Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗin da muna primary school na nemi na rasa kuma a lokacin baki da lafiya, kina fama da ciwon ƙoda daga ni har Daddy babu wanda kika faɗawa, a kiɗime muka je hospital ɗin, muna zuwa Dr yace mana an ƙodar gaba ɗaya biyun sun lalace, amma wani saurayi ya bada tasa an cira an saka maki, munce masa waye amma Dr yace shima bai san shi ba, Yanzu haka silarsa yasa kike raye a duniya da kuma taimakon Ubangiji, duk da hakan kike tunanin hankalina zai kwanta? Ko kuma kina tunanin ke kaɗai kike so na? Sara a mahaifa guda aka haife mu, dole Soyayyar junanmu da kasance abu nada ban, ina Sonki ba zan iya bari na rasa ki ba" Sairah ta ƙare zan can tana sakin kuka, ganin yadda hankalin Sairah yay masifar tashi, yasa Sara ta saki wani Murmushin ƙarfin hali, tana danne wani tarin da yazo mata, tace "Haba twin akan wannan kike kuka? Haɓo nayi fa" Sairah tace "No Sara, stop laying baki ƙarya kada ki fara yanzu, Meke damunki, saboda Daddy ya barmu a nan? Kasan dole zai dawo ba zai iya rayuwa babu mu ba, ƙilan yana da wata manufa daya sanya ya yi hakan" shiru kawai Sara tayi domin muguwar zuciya ce da ita, a halin da take yanzu bata ƙaunar ma, a kira mata sunan Daddy, wanda yake son su da ƙaunar su yau shine ya juya musu baya, akwai kidnappers, Arms robber, bad Animals duk a ciki jejin duk da haka ya tsallake ya tafi ya barsu.... Kallon Sairah tayi da tayi lamo a jikinta tana sauke ajjiyar zuciya, a hankali tace "Twin da gaske ba Daddy ya haife mu ba" da sauri Sairah tace "A'a shine Daddynmu shine ya haife mu" gyara zama sosai Sara tayi tace "Look twin kin san bana ƙarya ko?" Slowly Sairah ta ɗaga kanta, Sara tace "Good, as frm today zamu daina amfani da sunan Daddy, na maki Al'ƙawari, zan zame maki fiye da Daddy, da kuma uwar da muka rasa, tun muna ciki, zan baki farin ciki ko da zan rasa nawa, ki daina kuka kinji babu abinda zai same mu sai abinda Ubangiji ya tsara" Sairah tace "Twin to me zamu na cewa sunanmu?" A hankali Sara tace "I'll think about that.... sleep" ta faɗa tana ɗura kan Sairah a cinyarta, kwaɓe fuska Sairah tayi tace "I luv u twin" Sara tace "Luv u too..." Sanyin safiyar daya shiga kaɗawa shine ya farkar da Sara daga baccin da take, tana farkawa idanunta ya sauka akan Sairah wacce take zaune ta zabga tagumi tana kallon ƴar uwarta, da mmki Sara tace "Mene?" Girgiza Sairah tayi tace "naga baki tashi ba, ina tsoro ne" Sara tace "yanzu fa" Murmushi Sairah tayi tace "Naji daɗi" Miƙewa duk sukai, suka fara tunanin inda zasu samu ruwan alwala, hannun juna suka riƙe suka shiga tafiya cikin jejin cike da tsoro ƙarar ƙwari da dabbobi sun cika ko'ina, a haka suka isa wata gaɓar ruwa nan sukai alwala, Sairah ta kunce ɗan kwalinta ta shimfiɗa, kana ta yi sallah tana idarwa ta bawa Sara hijib tunda nata ya Faɗi.. shiru duk sukai banda yunwa babu abinda suke ji, juyawa Sara tayi jin cikin Sairah na ƙara, a hankali ta miƙe tsaye tace "twin tsaya a nan ina zuwa" tana faɗin hakan ta bar wajan, wajan ruwan ta koma tayiwa ruwan ƙuri da idanu can ta hangi wani ɗan ƙaramin kifi a gefen ruwan yana tsalle, da sauri