bata damar hakan, Saidai daƙar da siɗin goshi ta iya tashi, HAIRANAH takai mata wata shegiyar mangara aiko saiji kake GAF... Ta gwara MEENATUN jikin mota, Bala direba na ganin yanda MEENATUN ta nufi HAIRANAH gadan gadan yayi saurin shan gabanta, dan yasan ranta ya gama b'aci, danga muguwar tsanar HAIRANAH nan b'aro b'aro a idanta, yanzu koma miye zata iya mata... Yace "Gaskiya madam, Saidai nabar aikin nawa, zan kira Oga AHMAD na gaya masa komai, dan koda direba ya d'aukoni ya bani yarda da amana, Sannan ya tabbatar min amaryarsa bata da lafiya, Ganin tana zuwa wajen shaƙatawar gidan nan yasan zansan da zamanta, hakan yasa yace dan Allah idan naga wani abu ya sameta na kirasa cikin sauri, yanzu wannan fad'an da kukeyi komai ma zai iya faruwa da ita, dan ba ƙaramin jamin kunne yayi ba, na haƙura da aikin zan kirasa kawai...

MEENATU najin hakan tace "Akwai dalilin dayasa bani san ka gaya masa ayanzu, amma agaba koda zaka kirasa bazan hanaka ba, takai ƙarshen zancen da kallan HAIRANAH wacce taketa galla mata harara taci gaba da cewa, Wallahi kin qara jama kanki bala'i aguna, dan a zabar dazan gana miki na qara linka linkin ba linkin akanta, idan gidan AHMAD gidan ubanki ne zan gani...

HAIRANAH tatab'e baki da cewa, "Allah yakai damo ga harawa inji hausawa, Sannan ba ubana ba Saidai naki, kuma wallahi ki qara zagina kigani, ba abin dazai hanani fasa miki baki, shegiya babbar banza wawiya me wawan tunani, zama a gidan AHMAD daram dan Qauna da Soyayya ce tasa ya Auro miki ni, musamman zakiga ribar ƙaunar idan na bara fara kyawawan yara, kuma ki qara tab'ani kijama kanki bala'i... Ta faɗi hakan da yin shashinta, ai MEENATUN najin hakan ta wani bangaje Bala direban tayo kan HAIRANAN...
HAIRANAN na gani cikin zafin nama da hanzari irin na d'a namiji Bala direban ya kuma shan gaban MEENATUN, wannan karan harda magiyarsa kan tayi hakuri tadena biyama HAIRANAN dan ya lura da Yarinta a lamarinta.. Ya gayama MEENATUN hakan dan duk yasa ranta yayi sanyi...
HAIRANAH dataji hakan ta banko k'ofarta gararam ta saka mata key..
Tana me d'an tab'a mararta dan taji tana d'an mata ciwo, kana tayi cikin falan nata tana cewa "Hmm, MEENATUN nan bata sanni bane, amma ajuri zuwa rafi..

Anan ko kwafa MEENATU tayi, badan ranta yaso ba tajuya zuwa motar da Bala direban zai kaita gidansu.. Shima yana ganin hakan ya sauke ajiyar zuciya, "gaskiya akwai matsala a gidan nan, ya fad'i hakan a bayyane.. Kana yayi cikin motar ya bata wuta nan ya ficce da MEENATUN daga gidan...

Yana sauketa a gidansu tacemai ya koma gida kawai zata dawo da kanta, toh yace mata cikin ladabi yayi tafiyarsa.

Tana shiga falansu cikin kuka ta komai tagayama HASEENAH da momynsu tana meci gaba da cewa, "Wallahi saina baqanta rayuwar HAIRANAH, saina wulaƙanta rayuwarta, saina nuna mata isar tawa, kai daga qarshema kasheta zanyi...

