Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zauna yana harɗe ƙafarsa kafin ya ɗauki Wayarsa ya shiga dannawa, Yarima Yashim ya kalli Sara yace "Bari naje we'll talk tomorrow in sha Allah" ya faɗa yana Miƙewa tsaye itama Miƙewa tayi a hankali sukai waje Abeed ya bisu da kallo baka gane yanayin da yake ciki, domin idan ransa ya ɓaci ko ƙala baya iya cewa komai, suna fita waje Yarima Yashim yace "Wannan Uncle ɗin naki bai iya mu'amala ba" ta dai yi shiru yace "ko sonki yake?" Ta wani waro idanu tace "Kai tab, ba aure tsakanin mu har abada ai, shi ɗin da yake jin kansa" Calmy Yarima Yashim yace "Uhm, Allah yasa don't betray me please Sara" kanta a ƙasa tace "In sha Allah" mota ya shiga tana tsaye yabar wajan yana ɗaga mata hannu, tsayawa tayi tana tunanin shiga amma tana tsoro da ƙyar dai ta shige ciki yana ɗaure fuskarta. a Parlo ta same su Anuty Zulfa Auta sai kuma Oga da kansa, kanta a ƙasa ta kalli Anuty Zulfa tace "Good night Mami" Mami tace "Tun yanzu?" Tana shigewa tace "Mami kai na ciwo, gobe tun safe muke da exam ga walimar da Za'ai" Anuty Zulfa tace "Ayyah daughter, take your medicine before baccin" Anuty Zulfa ta kalli Abeed tace "Kai kazo sai zarewa Mutane idanu kake, nace abinci kai min banza, nace Coffee kayi shiru ko ruwa kaƙi sha" Miƙewa tsaye yyi ba tare da yace mata komai ba ya ɗauki key car ɗinsa yyi waje abinsa, Anuty Zulfa ta saki baki tace "Ji gantalalle ko fa gaisheni bai ba, ni wlh tsoran yanayinsa nake ko jikin ne? Duk ya wani rame fuska babu ɗigon fara'a" Auta tace "Mami, Amma kin faɗawa Amma da Yaa Zain, Yaa Abeed na nan?" Anuty Zulfa tace "A'a ƴar iya abinda kikace dai yanzu shi zanyi" Auta tayi dry tace "Am sorry Mami.... Abeed da ƙyar ya iya kai kansa zuwa wani haɗaɗɗan hotel tunda yaje kansa yake ƙasa hannunsa riƙe da kwalba idanunsa sunyi jajurr duk irin matan da suke kallonsa suke tattaɓasa amma babu wacce ya kalla bawai kuma dan baya buƙatar kasancewa dasu bane..... Zain na zaune akan bed abin duniya yyi masa zafi, ya rasa ta yarda zai kalli Du'a ya faɗa mata cewa duk yake daidai da rana ɗaya bai taɓa samun gamsuwa da ita ba, wani kalar infection ne da ita wanda baya jin daɗin komai sai a zaba idan ya shiga jikinta, Du'a data fito daga cikin toilet tana gyara sumar kanta tace "Meke damunka ne? Duk dare sai naga ka kasa bacci? What's up?" Murmushi ya saki tare da Miƙewa zuwa inda take yana zuwa ya wani rungome ta sosai yace "Kawai a gonna miss you Sweetheart.." ta ware idanunta tace "Kamarya U gonna miss me?" Yana warware towel ɗin jikinta yace "Kullum missing nki nake ai" ya faɗa yana jin wani irin ciwo a ƙasan cikinsa mace har mace amma bata da daɗin sha'ani" sakinta yyi ya nufi parlo kafin ya tashi ya shiga kicthen ya haɗa black tea with lemon ya shiga sha a hankali, sai da akai kiran sallah kafin ya
