Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikata hakan, ta aikata hakan ne saboda cin amanar da HEESHAM yayi mata, wacce irin Soyayya ce basuyi shida ita ba, amma dan tsabar cin amana yazo ya Auri NUWAIRAN yaqi Auran ta......

Cikin fusata, cikin jin haushi, cikin tsanarta da komai nata momyn HEESHAM tatashi cikin tsawa ta katseta wajen cewa, "Dakata dakata malama, uban waye yace miki HEESHAM yana Soyayya da HASEENAH, yau she ya tab'a bud'e baki yace yana santa, ina nan take zuwa gidana da k'okwan baranta kan ya karb'i Soyayyar dan Allah amma yake ce mata shifa baya santa, taje cikin masoyanta ta fitta wanda yake santa ta Auresa dan shi a gaskiya baya santa..
Bata tab'a zuwa ta gaya miki hakan bane, toni akan idona hakan take faruwa idan ke baki sa'ni ba...
Nan jikin momyn nasu yayi sanyi, kana dai gani kasan babu gaskiya a cikin al'amuran nata...

Sam batayi tunanin momyn HEESHAM d'in zata hayayyak'o mata haka ba, dan sanin da tayi mata kan mace ce me matuƙar hak'uri da shuru shuru.

Nan dai wata a dangi ana kiranta da Aunty Naja'atu tace "wannan ma wata irin banzar wujja ce, wane irin zancen banza ne zancen hofi, zancen y'an iska y'an tasha marasa imani da tarbiya, ace ma da gaske HEESHAM da HASEENAH sunyi Soyayyar, wannan shi zaisa HASEENAN dan rashin kunya taje ta kashe masa d'a har cikin gida saboda tafi kowace mace kishi da baqin hali a duniya...

Dadyn su HASEENAN Ya girgiza kai da tsaida kallansa akan momyn nasu yace "Wato dama duk wannan abun da yake faruwa da saninki shine kikayi kunnan uwar shegu kikaqi fittowa ki fad'a saboda tsabar baqin hali da d'ora yaranki kan mummunar turb'a ko...
Baki san dama hak'urin zama nake dake ba, Hmm kije na tsakeki saki uku ba Aure tsakanina dake....
Babah Alhaji ya girgiza, ko kad'an baiji dad'in hakan ba, amma hakan shine ya dace da ita, tunda ita muguwar uwa ce, me d'ora y'ay'anta akan mummunar turb'a...

Ba abin da HAIRANAH dasu Hannatu sukeyi sai kuka, kuka sukeyi sosai tare dajin tausayin HEESHAM da NUWAIRA, gefe guda kuma basu da abin tsana kamar HASEENAH...

Haka mamansu NUWAIRAN da Babansu ma, gaskiya lamarin ya shigesu sosai...

NUWAIRA da HEESHAM dai ba magana, dan shi HEESHAM d'in ma kula yarinyar HAIRANAH yake Ummi wacce ta d'ane kan cinyarsa sai mai magana tasu irin ta yara take. Yayin da NUWAIRA taqi d'auke idanta akan HASEENAN...


Babah Alhaji yaja numfashi zuciya cike da b'acin ran yanda komai ya faru yace "HASEENAH ta aikata aiki mefi muni a rayuwarta, kuma hukuncinta kisa ne, ba abin dazan iya cewa akan hakan.
Ina dai qara bama HEESHAM da NUWAIRA baki akan su kwantar da hankalinsu Allah shiyasan me yake nufi da hakan daya bari har hakan ta faru dasu, fatan mu hakan ya zama alkairi ayanzu dama can gaba, Allah ya muku albarka ya albarkaci rayuwarku ku samu yara masu albarka ya kareku daga sharrin maqiya, Baba Alhajin yakai ƙarshen zancen da kallan HEESHAM da NUWAIRA, nan suka sakar mai murmushin yaƙe da amsawa a zuci, dangin ko suka amsa musu a bayyane..

