Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ɗan ne, shiyasa burin kowa yazo Kano fa" Hanne tace "Bawai, ke dai kakarki ta yanke ƙaga, ɗanki sarki jikanki mawaƙi a kano ki gode Allah wlh ina faɗa maki" Naila ta ɗauki nama ta saka a baki tace "To ai zuciyar ce a tsarkake bana nufin kowa da sharri, imani ne ai ba duk musulmi ba shiyasa ai har yanzu mutuwa ta gagara ɗauka ta" Hanne tace "To yanzu yana ina,kira mana shi mana" Naila ta ɗauki sanda ta miƙe tace "Biyoni muje" Bayanta Hanne tabi hannunta riƙe da nama. Sashen Amma shiru babu kowa sai ƙarar t.v da Sara ta kunna, shigowa gidan Naila tace "A'a ya naga wayam? Ina mutunan gidan suka bar tangamemen gida haka a buɗe" Sara ta ɗan leƙo da kanta daga wajan dining room, Naila tace "Algunguma ashe kina ji, kike zare ido, ina jama'ar gidan" Sara da tayi raurau da idanu tace "Kowa yana part ɗin sa" Naila tace "Bawai, ƙila shalele na opis, to ina faɗa maki wannan ita ce matar da Junaidu zai aura, to ba sai dai muce Allah ya kaɗai fitina ba" Hanne tace "Alkur'an ƙyakƙyawa da ita, kamar ita tai kanta" Naila tace "Sai dai kyan ɗan macici, dan dai bana gulma dana cewa maki ita arniya ce" Hanne ta dafe ƙirji tace "Arniya fa? Bata sallah" Naila tana yin gaba tace "A'a bana son gulma kowa bada ƙaddararsa ba, to wlh bata Sallah masifa ce kawai Junaidu ya ɗauko mana" haka sukai gaba Hanne hadda juyawa ta sake kallon Sara tana faɗin "Bawai shiyasa gata nan jajurr wlh" Suna fita ta fito daga dining room ɗin hannunta riƙe da Apple, gaba ɗaya zaman gidan ya isheta, duk kowa ya shige Amma haushin Mai martaba ta keji, Mai martaba kuma fama yake da ciwon kai, yayinda Zain yyi ficewarsa. Tana sanye da duguwar riga Abaya blue wacce tayi mata kyau, ƙafarta sanye cikin flat show, tafiya ta keyi harta bar sashen su Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ta zagaya can baya gidan sarautar, wata ƙofa ta gani da alama ba'a fiya shigewa ta cikinta ba, samun kanta tayi da fita ƙofar, sosai tayi mamakin ganin wani kwantaccen titi mai masifar kyau, ga wasu red ɗin fitilo dake duhu ya fara, kamar daga sama taji ƙarar tsayawar wata baƙar mota a gabanta, baya tayi da ɗan sauri tana dafe ƙirji, buɗe motar akai aka fito wani dugun Mutum ne ya fito, fuskarsa rufe baƙi ne sosai, aka ƙara buɗe motar aka fito gaba ɗaya mutanan suka kalli Sara ɗaya yace "Ina tunanin itace wacce muke nema" Ɗayan Mai suna Gaza yace "Bari mu ƙara tabbatarwa" Wayarsa ya buɗe photon Saraa ya bayyana, ya kalli photon ya kalli Sara yace "Billahi itace, Kutumar uba duk wahalar nan da muka sha ashe tana garin Kano" Ɗayan yace "Gaza ma lokacin ɗauko ta muje kawai" jin hakan yasa Sara sakin kuka tare da yin baya ta rasa sunan waye zata kira can ta ƙwalla ƙara tare da faɗin "Twin......



