Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fara Handwriting mai kyau yana gamawa ya saka mata peper ƙasan pillow,a hankali yyi mata forehead kiss ya fito, Main Parlo babu kowa duk suna kwance suna bacci hakan yasa ya fita zuwa entrance ɗin gidan nan ma shiru, sai kukan tsuntsaye motarsa ya shiga hankali tashe yyiwa motar key tare da barin Masarautar, daidai nan kuma Abba ya fito kafin ya ƙaraso kuma Zain ya bar wajan tare da motarsa, ganin yadda ya figi motar babu nutsuwa yasa Abba juyawa zuwa sashinsa tare da ɗaukan wayarsa ya fara dailing number Zain ɗin tana ta ringing bai ɗauka ba, wajan 3miss calls sai kawai ya rabu dashi... Zain kai tsaye Garin Zahel ya nufa yana jin if anything happens to his wife ba zai taɓa yafewa kansa ba. Abeed ne tsaye idanunsa yayi jajur yanayin yadda yake sauke numfashi da sauri zaka san ran maza ya ɓaci, jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa, Daddy Salman ya ajjiye wayar da yake kafin ya juya kan Abeed yace "Be patient, everything will be fine, dole sai an bada umarnin zuwa Zahel zaka" Shiru kawai Abeed yyi domin baya jin zai iya cewa komai, Daddy Salman ma yasan ba lallai Abeed yace komai ba dan haka ya barsa ya cigaba da Wayarsa, ɗaya wayar Daddy Salman ce ta fara ringing ya ɗauka da sauri, shiru yyi yana jin abinda ake cewa kafin yace "Uhm, yanzu Sarki Mabus zai gane cewa ya tafka babban kuskure, ɗauke Sairah shine zai kawo ƙarshen sa, daman ina jiran confirmation akan shine yasa a ɗauke Sairah kowa? Yanzu kam tunda Shine ya ɗauke ta yanzu wasan zai zo ƙarshe, a matsayinsa na ɗan ta'adda ya fara wasan, a matsayin mu na jami'an tsaro zamu ƙarasa wasan daya fara" yana faɗin hakan ya kashe wayar tashi tare da kallon Abeed yace "Our time has started, let's go to Zahel now. either he kills us, or we kill him,Fight for the sake of Islam, fight for the nation of the Prophet" yana faɗin hakan yayi cikin gidansa, Abeed har lokacin yana tsaye kafin gently ya juya zuwa cikin gidan, zaune ya samu Sarah Idanunta yyi jaa alamar tayi kuka sosai, domin ita Allah kiyayeta har tayi niyyar fita sai kuma ta fasa, daga baya Mrs Zain tace zata wajan Grandmother ɗin su, shine tana fita kuma aka samu wasu suka ɗauke ta.. Kallonta Abeed yyi kafin yasa hannunsa ya ɗaga ta tsaye sukai very close da juna, ganinta tana shirin yi masa kuka yasa ya jawota jikinsa tare da rungometa sosai, yaƙi bata damar yin kukan, He wants her to encourage him, he gets to calm down with her before he leaves, He breathed slowly, yana ɗago fuskarta suka kalli juna He slowly said, "Do you want me to succeed in my job?" Kamar yarinya ta ɗaga masa kanta, He looked into her eyes and said, "Don't cry until I come back, don't you know how your tears affect my heart? I feel emty without you" numfashi ya sauke kafin yace "There are many things I want to tell you, save me your tears for my return" Idanunta na cikin nasa har lokacin ba tace komai ba ya kama haɓarta cikin ƙasa da murya yace "before now I have never asked you anything, now see in front of you Sarah, I need your prayers, kiyi min addu'a i donno What tomorrow bring, amma naji ba zan iya bacci ba idan ban kawo ƙarshen Sarki Mabus, ya cuci jama'a, ya zalunci addinin