Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai ni cikin ƙaddarar rayuwarta, ma'ana ka duba min Zanan ƙaddarar ta" Boka ya zube kayan aikinsa tsaf, hadda Madubin tsafinsa, Sara wacce ke kwance bayan an bata ruwa sai sauke numfashi take tana kiran sunan ƴar uwarta Sairah, ƙuri Boka ya yi mata da idanunsa, kafin ya kama miƙa hannu zai kama hannunta cikin sauri Mabus ya daka masa tsawa yace "Kada ka kuskura ka taɓa ta" Ya faɗi hakan yana matsawa kusa da Sara tare da kama hannunta ya nunawa bokan, sun jima a haka kafin bokan yace "Ya yi" Mabus yace "Labarta min me ka gani, yakai La'ananan boka?" Boka yace "Abu na farko, dole ka auri Yarinyar nan, auren ta shine zai kare ka daga sharrin wasu mazan da suke tunkaro ka, na biyu kuma Tabbas shigowar ta cikin Masarautar Zahel tsararran abu ne, ba ganganci ba, ka sani bakai ka kawo ta cikin Masarautar nan ba, Ita ta kawo kanta kamar yadda zanan ƙaddarar ta ya nuna, zaka samu ɗaukaka ta sanadin ta, wacce babu sarkin daya taɓa samu a masarautar Zahel, amma dole sai ka aureta, jininta ba zai taɓa shawowa a wajan Dodo ba, sai abu na ƙarshe wanda na kasa ganewa kuma shine mafi haɗari, amma zan ci gaba da dubawa tare da ƴan uwana bokaye" Jinjina Kai Sarki Mabus ya yi kana ya saki dariya yace "Dole ne ta zama Sarauniyar Zahel....

Today is Sunday, Misalin 3:30 na yamma Zain ya fito cikin wata haɗaɗɗiyar three-piece dinner suit, nevy blue ya sanya wani baƙin glass a idanunsa, sai ƙamshi yake, ga wani mars a fuskarsa, waya ce maƙale a kunansa yana magana da wani akan case ɗin fashin da akai wanda suke bincike akai, Zain yace "I'll try my own best, wlh ko zai zama aikina na ƙarshe dole sai na binciko duk wanda yake da hannu wajan wannan fashin" Mutumin dake sauraran Zain ta cikin waya yace "In sha Allah, I'm with you komai zai zo da sauƙi, jiran dawowarka muke" Zain yace "this week ina hanya" Mutumin yace "Ok, me kaje yi a Mascow?" Shiru Zain ya yi can yace "Wani aiki naje, Nama gama, I'll catch you later" Ya faɗa yana kashe wayar, juyawa ya yi suka haɗa ido da Abeed wanda shima ya yi shiga sak irinta Zain, ga wani haɗaɗɗan covet shoe a ƙafarsa, sumar kansa sai kyalli take, ɗan taune bakinsa ya yi, kamar ba zai magana ba sai kuma yace "U look like Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas" Zain yace "Daman shine, and you too u look like Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas" Abeed yana shafa sumarsa zuwa wajansa yace "Yeah" Zain yace "Idan na je maka show ɗin, nima ka zauna kayi min bincike Akan wata ƙasa wai Zahel" Lumshe idanun Abeed ya yi yace "Zahel?" Zain yace "Yap, ka haddace komai na binciken, nasa zaka iya ba sai kayi note ba" Abeed yace "Owk" Kallon juna sukai lokacin ɗaya sukai Murmushi kana suka rungome junansu, Abeed yace "Take care my singer" Zain yace "Ohh! Ai yau ne kawai, bye" yana faɗin hakan ya fita, Abeed kuma yaja idanunsa ya rufe, ya jima a haka kafin ya ja jikinsa zuwa bedroom, wasu Drugs ya ɗauka ya sha, kana ya dawo Parlo bayan ya cire kayan jikinsa ya zauna daga shi sai Cable-knit vest sai tracksuit trousers, System yaja gabansa, hannunsa riƙe da wani Apple juice mai sanyi yana sha, cikin nutsuwa yake danna keyboard na system ɗin, a hankali ya rubuta _Zahel_ waro idanunsa waje ya yi tashin farko da yaga an nuna masa wani ƙaton gunki, A zuciyarsa yace "Ohh God!" daga ƙasa kuma bayanin garin Zahel ya bayyana, zare