_Zain Abeed isn't free.... Kiji tsoran Allah ki sani ba haƙƙin ki bane.....zamu haɗu wata rana..08119237616 for more information_

Barka da juma'a❤️❤️ai weekend lafiya😍
[08-15 08:45] +234 703 831 1110: *17 Nimcyluv*
Baki Sara ta buɗe zata saki ihu, Gaza yyi saurin sanya hannunsa tare da rufe mata baki ya ɗauke ta cak zuwa cikin motar yana faɗin "Don't scream, calm down" Gaza ya faɗa bayan ya sakata a motar, suka ja motar da gudu tare da barin wajan. She can't cry sbd har yanzo bakinta yake a rufe, tsoro da fargaba sun cika mata ciki, tunani ne a ranta, domin a hankali nutsuwar ta ke dawowa jikinta, sbd ƙarfin addu'a da ruwan da take sha wanda Abeed ya bata, shiru tayi cikin motar tana sauke ajjiyar zuciya, bayan ta zame jikinta daga hannun Gaza, tunani ta fara da Zuciyarta, _Listen to your breathing Sara, Easy. Don't force it, Just concentrate. Listen_ wata ƙyakkyawar ajjiyar zuciya ta sauke Zuciyarta na bugawa da ɗan ƙarfi _What am i going to do now? How am i going to survive? Will i ever see Twin Again? What used to be my real life back in Nasarawa?_ Jin wasu tunani na zuwar mata ka wanda ya jima bata yisa ba, ya sanya tayi shiru dalilin sarawar da kanta yake mata, a haka har bacci ya ɗauke ta cikin motar suna sharara gudu. Wayar Gaza ta ringing da sauri ya ɗauka yace "Hello!" Shiru yyi can yace "Owk, we are on our way...." Kashe wayar yyi ya kalli driver yace "Heyyy, driver faster.." . Zain bai shigo gidan ba sai wajan 1:4 na dare, gidan shiru babu motsin komai har lokacin babu wanda yasan cewa Sara bata ciki, part ɗinsu ya shiga yay shower, kana ya shirya cikin kayan bacci, har ya kwanta yaji gaba ɗaya ɗakin yyi masa girma sosai, Miƙewa yyi gently ya fito Main Parlo ya kwanta, ya jima a haka kafin bacci ya ɗauke sa, Kiran Assalatu ya sanya Zain buɗe idanuna a hankali, ya miƙe bakinsa ɗauke da addu'a, part ɗinsu ya shiga yyi alwala, kana ya sauya kaya zuwa Jallabiya, a can mosque ya haɗu da Junaid da Dad Waziri sai Abba, ana idar da sallah bayan ya gaishe su, yayi tafiyarsa zuwa part ɗin Naila, domin ya ɗauke mata kewar Abeed, domin Abba yace kada wanda ya sake ya faɗa mata cewa baya gidan. Misalin 10 na safe Amma ta fito zuwa part ɗin Sara ganin har yanzu bata fito ba, tura ƙofar tayi shiru babu komawa a hankali cikin nutsuwa ta shiga kiran sunanta "Sara! Sara! Sara!" Shiru, ƙarasa shiga tayi sosai tayi mamakin rashin ganinta ciki, fita tayi ta gama zaga babban sashen nasu amma babu Sara, da sauri ta kira Jakadiya Abar, Jakadiya na zuwa ta zube bayan ta gaisar da Amma, tace "Uwar ɗaki na, naji kira na amsa" Amma tace "Ba kiga motsin Sara ba?" Jakadiya Abar na ƙara yin ƙasa da kanta tace "Allah ya ƙara girma Fulanin Bilhira rabona da Sara Tun shekaran jiya" Dafe goshi Amma tayi cikin kaɗuwa tace "Ya Salam, please ki duba ko ina ki sanya hadimai da fadawa su duba ta..." Tana faɗin hakan ta juya da sauri da ƙyar take kallon hanya sbd ciwon da kanta ke mata, hawan jininta na neman tashi, Amma nada hqr sosai, shiyasa hawan jini ya kamata in one time. Part ɗin su Zain ta nufa, bata tsaya jiran iso ba ta shiga bakinta