Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wajan Dodo, tasa kanta Gabas, tun a kabbarar farko sukaji wajan yana girgiza, da sauri Mabus ya nufi wajan abin bauta kabas ya shiga yi masa kirari...Sara addu'a take a sujjada for the first time hawaye masu zafi suka shiga fita daga cikin idanunta, zafin da Zuciyarta yake ya ɓaci, tana ganin duk abinda ya samesu mahaifinsu shine sanadi, tashin hankalin ta bai shige tunanin inda Sairah take ba, addu'a ta dingayi a hankali taji Zuciyarta na sanyi... Yayinda Mabus ma yake neman tsari daga sharrin mugwaye gefe guda kuma yana neman yardar Kabas wajan sahalewa masa kwanciya da Sara a matsayin sarauniyar Zahel. Gimbiya Noro ce zaune tana kallon Sairah wacce take shan ruwa da saurin ta kamar bata taɓa ganin ruwa ba, Sairah na gama shan ruwan ta sauke ajjiyar zuciya, kafin a hankali tace "where are you Twin, Ubangiji ka bayyana min ita, Allah ka kareta ka duba halin rashin lafiyar da take ciki" Gimbiya Noro tace "me kike cewa?" Gently Sairah ta girgiza kai tace "Cewa nayi zanyi Sallah" a ɗan tsorace Gimbiya Noro ta juya sai kuma ta saki ajjiyar zuciya ganin babu kowa a ɗakin kafin tace "mene sallah? Ohh wannan dunguran?" Kai kawai Sairah ta ɗaga alamar "eh" Gimbiya Noro ta miƙe tace "biyoni" Tashi Sairah tayi tabi bayan gimbiya Noro, tafiya sukai mai nisa, har suka kawo wani sashe da babu wanda yake shigarsa, kallon Sairah tayi tace "kiyi a nan, amma duk sanda wani ya ganki babu ruwa na" Sairah ta jinjina kai tace "Thank you Maahh..." Gimbiya Noro na kallon Sairah tayi sallah, bayan ta gama suka fita zuwa sashen gimbiya Noro, ɗawisu ta saka aka dafawa Sairah ba tare da Mabus ya sani ba, sosai kowa Sairah taci domin yunwa take ji kamar ta mutu haka ta keji, a nan bacci ya ɗauke Sairah ita kuma gimbiya Noro ta fita zuwa wajan Mabus. Mabus bayan ya kammala abinda yake ya dubi Sara yace "akwai sharaɗi idan har wani ya kasa cetonki to Tabbas zaki zama matata ko baki so.." Sara nada yaƙini addu'ar ta ba zata tashi a banza ba, hakan yasa ta ɗaga kai alamar ta amince, Murmushi kawai Mabus yay kafin yace "a kira min dakaro domin ƙarawa masarautar Zahel tsaro" yana faɗin hakan yaja hannun Sara zuwa inda yake ajjiye ta wajan da yafi ko wanne tsaro a cikin Masarautar... Da yamma Mabus ya kalli boka yace "Ina son a hargitsa min ƙwakwalar yarinyar, dukkan abinda nace tayi babu musu, koma a tilasta ta yiwa addinin mu biyayya" Boka yace "hakan nasu ayi tun farko, ashe tunaninka yafi nawa" Mabus yace "na barta ne, sbd bana son ta fahimci zan mata wani abu" Boka yace "Na fahimta, ita da sallah yanzu har abada, amma dole sai mun rabata da dukkan wani musulmi da zai shiga rayuwarta" Mabus yace "Kana tunanin wani zai iya shigowa masarautar Zahel ne? Balle har ya haɗu da Ita? Ya ruguza min tsarin da na shirya" Boka yace "Uhm, babu kam domin duk Musulmin daya shigo Zahel to ya shigo abakin ransa" daga nan ya tashi ya fita, shi kuma Mabus ya fara cin naman Aladen da aka dafa masa, bayan ya gama ya miƙe tsaye ya nufi sashen gimbiya Noro time ɗin tana zaune ita da Sairah har lokacin babu wanda yay magana, sai kafeta da ido kawai Gimbiya Noro tayi, motsin shigowar Mabus taji cikin sauri ta kama hannun Sairah zuwa cikin wani daƙi, sakata ciki tayi ta kulle, fuskarta