Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana bani akwai abinda ke shirin faruwa mara kyau nan kusa, Sarki Mabus ya shige tunaninka, tunaninmu, kafin samun nasara a kansa sai an rasa rai" Yaa Yashim yace "Rai kuma? Naga ai mun kusa kawo ƙarshen abun" Daddy yyi murmushi yace "Ko? Kafin Sarki Mabus ya zama sarki ɗan kasuwa ne, bayan rashin Mahaifinsa akace zai maye gurbinsa, hakan yasa aka buƙaci hukumar fikira ta binciko halayyar sa, a nan na fara aiki kasancewa ta shugaban hukumar fikira, duk wanda aka tura Zahel baya dawowa, lamarin ba'a nan ya tsaya ba mutuwar ko wanne members na hukumar fikira daban yake zuwa, wani a gidansa wani a wajan aiki wani shaƙawata, kafin mutuwar kuma sai an kwashi dukkan abinda Mutum ya mallaka na kadara, gaba ɗaya sun gama sanin sunayen jami'an hukumar fikira, shiyasa na buƙaci ƴan sanda cikin lamarin kuma na ɗauki sabbin jami'ai wanda abin zai girgiza kowa" Shiru Yarima Yashim yyi yana jinjina maganar Daddy yana kuma ƙara jinjinawa tunaninsa kafin kuma yace "Wanne sabbin jami'ai ka ɗauka to?" Daddy ya juya idanuna yace "Tsammaci abinda baka tsammani..... With time" kallonsa kawai Yarima Yashim keyi without blinking ganin kallon da yake masa yasa Daddy faɗin "Ka daina damuwa akan dalilan daya sanya na sadaukar da ƴaƴana, kasha tambayata mahaifiyarsu, to ka sani bata raye tun suna cikinta Allah ya amshi ranta, da ƙyar akai aiki suma aka ciro min su a raye...... I think there is nothing to say bayan haka, muna da abinyi" Daddy na faɗin hakan ya shige motarsa, jiki a sanyaye Yarima Yashim ya shiga mota shima..... Suna shiga cikin gidan Sarah ta nufi bedroom tare da faɗawa kan bed wani irin kuka ya kwace mata, tsanar Daddynsu ya ƙara ninkuwa cikin ranta ashe all this time yana raye amma yyi banza dasu, yace ba Shine ya mahaifesu ba idan haka ne su ɗin basu da uba, hakan an nufin sunanta TSINTACCIYA!.... Beeba ta kalli Sarah kamar zatai magana sai kuma tayi shiru kawai, domin ta fahimci Sarah bata jin daɗin Zuciyarta,kuma bata son aurenta da Yarima Yashim kawai halacci take son yiwa Anuty Zulfa, fita tayi daga cikin bedroom ɗin zuwa parlo, Anuty Zulfa tace "Ikon Allah, kaji wani abin almara Liman shine Daddyn Sarah? Hakan na nufin shine ya amshi Sadakin ƴarsa da kansa, Allhmd yanzu Sarah zata shiga Masarautar Zazzau da ƴan cinta lokacin bawa Kilishi amsa yayi" Auta tace "Mami Sarah bata farin ciki da ganin Mahaifinta, kuma kamar...." Auta kasa ƙarasa maganar tayi Anuty Zulfa ta kaɗa ƙafa ba tare da tace komai ba, Beeba dai taga ba zata iya shiru ba tace "Mami Sarah bata son Auren nan, bata son Yarima Yashim" Anuty Zulfa tace "Sannu rasai, Bilkisu ke kiyayan Wlh, ita ta buɗe baki tace bata so ko mene?" Beeba tayi shiru tare da Miƙewa ta nufi waje she's trying to call Junaid's digits..... Daddare Sarah na zaune ita ɗaya a Main Parlo watching TV, daga ita sai Short pencil jeans, da Ripped top designers sumar kanta a tufke da