Nan AHMAD ya gyara zama ya nuna malamin HASEENAN yace "Wannan kuma da kuka gansa shine malaminta wanda shima yake bata gudun mawa wajen cimma burinta, shine bayan ta yanka d'an HEESHAM d'in takaimai gawar, anan dai yasan abin da yayi da gawar amma bara ya fad'a da bakinsa kuji...

Kuka wiwi dangi suka fashe dashi shima suka shiga tsine mai..

Shugaban y'an sandan ya kwantaramai wata sanda damai tsawa akan ya bada labarin yanda yayi da gawar..
Nan ya fadin musu saida gawar yayi ga wani abokinsa me Siyan yara yana tsaface tsafacensa dasu..

Atare hawaye ya zuboma Dadyn HEESHAM da Baba Alhaji, jin amsar daya bayar...

Nan shugaban y'an sandan yace ya gaya mai inda za'a samu abokin nasa.
Aiko nan babu b'ata lokaci ya fadin masa, nan atake yasa wasu yaransa suje su kama masa shi.

AHMAD ya qara bada labarin Sadeeq yana asibiti, da dalilin daya kaisa asibitin, yanzu kam HASEENAH tsoro tasoma bama kowa..

Shugaban y'an sanda ma ya tabbatar ma da AHMAD way'annan mutanan da aka kama a gidan HEESHAM jiya sun fad'a ba wani abu sukeje yi ba kawai sunje kashe HEESHAM d'in ne, kamar yanda HASEENAN ta umarcesu...

Nan AHMAD d'in ma yake sanin wannan sabuwar mah..

Kowa qara jinjina kai yayi kawai, wai ace duk mace ce da wannan aikin, wacce batakai shekaru talatin ba.....

Nan dai Baba Alhaji yace baya san ganin HASEENAH da malamin nata ayimai gaba dasu..

HEESHAM yayi zarab wajen cewa "Wallahi baba Alhaji idan ba'a kashe HASEENAH acikin satin nan ba, toh wallahi ni zan kasheta da hannu na, dan nasan munafuncin qasarmu, za'a iya fittowa da ita idan aka zaga ta bayan gida...
Shugaban y'an sanda yayi murmushi da cewa, "wallahi idan kaga ba'a kashe HASEENAH ba bana numfashi, dan aduniya kaf a yanzu ba abun dana tsana kamarta, tunda nake ban tab'a cin karo da mace me baqin hali irin nata ba, komai ma zaka iya fad'a indai akammu ne bazanyi maka musu ba, ayau d'in nan zan tura zancen kotu, kasancewar dukkan shedu sun bayyana nasan kwana biyu yayi yawa a zartar mata da hukunci.. Yana zuwa nan a zancen nasa ya tasa qeyarta data malamin nata yayi gaba dasu...


Ashe NUWAIRA ta dad'e da ficcewa daga falan, tana can ƙofar gidan gidan tana jiran fittowar HASEENAN, hakan yasa tana ganin fittowarta a yanzu tayi saurin shan gabanta ta d'aga hannu ta tsinketa da wani mahaukacin mari, kan tadawo daga hayyacinta takai mata wani mugun naushi a daidai bakinta wanda yayi sanadiyar zubewar hak'uranta guda shidda nan take..
Cikin matuƙar tsana tayi wani nishi dayi mata wata muguwar cakuma, tahau jijjigata tayi wurgi da ita jikin bango ji kake gab tayi muguwar buguwa...
Hakan baima NUWAIRA ba tayi wani kukan kura zata haye kanta HEESHAM ya shiga tsakani yana cewa.. "Yauwa my Auntii, ko ba komai kin nuna mata shuru shuru ba tsoro bane kawai gudun magana ne, Kin nuna mata baki jin tsoranta ko kad'an...
Yanzu gaya min me kike ji aranki dangane da ita...