ɗauke da sallama, time ɗin Zain na zaune akan kujera idanunsa akan system, amma zuciyarsa babu daɗi, ganin Amma ya sanya ya ajjiye system ɗin yace "Amma lafiya?" Amma ta kallesa kana ta kalli parlon tace "kaga Sara?" Ware idanunsa yyi yace "Sara?" Tace "Eh, i was looking for her, amma kakaf gidan babu ita wlh" Miƙewa yyi tsaye yace "Subuhanallahi, gaba ɗaya na mance da ita, kin san kanta ba saiti zata iya yin wani wajan" Amma wace take cikin tashin hankali tace "Dan Allah Zunaiddeen kada na rasa Sara please, ita nake gani ma dadin ɗan uwanka" kallon Amma Zain yyi, this is the first time da take Mgn akan Abeed, hakan na nufin she missed him irin sosai ɗin nan, ajjiyar zuciya ya sauke yace "In sha Allah,tana nan Amma" gaba Amma tayi tace "I hope so..." Ta faɗi hakan yana dafe kanta, baya tayi zata faɗi sbd jirin da take gani da sauri Zain ya sanya hannunsa ya riƙeta yana faɗin "Be careful Amma" Hannunta ya kama zuwa Main Parlo ganin yadda take ɗan ya motsa fuska, daidai nan Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ya fito sbd tuni ya samu labari wajan Jakadiya Abar, Amma na ganin Abba tayi saurin juyawa zuwa part ɗinta, da kallo kawai ya bita, yasan haushinsa ta keji, shi kansa bai san lokacin da ya furta hakan ga Abeed ba, Abba yace "Ka ganta?" Zain yace "Yanzu zan duba Abba" juyawa Abba yyi zuwa sashinsa, Zain kuma yyi waje, duk inda ake tunanin ganin Sara amma babu ita, kowa kuma aka tambaya zai ce bai ga fitar ta ba, Zain cikin tashin hankali ya koma kai tsaye ya nufi wajan Amma samunta yyi kwance akan bed jikinta na rawa, da alama zazzaɓi,abin yyiwa Zain yawa, fita yyi ya ɗauki wayarsu tare da yin dailing number Junaid. Junaid na zaune saman kujera yana sauraran abinda Dad Waziri yake ce masa, shafa kai yyi yace "Dad, mene yasa za'a zubawa yarinyar nan idanu? Wait wama yace tana da ciwon zuciya? Haka masu ciwon zuciya suke, duk wani sign na masu ciwon babu tattare da yarinyar nan" Ummi dake shigowa Parlo tace "Ke nan ni zan maka ƙarya? Tunda baki na dana likitan yake shaida min ciwon zuciya ne da yarinyar nan, haba Bama dole ciwon zuciya ya kamata ba, Wannan tsana da kke nuna mata tame ce, nina haifi ƴarta dan haka ka saurara mata haka nan, daman kai tuntuni ai na sallamawa Saratu kai, tun ta fini a wajanka" Junaid ya kalli Ummi yama rasa me zai ce, Dad Waziri yace "Mene yasa kika haka ke Sadiya? Junaid fa shine babba idan Bama raye waye zai kula da Riya?" Ummi tace "Duk al'ummar duniyar nan sai na rasa wanda zai kula da ita sai Junaid, a'a wlh wannan ma zance ne" Junaid yyi ƙasa da kansa yana mai jin takaicin abinda Ummi keyi, yana ƙoƙarin Mgna Wayarsa ta fara ringing, zaro wayar yyi daga aljihunsa ganin sunan Zain ya sanya ya miƙe da sauri, a tunaninsa zai ce masa Abeed ya dawo, yana picking yaji Zain yace "Where are you, Junaid?" Junaid yana ɗan satar kallon Ummi yace "At home, something new?" Zain yace "Sara, is missing" Da sauri Junaid har yana ƙoƙarin yarda wayar yace "What? Sara missing? When? How?" Ya jera tambayar yana waje, tashin hankali na bayyana akan fuskarsa, Zain yace "Kazo dai, wannan