Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara kallon Abeed dake zaune yana kallon ruwan dake zuba a wajan, ɗaya budurwar tace "He's very arrogant.." Miƙewa tayi tsaye tare da nufar inda Abeed yake tana zuwa taje kujera ta zauna tace "Hi, my name is Nusaiba some people call me Nusy" ta faɗa tana masa fari, Cork ɗin daya sanya a kawo masa ya kalla, Miƙewa yyi tsaye tare da zube kuɗi ko shan Cork ɗin bai ba, Nusy kam ko inda take bai kalla ba, ya juya tare da ficewa daga cikin wajan, da kallo Nusy ta bisa tace "Finally nasan zaka sake zuwa na jima ina nemanka. Gidansa ya koma ya rasa Meke masa daɗi zuciyarsa duk a cunkushe ga wani abu dake damunsa wanda bai san ko menene ba, kasa bacci yyi sai ruwa da yake ta sakarwa kansa. Washegari Da yamma Anuty Zulfa ta fito daga cikin bedroom ɗin ta hannunta riƙe da wani cup tana zuwa ta kalli Auta tace "Kira min Sara" Auta tace "Mami idan naje sai naga tana ta kallo na kamar bata taɓa gani na ba" Anuty Zulfa tace "Ko? To tashi" Miƙewa tsaye tayi tana zuwa bedroom ɗin ta samu Sara zaune tsakiyar bed ta haɗa kai da gwiwa gumi na yanko mata, duk jininta rawa yake, Auta tace "Saraa Mami na kira" Shiru bata ɗago ba Ta sake cewa "Sara" gently ta ɗago da kanta tana ɗan ya motsa fuska cikin rashin sakewa da son nuna ko ina kula tace "Who are you? Meyesa nake na ehee? Ina Sairah fa? Where's my sister?" Auta ta ware idanunta ganin yadda Sara tai mata kwarjini ya sanya ta fita da sauri tace "Mami, Sara tana tambaya wai wacece ni nan ina ne i think ta dawo hayyacinta" Mami tace "Are You sure Sara ce tace haka?" Auta tace "Eh Mami" ajjiye wayar hannunta tayi ta miƙe cike da ƙasaita ta nufi bedroom ɗin tana shiga taga Sara tsaye tana kalle kalle, wani irin Murmushi Anuty Zulfa tayi tace "Allhamdulillah, akwai inda ke maki ciwo ne?" Shiru Sara tayi kanta a ƙasa Anuty Zulfa tace "kina son wani abu ne Sara?" Fararen idanunta ta buɗe tare da kallon Anuty tace "Wace ke? Ina ne nan, ina Sairah" Anuty Zulfa ta kama hannunta zuwa Main Parlo tare da zaunar da ita tace "Auta ɗauko min ruwa mai sanyi" Auta wajan deep frizeer tace ta ɗauko bottle water tare da cup, amsa Anuty Zulfa tayi ta zuba ruwan ciki ta bawa Sara tace "drink" ba musu ta amshi ruwan ta sha, ajjiyar zuciya ta shiga saukewa tana jin sanyin ruwan na ratsa mata zuciya ganin ta fara dawo nutsuwar ta tace "Sara ki kwantar da hankalin ki Nima kamar uwa nake wajanki, abubuwa sun faru wasu zaki iya tunawa wasu kuma a'a, Amma allahamdulillah accepted Yourself the way you're be kind yourself ok" kai kawai Sara ta ɗaga tana rufe idanunta domin samawa kanta nutsuwa, jin kiran Sallah yasa Sara ta miƙe Anuty Zulfa tace "ina zaki?" Murya a sanyaye tace "bacci zan" shiru Anuty Zulfa tayi kafin