ta ƙarasa ba wani tsoro ta kama kifin ta ajjiye can nesa har ya mutu, tana da tsaye ko zata ƙara ganin wani kifin amma babu, juyawa tayi ta hada itace kamar yadda taga anayi a film, ta samu fararen duwatsu nan take wuta ya tashi, a nan ta fasa kifin sai farin ciki take Sairah zata samu abinda za taci.... Kifin ta ɗauka har zuwa wajan Sairah ta same ta kwance riƙe da ciki, da sauri tace "Twin come and eat fish" ta faɗa tana ɗura kifin akan wani leaf mai faɗi, jikin Sairah har rawa yake saboda yunwa, tace "Sara na kema kici to" girgiza kai Sara tayi tace "Ai naci, nawa ma yafi naki yawa" ta faɗi hakan ne domin tasan kifin ko Sairah ba zai isa ba, balle su biyun duk da cewa itama tana jin matsanancin yunwa, da kallo kawai tafi Sairah yawunta na tsinkewa, ganin yunwa zata kashe ta, yasa ta miƙe tayi baya can, wani kuren ganye ga gani mai kyau ga ruwa duk a jikinsa, da sauri ta tsinka ta shiga ci kamar mayunwaciya, sai da taci gayen da yawa Sannan ta goge bakinta, ta koma wajan Sairah lokacin harta gama cinye kifin, Murmushi tayi tace "Taso mu tafi" Sairah tace "where?" Sara tace "muje ko zamu samu wani garin a gaba" tafiya suka fara hannunsu riƙe dana juna...

A can Mascow Abeed ne zaune, a gaban Dr siya, yana sauraran abinda yake faɗa, gaba ɗaya a tsorace Dr Siya yake, domin gani yake kamar Zain ne ba Abeed ba, duba da cewa komai nasu iri guda ne, babu wani bambanci, shigarsu, magana everything... Taɓe fuska Abeed ya yi, kafin a hankali ya ɗan ja numfashi, kamar wanda akaiwa dole yace "Uhm all ears" Dr Siya yace "Har kawo yanzu babu wani magani da aka samu na ciwonka, kuma binciken ya ƙara tabbatarwa Tabbas ba zaka shige wata biyar ba a raye,but..." Hannu Abeed ya ɗaga masa alamar ya isa haka, Miƙewa kawai ya yi tare da gyara zaman mars ɗinsa ya fita daga office ɗin, ko maganin da Dr Siya ya bashi bai amsa ba, a ganinsa shi da yake dab da mutuwa wanne magani kuma zai sha?. A hankali yake tafiya cike da nutsuwa he was so weak and sick, mota ya shiga ya yi mata key ya koma cikin hotel ɗin...Zain ne zaune da wani three gauther sai Red ɗin Armless, yana vedio call da Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, Murmushi Zain yay yace "Gashi ya dawo" A hankali Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas dake zaune kan wata tattausar ladduma gabansa cike da kayan marmari, yana tsaye da wata farar jallabiya mai kyau wacce tasha aiki irin ta sarakai, ga wata jar hula a kansa mai ɗan tsayi, wani ƙawataccen Murmushi Ya saki yace "Nuna min fuskarsa" Cikin e Sauri Zain ya saka hannu ya jawo Abeed dake tsaye yana sauraran abinda suke faɗa, zama yay kusa da Zain ya ɗan ɗura kansa a kafaɗar Zain ɗin, wani irin marairaicewa Abeed ya yi tare da ɗan kwaɓe fuska cikin Muryar shagwaɓa yace "Abba" wata mummunar faɗuwar gaba ce ta saukarwa Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas wacce bai san ko tame bace, addu'a ya yi kafin yace "Are You alright?" Shiru Abeed ya yi sai kallon mahaifinsa yake, can yace "Ina Naila?" Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace "gata" ya faɗa yana hasko fuskar Naila da sauri tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w, Jama'ar Annabi yau ga gantalallun yara masu son cutata, a'a wlh Ubangiji yay min tsari daku, maza ku bambance min kanku" Dry Zain yay kafin yace "Nine Abeed, wan can kuma Zain" washe baki tayi tace "Yau koda naji, ai tunda naga wan can yana zare ido kamar na gafiya nasan billahi ba shine Abidin ɗin ba" Murmushi kawai Abeed ya yi ganin yadda har yanzu ta kasa gane su, Zain yace "Naila ya tsofa?" Da sauri tace "A'a wallahi mugun nufinka ya ƙare a kanka, wani garin ne kuma tsofa? Kai dan kaji wallahi sai dai ka mutu ka barni a raye" dry sosai Zain yay yace "Ai ke yanzu kina tunanin kaiwa wani lokaci mai tsayi haka? To ai bana jin ko wata biyar zaki kai a raye?" Da sauri Abeed ya kalli Zain gabansa na ƙara faɗuwa, mene ya sanya suke maganar mutuwa ne? Ko dai ya tabbata cewa zai mutu ne? Haɗe fuska Naila tayi tace "Wlh ba zan mutu ba, idan na mutu Allah ya tsine.." da sauri Abeed ya miƙe tare da barin wajan ya shige cikin bedroom zuciyarsa na tsananin harbawa, Meke faruwa ne? Yanzu ne lokacin daya dace ya bawa kansa farin ciki tunda ya tabbatar Ubangiji bai ƙaddara zai yi rayuwa mai tsayi ba, yanzu wacce hanya zai bi ya samu farin ciki? Wata zuciyar tace masa kawai kayi rayuwa mai ƴan a hankali ya buɗe baki yace "Club.....


Dukkan wanda labarin yay masa share fisabilillahi🥰👏🏻

08119237616

SARAUTAR MARUBUTAPage 3
Zain dake shigowa cikin bedroom ɗin yace "Me ake a Club?" Da ɗan sauri Abeed ya juya yana shafa kwatacciyar sumar kansa, tare da ya tsuna fuska kamar ba zai magana ba, sai kuma yace "Yaushe nace Club?" Zain yace "Yanzu naji ka faɗa mana" ƙara haɗe fuska Abeed ya yi yace "Ba kaji daidai ba" Zain yace "Oh! Ƙilan, what about the show, kasan dan shi na rakoka daka matsamin ko? Kuma naga kamar baka da niyya" Zama Abeed ya yi akan kujerar dake gefen bed ɗin su, tare da harɗe ƙafarsa kamar yadda Zain ɗin ya yi shima yana faɗin "Gobe ne" Zain yace "Ok, Allah ya kaimu, Ni ma ina da Shari'a after we get back to Nijeriya" A hankali Abeed ya ce "Ok" Zain yana jan system yace "Baka tambayi wacce Shari'a bace" Abeed na ya tsuna fuska yace "Sorry mene?" Zain yace "Shari'a ce, akan matar da ake zargin ta kashe mijinta for no reason" shiru Abeed ya yi tamkar bai ji abinda Zain yace ba,kai Zain ya ɗaga tare da kallon Abeed gani ya yi ya harɗe hannayensa a ƙirji ya lumshe idanunsa, ya jima yana kallonsa kamar mai masa kallon ƙarshe can yace "Kaji me nace ai" a gajarce Abeed yace "Ko sake ta" da mmki Zain yace "A saketa kamarya, kisa fa tayi?" Abeed ya ware idanunsa tass tare da kallon Biyunin nasa ya numfasa yace "To kace zargi?" Zain yace "Gaskiya ne, amma zargi zan ce tunda ba'a haɗa hujja ba" taɓe baki Abeed ya yi yace "Kana bani sahihin labari mara ƙarya" yana faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa Toilet, girgiza kai kawai Zain ya yi shima ya miƙe ya shiga toilet. Da daddare misalin 10 duk suna zaune a Parlo suna kallon wani show da Abeed ɗin ya yi kwanaki, dake waƙar tasa cikin harsuna biyu yake, hausa da English a wannan karan waƙar Hausa aka sako mai taken *_Babu Kamarka_* Asalin