ɗauke da Murmushi tace "Abin bauta kabas ya taimake ka, an shigo lafiya" kallon ta kawai yay dai kuma yace "Akwai wani aiki dana shirya, gidan wani attajiri kece zaki aiwatar, akwai taron bokaye da Za'ai a wannan satin domin neman Masarautar Zahel kariya" kai ta jinjina tace "Abin bauta kabas ya bada Sa'a" hannu ya miƙa ya jawota suka faɗa gado... Washegari da safe Sara na zaune ta haɗe kai da gwiwa, yunwa ta keji tube tazo masarautar babu abinda take iya ci, face ruwan da take samu tasha, ta rame sosai time to time kuna gabanta na faɗuwa, ji tayi kanta ya sara da ƙarfi, da sauri ta dafe kan nata, ta shiga motsa bakinta da niyyar kiran sunan Allah, amma abin ya gagara jikinta sai rawa yake idanunta na zubar da hawaye, da wani irin ƙarfi ta ƙanƙame jikinta tare da faɗin "Abin bauta kabas ka taimake ni..... Jirgin su Abeed ne ya sauka a airport, wata haɗaɗɗiyar mota ce tazo ɗaukan su, wacce akaiwa tambari da Masarautar Bilhira, suna gidan baya driver na jansu, a haka suka isa cikin Masarautar Bilhira, idanun Abeed a lumshe yake, wlh dauriya kawai yake amma kamar ana jan gangar jikinsa zuwa garin Zahel haka ya keji. Ga wani matsanancin ciwo da ƙirjinsa yake masa, jijiyar kansa ta fito tayi raɗa raɗa, saboda masifar da kansa yake, driver nayin parking Zain ya juya ganin yadda Abeed ke sauke numfashi yace "What's wrong?" Girgiza kai kawai Abeed yay tare da buɗe murfin motar kusa dashi ya fita, shima Zain ya fita driver kuma ya shiga da kayansu, kamar mai counting steps ɗinsa haka Abeed ke tafiya, domin duk tafiyarsa guda ɗaya ji yake kamar kansa zai cire, ganin Abeed ya ɗauki hanyar sashen Naila yasa Zain yace "why not AMMA?" Abeed yace "i wanted to see Naila frist?" Zain yace "Ok then.." ya juya ya nufi part ɗin Amma domin ya tabbatar yanzu suna tare da Abba, Walking slowly Abeed ke tafiya, zuwa sashen Naila yana tafe jiri na neman ɗaukan sa, a bakin ƙofa ya tsaya, idanunsa ƙuri akan Naila dake zaune tana azkar, a jikinta taji ana kallon ta, ɗago idanunta tayi tare kallon Abeed, cikin sauri tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w saukar yaushe ɗan nan kamar wani mikiya, shigowa Abeed yay ba tare da yay mgn ba, hakan yasa Naila cewa "Shalele ne ko kuma wancan maƙaryacin lauyan?" Abeed yana zama kan kujera tare da lumshe idanunsa yace "Laywers na
wajan Amma" Naila ta washe baki tace "To wa nake dashi a duniyar nan ai sai kai ɗin, wallahi babu mai iya raba wannan Soyayyar tamu, sai munafiki shima Allah ya tsine" ta ƙare tana zama kusa Abeed, hucin zazzaɓi taji a jikinsa tace "Kai kuma lafiya, kake numfashi kamar wani zaki ɗan shekara sittin?" Murya a maƙale yace "Fever and headache Naila" Naila tace "Wani abu ne haka kuma?" Shiru yay mata yana ɗura kansa a cinyarta tare da lumshe idanunsa, try to force his self to sleep. Zain ya ƙarasa sashen Amma kamar yadda yay tunani suna tare da Abba, da murmushi Amma tace "wlcm back twins" Zain yay Murmushi yana zama ƙasan carpet yace "Abba, Amma good evening" Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas dake zaune yana shan dakakkiyar fura wacce tasha cikwi yace "Evening how are you?" Zain yace "Allahamdulillah" Amma tace "and where is your brother?" Kafin yay magana Abba yace "Yana wajan Naila" dry Zain yay yace "Ya akai ka sani Abba?" Abba yace "Abinda tun yana ƙarami,ya fifita Granny akan parents" Amma tace "Ai ya lalace, yanzu da zaka je yana kan cinyarta a kwance, tayaya zai saki jiki ya nemo matar aure tana sangarta shi, kayi magana kuma wlh kaji abinda yafi ƙarfinka" Abba yana shan furarsa yace "Soon zai aure, ai tace dole ayi aurensa da Riya" da mmki Zain yace "Abba Abeed doesn't like Riya, ko forcing nasa za'ai?" Abba yace "ni ɗan kallo ne, ɗaurin aure ne nawa, haka Naila tace" shiru kawai Zain yay sam baiji daɗi ba, baya son abinda zai ɓata ran Abeed musamman da yanzu yake fama da ciwo, miƙewa yay Amma tace "where are you trying to go...?" Yace "i wanted freshen up" tace "ok, let me get you something to eat..kafin wankan" fita yay zuwa haɗaɗɗan sashen su, yana zuwa ya faɗa toilet, yay wanka tare da gabatar da Zhur prayer, wasu ƙanan kaya ne a jikinsa farare, a hankali yake tafiya, har ya fito main Parlo, Amma ce ka ɗai zaune, domin idan tana nan kuyanginta baza shigowa, Kallonsa tayi tace "Lunch ɗin" yace "Bari naga Abeed" tace "ok a gaida Naila" fita yay zuwa sashen Naila, lokacin daya isa yaga Naila zaune ta zabga tagumi, ga kuma family doctor nasu, sai Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, da mmaki yace "hey, what's going on here?" Abba yace "Yanzu Naila ta kirani tana, kuka wai zazzaɓi yake hadda aman jini" gaban Zain ya faɗi, da sauri ya zauna kusa da Abeed dake bacci, ya ɗura kansa akan cinyarsa yace "We need to go to the hospital" Dr yace "No need, he will soon recovering" Mai martaba dai shiru yay, yana amincewa da auran da Naila za taiwa Abeed ƙilan hakan zai sanya ya samu lafiya. Can yamma Abeed ya farka time ɗin Zain ya fita zuwa Court, ganin babu Naila yasa a hankali ya nufi part ɗin su, wanka yay yazo saka kaya ya rasa, wanne zai saka number Amma ya kira bayan ta ɗaga yace "Wanne kaya Zain ya saka" dry tayi tace "Suit nevy blue." Kashe wayar ya yi, ya ɗauki irin kayan Zain ya saka yana wani irin ƙamshi, ya fito sashen iyayen nasa, Zaune ya samu Amma da Abba, gaishe su yay, daga nan bai sake magana ba, ganin yadda ya rufe idanunsa sosai yasa Amma faɗin "kana stressed kanka da yawa wlh,U look stressed out." Abeed ya girgiza kai can yace "Abba zan fita" Abba yace "where" Abeed yace "Waje zani" Abba yace "take care" yana fita waje wajan compound Riya na zuwa, cikin sauri tai hugging nasa ta baya tace "wlcm back my singer" hannu yasa ya ture ta, murya can ƙasa yace "Middle class..." Yau Monday kwannasu biyu da dawowa 9ja, Zain ne ya dawo gida da ciwon kai, saboda wata Shari'a daya gabatar kuma gobe yake son tafiya Zahel, Abeed da kansa ya kira Dr yaywa Zain injection, lokacin da akai masa allurar Abeed ya sauke wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, nan take kuma bacci ya ɗauke Zain, wayar Zain ya ɗauka, da komai nasa, kana ya saka key ya rufe sashen baki ɗaya, cikin sauri yake tafiya waya maƙale a kunansa yana faɗin "Abba, zamu somewhere, Kada abar kowa ya shiga shashen mu, akwai kaya masu muhimmanci, nan da 3 to 4days zamu dawo" Abba yace "Allah ya kiyaye" yana faɗin hakan ya shiga mota tare dayi mata key, gudu kawai yake yana duba map yana nuna masa direction ɗin da zai bi, cikin ikon Allah misalin 10 na dare ya shigo Garin Zahel....