miƙe yana zuwa ya sameta zaune tana share hawayen idanunta ya ware idanunsa yace "Are You cry Diva? For what reason?" Tana sakin kuka tace "Nasan cewa ba daɗin zama dani kake ba, amma mene amfani kayi min shiru ba zaka iya faɗa min na nemi magani ba? Kullum kaje Parlo ka kwana bayan lemon daɗin da kke sha? Eh What i have done to you? Zaman aure muke fa zama na dindin" jawota yyi jikinsa yace "Am sorry nayi laifi, gobe zamu je hospital stop cry" ƙanƙamesa tayi tana ƙara sakin kuka ƙilan shine yasa ko ɓatan wata bata taɓa yi ba.." washegari bayan sunyi breakfast sun gaida Amma da Mai martaba suka nufi asibiti....Naila na zaune a parlo yana faman cin nama aka buɗe ƙofa da sauri tace "Yau naga haihuwar Asara wacce masifa ce wannan ne,ai razana jama'a hankali tashe....," Shiru tayi lokacin da suka haɗa idanu da Junaid wanda yake sanye cikin wata Nevy blue ɗin Alkyabba washe baki tayi tace "A'a, lale lale da Junaidu mara ba, nafa ɗauka waccar tsumammiyar yarinyar ce wace take ta zuƙewa ba gaira babu dalili, nifa ita kaɗai idan na kalla sai naji tsoran Allah ya kamani" Junaid ya cire hannayensa da suke goye a bayansa idanunsa jajurr ya ƙarasa inda Naila take ganinsa haka kuma ya sanya duk jininta yyi sanyi, kafin tayi magana Junaid ya ɗura kansa a cinyarta yana wani jan numfashi Naila tace "Jama'a na shiga uku, akawo min ɗauki Junaidu, Junaidu, Junaidu....Hoooooo! A'a wlh ba lafiya ba nifa tun dana kallesa naji tsoran Allah ya kamani wannan uwar rama ta mece, kai faɗa min uban me kake so mene ya zuƙar da naman jikinka haka?" Ƙanƙame ƙafar Naila Junaid yyi wasu zafaffun hawaye na fitowa daga cikin idanunsa yace "I love her, ina sonta Naila zan mutu....." fitowarsu ke nan daga cikin exam hall kowa sai farin ciki yake, Sara dubawa tayi taga babu Auta a hankali ta zame ta nufi wani waje da babu mutane kanta na wani irin juya mata ga wani amai dake taso mata ciwon datai kwana biyu bai tasar mata ba shine yake ƙoƙarin kwantar da ita, zama tayi tana jan numfashi Idanunta yyi jaa da ƙyar take buɗewa, zamanta ke nan taji wani amai yazo mata kakarin aman ta fara amma yaƙi fita sai wahala take sha, gashi babu kowa a Wajan da ƙyar ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin tafiya gaba ɗaya tayi baya zata faɗi, kusan a tare Abeddeen da Yarima Yashim suka kai hannunsu domin tare ta Yarima Yashim ta tare hannunta Abeddeen kuma ya riƙe waist ɗinta, haɗa idanu sukai Sara kam bata gane komai idanunta ruf ya rufe saboda wahala, sunkuyawa Abeed yyi tare da ɗaukan ta baki ɗaya ya nufi mota da ita....