waƙar kuma Zain ya yiwa, gyara zama Zain ya yi yace "kasan duk cikin waƙar ka, Babu kamarka itace bakandamiyya ta" idanun Abeed akan iphone ɗinsa yana duba wani tweet da Arman Malik ya yi a Twitter, akan wata waƙarsa da ya yi show ɗinta, lumshe idanunsa yay alamar posting ɗin ya yi masa daɗi, a hankali ya shiga typing ya ruhutu _The show was so amazing, i like it_ not too long Arman Malik yay masa reply da _Buhut Buhut shukriya_ kashe datar ya yi, kana ya kalli Zain yana ɗan shafa kansa yace "kamar mgn kayi" Zain yace "Ohhu, this week zamu koma Masarautar Bilhira, be ready Mai martaba yace tare yake son ganin mu, na gaji da haɗin bakin nan naka, sai kasa inawa Mai martaba pretending cewa nine kai, idan kaso ƙin komawa 9ja" Murmushi Abeed ke son yi, sai kawai ya cije baki, yace "Oops, Ana show ɗin zamu tafi" Zain yace "when" A hankali Abeed yace "By tommorow morning" Zain ya harɗe ƙafarsa kamar yadda Abeed ya yi yace "owk, Ni ɗin zani?" Gently Abeed ya ɗaga kai, Murmushi Zain yay yace "Muyi ta rainawa jama'a hankali, sbd ba kowa yasan mu Twins bane, mene tittle n song ɗin?" Gyara zama Abeed ya yi yace "Waƙar biki ce, 5.m suka bada, gashi..." A hankali ya saita muryarsa, Zain kuma ya fara kiɗa da hannunsa, cikin golden voice ɗin ya fara baitin waƙar bikin..

_Fifita ga amare..,_
_Sassaita ga angwaye..,_
_Najwa ta zama amarya..._
_Khalee ne angonta._

Tsayawa ya yi, yana jan numfashi, Zain kuma ya shiga yi masa tafi yana faɗin "Bravo, kasan idan zanyi aure waƙa 10 zakai min" kamar daga sama haka Abeed yaji kalma tayi masa dirar mikiya da mmki yace "Aure zakai?" Zain yace "ka samu matsala sai nace maka ba zan aure ba? Sai ka fara yi zanyi" taɓe baki Abeed ya yi kana yace "Ashe ba zakai ba" cikin rashin fahimta Zain yace "A saboda ni ba namiji bane?" Ka faɗa Abeed ya watsa yace "Go Ahead" dry Zain ya yi yace "Anya kana da lafiya? Kai ba ruwanka da batun aure mata basa gabanka, kuma kai ne ma ya dace ace kana sabga da ƴan mata saboda waƙar da kake" gently Abeed ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa a cikin Aljihu shima Zain Miƙewa ya yi, tare dayin the same da abinda Abeed ya yi, cikin nutsuwa walking slowly Abeed yace "Ai nama fika lafiya"... "Kuma shine ba zakai aure ba, bayan age ɗinka ya kai, kuma babu abinda Mai martaba yake ƙauna sama da yaga duk munyi aure" Abeed yace "To! Kayi mn, tunda kana da ra'ayi" Cikin serious talking Zain yace "Kasan ai ba zan iya aure na barka ba" Abeed yace "then ka jira nan da 5mnt" cikin farin ciki Zain yace "Are You sure? Za muyi aure to suwa zamu aura, kasan matsala duk abinda zuciyata take so yanzu kai ma za kaji kana son sa, bana manta sanda mutunci da wata something like soyayya wlh ji nayi Nima ina sonta, duk inda identical twins suke mata dole mu samu so" kallon Zain kawai Abeed yake, wlh da gske ya lura Biyunin nasa aure ya keso, shi kuma wlh ya manta ana wani abu aure, infact bai ma san wacce kalar rayuwa ake idan an yi auren ba, ganin Zain na ƙoƙarin cewa wani abu, yasa da Sauri Abeed ya kama hannunsa suka nufi wajan gmy....Cikin dare bayan sunyi sallar Issha sun kwanta gaba ɗaya suna