Musulunci, ya ƙuntata rayukan al'ummar Annabi, zamuyi JAHADI muyi kuyi da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, tare da sahabbansa, zamu fita ɗaukaka kalmar ALLAH" Muryar Sarah na rawa tace "Uncle kada kaje... Ina tsoro" Murmushin ƙarfin hali yyi kafin yace "Dole naje, zani tare da Daddy And ur brother Yashim" ta girgiza kai tana kama ƙugunsa ta riƙe ƙam tace "Please, bana son komai ya sameka" idanuna ya buɗe sosai kafin yace "Ni ƙatoto, or have you forgotten kene kika faɗi haka?" Kwaɓe fuska tayi ita har Zuciyarta ba wasa take masa ba, kuka ta saka masa yyi saurin rungometa zuwa jikinsa yana ɗan patting bayanta a hankali kafin kuma ya ɗaga ta Cak ko girman cikinta bai ji ba, ya fara zagaye da ita a ɗakin yana cewa "Gaki ƴar fara, ƙyakkyawar Matana" bakinta ta buɗe ta shiga ɓangala masa dry, sauketa yyi a hankali tace "Uncle zo Kaji" matsawa yyi tare da ɗura kunnansa a bakinta a hankali ta shiga yi masa raɗa ya waro idanunsa kasa cewa komai yyi sai kawai ya kama bakinta ya shiga yi mata wani irin kiss na musamman, cikon nutsuwa Sarah ta kama tongue ɗinsa zuwa cikin bakinta wani irin sihirtaccen tsotsa ta kewa harshen sa cikin kwarewa da kuma son kwantar masa da hankali, da ƙyar Abeed ya samu kansa a wajan Sarah har mmkin ƙarfin halinta yake, domin abubuwa ta dinga yi masa wanda bai taɓa tunanin ta iya ba, numfashi ya fesar suka haɗa idanu tayi saurin ɗauke nata idanun ya galla mata hararar wasa, ba zai iya Mgn ba dan haka kawai sai ya kama hannunta zuwa waje, a entrance ya samu Daddy Salman cikin baƙaƙen suit, Yaa Yashim na kusa dashi kansa a ƙasa, domin tun bayan bayyanar cewa shi ɗan Daddy Salman ne, basu taɓa samun kusanci irin na yau ba, Sarah na gefen Abeed yyi ƙasa da murya yace "Uhm Ur Daddy" ya faɗa yana jan hannunta, gently Sarah ta Ƙarasa kusa da Daddy kanta a ƙasa tace "Allah ya tsare Daddy" Murmushi Daddy yyi mata kafin ya bata side hug yace "Amin Luluu.." ya faɗa yana shafa kanta, Daddy yace "Ur brother" Sarah ta kalli Yaa Yashim tace "Allah ya tsare" Murmushi yyi mata yace "Amin sister" Abeed ya kama hannunta zuwa cikin wata farar mota, bayan motar ya buɗe mata ta shiga yace "take care of yourself Sarah" tana daga cikin motar ta miƙe hannunta tare da kama sajansa ta ɗan ja kana ta shafa, a hankali ta zura masa yatsarta a bakinsa, slowly ya shiga tsotsar yatsar nata idanunsa lumshe, cikin ƙasa da murya tace "Ubangiji ya kiyayeka, daga kiyayewarsa, ya tsare ka daga tsarewarsa, Ya-mujibu ya taimakeka, ya baka Sa'a mijina" ta ƙare mganar tana shafa kwantaccen sajansa, hannunsa ya ɗura saman cikinta yace "Jazakallah bilkhair Wife, ki kula da kanki zan dawo maki da Twins ɗinki" yana faɗin hakan ya ranƙwafa yyiwa cikinta kiss kana yaja hancinta yace "Ina Sonki Maaama" da sauri ya fita yana rufe mata ƙofar, driver yaja suka bar cikin gidan zuwa Masarauta.... Daddy Salman ya shiga mota shida wasu manyan securities Abeed na ƙoƙarin shiga mota yaji Wayarsa ya ringing, tsayawa yyi kafin yyi answering yace "Abba.." Mai martaba dake tsaye Amma na gefensa yace "Do you know that Zain went to Zahel town?" Da ƙarfi Abeed yace "What? When?" Abba yaja numfashi yace "Tun safe.." Girgiza kai Abeed yyi idan hankalinsa yyi dubu