Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gaya miki, kuma wallahi bazaki tab'a zama matar HEESHAM ba har sai kin kawo min jininsa, tace "Ban gane ba, yace "kwantar da hankalinki yanzu zan ganar dake.
NUWAIRA tun asati biyu da Auransu sukaje suka karya asirin da muka musu, Sannan HEESHAM ya samar mata wani dafa'i tayi amfani dashi wanda da wiya anan gaba ki iya mata wani abu na asiri ya kamata...
Saidai tsakaninmu babu wani nuqo nuqo zan miki aikin da HEESHAM zai aureki ko yana so ko baya so idan kika kawo min jininsa, nayi miki wannan alƙawarin..
Tace "Amma abin da d'aure kai yake, tayaya akayi asirin ya karye ba tare daka sa'ni ba! tunda tisawa kakeyi kullum, yace "Sun samu malamin daya fini iya shed'ananci ne, kuma yaba HEESHAM dafa'in da indai wani ya qara jifan NUWAIRA da wani abu direct kansa zai dawo, idan dai kina san Auran HEESHAM to saiki kawo min jininsa zakiga aiki da cikawa.
Tace "Ba matsala, duk da hakan abu ne me wahala amma zan san yanda zanyi..

MEENATU tace "Nima HAIRANAH ciki ne da ita ya kenan, yace "MEENATU ki bar batun HAIRANAH, ki lallab'a da AHMAD a haka kukai qarshen rayuwa, dan HAIRANAH tana da yara sosai da AHMAD, idan kika matsa akanta zakije ki jama kanki matsala..
Tace "kana nufin yanzu banda mafitta kenan, yace "kina da mafitta guda d'aya, itace ki dage da shan magungunan mata kifita tanan wajen, ina ganin hakan shine abin daya dace dake.
Tace "Kar kace na munafunceka, wallahi bazan rayu da HAIRANAH har karshen rayuwa a matsayinta ta kishiyata ba, idan na samu wanda ya fika iya shed'ananci naje wajensa, tana gama gaya mai hakan tatashi ta tafi abinta, ko sallama batama HASEENAH ba.
HASEENAN ta kallesa tace, "Nima ina bayanta akan matsalarta, zan goya mata baya dan bazata rayu da wannan shegiyar ba..
Yace "Idan ta kwab'e mata banda asara, kuma karma kizo min da batunta..




Da gaske NUWAIRA yanzu tana tare da tsari sosai a jikinta, dan HEESHAM sosai yayi nasarar rainanta ta fara yin Addu'a yanda ya dace, haka nafula yana tashi zai tasheta, Sam yaqi barinta tayi baccin asara...
Kuma da gaske Baba Alhaji ya bama HEESHAM dafa'i yasha yace yaje ya kaima NUWAIRA
Ita kanta yanzu zata bada labarin tafi jin dadin rayuwarta..




Sanda cikin NUWAIRA yakai wata bakwai, Sannan HEESHAM yakaita gidan iyayen nasu..
Momy da mamanta basuyi mamakin su ba, sunyi sha'awarsu sosai..
Sai kuma akaci sa'a ranar ranar Sunan Khadija ne, ta haifi d'anta na miji, yaro yaci sunan Dadynsu HEESHAM..
Aiko yaro yaga gata, dan Ramlat da Hannatu da HAIRANAH NUWAIRA dangi ba qaramin kaya sukama yaran ba, bare kuma HEESHAM da AHMAD abin dai yama Sadeeq da Khadija dad'i sosai a zahiri da bad'ili.






MEENATU sai Addu'a take kan tasamu wani shahararran malami ko boka yayi mata aikin dazai sa HAIRANAH fitta daga gidan AHMAD da qafafunta.
HASEENAH ko ta yarda da maganar malamin nata, yanzu qoqarinta yanda zata samu jinin HEESHAM take, (Rahama Nalele tace Allah ya dubi nufunta).