Zain Abeed isn't free contact to subscribe 08119237616...... Kuji tsoran Allah😭👏🏻.***35***


Da idanu Yarima yabi Abeed dake ɗauke da Sara da kallo yana jin wani irin abu a zuciyarsa mai kama da kishi, yana so ya gane inda yasan irin fuskar Abeed amma ya mance...A hankali ya nufi motarsa da Sara wacce jikinta tuni ya ɗauki zafin zazzaɓ,i da ta buɗe idanunta sai taji kamar zata faɗi ƙasa, tana ji dai ana tafiya da ita amma bata san waye ba, ina kuma zai kai ta? Motarsa ya buɗe a hankali har lokacin kuma tana riƙe a hannunsa kwantar da kujerar gaban motar yyi kafin ya kwantar da ita kana ya rufe motar shi kuma ya nufi wajan driver, key yyiwa motar a hankali tare da yin reverse cikin nutsuwa da kuma son lallaɓa jikin na Sara ya fara driving a hankali yana cilla idanunsa akan hanya, yana fara tafiya ya juya ya kalleta har lokacin idanunta a rufe yake tana sauke ajjiyar zuciya da ƙyar jikinta yyi very weak haka...Yarima Yashim ji yayi jikinsa yyi sanyi yama kasa tafiya hakan yasa ya nemi waje ya zauna yana dafe kansa dake juya masa, yana tunanin Gwamma a ɗaura auren sa da Sara dadai ya bari wani abun yazo ya kifta ta zama ba tasa ba....A babban wani hospital yyi parking kana ya kashe motar ya fito yana ƙarewa hospital ɗin kallo, Ganin babu likita mace ko guda ɗaya a harabar wajan ya sanya ya ƙara shan kunu fuska ɗaure ya juya zai shiga mota yaji ance "Oh! Da gaske kai ne dai?" Dr Adyan ya faɗa yana sakin Murmushi, a hankali Abeed ya juya yana buɗe idanunsa ganin Dr Adyan ba ƙaramin mmki ya bashi ba yaushe yazo ƙasar to? Dr Adyan yace "Me kake cikin hospital ko jikin naka ne?" Girgiza kai Abeed yyi a hankali ya buɗe murfin gaban motar a lokacin wani zazzaɓi mai zafi ya kama Sara sai rawa jikinta yake, Dr Adyan yace "Oh! God bata lafiya ne, bai kamata ana barinta hk ba sbd gudun abinda zaije ya dawo" ganin yadda take rawar jiki yasa Dr Adyan ya ƙara cewa "Shigo da ita Emergency room 12 yanzu" yana faɗin hakan ya juya, rufe murfin motar Abeed yyi cike da nutsuwa yake tafiya zuwa ɓangaren driver ya shiga tare da jan murfin motar ya rufe, idanunsa ya ware zuwa kanta yana ƙarewa kayan jikinta kallo hakan kuma ya nuna kayan jikin nata bai masa ba, gashi su kaɗai ya isa su sanyata jin sanyi, jacket ɗin jikinsa ya cire wacce take da ɗan girman domin zatai covering jikin Sara yana cire jacket ɗin ya ajjiye gefe guda, a hankali kuma ya ranƙwafa kanta yana jin yadda numfashinta ke dukan fuskarsa fararen hannayensa masu taushi ya sanya tare da tallafo fuskarta, murya can ciki kamar me raɗa daidai kunnanta yace “Saaaa...." Ya faɗa yana ɗago ta baki ɗaya zuwa jikinsa, Idanunta ta buɗe da ƙyar tana Kallonsa kafin ta kwaɓe fuska tace "Uncle..." Ƙuri yyi mata da fararen idanunsa still hannunsa yana kan fuskarta kafin a hankali ya shafi kumatun ta kaɗan yana manna fuskarsa akan nata idanunsa cikin nata yace "Uhm..meke maki ciwo Saaaa?" Hawaye ya kawo Idanunta tace "Uncle cikina.." idanunsa ya lumshe kana ya buɗe kafin gently ya kama hannayenta data riƙe cikinta ya ware su tare da mayar dasu baya, da sauri ta kama hannunsa tace "A'a,kai na ne" baice mata komai ba ya shiga zame rigar jikinta, top ɗin ta manne da jikinta sosai, yana Zamewa ya kalli Idanunta yaga bashi take kallo ba domin ta