Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kallon ta, kafin Calmy yace "Su waye?" Tace "A can gida ne, ina fitowa suka ɗauke ni a mota suka kaini wani gida a can ma na kwana" ya ware idanunsa domin bai ɗauka da gske take fa yace "kika kwana tare dasu?" Ta girgiza kai tace "A'a" yace "to yane?" Tace "A bedroom na kwana" Abeed na haɗe fuska yace "na ɗauka kitchen ne" ta kallesa taga ita ɗin yake kallo, shiru tayi ganin ba zatai mgn ba yasa yace "Uhm inaji gantali kike a can gida ke nan?" Ta girgiza kai hawaye na zubo mata tace "A'a, shine gari na wayewa fa suka kawo ni wajan jirgi naji suna waya da wani wai idanuna zaiyi tsada gashi nan manya" Yace "To suna ina?" Tace "A nan waje suka zauna" shiru kawai yyi kafin can yace "To kowa ai idanun naki za su yi kuɗi" ta zare ido tace "Idon nawa" yace "A'a nawa, ai gwamma su siyar kowa ya huta ko?" Tana sakin kuka tace "To dame zanna gani?" Banza yyi mata baice komai ba, yana jinta tayi ta kuka sai can bacci ya ɗauke ta, Abeed kam mmki ne ya kamasa dama har yanzu a duniya akwai masu satar mutane su cire masa wani abu?. Ma'aikaciyar jirgin ta shigo ta tambayi Abeed me za'a kawo masa hannunsa riƙe da jarida yace "fruits.." tace "And what..." Ya ɗan sha kuno yace "Just" tace "Ok Sir" har ta juya ya tuna da sarkin ci yace "Wait..." Tsayawa tayi yace "Ki haɗa da wani mara nauyi haka" tace "Ok Sir" fita tayi ba jimawa ta dawo ɗauke da try, lokacin Sara ta farka daga baccin har wani zazzaɓi taji yana kamata, Abincin tabi da kallo kafin ta kallesa taga ko inda take baya kallo yama sauya kujera, shiru tayi tai masa ƙuri da idanunta, har ya kama shan oranges ya fara shan watermelon bai kalleta ba, sai da yasha duk fruits ɗin Banana kawai ya bari, juyawa yyi yana goge bakinsa da tissue suna haɗa ido ta ɗauke kanta yace "Zo nan" Miƙewa tayi tana zuwa tayi baya zata faɗi yyi saurin riƙe hannunta, yace "Ke kina hauka?" Girgiza kai kawai tayi, ya saki hannunta yana faɗin "take this.." ya nuna mata plate ɗin chips da egg, ɗauka tayi ta koma inda take, bata wani ci da yawa ba ta ajjiye ta sha ruwa, juyawa Abeed ya ɗauke kansa da sauri yana taɓe fuska, Miƙewa tsaye yyi ya nufi toilet, wajan 5mnts ya fito yana goge hannu lokacin ana sanarwar a saka belet jirgi zai sauka, wajansa ya dawo ya zauna ya ɗaura belet, Sara kuma tayi raurau da idanu kamar zatai kuka tace "I'm scared,zanyi amai" fuska ɗaure yace "Tsoro kike?" Ta ɗaga masa kai yace "To Allah ya ƙara" kuka ta saki tace "Please na riƙe ka" ya ware idanunsa waje yace "Sai kin riƙe ni zaki daina jin tsoran?" Ta ɗaga masa kai, kallonta yyi can yace "To bisimillah" ya faɗa da wasa Sara da sauri ta sanya hannunta cikin tafin hannunsu tare da maƙale fuskarta a shoulder ɗin tana wani sakin numfashi na tsoro. Kallonta yyi sai kuma ya ɗauke kai yana faɗin "Saura kimin hauka, duk abinda ki kaji nace kawai Kice eh, understand?" Tana maƙale dashi Zuciyarta na bugawa kamar yadda tasa take ta ɗaga masa kai, shiru yyi mata yana jin yadda take fidda numfashin tsoro.


