Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gayama Babah Alhaji cewa kina san ayi miki Aure za'a had'a bikinki danasu Hannatu, amma kisani idan na qara ganinki da saurayi wallahi bake ba harshi saina karya masa qafa, tace "Toh wai kai Yaya meye ruwanka dani ne, kabarni nazab'i wanda nake so da kaina mana, yace "Anqi abarki ki zab'a wanda kike san, kisa aranki kina da mijin Aure daga yau, dan haka tashi ki koma ciki...
Bata mai wata magana ba ta fitta daga motar tana kunkuni, yaji abin da take cewa wai ita bazata Auri kowa ba sai wanda yayi mata, shuru kawai yayi mata, yana ko ganin shigarta yaja motar tasa, ransa b'ace ya koma gidan nasa, da wani rangwad'a MEENATU tazo garesa danta taresa sai ya kauce mata da d'aga mata hannu. Kana ya ajiye mata wata Leda yace "gashi kici pls idan kina jin yunwa..
Sanda ya sakarma kansa ruwa Sannan ya d'anji dama dama, bayan ya kimtsa kansa kwanciyarsa yayi a room nasa yana tunanin ta ina zai b'ulloma HAIRANAH, kishinta yanaso yayi masa yawa, gaskiya zaije ya samu Baba Alhaji da batun a d'aura masa Aure da ita a satin nan, dan ya lura kanta nayi mata rawa dan haka zai sauke mata shi...

MEENATU ko shuru shuru taga bai fitto ba saita nufi room d'in nasa, anan tagansa kwance cikin tunani, tace "My love me yake damunka ne haka, yace "Ba komai, kije ki kwanta..
Shuru tamai dan tagane me yake nufi, gashi ba damar ta fitto ta gaya mai tana da buqatarsa, kasancewar har yanzun ba wani abun daya shiga tsakaninsu, dan haka ahankali tatashi tabar d'akin..
Yaji tausayinta, danya gane tana buqatarsa... Shi kuna gaskiya ayanzu ransa a b'ace..
Idan kuma ya matsama kansa zai mata b'arna da yawa, shi ayanda ma yake jin kansa yanzu zaiso ace HAIRANAH ce wacce zai fara biyan buqatarsa da ita, dan ya tabbatar saita gane kusanta duk wannan rawan kan nata zai sauke mata shi....

Hannatu ko bayan ta gama hira da AMAAR d'inta ta koma ciki saka HAIRANAH tayi agaba tace "ƴar-uwa dan Allah miye tsakaninki da Ya AHMAD, tace "waya san masa ne, duk yabi ya takuramin, ba dama ya ganni da saurayi, Ramlat ta sheqe da dariya tace, "HAIRANAH Yaya fa sanki yake, so yake ya had'a ki da MEENATU.. Hannatu tace "Masha Allah, gaskiya naji dad'in hakan, kinga idan kika zama mata agaresa naje da gayya gidansa na tare agunki, Ramlat tace "Wai dan Allah me MEENATU tayi muku ne duk kuka tsaneta, HEESHAM baya yinta, kema baki yinta, pls Ku gayamin me tayi muku, Hannatu tatab'e baki tace "Ni bana san naga mutum ya fiya iyayi ne da girman kai, gata da nuna ita wata ce alamar wulaqanci...
Ramlat tayi shuru, dan tasan duk MEENATU tana da wannan halin, bama ita kad'ai ba duk y'an d'akinsu suna da wannan d'abi'a... NUWAIRA najin su bata ce qala ba, damuwarta taji HEESHAM shine kawai matsalarta...
Aiko tana tunanin nasa taga kiransa, yace "my Auntii kenan.. Tace "Meya faru, yace "fitto falo kiji, bata mai magana ba ta kashe wayar tata, HAIRANAH tace "Aunty ina zaki, tace "Falo...