ribbon, idanunta ya kumbura ta ɗura ƙafarta ɗaya kan ɗaya time to time tana kallon Number sa, kamar zata kira sai kuma ta fasa can dai tayi ajjiyar zuciya tare da danna call ɗin ta kara a kunnanta, har tayi ringing ta gama ba'a ɗauka ba, ƙara kira tayi Still not answering idanunta ta rufe tana jin zuciyarta babu daɗi, she just to say hello to him taji ya yake domin taga ya rame sosai, Lokacin da Sarah take kiran Abeed yana zaune a parlonsa shi da Dr Adyan, Dr Adyan ya kalli wayar Abeed dake kusa dashi Abeed na ƙoƙarin ɗauka Dr Adyan yyi saurin ɗaukan wayar Murmushin takaici yyi kafin ya kalli Abeed daya haɗe fuska idanunsa akan t.v yadda yake kallon t.v kaɗai zai nuna maka baya fahimtar me ake, Dr Adyan yace "Better half" shiru shi dai Abeed yyi, har lokacin wayar ringing take, Dr Adyan bai sake Mgn ba har kiran ya ɗauke wani ya sake kira, sai a lokacin Abeed ya miƙa masa hannu yace "Bani" ya faɗa yana ya motsa fuska alamar baya jin daɗi, Dr Adyan yace "Wlh ba zan baka ba, Loser" still Abeed bai kula Dr Adyan ba, ganin haka yasa Dr Adyan yace "Are you stupid, you can't take action while watching her become someone else's wife,You can't fight about your love, but your bad attitude prevents you from doing anything, yanzu kai ka yarda ka amince ka barwa wani ita" shiru dai Abeed yyi ganin da gske ba zai magana ba Dr Adyan yace "Ka faɗa min idan kana son Sarah, ni kuma zanwa Anuty Zulfa bayani, tunda kai ka zama loser" rai ɓace Abeed ya juya ya cakumi wuyan Dr Adyan cikin wata kalar Murya yace "If I tell her that I love her, sai na faɗawa wani? When I brought her to the hospital, did I consult you?I will never marry someone else's wife, even if I lose my life for her love" ya faɗi hakan yana hankaɗa Dr Adyan baya da zafin zuciya kuma ya shige bedroom tare da kullewa, a hankali ya kwanta kan bed tare da yin lamo yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa, bai san wanne abu ya akaita har haka ba, a karo na biyu yana ji yana kallo ya ƙarasa rasa damarsa, ɗaya Wayarsa ce ta shiga ringing jin Algaita na tashi yasa ya miƙa hannunsa a hankali tare da yin answering cikin Muryar rauni sosai yace "Abba..." Mai martaba ya numfasa yana gyara zamansa akan ladduma kafin yace "Magaji" Abeed ya lumshe idanunsa kafin a hankali yace "Na rasata,Abba" Mai martaba yyi shiru kafin yace "Kuma ka faɗa mata komai?" Abeed ya langwaɓar da kansa yace "Uhm ni bance mata ina sonta ba..... But" Mai martaba yace "It's okay, komai ya faru it's your fault bana da abinyi Magaji kamar yadda yake sonta haka yake son matarsa, kuma munso zuciyar mu idan muka tilasta masa ya saketa, i can't so kayi hqr" Abeed ya miƙe daga kwancan da yake zuciyarsa na bugawa yace "Abba hqr fa kace?" Mai martaba yace "Allah has destined Goodness for you, Be patient..." Shiru yyi bayan yaja numfashi Abba ya sake cewa "Ride the wives, you will have hardship difficulty..." Shiru Abba ya sakeyi kafin yaja numfashi yace.