Jirgin su ne ya sauka a Newark Liberty International Airport. Dake New York, rufe idanuna yyi yana jin yadda jirgin ke sauka a hankali ya ɗan jijjiga, kafin ya fara tafiya a ƙasan titin da aka samar domin shi, Ƙara ƙanƙame hannunsa Sara tayi tana sakin kuka ji tayi gaba ɗaya abincin da taci yana neman dawowa, baice mata komai ba har jirgin ya gama samun daidaito a ƙasa, kafin a hankali ya sauke ajjiyar zuciya yace "Mun kawo sake ni" girgiza masa kai tayi tace "Wlh tsoro na keji" haɗe fuska yyi yana tallafo fuskarta da tafin hannunsa ɗaya, ya nuna mata ƙofar windown jirgin yace "Look! Middle class" kallon sauran jiragen da suke wajan tayi kafin tace "Soma suna tashi?" Yace "A'a kwanciya suke" zame jikinta tayi daga kusa dashi, ya miƙe tsaye yana gyara zaman p.cap ɗinsa ya sanya mars ya rufe fuskarsa, ganin yana shirin fita domin tuni an fara fita, ta miƙe da sauri ta biyo bayansa, a ƙofar vip su kaci karo da Gaza yana faɗin "Come out young lady" haɗa idanun da sukai da Abeed ya sanya Gaza yin baya yana faɗin "Ohh! Sorry" juyawa Abeed yyi ya kalli Sara kana ya kama hannunta ya fara tafiya, Gaza yace "Hello ina zaka da ita Malam?" Abeed ya ware idanunsa kamar ba zai Mgna ba sai kuma yace "Kai ka Kawo ta ne?" Gaza yace "Of course Yes! Tare muke ai" Abeed yace "Ohh really" Ya faɗa yana kallon Sara yace "Saaaa, d u knw him?" Sara tace "I don't even know him" da mmki yake kallonta Ke nan hankalinta ya fara dawowa gashi na masa English, Gaza da mmki ya cika masa zuciya yace "Ke ba tare muka shigo jirgin nan dake ba? Waye wannan ɗin?" Securities ɗin jirgin da suke ƙoƙarin fita suka tsaya suna faɗin "What's going on here?" Abeed ya ɗaga kafaɗa, Gaza yace "I don't understand, tare muka shigo jirgi da ita, sbd bana son a takura ta na kaita vip, yanzu kuma ta fito tare da wani" wani mai suna Sunday yace "Is she your sister?" Gasa yyi shiru bai Mgn ba, Abeed da surutun ya ishesa yasan kuma dan basu ga fuskarsa bane yace "She's my wife, right wify?" Ya faɗa yana kallon Saraa, Sara dai tasan wife na nufin mata, kuma yace duk abinda yace tace haka ne, Ta buɗe baki cikin golden voice nata tace "he's my husband too" hancinta Abeed yaja, Sunday yace "what a perfect couple...." Abeed yace "arrest him, ya faɗi inda ya san matata" Wanda suke tare da Gaza yyi saurin barin wajan, Abeed kuma ya zaro card ɗinsa ya bawa Sunday, kana ya kama hannun Sara zuwa fita daga cikin jirgin yana riƙe da hannunta ɗaya hannun yana jan trolly bag ɗinsa, suna fita yyi saurin sakin hannunta tare da yin gaba zuwa wajan wata haɗaɗɗiyar mota datai parking gabansa, drivern mai suna Khabeer yace "Wlcm sir, ban samu ticket na zuwa Albany County ba, har a Online sbd hazon da ake da zubar snow, Typically, it starts to snow in New York in December and the snow season stops in early March. January and February are the two most likely months to have snow in New York. Amma haka nan yanayin ya fara sauyawa, jinjina kai kawai Abeed yyi ya shiga motar Sara ta shiga Khabeer yaja motar da sauri zuwa Albany County.
