Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai tace "A'a" Calmy yace "Na zama farko" shiru tayi tana jin zuciyarta na bugawa kafin ta ƙanƙame jikinta tace "Uhm Thank you" banza yyi mata tace "Kace kuna kama da Abeed?" Sosai Abeed yyi mmkin tambayar nata kafin a nutse yace "Yhhh! But different behavior.." Sarah tace "Like how?" Kamar ba zai mgn ba sai yace "Yayyanki yafi ni kirki fa" ta wani waro Idanu tace "Tab, a'a kam shi bai iya bada kidney ɗinsa a samin, kullum fa cikin haɗe fuska yake gashi har shaye-shaye yake" wato ya lura shaye-shayen na ƙona mata rai sosai,jin shiru yasa Sarah tace "hello, are you there" Calmy yace "Uhm" sai kuma yace "Abeed nada tausayi, musamman kan mata, gasan taimako zai iya ƙarar da komai nasa idan mutum zai farin ciki." Shiru yyi ba tare da yace komai ba tace "Kayi shiru" ya ware idanunsa sai kuma ya kwaɓe fuska tare da langwaɓar da kansa gefe Calmy yana sakar mata nishi yace "Na gaji" Murmushi Sarah tayi mai sauti tace "Allah kai dai shagwaɓaɓɓe ne" ta faɗa tana sakin wani Murmushin, wani kalar cute smile Abeed yyi ba tare da yace komai ba, shiru itama tayi banda sautin bugawar zuciyoyinsu babu abinda suke saurare, ita Sarah idan har tana jinsa cikin wayar sam ba zata iya yin shiru ba hakan yasa ta tura baki tace "Nidai ka ƙarasa min" yadda tayi maganar tana narke masa Murya yasa Abeed rufe idanunsa babu shiri, fata fahimtar cewa muryarta ke sauke masa dukkan wani kuzarin jikinsa bata fahimtar hakan "please" Sarah nada naci idan bai faɗa mata ba, sam ba zata barsa ba, Calmy yana tura hannunsa cikin sumar kansa yace "yaushe kika taɓa ganinsa yana shaye-shaye?" Sarah ta wani murguɗa baki tace "Babu adadi" a hankali cikin nutsuwa yace "Ba zaki iya hanasa ba, idan baya da mai cewa bari?" Shiru tayi some seconds da sauri tace "No i can't, dukana zai fa, ni ban san mene yake ba na tuna sanda yana can gida akwai ɗan uwansa shine yake hanasa cold water" shiru bai ce mata komai ba tace "Kuma shi ai ƙato ne, yasan ba kyau" sai a lokacin Abeed yaja numfashi a hankali Murya can ƙasa yace "Idan ƙaddararsa ce hk fa, tunda kin san da ba yyi right, nidai ban wani san shi ba amma kamar baya tare da ƴan gidansu,babu mai cewa Abeed bar abinda kke bbu kyau,babu mai masa addu'a ko ya zauna dashi aji damuwarsa" jikin Sarah ne yyi bala'in sanyi tace "You're right, Jaan!" Zatai Mgn yyi saurin cewa "Pinky" a sanyaye tace "Na'am" wajan daƙiƙo kafin yace "Ki saka aranki ni na..." Da sauri kuma ya kashe wayar tare da mirginawa ya riƙe pillow yana sauke numfashi,baya sanin time ɗin da bakinsa ke buɗewa sosai idan yana tare da ita, duk wani miskilanci irin nasa a waya buɗe baki yake.... Shiru yasa Sarah cewa "Ina jinka me kace" shiru babu response, sai a lokacin ta lura yyi hanging up, ajjiye wayar tayi tana Lumshe idanu Allah ya sani babu abinda idanunta ke son gani sama dashi,ta gama believed dashi da Abeed kamarsu ɗaya, Abeed nasa ƙanan kaya shi kuma manyan kaya, Abeed bashi da tattoo Jaan ɗinta na dashi, Abeed bashi da Mgn Jaan ɗinta yana buɗe baki yyi Mgn ko ba sosai ba, Abeed nada zuciya taurin kai Jaan ɗinta kuma very simple ne, tana nan zaune bacci ya ɗauke ta, wajan 1:15 na dare Beeba ta shigo cikin bedroom ɗin bayan ta gama waya ganin wayar dake kusa da Sarah na haske yasa ta nufi wajan wayar, babu wani lock a wayar tana buɗe taga notification na message, a hankali Beeba tace "Jaan.." sai kuma tace "What a nice name, Wow!" Da sauri kuma tace "Oh! Jaan means LIFE Or MY LIFE... Gerret" saƙon ta shiga karantawa _“I do not know what to say, but you know my heart is beating fast”_ Beeba na gama karantawa tace "Ji banza, soyayya ce fa" Beeba akwai karambani cikin inbox ɗin ta shiga ta fara typing.