Yau asabar ya kama sunan MEENATU ta haifi d'anta namiji me kama da ita sak, yaran yazo da kyau ba qarya, dan itama dama ba baya bace wajen kyau.
Shima haka yasha hidima ba qarya, yaro yaci Sunan Babanta, dan ba qaramin shiri AHMAD yakeyi da Dadynta ba, mutum ne nagari...
MEENATU abin duniya ya samu, kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin mafificin farin ciki awannan ranah
Ta dai tafi gidansu wankan gida

HAIRANAH tace Allah ya raya, tama yaro hidima Amma MEENATUN taqi yabawa, HAIRANAH dai sanda ta tuno da cikinta na farko, tadai rok'i Allah ya basu me albarka...



Kwana uku tsakani Ramlat ta haifo nata Babyn shima namiji, abin dai yayi sweet, dan Sunan Babansu NUWAIRA aka saka mai, gaskiya dangin sunyi qoqari sosai, dan itama ta samu kaya bad'an kad'an ba, NUWAIRA da HAIRANAH Hannatu sun nuna mata ƙauna sosai ba qarya.
Momy ta d'auke ta wankan gida












_________ Yau da safe da misalin qarfe takwas HEESHAM na tare da NUWAIRA dan aihuwa ce tatashi mata gadan gadan...
Yana tare da nutsuwarsa, dan haka shi yayi mata komai ta haifo kyakkyawan d'anta namiji, yaran yazo dakyau ba qarya, abin ya tab'a HEESHAM, dan kamarsa da yaran ta b'aci..
Da gayya dangi sukazo ganin yaran HEESHAM, dan sun yarda yaransu zasuzo da kyau na ban mamaki.
Aiko sunga yaro, yazo dakyau ba qarya..

Qiri qiri momy tace zata d'auketa wankan gida HEESHAM ya nemi saka mata daru akan bazata d'auke ta ba, tace "HEESHAM ka fitta daga idona.. Yace "momy kibar min Auntii na dan Allah...
Tace "Wallahi baka isa ba.
Yana barin falan nata yayi wajen Baba Alhaji da gaya mai wai momy zata d'aukar mai matarsa wankan gida, Baba Alhaji yayi murmushi haka ya kira momyn yace tabar mai matarsa ba ruwanta dashi..
Kunya ta kama momy, washe gari da HEESHAM yaje gaisheta taqi kulasa, saiya dinga bata hakuri, tace idan yana san ta hakura ya yarda ta d'auki NUWAIRAN kawai, yace No, nidai kiyi hakuri, tace ba yanda zanyi dakai HEESHAM, fata na dai Allah ya qara maka kunya...
Saiya sunbaci hannunta, yace "ina sanki momyna.
Girgiza kai kawai momy tayi, ta yarda kunyar HEESHAM agaresu ragaggiya ce..



Allah sarki momy bata san abin dayaji akan yaran bane, dataji baza taso rabasa dashi na tsawan kwana arba'in ba.

Dan Yaji Soyayyar yaran nasa ne kamar bai tab'a san wani abu aduniya irinsa ba. 😔😔😔rahama Nalele tace to Allah ya kauda mummunar qaddara


Ranar suna me jego tayi fes da ita, abin dai ba'a cewa komai, yaro yaci sunan Baba Alhaji.. Duk da cewar Baba Alhajin yana da masu sunansa a family d'in da yawa amma baisan dalilin dayasa yaji wani mafificin dad'i da HEESHAM d'in yamai takwaran ba.
Abin yamai dad'i sosai ba'afa cewa komai, dan yaransa ma sunji dad'in har cikin ransu, duk da sun masa amma haka sukaji dad'in ya mamayesu.


Toh dake farin jinin a jikin HEESHAM yake, gaskiya yaran ya samu kaya wanda ya hauzik'a dangi. Suna Yaran kiransa da Ameer.