Amma ce zaune akan kujera tun ɗazo ake kiranta ta kasa picking call ɗin sbd tsoro, wani kiran ne ya sake shigowa a hankali tayi picking tace "Assalamu alaikum.... Anuty Zulfa" cikin faɗa tare da masifa Anuty Zulfa tace "Ba shakka Saratu, dole kiƙi picking call nawa, how dare you ehhh? Har ina kiranki kina sharewa" A sanyaye Amma tace "I'm sorry Anuty Zulfa, ina bacci ne" Anuty Zulfa tace "you're lying, bakya bacci a wannan time ɗin" Amma tace "Bana jin daɗi ne" Anuty Zulfa tace "And so what? Look Saratu ke baki da iko ne da gidanki? Har akan wata banza ki zubawa Mai martaba idanu ya kore ɗan da kika haifa? Kin san illar koran yaro daga gidan iyayensa kowa? Kin san me hakan ke nufi ehhh? Ciwo da baƙin ciki da kuma rashin kulawar iyaye zai iya sawa Abeed ya faɗa wani irin mugun hali, idan ɗan shaye-shaye Abeddeen ya zama kune, idan macinaci ya zama kune, idan ɗan fashi ya zama or kidnapper kone, billahi kada kiyi kuka da kowa Saratu, kiyi kuka da kanki mu dai ƴan uwanki mune komai naki banda Zain ya faɗa min da ko mutuwa Abeed yyi ba zaki faɗa ba, kin baida miji uwarki Ubanki banda faccala data saki gaba, akan banzar ƴarta, mu ba muna da yara mata ba muce ya aura mana? Amma auren yanzu ba'a haka musamman namiji ba'a masa auren dole, ni nasan har abada Abeed ba zai zo New York ba, domin yasan a can nake da zama" Kuka Amma ta sakawa Zulfa tace "What should I do Anuty Zulfa? Ƙirjina zafi yake nima ina buƙatar ɗana, da sanya hannu kin san ba zan taɓa cewa a kori Abeed ba, yana da naci, zuciya da lafiya haɗi da taurin kai abu ɗaya na sani ba zai taɓa ƙarya ba, no matter how worries he's, ban san ina zan samesa ba" Anuty Zulfa dake amsa gaisuwar Autar ta BIYA tace "Uhm, kuka yanzu kika fara sai kinga wani abu ya samu Abeed ma, so save ur tears" tana faɗin hakan ta kashe wayar duk da cewa tausayin Amma ya kamata amma idan ba haka tayiwa Saratu ba, b zata gane Allah ya fako ba, Zain dake tsaye yace "Amma ki daina kuka, kawai kiyi addu'a Ubangiji zai karesa Abeed baya layin mazan da zasu bi mata am sure" Tace "I hope so...., When zaku shige Zazzau ɗin?" Yace "Yau daddare a can zamu kwana Friday a ɗaura auren sai mu dawo" Amma tace "Har ita matar taka" yace "Ai mata zama matar ba Amma" harararsa Amma tayi tace "Ko? An gama gyara part ɗin maka an saka komai ba sai sunyi dakon kaya ba" Yace "Thank you Amma, amma ki daina damuwa idan kina damuwa ban san yaya zan ba, ina son nayi achieving goal ɗina musamman kane wancan azzalumin" tayi ƙasa da kanta tace "It's okay, Allah ya maka albarka a rayuwar auren ka" Ya shafa kai yace "Amma Abeed fa?" Tace "Allah yayi masa albarka ya kuma karesa" daɗi yaji sosai yace "Amin, you're a darling Amma" ya faɗa yana fita, Junaid ya samu a Main Parlo tsaye yana jiransa yana sanye cikin wasu fararen kaya masu kyau, yyi fresh dashi amma ya ɗan faɗa yace "Shall we.." Zain yace "Junaid ina kke son muje neman Sara? Bbu inda ba'a cigiya ta ba" Junaid yace "Ok bari naje hospital kafin time yyi mu shige gidan sirikan naka" yana faɗin haka ya nufi wajan motarsa tunani fal a ransa da yaji Ummi na cewa zasu Katsina me zasu yi a Katsina? Key yyiwa motar yyi waje yana addu'ar Allah yasa yaga ko mai kama da Sara ne. A can Albany County misalin 12:54 Abeed ne zaune a cikin babban gidansa dake New York, babu wanda ya san da zaman gidan, gida ne mai kyan gaske wanda kaf unguwar babu mai kyan sa, yana zaune kan kujera daga shiga sai 3Qauter ko riga babu jikansa, sai ƙirjinsa mai faɗi wanda yake da kwantaccen gashi mai kyau, hannunsa ya miƙa ya ɗauki chocolate ɗin dake gefensa ya sanya cikin bakinsa, operating system ɗin sa yake yana creating sabuwar waƙarsa Mai suna DEPRESSION.... Ajjiye system ɗin yyi baya da kayan aiki da a yanzu zai buga waƙar, idanunsa ya lumshe yana tauna chocolate ɗin wacce zaƙinta ke ratsa masa zuciya a fili kuma cikin daddaɗar muryarsa yace.