tace "Ki bari zuwa anjima sallar Asr ta kusa" jin an ambaci sallah yasa kan Sara ya buga, kafin kowa yyi mgn Anuty Zulfa tace "Yaushe misturation period yazo maki?" Da mmki Sara ta kalli jikinta wani irin runtse idanunta tayi gam sbd kunya ita bata sanin wannan abun ba, sbd bata taɓa yi ba a rayuwarta ki shine yasa tun safe take jin ciwon ciki da kuma amai? Anuty Zulfa tace "Muje ki wanke jikinki" shiru kawai tayi tabi bayan Anuty Zulfa ruwa ta haɗa mata tayi wanka kana ta gyara jikinta, tana fitowa kuma zazzaɓi ya kamata dauriya kawai tayi ta fito parlon kowa kallonsa kawai take, tana zaune ita ɗaya a parlon taji shigowar mutum cikin parlon ga wani ƙamshin Hugo boss daya daki hancinta, idanunta ta rufe tana jin Ƙamshin har ƙasan Zuciyarta, Abeddeen dake tsaye bakin door way ya ware fararen idanunsa akan Sara wacce yyi mmkin sauyawarta, jin ana tsaye ba'a shigo ba ga kuma alamun idanun mutum a kanta yasa Sara ɗaga kanta kaɗan ciki Sa'a suka haɗa ido yana tsaye cikin wani voyel mai masifar kyau gashi fari tass, mai manyan zane sumar kansa a kwance da sauri ta ɗauke idanunta tana mayar wa kan t.v tana wani kame fuska, taɓe bakinsa yyi kana walking slowly ya ƙarasa cikin parlon tare da zama kan kujerar dake farcing na Sara, ita dai tunda ya zaune kanta yake ƙasa shima bai ƙara kallon inda take ba, a haka Anuty Zulfa ta fito daga bedroom tana ganin Abeed ta haɗe fuska ta zauna saman kujera, ganinta yasa Abeed shafa kansa yace "Evening Mami.." banza tayi masa Calmy yace "Kina Lfy?" A fusace tace "kaji labarin nayi ciwo ne Abeddeen?" Shiru yyi mata Auta tace "Yaa Abeed wlcm" kai kawai ya ɗaga mata, a hankali Sara ta ɗaga kanta ta saci kallon Abeed ido suka haɗa ya ware mata manyan idanunsa, da sauri ta ɗauke kanta tana haɗe fuska ita ta rasa inda ta taɓa jin sunan Abeed, A hankali Anuty ta juya ta kalli Abeed ganin yadda ya ɗan faɗa tace "Kana shan maganin ka?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, tace "To ramar tame ce?" Shiru yyi mata kame fuska yyi yace "Ke tashi muje" Anuty Zulfa tace "Ina?" Kansa ƙasa yace "Naga she's feeling much better" Anuty Zulfa tace "Ko? Zaka iya tafiya kai idan kaso daman ba wani ya kiraka ba" tana faɗin hakan tace "Sara tashi kije ki kwanta" kamar jira Sara take ta miƙe tsaye sai a lokacin ya lura da riga da wando na Gucci brkwny dake jikinta, ta ƙara hasken da kyau, a hankali take tafiya har zuwa cikin bedroom ɗin su, Auta tace "Yaa Abeed bari na kawo maka Lunch" girgiza kai yyi tare da Miƙewa yyi waje abinsa, Ta window Sara take binsa da kallo yadda yake tafiya cike da kamala, yana cikin tafiya yaji kamar ana kallonsa juyawa yyi da sauri Sara ta saki labulan windown tana jan numfashi, motarsa ya shiga yabar gidan yana jan tsaki.