dalilin yasa hawan jinin Amma ya tashi" kashe wayar Junaid yyi ya nufi babban sashen dake cikin Masarautar Bilhira, Ruwa da drip Junaid ya sakawa Amma, Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas na zaune gefen bed ɗin Amma, ya kama hannunta ita dai tana jinsa ba tace komai ba, har su Junaid suka fita, Abba yana riƙe da hannun Amma yace "It's all my fault Hajiya Sarah, akan all these kike son kashe Kanki? Ni ya kamata kiyi punishing ba kanki ba, I'm the reason behind anything" Shiru Amma tayi masa, domin a wannan karan kawaicinta ya ƙare, hawayen dake sauka akan fuskar Amma, Abba ya sanya hannunsa kai taushi ya share mata yana ɗan share mata zufar goshinsa yace "I'm sorry wify, i hate your silence is hurting me" juyawa tayi ta kallesa suka haɗa idanu Mgn take sonyi amma ta kasa, da ƙyar tace "My Own child..." Sai kuma tayi shiru sharrr hawaye ya zubu mata, hawayen Mai martaba ya goge mata yace "It's okay, sleep" ya faɗa yana da shafa kanta idanunta ta rufe tana jinsa ya sumbaci goshinta..... Tafiya kawai Junaid yake cikin mota for almost 45 minutes not knowing that party direction she's heading to...He just can believe Sara is gone, ina zata? Wata sani a faɗin garin nan? Parking yyi a gefen titi lokacin kusan dab da magrib ne, kansa ya kifa akan string motar yana sauke numfashi, kafin a hankali yace "A karo na biyu na sake rasata..." Bayan sallar Issha Abeed ne zaune cikin Room ɗin daya kama a Tahir hotel, ya faɗa lokacin ɗaya idanuna ya fito sai kuma ya ƙara kyau, yana zaune akan kujera hannunsa riƙe da bottle water, tun ɗazo ya ɗauko zai sha amma ya kasa, damuwa tayi masa yawa, korar iyaye masifa ce, ace uban daya haifesa shine zai koresa daga cikin gidansa, ji yyi zuciyata tayi zafi tare dayi masa nauyi, idanunsa yaja ya rufe kafin a hankali ya ɗan sha ruwa, Wayarsa mai ƙirar iphone 13 pro max ta fara haske, ganin sunan Dr Adyan ya sanya yaja tsaki, wajan kira biyar yyi masa bai ɗauka ba, notification ne ya shigo wayar gently ya miƙa hannunsa message ne Dr Adyan yyi masa yace _Please Yariman Bilhira pic the call.....I went talk to you_ yana gama karantawa kiran Dr Adyan ya shigo, answering yyi tare da mannawa a kunansa yace "Uhm" Dr Adyan yace "Yarima try to understand abinda kke son aikatawa ba daidai bane..." Da sauri Abeed ya tsayar Dr Adyan cikin tsawa yace "Shut up, Adyan! I asked your advice because I respect your intelligent. I can't believe you're talking like one of those old Guy's....Uhm" yama kasa ƙarasa Mgnar sai ɗan cije bakinsa da yyi kawai, Dr Adyan yyi ƙasa da murya yace "Yarima kana tunanin zan cuceka?" Abeed na ɗan jan numfashi yace "Especially If someone's trying to run you over" Dr Adyan yace "But kasan ba zan maka haka ba, ina zaune dakai da zuciya ne ɗaya ne Yarima Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas, kawai ina faɗa maka gsky ne" Tsaki Abeed yaja yace "Bye..." Yana faɗin hakan ya kashe kiran baki ɗaya, Wayarsa ya duba yaga 10:45 ajjiyar zuciya ya sauke, zuciyata take samun nutsuwa ji yake kamar yyi ta ihu, idanuna ya rufe dif! dif! Haka zuciyarsa ke bugawa a haka