_Wannan labarin, ban fara ba sai dana tabbatar da ingancin cinsa, da kuma lesson ɗin da Za'ai leaning a ciki, ba zan ɓoye ba akwai Romance a labari, domin haka na tsara, so dan Allah Dukkan wanda ya san ba Zain Abeed zai siya ba, kada wanda yay min mgn for no reason, masu cewa a basu kyauta ko kuma saboda Allah basu da Kuɗi, kullum ina sadaƙa wlh, ga free book nan suna ta gantali a media, *Zain Abeed* na kuɗi ne, babu kuma wacce zan bawa kyauta ki biya Ni Sarauta na saki a original grp soon zanyi ending free pages.........._

*ZAIN ABEED*

BOOK 1,2,3
AMOUNT #500
6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank.... EVEDANCE 08119237616

Wanda suka biya za'a zasu a Original grp Na vip.



_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
[08-15 08:42] +234 703 831 1110: *🌈ZAIN_ABEED🌈*


_By Nimcyluv sarauta_

Page 7....

_Domin yin mgn da Marubuciyar_
http://wa.me/+2348119237616


*Nice dai Marubuciyar..*
Kwaila ce
Abu Maleek
Sirrin mu
Tsintacciya
Moon
Jidda
Juyayi
Uncle ne
The new emir
Raino ne sila
Sai na aureta e.t.c




Lokacin da Abeed ya isa Zahel dare da riga da yayi nisa, amma bisa tarin Mamaki sa, mutane ne ko ta ina kamar kasuwa ake ci a wannan daran, he was so surprised da ganin hakan he never sow something like that a all his life nasa, ajjiyar zuciya ya sauke trying to control his self, yanayar kuma da tayi masa yawa ne kuma ya sanya ciwon kasa motsawa, gashi bashi da wani medicine wanda zai iya kare kansa ga ciwon kan, iska ya fesar ta cikin bakinsa, a hankali ya zura dukkan hannunsu cikin sumar kansa ya shiga hargitsawa, he just wanted to pretend. Bayan ya gama baza sumar tasa, ya ɗan zuge glass motar, ware manyan idanunsa yay ganin gaba ɗaya babu kayan arziƙi a jikinsu, and idan har ya fita haka akwai prblm, cikin gajiya wa da al'amuran garin ya buɗe baki cikin cool voice nasa yace "you're mad Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas, ka kawo kanka halaka.." kayan jikinsa ya kalla yaga wani black ɗin yard ne mai taushi, rigar jikinsa ya cire tare da yaga ta, kana a hankali kamar mai tsoron taɓa jikinsa ya zame wandon kayan, ya naɗa rigar a waist nasa, in few minutes yay shiga irin nasu, slowly kuma ya fito daga motar can nesa yadda ba za'a gane sa ba, ya ɗauki wata ƙaramar Camera ya saka a jikin wata ƙaramar necklace daya sanya, wacce zata iya masa all recording na abinda yake buƙata. Cikin nutsuwa yake tafiya, nutsuwar sa na iya bayyana da waye shi, domin duk yadda yakai da ɓoye Asalinsa kallo guda zakai masa kasan cewa ya haɗaka jini da sarauta. Cikin kasuwar garin ya shiga yana ɗan taɓe baki fuskarsa babu walwala sam, ga wani wari da hancinsa yake jiyo masa, deep down na zuciyarsa sunayen Allah kawai yake kira, ga wata faɗuwar gaba wacce rabonsa da ita tun shekarun da suka gabata... Wani dattijo ya gani can zaune waje guda, ji yay ya samu gamsuwa da dattijon wajansa ya ƙarasa, har zai masa sallama sai kuma yay shiru, Dattijon ya ƙurawa Abeed idanu