Abin baima HASEENAH dad'i ba sam😔 sai yaso sata qaramar hauka.
Amma da malamin ta ya bata wata shawara nan baqin cikin nata ya koma farin ciki, babu abin da take hange ayanzu kamar lokaci,( ni RAHEEMAT nace zanga saban salo)


Momy bama Asiya magunguna tayi nasu kyau wanda zai matuƙar gyara me jego tace taba NUWAIRA, Sannan kuma harwayau ta tura ma NUWAIRA wata tsohuwa y'ar shuwa, ba qaramin gyara ta iya yima masu jego da amare ba.
Ita dai wannan tsohuwa taga abin mamaki, dan NUWAIRA biyema HEESHAM tayi take kwana da mijinta d'aki d'aya, duk da ba wani abun dayake shiga tsakaninsu, amma itama bazata iya gujema mijinta na kwana arba'in ba, dan ita kad'ai tasan waye mijin nata.

Harwayau, ni RAHAMA NALELE ina kira ga masoyana, babbar asarace ki wani qauracema mijinki na kwana arba'in a wannan lokacin, dan kina kwaranyar da wata zazzafar Soyayyar mijinki ne baki sa'ni ba, duk da ba wani abu dazai shiga tsakaninku acikin jini amma wannan jin ɗumin junan naku dukkan ku ukun da jaririn yana qara haifar Soyayya mara qarewa..






HEESHAM zaune a falansa yana d'auke da Ameer, sai wasa yake masa kamar bashi da wani aiki a duniya kamar hakan....
NUWAIRA na kallansa ta zubga tagumi tana tunanin wane irin so yakema Ameer ne, Sam tunda ya samu yaran baya shiga harkarta sosai, kullum yana tare dashi, hirarsa yaran, komai Ameer, a shagwaɓe ta kallesa tace "Dan Allah luv kaji dani ko kad'an ne, ya juyo a hankali ya kalleta da cewa "Ina jinki luv, menene, tace "Alamu sun nuna zakafi ji da yaranka fiye dani, yace "Yes, zakiyi kishi dasu ne, tace, "kwarar kuwa, dan haka sai kasan nayi.
HEESHAM yayi dariya, tare da tashi ya zare hannuwan nata daga tagumin kana ya dire mata Ameer d'in akan cinyarta tare da durk'usawa a gabanta, fuskarsa cike da murmushi yace "Toh gayamin! Miye matsalar, tace "Soyayya nakeji, gaskiya nagaji da jina haka.. Takai qarshen zancen dayin fuska kamar ba ita tayi maganar ba, ya qarayin murmushi dan gane me take nufi, sannan ya fad'a tunanin bai tab'a zatan zai iya barinta haka bayan yasan tayi arba'in harma da sati biyu ba, gaskiya baisan meyasa yake shagala da Ameer ba, idan ya dawo daga office bashi da wani aiki sai yima yaran wasa, dama ko da rana yaran yake yin bacci, dan haka idan tare yayi sai yakai sha biyu idansa biyu kafin yayi baccin, duk shine dai me rainan sa, dan haka idan yayi bacci shima nan take baccin yake kamasa, dake ya saba da sallar dare lokaci nayi yake tashi ya tashi NUWAIRA su gabatar, da asuba kuma koda yaje masallaci ya dawo ya shirya kansa ba wata hira tsakaninsa da NUWAIRAN, dan duk lokacin na Ameer ne, har yaran ya fara gane muryarsa, kwata kwata lokacin HEESHAM Yanzu na yaran ne,
dan haka ba wani batun raya luv tsakaninsa da NUWAIRA, toh shine yanzu da abun ya ciyota ta gayamai gaskiya, yana zuwa nan a tunaninsa ya fara shafa gefan fuskarta, yace "Toh fushin na miye, tunda shikenan matsalar ai saiki sake mun fuskar naji dad'i ko , tace "Banda tabbacin zaka gyara yanda nake so ne, yace "Nima fa nayi missing d'inki sosai luv, wallahi nayi missing d'inki, kawai dai bazan iya fifita buqatata bane akan ta Ameer, kinga kafin yayi bacci kin rigada Kinyi, haka yana yin baccin nake tsintar kaina cikin yin nawa, amma dan Allah kimin afuwa bazan sake barinki haka ba, yakai ƙarshen zancen da rage sautin muryarsa yanda zaifi shigarta da kyau, aiko nan tayi saurin kallansa tace, "Promise yace "Year..
Ahankali ta sakar mai murmushi, shi kuma ya sakar mata kiss, wanda sanda ta kusa rasa nutsuwarta kafin ya barta..