"إن مع العسر يسرا، إن مع العسر يسرا"
Abba ya sake yin shiru sbd ya jima bai magana mai tsayi ba kafin clamly yace "Indeed with hardship there is ease, and with the same hardship, there is another point of ease, You'll always have ease, look at the positive Do you not have faith in Allah? That should keep you focused, so take it as destiny..." Abeed idanunsa yyi jajur a hankali yace "Abba!!" Abba cut him out yace "Ka fara yiwa Sarah kallon sister ka cire so... Ni kuma na maka Al'ƙawarin zan zaɓa maka mace ta gari a cikin ƴar ƴan sarakuna" kasa magana Abeed yyi sai kawai ya kashe wayar yana Miƙewa tsaye key car ya ɗauka kai tsaye kuma ya nufi Club.... Zain na zaune shi da Sairah wacce take maƙale a gefen jikinsa suna kallo, a hankali tace "Deee" Zain ya kalleta kafin yace "Yes" kwantar da kanta tayi kafin tace "Gabana faɗuwa yake" ajjiye remote ɗin hannunsa yyi kafin ya juya ya kalleta yace "Kiyi addu'a, kada ki sawa kanki damuwa sbd abinda yake jikinki, damuwar zata iya taɓa abinda yake cikinki" kai ta ɗaga masa kafin tace "Please ka tayani dubawa Ahhali na, ina son sanin komai a kaina" Zain yace "Ko Sarah ce?" Shiru tayi masa ba tare da tace komai ba, yace "Ki sassauta ƙiyayyarki a kanta,kilama kin fita kwanciyar hankali" kwaɓe fuska tayi tace "To a bar mgnar" dry yyi mata yana jan hancinta kafin ya Sanya hannunsa ya ɗago ta zuwa kan cinyarsa yace "Bari na gaisa da My unborn child" murmushi tayi tana ƙoƙarin Zamewa tace "Uhm, nidai Allah ka bari nifa ba wani ciki" yace "Or Doctor ƙarya zai mki?" Kasa Mgn tayi sbd kiss daya sakar mata sun daga wuyanta har zuwa Cibiyarta, shiru Zain yyi yana jin yadda ɗumin cikin Sairah ke ratsa kunnansa, Sairah ta ɗura hannunta a kansa tana shafawa, gently ya ɗago kansa suka haɗa Idanu, ware masa idanu tayi tace "Wat?" Ya langwaɓar da kansa gefe yace "Kiss me Beee" kama fuskarsa tayi tare da ɗura bakinta saman nasa ta shiga kissing lips ɗinsa, riƙeta sosai Zain yyi yana jin wani irin daɗi, dukkan nutsuwar da yake son samu ya gama samu, he loves Sairah irin sosai ɗin nan, kwace bakinsa yyi yana ƙoƙarin yin mai gaba ɗaya Wayarsa ya fara ringing, dafe kai yyi yace "An shiga haƙƙina" dry Sairah tayi tana masa gwalo yace "Zan kamaki" ya faɗa yana ɗaga kiran, miƙewa yay yana faɗin "Ok, Allhmd in sha Allah" yana faɗin hakan ya kashe wayar, Sairah na tsaye a kitchen taji an rungometa ta baya tare da kissing ɗin Cheek ɗinta, juyawa tayi suka haɗa idanu ganin yadda ta ƙara girma da haske yayi kenan cikin ya fara ƙwari a jikinta kenan, Murmushi yyi tace "Mene?" Yace "Noting" ya faɗa yana rungometa a jikinsa yyi shiru kafin ya ɗauke ta cak zuwa bedroom yana faɗin "bari na rage aiki kafin magrib" saƙale wuyansa tayi tana sakin Murmushi..... Naila ce tsaye akan Mai martaba tace "A'a idan tsoran matar nan kake kwara ka faɗa kawai a tafi Leges, banda haka mace tai ta zuba iskanci hankali kwace ba dole tayi abinda taga dama ba, nifa banda kada ace min ƴar ta'adda ta kai zan ƙaddamar mata har Nep yunk ɗin" Mai martaba ya kalli Naila yace "Me zance?" Da sauri Naila ta juya ta kalli Daddy Waziri tace "Kaji wulaƙanci ko? To a gsky ba dani kake ba mene ma haɗani da kai, kiranta zakai yanzu maza maza kace ta sako Saratu a jirgi ta dawo da ita Naijeriya, wlh sai Saratu ta bar wajan ƴar dabar matar nan, ni ban taɓa yin al'ƙawarin na saɓa ba, ai banyi tsofan da zan mata hadisin ba, wanda yayi alƙawari ya saɓa wahuwa munafiqun" Junaid na zaune cikin jallabiya fara idanunsa cikin farin Glass Naila ta juya ta kallesa tace "Ai idan kaga baka auri Saratu ba, to ban cika tashin leges ba, Allah na tuba wani kallar Iskancin ne ba mu gani ba, banda bana son tuna Asiri Uwarka fa bayan ya gudu taka nan ɗin da ƙyar muka samu ta a leges" Junaid ya kalli Naila yace "To yaushe akace Sarah na wajan Mami?" Naila ta riƙe baki tace "A'a wlh an munafurce ka, amma yarinyar nan su suka bawa Zulfa'u da hannunsu sbd kada su aura maka ita, kawai dai ayi sha'ani a bar kaza cikin gashinta" Mai martaba dai baice komai ba, haka ma Amma haka Daddy Waziri, Naila ta ɗaga rigarta sama tace "Ƙilan idan yaga zan ɗaga masa nono yabi gabe zance na" Da sauri Daddy Waziri yace "Haba Naila mene kike haka ne" Mai martaba ya ɗaga wayar tare da ɗan dannawa ya kai kunne can kuma ya zame yace "Wayar a kashe" zama tayi tace "Tsinanniyya ce fa, ƙila tana can tana yanka cikin jama'a"....... After 2week har lokacin Sarah bata ƙara sanya Abeed cikin idanunta ba, gashi yanzu sun shiga last semester na level 2, tana zaune a entrance cikin duguwar na Abaya hannunta riƙe littafi tana dubawa sbd exam gaba ɗaya ta fita hayyacinta, amma hakan bai hana tayi wani irin mugun kyau na Abin mmki ba, ko'ina na jikinta glowing yake, a hankali ta miƙa hannunta ta sake trying na number sa amma a kashe yake, idanunta ta rufe ko ina yaje Ohhu? A hankali kuma hancinta ya fara shaƙar Ƙamshin Hugo boss, a ɗan tsorace ta buɗe idanunta tsaye ta ganshi a bakin gate ya Rungome hannunsa a ƙirji yana Kallonta, Miƙewa tayi tsaye jikinta ya ɗauki rawa sosai, walking slowly ya shiga takawa zuwa inda take ƙoƙarin ja baya take tana son guduwa a hankali yace "kin san Allah ki tafi uhm.." Cak ta tsaya kanta a ƙasa harya ƙaraso wajan, runtse idanunta tayi tana jin yadda yake sauke mata numfashi, da sauri ta buɗe idanunta sbd hannunta da taji ya kama bakinta na rawa tace "Ka sakeni, Mami za tai mgn please" banza yyi mata ya shiga tafiya da ita zuwa waje, motarsa ya buɗe ya Sanya Sarah ciki kana shiga ciki, Khabeer yaja motar da gudu sai da sukai nisa kafin Khabeer yyi parking a gefen titi, fuskar Abeddeen babu walwala yace "Za'a taruwa Mami latter akan zaku fita excursion a shcl.." kallonsa Sarah kawai take kafin tace "Amma ai mu ba'a ce mana akwai excursion ba" idanunsa lumshe yace "Tsari na ne haka, kuma koda wasa kika cewa Mami ba haka ba, Wlh wlh Sarahh..." Sai kawai yyi shiru idanunta ya cika da Hawaye tace "Amma kasan wannan ba daidai bane? Matar aure" bata ƙarasa faɗa ba ya buga mata tsawa yace "Sarahh.." jikinta har rawa yake, fuska ɗaure yace "Ki shirya kayanki.... Wanda zai ɗauke ki zuwa wata guda" zare idanu tayi tace "Wata fa? Kuma ina nidai gaskiya ba zani ba, kuma Auta ai tasan ba haka bane" banza yyi mata tare da fita daga cikin motar, ganin Abeed ya fito yasa Khabzuwa inda Abeed yake, Idanun Abeed akan Khabeer yace "Ka shirya min ticket zuwa Russia, tafiyar sirri komai a Sirri" Khabeer yace Yes Sir", cikin Motar Abeed ya koma har lokacin Sarah tana yadda ya barta cikin rawar Murya tace "Ban so ba zani ba, wannan ba daidai ba ne" tsawa Abeed ya daka mata yace "Zuwa babu fashi" kuka Sarah ta sakar masa a hankali ya jawota tare da ɗura kanta a shoulder ɗinsa a hankali ya shiga patting bayanta, Sarah ta ƙara rushewa da kuka tace "Uncle Why? Hurumin Ubangiji zaka shiga?" Idanunsa a lumshe sai kawai taji ya fisgota tare da ƙanƙameta a jikinsa yana sauke numfashi....


Zain Abeed isn't free contact to subscribe..... 08119237616..... It'
SARAUTAR MARUBUTA❤******59******️For some minutes yana riƙe da ita a jikinsa, kafin a hankali ya saketa not looking at her yace "Tommorow by 7pm zan sameki schl" yana faɗin hakan yyi shiru can kuma ya buɗe ƙofar ya fita, yana tsaye ba tare daya kalleta ba ya shiga danna Wayarsa, a sanyaye Sarah ta fito daga cikin motar da sauri kuma ta shige cikin gida, sai da taje bakin gate ta tsaya kafin ya buɗe baki tace "Kuma ni ba zani ba" tana faɗin hakan tai cikin gidan da sauri tana haki, gently ya ɗaga idanunsa tare da binta da idanu, wani cute smile ya saki da ɗan sauri kuma ya shige bayan mota, Khabeer ya rufe murfin motar, kai tsaye wajan ƙaddamar da Companies ɗinsa suka nufa, haɗaɗɗan Company wanda ya a gaji da haɗuwa, a hankali Khabeer yyi parking motar daga can parking lot, yana yin parking gurds suka ƙarasa wajan tare da tsayawa jikin motar Abeed, Danish dake tsaye riƙe da files da Ducoment, ya matsa kusa da motar cikin nutsuwa ya buɗewa Abeed motar kafin yaja da baya yace "Wlcm Sir" fararen idanunta ya liman yana ƙara jingina da jikin motar, slowly ya buɗe idanunsa bayan zuciyarsa ta tsagaita da bugawa, He was tired of this system, he didn't know why he agreed to keep it a secret, He got out of the car, his face was not cheerful, Danish ya kallesa yace "Shall we.... Kai ɗaya ake jira,Everything that is right is done" Danish ya faɗa a hankali, Abeed dake tsaye ya ware hannayensa cikin sauri wani guard ya sanya masa jacket ɗin Suit ɗinsa, walking slowly ya nufi ƙofar buɗe Babban Companyn, Danish da sauran ma'aikata na biye dashi,har haka ƙarasa wajan babu wanda Abeed ya kalla, yana zuwa ya tsaya Danish ya miƙa masa Scissors, ya tsuna fuska yyi kana yasa hannu ya amsa, zaren dake wajan ya yanka yana yankawa aka shiga watsa Flowers, ana faɗin "Congratulations" buɗe ƙofar akai Abeed ya fara shiga sai Danish kafin su Aryan da sauran wanda suka sanya hannun jari suka shiga, meeting sukai har lokacin Abeed baice komai kamar yadda bai kalli kowa ba.... Da daddare Sarah na zaune a ɗaki ta haɗa kanta da gwiwa tama rasa wanne kalar tunani zatai, Beeba dake tsaye ta zauna kusa da Sarah tace "Meke damunki Sarah?" Sarah taƙi cewa komai taƙi kallon Beeba, Beeba tace "Kina yaudarar ki kanki, ni na ɗauka a waye kike Sarah, a rayuwa zaman Aure da wanda baka so yafi komai masifa, firstly Everything that is appropriate for a woman to give to her husband, you can't, Yes u can't sbd tun farko baki sonsa,Secondly, you can't let go and show love to your husband,Love between spouses, and mutual acceptance is the guarantee of eternal marriage, Sarah Zaki kasance kullum cikin ɓacin rai, idan kika kalli Yaa Yashim mai makon kiyi farin ciki sai dai kiyi baƙin ciki,The reason for this is that you don't like him, idan baka son miji ko a kwanciyar Aure ba zaki iya yi masa abinda ya dace ba, kinga kenan zaki samu damar ɗaukar wa kanki zunubi cikin sauƙi,Tell him that you don't love him, he will be patient and marry another woman and divorce you,babu maganar kawaici ki zaɓawa kanki mafita tell him the truth of what is in your heart" kuka Sarah ta saka tana riƙe hannun Beeba bakinta na rawa tace "You're right Beeba, I don't have any reason ko ina so ko bana so dole na auri wancan Yaa Yashim zaɓin Mami ne... But what if I meet someone? What if I fall in love with someone else, this means that I will fight for him, me, us and our love? But what if I didn't find anyone wanda zai taimaken? Zuciyata babu daɗi I am speechless, kawai zan amshi Yaa Yashim tunda it's too late to cry.." Beeba tai shiru kafin tace "Kin yarda cewa baki son Yaa Yashim?" Gently Sarah ta ɗaga kai sai kuma tace "Dan Allah don't tell anyone even Auta" Beeba tayi Murmushi sosai kafin tace "To akwai wanda kike so ne?" Shiru kawai Sarah tayi Beeba tace "Don mind me, call Yaa Yashim kice kina son ganinsa gobe da wuri kafin ki tafi excursion ɗin" Sarah tace "Ni ba zani ba" Beeba ta daki shoulder ɗinta tace "C'mon.... Idan kika tafi after you tell him everything ƙilan Kafin ki dawo ya baki Divorce paper, Daman baki da idda sai kawai ki fisgi ki nemi wanda kike so, a to uban wani zai zauna maki dashi me zai sa kuma ki kashe wayarki kina yarinya dake" Sarah tai shiru Beeba tace "Common Beb" wayarta ta ɗauka tai dailing number sa, time ɗin yana kwance akan make bed ɗinsa, idanunsa akan system yaji Wayarsa na ƙara, Murmushi Yaa Yashim yyi kafin ya ɗauki wayar yana kashe murya yace "Princess.." Murmushin dole tayi kafin tace "How are you" Yaa Yashim yace "Ina ta tunaninki, na dai kusa mallakar ki kowa ya huta, wlh har mmkin irin son da nake maki nake, ko yanzu ina da iko dake fa kawai dai..." Shiru yyi Sarah dai na kallon Beeba ba tare da tace komai ba, Yarima Yashim yace "Are You Okay?" A hankali tace "Zani excursion" Calmly yace "Mami ta faɗa, kina dawowa Sai biki na kusa raba ki da ko wanne banza" shiru tayi sai kuma tace "Uhm, kazo kafin na shige" da sauri Yarima Yashim yace "Are You sure kina son ganina?" Tace "Uhm" wani Murmushi yyi yace "Thanks God, wai wife na son ganin mijinta" da sauri Sarah ta kashe wayar Beeba tace "Ji banza? Son masu wani, saura kuma gobe ki kwafsa" Beeba na faɗin hakan ta miƙe tare da shigewa bathroom.... Abeed na kwance saman bed bayan ya watsa ruwa daga shi sai boxer gaba ɗaya jikinsa ruwa ke zuba, yau matsanancin ciwon ciki da mara yake, amma sam a fuska ba zaka ce bashi da lafiya ba, idanunsa dake rufe ya buɗe kafin gently ya miƙe tsaye tare da nufar deep frizeer dake Bedroom ɗin nasa, buɗewa yyi ya ɗauki wata kalar chocolate mai kyau tare da ruwa mai sanyi, a saman Kujera ya zaune bayan ya ɗura ƙafarsa saman bed ya buɗe chocolate ɗin, slowly ya kai bakinsa yana gutsira yyi saurin fitowa da ita,sbd wani ɗaci da yaci cilli yyi da chocolate ɗin rai ɓace ya kira number Danish "Where the hell are you? You will buy me this unsweetened chocolate, no sweetness at all" Danish yace "Sorry Sir, but Sir Amedei chocolate ce" Tsaki kawai Abeed yyi tare da kashe wayar, bathroom ya koma ya ɗauki toothbrush ya wanke bakinsa kana ya dawo saman Kujera ya zauna, gorar ruwan ya buɗe dai da ya shanye tass ya ajjiye emty, Zain ne ya kirasa sun jima suna waya kafin ya kashe wayar, a hankali ya duba time yaga 2ta shige, bashi da wani zaɓi dole yabi zuciyarsa, number ta ya kira ga mmkinsa sai yaji ta ɗauka amma ba tayi Mgn ba, shiru Sarah tayi tana gyara kwanciyar ta, a tare Numfashinsu ke sauka kowa yana jin bugun zuciyar ɗan uwansa, turo baki Sarah tayi ba tare da tace komai ba kamar daga taji yace "Ni ko?" Kamar jira take ta kwaɓe fuska a hankali tace "Ina yini?" Shiru yyi mata ta ƙara Turo baki tace "Ina yini?" Kamar ba zai Mgna sai kuma yace "Bn sani ba" tace "Kamarya" Calmy Abeed yana rufe idanunsa yace "you never greeted me" shiru ita dai tasan tana gaishesa ba kullum ba, jin tayi shiru yasa a nutse yace "Ke Mala'ikun Allah" kwaɓe fuska tayi tace "da nayi me?" Yana sakin lallausan Murmushi yace "disobedience" da rashin fahimta tace "Disobedience kuma Uncle?" A hankali ya kwaikwayi muryarta yana langwaɓar da kansa yace "Ƴar kwaila..." Yana faɗin hakan ya kashe wayar yana sakin Murmushi tare da shafa sajansa... washegari tun 6 Abeed ya fita Danish ke driving nasa zuwa wani wajan sirri.... Sarah ta kasa kallon Yarima Yashim dake tsaye gabanta yana tsareta da Idanu, Murmushi yyi yace "Me kike son cewa?" Tai shiru dai fuskar nan nata babu walwala ta kuma kasa kallonsa, A hankali Yarima Yashim yace "I understood, u called me just to say goodbye shine kika kasa?" Tai shiru dai ta kuma ƙi kallonsa Zuciyarta na bugawa ita har ranta bata ƙaunar tafiyar bata kuma san nufin Uncle da ita ba, hannunta ya kama da sauri ta kallesa tace "Mene haka?" Yace "Like how? Mijinki ne ni fa ba wani ƙato ba" Sarah ta haɗa fuska tace "Nidai ka sakeni bana so" cikin damuwa yace "Ni kuma ina so, tafiya zaki wajan wata guda fa shine ba zaki bari ko hugging naki nayi ba" jikinta duk rawa yake tace "Allah ka sani bana so kuma..." Kafin ta Ƙarasa taji ya jawota gaba ɗaya zuwa jikinsa, with shock tace "Innalillahi, wlh bana so Allah zai saka min kaci Kani" a hankali shima Yarima Yashim yace "Tunda kike na taɓa hugging naki? Yanzu ina da iko a kanki ina da dama ki barni please" ya faɗa yana juyo da fuskarta and he's trying to kiss her... Yace "Just one kiss princess" kafin yyi abinda yake shirin yi daga baƙin ƙofa sunji ance "Heyyy" da sauri Sarah ta ƙwace kanta a tare suka kalli door way, Abeed ne tsaye ya Rungome hannunsa fuskarsa tayi jajur amma normly ba zaka gane yanayinsa ba, yana sanye da Silver crew neck t-shirt, sbd sanyin da ake yau da zubar dusar ƙanƙara yafi na kullum, sai wani Slim Fit Joggers daya sanya, tare da ɗura Autumn Winter High Neck a saman t.shirt ɗin, ya ɗura wata black Head Warp partial face, ƙafarsa sanye cikin white Xavier Woven Italian Leather (shoe) a hankali yake murza Anchor Leather Luxury Bracelet dake maƙale a hannunsa sai ka ɗauka Balarabe ne, musamman yadda sumar kansa tai kwace a wuyansa da wajan kunnansa, Yarima Yashim kallo ɗaya yyi masa ya ɗauke kai shi kam Abeed ko inuwar Yarima Yashim bai kalla ba, Yaa Yashim yace

Please Login or Register in order to submit comment