to ya tashi yace "bari na kira waya" Abba cut him out yace "Wayarsa na gida" Abeed bai tsaya magana ba ya kashe wayar kai tsaye wajan Yaa Yashim ya nufa yana huci kamar Mahaukaci yace "Who called Zain on the phone and told him that Sairah had gone astray?" Yaa Yashim yace "Nine" wani wawan mari Abeed ya saukewa Yaa Yashim guda uku ajere yana shaƙe wuyansa yace "are you crazy? do you know what you did?" Ya faɗa yana ƙara saukewa Yaa Yashim wasu marukan yace "You're mad... You're mad" da sauri wasu securities suka ƙaraso wajan Daddy Salman dai baice komai, da ƙyar suka ƙwace Yaa Yashim daga hannun Abeed wanda ya birkice ya zama kamar Mahaukaci, A fusace kuma ya shiga mota tare dayi mata key ya fita da wani irin gudu, ganin haka yasa Daddy Salman yace "follow him"...... Sarki Mabus na zaune yana sakin wata kalar dry yana bin tulin kuɗin dake gabansa yace "Babu wanda ya isa yaja dani, zanta yin abinda naga dama babu mutuwa a kusa dani" ya faɗa yana watsa kuɗin sama, Wayarsa tayi ƙara yana ɗauka yace "Ku gane gidan waye inda kuka samu yarinyar ciki?" Daga can cikin wayar madasin na'urar yace "Gidan shugaban hukumar fikira ne, yaransa guda uku ne, akwai namiji wanda ya kasance ɗan sanda, akwai yara mata guda biyu sune bamu san sunansa ba, ita wannan yarinyar mata ce a wajan lawyer dake kula da case ɗin ka" wata zabura Sarki Mabus yyi zufa na yanko masa yace "Na fahimci komai yanzu" yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da juyawa ya kalli Boka yace "me kace game da Yarinyar nan?" Boka yace "Zuwanta tsararre ne, ba haka kurum ta kasance cikin Masarautar Zahel ba" Sarki Mabus ya saki wata mahaukaciya dry yace "Kenan Salman ya shirya ɗaukan fansar kashe mahaifin matarsa da nayi ko? Shine ya turo min yarinyar sa, abinda ban gane ba mene yarinyar ta isa tayi? Me zatai min?" Boka dai baice komai ba, Sarki Mabus ya juya ya kalli Ayyana yace "Tabbas za'a biyo bayan wannan yarinyar, ki kula da ɓangaren ta, yanzu zanjen Subash a yau zai baƙunci lahira idan har bai dawo addinin Zahel ba, kuma duk inda Gimbiya Noro take dole ta fito" Ayyana ta jinjina kai, Sarki Mabus da boka sukai waje, suna fita Ayyana ta miƙe tsaye ta shiga tattara kuɗaɗan cikin wata ƙatuwar jaka, jakar ta shiga jaa cikin wani ƙaton rami tana zuwa ta cilla jakar cikin rami, kai tsaye wani ɗaki ta nufa tare da tsayawa a wajan ta rufe idanunta a hankali ta shiga rera waƙa cikin sanyin murya, Sairah dake zaune taci kuka ta ƙoshi ga wata yunwa da take ji tayi saurin Miƙewa tsaye, sbd jin Muryar matar data daɗe ba taji ba, a hankali ta fara takawa har zuwa wajan ƙofar tsaye taga Ayyana fuskarta rufe tana yin waƙa a hankali, Kallonta kawai Sairah take kafin Sairah tayi Magana Ayyana ya kama hannunta zuwa cikin ɗakin sirri, zaunar Sairah tayi ciki bayan ta ajjiye mata ruwa, da sauri kuma Ayyana ta rufe ɗakin ta nufi wani sashi nada ban.... tsaye Sarki Mabus yyi a gaban Subash wanda yake ɗaure da igiyar gaba ɗaya ya fita daga cikin hayyacinsa, Subash yaja numfashi a wahale yace "Kowa yana dace da Uba na gari amma ban dani, na tsaneka tsanake" Sarki Mabus ya karɓi tafasasshen ruwan zafi ya kwarara wa Subash a gadon bayansa, nan take fatar wajan