Aiko ganinsa tayi yana zaune kan hannun kujera, ta zauna kusa sashi kad'an tace "Toh gani..
Yace "Wow kwalliyarki tayi min kyau sosai.. Ya faɗi yana d'aukarta photo a wayarsa.. Sanda ya gama tace "yawarka zata cika da hotuna na, yace "Abin da nake so kenan, yanzu dai gaya min maganar nan tamu ta d'azu..
Murmushi tayi dan tuna abin da AHMAD ya gaya mata wanda zata gaya mai, tace "Maganar gaskiya abin danake so agareka shine ZUCHIYARKA... HEESHAM ya waro ido yace, "Auntii😳 ya za'ayi na baki zuciyata, bayan bansan a inda take ba... Oh! na tuna, naji mutane suna cewa anan take, ya nuna mata qirjinsa kana yaci gaba da cewa, kuma kinga tawa ba lafiya gareta ba, sam bazata miki amfanin da kikeso sosai ba, idanko kin dage kan saina baki, bazan hanaki ba, amma zakisha wahala sosai wajen nema mata magani..
Tace "Nifa nufina kadda ka bari san wata mace ya shiga zuciyarka, dan nayi maka mata, kuma tana sanka sosai, akan sanka komai zai iya faru da ita, wallahi HEE-SHAM akan sanka zata iya rasa rayuwarta, dan Allah kaji tausayinta kadda ka fara san wata, dan tana yimaka wani so wanda yafi qarfin akirasa da MASIFAR sO, takai ƙarshen zancen da shagwaɓemai kamar zatayi kuka..
Saiya sakar mata murmushi da cewa, "Kina nufin kar nayi Soyayya da kowa kinyi min mata.. Tace "Haka nake nufi HEE-SHAM, dan Allah karkace baka santa, kagani tana sanka sosai..
Yace "Ban gani ba, dan ban santa ba, dan haka gaya min wacece ita.
Cikin yimai kame kame tahau cewa.. "Iye, me kace, am um dama kaga ko, sai tayi shuru ganin ya zuba mata ido, nan take kuma jikinta ya fara rawa, ya qara yin murmushi cikin sanyin murya me tafe da wani salo yace "Nutsu my Auntii, kawai gaya min zakiyi wacece ita, nayi miki alƙawarin zansota danke my Auntii, pls ki gaya min kinji..
D'ago da kanta tayi zuwa ga kallansa nan take suka had'a ido, wani abu taji yana fitowa daga idan nasa yana shiga nata, ahankali tace "kamarmu d'aya da ita, kuma tace karna gaya maka yanzu, kuma tasani na d'aukar mata alk'awari.. Yace "Owkie, babu damuwa badai kuna kama da ita ba, tace "Sosai muke kama, dan Allah kaji kana santa, "Tukunna dai, dan sai nayi tunani, tace "Har zuwa yaushe, "Yace "No karki damu zan gaya miki idan nagama tunanin, tace "Toh dan Allah karka ce baka santa, yayi murmushi da cewa, "Kinga nama gama tunanin, bakince tace karki gayamin wacece ita yanzu ba, tace "Eh haka tace, kuma har tasa nayi mata alƙawari, yace "gud my Auntii, ina san mutum me daraja Alƙawari, idan har kina so nasota Saidai kizama ita agareni, tace "kamar Ya😟.. Yace "Ina nufin saidai mu fara Soyayya nidake, tunda dama kince kamarku d'aya, kinga sai indinga ganinki a matsayin ita, kinga shikenan duk ran data bayyana agareni ba ita ba samun matsala a Soyayyata, amma idan baki yarda ba gaskiya babu ni babu santa..
Murmushi tayi tace "Na yarda, tunda temako ne, bansan wane lada zan samu ba, HEESHAM yayi dariya da cewa, "amma akwai sharad'i, idan har kinsan bazaki iya sakankancewa muyi Soyayya ba toh akwai matsala, dan kinga yawan sakankancewarki yawan ƙaunarta araina.. Tace "Babu komai, karka damu, yace "Na lura kin shirya temakwanta da gaske, tace "Toh ai tausayi take bani, yace "Gaskiya ne, Soyayya dazafi take, yanzu dai zaki iya kirana da batun Soyayya aduk lokacin da kikaso, haka nima zan kiraki aduk lokacin dana so, tace "Hakan yayi..
Tashi yayi yana cewa "masha Allah, zanje na kwanta amma sai naga tafiyarki my dear
Tashi tayi ta nufi shashinsu sanda takusa shiga ta juyo ta kallesa ya sakar mata kiss da hannunsa, ta lumshe ido da cewa "Luv u my beloved.. Da murmushi akan fuskarsa yace luv u 2 my Auntii.. Sai ta shige da mafificin farin ciki aranta..
Shima da farin ciki yayi shashinsa, momy dake kallansu acan gefe basu sani ba tayi murmushi kawai tare da mamakinsu, duk da bata jiyo me suke cewa ta gane koma menene Soyayya suke..🤔 tace "ikwan Allah, alokaci d'aya Soyayyar HEESHAM takoma kan NUWAIRA, wato ya dena san HASEENAH ne koko yaya, ga AHMAD da HAIRANAH, ohni Allah kasa komai yazo da sauƙi, Allah kaga zuciyata banqi kowa acikinsu ba, amma kasani naji san yarannan biyu cikin raina saboda ƙaunar da tun farko uwarsu tanuna akan yarana, ina san ƴaƴana bazan kuma takura musu kan suso abin da basu so ba, haka bazan hanasu abin da suke so ba...