_“Understand why your heart is beating, when your heart is beating, Wannan shi ake kira da SO, don't worry jaan I'm urs forever and ever and ever, I Love u, Mu'ahh💋”_
Beeba na gama rubuta haka tayi sending, yana shiga ta goge message ɗin daga inbox ɗin wayar,a hankali ta ajjiye wayar tare da nufar bed ɗinta tana faɗin "A bawa soyayya haƙƙin ta, shine daidai matsalar ku Meye nawa" ta faɗa tana kwanciya kan bed ɗin... Kamar yadda Sarah ta saba duk dare sai ta tashi shan Madara juyi kawai take saman bed, bata saba da gidan ba, ko hanyar kitchen bata sani ba, gashi bata jima da gama period ba, a haka har aka kira sallah, Miƙewa tayi ta nufi bathroom tai wanka ta ɗauki sabon toothbrush da colgate ta wanke bakinta, tana fitowa suka haɗa idanu da Raudah wacce ke zaune, Sarah ta ɗauke idanunta tare da nufar inda kayanta yake, wata fara jallabiya ta ɗauka ta saka a jikinta ta fesa perfume kafin ta ɗauki hijab ta sanya, raka'atul fajr tayi ta zauna zaman jiran a tada sallah, duk Abinda Sarah take Akan idanun Raudah wacce ta rasa meke mata daɗi, Sarah batai mata komai ba amma kallo Guda tayi mata taji bata sonta gaba ɗaya, bata taɓa ganin mace mai kyau da tsarin halitta irin Sarah ba, ga wani gashi wanda har gadon bayanta ya sauka,ga shape cikin nan nata a lafe, girarta a cike taf da gashi, lip's ɗinta jajaye masu kauri, idanunta manya farare ta tas dasu, uwa uba manyan booms ɗinta, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Raudah take ba, ajjiyar zuciya Sarah ta sauke tana duba time ganin kamar da sauran lokaci yasa, ta ɗauki wayar Auta a hankali tayi dailing number sa, tana ta ringing ba'a ɗauka ba.... Abeed daman ya jima kafin yyi bacci hakan yasa baccin yyi masa nauyi, hannunsa riƙe da cikinsa, a wajan kira na uku ya motsa kaɗan ba tare daya buɗe ido ba, ringing da yaji yasan ita take kira, katse kiran yyi idanunsa na lumshewa ya kirata, tana fara ringing Sarah tayi picking tare da yin ƙasa da murya tace "Assalamu alaika" slowly Abeed ya ƙarasa buɗe idanuna yana mai jan pillow kafin yaja numfashi kaɗan yace "Uhm" ya faɗa bayan ya amsa Sallamar a zuciyarsa, jin muryarsa a sanyaye alamar bacci yake sosai yasa Sarah faɗin "Bacci kke?" A hankali ya ɗaga mata kai, kamar tana ganinsa tace "Sallah fa?" Ya rufe idanu ba tare da yace komai ba, ta ɗan turo baki tayi cike da shagwaɓa tace "Nidai ka tashi please,zaka makara ba'a wasa da sallah" zame duvet ɗin jikinsa yyi yana buɗe idanunsa da ƙyar kafin a hankali ya miƙe ya sanya slippers, Calmy yace "Oh! Ok" jin ya miƙe tsaye ta kashe kiran tana jin wani sanyi a ranta, tashi tayi tai sallah yana idarwa tai azkar kafin ta koma ta kwanta... Abeed na idar da sallah ya miƙe tare da zare jallabiyar jikinsa, wajan deep frizeer yaje ya ɗauki fresh milk da cup cikin kamewar nan tasa ya zauna saman Kujera tare da tsiyaya fresh milk ɗin a cup,a hankali yake sipping