Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riƙe da briefcase yana tafe a hankali shi da wani suna Mgn mai muhimmaci, har Zain ya isa wajan motarsa baice komai ba sai da ya buɗe motar ya shiga ya kalli Mutumin yace "Ina da cases da yawa, amma zan duba naga" yana faɗin hakan ya yyiwa motar key tare da fita daga cikin Court ɗin, driving yake a hankali amma zuciyarsa na can Masarautar Zahel kullum a zalzalarsa take akan ya koma ya ɗauko Sara, a haka har ya iso gida bayi da Kuyangi nata gaishe sa, A Main Parlo ya samu Amma ita da Amintacciyar kuyangar ta zama yyi yace "Barka da yamma Amma" Murmushi tayi masa tace "Sannu ya hanya?" Yace "Allahamdulilla" tace "Naila nata rigima tana neman shalele" ya zaro ido yace "Bari na freshen up na leƙa" ta jinjina masa kai. Part ɗinsa ya shiga Du'a na ganinsa ta miƙe da murna tare da rungome sa tace "Oyoyo gwarzona" ta faɗa tana sakar masa kiss a wuyansa idanuna ya lumshe ya riƙe ququnta tare da ƙanƙame ta yace "Ya gida wify?" Tace "Babu daɗi baka nan" yana kissing ɗin gefen kunnanta yace "Uhm Ayyah" ya faɗa yana ɗago fuskarta a hankali ya wani haɗe bakinsu waje guda domin gani yake hakan shine zai iya mantar dashi tunanin Sairah dake damunsa a zuciya, ɗaukan ta yyi cak zuwa bedroom sai da komai ya lafa yyi wanka ya shirya cikin kayan shan iska yace "Bari naje wajan Naila" Murmushi tayi masa shi kuma ya fita zuwa sashen Naila, tana zaune ta saka furar data dama a gaba tace "Ita duniya a ba aljanna mace, daga Kano har duniya ɗai ɗaiku ne masu gsky Alkur'anin Ubangiji" Zain yyi sallama ya shigo da sauri ta ɗauki ƙwayar data dama furar ta ɓoye a bayanta tace "Ya..Ya..Ya haka kamar ana yaƙi za'a faɗo min kai ko yaƙin badar ai ba'ai wannan tijarar ba na rantse, kowa ya zama gantalalle wacce lukutar masifa ke son damun ƴan arewa ne?" Zain yace "Ke kin san yaƙin badar ke nan" ta riƙe haɓa tace "A'a ba zan kula ka wlh, ba sai dai kaci kanka ba? Kuma ka ƙaryata Uwarka Saratu" zama yyi yana faɗin "Naila ance kina kirana" ta marairaice tace "Ayya Alqur'anin Ubangiji na ɗauka wani can sallamamman ne, kayi hqr kaji kada ka kullaceni, yanzu daman na gama dama maka furar" sakkowa Zain yyi yana Murmushi yace "Ina shi yana zan wajan matarsa" Naila na basa furar tace "A to, ai kowa ta kai daman kana ganinsa kasan bashi da kunya idanunsa a tsakiyar ka yake fa? Baya ganin kowa da gashi kuma har yanzu matar taƙi yin ciki fa, Allah dai yasa basa maka gorin auren, tunda dai babu wanda kasan zuciyarsa sai dai ace li'ilafi qurash" Murmushi kawai Zain yyi har ya gama shan furar ta ɗauke ƙwaryar tana faɗin "A'a daman ai dan Allah nayi bance a gode min ba, amma dai duk ɗan halarci akai masa abu yace ya gode Allah ya sauwaƙa kamar dai mai rawanin can ne yaban kuɗin daka furar?" Shi dai Zain baice komai ba ya shiga danna Wayarsa kasancewar e-mail ɗinsa yana kan wayar yana shiga idanunsa ya sauka akan saƙon Abeed