Da asuba bayan AHMAD ya dawo daga masallaci direct room na MEENATU yayi, anan yaganta tana qoqarin komawa bacci da alama tayi wanka da salla ne, ta gaishesa, ya amsa da jin tausayinta, anan yace ta biyosa room nasa, bayan ta bisa ne tagane yana san su raya ne alokacin, aiko baƙin ciki nan take ya kamata, dan yanzu tayi wanka saboda warin da jikinta yake na wanka da abubuwan bokayan da tayi amfani dasu jiya, data sani aida batayi wankan ba, da sun samu abin da suke so na mallakesa...
Da baƙin ciki dai komai ya wakana alokacin, aiko bayan gamawa AHMAD d'auketa yayi da mari, cikin zafin kishi ya shaqeta yana cewa "wa kika bama kanki....

*Qarshen part 1*
Afuwa afuwa afuwa👏🏻👏🏻👏🏻😃















Part 2

MEENATU najin shaqar da tunda take bata tab'a jin irinta ba ai ba shiri tace "Zan gaya maka, dan Allah kadda ka kasheni.. A fusace ya sakar mata wiyan nata yace "Ina jinki toh, aiko da kuka sosai tace "ni macece me yawan sha'awa, nayi wani saurayi Abdul, Abdul yana sona nima ina sanshi, ranar danayi masa magana kan Dadynmu yace ya turo iyayensa, a ranar ya nuna farin cikin sa sosai, yace zai turo su, amma zasu kai nan da sati d'aya kafin suzo dan ba anan garin suke ba a kano suke kamar yanda ya gaya min tun farkwan fara Soyayya ta dashi, nace mai toh, washe gari dayazo ya gayamin ya gaya musu kuma sunce zasuzo, baqamar murnar nayi ba, yace dan Allah gobe zaizo na rakasa gidan abokinsa, nace mai toh ba damuwa, da gaske gidan abokin nasa mukaje, a tunani na abokin nasa yana da mata Ashe baida mata, muna zama sai yaciro wani cingwam ya bani wai naci naji yana da dad'i ga kuma lemun sha na kwalba na had'a, zuciyata d'aya naci wannan cingwam din had'i da wannan lemo, tunda naci nasha naji bacci ya d'aukeni, lokacin dana tashi da tsamun jiki na tashi, da kuma muguwar gajiya, kayana yanda suke a jikina haka na gansu, yace min nasha bacci sannu da tashi.. Nace mai yauwa, daya dawo dani gida naje yin fitsari naga gabana ba yanda nasanshi ba, nan naji hankali ya tashi, ina da qawa Maryam wacce ma'aikaciyar asibiti ce, sai naje wajenta na gaya mata daga yin bacci na tashi saina ganni a haka, tace zan iya kwantawa ta dubani, nace mata eh, nan na kwanta ta dubani tace anyi amfani dani ne, hankalina ya tashi sosai nan nashiga tunanin ya akayi akayi amfani dani, amma duk iya tunani ban iya tuna komai, haka dai nayi wankan tsarki da kiran Abdul amma yaqi d'aukar wayata, bayan wata d'aya dama Maryam d'in tace min naje amin gwajin ciki, nan naje gareta tatabbatar min babu ciki, alokacin nagama ganewa Abdul ne yayimin hakan, dan bai qara zuwa gareni ba, ban kuma qara jin labarinsa ba, dama bawai nawani sanshi bane, kuma har yau ban tuna yanda akayi yayi amfani dani ba, wannan shine abin daya faru.. Takai ƙarshen zancen da qara volume d'in kukanta, tana me cigaba da cewa, dan Allah ka rayu dani wallahi ba qaramin sanka nake ba, ina sanka sosai, dan Allah kadda ka rabu dani...
Nan tausayinta ya kama AHMAD, dan ya gane bada san ranta komai ya faru ba, yaran ya mata wayo sosai.. Dan haka kallanta yayi da cewa, "karki damu komai ya wucce, Saidai zamuje asibiti na dubaki dan tabbatar da lafiyarki. yana faɗin hakan yayi toilet d'insa. Murmushi tasake, bata tashi ba har sanda ya fitto ya temaka mata, hakan ne yasa tatabbatar da gaske komai ya wucce d'in kamar yanda ya faɗin yanzu,
Ko breakfast bata tsaya had'a musu ba ya d'auke sai asibiti, shi da kansa yayi mata gwaje gawajensu na likitoci anci sa'a bata tare da kowane cuta... Dama da gaske labarin gaskiya ta gaya mai, Abdul d'in shine saurayin da HEESHAM ya tab'a ganinta dashi tana mai kiss... Wanda hakan ne yasa ta fitta daga ran HEESHAM d'in yadena ganin wani mutuncinta..