Amma zaune ita da Du'a a Parlo, Daga sama sukaji ance "Ban taɓa sanin na haifawa duniya salamamme ba sai yau, wlh sai na ɗaga maka nono kowa ya huta, hooooo wannan masifa har ina? A'a wlh bari nazo naji kan zan can" Amma ta kalli Naila tace "Naila ke dawa kuma?" Naila tace "A'a ba ruwanki, wannan kass ɗin pamili ne, ke kuwa ba dangin iya balle na baba sai ba zumuncin Allah da kuma kasancewar ki matar wannan mai rawanin" Amma tace "To kiyi hqr" Naila tana zama tace "A to, ai kin nemawa Kanki lafiya wlh yanzu sai na kullaceni ki kina shiga sabgar da bbu ruwanki mu a zamanin mu babu ruwa da kowa, kiji na faɗa maki kowa harkar gabansa yake" Cike da nutsuwa da tarin kamala Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ya fito daga shashinsa Naila na ganinsa tace "A'a kama miƙe nan ba fada bane zuwa nai ka faɗa min ina shalele yake?" Zuciyar Abba ta buga yace "Bai zo yace mki yana tafiya ba?" Tace "A'a wlh bani da labari kai bari kaji nifa ba zan lamunta ba, daman zuwa nai nace duk inda yake kada ya sake ya auri wannan Yarinyar Rariya yarinya har yanzu an rasa meke damunta kullum take a rame, to dan Allah haka kurum ta shafa masa wata muguwar cutar yarinyar da bata ganin kowa da gashi" ajjiyar zuciya Abba ya sauke yace "Ayyya, daman ke kikace ayi" afusace tace "To da nace ayi sai kuma kuka biye min? Ni baka san barkwanci ne dani ba, to idan nayi ba sai ya sake ta Alkur'an ba zan yarda ba" Amma tace "Ai ba'ai ba, tayaya za'ai baki sani ba?" Naila tace "Hoooooo, a yadda duniyar nan ta lalace ai sai ayi ban sabi ba musamman idan akwai ruɓaɓɓu a cikin Mgnar" ta ƙare zan can tana kallon tace "To ke har yanzu cikin bai samu bane? Kullum sai kuɗewa kike kamar wata kabewa to ai ba kyau irin wannan farin na kawo maki ai tagargaje" Murmushi kawai Du'a tayi. Da daddare Dua na tare da Zain da yake cewa "Beb gobe zamu tafi" marairaicewa tayi sosai tace "To wai dole ne, kai da kke Barister mene haɗin ka da shiga cikin criminal case hk? Kaifa kawai Shari'a ce taga kabar state Cid suyi aikin su" Kallonta yayi yana jan rigarta yace "Au hb, idan ina son tara hujjoji da yawa masu amfani dole naje naga wani abun da idanu na 2days kawai zan fa" tace "To Allah ya kaimu, zanta maka addu'ar neman samun Sa'a wajan Ubangiji" hancinta yaja kafin a hankali kuma ya ɗura bakinsa kan nata ya shiga yi mata wani kiss mai tsayawa a zuciya. Ummi ce ta kalli Riya tace "Ai munsha wahala sai dai Allah ya kare" Riya tace "Uhm, Ummi na fiki shan wahala wannan malamin bashi da imani kinga abinda ya dinga yi min na ɗauka mutuwa zan, ban taɓa jin wahalar saduwa da wani namiji ba sai a kansa" Ummi tace "Ba gashi dai anyi an gaba,kuma ya tabbatar aikin ya shiga jikinsa" Riya tace "SPIDER nake jira dazarar ya gama zai faɗa min inda Abeed yake"........ After 10mnt da Abeed ya bar ƙasar New York zuwa Cairo, rabonsa da Sara kuma tun zuwan da yyi gidan Aunty Zulfa. Fitowar wasu ke nan daga lecture a Columbia University School of Law: New York City, Auta ce ke tafiya tana cewa "Sara wannan sabon Malamin sai kallo yake anya bbu abu a ransa" Wacce aka kira da Sara ta ɗaga manyan idanunta ta kalli Auta ba tare da tace komai ba, a haka suka isa gaban mota zasu shiga daga bayansu suka ji ance "Assalamu alaikum" Auta ta juya Sara kam ko tsayawa ba tayi ba sai ma buɗe ƙofar mota da tayi zata shiga, Auta tace "wslm sannu" yace "kun gama lectures ne?" Tace "Eh" yace "Ok, sunana Yarima Yashim Al'khasim Abubakar Wahab, may i knw your name?" Auta tace "Why not" sannan ta faɗa masa yace "Ok sister taki fa?" Auta tace "Wa?" Yarima Yashim ya ware idanunsa yace "Gata can, ng kamar haushina ta keji" Auta tayi dry tace "Ita bata sanka ba, kawai hk take bata da mgn" Yace "I see, her name please" kafin Auta tayi Mgn daga bayansu akace "Saraaarh Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas....


