Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

huta da azabar ka" tana faɗin hakan ta juya kan Zain tace "Huce mana, kai ma badan halinka ba jiya jiya ya shiga yyi min sata fa? Raguwar alkaki na tass ya sacesa" sai kuma ta fashe da kuka tace "Wlh ban taɓa tunanin Ziff ya Shahara a sata ba sai jiya, yanzu dan Allah me zan cewa Laure? Yadda na dinga bata daɗin alkakin nan da irin sigarin da aka saka masa, wlh sai ta ɗauka ƙarya nake ko tace ni talaka ce" babu dai wanda ya kulata, Zain dawo hannunsa riƙe da paper Naila ta amsa ta ware tass, Takardar ta bawa Yaya Rooma tace "Karanto muji" Yaya Rooma ta amsa tace "Ni Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas na saki matata Du'a Al'khasim Abubakar Wahab saki biyu ba tare da laifin komai ba" sai kwanan wata da rana, Ƙwace takardar Naila tayi tana bawa Zain tace "Raguwar guda ɗayan da aka barsa yana lilo a duniya na mene? Kai ma kaso iskanci wlh kai da zaka rubuta saki uku a jere rerass......Zain did not speak, cos He's speechless.. har yanzu yana riƙe da Divorce paper ɗin, Dr dake tsaye akan Du'a wacce take kwance akan gado hannunta maƙale da Drip, A hankali Dr ya gama dubata yace "Ta samu hawan jini, da bugawar jini a brain ɗinta, at anytime zata iya samun shanyewar ɓarin jiki" Amma dake zaune akan kujera tace "Subuhanallahi, Hawan jini?" Dr yace "E, idan ana kula da ita, babu wata damuwa a Zuciyarta komai zai daidai" Zain daya kejin komai ya fita akansa yace "In sha Allah, thank you" Dr yace "I have to go" yana faɗin hakan ya tattara kayansa, har lokacin Mai martaba dake tsaye baice komai ba, gently ya miƙe tsaye not looking at them, a taushashe yace "Follow me... Zain" Zain yabi bayan Abba har zuwa haɗaɗɗan sashin sa... Abba ya kalli Zain yace "Are you happy now? Everything that happens to her, kai ne sila" Zain dai yyi shiru Abba yace "Mene yasa Ubangiji ya samar da iyaye ga yaransu? Mene yasa Ubangiji ya samar da Babba kafin ƙarami? Mene yasa Ubangiji ya samar da Ayar Suratul Nisa'i 34 ayet?" Allah maɗaukakin sarki yana cewa;
"اَلرِّجَالُ قَوَّامُوۡنَ عَلَى النِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ اللّٰهُ بَعۡضَهُمۡ عَلٰى بَعۡضٍ وَّبِمَاۤ اَنۡفَقُوۡا مِنۡ اَمۡوَالِهِمۡ​ ؕ فَالصّٰلِحٰتُ قٰنِتٰتٌ حٰفِظٰتٌ لِّلۡغَيۡبِ بِمَا حَفِظَ اللّٰهُ​ ؕ وَالّٰتِىۡ تَخَافُوۡنَ نُشُوۡزَهُنَّ فَعِظُوۡهُنَّ وَاهۡجُرُوۡهُنَّ فِى الۡمَضَاجِعِ وَاضۡرِبُوۡهُنَّ​ ۚ فَاِنۡ اَطَعۡنَكُمۡ فَلَا تَبۡغُوۡا عَلَيۡهِنَّ سَبِيۡلًا​ ؕاِنَّ اللّٰهَ كَانَ عَلِيًّا كَبِيۡرًا‏"
Abba yaja numfashi yace "Mene yasa Ubangiji ya saka maza a gaba da mata? Mata suna da rauni, mu maza bama tsayawa musan mene raunin mace? Muna amfani da son zuciyar mune, Ubangiji ya samar da iyaye akan yaransu saboda sauke wani haƙƙi, da nace maka ka saki Sairah ba haka Kurum bane, i have a reason, babu dacewa a saki mace me ciki musamman kamar Sairah, daka nuna biyayya ga Maganata na tabbatar zakai mmkin abinda Ubangiji zai saka maka dashi, Ubangiji da kansa yana tsananin jin Kunyar matar da harta mutu bata taɓa haihuwa ba, mene yasa zaka haɗawa Du'a zafi biyu? Mene yasa kake nuna bambanci a fili?" A hankali Zain yace "Abba ciki