sanye da kayan bacci iri ɗaya, hatta yanayin kwanciyar su komai ɗaya, buɗe ido Abeed ya yi, ganin Zain na bacci yasa ya miƙe tsaye a hankali ya fice daga bedroom ɗin, bai tsaya sauya kaya ba, key car kawai ya ɗauka ya nufi compound na hotel ɗin, lokacin wajan 1:30 gashi ana bala'in sanyi, ya manta ko sweater bai ɗauka ba da mars, motar ya shiga ya yiwa key bai tsaya ko'ina ba sai cikin wani haɗaɗɗan club, wanda Tun daga waje kiɗa ke tashi, Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara sama da glass ɗin motar wani mugun sanyi ne ke ratsa masa jiki, saboda duk fararan cinyoyinsa suna a waje ne, gaba ɗaya snow ta fara lullube motar, runtse idanunsa ya yi sosai yana mai datse laɓɓansa jin Numfashinsa ya fara wani bala'in sarƙewa, tuni daman gargasar jikinsa ta buɗe tsananin whlar da yaji yasa shi faɗin "Ya Rabbi, Ya Mujibudda'awati" ya faɗa yana ƙanƙame jikinsa waje guda, ganin zai iya rasa rai yasa cikin fitar hayyaci yaja motar da gudu ya koma hotel, yana zuwa ya hangi wani securitie, horn ya danna masa yazo da sauri, magana ya yi masa kaɗan, sai gashi ya dawo da wani ƙaton bargo na sanyi, amsa ya yi ya saka jikinsa, jiri na kwasar sa ya nufi room ɗin su.. Yana zuwa ya samu Zain tsaye hannunsa goye a bayansa sai zirga-zirga yake tsakanin parlo da bedroom, da sauri yace "Daga ina kake?" Kai tsaye Abeed yace "Club" he was shock da jin abinda Abeed ya faɗa, mene zai kai Biyunin nasa club ko dai ƙarya yake, amma Abeed baya ƙarya tunda yace haka Tabbas daga club ɗin yake, da wani irin kallo ya fara binsa ko dai ya fara bin mata ne? Cikin ransa yace "No!" Hannunsa kawai ya kama suka shiga ciki, har bakin bed ya kawo sa tare da kwantar dashi ya rufe sa da duvet, heater ya kunna kana ya ɗauko masa Inhaler nasa, a daran Zain bai bacci ba kamar yadda Abeed ya kwana da ciwo, gaba ɗaya basu samu bacci ba sai da sukai sallar Subhi, kana suka kwanta kan Abeed a hannun Zain a haka sukai baccin....

Gajiya sukai da tafiya, Sairah ta kalli Sara tace "Twin na gaji, yunwa ishi, I'm felling hungry" Juya Sara tayi can ta hangi wata ƙorama tace "Follow me" bayan Sara Sairah tabi, har zuwa wajan ƙoramar gaba ɗaya suka tsuguna, Sara tace "Open your hands twin" buɗe hannunta Sairah tayi daidai bakinta, ita kuma Sara ta dinga ɗebo ruwan tana zuba mata a hannu tana sha, bayan duk sun sha ruwan, Sara ta kalli Sairah tace "stay here, I'll be back" Girgiza kai Sairah tayi tace "Zan biki" Girgiza kai itama Sara tayi tace "Ba kince yunwa kina ji ba? To Abinci zai nemo maki ok, bana son ki Wahala" idanun Sairah ne ya cika da hawaye tace "to baki da lafiya fa" zaro manyan idanunta waje Sara tayi tace "Kai twin lafiya lou nake, yanzu zan dawo" kamar yarinya haka Sairah ta miƙa wa Sara hannu tace "promise?" Wani cute smile Sara tayi tun bayan zuwan su wajan tace "Promise, ohya come closer" juna suka rungome Sairah tace "I luv u twin" Sara tace "luv u too twin" Zame jikinta Sara tayi tare da ɗauko zoben hannunta ta bawa Sairah tace "Ajjiya, bye sai na dawo zan kawo maki abinci da yawa" Bye sukaiwa junansu, Sara ta tafi ita kuma Sairah ta zauna bakin ruwan tana jiran