Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai taji kuka yazo mata, da sauri ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka kamar wacce aka daka, driving kawai yake sai da yyi nisa kafin ya gangara gefen titi a hankali yyi parking, kashe motar yyi baki ɗaya kafin gently ya fito daga cikin motar kai tsaye kuma bayan motar ya nufa tarw da buɗewa ya shiga kana ya rufe motar, har lokacin Sara kuma take ya jima yana kallonta kafin, kafin cikin ƙasa da Murya yace "Keee...." Ƙin ɗago tayi ta kallesa, ya matsa kusa da ita tare da sanya hannunsu ya ɗago fuskarta da sauri ta rufe idanunta, Abeed yace "Open your eyes.....Saaaaa" shiru tayi masa tana ƙara sautin kukanta, cikin wani irin ɓacin rai ya sanya hannunsa tare da jawota gaba ɗaya ta faɗa jikinsa tana sakin wani kukan, ƙanƙame ta yyi a jikinsa idanunsa yyi wani jaaa, kukanta ya keji har tsakiyar kansa,kamar neman mafaka haka Sara ta rufe fuskarta a ƙirjinsa tana rusa masa kuka da iya ƙarfinta, shiru Abeed yyi yana sauraran yadda take kuka a hankali yake ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, yana ƙara Rungome ta a jikinsa, tun tana kuka har ta dawo shassheƙa ta dawo sauke ajjiyar zuciya. almost 10 minute kafin ya saketa yana ɗago fuskarta da hannayensa, idaniya ta rufe taƙi yarda ta kallesa, Murya can ƙasa yace "Uhm...U called me ɗan shaye-shaye, i didn't do anything, ban maki komai ba, na tsani kuka shine za kizo kina min ihu akai, why baki je wajan wancan banzan ba?" Da sauri ta buɗe Idanunta tana zame jikinta can gefe guda tace "Zaka iya komai, but don't ever trying to call him with that name again" kallon ta kawai Abeed yake da mmki, har zai Mgna sai kuma ya buɗe murfin motar ya fita zuciyarsa na wani irin zafi da ciwo, key yyiwa motar tare da fara tafiya, ganin direction ɗin daya ɗauka yasa Sara faɗin "Ina zaka kaini?" Banza yyi mata a babban wani haɗaɗɗan gida ya shiga Horn gatekeeper ya buɗe masa gate, da gudu ya shigar da motar cikin entrance na gidan, buɗe ƙofar yyi ya fito, wajan side ɗinta yaje yace "Get down.." kallonsa tayi ta ɗauke kai tace "Zaka iya aramin key car ɗin?" Wani kallon sama da ƙasa yyi mata yace "Ok fito" fitowa tayi fuska a kame tana miƙa masa hannunta ya bata key ɗin, durƙosawa yyi kamar zai wani abu ya ɗauke ta Cak, tsoran da Sara taji yasa tayi saurin riƙe masa gaban riƙa tace "Meye haka?" Banza yyi mata tace "Ni ka sauke ni,ni ba ruwana da kai mene haɗina dakai?" Riƙe da ita ya shiga Main Parlo ɗin part ɗin da yake zaune, Bai tsaya ko'ina ba sai bedroom ya sauke ta akan bed not looking up yace "take a shower." Yana faɗin hakan ya juya ya fita ba tare daya sake kallon ta ba, wani bedroom ɗin ya shiga tare da nufar bathroom yyi shower, farin towel ya ɗaura jikinsa na zubar da ruwa ya fito daga cikin bathroom ɗin, shirya yyi cikin Floral lace night wear men, yana zuba ƙamshi ya nufi Parlo wajan Deep frizeer yaje ya ɗauki Apple da chocolate, saman kujera ya zauna domin abin ya zame masa jiki sam baya iya bacci da daddare, yana kwanciya zaiji tamkar wani abu ya masa mararsa ga wani abu dake taso masa, yawancin baccin sa sai rana. Wajan