bacci ya ɗauke sa ba tare daya shirya ba. Washegari da safe bayan Riya tayi breakfast ta ɗauki mayafin ɗinta ta saka, iso ta nema wajan Mai martaba, yana zaune saman darduma gabansa cike da kayan marmari yana sha, fuskarsa shima ta ɗan faɗa, ya ɗan saki Murmushi yace "How the you feeling now?" Riya tace "Feeling much better Abba" shiru tayi tana tunanin abinda za tace, Abba dai kallonta yake bai magana ba, can tace "Abba daman na fasa auren Abeed ɗin ne, akwai wani wanda ke sona shi nake son aura" da mamaki Abba ke kallon ta, ya daɗe a haka kafin yace "What made you change your mind?" Riya tana sakin kuka tace "Abba, ina son Abeed amma na fahimci baya sona, kona auresa ba zan farin ciki ba, gashi dalili na ka kore sa hakan bai min daɗi ba, yanzu idan ya faɗa wani mugun hali ba? Ba zan yafewa kaina ba Abba, bana son zumunci ya samu rauni saboda ni" Abba yyi ta kallon Riya wlh bai san tana da hankali har haka ba, yace "Abeed zai dawo, na san ba zai wuce Dubai,
ko U.k ba ko Mascow daina kuka" Riya tace "Abba dan Allah kace ya dawo" kai kawai ya ɗaga mata kafin ta miƙe tsaye tayi waje. A Main Parlo taga Zain zaune ya gama shirin office damunsa tayi yana waya yana faɗin "Don't worry, calm down Sweetheart. Give me a minute to think ok" Du'a ta ɗan shagwaɓe fuska tace "Gaba ɗaya saura kwana uku bikin mu, amma baka taɓa zuwa inda nake ba" ta faɗa kamar zatai masa kuka, shi kam sbd kada ya kula Riya yace "Oh! Sweetheart ba dai rigima ba, ke da zaki zama tawa" Murmushi tayi masa tace "Ok I love you my man..." Yace "Love u too cute" tsaki Riya tayi domin sai taga Zain tamkar Abeed. Amma ce ta shigo jikinta duk a sanyaye tace "Yauma haka zaka fita baka ƙarya ba?" Zain yace "Amma bana jin daɗin komai, idan zan abu dana tuna cewa tare muke da Abeed yake fita a raina" Amma tace "Shi Abeed ai ba yaro bane, kuma zai dawo me, am sure ko bai nemi kowa ba definitely zai neme ka" Zain yace "Haka ne, Bye ina da meeting a watan nan zamu garin Zahel" tace "Ok then..Allah ya tsare. Riya na zuwa cikin gidan su ga saki ihu tace "Ummi shawararki tayi yanzu idan muka samu labarin inda Abeed yake fa?" Ummi tace "aiki zan saka ai masa, a sanya shi neman mata da shaye-shaye, da zarar kuma kinje yake zaiyi expecting naki, kinga idan muka samu kika haihu dashi dole zai amince da aurenki domin ba zai so sunansa ya ɓaci ba" Riya tace "Kai Ummi, you're the best mother in the world wlh" Ummi tace "Abeed millionaire ne, idan muka rasa shi munyi asara" Naila dake shigowa parlo tace "Asara tawa nawa kuma Sadiya? A'a Wlh mu a zamanin mu ba'a zaka, Wannan ai ɓakar rashin kunya ce ka zauna da ɗanka kana Shira, a lalace dai zamani ya lalace sai dai kowa yayi harkar gabansa, to daman Meye haɗina dake Sadiya? Zumunci ne fa kawai, Bawai nono na kika sha ba" Ummi dai ba tace komai ba, Can dai Naila tace "To gidan talauci kuke nan? Da banji ƙashin komai ba? A'a wlh wannan dai bayi bane rowa kuma sam bata da wani amfani ba sai kici Kanki ba? Allah ya bamu alkairi daman nazo naji ya Audillahi ya kwana da jiki kada ya kullaceni" tana faɗin hakan tayi waje abinta.. wata