kafin yace "Abin bauta ya taimake ka..." Wani irin runtse idanu Abeed, nan take jikinsa ya fara rawa amma ya daure can yace "Ina son shiga." Shiru yay domin sam bai san abinda zai ce ba, fuskantar hakan yasa Dattijon faɗin "Wannan lokacin kasuwa ne, gobe kuma ake bikin addu'ar bokaye" a sanyaye Abeed yace "biki? Boka?" Dattijon yace "ko baka da labari ne? Sarki Mabus shine ya buƙaci hakan domin ƙarawa masarautar Zahel tsaro" gently Abeed ya jinjina kansa yana jin confidence a tattare dashi, kamar ba zai Mgna ba sai kuma yace "da safe kenan?" Dattijon yace "ƙwarai, da safe ne, ko wanne boka zai je da kayan aikinsa yay addu'a, Sannan yaywa sarauniyar Zahel ta gobe addu'a, domin umarnin abin bauta kabas sarki Mabus yake jira da tuni ya kwanta da ita ta zama matarsa" gyara tsaiwa Abeed yay kafin yace "nazo a daidai" Dattijon yace "kamarya?" Fararen idanunsa Abeed ya lumshe kafin ya buɗe yace "ina nufin Nima boka ne, kuma dani za'ai addu'ar, zan shiga cikin Masarautar." kallon Tsaf Dattijon yay masa kafin yace "kuma ba kai kama da boka ba" ganin kamar zai samu wani bayanan wajan tsohon yasa Abeed ya ɗan tsuguna domin komai a ƙyamace yake yinsa, cikin sauke ajjiyar zuciya Abeed yace "like how?" Dattijon yace "I mean u don't look like Magician" with much surprised Abeed ya ware idanunsa yana mmkin jin turancin da dattijon yay, cikin ƙasa da murya yace "why are you speaking english? Inside of Hausa ko yare naku?" Dattijon yace "and you too, mene yasa ka shigo Zahel bayan ba ɗan garin bane?" Abeed ya shafa kansa, gaba ɗaya ya takura da wannan maganar can yace "something fishy" Dattijon yace "Of course, ni nan ɗan jarida ne, kamar yadda kazo neman sirri haka nazo, shekaru na, kusan 10 a nan, ban samu abinda nake so ba, na zama bawa a masarautar Zahel, babu wanda ya gane ni musamman da nake baƙar fata, kallo guda nai maka nasan akwai dalilin zuwanka, shiyasa nai saurin keɓe kai na nasan za kazo gareni" Abeed kallon mutumin kawai yake, kafin ya numfasa yace "to! Babu amfanin zuwanka ke nan?" Dattijon yace "haka kake gani? Duk wani information ni nake turawa,ta Ɓoyayyiyar na'ura, abu ɗaya zan faɗa maka ba zaka iya Sarki Mabus ba, da ace wani zaici galaba akansa da nine farko" lumshe idanu Abeed yay kana yace "Oh! Ni tabbacin abinda yake nake son samu, bawai cin galaba akan sa ba" Dattijon yace "idan haka ne, nine nan zan baka, akwai memory guda biyu a waje na, duk recording na abinda yake, kaga no need ka shiga ciki" jinjina kai Abeed yay cike da gamsuwa yana jin gaba ɗaya abin yazo masa da sauƙi, cikin ƙasa da murya yace "Me Sarkin yake haka ne?" Dattijon yace "Duk wani mummunan fashi daza kaji ance nayi shine, haka duk wasu ƴan mata da ake nema a rasa shine yake sace su, kawai dan ya kwanta dasu, yabawa dodo jininsu" Abeed ji yay kansa yana wani irin sarawa, faɗuwar gaba ta riskesa, he just thinking wani abu nada ban, can ƙasan zuciyarsa yace "No! Never" shiru ne ya biyo baya, babu wanda ya a sake cewa