Kallo d'aya MEENATUN tama AHMAD taga hankalinsa ya kwanta, da sakin fuska ya dawo da ita gida, amma sanda ya qara maimai tawa, dan gaskiya tayi mai, yo tasha maganin mata abin ba'a cewa komai..



Anan ko bayan tashin NUWAIRA ta gaida ubangijinta shiga kitchen tayi danta had'ama masoyin nata breakfast.
Yau su uku ne a kitchen d'in, dan HAIRANAH tace zata taya momy had'a nasu yau..
Momy sai kallan NUWAIRA take tana mamakinta, irin koya akayi tayarda da HEESHAM take Soyayya dashi oho, lalle wasu matan duk kyensu wasu mazan basa shan wahala wajen samunsu a bati.. Ita gani take ya akayi ta ammince da HEESHAM maraji, ta ina tafara dashi, bayan ta girme masa da shekaru biyu, Sam momy ta manta ba ruwan so da shekaru, dama tasan HEESHAM ayanda take ganin idansa ba wani abun mamaki bane yaje ya tunkari wacce ma tafi NUWAIRAN a shekaru yace yana santa, dan akwai wata rana da taji suna cacar baki da HASEENAH kan wai ita Yarinya ce, idan tana san suyi Soyayya to taje tasha maganin dazai sa ta qara girma....

NUWAIRA ta kalli momyn tace, "Yau momy sai kallona kike, tace "ina kallan qoqarinki ne kawai NUWAIRA, me zai hana kidena bama Kanki wahala wajen had'ama HEESHAM breakfast, idan kika saban masa duk ran dabaki masa ba damunki zaiyi.. NUWAIRA tace "Momy, yanafa jin daɗin hakan sosai, kawai so nake naga farin cikinsa, bana jin akwai wata ranar da zatazo naqi yimasa idan har dai ina da rai da lafiyata..
Momy ta gyad'a kai tace "Toh ai shikenan..
HAIRANAH shuru tayi ta fad'awa tunani, irin anya babu ayar tambaya tsakanin HEESHAM d'in da ƴar-uwar tata kuwa🤔..