ƙarfe 3 na dare yana zaune idanunsa a ɗan lumshe kamar daga sama ya fara jiyo ihun ta sama sama, har ya karaɗe cikin kunnansa idanuna ya buɗe kafin gently ya miƙe tsaye hannunsa zube cikin Aljihu, yana wani kalar tafiya a kasalance, handle ɗin Ƙofar ya kama tare da turawa, haske ya mamaye bedroom ɗin daman yasa ba zata iya kwanciya ba haske ba, ya jima a haka yana kallon yadda take kuka da ihu ƙasa ƙasa tana ƙanƙame jikinta, ƙarasa shigowa cikin bedroom ɗin yyi yana rufe ƙofar, walking slowly ya Ƙarasa bakinsa bed ɗin yana ƙara ware idanunsa akanta, ganin yadda take abun kamar mai mafarki ya sanya Abeed zama kan bed tare da sanya hannuna ya jawo tafin ƙafarta, a firgice Sara ta buɗe idanunta tana faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" with so surprised Abeed yake Kallonta, jin kalmar data ambata shi dai baice komai ba, yana ta kallon fuskarta wacce tayi wani kalar fresh, Ajjiyar zuciya Sara ta sauke kafin a hankali ta ɗaga kanta suka haɗa idanu da Abeed da sauri ta janye idanunta tana sauka daga kan bed ɗin, har ta nufi ƙofa ta tsaya kanta a ƙasa tace "Zanyi alwala, na manta ban sallar Issha ba" Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Abeed ya sauke yana jin wani sanyi a ransa, amma fuskarsa a kame still kuma baice mata komai ba, Jin shiru bai ce komai ba tayi tunanin ko baiji bane hakan yasa ta ɗago kanta suna haɗa idanu tayi saurin ɗauke kai murya can ƙasa tace "Alwala zan" Miƙewa tsaye taga yyi a hankali ya ƙarasa inda take tsaye, dab da ita yaja ya tsaya kafin ya ɗan leƙa fuskarta ganin yadda ta rufe idanunta yasa a hankali yace "Kalleni nan" ƙi tayi baya son surutu a daran nan hakan yasa ya sanya softness hands ɗinsa saman haɓarta ya ɗaga fuskarta cikin wata kalar Murya yace "Kalleni nan..." Idanunta ta buɗe suka haɗa idanu da sauri ta rufe idanunta tana ƙoƙarin ɗauke fuskarta taji yace "heeeee, hold on.." shiru bai mgn ba sai can yace "Sallah zaki?" Kamar ƙaramar yarinya ta ɗaga masa kai tana jin yadda yaja numfashi kafin yace "ki jira gobe to" da sauri tace "mene yasa? Idan kuma ban kai goben bafa?" Yana riƙe da fuskarta har lokacin kafin yace "Sbd a Yanzu sallah ta haramta a gareki, ke ba Musulma bace Saaaaaa" wani irin kallonsa take idanunta ya cika da hawaye tace "Ni ɗin
ce ba Musulma ba?" Ganin ba lallai ta fahimta ba ya sanya yace "Kin san Masarautar Zahel?" Shiru tayi trying to reconnect kafin ta ɗaga masa kai alamar ta sani yace "Oops, sune suka kafirtar dake, kin san adadin da kika ɗauka baka sallah,kina ambaton sunan Abin bauta kabas?" Fuskarta ta ƙwace daga hannunsa kafin a hankali ta zube a wajan nan gabansa ta shiga rera masa wani irin kuka tamkar Shine yyi mata laifin, ɗago ta yyi tsaye yana ƙoƙarin mgn yaji tace "I hate myself Uncle....Naji bana son kai na, ina matsayin Musulma ace na ɗauki lokaci bana sallah, sun cutar dani ba zan yafe ba" ta faɗi hakan tana wani irin kuka jikinta har rawa yake kasa ce mata komai yyi, sai hannunta ɗaya kama har zuwa bakin bed ya zauna kana ya zaunar da ita, hannunsa riƙe da nata yace "Saraaarh.." kasa kallonsa tayi yace "kalle ni Saaaaa" idanunta wanda sukai jaa