_I was tortured by the one_
_I love deeply on the globe_
_Feeling like I'm in my grave_
_Nl haven, safety or fortune_
_My life ornamented with a grief._
Shiru yyi domin anan ya tsaya da haɗa baitocin, ganin 1:15 ya sanya gently ya miƙe tsaye yana daukan system ɗin da raguwar chocolate ɗin, walking slowly ya nufi bedroom ɗin dake farcing na Sara, har zai shiga sai kuma ya nufi bedroom ɗin ta ya tura ƙofar bedroom ɗin, kwance ya sameta tana bacci ta takure waje guda alamar sanyi ya keji, domin sanyi ake sosai a garin windown ɗakin ya kalla yaga duk snow, heater ya kunna mata, kana ya kashe a.c kafin a hankali ya ƙarasa inda take kwance, kallonta yyi yaga gaba ɗaya ta zama wata kala irin bebies ɗin nan na turai shagwaɓaɓɓu, hannunta cikin baki, addu'a yyi mata ya shafa mata a kanta zuwa tafin ƙafarta, da sauri ta shigar da ƙafarta cikin duvet lokacin da yaji yaja mata yatsar ƙafarta. Fuskarsa ya shafa zuwa gemunsa kafin ya miƙe ya nufi bedroom ɗin, alwala yyi ya sanya kayan bacci yyi addu'a kana ya kashe wutar ɗakin ya kwanta, Can cikin dare wajan 3:20 yaji zazzafan numfashi na sauka a hankali kan ƙirjinsa, gashi gaba ɗaya an sanya hannu an riƙe masa waist, buɗe idanunsa yyi kaɗan ware idon ya ƙarasa yi sbd ganin Sara kwance kusa dashi koma a jikinsa kanta a kan ƙirjinsa....


_🤔🤔🤔 Lalacewa dai ta samu Sara.... A'a wlh mu dai babu ruwan mu musulmai dai basa haka wlh...._

Zain Abeed isn't free contact to subscribe...08119237616
[08-15 08:44] +234 703 831 1110: *19 Nimcyluv*
Hannunsa ya sanya tare da zame ta a jikinsa, tare da mayar da kanta saman pillow, yana kallon yadda take motsi da baki alamar ba taji daɗin abinda yyi mata ba, hannunsa ya miƙa tare da kunna hasken bedroom ɗin, fuskarta ya kalla bacci take sosai, irin baccin nan wanda ta jima ba tayi irinsa ba, tsaki yaja a hankali yana mai ɗauke fuskarsa daga kallonta. takaicin ya kama Abeed na yadda harta baro bedroom ɗinta tazo nasa, Miƙewa yyi yana duba lokaci ganin da saura kafin Subhi, ya sanya ya fita daga cikin bedroom ɗin tare da kashe mata wutar ɗakin, Parlo ya koma ya zauna kan 3seater a hankali ya rufe idanunsa trying to force his self to sleep, amma baccin ya ɗauke a idanunsa, Yaya zai yi da Sara? Baya jin zama da ita cikin gidan nan daidai ne, amma to ina zai kai ta? Ko dai sai sakata a jirgi ne zuwa 9ja? A fili yace "Kai i can't.." ya faɗa yana dafe kansa dake wani irin ciwo, har ya manta when last daya ɗauki maganinsa ya sha, kwanciya yyi saman kujerar duk yadda yaso yyi bacci kasawa yyi, yana nan zaune har aka fara kiran sallah, gently ya miƙe tsaye zuwa bedroom ɗin sa, har lokacin ɗakin duhu babu haske, bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower mai ɗan zafi, numfashi Abeed yake saukewa a hankali sbd Yadda ruwan yyi masa daɗi a jiki, daman sanyin garin yayi mafitar yawa, kashe showern yyi ya ɗaura toilet, ruwa ya zuba daga cikin sumar kansa yyi waje, sai a lokacin ya kunna hasken