ne fa da Sairah" Clamly Abba yace "Then? Kasan darajar da mace take da ita yafi na Namiji a wajan Allah? Mace al'ada take sai tayi ciwo, mace ta ɗauki ciki tsayin wata tara kana ta haife ta kuma raina, mata iyaye ne, jigo ne, a yanzu idan mugun hali Du'a ta shiga zai iya shafar wasu jama'ar, A man can find peace for himself, mace ƙashin haƙarƙari ce, Sairah Allah ya ƙaddara ko ba'a wajanka ba sai ta samu ciki kuma sai an saketa, bamu san mene Ubangiji ya ɓoye ba, no one knows what tomorrow will bring,Go and think, when the time comes you will understand everything" kan Zain a ƙasa yace "Thank you, Allah ya ƙara girma Abba" yana faɗin hakan ya miƙe tare da yin waje... That night Zain couldn't sleep, he was thinking of finding a way out, what would he choose among his wives?.. Du'a or Sairah? He doesn't think he can break up with Sairah, and he feels sorry for Du'a, gashi gaba ɗaya number Abeed baya shiga... Washegari da safe Zain ya fito daga cikin part ɗin sa sanye da white kaftan masu kyau fuskarsa ta ɗan kumbura sbd damuwa da kuma daɗewa da yyi yana istihara tare da neman zaɓin Ubangiji gashi har yanzu bai ji komai game da haka ba, walking slowly ya nufi bedroom ɗin da Du'a ke ciki a hankali ya tura handle ɗin ƙofar ya shiga, tana zaune Idanunta rufe hannunta dafe da kanta, idanunsa ya ware a kanta sosai, cikin nutsuwa yace "Du'a" da sauri ta ɗaga kanta She never thought she would see him this time, idanunta daya cika da hawaye ta shiga binsa da kallo dashi, da sauri kuma ta nufi wajansa tana zuwa ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙamesa ta saka wani irin raunataccen kuka tace "I love You with all my heart, dan Allah kada ka barni Wlh zan mutu, in sha Allah nima zan samu ciki na haihu kaji tausayi na, i can't life without you,dan Allah." Da sauri kuma ta sakesa tare da zubewa wajan ƙafafuwan sa, ta riƙe legs ɗinsa tace "Zanta addu'a Allah ya bani ciki Nima, zan faɗawa Mamana da Abba su tayi ni da addu'a, Wlh na maka Al'ƙawarin duk abinda Sairah ta haifa zan riƙesa da amana, Wlh idan ka sakeni mutuwa zan dan Allah kace baka sakeni ba" idanunta ne suka fara wani irin fari kamar zata sume da sauri Zain ya ɗago ta, gaba ɗaya tayi jikinsa tare da ɗura kanta a shoulder ɗinsa, Sosai Zain yaji zazzaɓi a jikinta gaba ɗaya jikinta ya saki, a hankali yace "Stop cry, ina tare dake" ya faɗi hakan yana patting bayanta just to calm her down, shiru tayi can ya janye ta daga jikinsa tare da kama hannunta, a saman bed ya kwantar da ita tare da rufe mata jiki da duvet, juyawa yyi zai fita ta riƙe hannunsa tace "Please kada ka barni" durƙosawa yyi a hankali yyi mata forehead kiss yace "It's okay, sleep" ta rufe idanunta a hankali yabar ɗakin.. Har aka kira Asr prayer number Abeed data Daddy Salman a kashe suke, Zain da Naila da kuma Amma suna zaune a Parlo Du'a ta fito, She looks so learn and waek, Da sauri Naila ta miƙe tsaye idanunta ƙurr akan Du'a Kallonta kawai take Without blinking, sai kuma can jikin Naila ya fara shaking idanunta yyi jajur, ganin haka yasa Du'a ta tsaya domin bata taɓa ganin Naila cikin wannan yanayin ba, Amma ta miƙe tsaye tana