ta buɗe ta kallesa tana jan numfashi, kafin yace "I'm worried too.." kallonsa kawai take kamar yadda yake Kallonta Abeed licked his lips and Said "Amma zanan ƙaddarar ya shige komai, yadda Ubangiji yaso shine zai kasance dkai, accepted Yourself the way you are...ok" ya faɗa yana sanya hannunsa saman fuskarta a hankali ya goge mata hawayen fuskarta, cikin ƙasa da murya tace "Kace zaka min aure ko?" Wani kallar kallo yake binta dashi baice komai ba tace "Ina son kayi min Auren Uncle" ba zaka taɓa gane abinda yake fuskarsa ba calmly yace "How old are you?" Ƙasa tayi da kanta tace "17 or 18 na manta" da mmki yace "Kuma at this age kike son Aure?" Shiru tayi yace "Uhm, ina jinki" tace "Uncle, nifa ban san Mamana ba, gashi Abbanmu da muka yarda dashi shine gatanmu a yanzu shine ya lalata mana rayuwa, ya rabani da ƴar uwata" taɓe baki yyi irin zan can mai damesa ba kafin yace "Ƴar uwa?" Ta ɗaga masa kai, ya ranƙwashi kan nata tayi saurin cewa "Aucchhh.." yace "da baki na tambaye ki" tana tura bakinta gaba tace "Nida ita twins ne, Her name is Sairah" shiru Abeed yyi yana son tuna wani Abu kafin yyi mgn tace "Mu tunda bamu samu gatan iyaye ba, ina son gina rawa rayuwar da iyali masu albarka da basu kular dana rasa Uncle, koda banyi tsayin rai ba nasan na bar baya mai kyau shiyasa nace ina son auren a yanzu" jajir haka fuskar Abeed tayi can yace "Ke nan kin san komai na aure?" Idanunta ta juya tace "Me kace" Miƙewa yyi ba tare da yace mata komai ba, yana fita bedroom ɗin sa ya shige tare da kwanciya ya lumshe idanunsa Zuciyarsa cike da tunani, yana kwance har aka fara kiran sallah, lokacin da akai Assalatu yaji an turo ƙofar bedroom ɗin sa, mirgina wa yyi yana jan duvet domin rufe jikinsa, idanunsa akanta ganin idanunsa biyu yasa Sara cewa "Naga an kira sallah ne" ya ware mata baice komai ba ta juya tare da fita, can ya sake dawowa tace "Zaka makara" a ɗan fusace yace "Out of my room.." mai makon ta fita sai ta leƙo tace "kamarya, Sallah ake fa" banza yyi mata ganin haka ta Ƙarasa shiga ciki duk da tana shakkar sa amma bata nuna masa, har bakin bed ɗin ta ƙarasa tace "ka tashi" wani irin juyowa yyi tare da sanya hannunsa ya fisgota zuwa kan gadon saura kaɗan ta faɗa jikinsa ya matsa yace "Ke dan Allah bana son takura, lokacin da baki naki sllah ubanwa ya takura ki ne? Ko addini kika fini sani" baki ta murguɗa masa ya sanya hannunsa ya make bakin kafin ya sake ta yace "Fitar min" yana faɗin hakan ya nufi bathroom tana zaune yyi Alwala ya fito lokacin tuni an fara Sallah, bai ƙara kallon inda take ba, yana ƙoƙarin zame wandon jikinsa tayi wani irin Miƙewa tare da zabura zata bar bedroom ɗin. kafin ta fita yyi saurin riƙo hannunta tare fisgota tayi baya zata faɗi yayi saurin riƙe ta, jikinta na rawa tace "Da...daman" kasa mgn tayi ganin yadda yake binta da wani kallo kamar ba Abeed ɗin data sani ba, can ƙasa yace "ina zaki? Ai baki isa ba kina nan zan gama komai" yana faɗin hakan ya saki wandon gaba ɗaya yyi ƙasa Innalillahi da wani Irin sauri ta ƙanƙamesa tana ɓoye fuskarta a ƙirjinsa...**30***_Zain Abeed Complete book 1, 2 ku shiga Arewabooks domin samun update fiye da ɗaya, kada a manta ayi following Acct nw_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62b1e5ccf0bafa279f2af05c