komai a cikinsu, can tsohon yace "dole sai dai ka kwana tare dani, asubar fari sai ka ɗauki hanya" jinjina kai kawai Abeed yay, domin baya jin zai iya cewa komai, infact ko bacci ba zai iya ba, he can't sleep serious, wajan ƙarfe biyu na dare Dattijon ya haɗe kayansa kaf, yaja Abeed zuwa can wani ƙaramin gida bayan gidan Sarautar... Washegari da safe Masarautar Zahel ta cika sosai, sbd bikin addu'ar da Za'ai domin ƙara wa masarautar Zahel tsaro, baka jin komai zai kaɗe kaɗe da raye raye, ta ko'ina bokaye ne suke shigowa cikin Masarautar, ƙarfe 10 daidai Sarki Mabus ya bada umarnin a rufe ƙofar shigowa cikin Zahel. Time ɗin Abeed na tsaye, shida Dattijon yana basa memory, cikin tashin hankali Dattijon yace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, munyi sake" Abeed ya juya fararen idanunsa alamar "what happened?" Dattijon yace "Shi ke nan, idan ba Allah ne ya rufa maka asiri ba, ka shigo Zahel ke nan, domin an bada umarnin a rufe ƙofar shigowa Zahel, babu kai babu tafiya kuma suna ganin motarka zasu ƙone ta" shiru Abeed yay, shi sam baya damuwa dan ya mutu ko an kashe sa, yasan JAHADI ne, kuma silar hakan sai ya samu NOOR a kabarinsa.. a zuciyarsa yace "what should I do now???..." Dattijon yace "baka da wata mafita kawai, ka shirya matsayin bokan mu shiga cikin Masarautar, akwai wata ƙofar sirri sai ka fita ta wajan" cikin few minutes Dattijon ya shirya Abeed cikin wasu kaya gaba ɗaya kamannin sa suka ɓata, daidai lokacin da ake ƙoƙarin Sanarwa a rufe ƙofar shigowa cikin Masarautar Abeed ya sauko ƙafarsa ta dama ciki, mai rufe ƙofar ya dakata yabi Abeed da wani irin kallo, bai dai ce komai ba, Dattijon ya biyo bayan Abeed kana aka rufe ƙofar.. shigowar Abeed cikin Masarautar yay daidai da lokacin da Sara take zaune akan wata kujerar mai azabar kyau, tun bayan abinda ya faru bata cewa komai, ta manta yadda ake komai, Sallah, azkar, karatun Alkur'ani she forgot everything, ga wani tsoro daya ɗarso a Zuciyarta, yanayinta ya sauya ta koma kamar wata zautacciya. Ji tayi ƙirjinta ya buga, da sauri ta miƙe tsaye tana dame kanta tare da faɗin "Abin bauta kabas ka taimake ni" ta faɗi hakan yana zame wani mayafi da yake jikinta, ya rage daga ita sai wani kaya wanda ya rufe mata kirji zuwa waist nata, ji tayi kamar ana janta zuwa wani waje ana kiran sunanta, fararen ƙafafuwan ta, ta ɗaga ta fara tafiya da ɗan sauri, har ta ƙarasu wata ƙofa data gani a rufe, Cak ta tsaya tana bin ƙofar da kallo tana tunanin ta ina zata buɗe ta. Babban boka ne ya kalli Mabus yace "daidai yanzu ya dace ka kwanta da yarinyar nan, domin samun albarkar abin bauta kabas" miƙewa tsaye Mabus yay yana jin wani irin farin ciki a zuciyarsa, abinda yake kwaɗayin samu yau gashi cikin sauƙi zai samesa, kai tsaye ɓangaren daya ajjiye Sara ya nufa... Sairah ce tsaye tun safe take wajan bayan fitar Gimbiya Noro wajan addu'a, samun kanta tayi da son fita domin shan iska tana son ganin yadda Masarautar Zahel take, wani ƙyalle da yake