baƙar mota ce ta shigo cikin airport ɗin da masifar gudu, lokacin jirgi yana dab da tashi, Gaza ne ya fito fuska rufe, sai kuma driver, bayan motar su kaje tare da buɗe murfin motar, Gaza yace "Keeee" Sara dake zaune ta kifa fuskarta a tsakanin cinyoyinta, rabonta da abinci tun jiya, yunwa ta keji sosai, haka kurum kuma yau tashi kanta a sake, tana ganin yanayin garin kamar ta san shi, lokaci zuwa lokaci take tuna jejin Zahel da kuma ƴar uwarta Sairah, kanta ta ɗago a hankali tare da ware manyan idanunta tayiwa Gaza kallo guda ta ɗauke kai, tana ya taɓe baki, Gaza yace "fito Malama, banda Oga ya nace ba tun a Nijeriya zai aiwatar da abinda muke buƙata ba, ido ne kawai ga za'a ƙwaƙwole" ɗayan yace "A'a Gwamma muje su ganta, su kalli idanunta ko irinsa ake buƙata" Gaza yace "Wlh shine ma, ba gasu nan farare ta tas ba, kuma manya wlh kuɗi za'a samu da yawa" dam! Gaban Sara ya faɗi, ke nan idanunta suke buƙata, tsoro ne ya kamata sai bata nuna ma, a zuciyarta kuma duk yadda tayi ƙoƙarin faɗin sunan Allah kasawa tayi, sai dai tace "Abin bauta kabas ka taimake ni" fitowa tayi ko kayan jikinta bata sauya ba, idanunta yyi jajur sbd kukan data kwana ta nayi. Tana tsaye suka gama komai, kafin Gaza yace "Muje jirgi" binsu tayi kamar wacce aka ja, kasancewar basa buƙatar ta faɗawa wani ya sanya suka kama mata vip, su kuma suka zauna a nrml waje, ƙirjin Sara na bugawa sosai, ta buɗe ƙofar vip ɗin ta shiga tunda ta shiga taji kanta ya tsara, ƙara sawa tayi wajan kujera ta zauna this is the first time data shiga jirgi, zama tayi ta ƙankame jikinta tare da kifa kanta a tsakiyar cibiyoyin ta, wajan 20 minutes da zamanta, aka buɗe ƙofar vip ɗin a hankali aka shigo, hannunsa riƙe da wayarsa ɗaya hannun kuma yana cikin aljihu, ƙana nan kaya ne a jikinsa wanda sukai masa kyau sosai, dugun Mutum mai faɗin ƙirji, sam bai kula da Sara ba, domin already shi kaɗai ya buƙaci zama cikin vip, kujerar kusa da Sara yaje na nema ya zauna, idanunsa ya lumshe ya jima a haka kafin a sanar kowa ya saka belet, Sara na jin Announcement ɗin ta ɗago kai, tsoro ya kamata juyawa tayi ta kalli mutumin dake kusa da ita ganin ko fuskarsa bata ta iya gani, yasa ta ɗauke kanta ta ɗaura belet ɗin kamar yadda taga yayi, a hankali jirgin ya fara tafiya a ƙasa alamar dai ya shirya tashi, Sara ta ƙanƙame jikinta tana ƙoƙarin cire belet ɗin sbd jirin dake kwasar ta, ga aman dake shirin zobu mata, Shi dai yana jinta duk abinda take, ko ɗaga kansa bai ɗago ba, balle yasan wace kusa dashi, Sara gani take tamkar kayan jikinta zai zube hakan yasa ta zare belet ɗin da sauri ta miƙe tsaye, tana Miƙewa jirgi na ɗagawa zuwa sama gaba ɗaya tayi baya tare da faɗawa kansa, jinta jikin mutum yasa gaba ɗaya ta ƙanƙamesa tare da sakin kuka, sai a lokacin ya ware idanunsa dake rufe kallon yadda ta ƙanƙamesa yyi, bai ce komai ba har jirgi ya samu daidaito a saman gajimare, idan ransa yyi dubu ya ɓaci domin baya ƙaunar mace mara aji, jirgi na fara gudu ya sanya hannunsa tare da ture ta, a gigice Sara ta saki ihu tana riƙe kanta tare da kallon mutumin wani irin zare ido tayi tace "Twin...