Sakinta Abeed yyi ta zame da gudu ta fice daga cikin ɗakin tana sauke ajjiyar zuciya, da jajayen idanunsa ya bita da kallo kafin a hankali ya zame tare da zama kan stool yana maida numfashi boxer ɗin jikinsa yabi da kallo kafin a nutse ya fara shirya kansa cikin Milk thobe jallabiya mai santsi da taushi, samun kansa yyi da abin umarnin Sara gently ya miƙe tare da ɗaukan pra mat ya nufi wani bedroom nada ban, a nan yyi sallah ya nayin sallar kuma ya miƙe ba tare da azkar ba, sallar ma da ƙyar ya kammala ya nayi yana jin tamkar ana buga masa guduma a tsakiyar kansa, idanunsa sunyi jajir bedroom ɗinsa ya dawo tare da zame jallabiyar jikinsa, system ɗin ya ɗauka tare da zama kan wata lallausar kujera wacce take kusa da bed ɗinsa, a hankali yake operating system ɗin wata sabuwar kwangila ya amsa dake time to time yana amsar kwangila, yana gama tura information ya shiga cikin E-mail ɗin sa, ya daɗe yana kallon tarin saƙwannin da aka tura masa, a hankali ya shiga na Zain sakwaninda Zain ya tura masa babu adadin yana gama karantawa, yaja idanunsa ya rufe yana jin wani irin so da ƙaunar Biyunin nasa na ƙara ratsa masa zuciya, shine rauninsa zai iya komai domin samun farin cikin Zain, Idanunsa ya buɗe for the first time da yaji ya samu full confidence na yiwa Zain reply, a hankali ya shiga typing. _“I think of you wherever I am, I wish you take care of Mom with Abba, give Naila happiness on my behalf, Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas always loves you and misses you”._ yana rubuta haka ya tura masa tare da kashe system ɗin, Miƙewa yyi a hankali ya fita daga bedroom ɗin zuwa parlon dake cikin part ɗin sa, wajan deep frizeer yaje ya ɗauki gorar ruwa guda biyu ya nufi wani side yana zuwa ya shiga cikin wani ƙwataccen waje gym ne kala kala, The muscle farm ya hau ya fara yana wani irin sakin numfashi few minutes ya shiga haɗa zufa ƙirjinsa ya buɗe sosai wajan 1hr ya sauka tare da ɗaukan gorar ruwa guda ya shanye tass, kana ya hau wani Bodycompworks gym shima yyi daga ƙarshe ya hau Boom fitness 9 daidai ya fito daga cikin wajan hannunsa riƙe da gorar ruwa yana sha, kamar wani basamude haka yake tafiya jikinsa duk ya Murmurɗe, akan kujera ya zauna na Main Parlo, a hankali kuma zufar jikinsa ta fara bushewa saboda sanyin a.c da kuma na garin ya jima nan zaune kafin ya ɗauki Madara mai ɗan zafi yasha, Ƙamshin da yaji ne ya sanya ya ɗaga kansa a hankali zuwa direction ɗin da take tsaye, tana tsaye sanye da Silhouette peach, sai wata kinomo data ɗura a jikinta, ƙafarta sanye cikin Slippers ga wani ƙamshin shower gel dake tashi a jikinta, kallo ɗaya yyi mata ya ɗauke kansa tare da rufe idanunsa, Sara ganin baice mata komai ba kuma tasan ba lallai yyi Mgn ba, shiru tayi itama kowa da tunanin da yake a ransa ganin lokacin na tafiya kuma tana da text na wanda Yarima Yashim zai musu daga yau kuma zasu fara shiga karatu exam, duk abinda take yana lura da ita can dai ta numfasa tace "Ina da text fa" idanunsa ya ɗaga