wani irin zabura yyi farin ciki a kama sa, bai taɓa tunanin zai ga wannan saƙon ba daman yasan ko mai daɗewa Abeed zai tuna dashi, da sauri ya fita daga sashen Naila tana zuwa tace "Kaga shasha tasono butulo kawai.." ta faɗa tana ajjiye Apple ɗin hannunta.....Har dare Anuty Zulfa na saka ran ganin Abeed ya dawo da Sara amma shiru ta kira Wayarsa babu adadin yaƙi ɗauka, Abeed kowa bai ma san meke damunsa ba shi kawai yaji baya so kuma baya ƙaunar Yarima Yashim idanma auren ne zai nema mata wani daban ba Yarima Yashim ba, Yana zuwa gida ya buɗe mota yace ta sauka ganin yanayinsa yasa ta shige ciki yana ganin shigarta ya rufe gidan ya fita har kusan 11 na dare bai shigo ba. Sara na zaune a parlo ta takure tsoron gidan ya kamata tayi wanka ta sauya kaya ta ɗan sha ice cream, 12 daidai taji motsin za'a shigo parlon da sauri ta miƙe tsaye Ƙafarsa ta fara shigowa cikin parlon sai kuma hannunsa dake riƙe da jacket ɗin Suit ɗinsa, kamar zai kifa haka yafe tafiya a hankali da sauri ta ja baya saboda warin abinda taji ga wata ƙatuwar kwalba a hannunsa, da ƙafa ya tura ƙofar parlon idanunsa da sukai jajur ya buɗe a kan Sara ya shiga Kallonta tun daga sama har ƙasa riga da wando ne a jikinta wando iya cinyoyinta ne, ko ɗan kwali babu a jikinsa, a hankali ya shiga takawa zuwa inda take tana ja baya yana binta juyawa tayi da gudu zata bar parlon ya sanya ƙafarsa tare da harɗe mata ƙafa gaba ɗaya tayo baya zata faɗi yyi saurin riƙe ta, bashi da wani ƙwari hakan ya sanya gaba ɗaya sukai baya tare da faɗawa saman Kujera itace a ƙasa shi kuma ya faɗa kanta tare da danne ta....**31***_Zain Abeed 31.... Complete book 1, 2 ku shiga Arewabooks domin samun update fiye da ɗaya_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62b1e5ccf0bafa279f2af05c

_Follow My Acct Habibaties🥰👇🏾_
https://arewabooks.com/u/nimcyluv

Numfashi Sara ta shiga ja da ƙyar sbd yadda Abeed ya sakar mata dukkan nauyin jikinsa, ga yanayin yadda abin shaye-shayen nasa yake dukan hancinta kamar zata amayar da kayan cikinta haka ta keji, idanunta ta buɗe da ƙyar ta zuba akan ƙyakkyawar fuskarsa, idanu suka haɗa wani irin kallo yake binta dashi kallon da ba kowa zai iya gaya ma'anar sa ba, bakin Sara ya shiga rawa cikin tsoron yanayin Abeddeen tace "Uhm, bacci zan ka ɗaga ni" shiru yyi mata Banda Kallonta babu abinda yake, Sara da Idanunta tuni ya gama cika da hawaye tace "kayi min nauyi fa" sai a lokacin ya ɗan juya jajayen idanunsa wanda suka janye kafin a hankali kuma cikin mutuwar jiki ya zura hannayensa ta bayanta ya wani irin haɗa cikinta da fuskarsa yana lumshe idanunsa da sauri Sara tace "Ni ka sake ni, Allah zan faɗawa Mami" shi dai ko yana jin abinda take faɗa to ba sosai ba sbd gaba ɗaya jikinsa ya saki, a kasalance a kuma yanayi na son samawa zuciya da gangar jiki nutsuwa ya zaro hannunsa guda ɗaya tare da manna shi a shafaffan cikinta a hankali ya zame rigarta tare da