bedroom ɗin, juyawa yyi a hankali ya kalleta, ta mirgina can ƙarshen bed ɗin ta tattare waje guda, gaba ɗaya rigar baccin daya bata jiya ta dawo cinya, ajjiyar zuciya ya sauke kaɗan ya juya zuwa wajan mirror, cream ya shafawa skin ɗinsa, kana ya ɗauki jallabiya mai kyau ya sanya jikinsa, pra mat ya ɗauka ya nufi mosque bayan ya rufe mata ƙofar part ɗin baki ɗaya. Mosque ɗin dake kusa da gidansa ya nufa, sai da yyi raka'atul fajr kafin a tayar da sallah, ana idarwa ya dawo cikin gida, bai shiga part ɗinsa ba ya tsaya nan a Main Parlo na farko, deep frizeer yaje ya ɗauki wata fresh milk kai ɗan sanyi yana zame jallabiyar jikinsa yana shan milk ɗin, cup ɗin ya ajjiye ya rage daga shi sai 3gauter da sport t.shirt, ya ɗauki bandana ya saka a sumar kansa, kafin ya ɗauki bottle of water guda biyu. Part ɗin Gym ɗinsa dake cikin gidan, gasu nan kala kala sai wanda kkeso zaka za kayi, wajan the muscle Bar ya nufa, kunnawa yyi ya shiga yi da ɗan sauri yana jin abin na saukar masa a ƙirji, few minutes ya haɗa zufa sosai, kusan 30mnts da farawar sa ya tsaya ya ɗauki bottle water ya shanye ta tas, kafin ya sauya injin zuwa six pack sai wajan 8:20 ya kammala jikinsa ko ina ya murmurɗe zufa na yanko masa, yana tafe yana shan ruwa, kai tsaye kuma part ɗin sa ya koma dan a lokacin ya mance da Sara wlh, bayan ya ajjiye komai nasa ya nufi bathroom ya saki ruwa a kansa, sai da yaji Numfashinsa na ɗan ɗaukewa kafin ya kashe showern, bakinsa ya wanke nan da nan ya shiga ƙamshi colgate Red hot mouth spray, ga wani ƙamshin shower gel dake tashi a jikin nasa, wajan kayansa yaje ya shiga dubawa, wata vest ya ɗauka mai ɗan kauri sai trousers ya saka, ya fesa perfume, bacci ya keji sosai, Wayarsa ya sanya jikin chaji, kana ya dawo kan bed ɗin zai kwanta idanunsa ya sauka kansa, ware idanunsa yay waje da mmki yake binta da kallo ta wani ƙanƙame pillow, tsaki yaja ya sanya tattausan softness hands ɗinsa akan tafin ƙafarta, ya jawo ta tun daga kan gadon zuwa ƙarshen sa, amma ko motsi Sara ba tayi ba, mmkin nauyin baccin ta yake, ganin zata bashi wahala ya ɗaga ta Cak ya dire a ƙasa, da sauri ta riƙe masa waist tana buɗe idanunta jin zata faɗi ƙasa, suna haɗa idanu ya galla mata harara ita kuma ta Turo masa baki gaba, fuska ɗauke yace "sake ni" sai lokacin ta lura da yadda ta riƙe masa waist, da sauri ta sakesa tana ƙasa da kansa, hannunsu ya ɗura saman waist ɗinsa yana Kallonta yace "who gave you permission na zuwa bedroom ɗina?" Shiru tayi masa taƙi ko kallansa, fuskarta ya leƙa yaga a hakan ma bacci take, hannunsa ya sanya ya bugi shoulder ta yace "kee" kuka ta sanya masa tace "To ba tsoro naji ba, naji kamar akwai dodo a ɗakin" kallonta yake frm head to toe kafin yace "Eh akwai ai" zare ido tayi tace "dodon?" Yace "shifa, but iya bedroom ɗina yake" ta ware hannayenta tace "to ai ban jisa a nan ba" yana harɗe hannayensa yace "Daman, to shine yasa na gudun ma" kamar zata saka kuka tace "To daya