ta saɓule yace "Zaka dawo addinin Zahel ko ba zaka dawo ba?" Subash yyi Murmushi yace “Da maganar Allah Ta'ala: _Ban halicci mutane da aljanu ba, face domin su bauta min_” shiru Subash yyi kafin yace "Zaka halaka, lallai ka zaɓa taɓaɓɓe, tsinuwar Allah da mala'ikunsa su Tabbata a gareka da kai da la'anannan Abin bauta kabas" Sarki Mabus yyi dry yace "Tabbas fushin abin bauta kabas zai tabbata a gare ka, ina tsananin jin kunyar wai ɗana shine zai juya mana baya" Subash ya kalli mahaifina cikin tsana yace "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa; Ka ce Ku zo in karanta muku abin da Ubangijinku ya haramta a kanku. Shine _Kada ku tara shi da wani wajan bauta_” Sarki Mabus ya saka hannu ya ɗauke Subash da mari, kafin ya ƙara kwasu ruwan zafi ya kwarara kasa a ƙirjinsa, Subash ya runtse idanunsa yana faɗin "Allahu Akbar, Allahu Akbar Allahu wahidul Qahr" A fusace Sarki Mabus yace "Ku sauke min macuci yau na gama dashi, Abin bauta ka taimake ni" kafin su kunce Subash, sunji Murya a bayansu ana faɗin "Sairah, Sairah Where are you I'm here to save you" gaba ɗaya suka juya, jinjina kai Sarki Mabus yayi ganin Zain tsaye da alama baiji ma da shigowa cikin Masarautar ba, Sarki Mabus yace "Kai ne? Yau a gabana? Duk shekarun dana ɓata a kanka, ina nemanka idanunka rufe" Sarki Mabus yyi dry yace "Abin bauta kabas aikin ka na kyau, na nemi taimako kuma ka amsa" Subash da baya cikin hayyacinsa sosai amma sosai gabansa ya faɗi sbd jin ance Sairah? Is that true ita ɗin aka kira? Tana cikin Masarautar ko mene? Zain yace "Ba wajanka nazo ba, masu wajan naka ina tabbacin suna hanya, ka bani matata macuci azzalumi" Sarki Mabus ya ware hannunsa yace "Matarka? Ita kake so na baka? To ka zaɓa ka shiga Addinin Zahel mu sake maka mata, kaƙi shiga mu kasheta tare da abin cikin nata" Zain ya gyara tsaiwa yace "Jinina fansa ne ga Annabi Muhammad, jinine sadaukarwa ne ga addinin Musulunci, ko mutuwa ne ina da tabbacin dacewa da samun Rahamar Ubangiji, ka kuma fa? Kasan yadda aka hallakar da mutanan Annabi Isa? Kasan yadda aka hallakar da fir'auna? Kasan yadda aka hallakar da Mutanan Annabi Luɗ? Lallai taɓewarka sai yafi nasu, addinin Musulunci shine gaskiya duk wanda ya mutu cikinsa ba zai taɓa wulaƙanta ba, idan na mutu sama za'ai da Ruhina har zuwa sama da bakwai, kai kuma fa?" Sarki Mabus yana zuwa inda Zain yake yace "Ni zan mutu? Boka ka faɗa masa babu mutuwa a rayuwarta, zanta dauwama naita Dauwama a duniya ina tara kuɗi da ƴan mata ina kashe na kashe wa na samu duniya a hannuna" kafin Zain yyi magana Subash yace "Jin daɗi baya tabbata,idan bana gidan Aljana ba, kayi ƙoƙarin tuba domin mutuwar tana gefen hannunka" Sarki Mabus yace "Ka jira,ina nan zuwa kanka" Zain yana ƙoƙarin juyawa yaji gaba ɗaya an ɗaure sa da igiya tare da kwantar dashi ƙasa, Sarki Mabus yace "Abin bauta yau zaka sha jini" Subash ya fara ƙoƙarin kunce kansa ganin abinda mahaifinsa yake shirin aikatawa, wani irin ƙarfi yazo masa ya shiga kokawa da sarƙar da aka ɗaure sa da ita... Sairah can cikin ɗaki zaune tayi saurin Miƙewa tsaye sbd faɗuwa da gabanta yayi, nan take kuma ɗan cikinta ya shiga juyawa da sauri tamkar zai fasa cikinta ta fito, dafe cikin tayi jikinta ya shiga rawa tana bubbuga ƙofar tana