ɗaga ta sama, rintse idanu Sara tayi sbd jin abinda Abeed keyi jikinta ya fara rawa na tsoro da kuma fargaba, domin gaba ɗaya taji tsigar jikinta na tashi, yunƙura tayi zata tashi ya ƙara sakar mata nauyin jikinsa, idanunsa da suke a lumshe ya buɗe kai tsaye kuma Kallonsa ya sauka a farar Cibiyarta mai kyau wacce take da ɗan zurfi ga ƙasan cibiyar wata baƙar tawadar Allah wacce ta ƙara haska fatar cikin nata, numfashi Abeed ya sauke tare da tsorawa wajan idanu kamar wanda yake neman wani abu, idanunsa yaja ya rufe ruf yana wani irin sauke ajjiyar zuciya, a hankali ya manna fuskarsa akan cikin nata bakinsa daidai wajan Cibiyarta ɗaya hannunsa kuma ya riƙe waist ɗinta ƙam! Wajan 2mnts suna haka kafin a hankali taji saukar tongue ɗinsa a cikin cibiyar nata wani ƙanƙamesa Sara tayi sbd jin abinda bata taɓa tunani ba, jikinta har rawa yake, Abeed jin riƙon da Sara tayi masa yasa shi ƙara zura tongue ɗin nasa yana ɗan juya shi tare da sakar mata wani irin numfashi mai zafi, a hankali kuma jikinsa ya ɗan fara rawa cikin wata kasalalliyar Murya mai tarin rauni damuwa baƙin ciki, buƙata, muradi ya buɗe bakinsa kaɗan daidai yadda Sara zata iya jinsa yace "Tashi a nan.." ya faɗa a kame kuma a wahalarce idanunsa yyi jajur sbd wahala da kuma abinda ya keji a gangar jikinsa, Sara ta yunƙura zata tashi taji ya ƙara ƙanƙame ta yana sakin numfashi yana ƙara manna fuskarsa a cikinta, kuka ta sanya masa tace "Dan Allah Uncle kayi hqr..." Ta faɗa tana turesa amma bai motsa ba, yana cewa ta tashi a wajan amma yana ƙara ƙanƙame ta, Sara ta shammace sa ta sakar masa cizo a gefen fuskarsa ya ɗan sassauta riƙon da yyi mata, da wani irin zafin nama ta sanya dukkan hannunta tare da turesa waje guda ta kwasa da gudu zuwa bedroom tana wani irin numfashi tare da dafe ƙirji, ƙofar ta rufe tare dayi mata key a hankali ta zube bakin ƙofar tare da saka kuka wanda ita kanta bata san dalili ba,amma har ƙasan Zuciyarta bata jin daɗin yadda take ganinsa yana shan kayan maye,ta jima a wajan kafin bacci ya ɗauke ta a wajan kuma a nan baƙin ƙofar. Abeed kuwa Sara na barin wajan yaji kamar ana zuba masa wuta a jikinsu domin har wani huci fatar jikinsa take, a hankali ya mirgina tare da jan pillown kujera ya ƙanƙamesa ko zai ji daidai, har aka kusan kiran Subhi idanunsa biyu kuma bai motsa ba, ana tsaka da kiran Assalatu bacci ya ɗauke sa.
Sara kamar a kunnanta aka kira Subhi jiki a matuƙar mace ta shiga buɗe Idanunta har ta kammala buɗewa Idanunta sun kumbura sosai gently ta miƙe tsaye har zata shige bathroom sai kuma ta ɗan buɗe ƙofar bedroom ɗin nata a hankali ta leƙa kanta zuwa waje, fararen tafin ƙafarsa ta fara hangowa kafin kuma ta hangi hannayensa da suke riƙe da pillow, fitowa ta ƙarasa yi zuwa parlon, cike da nutsuwa take tafiya tana son taga ya tashi yyi sallah amma tana tsoran abinda zai iya yi mata, fuskarsa ta leƙa taga fess ya wani ƙara haske da kwarjini