yana lumshe idanunsa, Wayarsa ya ɗauka domin duba abinda Danish ya tura masa, idanunsa ne ya sauka akan message ɗin da aka turo tun ƙarfe 1:15 na dare, ya jima yana duba saƙon ya karanta kalmar I love You yafi sai goma, banda Zain babu mai ce masa I love You,wacce kai tsaye ta ratsa zuciyarsa, ke nan tana sonsa? Ko kuma mene? Ajjiye wayar yyi a cinyarsa yana shan milk ɗin yana karanta kalmar I love You wacce gaba ɗaya tasa ya kejinsa wani iri, ya jima a wajan kamar zai mata reply sai ya share, Miƙewa yyi ya nufi wajan wardrobe ɗinsa ya ɗauki Gymashark sports t.shirt wacce ta kama jikinsa, da black ɗin Camouflage-print cargo trousers, ribbon ya ɗauka ya tattare sumar kansa ya ƙulle ta sauka a wuyansa wata kuma ta maƙale gaban goshinsa, wata short bag ya ɗauka ya zuba bottle water guda uku ciki, a hankali ya nufi Gym ɗinsa, yana shiga ciki ya sauke bag ɗin ya ajjiye waje guda kafin ya ajjiye Wayarsa, remote ya ɗauka ya kunna wata cold music kafin ya hau Elite Edge Walleness Energy, sa sauri yake gym ɗin nan da nan ya haɗa zufa sosai, ya jima ya nayi yana sauraran waƙar dake tashi, deep down na zuciyarsa yana tuna kalmar I love You! Yana gamawa ya hau ɗaya injin na Boom fitness har wajan 9:39 yakai kafin ya sauka a hankali yana sauke numfashi zufa na yanko masa, bottle water ya ɗauka ya shiga sha yana tafe yana shan ruwan, a haka ya isa cikin bedroom ɗin sa, wanka yyi ya shirya cikin Floral jacquard one button suit, dark brown, a hankali ya zame ribbon ɗin nan da nan sumar ta sauka ta wani irin nan na ɗewa, jikinsa na fitar da ƙamshin Hugo boss, sajansa sai ƙyallin Ginger Geminal Oil-hair yake, bakinsa na Ƙamshin LB Breath Herbal sugar-free Breath freshener spray, lokacin 10:00 walking slowly yake tafiya, harya fice daga cikin part ɗin nasa, ya nufi entrance yana fita Khabeer yyi saurin tashi ya nufi wajan sabuwar motar Abeed ɗin, wani guard ɗin sa ne ya buɗe masa ƙofar mota,a hankali ya shiga aka rufe ƙofar, motarsa ce a tsakiya ta bodyguards ɗin sa a gaba da baya, a haka suka nufi wani keɓantaccen gidansa wanda yake meeting a ciki, mutane ne wajan ashirin guest room, Danish na ganinsa ya miƙe tsaye tare da nuna masa Kujera, zama yayi akan 2seater gently ya ɗura ƙafarsa ɗaya akan ɗaya, idanunsa na yawo akan mutanan wajan wanda kallo ɗaya yyiwa kowa ya ɗauke idanunsa, Danish ne yyi masa bayanin komai duk suna son saka hannun jari ne a Company, information ɗin da ake buƙata duk suna dashi bisa tsarin Companyn, Abeed dai kansa a ƙasa idanunsa lumshe Danish yace "Sai Aryan Vice President's son da brother nasa, suma sun cike komai suna buƙatar saka hannun jarin, gently Abeed ya jinjina kansa alamar gamsuwa kafin ya amshi all files ɗin yyi signature akai ya bawa Abeed, Gdy sukai gaba ɗaya, bayan tafiyarsu Abeed ya fara dailing number da suke waya da Sarah amma a kashe, tsaki yaja kafin ya fara cin breakfast