Qarfe bakwai suka gama jera komai akan dining, duk sun taro HEESHAM ne kawai yayi latti yau, aiko yana zuwa idansa fara garwayewa yayi dana masoyiyar tasa, ya kalli Ramlat Hannatu HAIRANAH yace "barka da Safiya sisters, Atare sukace "Barka brother.. Sai ya kalli NUWAIRA cikin murya qasaqasa yace "good Morning Luv... Itama cikin murya qasa qasan tace "Morning my dear, katashi lafiya, yace "Lau n u, "Tace am gud... Momy ta girgiza kai, dan itace taji me suke cewa, nan taqara cika da mamakinsu 🤔, Dady ya kalleta yace "Momy na lura yau akwai abin da kike tunani, tace "Hmm ba komai, yace "Toh Allah yasa, Ameen tace mai idanta dai nakan HEESHAM d'in da NUWAIRA tana kallo bayan ya gama yin breakfast d'in ya tashi dayi musu sallama zai tafi, tana lura ya d'aga ma NUWAIRAN gira sai taga ta ture fulet na gabanta tana kallanta tace "Momy Nagama zanje na huta a d'aki.. Momy tace "Ina zaki raka Ramlat gidan Yayan naku dan kukai musu breakfast...
HEESHAM yace "Toh tazo muje na rage mata hanya mana, Momy ta kallesa tace "Ai ba ita kad'ai zata ba, ita da Ramlat ne, kuma idan kakaita HEESHAM wazai dawo da ita, saiya Sosa qeya yace "Toni na tafi, tace "Allah ya kareka Auta na, ka dawo lafiya dasamun cin nasara akan komai.. Yace "Ameen momyna, Dady saika fitto, da murmushi Dadyn nasu yace "Toh my son.
Sanda ya qara kallan NUWAIRA kafin yabar gun, tana ganin haka itama tabar gun, kuma direct farfajiyar gidan tayi kamar yanda momyn tayi harsashe.. Lokacin zai shiga motar tasa kenan, tace "Nidai ka had'ani da aiki, yanzu me zance maka na Soyayya, yace "Me kike gayama saurayinki idan kin tashi lafiya, tace "Ni bani da saurayi ai, sam bana kula samari, yace toh ba gashi ni kin fara kulani ba, tace "Toh Allah ya dawo dakai lafiya dan Allah ka kulamin da kanka kuma banda kula mata dan bana sansu dakai, yace "Ameen insha Allah zan kiyaye miki kaina, tace "I luv u... Da murmushi akan fuskarsa yace "luv u 2 nutsuwata.. Itama Murmushin tayi da d'aga mai hannu, sanda ya shiga motar tasa ya jata kana tabar wajen..



Sai kusan tara saura sukaje gidan AHMAD d'in, dan sun tsaya jiran wata mata ce wacce momy ta sama masu wacce zata dinga yi masu girki, MEENATU na ganinsu ranta ya b'aci, itafa bata ƙaunar NUWAIRA, bata san ta maida gidanta gidan zuwanta, kamar AHMAD ya sani yaja NUWAIRA harabar gidan nasa yana tambayarta ya sukayi da HEESHAM, nan ta gaya mai komai, babu b'ata lokaci ko ya shiga tunanin anya HEESHAM d'in bai gane tana sanshi ba, nan dai ya qara shirya mata wasu dabarun batare daya gaya mata tunanin dayayi ba..

Tofa wannan tsayuwar da sukayi sai MEENATU ta qara zargin AHMAD d'in daba ƙaramin san NUWAIRAN yake ba, nan zuciyarta taqara baqi, tana jin NUWAIRAN nayi mata sallama taqi kulata. Haka dai suka tafi suka barta da halinta.

Daga nan wani wajen shaƙatawa Ramlat ta wucce dasu, NUWAIRA tayi samari uku, tana qin kulasu amma saboda nacin da sukema Ramlat haka Ramlat d'in ta dinga basu adireshin gidansu, NUWAIRA bata damu ba dan tasan koda sunzo zuwan banza ne, bayan basa Auran bare kuma bazata iya yima HEESHAM kishiya ba😂...


AHMAD zuwa wajen Baba Alhaji yayi ya roqesa kan ya temakesa ya kira mitin a satin nan yana san HAIRANAH ta zama mata agunsa ne nan kusa.. Dariya sosai Baba Alhajin yayi dace mai toh zai kira ranar lahadi...

Aiko kamar HEESHAM ya sani yau daga office d'insa gidan Baba Alhajin ya wucce dan gaidasa..
Nan baba Alhajin yake gaya mai yanda sukayi da AHMAD sannan ya qara da cewa mai, "Sannan Saminu ma yazo min da batun NUWAIRA wai yana santa sosai..
Saminu d'ane ga Abdullahi wato ɗan ɗan kishiyar kakarsu HEESHAM d'in.. Dan haka HEESHAM najin haka yayi saurin gyara zama... Da wani b'ata rai sosai yace, "Ai tana da wanda take sO, Baba Alhaji ya kallesa yace "wa ita kuma take so, HEESHAM yace "kadai bari sai ranar mitin aranar zakaga wanda take so, Babah Alhaji ya tab'e baki yace "Nifa na lura daku jikokin Sa'adatu baku so ko kad'an wani adangi yace zai Auri y'an d'akinku, duk sai kubi Ku nannad'e y'an uwanku, HEESHAM yace "Babah Alhaji ba haka bane fah😳, kawai hakan yana zuwa ne daga Allah, yace "Toni ce maka nayi daga shed'an yake zuwa, kudai kuna da baqin hali, wato bane Auran y'an d'akinku ko, HEESHAM yaja numfashi yace, yanzu me to kake san ayi, yace "So nake kagayamin wanda yake santa na basa hak'uri ya nemi wata a dangi tunda ga matan da yawa, kaga kowa saiya cire wannan tunanin irin nawa akan y'an d'akin ita kakar taku Sa'adatu, kaga shikenan sai in had'a da auran su Hannatu dana Saminun na bashi NUWAIRAN ba shikenan ba....

HEESHAM najin haka ya tashi ba magana ya saka takalminsa Babah Alhajin yana cewa, kadawo ina zaka ne bamufa gama gamanar ba, amma HEESHAM ko kulasa baiyi ba ya qara gaba abinsa, yau ko shiga cikin gidan baiyi ba, danshi yafi kowa sanin Babah Alhajin, har cikin gidan zai iya binsa, yanzu yanzu sai ya juye zance tunda ya fara faɗin hakan, haka kawai yaje yayi mai salalan tsiya😂 danya san ba wani abun wahala bane yayi mai dad'in baki ya d'auke mai my NUWAIRANSA yabama Saminun🤣 ya kuma barsa da cizan yatsa...
Haka yayi saurin tada motarsa yabar unguwar dan ganinsa ya fitto daga falan nasa yana lekensa... Faɗi HEESHAM d'in yake abayyane, "Ai Saidai kata lek'ena, samun kaina ne dai bazakayi ba....😊
Yana kallan kiran Baba Alhajin na shigowa wayarsa amma yayi burus da kiran, dan yasan yana d'auka rok'arsa zaiyi ya dawo, yana cikin wannan hali saiga kiran wacce ta had'a rikicin wato NUWAIRAN, haka kawai yaji haushinta kamar ya gansu ita da Saminun suna hira.. Amma yana d'aukar wayar jin abin datace nan yasa ransa yimai sanyi... Cewa tayi.. "Barka da yamma mijina uban ƴaƴana, sanda ya lumshe yace "Barka dai my Auntii, fatan komai normal, tace "normal, Amma muryarka tayi min wani iri haka my dear, Yace "Auntii, kishinki ne ya kusantoni, tace "Kai haba, tun yanzu, bayan ba ganina kayi da kowa ba, yace "Hmm Zanji zafi sosai idan na ganki da wani, pls karki min hakan dan Allah.. Tace "zan kiyaye insha Allah. Yace "Gud, ina kan hanyar dawowa gida ne, tace "nima naga dad'ewarka ne yasani kiranka ko lafiya, yace "Ina lafiya amma akan sanki ba k'alau ba... Tace "Zan kwantar maka da hankali dazaran kadawo, "Toh Allah ya dawo dani lafiya, tace "Ameen.. sai suka ajiye waya a tare, shidai gaskiya baya san kowa yace yana santa, gwara ma Babah Alhajin ya kira mitin d'in ranar lahadin, gwanda ayita ta ƙare, Sam baya san yasha wata wahala a Soyayya...

Aiko koda ya dawo gidan da kalamai zafafa NUWAIRAN ta karb'esa dashi, tare da basa abincin daya dad'e baici ba ajerin abincikan da yake so, yako ji dad'i sosai, kamar ya rungumeta....


Akwana biyar d'innan NUWAIRA da HEESHAM sun b'ata juna da kalaman Soyayya, abin sai wanda yaji ya kuma gani, Ramlat HAIRANAH da Hannatu sun kasa gane dawa NUWAIRAN take zuba love haka, dan sha'awa take basu, tare dasan Susan waye wai shi wannan gwanin nata... Gefe guda kuma HAIRANAH taqi amsa kiran masoyanta dan momy ta gaya mata tad'an jinkinta fitta garesu😂.. Dan AHMAD zuwa yayi da kansa ya saka momyn agaba kan karta qara barin HAIRANAN fitta yayi mata maganar kamar zai mata kuka, atake tagane kishi ne yake damunsa, bataja ba, tace mai toh.. Lokacin HEESHAM nagun, murmushi kawai yayi..

Yau asabar kuma yau Baba Alhajin ya aikama da kowa kira kan gobe yana da taro yana san ganin kowa..
Ba wanda baiji kiran nasa ba, AHMAD dake tsaye da NUWAIRA Lokacin karfe goma sha d'aya da rabi ne na safe, gaya mata yake gobe Babah Alhajin tambayar kowa zaiyi acikinsu kowa ya yarda da masoyin nasa, NUWAIRA ta kallesa tace "Ya AHMAD bansan me HEESHAM zaice akaina ba, gashi ya qara dulmiyar dani akan sanshi, yazanyi, yace "gaya miki ne banyi ba, HEESHAM ya gane sanshi kike, kuma tunda kikaga ya baki wannan goyen bayan shima yana sanki ne, dan haka karki damu bazai tab'a kawo miki matsala ba awajen...



Tace "ina fatan hakan ya AHMAD, yanzu ya batunka da HAIRANAH, Yace "yana nan, ai dan saboda ita ne nasa Babah Alhajin kiran wannan taran, kishinta yana damuna sosai sister, tace "Ai yanzu tadena kula samari, yace "Momy ce tayi mata magana ai, Tace "Oho, shiyasa naga tadena fittan, yace "Wannan shine dalilin, tace "Wallahi Ya AHMAD nidai bana san ka had'asu waje d'aya ita da MEENATU, haka kawai jikina yake bani za'a samu matsala, yace "Ki bar batunfa samun wannan matsalar, nagaya miki zasu zauna lafiya.. Tace "Toh Allah yasa...


Da Dare da misalin qarfe takwas da rabi, HEESHAM ya shigo falan nasu da alama daga masallaci suke shida abokinsa Jabeer, sam hankalin HEESHAM nagun NUWAIRA bai duba da suwa take tare ba? Kawai ya nufeta wacce ita karanta wani novel na RAHAMA NALELE takeyi me suna *KATAR KAMAL*, ya zauna kusa da ita Yace "My Love, wane Nobel kike karantawa, tace "Sweetheart MATAR KAMAL nake karantawa, sabon novel na RAHAMA RUFA'I NALELE ne.. Yace "Wow kinsan ko Aunty nace, tace "Karkacemin ka tab'a karanta novel nata, Yace "Na karanta MASIFAR SO, yayi min so sweet, tace Kaga nima na karanta AMAKIRCI NAH, da HALIN WASU MUTANAN, da SADEEQ, da Y'AR ƘAUYE KO Y'AR BIRNI.. "baki karanta LIKITAN ZUCHIYA da SAMARIN BANAH ba ko, "Tace ban karanta su ba, "Yace sune basuyi daɗi ba🤨, karki karanta pls.. "Tace "Banzan karanta ba my love, yanzu kaci abinci, Yace "Me kika girka min.."Abin daɗi mana.. "toh zanje naci yanzu, Allah yasa da yawa na samma abokina, tace "Ai baka rowa ko ba yawa zaka sam mishi, yace "Indai girki naki ne kar kiyi mamaki dan zan iya hana kowa da gaske, NUWAIRA ta kalli Jabeer dake musu dariya tace "Toni dai ba ruwana dan yana bayanka yana jinka, juyawar nan da zaiyi yaga HAIRANAH da Hannatu Ramlat sun zuba masu ido, ya maida kallansa ga NUWAIRAN yaga itama kallansu take, alama dai ta nuna itama zubar tadinga yi batare data tuna suna tare da ita ba..
Saiya tashi yana cewa "Sannunku, HAIRANAH tace "Dama dakai Aunty NUWAIRA take hira..
Yace "Aa, inaga da wani can takeyi.. Yana faɗin mata hakan yaja Jabeer suka bar wajen.. Ramlat ta matso kusa da NUWAIRAN tace "ƴar-uwa, gayamin HEESHAM shine wanda kike Soyayya dashi, cikin murmushin yaƙe tace "bashi bane, "Toh amma me yasa ya kiraki da my love, "Au wai dama ke sai yau kika tab'a jin ya kirani da sunan, tace "Amma abin da d'aure kai yake, tace "Mamaki kawai nake san baku Allah dai ya kaimu gobe, tana gama gaya mata hakan tatashi tabar falan, Ramlat

Please Login or Register in order to submit comment