Aiko sun tsunci kansu cikin farin ciki kamar yau suka tab'a sanin juna, gaskiya ya qara santa sosai kamar ya cinyeta haka yake jinta aransa, itakam ba'a magana, dan gani take ba wani namiji a duniya da kai HEESHAM d'in sanin kan mace da yanda ake tafiya da ita, Gani take mijinta yafi na kowa..
Dama gyaran jikin nata data sha ne yasata jin muradinsa, dataga bazata iya da kanta ba shine tagaya mai, ko ba komai tasamu farin cikin da take san samu, tama samu fiye da tunaninta, kuma tasan a kwad'ayinta da HEESHAM d'in yake, tunda ya jita yanzu, tofa Saidai tayi hakuri dan zai kulata ne har saita gaji.


Tafishi san Ameer, kawai tana dannewa ne, dan NUWAIRA akan Ameer zata iya ja da kowa.
Dan haka itama da rana bata da aiki sai kula da shi, har mamaki take idan taga yana sharar baccinsa da rana, kamar dai yayo making d'in lokacin da ubansa yake gidan, saiya kasance idansa biyu.

Yanzu tana da y'ar aiki, amma matar Aure ce, tana zuwa dai tana mata abin da baza'a rasa ba, dan HEESHAM bai dena rage mata aikin daya saba ba, Asiya ce tasamo mata y'ar aikin, amma sanda NUWAIRAN ta gargad'eta kan matar Aure zata samo mata, shine fa tasamo mata Zuwaira, Zuwaira mace ce me ha kankali, wacce tasan abin daya dace,

NUWAIRA ta gama gane halin Zuwairan, ta gane macece Mara san abin duniya, kawai dai wahalar rayuwa ce tayi musu yawa shiyasa ta fittowa aiki, kuma mijin nata ya yarda da hakan dan ba yanda zaiyi, gane hakan yasa NUWAIRA kyautata mata da gaske, komai tasamu bata jin hassada danta bata, gaskiya ne, Zuwaira najin daɗin aiki da NUWAIRA, dan bata mata rowa akan komai.
Tana zuwa aikin kullum tatafi da yamma, dan ita ba batun kwana.

Ranar da HEESHAM yaga Zuwairan yayi mamaki sosai, dan yasan tsanar dake tsakanin NUWAIRA da y'an aiki, sanda ta tabbatar mai da matar Aure ce yace ai dama yasan gari banza bazaiga y'ar aiki a gidan ba..





A gidan AHMAD ko, kadaran kadaham tsakanin MEENATU da HAIRANAH, bame shiga harkar wani, MEENATU na rainan yaranta wanda take kira Abdul, cikin so da ƙauna suke rainansa ita da babansa AHMAD, HAIRANAH dai na fama da ciki, aihuwa yau ko gobe, yanzu normal take, tana cin abin da ranta keso batare data dawo dashi ba, wannan yasa hankalin AHMAD kwanciya, gaskiya yana san HAIRANAH so bad'an kad'an bah..