suka haɗa idanu tayi ƙasa da nata kan tana ɗan tura masa baki Kallonta kawai yake ba tare da yace komai ba, jin shiru yasa Sara buɗe idanunta tace "Nace ina da text by 11 time na tafiya" a wannan karan Miƙewa yyi tsaye bai ce mata komai ba ya shige bedroom ɗin daya kwana ciki, da Idanunta ta bisa wani irin abu nayi mata yawo a zuciya, Abeed na shiga cikin bedroom ɗin ya samu Wayarsa na ringing ganin sunan Anuty Zulfa yasa bai ma ɗaga kiran ba, bathroom ya shiga yyi shower, yana gama shiryawa ya ɗauki Wayarsa message ɗin Anuty Zulfa ya gani tace. _“Ba shakka, Ni zakaiwa tijara idan Saratu ce zakai mata haka? Ko bata faɗa baka tana da shcl ba”_ yana gama karantawa ya shafa sumar kansa zuwa sajansa kafin yyi mata reply da _“ Uhm, Auta ta tafi mata da kayan karatun I'll drop her”_ yana ruhutu haka ya ɗauki car key ɗinsa ya fita. Ƙamshin Hugo boss da yaji yasa ta ɗan kallesa yana sanye cikin Notch Lapel dark brown, sai Molianseng Euphoria daya sanya a ƙafarsa bakinsa na fidda ƙamshin Green cardamom (Chhoti elaichi).. kallo ɗaya yyi mata kafin a nutse fuskarsa a kame yace "Jeki shirya" kayan jikinta ta kalla tace "Na shirya ai" not looking at her yace "To zauna.." miƙewa tayi tace "To kayan bbu ai" sai a yanzu ya ɗago ya kalli fuskarta sosai kafin a miƙe tsaye yana zuwa ya fisgi hannunta zuwa bedroom ɗin data kwana ciki, har gaban wardrobe ya jata tare da buɗe wardrobe ɗin, yana buɗewa yaja baya yana zama kan bed ɗin sbd wani abu dake masa yawo a jikinsa, da mmki dake kallon kayan kana ya juya ya kallesa suna haɗa idanu ya ɓalla mata harara, turo baki tayi ba tare da tace komai ba ta ɗauki wata VGOLD palazzo trousers ta haɗa da wata Applique logo detail t.shirt, idanunsa akan waya ta shige bathroom ta sanya kayan tana fitowa ya ɗaga idanunsa ya fara ƙare mata kallo can yace "Nan kaya ne?" Ta ware idanunta tace "Kamarya" yana kame fuska tare da Miƙewa tsaye yace "A haka zaki shcl ɗin? Look at your self" jikinta ta shiga kalla sam batai tunanin nuni yake mata da ƙirjinta ba domin ko bra bata saka ba, kuma bata sakawa sbd ciwon ƙirji. da hannu yyi mata nuni da sauri tayi ƙasa da kanta tana juya masa baya,bai kulata ba ya nufi wajan inners ɗin da suke wardrobe ɗin ya ɗauki wata white ɗin padded bra ya ɗauko ba tare daya kalleta ba, ya miƙa mata ita Mmkin yadda akai ya ajjiye duk kayan nan a gidansa take, tana Turo baki tace "Nifa baransa ba" wata ƙyakkyawar tsawa yyi mata wacce tunda ta dawo hayyacinta bai taɓa yi mata irinta ba, duk yadda taso danne tsoran dake ranta kasawa tayi ta amshi bra ɗin, tare da komawa bathroom ta saka yana fitowa ya nuna mata wata Black jallabiya mai kyau batai masa musu ba ya cire kayan jikinta ta daka jallabiyar, kallo ɗaya yyi mata yabar cikin bedroom ɗin. Yana zaune a parlo yana waya a hankali kamar me raɗa ta fito ko inda take bai kalla ba, ya miƙe tsaye walking slowly yake tafiya sumar kansa na lilo tana biye dashi tayi wani irin kyau kamar wata balarabiya, wata motarsa Nissan Rogue ya nufa tare da buɗewa, ya shiga mazaunin driver tana ganin haka ga buɗe itama ta shiga bakinta ɗauke da addu'a, yana jinta a haka yyiwa motar