dawowarta. Ta shafe awanni tana tafiya cikin tsakiyar jejin amma babu wani abu da ya yi kama da abinci, Banda ganye, yunwar daya isheta yasa, ta fara ciyar ganye tana ci, sai ajjiyar zuciya take saukewa, Sara sam bata yadda tayi kuka ba a rayuwarta, No matter what happen to her she will never cry, tace kuka alamar raƙwanta ce, babu wanda take tunanin zai iya sata kuka, tana cikin cin gayen taji ƙirjinta ya buga da ƙarfi, runtse idanunta tayi tana kiran sunansa Allah, a hankali kuma jini ya fara biyowa ta hancinta, karo na farko data fara karaya da abinda yake damunta, tunanin komawa wajan Sairah tayi kada ta mutum a nan, ta juya ke nan zata tafi taji daga bayanta ance "Kaiiii" da ɗan sauri ta juya wasu maza ne manya majiya ƙarfi, kayan jikinsu duk iri guda kamar arnan daji kamar maguzawa, gaba ɗayansu suna kan doki, hannunsu riƙe da igiya, shiru tayi kanta a kasa, ɗaya daga cikin mutanen yace "Wannan kamar tayi ko?" Ya faɗa cikin wata iriyar gurɓatacciyar Hausa, Wani yace "Eh tayi, kai ko ba tayi ba haka zamu kai ta, dan idan muka koma babu wata mace to kisan gilla MABUS zai mana" dry duk sukai wani yace "Mutuwa ba yanzu ba kowa, Sai abar Bauta ta sahale mana" Jin haka yasa Sara tace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Am sorry twin, na kasa kula dake kamar yadda nai maki Al'ƙawari, ina tunanin lokacin mutuwa ta ya yi, ki yafe min zaki rayu a jeji babu uwa babu uba, babu ni" ta faɗa acikin zuciyarta tana jan wani irin ajjiyar zuciya, necklace ɗinta ta cire ta wurgar a wajan, kana ta zame ribbon ɗinta shima ta yar a wajan, ƙafa ta ɗaga da niyyar guduwa taji an naɗeta da igiya tare da yin sama da ita....
Page 4
Mutanan masu kama da arnan daji sabis yanayi kirarsu da kuma halayya, sune suka ɗauki Sara wacce ko kuka ta kasa yi sai wata wahalalliyar ajjiyar zuciya take saukewa, she wish ace Ubangiji ya ɗauki ranta a yanzu, babu Abinda yake damunta kamar halin da biyuninta Sairah zata shiga, tana can tana jiran ta kawo mata abinci, ga wata ƙaddarar ta faɗa mata, bayan ƙaddarar data sanya Mahaifin daya haifesu da cikinsu shine sanadin faruwar hakan, da ace bai kawo su jeji ya zube ba, ya jasu a ciki kamar yadda ya saba, babu dalilin da zai saya su shiga wannan wahalalliyar rayuwar, a yanzu babu abinda ta tsana a duniya sama da Mahaifin daya haifeta....Gaba ɗaya kan doki suka hau yayinda ɗaya daga cikinsu ya saba Sara a ka faɗa suka juya tare da nufar cikin gari, tafiya sukai mai nisa har suka iso ƙofar shiga wata ƙatuwar masarauta mai suna *Zahel* Masarautar Zahel Masarauta ce mai ƙarfi, wacce ta shahara a ɓangaren tsafi, Masarautar ta gino a can baya wajan Shekara ta 2,000 da doriya da suka gabata, Masarautar Zahel sun ƙware wajan bautar Gumaka, Dodo, Rana, Ɗan-maraki...Domin girma ne da masarautar saboda girman ta ne yasa suke tunanin samar da sarakuna guda biyu, amma tsananin tashin hankali da son zuciya yasa komai ya gagara, har kawo lokacin da Sarki Mabus ya hau kan kara ga, mutum ne mai ƙarfin iko, wanda ko kallonka ya yi sai da dalili, babu ruwansa da sabo, duk yadda kuke dashi idan Dodo ya buƙaci jininka bashi zai, gashi