Zain Abeed isn't free contact to subscribe please 08119237616

Yanzu zamu fara wasan🤘🏼sannu a hankal[08-15 08:45] +234 703 831 1110: *27 Nimcyluv*
Juyawa sukai domin ganin mai mgnar, Auta tai murmushi tace "Mami, where are you here?" Mami dake rufe mota ta ƙarasu wajan idanunta akan Yarima Yashim daya ɗan sunkuyar da kansa ƙasa, Kallonta ta bayar kana Auta tace "Kun gama lectures ne?" Auta tana amsar bag ɗin hannun Mami tace "Eh, Mami me kikazo yi?" Kafin Anuty Zulfa tayi mgn Yarima Yashim yace "Barka Mami" Anuty Zulfa tace "Kana lafiya?" Yana shafa kai yace "Allahamdulilla, bari naje" kallon gefe tayi sai kuma ta kalli Sara wacce take gaban mota wajan driver tace "Oh! Sorry na ƙatse ka" yace "Babu komai" ya faɗi hakan yana satar kallon Sara yaga ita kanta a ƙasa take tana duba wani littafin turanci na _Past perfect_ Juyawa Yarima Yashim yyi zuwa wajan motarsa, yana tafiya gently Sara ta ɗaga kanta tare da juya fararan idanunta a hankali kuma ta zuro fararen ƙafarta dake cikin wani takalmi hill, jikinta sanye cikin wata sky blue ɗin Abaya tayi rolling kanta da veil ɗin kamar wata balarabiya, fuskarta ɗauke da wani kwantaccen Murmushi daya sanya manyan dimples ɗinta lomawa, ta ƙarasa wajan Anuty Zulfa tana ɗan Shagwaɓewa sai ka rantse ita ce Autar Anuty Zulfa tace "Wlcm Mami...Mami kin siyo min Chocolate ɗin?" Anuty Zulfa tace "Jama'a na shiga uku, Sara bakya girma ne?" Murmushin kawai Sara ta yi bata ƙara cewa komai ba, Auta tace "Mami ni kuma perfumes ɗina sun ƙare i need more..." Anuty Zulfa tana kama hannun Sara tace "Oh..Ok yanzu dai akwai wanda nazo gani we will take idan na dawo gida ok, waye zai driving naku?" Auta tace "Mami na gaji ni dai" Anuty Zulfa ta kalli Sara da key ɗin key hannunta tace "Ayi driving a hankali my dear" idanunta kawai Sara ta lumshe tare da buɗewa, kana ta nufi wajan driver, Auta ta shiga tana having na Anuty Zulfa, suna shiga motar Sara ta ɗan ya motsa fuska kafin tayiwa motar key, a hankali ta fara juya string motar driving ta fara cikin nutsuwa suna haurawa saman titi Sara ta warware rolling na kanta ta ajjiye vail ɗin can gefe kalbar dake kanta ta sauka har bayanta da gefen fuskarta, Auta tace "Daman kasan saikin cire, mene yasa baki son rufe kai ne?" Murmushi kawai Sara ta yi ba tace komai ba, Auta tace "Saura ɗayan" Sara na kunna wata slow song mai daɗi ba tare data kalli Auta ba cikin kamilalliyar muryarta tace "Uhm... Gulma" Auta tace "yanzu ba gashi Kinyi mgn ba, nikam ina son tambayar ki Sara" sai a wannan karan Sara ta juya tare da kallon Auta na few seconds kana ta maida kanta zuwa kan titi, Auta tace "Mene yasa kike son waƙa?" Wani cute smile Sara tayi tana juya idanunta sosai akan titi muryarta na fita sbd waƙar da take bi, ita dai bata kula Auta ba, har suka kawo gaban haɗaɗɗan gidan nasu, Horn tayi gatekeeper ya buɗe musu gate ɗin, bayan sunyi parking a parking space Auta ta fara sauka kafin Sara ta ɗauki kayanta Vail ɗin ta riƙe a hannunta, tana wani irin tafiya mai cike da nutsuwa idan ka ganta sai ka ɗauka iyayi ne but babu iyayi ita ɗin ce a haka.... Misalin 10 na dare jirgi