NUWAIRA ta rungumesa cikin kuka tace "Wallahi Luv, ji nake kawai na kasheta na huta saboda tsabar tsana, wallahi na tsaneta bana santa, kubani wuqa nima nayi mata yankan rago...

Hawaye ne ya zuboma shugaban y'an sandan da yaransa suka girgiza kai dan sun san babu dad'i ne fa a zuciyar NUWAIRAN, shiyasa suka barta tayima HASEENAN yaga laga kafin a zartar mata da hukuncin..

HEESHAM ya d'ago da fuskar NUWAIRA ya shiga lashe mata hawayen cikin so da ƙaunarta cike da muradi yace "kwantar da hankalinki Matata, komai yazo ƙarshe, dan bata yanda za'ayi yawan jama'ar nan su tsine mata bataga bala'i a rayuwarta ba, qila kafin muyi wani kyakyawan mutsi Allah yayi ikwansa akanta, ni dai nayi miki alƙawarin idan har ba'a kasheta ba ni zanbi dare da rana na kashe miki ita...

NUWAIRA zata kalli inda HASEENAN take sai HEESHAM d'in yayi saurin juyo da kallan nata garesa yana cigaba da cewa... Bana san ki dinga kallanta..
Sai kawai ta kwantar da kanta akan qirjinsa tana cewa, "Muje gida Luv, muje kaban nutsuwa da kwanciyar hankali, wallahi ina jina ina shiga cikin wani hali, yace "Na gani my Auntii...

Nan shugaban y'an sandan ya qara gaba dasu HASEENAN.. Sai HEESHAM d'in yaja NUWAIRA ciki inda su Baba Alhajin suke, kowa sakama rayuwar tasu albarka yayi dajin qaunarsu aransa, kana HEESHAM yama su Momy da Baba Alhajin sallama suka bar gidan...


HASEENAH ko suna sauka a kofar y'an sandan, ta nemi arcewa duk da hannunta da ankwa, Saidai karyawar wata kwanar da take tunanin idan tayi zata fara samun tsira kawai ba zato ba tsammani saiji tayi taci karo da wani situriti karfan jami'an tsaran, ya huda mata ciki har baya tare dayin sama da ita, nan take ya rabata biyu..
Allah sarki abin dai babu kyan gani sam, dan dama su jami'an tsaran da sukaga tayi wajen sun tabbatar takai kanta da kanta inda mutuwa take ne, shiyasa Sam basubi bayanta ba..

Nan wasu cikinsu suka je suka d'auki mummunar gawar tata...
Sannan suka qarasa ciki da malamin nata..

Kana shugaban y'an sandan ya kira AHMAD ya gaya mai abin daya faru..

Dake AHMAD d'in har lokacin yana Gidan Baba Alhajin nan ya gayama Babah Alhajin abin daya faru, Babah Alhajin ko ya gayama kowa na wajen, nan dangi kowa yaji HASEENAM ma ta mutu kan a zartar mata da hukuncin..

Ba wanda ya shiga damuwar hakan saima Allah shi qara da wasu ke cewa, momyn su MEENATUN ce dai ta fad'i, toh ga duka ga tsinka jaka, tana cikin jin zafin sakin da mijin nata yayi mata gashi kuma wai HASEENAN ta mutu, duk da dama tana sane da dole a kasheta, amma magana ta gaskiya taso tayi ban kwana da HASEENAN, kasancewar itace yarinyar datafi so aduk cikin yaran nata..

Wannan faɗuwar da tayi tajawo mata shanyewar b'arin jiki.
Sam uwarta data haifetama bata ji komai ba dan gane da hakan ba, dan tunda taji abin da HASEENAH tayi a Yanzu taji ta tsani maman nasu, toh idan ita bataji komai ba, waye zaiji... ( rahama nalele tace MEENATU mana)

Ina MEENATU gabaki d'aya hankalinta baya wajen, Sam bata damu da fad'uwar uwar tata ba, tafi damuwa da gidan Auranta...
Bata san mijin nata ya saketa, bata so..


