Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinsa, jin na Numfashinsa na neman ɗaukewa ya sanya ya janye jikinsa da ƙyar, idanunsa yyi jajur almar ruwa ya shige su, bathrube ya saka jikinsa ganin da sauran lokaci kafin magrib, ya sanya ya fita zuwa bedroom, da ɗan sauri ya shiga sanya wasu jajayen ƙana nan kaya, wanda ake musu ado da zanan jiter, white ɗin p.cap ya ɗauka ya saka a saman sumar kansa wacce take zubar da ruwan, gaban p.cap ɗin an rubuta _“Star”_ (tauraro) yyi wani irin kyau, baka ganin komai sai jajayen laɓɓansa wanda suke jiƙe da ruwa, walking slowly yake tafiya fuskar nan babu walwala, ya nufi wata ƙofa dake cikin bedroom ɗin su, yana fita kuma ƙofar ya fitar dashi wani haɗaɗɗan part, tun a parlon farko zaka san shashen mawaƙi ne, domin photon jiter da ko'ina, ga pictures nasa birjik, sai wani ƙaton photon sa, wanda yake tsaye a bakin ruwa, da alama wajan beach ne, hannuna riƙe da jiater, yyi wani kalar cute smile tare da ɗaga hannayensa sama, da alama irin slow song ɗin nan yake rerawa aka ɗauke sa, a saman photon an saka _“Rock star”_ fita yyi daga parlon zuwa wani parlon, a nan kuma gaba awards ɗin daya samu ne da dukkan awarded ɗin da akai, har na best Singer 2021. Daga nan kuma ya shiga wani ɗakin Wow! Ashe studio ne, komai na waƙarsa a nan yake. Zama yyi kan kujera, bayan ya saita abar ɗaukan murya cikin wata zazzaƙar murya mai tsananin daɗi da amsa kowa yace.

_“WHY I'M ENAMORED..”_
shiru yyi wanda da alama wannan sunan shine tittle ɗin waƙar kafin slowly ya lumshe idanunsa yana sauke ajjiyar zuciya ya fara jero baitin waƙar kamar haka;

_Why I'm enamored at a glance,_
_Eyes failed to picture a dimpled face._

_If not for the daunting of the blowing wind,_
_I would domicile you on my pterygoid._

_I saw my blood on your cheek,_
_Your eyes failed to contend._

_I'm jealous of cup, debar it,_
_Never allow it to touch your lips._

_My heart asked for_ _clemency,_
_How aggrieved will i be after you set forth?._

_Which kind of look is attached to your eyes,_
_That is neither tiring nor satisfying._

_I sent my sight to repel your picture,_
_But you were absconded so it turned desolated._

_I beseech you not to castigate,_
_Because my love is a living proof of your life._

_Whenever I smell the roses of life,_
_Everything ceases except your cravenness._