ɗin da Danish yasa aka jera masa, kaɗan yaci ya miƙe tsaye haka kurum yau yaji yana son zuwa club.... Zain ne zaune gaban Du'a dake kuka kamar ranta zai fita cikin kuka tace "Sbd Allah ya ɗura min Lalura ka ƙara Aure? Sbd baka sona na kasa kula dakai Shine zakai min kishiya bayan kasan yadda nke sonka? Ko kuma sbd ni na nuna so gareka tun farko shiyasa kai min wannan wulaƙancin?" Twins ta fara mgn yake kallonta da tsananin mmki,kafin a hankali yace "Wlh wlh da bana sonki ba zan taɓa amincewa na aureki ba, sbd ba zan auri wacce bana so ba, kiyi min adalci ƙarin aure na akwai dalili kuma Ubangiji ya ƙaddara min haka and..." Wata tsawa ta buga masa tana nuna masa ƙofa tace "Out....Out of my room Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas fita kaban waje,bana buƙatar jin komai na tsaneka." Ta faɗa tana sakin kuka ƙoƙarin jawota jikinsa yake, amma ta sanya ƙafa ta tura sa da ƙarfin gske tace "Ka fita bana son ganinka wlh, naji na tsaneka idan naci gaba da kallonka zan iya akaita wani abun, i hate you" ta faɗa tana ƙara sakin ƙara, Calmy Zain yace "But, I love you" da ƙarfi tace "Ƙarya kake, munafuki azzalumi wlh sai Allah ya saka min ka fitar min a ɗaki" ta faɗa tana ɗaukan wata kwalbar humura zata buga masa yyi saurin matsawa gefe, mmki duk ya gama cikasa ydda take da addini bai tsammaci zatai hakan ba, juyawa yyi ya fita Naila da Amma duk na zaune a Main Parlo suka bisa da kallo Naila tace "Tirrrrrrrrrrrrr,kaci kanka billahil lazi" fita yyi yana zuwa harabar Masarautar suka haɗa idanu da Junaid dake fitowa daga cikin motarsa kallo ɗaya yyi masa ya shige mota tare da nufar ɗaya gidan nasa, Sairah na zaune a parlo daga ita sai vest da pencil jeans mai flowers, ganinsa ya shigo wani iri yasa ta miƙe tsaye, a hankali ta ƙarasa wajansa tana leƙa fuskarsa da yaƙi yarda su haɗa idanu a nutse tace "Ta maka ihu ko? Bata amince ba ko?" Ta faɗa a sanyaye kasa mgn Zain yyi sai kawai ya jata jikinsa ya rungome ya shiga sauke ajjiyar zuciya, holding nasa back tayi tace "Am sorry, it's my fault" girgiza mata kai yyi yana ƙoƙarin Mgna wayarsa yyi ƙara,ciro wayar yyi Still holding onto her zare idanu yyi ganin saƙon e-mail daga Abeddeen, ɗaukan Sairah yyi ya shiga juyi da ita yace "Ina jin Zuwanki rayuwata Alkairi ne, yau Biyunina yyimin message, Wow can wait to see him" ya faɗa yana kissing lip's ɗinta ƙanƙamesa tayi tana dry kafin ya ɗauke ta zuwa bedroom..... Sarah na zaune a Main Parlo da Yamma a hankali take kallonsu duk sun shirya gwanin sha'awa, Auta tace "Sarah ke ɗaya zamu bari fa, tunda kince ba zaki ba ko?" Ba tace komai ba Beeba tace "Rabu da ita, tunda ba zata taga yadda Masarautar Zazzau take ba, mukam yanzu muka fara shiga zamu sha casu wlh" Raudah dai na tsaye tana danna wayarta fuskarta bbu walwala, amma taji daɗin rashin zuwan na Sarah, Umma dake tsaye tace "Ku saman a waje, Sarah take