Ramlat da Hannatu kam gidan momy sukayi tare da momyn, dan su kwantar mata da hankali duk da suma nasu hankalin ya gama tashi, Sam idan abu yazo daga HEESHAM ne tada musu da hankali yake, dan sanshi da ƙaunarsa suke gabaki d'aya...

HAIRANAH ma bin mamanta tayi, sai kwantar mata da hankali maman take dan tasan halin futunar HAIRANAN saita iya zuwa yanzu tajawo wata futunar a gidanta tunda MEENATU ce tazo a abokiyar zamanta....



Dadyn su MEENATUN hak'uri ya dinga bama Dadynsu HEESHAM da Baban su NUWAIRA da Babah Alhaji, sun kuma fahimce shi sunce babu komai ai baisan hakan zata faru ba daya sani tabbas da hakan bata faru ba.. Nan suka dinga kwantar mai da hankali ganin duk ya fisu shiga tashin hankali...


Ai kamar maman su NUWAIRA tasani, HAIRANAH na komawa gidanta tahau tattara kayanta na sawa wai wallahi bazaka zauna da MEENATU ba, tana kallanta a matsayin wacce k'anwarta ta kashema y'ar uwarta d'a ba....

Lokacin data kira AHMAD tana gaya mai haka hankalinsa ba qaramin tashi yayi ba, nan yace tofa, wai wata sabowa inji y'an caca..

Nan ya karyo dakan motarsa sai gidan nasa..
Aiko ganinta yayi tana tattara kayan nata..
Cikin fusata yace "Waike me yake damunki ne, meyasa kike da futina ne, tace "Nifa bazan zauna da matar da qanwarta ta kashema y'ar uwata d'anta ba, Yace "Baki da hankali Baby, me zaisa bazaki gane babu sa hannun MEENATU akan wannan al'amarin ba..

Yarinyar nan tayi nadama abin ma data aikata a baya, bata fatan ta aikata irinsa a gaba, tana sona sosai tana tsoran na rabu da ita sanadin hakan ni naga hakan a kwayar idanta..

Oho, Shi kenan mutum bazai tab'a canjawa ba kenan a rayuwarsa, kawai idan kamasa shedar cewa shi mugu shi kenan sai hakan yasa maka yardar cewa bazar tab'a canjawa ba, saboda Kaine ka halicce shi..

Ki duba fah, itace fa takaini har inda malamin HASEENAN yake, kina ganin inda sona da ƙaunata basu mata illah ba yaushe zata yarda takaini.. Me yasa bakiyi tunanin wannan zai qara zama qarin ishara agareta ba...

Toh bari kiji na gaya miki, dukkan mugun halin mutum daga lokacin da yayi nadama karb'arsa ake da hannu bibbiyu ba'a nuna masa ƴama da hantarar ba'a yarda dashi ba, hakan shiyake sawa wasunsu su koma ruwa.

Bani da abin so sama dake HAIRANAH, dan ina miki wani so wanda ban tab'a yima wata y'a mace ba, ina zama da MEENATU ne kawai saboda qaunar da take min, ayanzu kuma zan zauna da ita ne saboda na yarda da nadamarta, zan tallafi rayuwarta dan nasan bata da makama ayanzu, zuciyarta cike take da tsoron karna barta, Wannan dalilin yasa bazan rabu da ita ba...

Amma tunda kince bazaki zauna da ita ba, hakan yayi, dan kina da damar da zakiyi duk yanda kikaga dama ayanzu, nasan kinsan na damu dake ne, shiya kowane banzan tunani idan yazo miki kike karb'arsa batare da lissafi ba, zaki iya zuwa Gidan momy ki tare har zuwa ranar dazan gama Gina miki inda zaki zauna... Yana kawo nan a zancensa ya fitta daga falan nasa ransa a matuƙar b'ace...