_Don't leave me unsympathetically,_
_Like my expression is not sounding to you._

_My heart sheds tears,_
_But you refuse to_ _embrace._

_You enclose my heart,_
_It is neither crook nor_ _forsaken_

Wani numfashi Abeed ya sauke, bayan kammala ƙana nan baitocin daya haɗa yanzu, sometimes sai ransa ya ɓaci wata ideas na waƙa yake zuwar masa, lumshe idanunsa yyi dan wlh bai ma san yaya akai yyi wannan luv song ɗin ba, shi dai ya samo kansa kawai dayi ne, gently ya miƙe tsaye ganin amma yi kiran sallah yanzu, cike da jarumta yake tafiya har zuwa asalin part ɗin su, yana zuwa yaga Zain ya fito daga toilet alamar alwala yyi, idanu suka haɗa shi dai Zain bai ce komai ba, domin kwana biyu baya gane kan Biyunin nasa, can ya nisa yace "Uhm, lokaci kayi alwala" kai kawai Abeed ya ɗaga ya nufi toilet ɗin kafin ya fito daga toilet ɗin Zain ya ɗauko masa wata Arabian jallabiya mai santsi da taushi irin tasu ta masu sarauta, fitowa yyi ya saka jallabiyar, nan da nan suka rikiɗe zuwa identical twins ɗin su, waje sukai nan suka samu Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas a tsaye cikin kayansa masu kyau shima zai shiga nan masjid ɗin wanda aka keɓe na masu sarautar, Abba ya ɗago kansa ya kalli Tagwayen nasa, ya jima yana kallonsu Zain na kallon Abba, Abeed kuma kansa a ƙasa hannunsa cikin Aljihu, ɗauke kai Abba yyi tare da yin gaba suka bisa a baya. Bayan an idar da sallah, Abba ya kalli Zain yace "Dadynku Waziri bai ji dɗi ba, ko laƙa ko gaida sa" Zain yace "To Abba" Abeed dai yana tsaye domin a yanzu ko yaya ya fara Mgn wani irin ciwo ya keji a ƙirjinsa, zuciyarsa sam bbu daɗi how long zai kasance cikin haka ne? Sallama Zain yyi cikin parlon Ummi ce a parlon ita da Riya suna shira, Riya ta miƙe da sauri domin batai tunanin ganin Abeed ɗin ba, tasha wahala na rashin kullum sai tayi yunƙurin zuwa Ummi ta hanata, fuskarta ɗauke da Murmushi tace "Wlcm" Zain ya nemi waje ya zauna, Abeed kuma ya ɗan zauna a Arms chair, Ummi ta kalli Zain tace "Allahamdulillah, ya Amma?" Zain yace "she's fine" sai a lokacin Abeed ya ɗan shafi kansa kafin Calmy yace "Daddy fa?" Kallonsa Ummi tayi tace "he's in the bedroom" Miƙewa yyi ya nufi part ɗin Daddy Waziri, da sauri Riya ta miƙe tabi bayan Abeed, Zain dai na zaune suna shira da Ummi. Gently Abeed ya tura ƙofar parlon Daddy Waziri bakin ɗauke da sallama a nutse, Waziri ne zaune gabansa kuma Junaid suna mgn a hankali, Shima Junaid ɗin wata blue black ɗin jallabiya ne jikinsa mai ƙaramin hannu, yana zaune idanunsa cikin glass kamar ko yaushe yana duba drip ɗin daya sawa mahaifin nasa, Abeed ya zauna gaban Waziri Murya kamar kullum a kamalance yace "Daddy ya jiki?" Waziri yace "Allahamdulillah, shalelen Naila ne ko Zain?" Junaid ya juya ka ɗan, yadda yaga Abeed ya ɗan haɗe fuska kaɗan da suka haɗa ido yasan cewa ba Zain bane, infact yyi musu mugun sani amma duk da hakan wani time ɗin sai a hankali baya ganewa, Abeed ya shafa kansa yace "Nine Daddy, Abba yace baka ji daɗi ba" Waziri yace "Wlh ciwon kai da zazzaɓi ɗazo sai ciwon ciki, kamar ba zanyi rai ba" Abeed ya numfasa yace "Oops, Allah yasa kaffara ne" Daddy