care of yourself ok" A hankali Sarah ta buɗe baki tace "Bye Umma" fita duk sukai banda Raudah dake tsaye sai da suka fita,Sarah ta miƙe zata shige part ɗin da suke taji Raudah tace "Heee You" Cak Sarah ta tsaya ba tare data juya ba, Raudah ta ƙarasa wajan Sarah ta kalleta frm head to toe Tace "Ga dai kyau iya kyau, amma babu asali ni Allah yasa ma ke ba mayya bace wlh" Sarah ta ware Idanunta ta shiga kallon Raudah, Raudah ta watsa hannunta tace "Yhhh, ko nai ƙarya kawai kin shigo family namu zaki takura mana, and kin samawa kanki lafiya da ba zaki je cikin Masarauta ba, domin iya masu gata da ƴanci ke shiga, kyan ɗan maciji watsastsiyya" tana faɗin hakan tayi gaba tana bangaje Sarah, Sarah tuni idanunta ya sauya amma sam ko hawaye ta hana kanta yi sai ajjiyar zuciya take saukewa, da ƙyar ta shige cikin bedroom tana auta maganganun da Raudah ta faɗa mata, kuka take sonyi amma ta kasa, bathroom ta shiga tare da sakarwa kanta ruwa ta jima ta fito, a hankali ta shirya cikin Silk short robe, mai faɗin wuya har Cibiyarta ana gani sai wani rubber Palazzo trousers wanda ya kama waist ɗinta, kanta bbu ko hula, ga wata siririyar necklace a wuyanta sai ƙamshi take na Valentino, shiru tayi akan bed idanunta rufe, ya kamata ta san wace ita tunda har an fara yi mata gorin iyaye, wata tsanar Daddynsu ya ƙaro a Zuciyarta, gashi yau gaba ɗaya wayar Jaan a kashe take, almost 10 minutes tana kwance taji wayar Auta na ringing idanunta ta buɗe tare da ɗaukan wayar da sauri ta miƙe zaune ganin sunan Jaan na wayo saman wayar, answering tayi a hankali tace "Hello"
sauke ajjiyar zuciya yyi sbd jin muryarta wata kala, ya jima kafin yace "Kina ina?" Tana kwaɓe fuska kamar zatai masa kuka tace "Gidan Yaya Rooma" Calmy yace "I knw, i mean a nan ɗin" tace "Oh! Ina bedroom" some minutes kafin yace "Fito entrance kiga" tace "Mene a entrance ɗin" yana rufe idanunsa yace "Ance za'ai ruwa a Nigeria, Just to confirm" tashi tayi tsaye har zata ɗauki hijab tunawa bbu kowa a gidan ta saka slippers tare da yin waje har lokacin wayar na maƙale a kunnanta, a hankali take tafiya jikinta na juyawa, kalbar kanta na lilo, a haka ta buɗe ƙofar shiga Asalin cikin gidan, tana fitowa entrance ɗin tace "Na fito,amma hadarin ba sosai ba" ta cikin wayar ya saki wani sauti yana raina wayon Sarah a hankali yace "juyo" yana juyawa idanunta ya sauka akansa yana tsaye ya juya mata baya ya ɗan jingina jikinsa da jikin motarsa, tun daga sama har ƙasa Sarah ke kallonsa, yana sanye da wata farar gezner ɗin kin jumper da babbar riga ya ɗura half jaddara akansa hular red ta haska fatar wuyansa, sumar kansa ta sauka ƙasa, binsa kawai take da kallon mmki, yana jin lokacin ta buɗe baki tace "My Man.." wayar ya zame daga jikin kunnansa a hankali ya mayar cikin Aljihu kafin gently ya juya....


😂😂 Finally
Me zaku ce??????
Me kuke tunanin zai faru???
Abeed or Jaan???