da mahaukacin kuɗi wanda ba kowa yasan inda yake samu su ba, Yana da mata sama da 20, banda ƴan matan da yake duk wata ya kwanta dasu, idan Allah ya yi a lokacin Dodo ya buƙaci jinin budurwa yana gamawa da ita, zai bada jininta.. Yanzu haka ƴan mata ne sukai ƙaranci a cikin Masarautar babu wanda zai kwanta dasu babu wanda zai bada jininsu a bisa wannan Dalili ya baza dakarunsa wajan samo masa mata, shine sukai katari da Sara.. Sarki Mabus na zaune akan karaga daga shi sai wani ƙaramin abu ɗaya ɗaure ƙugunsa dashi sai wata babbar laya a ƙirjinsa, da wata ƙatuwar wular fata akansa, fuskar nan tasa baƙa ƙirin kamar yadda zuciyarsa take ɓaka, sai muzurai yake gefensa kuma ƙaton wani gunki ne wanda aka ajjiye a cikin fadar na musamman... Ɗaya daga cikin dakarun da suka kama Sara ne ya shigo cikin fadar tare da zubewa a wajan, ya buɗe baki zai masa kirari Mabus yay saurin ɗaga masa hannu alamar ya dagata, cikin wata kakkausar murya yace "Kun samo?" Jikin Badakaren na rawa yace "Ai mana afuwa, munyi neman duniya a wannan gari na Zahel babu wasu ƴan mata face raguwar ƴan matan da suka rage mana a cikin Masarauta, Amma munyi karo da wata ƙyakkyawar budurwa a cikin jejin Zahel, idan ka bamu dama yanzu mu shigo da ita" Mabus ya kalli Badakaren jin yace "ƙyakkyawar budurwa, yasan gaba ɗaya ƴan matan Zahel baƙaƙe ne, amma wacce halitta ce take rayuwa cikin jejin Zahel kuma budurwa ƙyakƙyawa? Kada fa yana zaune a wargatsa masa sihirin da yake jikinsa na shekara da shekaru, kada a hanashi shiga cikin gari ya aiwatar da abinda ya saba, a fili kuma yace "Ƙyakkyawar budurwa fara?" Badakaren yace "Na rantse da abar bauta kabas ƙyakƙyawa ce, ban taɓa ganin mai kyanta a wannan garin na Zahel ba" Miƙewa Mabus ya yi yana zagaye cikin Fadar tasa, kafin yace "A shigo da ita" fita Badakaren ya yi babu jimawa, suka shigo da Sara wacce take ɗaure da igiya ta galabata sosai, wata zabura Mabus ya yi lokacin da idanunsa suka sauka akan ƙyakkyawar fuskar Sara wacce tai wani irin fari na wahala, gashinta mai matuƙar tsayi duk ya wargatse, "Gadiya ta tabbata ga Abin bauta kabas, kunce ta" Mabus ya faɗa yana mai kallon ɗan aikensa yace "Maza kira min boka" Da sauri ɗan aiken ya fita zuwa sashen da bokan masarautar Zahel ɗin yake.. Kunce Sara sukai wacce bata ma san abinda yake faruwa ba, sai bakinta da yake motsi a hankali tana faɗin "Twin Ruwa, Ruwa Twin" Kallo guda Mabus yaywa wani sai gashi ya dawo da wata ƙatuwar ana kamar kuttu, ya buɗe ya kafa a bakin Sara, da sauri ta janye bakinta tana girgiza kai saboda jin ba ruwa bane, Burkutu ce (Giya) A fusace Mabus ya miƙe tsaye tare da ɗauke mutumin da mari yace "Ubanwa yace ka bata Burkutu? La'ananne, Abin bauta kabas ya yi Allah wadai dakai, ku fice min" gaba ɗaya fita sukai, not too long Boka ya shigo tunda idanunsa ya sauka akan Sara yaji gabansa ya faɗi, wata zallar kama idanunsa suke hango masa a fuskarta wacce ya kasa fahimtar kamannin waye? Zama ya yi tare da gaida Mabus, Mabus yace "A kallo guda naji ina kwaɗayin yarinyar nan, ka duba min gobenta yanzu na gani ko

Please Login or Register in order to submit comment