duk da bacci yake, juyawa tayi ta rasa mene Zatai sai kawai ta ɗauki Wayarsa tare da yin connecting wayar da t.v jikinsa Sa'a kuma yyi Suratul Yaásin ta kunna gaba ɗaya ƙira'ar ta karaɗe duka Parlon da sauri ta ajjiye wayar ta juya zuwa bedroom ɗin ta, Abeddeen yana cikin bacci yaji saukar karatu a kunansa duk yadda yaso ya share kasawa yyi a hankali ya shiga buɗe idanunsa wanda suka dawo kamar yadda suke, da mmki yake min parlon da kallo da kuma inda ya kwanta ɗin bai san yaya akai ya kwanta a Parlo ba, ko wanka bai ba Miƙewa yyi sai a lokacin ya kula da kwalbar dake yashe a parlon kansa ya dafe lallai yau ransa ya ɓaci da yawa, walking slowly ya nufi bedroom ɗin sa yana zuwa ya shige bathroom tare da sakarwa kansa shower yana jin gajiyar jikinsa na warware wa brush yyi bayan ya gama ya fito ɗaure da towel, a nutse ya shiru cikin farar jallabiyar yana sabga ƙamshi Hugo boss yana gama shiryawa ana tayar da sallah, zama yyi kan bed yana runtse idanunsa kamar wanda aka tsikara kuma ya miƙe tare da ɗaukan pra mat ya nufi waje, Sara na ganin ficewarsa daga cikin gidan baki ɗaya ta sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, bathroom ta shige tayi wanka itama ta shirya cikin thobe jallabiya tana zaune dai a Zuciyarta tana istigifari Tunda Abeed yace babu dama tayi sallah dole sai ta sake amsar musulunci. Ƙarfe 7 ta miƙe daga kan bed ɗin a hankali take tafiya har ta ƙarasa cikin haɗaɗɗan kitchen ɗin gidan, ga mmkinta kaya ne da yawa a deep frizeer ɗin dake kitchen ɗin, ƙilan ba'a taɓa amfani dashi Bama, dankali ta kwasa ta shiga ferayewa tana gamawa ta haɗa kayan miya iya albasa da papper, kana ta ɗauki wani bushasshen kifi mai kyau ta gyara fatan dankali tayi yaji bushasshen kifi sai tea da kuma Chips, tana gamawa ta gyara wajan ƙamshi duk ya cika wajan, fitowa tayi daga kitchen ɗin zata bedroom ƙamshin turaren sa ya shiga hancinta, kasa kallon inda yake tayi ba tare da tace komai ba ya shige bedroom ɗin ta sauya kayan jikinta zuwa Abaya mai ɗan faɗi red and black. Abeed dake zaune a Parlo watching TV na labarai ya ɗan saci Kallonta lokacin da zata shige kitchen idanunsa ya mayar kan t.v yana zaune har ta fito ɗauke da plate da cup da kuma wata ƙaramar warmer, tana zuwa wajan ya miƙe tsaye ganin haka yasa Sara tace "Mrng.." bai amsa ba ya shige cikin bedroom abinsa yana zuwa ya kwanta kan bed yana lumshe idanunsa abu ne a zuciyarsa yake masa yawa dole ya nemi ma fita ta hanyar nisa daga inda take.