ya sauka a airport, a hankali mutane ke fitowa daga cikin jirgin, wajan 10 minutes da saukar jirgin kafin a hankali ya miƙe daga kan kujerar da yake, yana sanye da Slim Fit Suit ga wani ƙamshin Hugo boss dake tashi a jikinsa, sumar kansa ta ƙara yawa sosai, domin har kusan rufe masa ido take daga baya kuma har lilo take kamar ta mace, yana fitowa Danish ya fito ɗauke da kayansa, a hankali yake tafiya yana jan numfashi rabonsa da New York wata goma ke nan, ya tafi cikin fushi da ƙunci wanda bai san na mene ne ba, gaban wata Chevrolet Silverado ya tsaya fuskarsa kame yana kallon Khabeer, jikin Khabeer har rawa yake wajan bawa Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas key ɗin motar, amsa kawai Abeed yyi ba tare da yace komai ba, ya buɗe murfin motar ya shiga da wani irin gudu yaja motar da ƙarfi yabar cikin airport ɗin, da kallo kawai Danish yabi bayan Abeed baya jin daɗin halayyar sa a yanzu. A gudu yake sosai a motar yana tafe yana cire jacket ɗin jikinsa, yabar singlet ɗin ciki, idanunsa jajurr yana jan wani irin numfashi a haka ya ƙarasa wani Paul’s Casablanca, lokacin daya isa wajan 11 saura, a entrance ɗin club ɗin yaga wasu zafafan motoci duk haɗuwar su bata kai tasa ba, ko a kuɗi kashe motar yyi shi kansa bai san meke damunsa bai san wanne kalar abu ke jan ragamar rayuwarsa ba, wani lokacin ji yake kamar yyi kuka sbd ƙunci da baƙin cikin yadda rayuwa ta juya masa salon ƙaddararsa, fesar da numfashi yyi mai zafi kafin gently ya buɗe murfin motar ya zura da ƙyakkyawar farar ƙafarsa zuwa waje, ƙarasa fitowa yyi yana kame fuska key ɗin motar ya sanya cikin Aljihu tare da ɗaukan Wayarsa walking slowly yake nufar cikin hotel ɗin, wanda gaba ɗaya sautin kiɗa ya sanya ba'a jin Mgnar Mutane, iya haɗuwa ya haɗu matane kala kala masu ajin gske yawancin su da skirt iya gwiwa, sai wata riga wacce bata shige half vest ba, rabin ƙirjinsu duk a waje, yana shiga gaba ɗaya maza ta matan wajan suka miƙe suna Kallonsa tare da nunasa da mmki, domin babu wanda ya tsammaci ganinsa a yanzu, kansa a ƙasa tunda yyi musu kallon farko ya ɗauke kai, can ciki ya shige waje mai kyau mara hayaniya yana zuwa ya zauna saman Kujera idanunsa a lumshe kafin ya buɗe ya shiga danna Wayarsa ringing wayar ya fara yaga sunan Dr Adyan kamar ba zai picking ba sai kuma ya ɗaga yana saita bluetooth ɗin kunansa, daga can ɓangaren Dr Adyan yace "Akan na faɗa maka Gsky kaji haushi ko? Nasan ba kai tunanin ganina a Cairo ba, wlh Abeed idan wani yace min kai ne kake abinda kake yanzu sai na kaishi ƙara" shiru Abeed yyi yana ɗagawa wani ma'aikacin wajan hannu tare da yi masa alama ya kawo masa abin sha, Dr Adyan yace "Tunda baza kaji ba, zan kira Zain na faɗa masa komai tare da inda kke zaune" Calmly cikin kamewa fuska Abeed yace "idan kayi hk babu ni bbu kai har abada Adyan..." Yana faɗin hakan ya kashe wayar, ma'aikacin yana cikin shiryawa Abeed abin sha Nusy ta ƙarasa wajansa tace "Hi" Ma'aikacin yace "Hi Ms Nusy" da hannunta wanda yasha farce tace "Me yace ka kawo masa?" Yace "Galaxy Mini Wine Rack" Murmushi tayi tace "ka kai masa Whiskey" da mmki Ma'aikacin