manyan idanunsa ya ƙara yi, abubuwan da yake karantawa akan Zahel ya munana, a yadda yake gani duk Musulmin daya kuskura ya shiga garin kisan gilla ake masa, shi kowa tayaya zai bar biyuninsa yay wannan aikin na kuskure, daman shi wata biyar suka rage masa, ko sun kashe sa bashi da matsala, amma ba zai yiwu ya mutu kuma a kashe ɗan uwansa ba, Mai martaba ba zai jure rashin su ba, haka ma Naila, Kamar yadda Zain ya tafi wajan show ɗin sa, shi ma zai ɗauki Wannan kasadar shi da kansa Zai je Zahel domin gano asalin abinda yake ɓoye, Sosai Abeed ya girgiza da ganin yanayin Zahel, bai taɓa tunanin har yanzu akwai irin wannan mutunan ba, kashe System ɗin ya yi gaba ɗaya, tare da jan numfashi ya ɗan kwanta jikin kujerar, ji yay gaba ɗaya ya kasa samun nutsuwa ba zai taɓa zuba idanu Zain yaje wannan garin ba, Tabbas a gobe zasu koma 9ja daga nan zai san duk yadda ya yi ya samu fita shi ɗaya. Wayarsa ta fara ƙara yana jinta yay banza da ita, wajan kira uku akai masa, tsaki yaja a kira na huɗun ya ɗauki wayar ashe vedio call ne, ya mance data akwai Wi-Fi a hotel ɗin, sunan RIYA ne ya bayyana, answering ya yi nan take fuskar wata budurwa ya bayyana, tana zaune akan kujera tasha kitso kwaɓe fuska tayi tace "Haba My singer, me nayi kake azabtar dani haka, tun kuna 9ja nake kira, hankali na yaƙi kwanciya, na kira Twin Zain yace kana wajan show, hope everything is ok?" Idanunsa a rufe ba zaka taɓa cewa dashi take magana ba, Riya shiru tayi ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa ido, bata taɓa ganin mutum mai faɗin ƙirji irin na Abeed ba, ga wasu kwantattun gashi a ƙirjin nasa, sunyi kwance sai kyalli suke, jin shiru yasa Abeed ware idanunsa tsaf akan Wayarsa ganin kallon da take masa, yaja tsaki yana faɗin "Mayya" Murmushi Riya tayi tace "how are you?" Banza ya yi mata yana covering ƙirjinsa da hannayensa domin ya tsani kallo, ganin yay mata banza ya sa ta marairaice tace "Haba My singer, ni ban kai matsayin mata bane? Dako kallo na baka son yi? Kasan irin wahalar da nake sha akan soyayyarka" kai tsaye yace "to ki daina son mn" Riya hawaye na cika mata idanu tace "I can't, ina masifar sonka, ban damu ka soni ba, burina na ganni a gidan ka matsayin matarka" Idanunsa ya buɗe tare da kallon ta, kanta ta sunkuyar domin bata tunanin zata iya jure kallon ƙwayar idanunsa, ya ɗau lokaci a haka kafin yace "Zaki mutu babu aure ke nan" Tace "Pardon, kana nufin ba zaka auren ba" girgiza mata kai ya yi yace "Babu soyayya a zanan ƙaddara ta, look Riya ke mace ne, kiyi amfani da time da kike dashi ki samu wanda zaki aura, ni Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas wlh ba zan aure ki ba" Kuka Riya ta fashe dashi tana ƙoƙarin Magana ya kashe kiran baki ɗaya, banda tsaki babu abinda Abeed ke ja, ya tsani mace mara aji sam a rayuwarsa, duniya ta lalace Mata suyi ta tallan kansu, wacce irin gantalalliyar rayuwa ce wannan, wani kiran ne ya sake shigowa ganin sunan Mai martaba yasa with so much respect Abeed ya ɗaga kiran, tare da marairaice yana narke murya yace "Abba.." Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas dake Zaune cikin shiga ta alfarma yace "Shalelen Naila" Abeed ya kwaɓe fuska yace "I'm nothing without you Abba" Mai martaba yace "Iyee kamar ni ne Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas" Abeed yay wani ƙawataccen Murmushi yace "Abba.." A hankali Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace "Ina Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas" Abeed yace "Yes Abba.." Mai martaba yace "mene ya haɗaka da Riya?" Abeed yace "Wace Riya?" Caraf Naila tace "Wata gantalalliya ce mana, to idan ka aureta Allah ya tsine, sai ɗagawa Uban naka nono kowa ya huta idan ya matsa, Meye wata Biya? Ba dangi iya balle na baba, banda lalacewa ta zamani mace tana tallan kanta, wlh Allah ya tsine idan ka aureta, shiyasa kullum a bushe take ashe masifa ce take damunta zata lalata min jika, ƙur'anin Allah bata isa ba, babu ruwana hisba zan kai ta ai min iyaka da ita, banda ma ɗa na kowa ne meye haɗin mu da ɗan gidan Waziri, to wlh imani ne kawai ya yi min yawa shiyasa nake amsa kasuwar yariyar,mai idanu a tsakar ka..." Tunda ta fara mganar Abeed ke Murmushi yana masifar son Granny ɗin tasa, Mai martaba kowa kallon mahaifiyar tasa kawai yake, wai Waziri da yake ɗan ta wanda ta shifa shine ba dangi iya balle na baba... Abeed yay Murmushi yace "Wlh Naila lalata ni kawai take son yi gaba ɗaya nawa nake" Kuka Naila ta saka tace "Allah sarki abin tausayi, wlh tsayin ƙafa ne kawai, yaushe ka girma gaba ɗaya ma, zata ja mana jafa'i wai kayi aure, to Allah ya tsine idan ka aureta....
Page 5


Abeed ya ɗan shafa fuskarsa zuwa gemunsa, feeling happy yace "Naila ko kallo na bana son tayi,tsoro nake" Naila ta ƙara fashewa da kuka tace "A'a wlh masifa ce da maita irin ta matan yanzu, yanzu fisabilillahi kallon na mene? Koda yake muna zaune da ita ne amma wlh babu da tabbaci da Zuciyarta, rufin asiri dai yana da daɗi amma da nace Audil ya jawo mana masifa ya kawo mana Mayya" Ta ƙare zan can tana matse hawaye, ganin hakan yasa Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ya ɗan lumshe idanunsa cikin nutsuwar sa, da kamewa yace "Naila kiyi hqr" Kallonsa tayi tsaf tace "A'a bana son munafurci meye hqr kuma? Ina raga maka ne sbd wannan tafkeken rawanin, maza ka kira min Audillahi (Waziri). Shiru kawai Mai martaba ya yi domin ya san rikicin mahaifiyar tasa, Wayarsa ya ɗauka kasancewar ya bar fada ya ɗan nemi hutu, kiran Waziri ya yi, bayan sun gama waya ya ɗauki Apple a hankali yana ci, can ya nisa yace "Naila Oumarar fa?" Tace "Ai dole naje gaban ma'aiki, na kai masa kuka na, Wannan yaran da baya ƙaunar aure ƙilan shafar aljanu ce billahil lazi, ai su mugwayen mutane ne, basu da kama babu mamaki wata matashiyar aljanarsa ta aure sa" Shiru Mai martaba ya yi idanunsa a lumshe, yana sauraran yadda take zuba magana ta rikici, Sallamar Amintacciyar kuyangar Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas ne ya katse wa Naila Maganar ta, taɓe baki tayi tace "Ke kuwa kiyiwa kanki liɗifi, ko masilin ne kina shafawa, haba wannan baƙi kamar an maki baki" Kuyanga Bira tace "Allah ya ƙarawa Naila lafiya da nisan kwana, daman Wazirin Masarautar Bilhira ke neman iso" Naila tace "Shidai wannan da nema min mgn yake, wallahi wasu sai suce bani na haifesa mene iso kuma Allah na tuba?" Numfashi Mai martaba yaja ya ɗanyi gyaran Murya hakan ya tabbatar da cewa ya bada dama, Fita Kuyanga Bira tayi, tana zuwa ta samu Waziri tsaye cikin shigarsa ta wata alkyabba mai taushi, rusunawa tayi tace "Allah ya taimaki Waziri Mai martaba uban manyan goben wannan masarautar ya bada dama" Jinjina Kai Waziri ya yi yace "Gdy nake Bira" yana faɗin hakan ya shige cikin ƙyakkyawar tirakar ta Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, yana