Yau da misalin qarfe d'aya na dare nak'uda ta kama HAIRANAN...
Dama AHMAD yana ankare da ita, Sam baya wani dogwan bacci idan yana tare da MEENATU, gabaki d'aya hankalinsa nakan HAIRANAN, sai yaga ta rabu da cikin lafiya kafin hankalinsa ya kwanta.

Ya tashi kenan dan gabatar da lafula yaga kiranta ya shigo wayarsa, dake ba itace dashi ba, cikin sauri ya d'auka, nanko yaji tana cemai cikinta na ciwo, bai tsaya bata amsa ba yayi saurin yin shashin nata, yana shiga ko yaganta tana dafe ciki tana yamutsa fuska yace "Baby yadai, tace "Cikina ne yake min ciwo, shuru yayi mata da nufar inda kayan aihuwanta suke, nan ya had'a komai da kinkimarta sai mota .
Haka a gurguje yaje ya gayama MEENATU cewa yayi asibiti da HAIRANAH zata aihu, toh tace mai dama HAIRANAN fatan aikairi na munafunci, shidai yayi gaba abinsa...

Gaskiya tuqin ganganci yakeyi, Allah ne dai ya kaisu lafiya...
Shine ya mata aikin komai, ta samu y'arta mace, kyakkyawa ko da ita, yarinyar tazo dakyau ba ƙarya, Sam batayo HAIRANAN ba, idanta kawai ta ibo, amma komai nata na AHMAD d'in ne.
Wannan yarinya ta shiga ran AHMAD sosai, dan anan take yaji santa da ƙaunarta ya mamaye ransa, kodan yana MASIFAR san mamanta ne😒.
Sanda ya bari yayi sallar asuba Sannan ya kira su momy da mamansu HAIRANAN ya gaya musu ta haihu.
Aiko sunyi murna Sosai abin ba'a cewa komai

Kan kace me, nan dangi sukaji aihuwar tata, sun tayata murna suma Sosai...

Dama tun a daran MEENATU bata iya komawa baccinta ba, sai aikin safa da marwa takeyi da fad'awa tunanin me HAIRANAN zata Haifa, hankalinta fa a mugun tashe yake, Addu'a take Allah yasa karta haifi mace, idan ma ta haifi macen Allah ya kashe yarinyar, (Rahama nalele tace Allah ya kyauta ma MEENATU da wannan baƙin halin nata) aiko washe gari tana jin AHMAD ya kirata tayi saurin d'auka.. Yace "My Baby ta sauke lafiya, ta samu Baby girl..
Sanda AHMAD yaji saukar ajiyar zuciyarta, tace "Mungode ma Allah, yarinyar dai tana lafiya ko, takai ƙarshen zancen da dasan taji amsar dazai bata, yace, "tana lafiya lau d'inta, cikin k'oshin lafiyar dana qara godema Allah..
Nan take jikinta yayi sanyi, taso da Allah ya karb'i Addu'arta, ya kashe yarinyar😂.. Haka dai cikin sanyin jiki tace "Masha Allah, ka gaishe min da HAIRANAN gani nan zuwa, yace "No ki zauna bazamu dad'e ba zamu dawo gidan, dan jikin HAIRANAN da sauƙi Sosai, zan bata sallama nan ba dadadewa ba..
Tace "ok, sai kun dawo..