Momynsu ta furzar da wani huccin b'acin rai, tace "Tashi muje wajen malamin nan, dani uwarta take zance, d'aurin gindin uwarta tasamu shiyasa take ganin ba wani abun da kika isa ki mata... HASEENAH ta katse momyn tasu da cewa, "Eh mana shiyasa ta cika mata baki, tab da'ace ke nice wallahi bazan bar gidan ba saina b'allata na mata raga raga, sai dai komai ya faru.😖

Haka dai sukayi wajen la'anannan nasu boka, dan bazan kirasa da malami ba, dan duk malamin dazai aikata asiri sunansa boka, wani jibgege dashi, bayan ya gama jin tabakinsu akan matsalar MEENATUN yace, "HAIRANAH..... HAIRANAH..... HAIRANAH..... Ya kira Sunan HAIRANAH sau uku, kana ya kalli MEENATU yaci gaba da cewa, akwai wata Addu'a da takeyi wacce take rufe mata ƙofofin laba'i a kullum musamman ta aljanu way'anda muke aiki dasu, sai kuma take bud'e mata hanyoyin alkairi akowace ranah, idan har bata dena wannan addu'ar ba bata kuma dena sauran addu'o'in da takeyi ba bazaki samu nasara akanta ba... MEENATU ni cikakken malamine, binkice na ya nuna min HAIRANAH tana da Addu'a sosai akanta, tafi y'ar uwarta kulawa da hakan, shiyasa danama y'ar uwarta wannan asirin yayi tasiri akanta, mu muna da ƙarya, amma tunda na fara aiki da HASEENAH nace bazamma kowa nata qarya ba, dan ina santa, ta kuma tabbatar min zata dinga mu'amala dani koda tasamu HEESHAM, yanzu dai me kikeso ama HAIRANAN...
Tace "So nake kota halin Ya'ya a baqanta min rayuwarta, tabar gidan mijina, bayan haka kayi mata aikin da zata kasa auruwa..
Yace "Zata bar gidanki, idan zaki lura da Lokacin da bata da tsarki, lokacin da take yin al'ada, awannan lokacin bata damuwa da Addu'a sosai, hakan zaisa mu samu nasara sosai akanta, bacin hakan ba abu bane me sauƙi kisamu nasara akanta, dama dai ita NUWAIRA ce bata da kulawa akan Addu'a...

MEENATU shuru tayi zuwa can tace "Yanzu ni yaushe zan gane tana al'ada, bayan kowa wajensa daban, ba had'a abinci Muke ba bare nagane.. "wannan kuma ke kika sa-ni, zandai baki wani Magani kisa mata a abinci ko a abin sha, zakiga mijin naku baya santa, Soyayyarki ce kawai a gabansa, Ya kai qarshe zancen da kallan momynsu yaci gaba da cewa, Mijinki Aure zaiyi, kuma anan dangin naku zaiyi Auran, Yarinyar tana sanshi sosai...
Ai momyn nasu najin hakan ta gyara zama tace "Na shiga uku, ina aikin danayi mai abaya, wani bokana ya tabbatar min bashi bayin Aure har abada, Yace "Na gaya miki mu maqaryata ne, ba komai muke gayama mutum gaskiya ba, amma tabbas mijinki zaiyi Aure.. Tace "Toh a b'ata Auran, yace "Ko an b'ata agaba zaiyi, tace "Toh adai b'ata na yanzu, kuma na tabbata ko a gaban ne bazaka bari yayi min ba, Sannan ina so ya dawo hannuna, yace "Baki da matsala, dama ai a hannunki yake, saiya maida kallansa kan HASEENAH yaci gaba da cewa, zasu tafi su barmu tare, kya bisu daga baya..
Tace "Baka da matsala, ai kana biyamun buqatata, yace "mutananki suna can cikin wani hali.. Tace "Ai haka kawai na yarda da aikinka, yace "HEESHAM yana da Addu'a sosai, yana san ture aikin, amma ina tisawa.. Tace "Ai shege ne. Yace "Naga alama.
Nan dai yayi musu surkullansa da tsaface tsafacensa, ya bama MEENATU maganin daya gaya mata tasama HAIRANAH a abinci, sannan ya bama momynsu yace ta sakama Dadynsu shima a abinci, idan yaci bazaiyi Auran ba Saidai a gaba, tunda yana Addu'a a hakan, toh a hakan dai suka tafi suka barshi da HASEENAN, masha'a dai ba irin wanda bayayi da ita, Allah dai kyauta Ameen...