zuwa ya samu Naila zaune tana lumshe idanu, Sallama ya yi Mai martaba ya amsa a ladabce, yana ɗan gyara muryarsa, Gaisawa sukai, Waziri yace "Barka da hutawa Naila" Naila tace "yanzu nake cewa sashinka zani, gari da yawa ai maye ba zai ci kansa ba, tunda na shigo Yake haɗe fuskarsa, shine nace to ka dan nace a haɗe zumunci ne wannan yaran da Riya take masifar so a bata shi kada ta mutu taja mana masifa, Itama dai ƴar wallahi ruɓaɓɓciya ce me zatai da wani Tagwaye fisabilillahi, nidai ba zan hana ba idan na hana sai na mutu ayi ai" da mamaki Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yake kallon mahaifiyarsa, yanzu tace idan Abeed ya auri Riya Allah ya tsine amma yanzu ga abinda take faɗa, shi dai bai ce komai ba, domin yana faɗa zai jawo wata maganar, Naila tace "Yanzu kaje ka tattaro abinda Allah ya baka ka fara shirin biki, shi kuma wancan tunda ƙaddararsa ke nan, sai dai ya dawo yaji na kai masa kuɗin na gani ina so" Waziri yace "Amma Naila a bari su fara haɗa kansu mana, ban sani ba ko Abeed baya son Riya kada a shiga haƙƙin sa" Naila tace "Nice na haifi iyayen yaran, kuma nice nace a haɗan auren duk wanda zai mutu ya mutu mana billahi wa'adinsa ne ya yi" tana faɗin hakan ya miƙe tare da ɗaukan sandarta tayi waje, gaba ɗaya suka bita da ido, Waziri yace "Bana son wannan haɗin, za'a shiga haƙƙin Abeed, nasan Riya na sonsa, amma shi fa?" Mai martaba yay shiru kamar ba zai magana ba sai kuma yace "Nikam ba ruwa na, abinda tace shi za'ai ina da tabbacin komai zai daidai" Waziri yace "To Allah ya tabbatar da alkairi, amma kada a faɗawa Abeed" Mai martaba ya jinjina kai tare da yin shiru.

Abeed ya taɓa baki yace "Class zero, beauty zero, girki zero, Mtwss" wayar ya ajjiye can gefe, sannu a hankali kuma tunanin Masarautar Zahel ya shiga yi masa yawo cikin tunaninsa, Ya san har abada Zain ba zai hqr da zuwa binciken ba, an yarda dashi a matsayin na gartaccen lawyer, wannan dalilin yasa aka haɗa shi da wasu police na state Cid. Miƙewa ya yi tsaye zuwa wajan fridge ya ɗauki ruwa mai sanyi zai sha yaji ance "Ohh! Hello" juyawa yay da sauri, Zain ne tsaye hannunsa zube cikin Aljihu sai rigar suit ɗin daya cire ya ɗura saman shoulder ɗin sa, he looks so worried, na ganin abinda Abeed ɗin yake, cikin damuwa yace "Baka jin magana Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas" ya faɗa yana buɗe wani fridge ɗin nada ban, ya ɗauko masa bottle of water mai ɗan dama, tare da tsiyaya masa a cup yana faɗin "drink this, and drp that..." Amsa ya yi idanunsa akan Zain so yake yace "how was the show going..?" Amma kalmar tayi masa nauyi da girma a baki, after ya gama shan ruwan ne, ya kalli Zain ɗin wanda yake cewa "Is Riya called?" Gently Abeed ya ɗaga kansa alamar "Eh" Zain yace "I see" Abeed ya buɗe baki da ƙyar yace "Ykk, i mean ya show ɗin?" Zain yace "Ohhhu, ashe mahaukaci mutum yake zama a wajan?" Abeed yay cute smile yace "kaso ka zama dai" Zain yace "pardon?" Shiru kawai Abeed yay tare da ɗaukan ruwa mai sanyi ya bawa Zain, Zain kuma ya girgiza kai yace "murya nake bani mara sanyi" ya yi hakan ne sbd bazai iya hana Abeed sha ba, shi kuma ya sha, Zama Abeed ɗin ya yi kusa da Zain, shi kuma ya shiga bashi labari yana cewa "ban san haka ka tara fans ba, wata budurwa kam wlh na ɗauka rungome ni zatai" taɓe baki Abeed yay kana yace "Oops, nace shari'ar nan, ba zaka iya bawa wani case ɗin ba?" Zain yace "bani na amsa ba, bani akai sbd an yarda dani kuma dole zan tabbatar da gsky tayi halinta" Abeed yace "to kace ba zakai ba mana?"