kallon Zain tace faɗin "Take Naila to her side" Ajjiye spoon ɗin hannunsa yyi daman ba wani abinci yake ciba sosai, kafin ya Ƙarasa wajan Naila, Naila tayi wani kalar ihu ta nufi kan Du'a tana faɗin "ƙarya kuke, wallahi baku isa ba ɗiyar mu za'aiwa haka? Ko tsoran Allah ba kuyi? Wlh sai naga bayanku baku isa ku cutar da ita ba" Naila said that while shouting, it seems that she is not in her senses, Amma tace "Subuhanallahi yau kuma" Zain ƙoƙarin riƙe Naila yake kafin ya Ƙarasa kuma ta zube a wajan bacci ya ɗauke ta, Ita dai Du'a ta kasa motsawa sbd tashin hankali ita kanta ba ƙwari ne da ita ba, Zain ya kama Naila zuwa duguwar kujera tare da kwantar da ita, Amma kuma tace "Koma ciki, za'a kawo maki lunch, idan Naila na nan ki daina fitowa" Juyawa Du'a tayi zuwa cikin bedroom ɗin ta, Amma kuma was speechless na tambayar da Zain ke mata, cikin Mmki Zain yace "Damar har yanzu akwai aljanu jikin Naila?" Clamly Amma tace "Ya shige wai" girgiza kai kawai yyi, ya nufi part ɗin Abba hannunsa riƙe da paper, a zaune ya samesa saman Ladduma mai kyau ga kayan lambu cike a gabansa, Abba ya kalli Zain kafin yace "Allhmd" Zain bai faɗawa Abba abinda ya faru ba, kansa a ƙasa ya miƙa wa Abba paper, Abba ya amsa tare da ware paper a hankali ya saki Murmushi yace "Allah yyi maka albarka" Zain yace "Amin Abba" shiru duk sukai, Abba dai ya kasa hqr yace "Warin naka fa?" Zain yace "Har yanzu wayoyinsu a kashe" Abba ya jinjina kai yace "Ikon Allah, Allah ya shige musu gaba" Zain yace "Amin" kana ya tashi ya fita.... Zain na zaune idanunsa rufe zuciyarsa na bugawa kallo ɗaya zakai masa kasan ko baccin kirki ba yayi, idanunsa ya buɗe jin ance "Hello" Junaid ya gani tsaye hakan yasa ya saki Murmushi kamar babu komai a ransa yace "Wlcm" Junaid ya nemi waje ya zauna idanunsa ya buɗe sosai kafin yace "Sai kai ɗaya?" Zain yace "Amma da Yaya Rooma na ciki, Du'a ma hk" Junaid ya shafa kansa yace "Ok, Raudah, Beeba,Sairah, Sarah?" Kallonsa kawai Zain yay kafin yace "Raudah da Beeba nan, Twins sunyi tafiya" wani iri Junaid yaji sai kuma ya ɗanyi Murmushi yace "Ok, nayi busy 2days, shiyasa ban san basa nan ba, ashe nisa sukai har haka" Zain yace "Ai fa" Kafin Junaid yyi magana Wayarsa ta fara ringing, da sauri jikinsa har rawa yake wajan picking call ɗin, domin ringing ɗin ya bayyana mai kirar, ajjiyar zuciya Zain ya sauke yace "I am always in your thoughts, Biyuni,I couldn't calm down, your phone is always off, Tell me what's wrong? Kun kama Sarki Mabus ne, da kuma matar dake taimaka masa?" Daga can Jamani cikin wani haɗaɗɗan office na hukumar fikira na ƙasar, Abeed ne zaune daga shi sai farar singlet daga left hannunsa farin bandeji ne gaba ɗaya an naɗe masa hannunsa zuwa shoulder ɗinsa da bandejin, ga jini har time ɗin maƙale jikin bandejin, numfashi ya sauke yana lumshe fararen idanunsa a hankali yace "How are you?" Zain yyi shiru sai kuma yace "Are You alright?" Abeed ya ware idanunsa ya daɗe kafin ya buɗe baki yace "Uhm" Zain da hankalinsa bai kwanta ba yace "Baka ƙarya, ka tabbatar lafiya kke?" Kamar Abeed ba zai magana ba sai kuma yace "Sure" Zain ya jinjina kai yace "Ya aikin? I mean is everything okay? Ina Daddy" Clamly Abeed yace "In sha Allah, Amma, Abba, Naila?" Zan yace "They're all fine, when zaka dawo?" Abeed ya kalli Daddy Salman dake shigowa cikin baƙaƙen suit masu kyau, idanunsa ya ɗauke yace "Do me a favor" Zain ya kalli Junaid wanda har yanzu yake zaune kafin a hankali ya ƙara rage Muryar wayar yace "Ok, All ears" Abeed ya cije bakinsa yace "Today, I feel relieved I mean easy work" shiru yyi yana sauke numfashi kafin yace "I called my wife's phone was off, I knew she was angry, no phone calls, no messages for a month, kaje Zazzau Just to check her, madadi na.. I don't know when we will be back, and from today I won't be able to call" kafin Zain yyi magana yaji wayar Abeed ta katse, wayar yabi da kallo ba tare da yace komai ba, Junaid yace "Hope he's okay?" Zain yyi Murmushi yace "Eh, yana ma wajan matarsa ashe" Junaid bai sake magana ba, Zain ya tashi ya nufi part ɗin Amma a ransa yana jin something fishy.... Gently Abeed ya zame wayar daga kunnansa, sam bai damu da halin da yake ciki ba, matarsa kawai yake son gani da kuma cikin jikinta, Daddy Salman ya kalli Abeed yace "I hope you didn't tell him about your shooting" Abeed ya jinjina kansa, Daddy Salman yace "Bana son kowa daga family yaji cewa harbinka akai, U did a great job" Abeed dai yyi shiru, bai taɓa sanin rashin imanin Sarki Mabus yakai haka ba sai yanzu, he was shock na abinda ya faru, ya kuma ji cewa koda zai mutu sai ya kama Sarki Mabus, tashi yyi a hankali ya nufi wata ƙofa yana shiga ya kwanta saman bed idanunsa buɗe yana, ya daɗe rabon da yyi bacci mai daɗi baya ji kuma zai iya indai baiji Sarah kusa dashi ba... Ranar friday bayan sakkowa daga masjid Zain ya nufi Main Parlo na gidan cikin wata farar shadda ɗinkin jumper da babbar riga, walking slowly ya Ƙarasa saman Kujera ya zauna, tunda ya shigo Amma take binsa da kallo kamar bata taɓa ganinsa ba, yanayin kallon da take masa ya sanya ya miƙe ya koma kusa da ita yana sakin Murmushi tare da ɗura kansa a cinyarta yace "Mom" bata ce masa komai ba da Idanu kawai take binsa, a hankali yace "Zani Katsina" tace "Allah ya tsare" Murmushi yyi yace "Amin, zanyi missing naki" ta dai kallesa ba tace komai ba, tashi yyi daga jikinta kafin yyi magana Naila ta shigo hannunta riƙe da wata jarka, tana zuwa tace "Ina Wuwaa take kowa? Maza maza a kiramin Ita ojent" Zain yace "Ina yini Naila?" Naila ta runste idanunta tace "Naji jaraba? Cewa akai bansan da gaisuwar bane? Kaga a yadda nake jina banƙi na yiwa kowa rashin kirki ba, babu abinda ya daman wlh, jama'a kamar basu da aikinyi sai gaisuwa? A can fa leges ba ruwan kowa da kowa idan ma gaisuwa ne, sai dai a bugi hannu da ƙafa ace Shaloo, to nidai a tsahirta min" shiru tayi sai kuma tace "To, ba dai laifi yau kayi kyau fa, kamar sabon ango Nidai tunda aka haifeka baka taɓa kyau irin na yau ba" ta faɗa tana cire zoben hannunta tace "Maza maƙala wannan a hannunka maganin baki, Shidai Shalale a rayuwa babu wani bakin gantalalle daya isa ya kamasa Wlh" Zain ya amshi zoben ya saka yace "To Ngd" yana faɗin hakan ya miƙe ya nufi
part ɗin Du'a, tana kwance sanye da duguwar riga ƙarasa shiga yyi ya zauna gefen bed ɗin, fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "Lafiya?" Juyawa tayi suka haɗa Idanu tace "Kawai gabana ke faɗuwa, ban san dalili ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai, yana mata Murmushi yace "kuma baki iya addu'a ba? Look at you" ya faɗa yana jan hancinta, kafin ya miƙe yace "Naila na kiranki" yana ƙoƙarin fita yaji ta rungomesa ta baya tare kwantar da kanta a bayansa ta shafa ƙirjinsa, rufe idanu Zain yyi domin babu abinda yaji game da abinda Du'a take masa, gaba ɗaya he's not in the mood, babu feelings a tattare dashi game da ita, bashi da zaɓi babu yadda zai, yana daurewa ne baya nuna damuwarsa sbd Abba, jawota yyi gabansa yana kallonta kamar yadda take kallonsa, a hankali yace "What?" Girgiza masa kai tayi a hankali ta ɗura bakinta saman nasa, She was kissing his lips in a loving way, since they were married she never kissed him like that, fuskarta ya riƙe sam bai hanata abinda take ba, sai ta gaji ta zame bakinta tare da hugging nasa, sun jima a haka kafin ya zameta daga jikinsa yace "muje" gaba yyi tabi bayansa, Naila na ganinta tace "A to, da har zanbi sahu ai, babu komai dai yanzu a tsakaninku mene kuma na ƙulewa ɗaki banda lalacewa?" Du'a ta kalli Zain yyi mata alama da tayi shiru, Naila ta miƙa mata jarkar tace "shanye tas kiban" Du'a tace "Mene wannan Naila?" Naila tace "Bani idan ba zaki sha ba, wlh ko Mai rawani bai isa na bashi amsar abinda ban niyya ba, balle ke da babu dangin iya balle na baba? To wace kema? Kawai na hana kaina zaune da tsaye sbd na damu da al'amarin ki" Du'a ta buɗe jakar tayi Bisimillah tasha, sai da ta shanye tas, Naila ta amsa tace "To Allah babu alkairi" Amma tace "Tun yanzu?" Naila tace "A'a, abubuwan da nake gani cikin gidan nan sun fara fin ƙarfina, idan nace zama zanyi sai na haɗa fitina, babu ruwana da raba zumuncin Allah" tana faɗin haka tayi gaba abinta, Beeba data fito daga cikin bedroom tace "Amma bari na leƙa na gaida Ummi" Amma tace "Ok" Beeba ta nufi sashin Ummi tana addu'ar Allah yasa ta samu Junaid can..... Sarah ce zaune cikinta ya fito sosai ta ƙara girma da faɗi sosai, ƙafarta ya fara kumbura, kanta a ƙasa Zain yace "Kiyi masa addu'a, but Duk inda yake hankalinsa na kanki ai, kuma sun kusa dawowa ai" shiru tayi masa, ya miƙe tsaye ya nufi waje, Mrs Zain dake tsaye bakin ƙofa tayi saurin juyawa, daman ta tsaya ne taji ko zai tambayeta, sai gashi kuma bai tambayeta ba, kafin ta Ƙarasa guduwa yace "SAIRAH" tsayawa tayi har ya Ƙarasa inda take, ba tare daya taɓa ta ba yace "How are you?" Tai masa shiru yace "Talk to me, Ya kike keda Baby?" A hankali muryarta na rawa tace "Not good" sai kuma ta nufesa tana zuwa ta faɗa jikinsa duk da cikin dake jikinta,kuka ta sakar masa tace "No phone call's, no messages?" Da sauri ya zameta daga jikinsa yana riƙe hannunta a hankali yace "Sorry, kina raina ba gashi yanzu nazo ba? Aiki yyi min yawa ne" ta jinjina kai tace "Ina yini?" Ta faɗi hakan tana ƙoƙarin sake kwanciya jikinsa, yana juyawa yace "Allhmd,bari na amsa kira I'll be back" yana faɗin hakan ya bar wajan idanunsa na zubar da hawaye...


Zain Abeed isn't free contact to subscribe 08119237616

Stop reading Zain Abeed, if your heart won't take it😌
Ra'ayi na faɗa🤞🏽******page73****If you know you will complain, or abuse, or bad language, or I don't know what I'm doing.... U better Stop reading My book... ZAIN ABEED.. Ban taɓa tsara labari na sauya ba, yana da kyau ku daina karatu san daɗi ko farin ciki... Read a book because of the knowledge in it, or the preaching and warning and the lesson of life in the book, Gaba ɗaya muna rayuwa ne amma babu wanda yasan mene gobensa zata haifar, kana tsarawa kanka rayuwa amma Ubangiji ya gama tsara maka yadda rayuwarka zata kasance.... Ni Na'ima Sulaiman sarauta nace Whoever feels that her heart cannot accept what the book contains, ta daina karanta Zain Abeed, ta daina karanta Zain Abeed.. Ya kamata for now kusan ƙarfi da kuma girman ƙaddara, cikin imanin mutum shine yadda da ƙaddara... Faáman ƙaddaral Lááhu haƙƙa ƙadrihi....*






The weather was very cold that night, sbd yayyafin da ake na shigowar farkon damuna, sarah ce zaune cike fararen nightwear na pyjamas, ta miƙar da ƙafarta saman table, hannunta riƙe da waya trying to call abeed's details, amma baya going... Sarah was forced sairah to eat some food, although she was not in the mood, she ate little out of it, ganin kamar Mrs Zain bata cikin nutsuwar ta yasa a hankali tace "sairah, i need to ask you some questions,may i?" a hankali Mrs Zain da ƙirƙiri murmushi tace "sure" Sarah tace "akwai abinda Zain yyi maki ne?" Mrs Zain tace "pardon? abu like how?" Sarah tace "don't pretend, i'm your sister babu wanda ya kaini sanin wacece ke, mood ɗinki ya sauya idanunki yyi jaa kamar kinyi kuka what's happening?" Sarah ta faɗa tana ɓoye nata damuwar, Mrs Zain tace "no, ba komai fa" she said the last words playing with her fingers turning away, Sarah ta girgiza kai tayi kamar zata tashi amma ƙafarta yyi mata nauyi tana daga zaunan tace "idan baki sharing feelings ɗinki dani ba dawa zaki? Daddy? grandpa? grandma? or Yaa Yashim?, no body a cikin su kin san rabon da nayi waya da uncle? ko text message? i can't remember.. why ke gashi Zain yazo har wajanki mai makon kiyi farin ciki sai baƙin ciki? shine fa yake cemin na kwantar da hankali na" Sarah ta faɗa cikin damuwa, Mrs Zain tace "i don't know what is happening to me, i feel scared,he doesn't want me to touch him, he doesn't want to be close to each other" sai kuma ta fashe da kuka tace "ko mgnar kirki bai min, he changed me" Sarah tace "akan haka kike damuwa? kin san Du'a yake son saki, Abba yace shi kuma ke za'a saka, ina tunanin kece ya kamata ki kwantar masa da hankali, duk sauyawar da yyi a dalilin ki ne... you're d reason behind anything" Mrs Zain tai shiru tana jin kamar Sarah ta faɗi gsky, miƙewa tsaye tayi tace "bari naje na duba sa, zan kwanta bedroom ɗin Grandma, bye take care of yourself" Sarah tana sauke numfashi tace "same.. night" bayan Sairah ta fita Sarah ta ƙara kiran number abeed baya tafiya, wani irin kewa da ƙaunar ganinsa take, sometimes ji take kamar tana cikin jikinsa ga cikinta daya fara motsawa sosai, duk scanning daya dace an musu, gaba ɗaya cikinta wata biyar zuwa shida ne amma zaka ɗauka yaje irin 8mnts ɗin nan, fruits data saba sha duk dare ta fara sha, tasan cikin dare ba zata iya tashi ba, tana cikin shan apple aka turo ƙofar bedroom ɗin ɗaga kanta tayi suka haɗa idanu da fulani Bilkisu, murmushi tayi tace "sannu da hutawa" ƙasa Sarah tayi da kanta duk da cewa granny ce, amma tana jin tsananin kunyarta sosai, zama Fulani Bilkisu tayi hannunta riƙe da magani na masu ciki ta ɓalla ta bata, kwaɓe fuska Sarah tayi tace "please granny" Fulani Bilkisu ta harareta tace "c'mon, da wannan ƙaton cikin naki za'a barki ba magani?" nan da nan Sarah ta marairaice tace "wlh ba ƙato bane, nidai bana so duk ya daman" Fulani Bilkisu tace "iyeee, bari mai gidanki ya dawo u most explain to him." Sarah ta fara share hawaye jin Fulani Bilkisu tace mai gidanta, gaba ɗaya haushinsa ma take ji ya tafi ya barta, babu ruwansa, da ƙyar ta amshi maganin tasha, Fulani Bilkisu was just staring at her ganin yadda foots ɗinta suka kumbura sosai, cikin tausayawa tace "u have to rest... kiyi bacci sosai" Sarah dai kanta a ƙasa bata jin zata iya tashi, miƙewa Fulani Bilkisu tayi tace "good night, gobe za'a kawo lefen ki" tana faɗin hakan ta fita tare da ja mata ƙofar ɗakin, Sarah duk yadda taso tashi kasawa tayi so take ta kwanta saman bed amma gaba ɗaya ƙafarta yyi mata nauyi sosai, tana na wajan saman duguwar kujera bacci ya ɗauke ta....... at two o'clock in the night, abeed's plane landed, kai tsaye cikin masarautar ya nufa, Yaa Yashim dake zaune saman wata farar kujera daga wajan wani corridor ya miƙe tsaye ganin kamar Shadow yake gani na mutum, a hankali ya nufi wajan Abeed na tsaye hannunsa zube cikin aljihu ko waya babu a tare dashi, yana sanye cikin sleeveless jersey tank top, wacce bata kamasa ba sbd ciwon jikinsa, sai camouflage-print cargo trousers, ba'a iya ganin fuskarsa sbd murɗaɗɗan gashin kansa wanda ya sakko ya rufe duk gefen fuskarsa, sai fararen idanunsa da kuma red lip's ɗinsa da ake iya gani, duk da cewa yyi jinya amma ya ƙara ƙiba sosai da haske fuskarsa a kame kamar kullum, buri uku yake dashi a yanzu ya zauna da Sarah zama na har abada, ya taya biyuninsa samun cikon nasa muradin, ɗaya burin nasa shine kawo ƙarshen Sarki Mabus, koda zai zama silar rasa ransa, Yaa Yashim ya ƙaraso wajan Abeed fuskarsa sake yace "Assalamu alaika" idanun Abeed akan wani wajan kamar ba zai mgna ba sai kuma yace "how are you?" Yaa Yashim yace "i'm good" shiru duk sukai can kuma Yaa Yashim yace "the room that is in front of the other part, here you will find it" yana faɗin haka ya juya abinsa, bayan tafiyar Yaa Yashim da seconds 10 walking slowly Abeed ya nufi inda yace masa, tsaye yyi bakin ƙofar a hankali kuma ya kama handle ɗin ƙofar ya tura without making any sounds, yana shiga ya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, sbd idanunsa daya sauka akanta, kanta akan armchair, ƙafarta saman table hannunta kuma ta ɗura akan cikinta, ta kwaɓe fuska kana kallonta kasan baccin baya mata daɗi, gently ya nufi wajanta yana zuwa ya durƙusa daidai inda ƙafarta yake, wani so da ƙaunarta ya ƙara ninkuwa a zuciyarsa, ga wani tausayinta da yake ji, softness hands ɗinsa ya ɗura akan fingers ɗin ƙafarta, a hankali ya matsa sukai ƙara, farar

Please Login or Register in order to submit comment