Anan harabar gidan kuma yaci karo da MEENATUN, wacce shigowarta kenan.. Tana ganinsa ta zube a gabansa, hawaye na zuba mata cikin kuka sosai tace "Dan Allah dan Annabi naci Arzikin Soyayyar da kakema HEESHAM da NUWAIRA da HAIRANAH da Momy da Dady *KA RAYU DANI* Wallahi nayi nadamar da tunda nake a duniya ban tab'a yinta ba, dan Allah kabarni har gobe naci gaba da amsa Sunan matar ka.. YA AHMAD ina MASIFAR SANKA, ina ƙaunar ka, dan Allah ka fahimceni ayanzu, duk zan gyara halayena...

D'agota yayi cikin sanyin jiki ya rungumeta tare da d'anta yace "ZAN RAYU DAKE MEENATU, fatana karki cutar min da HAIRANAH, ina santa fiye da kowace Y'a mace, ammafa kina da damar da zaki ja hankalina kema nasoki kamarta...
Murmushi tayi da d'ago kanta tana kallansa da cewa "Kayimin halacci a Soyayya YA AHMAD, insha Allah bazan tab'a baka kunya ba, bazan qara yunk'urin cutar da HAIRANAH ba, kuma zanyi qoqari iya qoqari wajen binka kasoni fiye da itan. Yayi murmushi da cewa aransa _baki san yanda HAIRANAH tayi nisa a al'amurana bane,_ afili ko cewa yayi, "Naji dad'i, fatana ki cika alk'awarin zama da ita lafiya, dan idan kika sab'a hakan makomarki gareni baza tayi miki kyau ba.. Yana gama gaya mata hakan ya saketa da sumbatar yaran nasa ya shige motarsa...
Ita kuma tayi shashinta cike da nadama dajin dad'i..

Hawaye ya zuboma HAIRANAH, dan a kan idanta komai ya faru, dan window na room d'in nata a bud'e yake, Sam AHMAD ya manta a wajen ya barta, kuma gaskiya MEENATU bata san da ita awajen ba...
Taji dukkan abun da suke cewa..
Hakan yasa ta goge hawayenta, a bayyane tace "bazan tab'a baki damar da za kiyi wani abu wanda zaisa mijina ya soki fiye dani ba...
Tana fad'in hakan tahau maida kayanta tana kuma cigaba da cewa, anan zan zauna har zuwa ranar da zaka raba mana gidan, dan bazan tab'a zuwa gidan momy na barku cikin Soyayya ba, Sannan ba boka ba malam saina qara mallakeka yanda bazaka tab'a shagala da ita ba kai gama kowace mace mah.. ( Ni RAHEEMAT nayi dariya nace su HAIRANAH sankin wayo da kishi😂 )




Da gaske sanda HEESHAM ya samar ma da NUWAIRA da kwanciyar hankali Sannan ya samu kanta, kawai ku yarda sun danne zuciyarsu sun bama Luv hakk'insa..


A wannan rana yawancin dangi sukaje suka duba Sadeeq, Sam momy dasu Ramlat mantawa sukayi dashi, sai can da yamma suka tuna dashi, nan a gidan momyn suka mai abinci me kyau. Suka had'u da momyn wacce a yanzu tasamu nutsuwar, sukaje asibitin, anan suke gayama Sadeeq d'in kaf abin daya faru, murmushi yayi da godema Allah..
Haka Khadija ma ta qara bama su Ramlat labarin komai..
Anan suka kira NUWAIRA suka dinga mata kuka tace su kwantar da hankalinsu komai ya wucce, dan tasamu dangana a ranta, suma su kwantar da hankalinsu, indai yara ne zata samu fiye da Ameer albarkacin manzan Allah ( S AW )...