Tana zaune a Parlo bayan taci abinda zata iya ci ta gyara wajan kallon t.v. take amma hankalinta na wani wajan har bata san lokacin da aka buɗe ƙofar aka shigo ba, da sauri ta miƙe tsaye tana faɗin "Mami..." Wata harara Mami ta watsa mata kafin ta zaune saman Kujera hannunta riƙe da key car fuskarta a haɗe, Sara ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da tsugunawa tace "Ina kwana Mami.." ba tare da Mami ta kalleta ba tace "jeki kira min shi" shiru Sara tayi domin tana tsoran fushin Mami ba kaɗan ba, A fusace Mami tace "Ko ba zaki iya zuwa bane? Ki zuba min idanu Sara?" Girgiza kai Sara tayi Idanunta na cika da hawaye kafin ta miƙe tsaye tare da nufar bedroom ɗin sa, yana kwance har lokacin idanunsa a rufe jin Sallamar ta ya sanya ya juya a hankali tare da kafeta da fararen idanunsa, kanta a ƙasa tace "Mami na kira" idanuna ya ware kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "Mami?" Kai ta ɗaga masa alamar eh, ya miƙe zaune ya zuro ƙafafuwan sa ƙasa fuskarsa a kame yace "Zo nan" ƙara sawa tayi wajansa ya haɗe fuska yace "Ba shige min nace kiyi ba" baya ta ja kaɗan yace "Ke kika kirata?" Ta girgiza masa kanta ta a haɗe fuska kamar yadda yyi yace "Ni kike haɗewa fuska?" Tai masa shiru calmly yace "Idan kika sake kika faɗawa Mami wani abu ko....uhm" ta buɗe Idanunta ta kallesa tana watsa hannunta tace "Kamarya" ya haɗe fuska yace "ban sani ba" juyawa tayi zata fita yyi saurin sanya hannunsa tare da kamo ta, kwaɓe fuska tayi cikin ƙasa da Murya tace "Ni ka sakeni mene haka wai" ƙin sakinta yyi sai ma matse hannunta da yyi tana shirin sakin kuka yyi saurin sakinta tare da Miƙewa ya shige bathroom, fita tayi zuwa Parlo Mami ta bita da kallo tana zuwa tace "Yana zuwa" harararta Mami tayi tace "Meya zaunar dake?" Kan Sara a ƙasa tace "Yana bathroom ne yanzu ya fito" Anuty Zulfa tace "Sai akace ki zauna kuma?" Shiru kawai Sara tayi kanta a ƙasa ta ɗan jima wajan, kafin ƙamshin Bois elite ya shiga karaɗe parlon, zuciyar Sara ta buga da ƙarfi yana sanye da Ralph Lauren Kaftan st, Zama yyi kan kujera idanunsa na can wani wajan yace "Mrng Mami" Anuty Zulfa tace "Bashi ya kawo ni wajanka ba Abeddeen kullum yaran dana haifa suna gaida ni riƙe taka na gode" a hankali yace "Uhm" shima fuska ɗaure yake kallon wani wajan Anuty Zulfa ta kalli Sara tace "jeki ɗauko mayafin ki" Sara ta ɗaga Idanunta tare da kallon Anuty Zulfa ganin yadda Anuty Zulfa ta haɗe rai yasa ta miƙe ta nufi bedroom, Anuty Zulfa ta kalli Abeed da yake danna Wayarsa tace "Wato Abeed ni zakaiwa tijara, ga dai yara kaca kaca a gabana ba, so ban damu ba dan kaƙi ganin kima da daraja ta, kai ne Ruɓaɓɓe wlh, daga yau sai yau kada ka kuskura ka ƙara ɗaukan Sara zuwa wannan gidan, mene haɗin ka da ita?" Sai a lokacin ya juya ya kalli Anuty Zulfa yana Kallonta ya ɗauke kansa baice komai ba, tace "Mene dalilinka na kawo ta gidanka,ehhh Abeed? Ko kuma ita tace ta gaji da zama dani?" Shiru kawai yyiwa Anuty Zulfa idan yace zai mgn to fa iya gskyar abin zai faɗa mata, Murmushi Anuty Zulfa tayi tace "Ko son Sara kake?" Nan ma ya juya ya kalli Anuty Zulfa daidai lokacin kuma Sara ta fito daga cikin ɗakin gaba ɗaya suka zuba masa idanu suna jiran suji mene zai faɗa.

Sorry for the short typing....Ina wajan aiki yau currr, to ba sai dai hqr ba don Allah? Contact to subscribe.... 08119237616.