[08-15 08:47] +234 703 831 1110: 👑👑48👑👑
Fararen idanunsa ne ya sauka cikin idanunta, gently yyi baya kaɗan tare da jingina bayansa da jikin mota, kafin ya harɗe hannayensa a ƙirji, a hankali yake bin Sarah da kallo frm head to toe, musamman fararen cinyoyinta da suke waje da kuma yanayin yadda wuyanta ya bayyana sbd faɗin rigar, idanunsa ya sauke akan ragowar zanna lallan ƙafarta yabi dugwayen yatsun ƙafar da kallo, kafin gently ya ƙara maiyar da idanunsa cikin nata, tayi tsaye kamar an dasata she can't believed cewa shi take gani a gabanta,ko dai gizau idanunta ke mata ne, Sarah bata taɓa ganin Mutumin da Manyan kaya sukai masa bala'in kyau irin Jaan ɗinta ba, babu abinda ke ɗaukan idanunta irin saje da kuma sumar kansa, banda zanan tattoo ɗin da take gani a hannunsa,babu abinda zai sanya ba tace Abeed bane, babban abu kuma manyan kayan daya sanya, Abeed ba zai taɓa sanya manyan kaya ba, hannunta ta ɗaga tare da taɓa fuskarta irin ko mafarki take, ganin hakan yasa a karo na farko akan idanunta Abeed ya ɗaga jagirarsa guda ɗaya ɗaya tare da kashe mata idanu guda, a hankali kuma ya langwaɓar da kansa gefe, da gudu Sarah ta nufo inda Abeed yake idanunta ya cika da hawayen farin ciki, ganin da gaske wajansa ta nufu yasa ya ɗan miƙe daga jinginar da yyi slowly yake Girgiza mata kansa, yana mata alama da cewa ta duba kayan jikinta,ga kuma entrance ɗin gidan akwai masu bawa flowers ruwa ga gatekeeper, Sarah bata fahimci kurman baƙin nasa ba, da gudu tayo kansa batai wata wata ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙamesa ta sakin wani irin gigitaccen kuka, yanayin yadda ta faɗa jikinsa ba tare daya shirya ba, yyi saurin yin baya tare da sanya hannunsa ya dafe jikin motar, ɗaya hannunsa kuma yyi saurin riƙe waist ɗinta dashi, a hankali ya daidaita tsaiwar sa a jikin motar, kafin gently ya sanya duka hannunsa biyu yyi holding nata back, yana jin yadda take kuka sosai hawayen idanunta na sauka a gaban babbar rigarsa, a hankali ya ɗura kansa akan shoulder ɗinta ita kuma ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, shiru yyi mata hancinsa na shaƙar ƙamshin Valentino wanda take amfani dashi, slowly kuma yake manna mata tattausan kwantaccen sajansa, almost 10mnts suna a haka ganin har lokacin ta kasa daina kukan yasa a hankali ya ɗura bakinsa a kunnanta kafin ya sakar mata iska mai sanyi yana hura mata a hankali a hankali, ɗaya hannunsa ya ɗura saman kanta ya shiga shafawa a nutse yana jan numfashi, cikin wata kalar kasalalliyar Murya mai nuni da yanayi na kewa da kuma buƙatar miji zuwa ga matarsa,ya buɗe baki a hankali daidai kunnanta da ƙyar ya iya cewa "Pinky..." Ya faɗa a kame yana mai jan numfashi, domin iya wannan kalmar ce kawai tazo masa, Sarah kam ganin Abeed wanda take masa kallon wani Mutum nada ban,ya taso mata da irin maganganun da Raudah ta faɗa mata, na rashin asali da tushe, hakan yasa a yanzu take ganin Abeed kamar wani ɓangare na ahhalinta ko babu komai, shine ya santa tun tana ƙarama ya santa a lokacin da take da gatanta, ganin tayi shiru da kuka sai ajjiyar zuciya take saukewa yasa gently ya zame ta daga jikinsa, ba tare daya kalleta ba Murya a kame yace "Go and wear your hijab.." idanunta ta ɗaga taga waya yake dannawa, jin idanunta a jikinsa yasa ya ɗaga fararen idanunsa suka haɗa idanu, ware mata manyan idanunsa yyi sosai hakan yasa ta kwaɓe fuska tare da turo baki, sajansa ya