Tana sauke wayar daga kunanta kiran HASEENAH yashigo mata, tana d'auka HASEENAN tace "Wai naji kishiyarki ta haihu ko, "bawai bane da gaske ne, yanzu na gama waya da wanda yayi sanadin zuwan cikin da haihuwar..
"Toh kiyi qoqarin d'aukar mahaifarta malam yace zai miki wani aiki a jikinta, MEENATU tace "Ga samu ga rashi, ni tayaya zan wani iya samun mahaifarta. "aa baso kike tabar miki Gidan naki ba, da kina so da kinsan yanda za'ayi ki samota, HASEENAH ta faɗin mata hakan cikin matuƙar jin haushinta, cikin murmushin yaƙe MEENATUN tace "ke da kike tayani san tabar min gidan nawa mezai hanaki zuwa ki d'auko min, tace "kema dan kinsan mijinki yaja min kunne akan zuwa gidansa da shiga al'amuranku ne, da zuwa har asibitin zanyi na d'auko miki kinsan wannan qaramin aiki ne agareni .
Tace "hmm, Na gaya miki ban b'oye miki ba, nadena tsayawa b'atama kaina lokaci akan wannan shegen malamin naki, kije kita biyema aikinsa tunda ke yana miki, dan Allah kidena min batunsa, idan har ba nemomin wani zakiyi ba to karki qara mun batunsa.
HASEENAH tace "kinja min kunne akan hakan yafi sau a qirga, amma da zaki daure ki kawo masa mahaifar tata da kinga abin dazai miki, tace, "Ni bazan qara sauraransa ba, Kawai idan zaki samo min wani ki samo min..
Tace "Toh saina samo..
Atare suka ajiye wayar tasu, kowa da abin da yake tunani, HASEENAH dai gani take tata matsalar ta kusa barinta, ita kuma MEENATU tunani take akan zuwa wajen wata qawarta Halima, wata shed'aniyace wacce take da bokaye da malamai kala kala, tana ganin idan taje wajenta komai ya wucce ....


Ita kam kunsan ba yanda AHMAD zaiyi da Momy dan tun a asibitin dasu Momyn sukaje tace mishi daga nan direct gidanta zatayi da HAIRANAH, lokacin NUWAIRA da HEESHAM suna wajen sai HEESHAM yaje kunnan AHMAD d'in ahankali yake rad'amai "hm um, YAYAH kace baka yarda ba, tabaka matarka, AHMAD yayi murmushi, Momy dake kallansu ta gallama HEESHAM harara kamar tasan me yace masa tace dashi, "Ai shi bazai yimin musu ba, bare ya kaini qara, ai wannan saikai futsararre, HEESHAM ya kalli AHMAD yace "Allah YAYAH idan baka so zanje na gayama Baba Alhaji...
AHMAD yayi saurin waro ido still yanzu ma baice mai komai ba, momyn kuwa najin haka gabanta ya fad'i, tasan kad'an da aikin HEESHAM yanzu yaje ya gaya mai, dan haka cikin sauri tace "Wallahi HEESHAM kafita daga idona, takai ƙarshen zancen da nunasa da yatsa, ya kalli hannun da murmushi yace "Sorry Momyna, tace "ba hakuri nake san kabani ba, so nake naji kace baka ba zuwa wajen Baba Alhajin.
HEESHAM ya maida kallansa ga AHMAD yace "Wai ince haka..
AHMAD ya kallesa da mamaki, tare dayin dariya yace "eh kace mata hakan, kuma da gaske kar naga qafarka agun Baba Alhajin.
HEESHAM ya tab'e baki da kallan momyn yace "Toh shikenan, bani ba zuwa wajensa...
Momy tasaki baki da mamaki, wato sanda yabi umarnin AHMAD d'in kafin nata, oho ho, Allah kabarni da wannan yaran, gaskiya duk yaran da kafi so a cikin y'ay'anka zakafi ganin abin mamaki akansa, da bata ja shi a jiki ba, da babu wannan wasan Soyayyar tsakaninta dashi, dan bazai sake da ita ba sam, hakan kuma bai dace da iyaye masu ilimi ba, dan idan bakija y'ay'anki ajiki kin nuna musu qauna da soyayya suna janki da hira da wasa da dariya ba! to ke ba uwa bace, dan wata can zata musu hakan, tabarki nan hoto, wai a dole baki san yaranki su rainaki, wannan yasa baza suzo da matsalarsu gareki ba, kin bud'e musu hanyar bud'e sirrinsu ga wata can da bata san zafinsu ba, itakam har a ranta zata iya rasa kowa cikin y'ay'an nata bazata damu ba, amma idan ta rasa HEESHAM akwai matsala, dan sanshi daban yake dana sauran y'an uwan nasa aranta.
Tana kawowa nan a tunaninta ta d'auke kanta daga kallan HEESHAM d'in wanda yake ta mata murmushi dan yasan ya bata mata🙈 tace "Allah ya shiryeka HEESHAM..
AHMAD ya fitta yana cewa "Ameen momyna