**34**she never thought of herself, she had never found herself in such a situation, jikinta sai rawa yake ta wani rufe idanunta sbd tsoro da fargaba,a kind of kiss kisses her, further inserting her into his body, da wani irin sauri kuma Abeed ya saki Sara yana juya mata baya tare da nufar wajan sink a hankali ya tari ruwa a hannunsu ya shiga kuskure bakinsa zuwa fuskarsa, Sara dai har lokacin bata dawo daidai ba, tana jin bakinta na mata wani irin zafi da zugi tamkar fatar wajan zata cire sbd zafi. Kallon yadda ta rufe idanu yyi hannunta akan baki sai kuma sharr hawaye ya shiga zubu mata daga cikin Idanunta, walking slowly ya nufi inda take tsaye yana zuwa ya shiga ƙare mata kallo frm head to toe, har ya juya sai kuma ya sake kallon ta fuska kame babu alamar wasa yace "Keee..." Kin buɗe ido tayi a ɗan tsawace "Open your eyes" buɗe Idanunta tayi hawaye har lokacin bai tsaya mata ba, hannunsa ya zuba cikin Aljihu kafin Murya can ciki kamar me raɗa ya ƙara matsawa inda take Numfashinsa na haɗewa waje guda har yana iya jin yadda ƙirjinta ke ɗagawa, gently ya ranƙwafa daidai fuskarta da wata kalar Murya yace "Uhm, na haɗiye ƙwaro,za kici abinci amma sai kin ɓata baki? Bani da hanky shiyasa...." Ya ƙare maganar a hankali yana manna mata kwantaccen beard ɗinsa a matar wuyanta tana ƙoƙarin mgn kuma taji saukar wani fitanan nan kiss a ƙasan ƙunanta wanda ya sanya har danshin softness lip's ɗinsa.... Wani numfashi taja da ƙarfi tana buɗe idanunta babu kowa a kitchen ɗin kamar walkiya haka yabar wajan baki ɗaya, to ! Kodai bashi bane daman? Amma ga ƙamshi turaren sa nan, ta jima a wajan daga ta shafa baki sai ta shafa ƙasan kunnanta Ita dai bata taɓa ganin Tijara irin wannan ba, fuskarta ta wanke ba tare data ɗauki pancakes ɗin ba ta nufi Parlo, nan ma babu kowa da alama tuni yabar gidan ma, bedroom ta nufa tana zuwa ta kwanta kan bed tare da ƙanƙame jikinta tai shiru data rufe idanunta sai kuma ta buɗe tana ganin kamar lokacin ne yake mata dukkan abinda yayi a yau ɗin. Abeddeen na barin kitchen ɗin ya fito Parlo bai tsaya jiran komai ba yyi waje yana haɗa hanya yana jin kansa na sara masa, a hankali kamar mai tsoron takawa haka ya nufi cikin motarsa yana zuwa ya shiga mai gadi ya buɗe masa gate yabar gidan baki ɗaya, yana tafiya kan titi ya gangara zuwa gefen titi tare da kifa kansa a string motar yana fidda numfashi yana jin wani sanyi na shigar masa jiki, idanunsa da sukai masa nauyi ya buɗe sosai kafin ya ɗauki bottle water mai sanyi tare da ɓalle murfin ya shiga tsiyayawa tsakiyar sumar kansa sai dai yaji ya samu sauƙi akan abinda ke masa yawo a jiki kafin ya tayar da motar ya nufi wani haɗaɗɗan pharmacy ya siyi magani 5 pack kana ya nufi gidansa, yana tafe mota na bin bayansa tsaki yaja a hankali kuma ya tsayar da driving da yake yana kallon motar ta cikin madubi..... Sarki Mabus dake cikin motar shi da Ayyana yace "Shige kada ki tsaya.." hakan yasa suna zuwa sukai gaba ba tare da sun tsaya ba, kasancewar Ayyana ba tafiya magana ba ya sanya ta ɗanyi shiru kafin a hankali tace "Ba'a gyara biyar ba, goma zata ɓaci" Sarki Mabus yace "Kamar ya ya fa?" Ta ware idanunta dake cikin glass fuskarta a cikin liƙab tace "Ba'a samu Abeddeen ba, Zahel kuma zata lalace" bai gane me take nufi ba dan haka sai kawai yyi mata shiru ta kuma cewa "Samun nasara akansa abu ne mai wahala..." Sarki Mabus yace "Me muke buƙata ne? Ba kuɗin sa da dukkan abinda ya mallaka a rayuwa ba? Sai fa yaƙi bada haɗin kai sannan ne zamu kaiwa rayuwarsa hari" Calmy Ayyana tace "Uhm, gashi wani Company yake ƙoƙarin buɗewa a yanzu" da mmki Sarki Mabus yace "Wanne Company ina kika sani?" A karo na farko ta