Bayan sati biyu haka rayuwar taci gaba da tafiya, HEESHAM da NUWAIRA sun dage da Addu'a sosai, musamman HEESHAM, dan da gaske NUWAIRA bata damu da yin Addu'a ba, mace ce wacce ko sallah idan tayi tana idarwa baifi abu uku zata rok'a ba sai tatashi, to bare azo batun wata wai lafula, ita dai zatayi sallah akan lokacinta, bata wasa da sallah akan lokaci Sam, lokaci nayi zatayi abinta, amma batu na tsayawa yin Addu'o,i bata da kulawa akan hakan sam...
A d'an zaman da sukayi da HEESHAM ya gama ganeta tsaf, farin cikinsa d'aya yanda take yin sallah akan lokacinta, kuma ya udiri niyar zai canjata wajen nuna mata tsayawa yin Addu'a shine mutum, kuma yana tunkud'e masifu da balak'ai..
Har yanzu dai shuru suke,HEESHAM daya duba sau uku yaga dai hanyar rufewa take da zaran yazo da buqatarsa sai kawai ya barta bai qara tunkararta da batun ba, ya saka Addu'a kawai a gabansa...

MEENATU sai ajiyar Maganin malamin HASEENAN take, ta rasa yanda zatayi dashi, itadai tasan ko tayi hauka, baza taje ta kaima HAIRANAH wani abun ci tace taci ba, kuma in ba haka ba bata san me zatayi ba, ta gayama HASEENAH tace mata tanema musu y'ar aiki, saita had'a baki da y'ar aikin kawai, MEENATU najin hakan tace da AHMAD a nema musu y'ar aiki, ta dinga rage musu aikin gida, amma ya d'auko musu d'aya dan aikin nasu ba wani me yawa bane, dayazo ma HAIRANAH da batun tace "Ita bata buƙata, yace shi yana santa da Y'ar aikin, kuma dama yaga aiki ya mata yawa, tace mai ita bataga wani aikin da yayi mata yawa ba, bata buqata kawai, shuru yayi mata, shi yana santa da y'ar aikin ne dan yaga tana san bama cikinsa wahala, sam bata zama waje d'aya, daga tayi wannan sai tayi wancan, daga kawota gidan har ta canja yanayin tsarin d'akinta sau biyu, sab'anin MEENATU da har yanzu bata canjama komai waje ba, dama shi ya dad'e da tunanin kawo ma kowa a cikinsu y'ar aikinta, sai kuma ya fuskanci duk basa buqata, shiyasa da Yanzu da MEENATU tazo masa da batun ya karb'a da sauri dan yana san HAIRANAH tad'an huta, dan har a zuciyarsa baya san yaga tana aiki, ya fisan ganinya shuru a zaune, idan cikin yayi kwari tata sanb'elanta, tunda shidai baida niyar gaya mata ciki ne da ita, dan haka dagewa yayi akan saiya d'auko musu Y'ar aikin ko tana so ko bata so, ya fad'in mata hakan yana me rayawa aransa da hakan zai dinga fakewa yana hanata aiki yana cewa ga y'ar aikin tayi, idan cikin yayi kwari ya dinga kaita tirenin..
Kwana biyu ko ya kawo musu y'ar aikin, wacce momy ce ta nemo masa, sunanta Asiya, Asiya dai wata mata ce y'ar kimanin shekara Ashirin da tara, bazawarace, a qauye take, irin mutanan nan ne masu cin baqar wiya a ƙauyen, ba qaramin jin daɗin aikin tayi ba, da Momy ta gaya mata aikin da zata dinga yima MEENATUN da HAIRANAH, aganinta aikin bashi da wani wahala, gashi za'a bata d'aki, amma nad'an wani lokaci ne idan tasamu miji ta fitto dashi tayi auranta, amma ta riqe amana, nanko tayi ma momy rantsuwa zata riqe amana...