key gatekeeper ya buɗe musu suka fita.....kusan a tare suka shiga makarantar shi da Yarima Yashim gajeren tsaki Abeed ya saka yana duba wrist ɗin hannunsa, parking tana ƙoƙarin fita ya sawa motar key, Kallonsa tayi cikin nutsuwar ta a hankali tace "Nayi late" Maimakon ya buɗe mata sai ya shiga danna motarsa time to time yana kallon harabar Makarantar, sai da yaga shigewar Yarima Yashim Sannan gently ya juya ya kalleta a kame yana ya motsa fuska yace "Wane time zaku gama?" Kanta a ƙasa tace "By 2" bai ce komai ba ya buɗe gaban motarsa ya ɗauki ƴan 1k guda biyar ya miƙa mata, Idanunta ta ɗaga tare da kallonsa tace "Wannan fa?" Kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "for breakfast.." tace "Auta zata zo mana dashi" kusa da ita ya matsa da sauri taja baya Kallon fuskarta yyi da yadda ta ɗura hannunta a gadon bayansa ganin kamar zai shige jikinta tsaki yana ya miƙa hannunsu ya buɗe ƙofar motar yana buɗe yace "Idan kinfa ki zubar da kuɗin" ya faɗi hakan yana komawa mazauninsa. Fita Sara tayi daga cikin motar ta shiga tafiya a hankali ta cikin motar yake hango tafiyarta, tayi nisa ta ɗan juya tare da kallon motar ta tsorawa motar idanu, Abeed ya lumshe idanunsa kana ya buɗe a hankali ya danna mata Horn alamar ta tafi, jin Horn yasa Sara ta juya yana sakin Murmushi tare da tafiya a hankali har ta shige hall ɗin daza suyi text, a hankali ya sauke numfashi tare da yiwa motar key ya juya zuwa wani hotel. Kusa da Auta taje ta zauna kallo ɗaya Yarima Yashim yyi mata ya ɗauke kai yaci da abinda yake a nutse. Har yyi nisa da tafiya ya juya wani pack mai kyau mata da maza ne a wajan kowa yana harkar gabansa, a hankali ya fito daga cikin motar nan idanun ƴan matan wajan suka dawo kansa, kai tsaye inda yake hango wata matashiyar mace zaune ta rufe fuskarta gabanta an ajjiye mata lemon wine tana sha, gently Abeed yaja Kujera ya zauna matar dai na jinsa bata ɗago kai ba, numfashi yaja cike da nutsuwa yana ɗaukan wine ɗin da aka ajjiya masa idanunsa akanta, ganin yadda ya kafe ta da idanu yasa ta miƙe tana ƙoƙarin barin wajan A hankali Abeed yace "Ayyana..." Cak ta tsaya Zuciyarta na bugawa tare da fargabar inda ya san sunanta, domin ko a masarautar Zahel ba kowa ya san sunanta ba, wine ɗin ya ajjiye ya kaɗa ƙafa Murya a kame yace "Have a site" Zama tayi a karo na farko da tayiwa wani magana tace "Kana da wayo" Murmushi bai wani damu Abeed ba amma a wannan karan wani irin cute smile yyi yana ta kallon ta can yace "Zaku iya rainawa kowa hankali,You do not know how much wisdom I have, I despise your ingenuity" shiru yyi yana binta da kallo yace "Uhm...I am stronger than you, you can not Ayyana, nasan tunaninki zai baki zuwa nan kikai ko?" Miƙewa tsaye yyi yana ɗaukan Wayarsa tare da ajjiye kuɗi yace "Zuwanki wajan nan tsarin Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas ne" yana faɗin hakan ya juya tare da barin wajan, jin numfashinta na neman ɗaukewa tayi saurin ɗaukan ruwan wajan ta sha, tana sauke ajjiyar zuciya bata taɓa tunanin shine abin harin da suke nema ba, yaya akai ya san sunanta? Tayaya ya shirya zuwanta nan wajan bayan ita ta nemi dukkan wajan da yake yawan zuwa, motarsa tabi da kallo a hankali tace "Clever"... 