kamani fa" yace "shi ke nan mun huta ai, ohya out of my room" kallonsa tayi zatai magana ya harareta yace "Saura ki koma bacci ai, kiyi wanka da brush akwai kaya ki saka" kai ta ɗaga masa ta nufi waje shi kuma ya zauna gefen gadon, yana maida numfashi ya jima bai mgn haka ba, idanunsa ya buɗe zai Mgna ya kanta tana Kallonsa ya zaro mata ido ta kwaɓe fuska tace "To bana jin bacci" yace "To" tace "Abinci fa?" Dafe kai yayi yace "wayyooo Amma, ke wacce yarinya ce nan, baki na za kisa yyi tsini da safe, Wlh na sake mki Mgn sai na dake ki" ya faɗa yana jan tsaki tare da kwanciya ya rufe idanunsa numfashinta na sauka a hankali.

Bedroom ɗinta ta shige da sauri tsoran sa ya kamata, tana zuwa bedroom ɗin ta saki kuka tana faɗin "ƙatoto kawai" sai da tayi kuka mai isarta sosai, kafin ta shige bathroom tayi wanka sosai tai brush, tare da wanke sumar kanta, jikinta sai ƙamshin shower gel yake, ko'ina na fatarta ruwa yake zubarwa ga wasu gashi sun kwanta saman skin ɗinta, wajan mirror ta nufa, ta zauna tare da zabga uban tagumi tace "Idan na shirya me zanci to?" Ita harga Allah yunwa ta keji sosai, cream ta ɗauka ta shafa a skin ɗinta, tana gamawa ta ɗauki body spray ta saka, cump ta saka ta taje kanta ba wani sosai ta iya ba, amma ya sauka har bayanta, Miƙewa tayi zuwa inda yace ya ajjiye mata kaya, gaba ɗaya abayas ne sai ƴan kanti, wani Applique logo detail T.shirt ta saka mai ɗan faɗin wuya, red colour, sai Teyana wide-leg trousers, bandana ta gani irin tasa amma ta mata, wacce aka rubuta his Queen ta ɗauka ta saka ita kuma black kalan wandon jikinta, gashin nata ya sauka har baya, sosai tayi kyau, zama tayi ta sabga tagumi, can kuma ta miƙe ta buɗe fridge taga babu komai sai fresh milk, ɗauka tayi yyi sanyi ma da yawa, ga Olser ta, domin har wani tiriri ta keji, tana fara shan fresh milk ɗin ta ajjiye sbd wani irin kartawa da cikinta yyi mata, tashi tayi ta dawo Parlo ta zauna lokacin 11 na safe, tun tana kwaɓe fuska harta fara kuka daga ƙarshe kuma bacci ya ɗauke ta ƙasan carpet. 12:30 ya fito cikin wasu haɗaɗɗun suit masu bala'in kyau, nevy blue sai ƙamshi yake idanunsa sanye cikin baƙin glass, hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu ɗaya kuma Wayarsa ce, sumar kansa sai kyalli take taji Ginger Geminal Oil-hair ga wani Luxury Beard oil daya sanya gemunsa da beard ɗinsa sukai wani kyau, bluetooth ne kunansa ya gyara masa zama, da alama tunda ya fito waya ya keyi a hankali, numfashi ya sauke yace "Ok, Danish see you later" yana faɗin hakan ya kashe wayar, ashe tunda ya fito ya kula da ita, bushasshen hawayen fuskarta yabi da kallo, yana daga tsaye ya sanya hannunsa akan shoulder ɗinta ya ɗan daga, da sauri ta buɗe idanunta tana ganinsa ta Turo baki tare da ɗauke kanta, tsora mata shanyayyun idanunsa yyi kafin can yace "jeki wanke fuskar karki, Miƙewa tayi ta nufi bedroom ɗin babu jimawa ta fito kayan jikinta yabi da kallo kafin yace "jeki sauya kaya" kallonsa