Masu karanta littafi na as free.... Kada ku damu ba zan Allah ya isa ba, amma nasan akwai haƙƙi na akan ku...... It's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank...08119237616[08-15 08:44] +234 703 831 1110: *18 Nimcyluv*
Idanunsa dake rufe ya buɗe da ɗan sauri, jin kamar ya san mallakin mai Muryar, kallonsa ne ya sauka akan ta lokacin kuma tuni Sara ta sunkuyar da kanta sbd ciwon data keji, bai iya kallon fuskarta ba sai kanta dake sunkuye ya jima yana kallonta a haka, kafin gently ya ɗauke idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa, Numfashi Abeed ya sauke yana tunanin yadda Muryar tayi masa kala data “Saaa...” Miƙewa Sara tayi tsaye tana riƙe da kanta matsawa tayi kusa dashi kaɗan kamar zatai kuka tace "Uhm..Amm..." A wannan lokaci bugawa zuciyar Abeed tayi da ƙarfi domin ya gaba tabbatar wa Muryar Sara ce, idan itace mene ya kawo ta nan? Tayaya tabar masarautar Bilhira tazo nan? Ko har an ɗaura aurenta da Junaid ne ya taho tare da ita? Kasa ɗago kansa yyi sai ci gaba da sauke ajjiyar zuciya da yyi, Sara dake tsaye cikinta na juyawa ta fashe da kuka tana ƙanƙame jikinta, ganin ko inda take Abeed bai kalla ba, amai take son yi amma bata san inda zatai aman ba, gently ya buɗe idanunsa ya kalleta suka haɗa ido, suna kallon juna ta ƙara sakin kuka, was shock Abeed ya bita da kallo frm head to toe, gaba ɗaya tayi datti ga yunwar dake damunta wacce duk a lokaci ɗaya ya fahimci hakan, kasa magana yyi sbd mamki juyawa yyi ya fara kallon vip ɗin bbu kowa sai su ɗaya, Sara ta buɗe baki da ƙyar tace "Aman zanyi" Abeed ya ware idanunsa sosai a kanta da ƙyar ya buɗe baki yace "Yi akai na" ba musu ta matso kusa dashi tana riƙe ciki, haɗe fuska yyi sosai kafin yace "Ashe ba hankali?" Turo baki tayi tace "cikina ciwo fa" yana daga zaune ya nuna mata wani waje, da sauri ta tafi wajan ya bita da ido, not too long ta fito fuskarta duk jiƙe da ruwa, kallo ɗaya yyi mata ya ɗauke kansa tsaye tayi kansa tamkar shine ya kawota jirgin, tsaki yaja yace "Matsa kai na" matsawa tayi zuwa kujerar data tashi tana maida numfashi, shiru wajan yyi babu wanda ya sake mgn, sai da Sara ta gaji tace "I'm hungry" bai kalleta ba yace "Cinye Ni" kwaɓe fuska tayi tace "Olser na zai tashi, idan ya tashi ji nake kamar zan mutu kuma ance yaci ƙarfi na fa, ya kusa taɓa hanjin cikina" gabansa ne ya faɗi sai bai nuna ba, kawai ya tura mata abincin da aka kawo masa, kamar wacce ta shekara da yunwa haka ta fara cin abincin sai da ta cinye tass, ta sha ruwa ta kallesa tace "Na cinye" yace "Owk" ta marairaice tace "I'm sorry.." shiru yyi sai kuma yace "For..?" Duk abinda yake idanuna a rufe yake tace "Na cinye maka Abinci, kuma kai baka ci ba" banza yyi mata, lokacin da take cin abinci bata tuna baici ba sai yanzu data cinye komai, sunkuyar da kai tayi hawaye na sakko mata, yanzu shi ke nan idanunta za'a cire? Kuma ta san ba lallai Twin yyi komai ba, tunda ko kallon ta baya son yi, kuka ta saki tana faɗin "Wayyo Idanuna" sai a lokacin ya buɗe idanunsa ya kalleta ganin yadda take kuka da dukkan ƙarfin ta ya sanya yace "Keee" ƙin ɗagowa tayi taci gaba da kuka abinta, tsaki ya saki yace "Tashi kibar nan wajan, Mtwss ban son ihuu hk nan for no reason ok" sai a lokacin ta ɗaga kanta suna haɗa idanu tayi ƙasa da nata kan tace "Ba wasu ne suka ce zasu cire min idanu ba" hannunsu ya sanya ya harɗe ƙirjinsa

Please Login or Register in order to submit comment