Sai can Kusan karfe tara AHMAD ya koma gida baiyi tunanin ganin HAIRANAH ba, dan yasan halin futunar ta sarai zata iya tafiya gidan momyn...
Amma yana yin parking bayan yaje ya duba MEENATU dama ba itace dashi yau ba HAIRANAN ce, sai kawai yayi part d'insa, yana qoqarin cire kayansa dan shiga wanka sai HAIRANAN ta shigo, sai yayi mata fuska, ganin bashi da niyar kulata sai kawai tasha gabansa da marairaicewa ta kama kunnuwanta biyu tace "Nayi nadama Dadyn Ummi, nayi nadama my blood, nayi nadama, pls kaji tausayina ka yafemin bazan qara ba..

Yaja numfashi da yawota jikinsa gabaki d'aya suka fad'a akan gado yace "Ya zanyi dake Baby, tace "Hakuri my Luv, Allah bazan qara ba..
Yace "toh na hakura, yanzu a ina muka tsaida zancen.
Tace "Kawai ka fara shirye shiryen gidana min gidana, dan gaskiya bana san na dinga ganin Aunty MEENATU dan Allah ka fahimceni..
Yace na fahimceki Babyna, zan fara insha Allah. ina kika baro min yarinya TAH..
Tace "tana can tana bacci, karka damu na tufeta da addu'a..
Jin hakan yasa yahau aika mata da wasu sakwanni..







Sadeeq dai sati uku ya d'auka a asibitin ya warke sarai...

Zuwa wannan lokacin kuwa tuni an tsige malamin HASEENAH, dan anyi binkice sosai a kansa an kuma ci karo da mugayan abubuwan daya dinga aikatawa a rayuwa..


Babah Alhaji kullum aikinsa bama su HEESHAM magungunan tsari, gaskiya ne HEESHAM yafa gama yarda da qaunar da Baba Alhajin yake masa..


MEENATU na lura da qannanta, tunda yanzu momyn nasu bata gidan Dadyn nasu, tana can asibiti tana jinya dan har yanzu shuru ne..

Bayan wata biyu Dadyn nasu ya samu wata me sanshi a dangi Baba Alhaji ya aura masa ita, ba qaramin ciwo kuwa momyn nasu taji ba..



Tsakanin Ramlat da HAIRANAH Hannatu da NUWAIRA Khadija kuwa ba komai sai qarin qaunar juna....


Bayan shekara d'aya ne Hannatu ta haihu, bayan b'ari da tayi, ta samu d'anta namiji yaci Sunan Dadyn mijinta AMAAR...


NUWAIRA dai bata samu ciki da wurri ba, dan a yanzu ne take dana wata hud'u..

Wannan dai halin da HEESHAM ya nuna mata a cikin Ameer shine yake nuna mata a wannan cikin ma..
Amma yayi qari dan sosai yake san yaga ta harfe masa..
Tare suke yin komai, gaskiya ne HEESHAM yana ƙaunar NUWAIRA, dan idan kaje gidansu kaga yanda suke mu'amala nan zaka tabbatar ba qaramin so yake mata ba...


Kamar yau ranar lahad'i.. Suna kitchen suna girki, Rabin aikin shikeyi, ya kalleta cikin muradi yace "Wallahi aunty na matso ki aihu, naga wannan kuma wazai yo..
NUWAIRA tayi murmushin da rungumarsa ta baya tana cewa, "Ai kafini qarfin jini inaga da wiya na haifo me kamata..
Yace "kinsan Allah Addu'a nake miki kibani y'an biyu.. Tace "Serious yace "Allah da gaske, tace "insha Allah su zan baka, dan zan fara tayaka addu'a tun daga yanzu...
Juyowa yayi da rungumar ta ta gaba yace, "Nagode Luv, ina kuma qara godema Allah daya had'amu cikin ƙauna, dana nasara Auntii NUWAIRA danayi Babban rashi, zan kula dake dan Allah ki riqeni amana...
Tace "Nafasan kafini wayo, kai nake so ka riqeni amana, takai ƙarshen zancen da had'e bakinsu..