Sai HEESHAM d'in yayi saurin zuwa kusa da ita, ya kama hannunta yace "LA, bafa na d'aukaka jin YA AHMAD bane akan naki momy, Sam sai nabi umarnin ki kafin nasa..
Momy ta galla mai harara da cewa, "Wai kai me wayo ko, dan kaga ya fitta shine yasaka cewa hakan ko..
NUWAIRA bazata iya da rashin kunyar HEESHAM ba, dan haka fitta tayi tana murmushi, HAIRANAH ko kanta na qasa da Ameer a hannunta, tana ta mai wasa kamar bata jin me suke tattaunawa..


Ahaka dai sukayo gidan Momy gabaki d'ayansu
Anan sukaga Hannatu da Ramlat dan momy ta kirasu tace su wacce gidan nata kawai...


MEENATU ma kiran AHMAD tayi tana cemai bata gansu sun dawo ba, yace mata eh sunyi gidan momy anan HAIRANAN zata zauna..
Nan ran MEENATUN yayi mata dad'i sosai, irin zata sake da mijinta na tsawan kwana arba'in..
Haka ta shirya kanta da yaranta Abdul sukayo gidan momyn..

Mamansu HAIRANAN ko sai washe gari taje taga Yarinya..




Yau ya kama suna, tun qarfe bakwai NUWAIRA tagama komai na gyaran gidanta..
Suna dining dan sun gama breakfast kenan, hannun HEESHAM yana d'auke da Ameer yana mai wasa, NUWAIRA tace "dan Allah luv ka tashi mutafi ka sauke mu, yace "Yauwa my Auntii, bawai naga kinata zumud'i zaki cikin mutane ba, wallahi ki kula min da yarona, dan idan wani abu ya same shi, kinsan Allah keya sama...
NUWAIRA taja numfashi da ajiye cup d'in hannunta tace, "wannan idan karatu ne ya dace kagane na dad'e da haddace shi, dan kullum idan zan fitta sai kaja min kunne akan hakan, wallahi ina san Ameer bazan tab'a maka wasa da yaro har wani abu ya same shi ba...
Kallanta yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya tashi da sab'a shi a kafaɗa ya bar falan, NUWAIRA ta girgiza kai da kallan laptop d'insa da wayarsa harda key na motarsa, irin ya fitta da d'ansa tabiyosa da waƴannan..
Haka takai kayan da sukayi break d'in dasu kitchen kana ta dawo ta yafa gyalanta da ibar masa kayan nasa..

Daya sauketa a gidan momyn ma sanda ya qara ja mata kunne, ayanzu kam bata wani jasa da doguwar magana ba, kawai cewa tayi zata kiyaye..


Momy ba qarmin san Ameer take ba, dan haka NUWAIRAN na shigowa tabi ta d'aukesa tunkan su gaisa.
Haka da dangi da suka taru kowa idansa na kan yaran, dan yaran yazo da wani kyau wanda ƙaryane ka gaji da kallansa, hatta MEENATU sanda taji sanshi har cikin ranta..
Ganin yanda kowa yake san d'aukar yaran hakan yasa gabaki d'aya hankalin NUWAIRA yake kansa, Sam taqi yin aikin komai saina kallan d'anta daga wancan hannu zuwa wancan hannu.
Momy ta gane manufar NUWAIRAN naqin yin komai d'in, sam bata kulata ba, dan tasan idan tayi kuskuran da wani abu ya samu yaran tana ganin duk garin Abuja sai sunji kan HEESHAM da ita, dan ita da Dadynsu sunyima HEESHAM d'in farin sani akan qaunar da yakema Ameer d'in..