shafa Calmy yace "Go Sa... Saraahh" idanunta yyi rau rau tace "Uhm A'a ni" ta faɗa tana ɗan dire ƙafarta ƙasa hakan yasa jikinta motsawa baki ɗaya, lip's ɗinta daya motsa har yyi Mgnar yake bi da kallo can yace "Ba tafiya zan ba" ka faɗa ta maƙale tana miƙa masa yatsarta kamar yarinya tace "Promise?" Sai hakan ya tuna masa lokacin da zai bar Masarautar Bilhira, hannunsa ya zame daga cikin Aljihu ya miƙa mata Hannun da sauri ta sarƙe ƙaramar yatsarsa tace "Mun ƙulla" tana faɗin hakan ta sakesa a hankali take tafiya da baya baya, duk tunaninta tana juya zai tafi ya barta, Abeed kam gajiyayyun idanunsa ya sauke akanta kamar yadda take kallonsa, sai yanzu ya ƙara raina shekarun Sarah, kawai jiki Allah ya bata da kaifin tunani da kuma tarin nutsuwa, haɗi da dakakkiyar zuciya... Ajjiyar zuciya ya sauke lokacin data shige gidan, walking slowly ya juya zuwa side ɗin driver kafin kuma ya buɗe ya shiga, yana zuwa ya zauna tare da kafe ƙofar da kallo, Sarah da gudu ta shige bedroom, tana jin kamar zai tafi ne bayan ta samu yazo, wani white lace ta ɗauka mai sky blue ɗin torch, fitted gown ne wanda daga saman wuyan aka buɗe shi ya zamana kamar anyi mata wuyan bubaa mai faɗi sai ƙaramin zip daga tsakiya, shape ɗin ya fita sosai da can ƙasan gwon ɗin wata tattara akai mai kyau bata da bazaa, simple ɗauri tayi na ture kaga tsiya, sai wata siririyar necklace mai white stone a tsakiya ta saka, samun kanta tayi ta ɗaukan lip balm ta shafa a lip's ɗinta, ta ɗauki perfume ta ƙara, veil ta ɗauka white ta yafa a shoulder ɗinta, Wani Metro shoe ta saka, kafin a hankali ta juya tana kallon kanta a mirror ita Mmkin kanta take mene yasa tayi wannan kwalliyar to? A hankali ta fito daga cikin bedroom ɗin duk tafiya sai hips ɗinta ya juya, fita tayi bayan ta rufe ko'ina tunda ta fito idanunta ya sauka akan ta, bai san dame zai kwatanta Sarah ba, sai dai kawai ya bita da idanu, kanta a ƙasa ta ƙarasa tsaye tayi domin bata san mene zatai mata, hannunsa ya miƙe ya buɗe murfin ɗaya side ɗin still idanunsa na kanta, bayan ya buɗe motar ya koma ya jingina, kanta ta ɗaga ta cikin glass ɗin motar suka haɗa idanu da sauri ta zame bata sbd kwarjinin da yyi mata, ganin still tana tsaye yasa Abeed taɓe bakinsa kana ya danna mata Horn, a nutse ta ƙarasa wajan motar tare da shiga ciki ta zauna kana ta rufe ƙofar, shiru wajan yyi jin shirun yyi yawa yasa ta juya, tana juyawa suka sake haɗa idanu ashe ita yake ta kallo, idanuna ya ɗauke tare da yiwa motar key a hankali yyi reverse da gudu yaja motar zuwa waje bayan mai Gadi ya buɗe musu gate.... Tunda suka hau kan titi babu wanda yace komai driving yake a nutse ƙamshin Hugo boss dana Valentino da sanyin a.cn cikin motar suka haɗu waje guda tare da bada wani irin kalar yanayi, tunda suka ɗauki hanya babu wanda yyi magana, sai can dai Sarah tana wasa da yatsun hannunta tace "Ina yini" a hankali ya juya kaɗan daidai lokacin itama ta ɗaga kanta suka haɗa idanu, ba tare daya amsa ba ya ɗauke idanuna yaci gaba da driving, a cikin wani haɗaɗɗan pech mai kyau taga yyi parking, kashe motar yyi a hankali ya juya zuwa inda take zaune matsawa yyi kusa ita a breathing nasa yana sauka a fuskarta, idanunta ta rufe shi kuma ya tsorawa fuskarta idanu, yana kallon yadda ta ɗura hannunta a bayansa, idanunsa ya ɗauke tare da buɗe murfin motar, kana yaja baya ƙara haɗa Idanu

Please Login or Register in order to submit comment