Wata ranah ranar litinin da misalin qarfe goma sha d'aya AHMAD ya kai MEENATU wani gida a jerin unguwannin manya, yace mata gidanta ne..

Murnar da tayi ba'a magana, ya gaya mata yama HAIRANAH mah, nan ya nuna mata kotan gidan HAIRANAN, murna dai tayi mai godiya, duk da dai tad'anji kishin yanda tsarin gidan HAIRANAN yake, amma ganin nata yazo sak da zab'inta hakan ya wanke zuciyarta..


Haka ya dawo ya d'auki HAIRANAH itama yakaita layin da HEESHAM yake cikin wani masharufin gida ita dai idan tazo duba NUWAIRA tana ganin ana ginin gidan, bata tab'a kawowa gidanta bane, shine ayanzu yace shine Gidan da yayi mata..
Sanda HAIRANAH ta kusa sumewa dan jin farin ciki.. Itama ya nuna mata Gidan MEENATU, murna tayi sosai, musamman dataga komai na gidan zab'unta ne, dan kowacce a cikinsu sanda ya nemi zab'inta, amma basuyi zatan zaiyi amfani da hakan bane wajen Gina musu gidajen nasu... Shiyasa dukkansu suna gani suka san zab'insu ne..


HAIRANAH dai murnar biyu ce tayi RAM da ita, gata kusa da y'ar uwarta, gashi ba ita ba ganin MEENATU..


NUWAIRA tafi kowa jin daɗin hakan, nan tace ma HEESHAM Ashe dama gidan HAIRANAN ne shine bai tab'a gaya mata ba, murmushi yayi mata da cewa tamai hakuri dama sun shirya yi mata ita da HAIRANAN bazata ne...


Haka kowacce taje ta kwaso kayanta da gyara gidan nata, HAIRANAH dai ta cinye MEENATU a kayan d'aki, dan Yayanta SABEER ya tsaya mata akan abubuwa da dama, haka NUWAIRA ma, komai yazo mata da sauqi matuƙa...
Har yanzu kuma tana tare da Asiya, dan Asiya ta Auri me gadin nasu, anan AHMAD ya fidda musu wani shashi na y'an aiki, suna dai zaune abinsu zaman mutunci da amana..

Haka MEENATU ta nemi wata yar aiki itama, itama agidan nata akwai shashin y'an aikin...




Gaskiya ne momy tana yin NUWAIRA da HAIRANAH hakan yasa sukejin dad'in mazajen nasu, dan suma suna kyautata mata, dan kyautata uwar miji yana temakawa sosai wajen d'auke idanta akan sirikanta.. Haka Ramlat tana kyautata ma mamansu.. Haka Hannatu tana kyautata ma tata uwar mijin..




Yau daran Jumma'a da misalin qarfe huɗu da rabi nak'uda tatayarma NUWAIRA...
Haka HEESHAM ya kin ki meta yakaita asibitin nasu, shiya shirya danyi mata komai shida wata matemakiyarsa Hawwa.
NUWAIRA ta haifu d'anta namiji, qatoto, sai kuma ta qara wani nishin sai ga wani ya biyu bayan na farkon...

Allah me iko me kowa me komai, miqa masa al'amuranka kaga ikwansa akanka, duk wata jarabta da zata sameka karka manta da Allah, gashi kuna dai gani ya bama HEESHAM y'an biyu lokacin dabaiyi zato ba...
Dan zai iya rantsewa kan shidai tunda yake duba NUWAIRA bai tab'a ganin yara biyu a cikin nata ba..
Wannan abu ya qarama dangi da y'an uwa dasu kansu ishara...

Momy da Dady ba qaramin murna sukayi ba, saikace sune fankwan jikokinsu, haka kaf dangi kowa da gaske har cikin ransa yayi murna da zuwan waƴannan yaran, ba abin da kuma ya rabasu da Ameer kamar dai an tsaga kara tsakaninsu dashi, gaskiya yaran sunzo dakyau yanda kasan yaran larabawa, ga farin jini da suka samu fiye da Ameer, haka kamar yanda akayi rubibin ganin Ameer kowa san ganin yaran yake yi...