maida idanun ta rufe alamar dai sosai take jin ciwo, Numfashi Abeed ya sauke lokacin daya gama zame rigar jikinta bai yarda ya kalleta ba idanunsa akan fuskarta a karo na farko daya shiga ƙare mata kallo jacket ɗin ya ɗaga ya sanya mata saman farar t.shirt ɗin ta, kana ya mayar da top ɗin hakan kuma ba ƙaramin daɗin yyi mata ba, gently ya ƙara matsar da fuskarsa saman nata goshinsa akan nata a hankali ya shiga goga mata kwantaccen sajansa kafin ya manna bakinsa ta ƙasan wuyanta ya sakar mata wani hot kisses daya sanya ta saki ajjiyar zuciya, so take ta buɗe idanunta amma ta kasa, ƙara shigar da hancinsa yyi sbd fitinan nan ƙamshi da yake shaƙa bai taɓa jin ƙamshi mai daɗin sa ba, bakinsa ya sanya a kunnanta tare da wura mata iska kaɗan wanda ya sanya Sara saurin fisgar numfashi a hankali tace "Uhm... please" bai ɗago ba sai daya ɗan tura bakinsa ya fesa mata wani numfashi tare da kama skin ɗin wajan ya bata wani ƙyakƙyawan sumbata mai tsayawa a zuciyar mace a hankali a taushashe cikin nutsuwa da kamewar sa wacce take shirin gudu a yanzu ya buɗe Murya with a very low tone yace "Sowwiee.....Saaaaa" ya faɗa Murya kame yana wani irin murza mata fuskarsa a wuyanta, yunƙurin aman data fara ya sanya Abeed saurin buɗe ido wanda suka fara janyewa, ganin yadda take yunƙurin aman amma baya zuba jikinta duk yyi sanyi ya sanya ya ɗago ta tare da mannata a shoulder ɗinsa kamar wata baby ya shiga shafa bayanta ba tare da yace komai iya wahala kam tana wahala, shi kuma yaƙi fita ne sbd mazan da suke wajan, kuka ta fashe masa dashi a hankali ya sakko ta zuwa cinyarsa yana kallon yadda take kuka shi ba wani iya rarrashi yyi ba, hakan yasa kawai ya jawota jikinsa sa sosai tare da rungometa kamar wani zai ƙwace masa ita, gaba ɗaya ta jiƙa masa gaban riga da hawaye sai da yaji kukan yyi yawa ya sanya ya cirota a hankali daga jikinsa yana kallon fuskarta firr kuma taƙi buɗe idanunta, gashi dai so take ta ƙwace kanta amma bata da ƙwari, fuskarta da tayi jajur sbd zafin ciwo da kuma kukan da tayi, fuskarta ya kalla kamar wanda zai ɗauki wani abu haka ya miƙa hannunsa zuwa gaban motar bakinsa ya sauka akan goshinta a hankali ya buɗe bakin kana ya tsuke ya bata wani sauti na sakar mata light kisss da yyi a forehead "Uhm" Sara ta sauke numfashi tare da buɗe Idanunta suna haɗa idanu ya sha kunu kamar bashi ba, zame fuskarsa yyi daga nata zai fito da ita a hannunsa a hankali tace "Sake ni" ta faɗa fuska babu walwala ga zafin ciwo ga baƙin cikin abinda yyi mata, kallon ta yyi bai ce komai ba ya saketa daman kanta a rufe yake, ya fita ita kuma ta sakko ƙafarta a hankali zuwa waje da ƙyar take jan numfashi dauriya kawai take bata son abinda Abeed ɗin ke mata... tana gaba yana binta a baya hannunsa zube cikin Aljihu da tayi tafiya sai ta tsaya, tsaki yaja kawai ya sunkuya tare da ɗaukan ta yyi gaba Mutane suka bisa da kallo, Idanunta ta runtse kawai amma wannan abin kunyar har ina, bai sauke ta sai a baƙin ƙofar shiga cikin room yana sauke ta, ta murguɗa masa baki bai kulata ba ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga, Dr Adyan na tsaye ya gama haɗa komai ganinsu kuma ya sanya yace "Sannu, Sara" da mmki Sara take kallonsa jikinta har rawa yake wajan ƙara sawa inda Dr Adyan yake tace "Dr ka