saki wani Murmushi tace "Company biyu ne, dana kayan kiɗe kiɗe wanda za'a dinga fitar dasu ƙasashe, sai kuma na haɗin gwiwa mutum zai zuba hannun jari duk shera yana ɗaukan kason sa, wanda Company ya samu riba,amma kaso mafi yawa duk na Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas ne..." Shiru Sarki Mabus yyi kafin yace "Idan haka ne muma zamu saka hannun jarin, daga ƙarshe kuma zamu ƙwace Company ya samu mallaki na baki ɗaya, zamu tura mutane biyu wanda zasu je zuwa ga Abeddeen" Ayyana ta jinjina kai alamar hakan yyi kafin su shiga hotel ɗin da suke ta tsaya Sarki Mabus ya sauka daga motar ita kuma ta shige ciki, 30 seconds da shigewarta Sarki Mabus ya shiga.....wani mutum dake tsaye kusa da hotel ɗin ya ɗauki Wayarsa sai da ta kusa tsinkewa aka ɗauka cike da girmamawa mutumin yace "Sir, zargin ka ya tabbata,ina tunanin matarsa ce amma suke pretending sbd kada a gano su" yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da shigewa cikin hotel ɗin. Da ƙyar Abeed yaja motarsa zuwa can gidansa yana zuwa ya shiga toilet tare da sakarwa kansa ruwa ya fito yana ƙamshi shower gel kana ya shirya cikin kayan shan iska kafin gently ya fito daga cikin part ɗin sa, ya ɗauki madara mai kyau da system ɗin ya nufi cikin lambun dake cikin gidansa, yana zaune kusa da ruwa ƙafafuwan sa miƙe a hankali yake operating system ɗin yana shan Madara, ya jima a wajan kafin ya gama ya miƙe tare da komawar ciki, kwanciya yyi saman Kujera ya rufe idanunsa da sauri kuma ya buɗe idanun daga ƙarshe Miƙewa yyi ya nufi gym ɗinsa....... Bayan sallar Issha Sara na zaune sanye da wata maroon ɗin Diva Abaya mai kyau tayi rolling kanta sai Gucci shoe dake ƙafarta, sai ƙamshin take wanda yake ƙara narkar da zuciyar Yarima Yashim dake zaune kujerar dake farcing nata, a hankali yace "Kinji yadda na keji kowa Sara?" Tayi ɗan Murmushi ba tare da tace komai ba yace "Gobe zaki zo ɗin? Ta ware idanunta tace "sai na tambayi Mami" yace "Mami ba zata hana ba, please zanji daɗi idan za'a bani Award ɗin da ƙaramin matsayi na ganki kina min Murmushi" a hankali Sara tace "To zan zo" yace "Good gal" ya faɗa yana jan hancinta kaɗan kafin yace "Zan koma gida daga nan zanwa Mai martaba bayani sai a turo" ta wani kwaɓe fuska tace "To kuma tun yanzu?" Kallonta kawai Yarima Yashim yyi kafin yace "Ehmn, ko baki so na ne?" Ta girgiza masa kai yace "To mene matsalar?" Murya a shagwaɓe tace " Zan ƙarasa sclh" shiru yyi sai kuma yace "Shekara uku Sara?" A hankali duk ta wani narke masa tace "Idan na gama schl sai yafi Yaa Yashim please.." ya jinjina kai yace "A bari kawai kina last semester na level 2 Sara please don't say no...I luv u so much" Turo baki tayi tace "Bana son karatu da Baby fa" wani kalar Murmushi Yarima Yashim yyi yace "To ba zan bari ki samu baby ba har ki gama schl" kamar wata ƙaramar yarinya tace "Da gaske?" Yace "Eh, idan kin amince zaki aure ni ba, ina tsoron rasaki sosai Sara" shiru tayi masa a hankali ya matsa kusa da ita yana ƙoƙarin kama hannunta, ƙamshin Bois elite ya cika gaba ɗaya Parlon ƙasa Sara tayi da Idanunta Yarima Yashim tuni ya fahimci waye, hakan yasa yayi baya fuska ɗaure shima, Sara da taji ba zata iya jurewa ba ta ɗaga fararen idanunta zuwa direction ɗin da yake, abinda bata taɓa gani ba ke nan, yana tsaye cikin wani tattausan farin voyel mai Manyan zane domin har farar singlet ɗin jikinsa ana gani ga wata Black half hula daya sanya sumar kansa tayi baya yyi wani irin kyau baka ganin komai sai fararen idanunsa haɗa idanu sukai dashi tayi saurin ɗauke kanta, a hankali Abeed dake tsaye ya shige zuwa cikin parlon kan kujera ya

Please Login or Register in order to submit comment