Ita dai NUWAIRA sanda d'anta ya dawo hannunta Sannan hankalinta ya kwanta..


HAIRANAH dai tayi kyau har ta gaji, batun kaya ko sai wanda ya gani, dan ta samu kaya mesa maqiyi cakama kansa wuk'a, yarinya dai taci suna Sa'adatu, Sa'ar mata, taci Sunan kakarsu AHMAD d'in.. Suna san kiranta da Ummi
Hakan ko yayima HEESHAM dad'i dan baya san wani ya rigasa yima momyn nasu takwara..
Yana fatan ya fara mata kafin kowa...




AHMAD ba kamar HEESHAM bane, ya d'auke idansa akan HAIRANAH, Saidai suna yin waya Sosai, musamman da daddare, lokacin momy na shashin Dady, dan haka HAIRANAH bajewa takeyi susha hira abinta dashi, kullum idan yazo duba su saiya yima yarinyar photo, wannan abu yana baqanta ran MEENATU, dan tana gani saboda d'aukar mai wayansa da takeyi, nan maganar malamin HASEENAH ya fad'o mata kan AHMAD zaiso yaran HAIRANAH sosai, tana kawowa nan a tunaninta tace sam hakan bazai yuhu ba, dole taje ta nemo qawarta takaita inda zata samu mafitta.. (Ni RAHEEMAT nace, um um MEENATU kibi a ha kankali.)



Ahaka HAIRANAH tayi arba'in, gyara kam tasha shi agun momy, abin ba'a cewa komai.

AHMAD yayi mamakin jin gyaran, da badan ga Ummi ba, da cewa zaiyi yanzu ya Santa..

Takaici dai MEENATU tashashi, dan dole sanda AHMAD yayi rawar kai kamar ya sake yin amarya...


Asiya dai har yanzu tana tare dasu, dan suna Soyayya ita dame gadin gidan, sunansa Yasir, bak'auye ne, amma me cikakken ilimi ne, dan bashi da ilimin duniya, nacan lahira yake dashi, wata na muhammadiya..








******************
Bayan wata uku

Yau dai MEENATU ta samu yanda take so, gata da wata qawarta Halima gaban wani katoto la'ananne wato boka, tunkan MEENATU tace ga matsalarta yace "Dakata MEENATU, kina san HAIRANAH tabar miki gidanki, baki kuma san tasamu mijin Aure idan tabar miki gidan naki, kuma baki da wani buri ayanzu face Ummi ta mutu, yarinyar HAIRANAN wacce AHMAD yake MASIFAR santa ko..
MEENATU tace "yes..hakan komai yake ranka ya dad'e, gayamin ko nawa kake so na baka! fatana dai ka cika min Wannan burikan nawa..

Yace "bana karb'ar kud'i, Saidai kawai kiga aiki, ladan aikinmu kawai biyan buqata ne, zaki bamu had'in kai mu kusanceki iya adadin aikinki wannan shine ladan aikin mu..
MEENATU najin hakan ta kalli qawar tata da damuwa, Halima ko ta gyad'a mata kai, alamar ba wani abu ai, badai biyan buqata take nema ba.
MEENATU taja numfashi tace "Gaskiya sai nayi tunani, kabani lokaci zan dawo, yace "Yarinya zakiyi wasa dadamar ki, aikinmu kamar yankan wuk'a yake, Sannan idan kin san gaba bazakizo da shirinki ba to karki soma zuwa, danmu bamu d'aukar shashanci, HAIRANAH dai zata bar gidan mijinki, Ummi kuma zata mutu, Sannan babu wani Aure dazai qara hawa kan HAIRANAH, duk zamu biya miki wannan

Please Login or Register in order to submit comment