gano inda yake? Please faɗa min dan Allah ka faɗa min ka samu labarin inda yake?" Dr Adyan ya ɗan saci kallon Abeed, kafin yace "Be patient Sara" Sara tace "Wanne irin be patient Dr? Shekara nawa? Ban taɓa tunanin zan sake ganinka ba number daka bawa Daddynmu baya tafiya dan Allah ka tausayi na ka faɗa idan kasan wani abu game dashi" Abeddeen dai na tsaye fuska ɗaure idanunsa akan Wayarsa yana dannawa, girgiza kai Dr Adyan yyi yace "Ba wani information, amma soon zamu samu nasara ina ta bincike" baya tayi ta zauna saman bed Sbd jin ciwonta na dawowa sabo, kasa magana tayi sai kawai ta kifa kanta a cinyoyinta ta shiga rera kuka ƙasa ƙasa, taɓe baki Abeed yyi tare da juyawa ya fita ya jima a waje lokacin daya dawo tana kwance tana bacci drip maƙale a hannunta, zama yyi kan kujerar dake kusa da ita idanunsa akan fuskarta data faɗa, ya daɗe yana kallonta kafin ya kama left hand ɗin ta, hannunsa ya saka cikin Aljihu ya zaro wata box mai masifar kyau, buɗe box ɗin yyi wani silver gold ring ya bayyana mai kyau sai sheƙi yake, ga wata ƴar blue ɗin danja sai kuma rubutu da aka sanya kalmar _Absar_ yatsarta ya kama tare da sanya mata, ring ya wani kama hannun sosai yyi mata kyau sakinta yyi da sauri, shifa babu soyayya a lissafin ƙaddararsa bawai mancewa yyi ba, kawai dai ya siyi Ring ɗin zai bawa Naila sai kuma ya bata shi domin itace kusa dashi a yanzu ba Naila ba.... Sai bayan sallar Asr Sara ta motsa daga baccin daya ɗauke ta, a hankali ta shiga buɗe Idanunta ganin babu kowa room ɗin ya sanya ta mayar da Idanunta ta rufe da kuma sauri ya buɗe tana ƙoƙarin tashi ya turo ƙofar a hankali tare da shigowa sai Dr Adyan ya biyo bayansa da alama gaba ɗaya daga Mosque suke ganin yadda take ƙoƙarin tashi ya sanya Abeed nufar inda take yana zuwa ya zauna tare da sanya hannunsa akan shoulder ɗinta a hankali ya mayar da ita kwanciyar yana kallon yadda ta haɗe fuska yyi mata banza, Dr Adyan yace "Sannu, ya kike jin jikin" tana haɗe rai kamar ba zatai mgn tace "Better" ya jinjina kai yace "Ki daina zama da yunwa ok" kafin ya hankali Abeed da idanunsa ke kan waya yace "Za'ai mata injection sai ku shige" gaban Sara ya faɗi a fili tace "A'a ban so" Dr Adyan yace "Ai aman zai taso maki dole sai anyi maki" ƙoƙarin sauka take daga kan bed tana faɗin "No, thank you am feeling much better" hannunta Abeed ya riƙe yana kallon Dr Adyan yace "Bisimillah" ya faɗi hakan yana riƙe da hannunta Sara tace "Ka sake ni bana so, dole ne? Ni banso Allah" Dr Adyan dai na tsaya yana kallon ikon Allah Abeed ya fisgo hannunta gaba ɗaya tayo baya saboda bata da wani ƙwari zaunar da ita yyi akan cinyarsa, a hankali ya sanya hannunsa tare da juyo da fuskarta zuwa nasa yace "Zaki sha mmki idan baki tsaya ba" ya faɗa yana ƙara riƙe ta kafin ya kama hannunta ya riƙe idanun Sara ya cika da hawaye ta shiga turesa tace "Wlh ban so, daman kai mugu ne mene haɗi na dakai kake tayi min mugunta" ta faɗa tana dukan ƙirjinsa sakar mata nauyin sa yyi baki ɗaya yana ƙara kwantar da kanta bakinsa daidai kunnanta yace "Shiiiittt...." Da idanu yyiwa Dr Adyan mgn akan yyi mata, wani ihu Sara ta saka lokacin da Dr Adyan yyi mata allurar da sauri ya saketa tare da bar musu ɗakin, wani kalar ihu take da kuka ta shiga birgima akan bed ɗin, wani cute smile Abeed ya sauke ganin da gaske bata son allurar shima kuma ba wani so yake ba, sunkuyawa yyi ya sunkuceta tare dayi sama da ita yana sakin Murmushi yace "Shiit, am sorry Sahraah.." ya faɗa yana zama da ita akan bed ɗin bata ko kulasa ba sai kuka take tana ƙoƙarin sauka daga jikinsa, fuskarta ya kama a hankali tare
da manna fuskarsa a saman nata, saukar bakinsa da taji a a cikin nata ya sanya cak ta tsayar da kukan nata, Idanunta wanda sukai jaa sosai ta buɗe suka haɗa idanu ya lumshe mata idanu tare da buɗewa alamar _“Begen”_ gaba ɗaya Sara neman kukan tayi ta rasa sbd fargabar jin abinda Abeed ke mata,bata san mene yake damunsa a yanzu ba, gaba ɗaya ya sauya, yatsarsa guda ɗaya ya sanya a daidai wajan allurar ya shiga murzawa kaɗan, still kissing her wani kalar kiss ya kewa lip's ɗinta, ƙoƙarin ƙwace fuskarta take amma ta kasa da sauri ta sanya hannunta tare da riƙe waist ɗinsa tana rufe idanunta tana jin yadda yake shan bakinta tamkar ya samu chocolate ɗin daya saba sha a kullum... Sara bata sare da al'amarin nasa ba sai da taji saukar tongue ɗinsa a saman Idanunta a hankali yake bi yana tsotse all hawayen dake zubu mata, sai daya shanye hawayen tass kana ya zame fuskarsa a hankali tare da ɗago ta ya zaunar da ita sosai magana ya ke son mata amma ya kasa dan haka kawai sai ya ɗauke ta baki ɗaya ya nufi waje da ita, Sara sbd kunya kamar zata zunduma ihu haka ta keji, har mota ya sanya ta kana ya zauna wajan driver yana ƙoƙarin tashin motar wani securitie ya kwankwsa musu glass ɗin motar, a hankali ya zuge glass ganin mutumin a side ɗin Sara ya sanya Abeed ya kafe securities ɗin da idanu yana jiran yaji me zaice, securitie ɗin ya kalli Sara yace "Kece Sara Salman?" Sara ta waro idanu waje sbd jin sunan daya kirata dashi,kai ta ɗaga masa ya miƙo mata wata rose mai kyau red and white sai ƙamshi take sosai, gefe guda na rose ɗin farar paper ce da zanan heart sai hoto nan mutane biyu mace da namiji suna rungome da juna, yana bata yace "Wani yace na baki" har zatai magana sai kuma ta amsa a hankali ta shiga ware paper ƙirjinta ne ya buga ganin abinda yake jikin paper.
_Zan iya bada Rayuwa ta a kanki SARAHH, ba iya kidey ba, dake nake kwana nake tashi i wish my dream to come true_
Fita tayi da sauri daga cikin motar jikinta na rawa tace da securitie "Please waye? A ina yake zaka iya gane sa, shi nake nema tsayin shekaru" securitie ya watsa hannu yace "I have no idea, kawai ya bani ya tafi fuskarsa a rufe" dafe kai tayi hawaye na neman zubu mata, Abeed dake cikin motar yaja tsaki yace "Ke zan tafi" motar ta buɗe ta shiga tana shiga ta kifa kanta a cinyarta ta shiga rera kuka, tana jin zuciyarta babu daɗi abu goma da ashirin yyi mata yawa, har suka isa gida bata daina kuka ba, a hankali Abeed yyi parking tana ƙoƙarin fita yace "Wait..." Banza tayi masa ya daka mata tsawa yace "Am i your mate? Da ina mgn zaki min banza?" Ɓata fuska tayi tace "To me zan maka?" Tsaki yaja yace "Who is he?" Ta waro idanu tace "Wa?" Yace "ban sani ba" tai shiru can kuma tace "I don't even know his name bare ganin fuskarsa" Calmy yace "kuma hadda kuka?" Kallonsa tayi tace "Shi fa ya ceci rayuwata ya bani kyautar kidney ɗinsa" yace "And so what?" Tace "Noting,kawai ina son ganinsa ne, i have looked for him babu labari Daddy na da duk ƴan gidanmu shine yazo naga Dr kuma shine yyi min aikin gashi kuma yanzu ya bani wasiƙa with rose ke nan shima nema na yake" Abeed ya taɓe baki yace "Out..." Fita tayi tana ɗaukan rose ɗin jikinta babu Kwari ga fargabar abinda zata faɗawa Anuty Zulfa, tana fita daga motar Abeed ya kifa kansa a string motar yana dafe ƙirjinsa dake masa zafi kamar zuciyarsa zata fito waje.