kanta ta jawo ta rufe fuskarta dashi, cikin sauri ta fito cikin farfajiyar masarautar ta fara tafiya, kanta a ƙasa tana tsaka da tafiyar taji tayi karo da ƙafar mutum, cikin sauri ta ɗaga kanta nan take sukai idanu huɗu da Sarki Mabus, wanda tunda ta shigo masarautar bata taɓa ganinsa ba, Sarki Mabus kuwa mamakin yadda akai ta fito yake, domin a tunaninsa Sara ce, nan kuwa Sairah ce, bai ce mata komai ba ya kama hannunta zuwa sashinsa, yayinda tsoro da fargaba ya hana Sairah cewa komai.... Dattijo ne a gaba sai Abeed suna tafiya da sauri gudun kada su sake makara, gashi hanyar da zasu bi dole ta sashinsa Sarki Mabus ne, cikin ikon Allah har suka ƙaraso sashinsa ba wanda ya gansu, suna ƙoƙarin buɗe wata ƙofa, kamar daga sama haka Abeed yaji saukar muryarta, tana faɗin "Twin.. Twin.. Twin" kalmar da take faɗa ke nan, Zain ya faɗo masa a rai, domin wani lokacin haka yake ce masa “Twin” Cak ya tsaya tare da ɗan juyawa ya kalli Ƙofar, zuciyarsa na tsananin bugawa wacce bai san ko tame bace, Dattijon yace "Babu da lokaci ka taho mutafi, mun kusa ƙara sawa ƙofar" Abeed kamar me neman wani abu na shekara da shekaru haka yake bin ƙofar da Sara take bugawa da kallo, kamar zaibi Dattijo sai kuma ya tsaya, ganin kamar Abeed ba zai taho ba yasa Dattijo ya shiga jansa da ƙarfi, sun kusa kawai ƙofa Sara ta saki wata ƙara tare da faɗin "Twin" Abeed bai san lokacin daya hankaɗe Dattijon ba, cikin sauri ya nufi ƙofar yana zuwa ya sanya ƙafa ya daki ƙofar nan take buɗe tana shirin faɗawa kan Sara yay saurin riƙe wa, a tsugune ya sameta ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, gashinta duk ya baje ya rufe mata gefen fuska, wata faɗuwar gaba ce ta ƙara saukarwa Abeed wacce ya daɗe bai samu kansa a ciki ba, cikin sauri ya dafe ƙirjinsa yana faɗin "Ya Salam!" Ya ɗan jima a haka, idanunsa kuma ƙuri a bayan Sara, Sara jin kamar mutum a kanta yasa ta ɗaga jajayen idanunta kai tsaye idanunta ya faɗa cikin na Abeed, cikin sauri Abeed ya janye idanunsa, a lokacin nan wallahi Numfashinsa kusan ɗaukewa yay, he can't believe abinda yake gani yanzu, juyawa yay har yana shirin faɗuwa da niyyar barin wajan, Ya Rabb, da ƙyar Abeed ya samu ya tsaya da ƙafafuwan
sa, saboda wata iriyar rungoma da Sara tayi masa ta baya, tare da kecewa da kuka tana faɗin "Twin" jarumta ya arowa kansa, ya ɗan sanya hannunsa tare da zameta daga jikinsa, sam yaƙi yadda ya ƙara kallonta, Dattijo da yake tsaye yana kallon ikon Allah, domin kallo guda yaywa Sara yasan cewa sato ta akai, da sauri Dattijon yace "maza ɗauko ta, wlh sato ta akai" girgiza kai Abeed yay, yana ja baya abin mmki yana ja baya Sara na ƙara matsawa wajansa, a wannan karan gaba cakumesa tayi tana ɓoye fuskarta a ƙirjinsa tana kuka kamar ranta zai fita, ganin cewa shima a yanzu komai na iya faruwa dashi ya sanya ya hankaɗe Sara daga jikinsa, yana zuwa baƙin ƙofa Dattijon yace "Ai kuwa ina tunanin itace wacce Mabus zai

Please Login or Register in order to submit comment