yace "Amin" Riya ce ta shigo sbd neman suna kusa da Abeed ta zauna har tana ɗan ɗura hannunta akan nasa tace "Daman Abeed yace zaizo nine na manta ban faɗa ba" Junaid ya cillawa Riya harara sam yarinya ba aji,ko a gidan ubanta yace mata zaizo Ohhu, mutumin da ko call nata baya picking tayaya zai kirata, Kafin kowa yyi mgn Zain ya shigo fuska ɗauke da Murmushi sai a lokacin Junaid ya miƙe yana sakin nasa Murmushin yace "late comer" Zain yace "Na tsaya wajan Ummi shi Abeed baya Shira shiyasa ya rigani zuwa" Junaid yace "Ok, sai kun fito" Zain yace "Dinner fa?" Junaid yace "Zanzo" yana faɗin hakan ya fita, Zain ya gaida Waziri, Daddy Waziri dai Riya da Abeed yake kallo, inama Abeed zai so ƴarsa, yana da tabbaci za tafi ko wacce mace Sa'a, Abeed nagartaccen mutum ne, sanin ya kamata bashi da sabgar mata saɓanin wasu mazan musamman yadda zamani ya lalace, amma bashi da iko da hakan abinda Allah yyi shine daidai. Abeed ya miƙe fuska ɗan sake yace "Allah ya ƙara sauƙi" Riya ta miƙe tace "Tafiya zakai Baby?" Kallonta yyi ba yabo ba fallasa yace "Yap" tace "Na raka ka?" Kai ya ɗaga, cikin farin ciki Riya ta kama hannun Abeed sukai waje, da idanu Zain da Waziri suka bisu abin ya zame masu sabo ga Abeed. Babu kowa a Parlo har suka fita waje, zuciyar Abeed har wani ta fasa yake, suna zuwa waje ya zame hannunsa daga nata yana harɗewa a ƙirjinsa kallo up and down yyi mata, shifa wlh duk abinda ake buƙata jikin mace bai gansa jikin Riya ba, Calmy yace "Yaushe zaki hankali? Ke dole sai kin lalata ni? Riya wlh ba zan iya aurenki ba, ki rubuta ki ajjiye" Riya tai Murmushi mai ciwo tace "Ni kuma idan har baka aure ni ba, ka tabbatar ni da kai zamu zama lalatatto yaran da Ubangiji ya ƙaddara zamu samu a aure sai mu same su a titi" Abeed yace "Au ke nan har mafarkin zamu samu yara kike? Ji hauka dani kuma? Mtwss" ya faɗa yana gaba abinsa, binsa tayi da idanu hawaye na zubo mata. Babu kowa a parlon a haka Abeed ya shiga, har ya nufi part ɗin su, sai ya juya zuwa part ɗin Sara, shiru parlon har bedroom ɗin ga kan bed nan tayi kaca kaca dashi, taci cake duk ta zubar ga wani ƙarin Teddy daya gani saman mirror juyawa yyi yaga tufin da yyi mata sam ta daina sha, ƙugo ya riƙe yace "Shekarar Yarinyar nan nawa ne?" Ya faɗa yana mmkin yadda gaba ɗaya bedroom ɗin nata ya zama kamar na mahaukata, har zai fita ya jiyo sautin Dryarta a bathroom, kai tsaye kuma ya nufi toilet ɗin a hankali tare da ɗura hannunsa saman handle ya murɗa tare da turawa ciki, tsaye ya ganta gaban shower ruwa na sauka a jikinta, sai tsalle take tana rawa tana sanye cikin wasu pech ɗin nightwear jikinta, gaba ɗaya duguwar rigar bata shige gwiwar ta ba, fararan cinyoyinta duk a waje, sai wani bathroom slippers a farar ƙafarta, gashin kanta duk ya manne jikinta banda dry babu abinda Sara take ruwan kuma sosai yake sauka jikinta, harɗe hannayensa kawai Abeed yyi ya zuba mata fararan idanunsa, ya jima a haka ganin yarinyar ba saiti ne da ita ba ruwan zai iya yi mata illa ya sanya a hankali ya shiga cikin bathroom ɗin tare da rufe ƙofar without making any sounds ya nufi inda take fuska babu walwala...



*ZAIN ABEED* na kuɗi ne, kiji tsoran Allah kada kifitar min dashi kada ki karanta ba tare da kin biya ba, akwai free book kaca kaca a gari suka gantali.
It's ₦500 👌🏾special grp double posting in the day 1k via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank Evidence...08119237616.



Sarautar marubuta✍🏾[08-15 08:44] +234 703 831 1110: *13 Nimcyluv*
Ya kusa zuwa dab da ita, yaja ya tsaya yana noticing ɗinta, tsaki yaja a ransa yace "Gayyar aljanu" kafin a fili cikin tsawa yace "Keee" da sauri ta tsaya da rawar da take a cikin ruwan, tare da juyawa suka haɗa ido da Abeed dake tsaye, jiki na rawa ta sukuyar da kanta ƙasa tare da ƙanƙame jikinta saboda sanyin daya fara ratsa mata kofofin jikinta, frm head to toe yake ƙarewa jikin Sara kallo, kafin gently ya juya Murya can ƙasa yace "fito" bayansa ta biyo ta ƙarewa kwatacciyar sumar kansa idanu, wacce ta matuƙar ɗauke hankalinta, fitowa tayi daga cikin bathroom ɗin ta samesa zaune kan mirror ya harɗe hannayensa a ƙirji kamar yadda ya zame masa jiki, cikin jin haushin yadda take abu kamar mahaukaciya yaja tsaki yace "come here" maƙale masa kafaɗa tayi tana turo baki gaba, ƙaramin bakin Sara Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas yabi da kallo, kafin ya ɗauke idanunsa ya mayar zuwa kan bed ɗin yace "Zo nan" Shiru tayi masa domin bata mance bulalar daya zirara mata ba, cikin wata tsawa tare da harguwa wacce ta sanya Sara saurin ƙarasa wa wajansa tare da ƙanƙame jikinta domin sallah bata ɗauka shine yyi tsaiwar ba, ganinta kusa dashi ya sanya ya ɗaga hannunsa tare da sakar mata ranƙwashi yace "Ubanwa yyi haka da ɗakin nan?" Idanunta ta ɗaga wanda ya cika da hawaye ta shiga kallonsa, domin sosai taji zafin ranƙwashin haɗe rai yyi yace "matsa sai wari kike" gefe taja ta tsaya yace "Maza na daina ganin kayan haukan nan akan bed ɗinki" jikinta na rawa ta motsa baki tace "ban iya ba" ya ware fararen idanunsa wanda suke narkar da zuciyar mace ganin yadda yyi ya sanya Sara ware idanunta itama, haɗe fuska yyi yace "To Allah baki gyara ba sai na zaneki ki bari na dawo kiga" yana faɗin hakan ya miƙe tsaye cikin sauri tace "Zanyi" bai ƙara kallon inda take ba, yyi waje abinsa da idanu ta bisa tana murguɗa masa baki, tuni jikinsa ya basa baki da murguɗa masa, domin yaga sararta ke nan. Fita yyi zuwa part ɗin su yana ƙoƙarin shiga Zain yace "Ohh,kana ciki ke nan time ɗin Issha yyi" kai kawai ya ɗaga ya shige cikin part ɗin, yana zuwa ya faɗa saman bed yana sauke numfashi tare da dafe ƙirjinsa dake masa wani zafi, ga wani nauyi da ƙirjin yyi masa. Ya jima a haka kafin ya shiga toilet ya sake Alwala ya fita, yana fita Zain ya miƙe suka nufi masjid. Ummi ta kalli Riya sosai cike da takaici tace "Wlh ke dai haihuwar asara ce, ban taɓa sanin cewa baki da hankali ba sai yanzu, ace namiji guda ɗaya kin gagara jawo hankalin sa? Ki sami auren Abeed shine zai bamu damar samun abinda muke so, infact yafi Mai martaba kuɗi, kina nufin duk da haka zuba ido za mu yi ya auri wata? Get back to your right sense Riya! Ko mutuwa Mai martaba yyi Abeed shine zai zama sarki" Riya ta buɗe rinannun idanunta ta kalli mahaifiyarta tace "Sarki kuma Ummi? Zain ɗin fa?" Ummi ta watsa mata harara tace "Ke dallah can Shasha, Wlh kawai asarar kuɗin makaranta mukai duk iliminki da hawayewarki a banza, abinda baki sani ba Abeed shine ya fara shaƙar iskar duniya, hakan yana nufin shine gaba da Zain" Shiru Riya tayi kafin can tace "So what am I supposed to do now?" Ummi tace "First, calm down, dole ne duk yadda za'ai Abeed ya zama mijinki for now dai keep trying wajan jawo hankalinsa" Junaid dake tsaye bakin ƙofa ya ɗan jingina kaɗan yace "Uhm, is better ta nemi wanda ke sonta Ummi" Ummi tace "Ni bana haɗa sabga dakai, domin ka fifita uwar data haifeka akan Amma, nidai nasan Ni nayi dakwan cikinka na haifeka, amma duk wani magana da Za'ai na gidan su Zain baka ƙwauna" Riya tace "Ummi kuma.....," “Keeee Shut up wlh ko na ɗauke ki da mari stupid gal kawai" Junaid ya faɗa har yana zare glass ɗin idanunsa domin shima baya ɗaukan raini, Ummi tace "To ba sai dai kaci kanka ba, a doke dai ni ba zan doku ba, gsky ba zan fasa faɗa ba" Junaid yace "Ke tashi fita a nan" Riya na kumbura baki tabar parlon, Zama Junaid yyi tare da ƙasa da kansa, yana sauke numfashi can kuma ya ɗaga idanunsa ya kalli Ummi Calmy yace "Ummi mai Amma tai maki ne?" Ummi ta kallesa tace "Ban sani ba Abubakar" sunan babanta ke nan, Miƙewa yyi yace "Am sorry" ya Faɗi hakan yana yin waje abinsa zuciyarsa bbu daɗi sam, yadda mahaifiyarsa ke nuna tsana ga Amma for no reason, kai tsaye shashen Gidan Amma yyi kamar yadda yace a can zaiyi dinner... A Parlo ya samesu hadda Mai martaba amma babu Abeed wajan, Murmushi Abba yyi yace "Dr Junaid.." Junaid yace "Barka da tare Abba, Allah ya ƙara girma" jinjina kai Abba yyi, Amma tace "I was thinking ko baza kazo ba" Ya ɗan shafa kansa yace "Nazo yanzu" tace "Am glnd" Miƙewa tayi tsaye tace "the dinner is ready Olrdy.." Mai martaba yace "Bari na shiga ciki" tace "To, Mai martaba Allah ya ƙara sayin rai" Zain yace "Shall we..?" Junaid ya miƙe yana shafa kansa tare da juya idanunsa zuwa parlon kamar me neman wani abu, a haka suka ƙarasa dinning area, not too long da zaman su Abeddeen ya ƙaraso cikin parlon yana zabga ƙamshi, yana sanye da wando 3gauter sai Gymashark sports t.shirt sai wata farar bandaner a gaban sumar kansa, ƙamshin perfume duk ya cika wajan, bakinsa yana fidda ƙamshin Spraymintt mouth freshener. Zama yyi kan kujerar dake zagaye da dinning idanunsa a ɗan lumshe kafin ya kalli Amma yace "Ammaa.." ya kira sunanta a taushashe kallonsa tayi tace "Ya akai" Girgiza kai yyi ba tare da yace komai ba, yaja idanunsa ya rufe, Abinci Junaid ya fara ci ba tare daya kalli Abeed ba, kamar yadda shima Abeed ɗin bai kalli Junaid ba, kowa girman kai na cinsa. A hankali Sara ke ɗan leƙo kanta tana son fitowa waje amma tsoro ya hanata sbd bata son cin karo da Abeed balle ya ƙara dukanta, Junaid ya ɗan runtse idanunsa sbd zuciyarsa da yaji tana bugawa, spoon ɗin hannunsa ya ajjiye tare da daukan ruwa ya sha, gently ya buɗe idanunsa kai tsaye ganinsa ya sauka akan Sara, buɗe idanunsa yyi sosai, sai kuma ya ɗan janye ya kalli Abeed ganinsa yyi shima Sara yake kallo, idanu suka haɗa da Abeed da Junaid, miƙewa Abeed yyi ya koma Parlo tare da kwanciya kam 4seater ya miƙe ƙafafuwan sa, Zain ne ya kalli Sara data ƙaraso wajan yace "Sai yanzu Mamana?" Kai ta ɗaga tana ɗan washe bakinta yace "Zauna kici abinci" ya faɗa yana ja mata kujera, zama tayi tana ƙarewa abincin kallo, idanunta ya sauka akan farfesun naman rago wanda yaji kayan ƙamshi sai tiriri yake, Hannunta zata saka cikin kwanon Junaid dake kallon ta yace "Why not spoon?" Ya faɗa yana goge bakinsa da tissue, kallon Junaid tayi suka haɗa idanu sai kawai ta ɗauki spoon ɗin ta fara ci, Zain ya miƙe tsaye yace "Bari naje,ina da meeting gobe by 9 zan kwata bacci" Junaid yace "all the best" ya faɗa yana danna Wayarsa, ya ɗan jima a haka Sara kuma na cin Naman ta hankali kwance, slowly Junaid ya kalli Sara bayan ya rufe Wayarsa kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "What's your name?" Cikin siririyar muryarta tace "Saraa." Ya jinjina kai yace "Ok, can we be friends Saraa?" Ya faɗa yana miƙa hannunsa, dry tayi tace "Friends?" Ta faɗa tana ware idanunta kamar yadda taga Abeed nayi yace "Yap" shima ya faɗa yana ɗaga mata gira ɗaya tare da miƙa mata hannunsa, tana ƙoƙarin miƙa masa nata hannun Abeed ya ƙaraso wajan tare da zama saman kujera ba tare daya kalleta yace "jeki ɗauko min ruwa" ya faɗa yana jan basket ɗin fruit, tare da ɗaukan Apple bawai dan yana jin daɗin ta ba, ya shiga taunawa a hankali yana ɓata fuska, Junaid yyi Murmushi yace "How was your body, ance baka da lfy, U looks so learn" Abeed yace "Allhamdulillah" Sara ta ɗauki bottle water ta kawowa Abeed tana shirin zama yace "Jeki, idan na bar parlon kya dawo" ya faɗa ba tare daya kalleta ba, Sara tana tura baki gaba kamar zatai kuka tace "To" suka haɗa ido da Junaid shima ya ɗauke kai tare da Miƙewa yyi waje abinsa daman yyiwa Amma night tun ɗazo, ganin fitar Junaid yasa Abeed ya sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya a hankali ya juya kalli Sara dake tafiya yace "Saaa" juyawa tayi suna haɗa ido tayi ƙasa da kanta, yace "Zo nan" inda yake ta ƙarasa tana zuwa ya kama kunnanta yace "Ke how old are you?" Tayi masa shiru tuni hawaye ya far sauka idanunta, yace "Ba nace ki daina barin kai buɗe ba? Allah zan mammareki" ya faɗa yana murɗe kunnan tare da ranƙwashi ta, baki ta buɗe zata saki kuka yayi saurin rufe mata bakin yace "shittt" shiru tayi ta shiga jan ajjiyar zuciya, Abeed Apple ɗinsa yaci gaba daci sai da yaci guda huɗu ya sha ruwa, ya miƙe tsaye ganinta yyi tsaye da mmki ya ware idanunsa yace "Are You still crying?" Tayi shiru ya ɗago fuskarta da hannunsa hawaye ya gani kwance saman idanunta, a hankali ya share mata hawayen yace "Muje" gaba tayi yana binta a baya, time to time sai ta juya suna haɗa ido yake ware mata manyan idanunsa masu kaifi, har bedroom ɗin ta ya shiga ta gyara ba sosai ba, yace "kwanta" ta kwanta zama yyi a gefen bed ɗin domin meeting ne dashi a zoom, link ɗin meeting ɗin yabi na zoom ɗin ya saka code nan da nan jama'ar dake zoom ɗin suka bayyana, bai wani saka Camera ba kawai yabarta iya audio ya fara sauraran abinda ake cewa, sai wajan 1:30 aka gama meeting ɗin ya juya yaga tuni tayi bacci, ta ƙanƙame pillow gashi ya rufe mata fuska, durƙosawa yayi ya ɗauki ruwan addu'ar ya shafa mata a fuska zuwa tafin ƙafarta, kana yyi mata addu'a tare da ja mata duvet, a.c ya ƙaro ya fita daga cikin ɗakin a ransa yana jinjina yanayin da take ciki, he just help her daga matsalar aljanun da suke damunta, da kuma ganin ya jawo hankalinta zuwa ga addinin Musulunci. Da wannan tunanin shima ya shirya ya kwanta.
Washegari tun 8:30 Zain ya shirya cikin Suit ya ɗauki briefcase ya ɗauka, har zai tashi Abeed yace masa goodbye sai kuma kawai ya shige baya son takura masa. 11:00 duk suna kan dinning area dake weekend ne, daman duk weekend a gidan Abba ake breakfast, lunch dinner. Waziri, Ummi, Riya, Junaid da Uncle AY duk suna zaune sai Mai martaba da Amma da kuma Sara wacce take wani iri, ga duk sanda zata ɗaga ido sai sun haɗa ido da Junaid ko Riya, yanayin kallon kowa ya bambanta. Daga bakin kofa sukaji ance "Yaya kamar ana yaƙi sai kace an daina sarrafa shinkafa a duniya, tun fa kafin nazo ake ta shela zan zo ko ba kuji bane? Wlh fa sai da aka Sanarwa" Naila ta faɗa tana ƙarasa shigowa cikin parlon, Junaid yace "Wace ke da za'a sanar?" Naila tace "A'a aikai ba wani imani ne dakai ba, duk wanda zai saka wuƙa babu tsoran Allah ya yanka mutum ai Wlh abin tsoro ne, nan nan naga wani likita ya yanka cikin mutum babu kunya babu tsoran Allah" sai kuma ta fashe da kuka tace "Kai dai Ubanka ya cucemu, ya rasa wanne karatu zaka sai na likitoci? Yanzu fa lalle ace akwai ɗigon tausayi a zuciyarka ba ko Juwal?" Junaid yace "Daman, na ɗauka kin mutu ai?" Da sauri tace "A'a wlh da Uwarka kke gata nan a kusa dakai, daka gani baƙin halinta kwaso" Waziri yace "Junaid zaka bar wajan nan" shiru Junaid yayi, Naila tace "Daman fa ina zaune naji ana sanyawa Mai martaba albarka wai yana da hankali, nace nidai bawai rashin kirki ba, ba wani hankalinsa na gani tunda ƙiriƙiri ya saka baki a auren yaran nan yaƙi, to dai ba ance hannunka baya ruɓewa ka yarba da nace wani, amma dai wlh duk duniya da kuma Nijeriya sun shaida ban taɓa haihuwar banza ba, wankakkun yara nake haifa, shiyasa duniya ake ta shela tun safe ba yar yanzu wai na iya haihuwa" dry taso kama Junaid amma ya dake, wai ta iya haihuwa kamar wata akuya. Riya tace "Amma Abeed fa?" Tace "Yana part ɗin su" Tace "Bari naje" sauri Naila tace "A'a ke kuma awa? Babu dangin iya balle na baba dan Allah? Yarinyar nan kowa lafiya kike? Sai bushewa kike kamar wacce cutar yunwa ta kama? Muhammadur Rasulullah s.a.w nafa ɗauka Jakadiya Abar ce,kuji na faɗa maku to Allah ya tsare mana imaninmu" ta faɗa tana jan kujera. Mai martaba taba ya numfasa a hankali tare da cewa "Ina tinani this week ya dace a ɗaura Abeed da Riya aure, I'll talk to Zain naji wacce yake so, kai ma Junaid kafin ranar ka fito da matar aure" Naila tace "To, to! Yanzu na san na iya haihuwa da wlh na ɗauka ƙarya ƴan gidan rediyon suka shuka, yanzu kuma dan Allah nace mutum ne ke Wannan surutun ko kuma dai matar cikin sailola ce?" Amma tayi Murmushi tace "Mutum ne" Naila tace "To idan yana da hankali Allah ya tsine..." Da yamma Abeed na kwance saman kujera a parlonsu tunda ya samu Maganar aurensa da Riya zuciyarsa ta cunkushe,yaya zaiyi yanzu? Idanunsa ya rufe sosai zuciyarsa na bugawa yama rasa mafita baki ɗaya, a sanyaye ya miƙe tsaye tare da nufar Kofar main Parlo tun daga nesa yaji Mai martaba na cewa "Junaid yace bashi da wacce yake so i think zan haɗasa da wannan yarinyar Sara......


Zain Abeed isn't free, if you read for free🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️ it's 500 masu son double posting mrng and night 1k via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank evidence of payment 08119237616




Sarautar marubuta
[08-15 08:44] +234 703 831 1110: *14 Nimcyluv*
Abeed bai tsaya jin Abinda Mai martaba zai ƙarasa faɗa ba, ya juya a hankali ya nufi part ɗin da Sara ke ciki, kallo guda zakai masa ka fahimci how sad he's. Shi a gobe ma zai bar 9ja sai yaga yadda za'ai ya zauna da wata mace, macan ma wai Riya? Tura ƙofar parlon yyi

Please Login or Register in order to submit comment