Kallo d'aya HAIRANAH tayi mata tasan Asiyan tana da wayo sosai, haka dai takema HAIRANAN abin da baza'a rasa ba da itama MEENATUN.
Asiya ta gane HAIRANAH bata da sakewa da mutane dan taqi sakewa da ita, MEENATU kuma tafi sakewa da ita sosai, dan hira harda dariya ne tsakaninsu, gashi ita tafi san HAIRANAH ta sake da ita dan a lura irin tata ta gane me gidan yana san HAIRANAN sosai, daga yana yin kallansa gareta Asiyan tagane yafi san HAIRANAN nesa ba kusa ba..

MEENATU dai har yanzu bata fittoma da Asiya manufarta ba, amma ta kusa fitto mata da manufar tata.


Momynsu MEENATUN tuni ta bad'ema Dadynsu Maganin a abinci yaci ya tashi, aiko ta samu yanda take so, dan ya qara shiga hannunta sosai.


Hannatu bata tare da kowace matsala a gidan auranta dan AMAAR santa da yawa yakeyi, yana bata kulawa itama tana basa tata.

Haka Ramlat gani take tafi kowace amarya jin daɗin Aure a ganinta, kullum godiya take ga Allah daya bata SABEER, yayi mata💯 bata mafarkin wata matsala ta shigo tsakaninsu...

Sadeeq da matarsa Khadija ko dama su ba'a jinsu, dan sunfi kowa sanin darajar Soyayya a tunainsu..





Yau da misalin qarfe had'u na yamma HEESHAM ya tashi daga office, dan satinsa d'aya da amaryarsa ya koma aikinsa, yau yana san zuwa gaisar da Baba Alhaji ne kuma yana san sud'an tab'a hira dan gaskiya yayi missing d'insa sosai.
Shi kad'ai ne baya zuwa wajensa ayanzu, amma Dady da Momy kullum sai yaje wajensu da safe da yamma, anan yake haɗuwa da Yayansa Sadeeq dama AHMAD kullum shi suke zuwa su tarar..

Lokacin daya shiga falan Baba Alhajin na cikin gidan nasa Yana tare da bak'o, dan haka kwanciya yayi akan doguwar kujerar falan, yayi shuru yana jin hirar dasu Baba Alhajin suke yi, can saiya canja tunani ya koma tunanin matsalar NUWAIRA, wallahi yana santa sosai dan sai yanzu yak'e qara santa, tunda sun fara sab'awa da d'umin juna, idan har yana gidan maqalesa NUWAIRA takeyi, tana da san jiki sosai, yanda tamaida jikinsa kamar nata har fara tausayinta ya shiga yi, irin ran da suka raba makwanci ya zatayi kenan, ko mutuwa ko wata kadda wacce ba fata yake ba..
Yana nan a haka yana ta tunaninsa har b'akwan Baba Alhajin ya tafi Baba Alhajin yadinga mai magana amma shuru, dan HEESHAM tunda yake a rayuwarsa ma bai tab'a shiga dogwan tunani irin wannan ba.
Nan hankalin Baba Alhajin ya tashi, baya san yaran da tunani, dan baya san yagansa cikin rashin lafiyarsa na CIWAN ZUCHIYA, babu b'ata lokaci ya tashi yazo kujerar da HEESHAM d'in yake ya kama hannunsa sai a Sannan HEESHAM ya dawo tunaninsa, Yace mai, "Ka duba girman Allah da kuma dajarar Annabi Muhammadu sallallahu-alayyiwassallam ka gayamin me yake damunka HEESHAM, me yasaka shiga dogwan tunani haka.
Tashi HEESHAM d'in yayi da sulalewa qasa ya zauna da kwantar da kansa a kan cinyar Baba Alhajin yace "Baba ina da matsala, Matata tana d'auke da wata lalura, kuma ina santa, zan kuma iya zama da ita a hakan, amma ina tsoran lafiyata, Sannan bana san na had'ata kishi da kowace y'a mace...
Babah Alhaji yace "Menene matsalar HEESHAM, gaya min indai batafi qarfina ba zan maka maganinta da izinin Allah.
HEESHAM najin hakan ya kwashe komai ya gaya masa, ko kad'an bai b'oye masa komai ba, shi baima san ya akayi yake gaya masa komai d'in ba, bare yayi tunanin wata kunyar baba Alhajin...
Shuru Baba Alhajin yayi da fad'awa
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment