Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan kuma Sani abokinsa ya shigo d'akin...
MEENATUN ta gaida shi a sanyaye, ya kalleta da cewa, "Amarya sai hakuri kaddara tayima amarcinku yankan ƙauna, bare muzo mu kwashi girkin amarya, tayi murmushi da faɗin, "Yauma kamar kullum da kake fadin hakan, indai abincina ne zaka cisa insha Allah, fatana dai mijina ya samu lafiya in baka mamaki..
Yace "Jiki kam Alhamdulillah, gashi yana kyau, nan kusa ai zaki gammu bar sauri..
Tashi tayi kawai tana meyi mai murmushin yaƙe, kana ta ficce daga d'akin..
Sani ya kalli AHMAD yace, "Abokina ya jikin dai, AHMAD yace " Da sauƙi, yace "Toh madalla, dama ina san na tambayeka HAIRANAH ne, gaskiya Abokina SO da ƘAUNAR yarinyar ya kamani, tun ran dinner naku, ina santa AHMAD dan Allah kamin hanyarta..

Tunda sani ya faro maganarsa yana ambatar HAIRANAH gaban AHMAD ya yanke ya fad'i, nan take yaji baya santa da Sanin, toh me yake damunsa, yaji baya santa da Hashim dan munanan halayen Hashim d'in, amma me yasa yanzu yaji baya santa da Sani, bayan yafi kowa sanin Sani cikin abokansa yana da hankali nutsuwa hali mekyau, sam bashi da wata makusa, bashi da wani mugayen d'abi'u.. Wai me yake damunsa ne akan HAIRANAH, haka fa idan tazo dubasa idan abokansa sukazo gaishe shi idan yaga suna kallan HAIRANAN ransa b'aci yake sosai, yana mamakin hakan, dan bayajin hakan akan MEENATU da NUWAIRAN dayake b'ab'atun yana so, amma saiya dinga jin hakan akan HAIRANAH...
Ahankali ya kalli Sanin yace dashi, "Gaskiya kayi hakuri Sani, Bansan me zance maka ba, amma kasan mu bama Auran bare, idan ka damu zuciyaka da san HAIRANAH zakayi asarar lokacinka ne kawai, qilama yanzu Baba Alhaji ya had'ata da wani bamu sani, amma kayi hakuri..
Sani yayi shuru, dan gaskiya ya kwallafa HAIRANAH aransa, haka dai ya kad'a kai, yace "Zanyi Addu'a idan rabona ce zan sameta idanko ba rabuna bace nasan bazan sameta ba..
Shuru AHMAD yamai kawai...


MEENATU ko wajen shaqatawar gidan tanufa, tahau safa da marwa a wajen, ranta nayi mata suya, can taga kiran wayar qanwarta HASEENAH, aiko cikin sauri ta d'auka da "Hello, HASEENAH taja numfashi tace "Gani na kusa qarasowa gidan momy, ki gayamin inda kike kawai, dan bana san na fara haɗuwa da wannan shegiyar yarinyar..
MEENATU tace "ina wajen shaqatawar gidan, kai tsaye kina yin parking kishigo wajen. "Toh.. Shine abin data ce mata... Aiko MEENATUN bata wani dad'e ba taji shigowar motar HASEENAN saita ja d'aya daga cikin kujerun wajen ta zauna, HASEENAN ta shigo wajen itama taja wata tazauna, tana cewa, "Yana ganki haka kamar da b'acin a attare dake.. MEENATU tace, "Hmm kedai bari, nan ta kwashe komai tagayama HASEENAN sannan taqara da cewa, wallahi idan zanyi yawo tsirara bazan bar AHMAD ya Auri NUWAIRA ba, dan idan ya Aureta na kad'e, kallo d'aya zaki musu ita da HAIRANAH kisan yaran karuwai ne, kallansu ma irin na munafukai ne, HAIRANAN nan ga tsinan nan rashin kunyar tsiya, dukkansu na tsanesu bani sansu, dama ko baki gayamin gaki nan ba nayi niyar kiranki dan kizo kiji ki gayama momynmu...
HASEENAH tace "Lallema, ammako AHMAD d'in nan bashi da mutunci, shi yanzu tsakaninsa da Allah idan akace ya qara Aure ko nan da shekara goma ne ya qara... Tace "kinma kaisa da nisa, a shekara d'aya yake san yin rayuwa da mata biyu.. Yanzu dai pls kije ki gayama momyn tamu, gobe duk yanda Ake ciki sai kizo ki gaya min.. HASEENAH tace "Toh, wallahi ba ƙaramin tsanar HAIRANAH nayi ba, "ke dai kibari na tunkud'e matsalata naki me sauƙi ne..
Shuru HASEENAH tayi ma MEENATUN, can dai tasake sukaci gaba da hirarsu tayau da gobe, kana MEENATUN tace mata su tashi su shiga ciki, suna shiga falan gidan sukaga maƙiyan nasu wato su NUWAIRAN, momy ce dai Kawai bata falan, tana can wajen AHMAD..

Kallo d'aya NUWAIRA tama HASEENAH tad'auke kanta..... Dama HAIRANAH ko kallansu batayi ba tunda tagane sune, Ramlat da Hannatu ne kawai suka kulasu...
HASEENAH tatab'e baki da gallama HAIRANAH harara, dan a duniya da gaske babu wacce ta tsana sama da ita, bata san HAIRANAH sam.. Haka dai sukayi d'akin AHMAD d'in dan HASEENAH ta gaidashi...


Lokacin da HASEENAH tajema da momynsu da maganar da suka tattauna da MEENATU hankalin momyn nasu ya tashi sosai, matace me kwad'ayin tsiya, tana san yaranta duk su Auri Yaran Dadynsu HEESHAM dan ganin duk yafi qannan nasa kud'i, kuma Ga yaran nasa kowa yana gama karatunsa yake samun aikinsa..
Wannan dalilin yasa taso MEENATU da AHMAD, HASEENAH kuma da Sadeeq amma sai HASEENAN ta nuna ita tafi san HEESHAM..
Sanda tahad'a da aikin boka suka samu kan AHMAD, danshi yana da wacce yake so tun Soyayyar skull, amma lokaci d'aya yaji yarinyar da yake so yaji tafitan masa arai, gashi dai yana dasan ibada amma sanda asirin yad'an shafesa kad'an haka, shiyasa yad'anji san MEENATU kad'an haka aransa, data shige mai kuma saiya gaya mata zai Aureta amma da sharad'in bada ita kad'ai zaiyi rayuwa ba, dan shi dama bashi da burin zama da mace d'aya kamar wani Maraya😂 shi baima yarda mata zasu iya caja kan namiji arayuwar Aure ba, bai yarda ba sam, (Rahama Nalele tace zaka yarda AHMAD)..
Toh wannan shine dalilin dayasa yanzu ya nanatama MEENATU kan basuyi zaiyi rayuwa da ita ita kad'ai ba..

Momyn ta kalli HASEENAH dakyau tace "zani wajen wani malamj me aiki yayi min aikin da babu Aure tsakanin AHMAD Da NUWAIRA haka babu tsakanin HEESHAM da HAIRANAH..
HASEENAH tarungume mahaifiyar tata tace mata tana santa sosai...
Aiko babu b'ata lokaci tare da HASEENAN sukaje wajen bokan data kira malami.. Yayi muku surkullansa yace ai dama babu Aure tsakaninsu dukka..😂
Sai hankalin momyn nasu ya kwanta dana HASEENAN..
Haka suna dawowa HASEENAN ta kira MEENATUN tabata labarin komai, sai hankalin MEENATUN ya kwanta..


HEESHAM yana hospital aiki yakeyi hankalinsa nacan wani waje daban, dan ya karanta part 1 d'in wani novel na Rahama nalele, wato SAMARIN BANAH, acikin wani group da yake a WhatsApp aka turo document na novel d'in, gaskiya labarin ya tsaya masa arai matuƙa, Allah Allah yake lokacin tashinsa yayi yasamu nutsuwa cikin dare yakai ƙarshen labarin..
Aiko yana tashi qarfe shidda yayi gida ba wanda yasan da dawowarsa, dan shima kofa biyuce dashi, data waje data ciki, wanka yayi da d'auro alwala ya gyara kansa yayi masallaci, sanda akayi sallar isha dashi kana ya dawo, yaje ya duba Yayan nasa AHMAD, yaga jikin da sauqi sosai, dama anan yaga Momy sai yayi kitchen ya ibi abincin dayaga zai iyaci yayi part d'insa, dan zumud'i ko abincin baici ba ya fara karanta cigaban labarin..
Sai kusan qarfe goma sha biyu da rabi na dare yakai ƙarshen labarin... Tunda yake bai tab'a karatu a online ba sai sanadin SAMARIN BANAH, kuma bai tab'a ganin Mara kunyar Marubuciya kamar Marubuciyar ba... "Tab amma wannan writer kinyi b'arna, ya Faɗi hakan a bayyane, ganinsa Marubuciyar tayi rashin kunya da rashin tarbiya sosai a labarin, bai dace ta faɗi wasu abubun ba.. Dan shi harga Allah bai tab'a tsintar kansa cikin wani hali ba, amma sanadin SAMARIN BANAH ya tsinci kansa a cikin wani halin, zai kirata ya yabama basirarta dan daga yanayin rubutanta yasan ta'iya novel bazadai ace bata iya ba sannan baza'ace ta iya sosai ba..
Daga baya idan ya gama yaba mata ya nuna mata bai dace da ita y'a mace ta dinga rubuta abubuwa haka ba..
Nanya sebern number nata, danta saka a qarshen labarin, Akan Dp nata yaga bayan SAMARIN BANAH har tayi LIKITAN ZUCHIYA da HALIN WASU MUTANAN.. Ko su me suke d'auke dashi, nan ya duba HALIN WASU MUTANAN dan da aka tashi turo SAMARIN BANAN dashi aka turo, ya bud'e yaga ainihin sunansa tantiranci, daga baya ne tacanja mai suna yana ganin hakan ya fitta..

... Shi harga Allah ayanzu yaji sha'awar Auran wacce ta girme masa, kasancewar a labarin SAMARIN Auran way'anda suka girme musu sukayi..
Haka badan ya tsinci kansa cikin najasa ba, haka ya tashi yayi wanka kana yadawo yayi sallar lafuna Raka'a goma sha biyu Sannan fa ya tuna da abincinsa, kuma a wannan Lokacin yaci..

Washe gari Monday da misalin qarfe bakwai ya gama shirinsa na zuwa asibiti, sai ƙamshi yake, kallo d'aya zaka mai ya baka sha'awa dan tsaftarsa da iya wankansa, ga uwa uba qamshinsa.

Ba tare da b'ata lokaci ba haka ya lalubo number na Rahma Nalele ya hau kiranta, lokacin Rahama na falo, dan tunda tayi sallar asuba da laziminta bata tashi ba, ta zubama TV ido, tana kallan tashar ZEE WORLD, wanda awanan lokacin k'arfe bakwai d'in ana tsaka da maimaita wani film dinta me suna twist of face.. Tana tare da ƙanwarta, taga kiran nasa, tad'auka da mamakin makarantanta, kira ba dare ba rana, "Assalamu'alaikum... HEESHAM ya fad'i ahankali... Aiko nan take gaban Rahama ya fad'i, dan ji d'ayan da tama muryar tasa tasan yau kuma tatashi da kiran SAMARIN BANAH...😂 Saboda tana ganewa abu yau da kullum.. Tace "Wa'alekumussalamu.. Yace "Yauwa ina magana da Rahama Nalele ne ko Auntyn Luv, cikin damuwa Rahama tace "Dukka.. Dan tana tare da ƙanwarta, kuma bata san tasan ba da mace take waya ba, ita dai tayi kuskuran saka number nata tun farko a novels nata..
HEESHAM yaja numfashi yace, "Haka kikema masoyanki magana a gajarce, Rahama tace "Eh wani abu ne..😟 wayasaki kiran number nawa bayan nace miki karki kuskura ki kirani ban Faɗin muku hakan bane..
HEESHAM yayi shuru, can ya gane me take nufi, yace "Ok zan kiraki anjima sak'o zan baki da alama akwai wani akusa dake na barki lafiya..
Rahama ta ajiye waya da sauke ajiyar ZUCHIYA, ita magana ta gaskiya bata san fans nata maza su dinga kirata ko suna damunta a message, tasaka phone number nata ne kawai dan fans nata mata, amma dole sai mazan sun kira, koda ko zatayi rashin mutuncin wasu zasuce sai sun kira, amma tagane wannan yaran yana da wayo... Qanwarta ta kalleta tace "ke da waye haka, tuni kwakwalwar Rahman ta kisa mata tace, "ni da wata ƙawata ce, bana santa, naja mata kulle kan tadena kirana bataji, tace "babu kyau wulaqanci Aunty Hajju, idan kinsan bazaki iya dasu ba, toh ki kulle Layin naki Kawai mana, tayanda bame samunki, bare ya zargeki... Tace "Tun farko nayi kuskure ne, y'an uwana sunfi sanina da layin ne, sai banyi tunani ba na rabama fans nawa ita, amma zan kulle insha Allah dazaran na gama kwashe numbers nawa, dan shawararki itace akan layi... Tayi murmushi da cewa hakan ne idan kikayi zaki samu sausauci... Kinga Saidai kawai kudinga yin catin naki da mutane, tunda kinfi buqatar hakan, kira kuma sai kiyi da Way'anda kike tare dasu sosai, zama ki iya basu saban layin naki..
Tace "insha Allah babu ja'inja hakan zanyi..


HEESHAM ko idan tunaninsa ya basa daidai, ba mamaki tana dare da mijinta ne ko iyayenta.. Idanko tana da miji nasihar dazai mata zatafi shigarta...
Haka yayi shashin Momy ya gaisheta, kana yayi dining danyin breakfast, NUWAIRA ce kawai yagani awajen..
Yaja kujera yana cewa "Auntii kin tashi lafiya.. saita zubamai ido, dan dama shine yasata fittowa da sassafe, jiya haka bata gansa ba gaskiya zai fara sa mata ciwo, dan tana jin bacci haka ta hana idanta baccin safen dan kawai tagansa hankalinta ya kwanta, kuma da gaske har wani zazzab'i ne ya kamata..
Auntii me yake damunki ne... Ya qara fadin hakan a gareta... Ai nan take tarikice tace, "Hmm Am me kace, ya mata kallan k'asan ido, batare dayace mata komai ba, ganin hakan yasa tatashi zatabar wajen yaci gaba da cewa, koma me yake damunki, ki d'aukesa ahankali gudun kadda kijanyoma Kanki wani ciwo..
Jikinta rawa ya fara dan haka da gudu tabar wajen, HEESHAM ya bita da kallo, tana da damuwa... Ya faɗi hakan a bayyane, daidai nan momy tazo wajen ta zuba mai abin datasan yana ci kana ta zauna tana cewa, "Ina NUWAIRA take, yace "tayi shashinsu, tace "Kuma banga tayi breakfast d'in ba, tun asuba tatashi take tayani had'awa, dan abin da kakeso ma itace tayi maka, kuma tayi min qorafin yau tatashi dajin yunwa, ya kamata dazo ta ƙarya ai..
HEESHAM yace, "nafa lura da ita momy kamar bata sakewa cikin maza tayi al'amuranta..
Momy tayi murmushi zata bashi amsa sai tayi shuru ganin Dadynsu ya qaraso wajen..
Zama yayi momyn ta had'a masa komai, HEESHAM ya durƙusa ya gaishesa ya amsa cikin kulawa da ƙaunarsa..
Kana momy taje kiran NUWAIRAN, amma tasameta tana toilet haka Ramlat tace mata, tana qoqarin fitta danyin breakfast d'in, HAIRANAH da Hannatu tunda suka kwanta bayan sallar asuba basu tashi ba, itama Ramlat d'in yanzu tatashi..

NUWAIRA kam kuka tadingayi sosai a toilet d'in, bata san HEESHAM ya gane tana sanshi, Sannan tana so taga suna Soyayya, amma fa bata san yasan tana maseefar sanshi, (Rahma Nalele tace zataga ikwan Allah)
Yanzu dai tasaka aranta bazata qara yarda magana ta qara had'asu da juna ba, daga nesa zata dinga kallansa tunda kallan nasa ya zame mata MASIFA...



Da rana da misalin qarfe biyu bayan HEESHAM ya dawo daga masallaci, ya qara kiran number na Rahma Nalele, lokacin tana zaune ita kad'ai, a d'akinta, ta d'auka da sallama yace "Nine saurayin d'azun nan wanda kika dangantani da y'a mace, sunana HEESHAM..
Rahma tagyara zama tace, "Toh meyasa ka kirani, Yace "na kiraki ne dan na jinjina miki akan basirarki, Sannan na tambayeki ke Matar Aure ce ko budurwa..
Rahma tace "Ni Matar Aure ce, Sannan dan Allah karka qara kirana.. Takai ƙarshen zancen nasa dasan kashe wayar tata dayin blocking nasa, ai tamkar ya ankare yayi saurin waro ido yace "Yanzu ke Matar Aure ce amma kake rubuta Littafi haka babu jin kunya..
Rahma tatsaya daga niyarta nasan kashe wayar, tace "me kake san cewa ne, me kake nufi, kana san kace...
Saurin katseta yayi wajen cewa, "Bani san cewa komai, amma amatsayina na K'aninki zan baki shawara, dayi miki nasiha dan gobenmu, wala Allah kin haifa, ko baki Haifa ba, amma nasan baza'a rasaki da y'anne ba, ina rokwanki da Allah bayan LIKITAN ZUCHIYA da tantiranci wanda kika canja mai suna da HALIN WASU MUTANAN karki qara rubuta novel da saka dukkan abin da kika saka ana baya, dan Allah badan ni ba, badan kin Sanni ba saidan kawai naji ina san ki zama Yaya agareni, dan haka kawai naji ina sanki a matsayin y'ar uwa agareni..
Rahma tayi shuru, tunda take rubuta novel bata tab'a jin wanda yayi mata roq'o akan hakan ba, nan take nadama ta qara shigarta, tace "Nagode HEESHAM kuma nayi maka alk'awari zan dena, nama dena, tana jin sautin murmushinsa yace, "Gaskiya banyi tunanin zan sameki ahaka me sauqin kai ba, Allah ya qara miki basira, kiyi Rubutu akan love zallah amma banda rubuta abubuwan da basu da amfani... Rahma tayi murmushi tace "Zan rubuta abubuwan daya dace anan gaba HEESHAM nayi maka alk'ari.. Yace "Gud kasancewarki Matar Aure bazan qara kiranki ba, amma duk ran da nayi Aure zan bama matata number naki kugaisa, Sannan ki gaishemin da Yayana.. Tace "Nagode sosai HEESHAM amma bazan saka number naka cikin wayata ba karya jamin matsala, amma insha duk ran da Allah yayi zaka Sadani da matar taka mu gaisa kana cewa HEESHAM ne zan gane, Nagode sosai.. Yace "Nine da godiya da kika fahimceni lokaci d'aya, zanbi next novel d'inki na gaba idan kika kuskure har dani acikin waƴanda zasu zageki.. "Hakan ma bazata faru ba HEESHAM, Nagode sosai, zanyi amfani da sunanka a littafina na gaba, dafatan babu matsala
Murmushi HEESHAM d'in yayi da cewa babu matsalar komai, tace "Toh Nagode, saiya kashe wayar tasa.. Nan kuma ya cire Num nata daga wayarsa, duk ran da yayi auran yaso sada Matar tasa da ita ya nemata acikin novels d'inta...
Haka kawai yaji dad'i aransa, ko ba kamai idan tagyara zai samu lada....




Hadai abubuwa suka dinga faruwa lokaci na waccewa...
Kowa da matsalarsa acikinsu, shidai AHMAD soyayyar NUWAIRA na damunsa, ga abokansa kusan mutum shidda sun damesa da maganar HAIRANAH, gaskiya ransa yana b'aci sosai, musamman daya gane yawan kula dashi da HAIRANAN takeyi shike sawa har abokan nasa suke tsintar kansu da santa idan sun ganta..
Hakan yasa yace mata tadena zuwa kulawa dashi ko gaisuwa ne baya so..
HAIRANAH tayi ZUCHIYA dan bata san meyasa shi gaya mata hakan ba, sai kawai tad'auke masa fad'a gabaki d'aya, tadena yini ma agidan kwata kwata, daya lura da hakan sai kuma yaji ya damu, bai san yama aka yaji yad'an shak'u da ita ba, dan yawanci idan zaicema MEENATU tabashi abu da HAIRANAN yake kiranta...
Dan haka cikin wayo da dabara yama HEESHAM dabara akan meyasa HAIRANAH bata yini a gidan, kamar NUWAIRA bata san hakan, Toh sanadin HEESHAM HAIRANAH tadawo kamar da amma tadena zuwa inda yake, dama shi hakan yafi so..

Yanzu dai yasamu lafiya, dan ya fara taka k'afar tasa yana me yawo a harabar gidan nasu da cikin layin nasu, kowa yaji dad'in hakan sai murna Ake tayasa musamman HEESHAM..

Yayin da ciwan SON HEESHAM yake barazanar tarwatsa rayuwar NUWAIRA, ta rame ta fige kana dai ganinta kasan akwai abin da yake damunta, kwata kwata bata jin daɗin komai arayuwarta, dan tasaka HEESHAM d'in sosai aranta, idan ta qara d'aukar lokaci ahakan komai zai iya faruwa da ita, danta janyema ganinsa, bata yarda su had'u, Saidai kaga tana leqensa zuciyarta nayi mata dad'i, dazaran kuma yabar gidan sai damuwa tace mata salamu alaikum, tambayar duniya kowa ya mata taqi bama kowa amsa Saidai tace kanta ne yake mata ciwo, sau biyu momy tana kaita asubitinsu HEESHAM ana dubata amma likitocin cewa suke kawai damuwa ce tamata yawa, da alama akwai abin da tasaka aranta yake damunta..
Da momy ta qara tambayarta qin gaya mata komai tayi, face cewa da tayi kawai kan natan ne yake damunta da ciwo
Har ran momy ya b'ace tace takoma wajen mama tunda ita bata isa da ita ba qila ta gayama maman nasu damuwarta..
NUWAIRA najin haka ta rungumi momyn tana kuka take ce mata tayi hakuri, tabbas akwai abin da yake damunta amma bazata iya fad'a ba, danta yima zuciyarta alkawarin bazata gayama kowa ba,
Kuma idan tabarta ta koma wajen mama damuwar zatafi mata yawa..
Momy najin hakan hankalinta ya tashi taji tausayinta ya kamata...
Bata matsa mata kan lalle saita faɗa mata ba nasiha dai tamata me shiga jiki kan tarage damuwar dan kar hakan ya harfar mata da matsala, Toh tacema momyn...

Amma momyn tasa aranta zata d'ora ido sosai akanta tagano miye matsalarta...

Shi kansa HEESHAM d'in ya tsinci kansa cikin damuwa da ramarta, da kuma canjin yanayinta, dan yana ganinta idan yazo wucce ta window nasu idan zai fitta, Sam bata sanin yana ganinta, tanan d'inne ya gane ramewarta..

To bare AHMAD, wanda dama shi ako da yaushe yake ganinta dan tana zuwa kullum duba jikinsa ta gaishesa, sau uku yana tambayarta me yake damunta bata bashi cikakkiyar amsa..

Ashe ta gayama mamansu abin da yake damunta, hankalin maman nasu ko ba ƙaramin tashi yayi ba, amma ta kwab'eta kan kadda ta gayama kowa abin da yake damun nata tadai dage da Addu'a ko Allah zai warware abun cikin sauqi, toh tace ma maman nasu..


Ana cikin haka yau AHMAD ya fitto wajen shaƙatawar gidan.. Yana takawa kamar dai yanda yake da, tabbas ya samu lafiyar qafar tasa, amma gaskiya bazai koma aiki ba sai yaci amarcinsa, tunda gobe ne zai gayama momy akai MEENATU can gidan nasa, zai bari sai bayan sati d'aya ya koma aikin.

Dake wajen shaƙatawar yana da kusurwa da yawa, bai zama lalle kana shigowa kasan wani yana wajen ba, ko wanda yake wajen yasan da shigowar wani wajen ba, musamman idan ya shigo batare da magana ko wani hargawa ba, hakan ce tasa AHMAD shiga wajen NUWAIRA bata san ya shiga wajen ba...
Rike take da wayarta ahannunta idan nan nata sai zubar hawaye yake, duk ta jik'a fuskar wayar da hawayen nata, kallan hotan HEESHAM takeyi kawai tana wannan hawaye, Sai kuma akayi sa'a shigar AHMAD wajan kenan tafara sambatu kala kala kamar haka, "Dan Allah HEESHAM kaji kana sona ko sau d'aya, Wallahi sanka da ƙaunarka zasu iya kasheni wata rana, dan gashi sun hanani samun nutsuwa sun hanani samun kwanciyar hankali, bani da wani farin ciki bace ganinka, gashi illar tayi min yawa har tasa nake kishi da duk macen da naganka tare da ita, tana kaiwa nan tafashe da kuka wiwi, tana cigaba da cewa, Y'ar uwata HAIRANAH nafara jin tsanarta saboda kai, bana sauraran duk wani zance nata sabo dakai meyasa kake santa bayan ita ba sanka take ba nice me sanka ni yadace kajuyo ka kalla ba ita ba, dan So take maka irin nako oho, haka kaima irin kake mata, dan Allah kajuyo ka kalleni kaji aranka ina MASIFAR SONKA,
Wallahi ji nake Nafi kowa sanka aduniya harda iyayanmu...
Bana san kowace y'a mace indai zata kulaka, nayi Addu'a nayi kuka amma sanka qaruwa yake araina... Takai ƙarshen zancen da qara fashewa da kuka, abin gwanin ban tausayi..


Kan AHMAD ne yaji ya Sara masa, nan yayi saurin dafewa da lumshe idansa, ba abin da yake cewa aransa sai Innalillahi-wa'inna'ilaihirraji'un..
Ahankali yaja kujera ya zauna..
Jan kujerar da yayi shiya ja hankalin NUWAIRAN tata shi da sauri tana kallansa tare da saurin boye hannuwanta baya, hankalinta ya bala'in tashi, daga yanayin kallan da yake mata kad'ai tasan yaji komai na sambatun datakeyi...
Nan taja kujerar da take zaune baya, tafara nufosa tazo gabansa ta tsaya duk jikinta na rawa taci gaba da cewa, "Dan Allah Ya AHMAD ka rufamin asiri dan Allah...

Yaja numfashi da cewa... "Yanzu NUWAIRA dama matsalarki itace HEESHAM, shine kikaqi gayama kowa kika gwammace gwara ki fad'a ciwo dadai ki gaya ma wani, kin san me ake kira lafiya kuwa, kinsan ya lafiyar take ajikin ɗan-Adam kuwa..
NUWAIRA tamai shuru in banda kuka, yaci gaba da cewa, HEESHAM baisan kinayi ba, yana da tausayi sosai, nayi imani koda ace gab yaje da'a d'aura mai Aure da wacce yake so zai iya yakice wacce zai aura ya Aure ki.
ranar nagansa cikin damuwa na tambayesa meye yake cemin ya rasa me yake damunki, kina da damuwa amma baya tunanin zaki iya gayama kowa, dan ya lura kina d'aya daga cikin matan da suke b'oye abu aransu..
Toh ni yanzu zan gaya masa cewa shine damurki, shikenan.. Ai NUWAIRA najin hakan ta durƙusa ta kama qafarsa tana cigaba da kuka tace "Dan Allah Ya AHMAD karka gaya masa, nidai bani da abun so kamarsa amma bani san yasan ina sanshi, dan Allah kabarshi yazo gareni da kansa..
"Baki da hankali NUWAIRA, tayaya kike tunanin zaizo gareki bayan baisan manufarki akansa ba... AHMAD ya katseta da faɗin hakan, cikin tashin hankali tace "wallahi Addu'ata bazata tab'a faɗuwa ƙasa banza ba Ya AHMAD, ni ina ji ajikina zaizo gareni da batun Soyayya, dan yana da zuciya, zaiji ajikinsa yana tare da wacce take matuwar sanshi, wallahi ban tab'a san wani abu aduniya kamar HEESHAM ba, neman zautar dani yake, mezaisa kace bazaiji hakan aransa wata ranah ba.. Dan Allah dan Annabi karka gayama kowa amma kana da damar da zaka iya temakona takowace hanya, amma karka gaya masa pls na rokeka..

Tausayinta ne ya kamasa sosai, dan shi baima tab'a sanin so yana wahalar da mutum haka ba, duk da shi yasan miye so dan yayi lokacin da yake karatu, amma bai dauka akwai mutanan da suke yin so irin nata ba..
Tashi yayi da juya mata baya yace, "bazan gayama kowa ba amma kisani dole a ƴan kwanakin nan ki dinga bar masa alama na abubuwan da zaki dunga barinsa cikin tunani, amma kika bari ya ganoki nasan waye HEESHAM yana da wayo sosai zai iya baki wahala dan haka ki kiyaye, idan naga kin kasa zan dinga cusasa gareki, idan kikaqi k'arb'arsa wallahi zan gaya masa kinji na rantse..
Tace "Zanyi duk abin da kace.. Yace "Gud, Sannan kidinga cin abinci akan lokaci dan kullum naga momy tana miki qorafi.. Tace "bana iya zama a inda yake, Sannan idan nazo zanci abincin tunaninsa baya iya barina..
Juyawo yayi ya kalleta ta sunkuyar da kanta, yace "Idan baki rage sanshi ba ya ganoki HEESHAM zai baki wahala, dan idan yace saikin gayamai da bakinki saikin gaya mai, dan nasan wainaki zaitayi lokacin da zakije kice kina sanshi ba sani zakiyi ba, dan haka kirage sanshi ko kad'an ne..
Tace "toni ya zanyi na rage, yace "Yauwa idab kina b'ata awa Ashirin kina tunaninsa,

Please Login or Register in order to submit comment