yace "sorry Maaah, i can't do it.." jakarta ta buɗe ta ɗauko kuɗi mai yawa ta ajjiye masa, cikin sauri ya ɗauke kuɗin yana sauya abin shan Abeed zuwa Whiskey (Alcohol). Wajanta ta koma cikin friends ɗinta, Abeed na zaune Ma'aikacin ya kawo masa Whiskey ɗin wacce bai tunanin ita bace, ya jima kafin ya ɗauka yana ƙare mata kallo yana juyata a hannunsa, a hankali ya nufi bakinsa da ita nan take ya ajjiye sbd warinta daya daki hancinsa, runtse idanunsa yyi sosai da sauri kuma ya kifa kansa yana jan numfashi, a hankali daga samansa akace "Hy Singer" shiru bai ɗago ba Nusy ta zauna kusa dashi tana ɗura hannunta akan cinyarsa Abeed da wani kalar sauri ya ɗaga kasa sbd wani masifaffan abu daya ratsa masa zuciya abinda bai taɓa jinsa ba ke nan iya kacin rayuwarsa, ya jima yana kallon Nusy frm head to toe kafin ya wani kalar sanya hannunsa ya ɗauke ta mari yana huci kuma ya tashi kamar walkiya yabar cikin wajan bayan ya ajjiye kuɗi mai yawa, gaba ɗaya guys ɗin suka fara mata dry baƙin cikin duniya ya kamata itane ne gayan nan zai mata haka? Wlh idan har tana raye sai ta rama abinda yyi mata. Abeed na fita ya shiga motarsa tare da barin wajan kamar zai tashi sama, sam bai ba lura da wata mota dake bin bayansa ba har ya shiga cikin gidansa, da ɗan sauri yake tafiya yana zuwa ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa sai numfashi yake fitarwa ga wata azaba daya keji a mararsa ya rasa mene yake so mene kuma yake buƙata, baya iya bacci sai ya haɗa da maganin bacci, kwanciya yyi abin tausayi tare da yin lamo saman bed, jin mararsa ta ƙara murɗawa har Abeed ɗinsa na ƙoƙarin Miƙewa ya sanya ta sauri ya miƙe ya nufi bathroom ya ƙara sakarwa kansa shower, ga Asthma bata son sanyi data takura abin duniya duk ya damesa sai wajan 3 bacci ya ɗauke sa, yana ji ana sallar Subhi amma bai iya tashi ba...

Zain ya kalli wani ɗaya ɗaya daga cikin state Cid ɗin da suke tsaye a ƙofar shiga Masarautar Zahel, yace "Sau uku ke nan muna zuwa prvt investigator ɗin mu na shaida mana Sarkin baya nan" Jabir yace "Ba zamu saki mu shiga ba" Zain a hankali cikin nutsuwa yace "But Why?" Jabir yace "Mutanan Masarautar Zahel basu da imani suna iya yanka mutum ba, kafin shiga dole mu tabbatar Sarki Mabus yana nan idan sunga shi muka kama da kansa babu abinda suka isa suyi mn" Zain yana ware idanunsa sosai yace "You're right.." har zai juya sai kuma tsaya domin kamar daga sama yake ganin wata kamar Sara, Subash ya kalli Sairah yace "Ba zaki iya aure na ba?" Girgiza kai Sairah tayi tace "Ba zan iya rayuwa a nan ba, ina buƙatar barin Masarautar nan" shiru yyi mata kafin can yace "Ok yanzu Sarki baya nan zamu fita ai" tace "Har kai?" Yace "Zan biki, domin rabauta kince idan har sbd ina son na aureki na keson musulunta Gwamma ban musulunta ba, idan na biki kuma zanta ganin yadda kike wannan dunguran har Abin ya zauna a Zuciyata" Cikin nutsuwa Sairah ta kalli Subash tace "Salla ake cewa" yace "Ohh, afuwa" tace "Never mind" ɗago kan da zatai idanunta ya sauka Zain wanda take tunanin Abeed ne, da wani irin sauri tayi bayan subash hankali tashe a Zuciyarta tana tunanin ko