HEESHAM ya rungumi NUWAIRA yace "Luv kin gani ko, kinga ikwan Allah ko, kinga yanda Allah yake ikwansa ko, wannan ya ishemu ishara, wallahi ba abin da yafi qarfin Allah, lokacin daya jarabceka kayi Addu'a garesa kawai ka kuma gode masa sai ya baka fiye da wanda ka rasa, ina sanki NUWAIRA please ki Bari na qara baki wasu yau da yardar Allahn namu...

NUWAIRA ta waro ido tace "Yaufa na haifo su, me kake cewa ne...
Qara rungumar ta yayi da cewa "Har gobe bazaki dena tsoro ba my Auntii, Sannan bazaki dena rashin wayo ba, inda nine ke cewa zanyi na bari na baka dama k'ara bani wasu yanzun HEESHAM..🤪🤪🤪
Kina cikin jini my Auntii, kinsan bazan iya kulaki ba...

Murmushi tayi da dukansa a qirji tana cewa "Fatana *KA RAYU DANI* ni kad'ai... Cikin tabbatar wa yace *"ZAN RAYU DAKE* Luvly, dan kice kad'ai matar HEESHAM anan gidan duniya dacan gidan aljanna....
Tace "godiya ga Allah me kowa me komai...

Dangi dam suka cika asibitin, Baba Alhaji kamar ya cinye yaran, dan kallo d'aya zaka mai kasan sun shiga ransa...



Momy ta b'ata rai sosai ta kalli HEESHAM tace "Zan d'auki NUWAIRA wallahi saura kaje ka had'ani da Baba Alhaji, ranka saiya b'aci..

HEESHAM ya kalli AHMAD da Sadeeq da Dadynsa, dan fitar baba Alhajin kenan ta fad'i hakan... Sai yaga dukkan murmushi sukeyi.. Maman su NUWAIRAN ce dai take kallansa cike da jin daɗin ganin farin cikinsa...
Saiya matsa kusa da NUWAIRAN yakai bakinsa kunnan ta yace "Wallahi tallahi Auntii idan kika bari momy tatafi dake wankan gida kinji na rantse kan ki dawo zan miki kishiya, qila ki jita a gidanki kan ki dawo ko idan kin dawo kisan da zaman zuwanta, wallahi Auntii har gobe bina suke ina ce musu kin isheni, amma idan kinji kenan... Ya kai qarshen zancen nasa da janye fuskar tasa daga kunan nata...

Saboda rantsowar da yayi, nan idan NUWAIRA yaso kawo ruwa...
Dama Momy tasan b'ata tunaninta ya shiga yi, dan haka ta kalleta da cewa "Meya gaya miki..

Cikin rawar murya ta kalli momyn tace "Cewa yayi zaiyi min kishiya idan har na yarda kika d'aukeni wankan gidan..

Momy ta galla mai harara tace "Rabu dashi qarya yake yi...

Ai momy bata ankare ba sai gani kawai tayi NUWAIRA na hawaye da kuka qasasa tana cewa "Allah momy zaiyi min, dan Soyayyarki da manzan Allah Karki d'aukeni, takai ƙarshen zancen da rushewa da kuka.....

Me HEESHAM zaiyi imba dariya ba... Nan ya kwashe da dariya...
AHMAD yayi murmushi kawai da ficcewa daga d'akin, murmushi Dadyn nasu shima yayi, Mama ma murmushin tayi da ficcewa...

Dadyn yace "kwantar da hankalinki ba ita ba d'aukarki NUWAIRA, kuma bashi ba miki kishiya, insha Allah bame rabaki da mijinki...

Momy ta saki baki kawai tana

Please Login or Register in order to submit comment