faɗin "Is any body here? Help... Help... Please open d door" Amma shiru babu alamar da mutane a wajan, Sarki Mabus da yake riƙe da wuƙa yace "Yau zan faɗa maka abinda baka sani ba, Nine wanda ya kashe mahaifin sirikar ka, mahaifin sirikar shine shugaban hukumar fikira na farko, bayan na kashe sa aka ɗura Salman akan Kujerar, nemanka nake idanu rufe, yau kuma kazo har gari na, har cikin Masarautar kayi tunani zan Barka, babu wanda ya isa ya ceceka babu shi, Abin bauta kabas kabani Sa'a" Wani kalar Ihu Subash yyi yace "Kada ka aikata, zaka tafka kuskure, zakai ladama" Amma ina tuni Sarki Mabus ya ɗura wuƙa a wuyan Zain, Idanun Zain rufe sbd wani haske daya shiga yi masa yawo cikin idanun, wani ƙwataccen Murmushi ya saki kafin yace "Allahu Akbar, Allah ɗaya ne Annabi Muhammad S.a.w shine Manzo, La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah S.a.w" ya shiga faɗa cikin rashin imani Sarki Mabus ya kama wuyan Zain ya shiga yankawa, Zain ya shiga fidda wani irin numfashi, amma duk da haka Murmushi yake saki yana kiran sunan ALLAH, lokacin da Sarki Mabus ya samu nasarar yanka wuyan Zain daidai nan Subash ya ƙwace daga ɗaurin da akai masa a kuma daidai lokacin Motar Abeed ta shigo cikin Masarautar, Abeed ko tsayawa motar ta gama mutuwa bai ba, hankali tashe ya nufi wajan Sarki Mabus, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un cak Abeed ya tsaya ganin abokin haihuwar sa, abokin faɗan sa, abokin shawararsa, Biyunin kwance a ƙasa ɗaure da igiya jini ma zuba daga wuyansa, kasa tantance mai idanun ya gane masa yyi, yayi baya zai faɗi Yaa Yashim yyi saurin taresa, Sarki Mabus ya ɗaga kansa jin footsteps na mutane, Cak idanunsa ya tsaya akan Abeed da shock yake kallon Abeed da kuma kallon Zain wanda yake kwance Numfashinsa na fisga jini nayin tsartuwa daga wuyansa, Sarki Mabus ya murza idanunsa kenan su Biyuni? Ko kuma gizau yake masa? Da sauri ya nufi kan Abeed kafin ya Ƙarasa wajan Abeed Subash ya ɗaga wuƙar hannunsa tare da sauke ta a gefen Sarki Mabus yana faɗin "Allahu Akbar" ihu Sarki Mabus ya kwarara nan take kuma hannunsa ya fita daga cikinsa, Abeed kasa yadda yyi cewa Zain kwance jikinsa na rawa ya nufi wajan Zain yana zuwa ɗago sa, idanunsa ya sauka akan wuyan Zain daya rabe biyu, ƙam Ƙam! Zain ya riƙe hannun Abeed mgn yake sonyi ya kasa, fitar rai ba wasa ba, Daddy Salman juyawa yyi da sauri tare da zubewa akan motarsa, Yaa Yashim tuni hawaye ya fara fita daga idanunsa, Zain yana jan numfashi yace "Don't Cry, Don't Cry, Don't Cry, ban yafe ba idan kayi" shiru Zain yyi sbd jinin dake tsartuwa daga wuyansa, idanunsa nayin sama yana ƙanƙame Abeed yace "Amma, Abba, Sairah, Du'a, Cikin Sairah.. ka kula ka kula ka kula" shiru yyi Abeed jikinsa yana rawa da karkarwa idanunsa na juyewa da ƙarfi yace "Nooo! Yanzu zan kai ka hospital Noting will happen to you noting, kai jarumi ne, kace zamu mutu tare don't leave me Kada kai min haka" Murmushi Zain yyi kafin yace "Ina Sonka Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas.." nan da nan kuma jikinsa ya saki a hankali yace "La'ilaha illallahu Muhammadur Rasulullah s.a.w" Cak Numfashinsa ya tsaya idanunsa yyi sama jikinsa ya saki a cinyar Abeed alamar rai yyi halinsa.....



😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭👏🏻👏🏻 Forgive me, kuyi min adalci kada kuce nayi ba daidai ba dan Allah dan Annabi, mutuwa wajibi ne akan ko wanne ɗan Adam, ko wanne mai rai sai ya ɗanɗani ɗacin mutuwa, Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi.. babu da tabbacin za muga anjima balle gobe, Ɗa aciki yana mutuwa yabar Mahaifiyarsa, uwa na mutuwa tabar jariri, Mijina na mutuwa yabar mata, mata na mutuwa tabar miji...... Ni kaina da nake wannan Rubutun bana da tabbacin zan kai anjima balle gobe, kada na mutu da haƙƙina akan ku, kada ko mutu ku tafi da haƙƙina... Banawa kowa dole amma littafi na kuɗi ne akan ₦500 duk wanda ya shirya biya na via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank via evidence 08119237616.... Ubangiji ya cecemu rana gobe ƙiyama👏🏻😭😭😭*ZAIN ABEED 77*
_🎂🎂Thank God, I thank my loving biggest fans, who wished me a happy birthday, writers, Reader's, my relatives, I am happy, God bless you..... Wlh naga fatan alkairi kaca kaca sunata gantali a media, to me za kace? Allahamdulilla kawai... Don't forget I'm waiting for my Birthday gift💋💋😍 Cheers🥂🥂🥂..... Because of the happiness I am in, I returned three hundred books of Zain Abeed... Duk mai son Zain Abeed daga yanzu zuwa gobe 300 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank... show ur evidence 08119237616.... Babu abinda zance sai Gdy wlh nayi Mmkin alert ɗin da nake gani kawai matsayin gift😍😅🥂 See luv ehmnnn... Anywhere I luv u...






Abeed na kwance akan bed yana bacci Mai martaba na gefensa sai kuma Sarki Al'khasim Abubakar Wahab, ajjiyar zuciya Daddy Salman ya sauke cikin damuwa yace "Akwai matsala" Abba bai iya Mgn ba sai Sarki ne yace "What's the problem?" Daddy Salman yace "Anyi kuskuren barin Abeed yyiwa Zain suttura, yanzu duk jarumtar daya nuna sai ya tambaye sa, mutuwar sai tafi tsaya masa, da wannan juriyar gwamma yyi kuka da ihu asan yayi" Abba dai baice komai ba, dan yafi kowa sanin waye Abeed ya kuma halinsa yake... Clamly Abba yace "Before Abeed forgets Zain's death it is very difficult,I'm afraid that it has raised the pain in his memory" Sarki Al'khasim ya Girgiza kai yace "In sha Allah, hakan ba zai faru ba, ya kamata a haɗa masa da rubutu na dangana" Daddy Salman yana Miƙewa tsaye yace "Take away all the photos that are related to Zain, da duk wani abu daya shafe sa,Don't talk about Zain again if Abeed is around, that will help him to forget about it soon" Sarki Al'khasim yace "In sha Allah" Abba dai kasa cewa komai yayi, Abeed's affair scares him, he knows that he wants nothing more than Zain, Ever since they were children, Abeed has always loved Zain more than them, su kwana tare, suci abinci tare wasa tare, idan rashin lafiya ɗaya yyi sai ɗaya ya kwanta, bayan sun girma da ƙyar Abeed ya yarda Zain ya zama Lawyer, ko Court Zain zashi Tare suke zuwa da Abeed ya jirasa a mota, haka duk garin da Abeed zashi show Zain yana tare dashi, idan akwai wanda akaiwa mutuwa bai shige Abeed ba... Juyawa yyi a hankali ya kalli fuskar Abeed wacce lokacin guda ta faɗa, hannunsa ya ɗura saman sumar kan ya shiga shafawa kana yyi masa Peck kiss tare daja masa duvet yabi bayansu Sarki Al'khasim Abubakar