Sara ce ta gudu yazo zai kamata? Ko ita tace masa ba ita ta caka masa wuƙar ba?" A karo na farko Subash da yaji mace ta riƙe masa jiki da kansa ba shine ya nemi hakan ba,sai hakan ya haifar masa da wani irin sabon yanayi a jikinsa, sakinsa tayi yace "Menene?" Girgiza kai tayi tana ƙara kallon ƙofar ga mmkinta bbu kowa, to ko gizo yake mata ne? Subash yace "Na rantse da abin bauta kabas babu wanda ya isa ya cutar dake" Sairah tace "Abin bauta kabas ɗin banza? Dukkan wata kariya tana wajan Ubangiji, shine yake da ikon bani kariya a lokacin da yaso, iko,isa, mulki ta ƙama duk tana wajan Ubangijin talikai Ubangijin daya hallici mutum da aljan, yayi duniya da abin ƙawa haka kuma ya halicce lahira da abin ƙi" da mmki Subash yace "Kamar ya duniya da abin ƙawa lahira da abin ƙi?" Murmushi tayi tace "Akwai lokaci zan faɗa maka" tana faɗin hakan tayi gaba da sauri zuwa sashin da take, Subash kuma ya fita da kallo so dana ƙauna... A rikice Zain yace "Bana ko tantanma Sara ce wannan, ke nan aljanun nan suka dawo da ita? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yaya zanyi yanzu, Wlh ba zan iya barinta a nan ba" Jabir yace "Look Zain, zamanka a nan hatsari ne ka bari muyi shiri baki ɗaya sai muzo kawai" shiru kawai Zain yay can kuma yace "Ok" mota suka shiga tare da barin Zahel baki ɗaya....... Kasancewar yau weekend ne babu shcl yasa duk suna gida, Sara na zaune bedroom ɗin ta daga ita sai vest da wanda 3Qauter hannunta riƙe da ice cream tana sha, sai kuma game ɗin da take jikin system, Mami ce ta Turo ƙofar bedroom ɗin ta shigo Sara ta ɗaga fararan idanunta ta kalli Anuty Zulfa, Anuty Zulfa tace "Sara ba zaki shopping ɗin ba?" Kai kawai Sara ta ɗaga tare da yin Murmushi alamar Eh ba zata ba, Anuty Zulfa tace "Ok ki fito Parlo,kafin mu dawo zuwa anjima" A hankali cikin nutsuwar ta Sara tace "A dawo lfy Mami" Murmushi Anuty Zulfa tayi tace "A tawo maki da chocolate da kuma Ice cream?" Sara ta miƙe tsaye Anuty Zulfa tana mmkin yadda kullum jikin Sara ƙara buɗewa yake, Tace "You're right Mami..." Juyawa Anuty Zulfa tayi ta fita tana faɗin "Ok dear Kada ki zauna da yunwa" kai ta ɗaga bayan Anuty ta fita Sara ta shige bathroom shower tayi har lokacin kuma bata sallah, da Anyi mata Maganar ranar babu wanda zata kula har dare, wanka tayi daman ta safe sukaje wajan Saloon aka maita wata sabuwar kalbar manya masu kyau aka saka bit, fitowa tayi tana Ƙamshin shower gel, wani Body oil ta shafa kafin ta ɗauki Teyana wide-leg trousers da Silk short robe wacce ta kama ta, amma tana da faɗin wuya da siririyin hannu, jikinta na Ƙamshin Valentino, slippers ta saka kanta babu komai ta nufi Main Parlo, jikinta na wani irin motsawa, tana zuwa parlon taji ƙamshin Bois elite yana shiga cikin hancinta babu wanda yake amfani da perfume ɗin a gidan hakan yasa ta shiga ware idanunta, a zaune ta gansa kan kujera sanye da Paisley tank top, da Tracksuit trousers ya ɗura ƙafa ɗaya kan table idanunsa akan Wayarsa dake dannawa, Jikin Sara ne ya ɗauki rawa domin duk ƙarfin zuciyar mutum taga Abeed sai Zuciyarta

Please Login or Register in order to submit comment