**36**Fitowa Abeddeen yyi daga cikin motar a hankali yake tafiya cike da nutsuwa da kamewar nan tasa a ko da yaushe,
Yana shiga cikin parlon ya ganta tsaye kanta a ƙasa sai kuma Anuty Zulfa dake zaune kan kujerar hannunta riƙe da ipad, idanunsa ya juya kaɗan sai kuma ya juya a hankali, Anuty Zulfa dake zaune tace "Ina zaka? U have to stay..." Cak ya tsaya daga tafiyar kafin gently ya nemi saman Kujera ya zauna tare da harɗe ƙafarsa, Anuty Zulfa tace "Magana nake kina jina?" Sara tayi rau rau da Idanunta murya can ƙasa tace "Mami hospital aka kaini dg schl" Anuty Zulfa tace "Hospital? Ke dawa?" Sara dai ba tace komai ba can dai Anuty Zulfa taja tsaki tace "Ba kijin magana, matsa a kai na" kamar jira take da ɗan ragowar ƙarfin ta, tayi saurin shigewa bedroom ɗin su, Auta ta gani zaune tana waya tana ganin Sara tace "Yawwa, she's back Yaa Yarima" daga can cikin wayar Yarima Yashim dake zaune cikin gidan da yake sanye da farar jallabiya mai kyau hannunsu riƙe da coffee yace "Bata wayar" Auta ta miƙa wa Sara wayar, a hankali Sara ta nemi waje ta zaune jikinta duk yyi sanyi, jin yadda Yarima Yashim yyi shiru ya sanya a cikin nutsuwa tace "Ina yini?" Shiru yyi mata kwaɓe fuska tayi sosai tace "Ina yini Yaa Yashim?" Shiru yasa keyi da alama yau sarautar na kansa shima kamar zatai kuka tace "Ko baka ji ne?" Wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke Calmy yace "How was your body, Sara!?" A hankali tace "Da sauƙi" a hankali Shima yace "G.w.s sweetheart" shiru ya biyo baya kafin Yace "Kinci abinci?" Ta girgiza masa kanta yace "I see...eat first I'll calling later" bai tsaya jiran mene za tace ba ya kashe wayar, shiru tayi bata san adadin son da Yarima Yashim ke mata ba, itama kuma bata ƙinsa amma what about the secret lover? Idanunta ta rufe kaɗan kafin ta miƙe ta shiga zame kayanta a hankali ta shige bathroom bayan ta haɗa warm water..... Anuty Zulfa takalli Abeed sosai kamar me nazari kafin tace "What's wrong with you?" Fararen idanunsa ya ware sosai ga wani ƙamshin Spraymintt mouth freshener dake fita daga cikin bakinsa, a nutse cike da nutsuwa da kamewa yana wani rufe idanunsa sosai a hankali cikin golden voice ɗinsa yace "Uhm.." Anuty Zulfa tace "Baka ƙarya ko zaka fara yanzu ne? I'm asking you meke damunka" a lokaci na farko Abeed ya marairaice fuska tare da langwaɓar da kai yace "Mami me nayi to?" Harararsa tayi tace "Are You answering my questions with a question Abeed?" Shiru yyi mata tace "Kana shan maganin ka?" Ya girgiza mata kai tace "To why?" Kwaɓe fuska yyi calmly yace "Mami, ba naji sauƙi ba?" Tace "Shiyasa gashi nan kake ramewa sbd samun lafiya, and wannan jan idanun na mene?" Shidai shiru yyi mata can ya miƙe zai fita tace "Anjima jirgi na zai tashi zuwa India, akwai wani abu da zamuyi na

Please Login or Register in order to submit comment