1:30 suka fito daga cikin hall ɗin Auta tace "Yaa Abeed yana da matsala meye zai wani ɗauke ki?" Ita dai Sara shiru kawai tayi ba tace komai ba har suka ƙarasa wajan cin abinci, waiter ta kawo musu abinci Sara Patatoes da meat shawarma aka kawo mata sai Green tea, Auta kuma Chips ne da Egg, suna cikin cin abinci su kaji zuwan mutum wajan ƙamshin turaren Jean paul Gaultier ya kama wajan, Cikin kasaita tasu irin ta masu mulki Yarima Yashim yyi sallama a taushashe, Auta ce ta kallesa tana Murmushi kafin ta miƙe yyi saurin cewa "No please zauna mana" ta ɗanyi dry yace "Zanyi wani abu, I'll be back" tana faɗin hakan tayi waje sai a lokacin Sara ta ajjiye spoon ɗin hannunta tare da ɗagowa ya kallesa Murmushi ya sakar
mata a hankali tana ƙasa da kanta tace "Ina yine" Yana ta Kallonta jin baice komai ba yasa ta ɗaga kanta suka haɗa idanu idanu ɗaya ya kashe mata yace "Amin cin Allah ya tabbata ga ruhin Yashim Al'khasim Abubakar Wahab" Murmushi tayi yace "Kinyi kyau my princess" a hankali tace "Thank you" shiru yay can yace "Next week sai exam ko?" Kai ta ɗaga masa ya jinjina kai kafin yace "akwai bikin da Za'ai na kammala wani abu da ƴan low sukai ƴan level 3" tana wasa da yatsun hannunta tace "Naji an faɗa.." yace "Zadai kizo?" Tace "Not sure.." yace "U most come, nima ranar za'a ƙara min girma" ta juya idanunta kamar ba zatai mgn ba sai kuma tace "A nan makarantar kuma?" Ya girgiza mata kai idanunsa akan yana jin wata soyayyar ta a zuciyarsa yace "Wane yace maki ni University teacher ne?" Hannunta ta watsa masa tace "naga kana ɗaukan mu darasi ne" Murmushi yyi mai kyau yace "To ni ba Malami bane akwai dalili" kamar ta tambaye sa mene aikinsa sai kuma tayi shiru. Matsar da kujerarsa yyi sosai a hankali yace "Sarahh.." har ƙasan Zuciyarta taji kiran da yyi mata yace "Kalleni Sarahh" ƙin ɗago kanta tayi ya sanya ta tattausan farin hannunsa tare da tallafo haɓatar a hankali ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna, Abeed dake tsaye yana kallon duk abinda Yarima Yashim keyi ya juya a hankali ya bar wajan, yana zuwa bakin motarsa yace da Auta "kice mata idan na shigo wajan zata gane bata da wayo" tsoro duk ya kama Auta ta juya da sauri zuwa cikin wajan, Calmy Yarima Yashim yace "Uhm, shy baby I love You Sarahh i am in love with you madly, Zaki auren?" Har lokacin fuskarta na hannunsa tace "Uhm, zan tambayi Uncle" Kallonta yyi tayi kafin ya zame hannunsa yace "Ok Promise me idan har ya amince zaki auren" a hankali tace "I promise in sha Allah" hancinta yaja yace "Thank Beb.." miƙewa tayi tsaye tace "Zan tafi" yace "ok sai munyi Mgn" tana fita Auta na zuwa tace "Sara kin shiga uku Yaa Abeed yazo" Idanunta ta juya ba dai tace komai ba tayi waje, Sara na zuwa ya kalli Auta tare da ciro kuɗi ya bata yace "Ki nemi abun hawa" Sara da kanta ke ƙasa sai ji tayi ya fisgi hannunta tare da cillata mota ya rufe da wani irin sauri yyiwa motar key tare da barin cikin makarantar......... Zain ya fito daga cikin Court hannunsa

Please Login or Register in order to submit comment