tayi taga ita yake kallo tace "me sukai wannan?" Yana ɗauke idanunsa yace "kada na sake Mgn" juyawa tayi tana murguɗa masa baki, yana Kallonta yyi mata banza, blue black ɗin abaya ta saka, ta ɗaura ɗan kwalin a kanta, Miƙewa yyi yana nufar inda take, juyawa zatai yace "kee" tsayawa tayi kanta ƙasa, matso ta yyi zuwa gabansa ya kunce ɗan kwalin, gashinta ya bayyana ɗan shanshana gashin yyi ya ɗauke hancinta, rolling ɗin veil ɗin yyi mata kafin yaja baya yana ƙare mata kallo, baice komai ba ya nufi waje, bayansa tabi tana ƙarewa tafiyarsa kallo mai cike da ƙasaita, kamar baya son takawa, wata Mercedes benz iya motar ta haɗu, zama yyi yana saita komai ya shiga danna Horn, Sara ta buɗe gaban motar ta shiga, tana shiga yaja da gudu aledy gatekeeper ya buɗe masa gate, kai tsaye ya fita tunda suka fita babu wanda yyi mgn Sara sai ta kure jikinta waje Guda take sbd sanyi, snow Duk da maƙale jikin glasses ɗin motar, Abeed kam yasan yanayin garin shiyasa ya sanya kaya masu ɗan nauyi, driving yake cike da ƙwarewa motar kamar zata tashi sama a haka suka kawo wani Restaurant mai kyau da tsari few people ke zuwa cikinsa sbd tsada.

Katsina/ Zazzau
Motoci ne masu azabar kyau wajan guda goma suke fitowa daga cikin harabar airport ɗin da jirgin ya sauke su, a hankali motocin ke tafiya gwanin sha'awa, motar farko tasu Uncle AY (Choroma) shi da Choroman Zazzau, sai ta biyu tasu Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas da kuma Sarki Al'khasim Abubakar Wahab, sune zaune bayan mota kowa yana sanye cikin adon su na tamfarin ko wacce masarautar, Shira suke ƙasa ƙasa, mota ta uku kuma Dad Waziri ne, da Yarima Yashim Al'khasim Abubakar Wahab, sai Junaid a gaban motar shima yana sanye cikin kayan sarauta, mota da huɗu kuma Yarima Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas ne a ciki, sai kuma Amaryar sa Du'a Al'khasim Abubakar Wahab, wacce take sanye cikin wata haɗaɗɗan jallabiya ta masu sarauta fara tas da ita, ƙyakƙyawa ce sosai kamarta ɗaya sak data Sarki Al'khasim Abubakar Wahab, farin cikin ganin Zain ya kasa ɓoyewa a fuskarta, juya yyi a hankali ya kalleta suna haɗa ido tayi ƙasa da kanta, Murmushi yyi yaja hancinta yace "Kamar bake kike kuka nazo ba ko?" Sai na koma ai" marairaicewa tayi tace "I'm sorry Kalb, kawai farin ciki yasa na kasa mgn" hannunta ya kama ya riƙe tare da tsorawa zanan henna ɗinta idanu, kafin yace "Yyi kyau mene sunan wannan abun?" Du'a tayi Murmushi tace "We call it Henna" yace "Henna?" Tace "In sha Allah" ya jinjina kai yace "It's Expensive, i lyk it" Ɗan Murmushi Du'a tayi tana da kunya sosai duk wannan taɓarar da take masa iya waya ne, tace "Daman kai nayiwa" Zain yace "Sure??" Tace "In sha Allah" ya lura sunan Allah baya barin bakinta yajin daɗin hakan, hannunta ya miƙa bakinsa ya sumbata ka ɗan yace "Thank you Sweetheart" tace "It's my pleasure, babu labarin ɗan uwanmu till

Please Login or Register in order to submit comment