Wahab. Har dare Amma bata farka ba ita da Du'a sai addu'a ake musu, tuni masallatai suka fara saukar Alkur'an, Mai martaba yace baya son zaman makokin nan dan haka dare nayi kowa ya kama gabansa, na nesa ne kawai suka zauna... Washegari ɗaya ga rasuwar Zain, Aunty Zulfa ce da Yaya Rooma zaune a female surgical Ward, suna zauna Gimbiya Noro ta buɗe ƙofar office ɗin Dr ta Fito,She bowed her head and looked as if they were angry with her, tsaye tayi ta ƙasa cewa komai, Yaya Rooma ta kalleta tace "Ya masu jikin?" Gimbiya Noro da babu magana a bakinta sosai tace "Lfy ne" tsaki Aunty Zulfa taja She stood up, she didn't look at where the princess was, she went to the doctor's office, bayanta kawai Gimbiya Noro tabi da kallo, ko kaɗan ba taji wani abu ba.. A hankali Aunty Zulfa ta murɗa handle ɗin Ƙofar, daga cikin office ɗin akace "come in" ta tura ta shiga, Dr ya nuna mata Kujera yace "Have a site please Madam" tana zama tace "ya jikin Sairah, What kind of situation is she in now?" Dr ya zame glass yace "Ohh, Sairah Salman Al'khasim?" Anuty Zulfa tace "Yhhh" ya ware wani file yana dubawa kafin yace "An mata c.s ai" Anuty Zulfa ta ware idanu tace "C.S and whose signature?" Dr yace "Akwai wata mata, su bama buƙatar saka hannun mace, na namiji muke so, gashi duk suna cikin tashin hankali, ba zamu iya jira na wani lokaci ba, hakan yasa ɗaya mara lafiyar mai suna Subash ya saka hannun" jinjina kai kawai Anuty Zulfa tayi tana nanata sunan Subash, kafin tace "If there is no problem I would like to see her now with her baby" Dr ya miƙe tsaye yace "Why not? But babyn bai cika kwanakin haihuwa ba, zamu saka shi cikin kwalba duk da cewa lafiyayyan ne"..... "Mace ta haifa ko Namiji" Dr yana yin waje yace "It's a baby boy" bayansa tabi a nan waje suka samu Gimbiya Noro da Yaya Rooma, Yaya Rooma tabi bayan Anuty Zulfa... Gaba ɗaya tsayawa sukai suna ƙarewa jaririn kallo mai tsananin kama da Zain, babu inda ya barsa sai motsi yake da hannunsa, fari tas dashi ga tulin suma irin ta Abeed, wasu hawaye ne ya sakkowa Anuty Zulfa da sauri ta juya tana goge Idanunta, Yaya Rooma ma tabi bayanta suka shiga Room ɗin da Sairah take ciki, tana kwance flat saman bed hannunta maƙale da ruwa ɗaya kuma jini, a hankali take sauke numfashi ta rame sosai sai haske da tayi masa kana ganinta kasan ta Wahala, suna zaune a wajanta wayar Anuty Zulfa ta fara ƙara, a hankali ta ɗauki wayar ganin sunan Yaa Yashim yasa tayi answering call ɗin, tana ɗagawa Murya a sanyaye Yaa Yashim yace "Amma ta farka, bata hayyacinta" Miƙewa Anuty Zulfa tayi kafin tace "Gamu nan" Yaya Rooma ta biyo bayanta suka fito, ganin Anuty Zulfa na shirin yin entrance na hospital yasa Yaya Rooma faɗin "Anuty bamu duba ɗaya mara lafiyar ba" a fusace Anuty Zulfa ta juya tace What have you connected with him that you want to know his situation? don't forget it was his father who killed our child Zain... After all this kike son sanin halin da yake ciki Roomana?" Yaya Rooma ta girgiza kai ta kasa fahimtar wacce zuciya ce da yayar ta ta, mene laifin Subash? Bayan shima yasha wahala Allah ne kawai yyi da tuni shima an jima da kashe sa, tayaya laifin Uba

Please Login or Register in order to submit comment