... "Kana hauka? Tabbas zanyi" "Owk" kawai Abeed yace yana lumshe idanunsa, can ya nisa yace "Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas" Zain yace "Na'am" Abeed yace "kana son yin aure ko?" "Of course" A hankali Abeed yace "To Promise me" Zain yace "About?" Kai tsaye Abeed yace "Ni da kai na zan nema maka matar aure, kaban wannan damar" Murmushi kawai Zain yay domin ya san Abeed baya hulɗa da mata, tayaya zai gane nagartacciyar mace har ta zama matarsa? A fili kuma yace "Promise, ko wacce kaban zan aura zan kula da ita daidai iyawa ta"... Washe gari da safe Abeed ya fito cikin voyal irin na sarakai mai masifar kyau, Black colour ya haska fatarsa, sumarsa har baya, cikin nutsuwa yake tafiya a hankali without making any sound, a haka ya fice daga cikin bedroom ɗin zuwa reception, kai tsaye kuma waje yay tare da shiga motar hotel ɗin, gudu yake sosai a tsakiyar titin da zai kaisa hospital, can ya ɗauki Wayarsa ya kira wata number, babu jimawa akai answering yana shiga hospital ɗin yace "Something new?" Dr Adyan dake zaune a office ɗin sa na ƙasar 9ja yace "till now ba wani labari,buhh I'll try my own best, u don't have to be worried za'a nemo." "Ok" kawai Abeed yace yana kashe wayar, zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, har farkar tambayar Dr Adyan yake yaji yace masa ba wani labari. parking yay kana ya fito bayan ya sanya maras har office ɗin Dr Siya ya shiga... Dr Siya yace "me zakai da allurar kwana biyu Mutum yana bacci?" Haɗe fuska Abeed yay yace "stop asking too much" Dr Siya yace "Ok, bari na rubutu maka akwai a pharmacy idan akai allurar mutum zai kai kwana uku har huɗu yana bacci ba zai fahimci komai ba" rubuta masa yay kana yaje pharmacy ya siya, daga nan ya nufi hotel ba. Misalin 11 na safe jirgin su Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas da Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas ya ɗaga zuwa Nigeria.

Masarautar Zahel.
Tsananin Wahala ya sanya Sairah ko gabanta bata gani, tayi kuka ta kira sunan twin babu adadi, hakan yasa ta fara tafiya ba tare data san inda take zuwa ba, har ta iso ƙofar shiga Masarautar Zahel. Daga can taji ance "Kamar baƙuwa ce?" Gimbiya Noro wacce take cikin keken sarautar ta dakatar da kuyanginta, tare da masu izinin sauke ta, a wahale suka sauke keken da yake wuyansu, Kallon Tsaf Gimbiya Noro tayi mata tana ƙara ware idanunta, gabanta ne ya faɗi kanta ya shiga sarawa, da ɗan sauri ta shafa cikinta, can tace "ku kirata" Wata Kuyanga ta ƙarasa Wajan Sairah wacce take shirin faɗuwa, hannunta tasa ta shiga janta wata ƙyakkyawar tsawa Gimbiya Noro tayiwa kuyangar hakan yasa ta daina jan Sairah wacce bata gane komai, tana zuwa Gimbiya Noro ta kama hannun Sairah tare da shigar da ita cikin keken, hakan yasa wata Amintacciyar kuyangar ta tace "Abin bauta ya taimake ki, amma hakan ya saɓa dokar masarautar Zahel" Gimbiya Noro tace "na sani, ki tabbatar wannan mganar bata isa wajan Mabus ba, zan ajjiye ta a waje na akwai amfanin da Zatai min" tana faɗin hakan suka ɗaga keken zuwa cikin Masarautar daman ta fita shan iska ne a lambun Kan'an. Mabus na zaune yace "Ba'a fito da sanyin idaniya ta bane? Dodo ne zai sanya mata albarka" Wani dogari yace "Ana shirya ta ne" Mabus yace "tsoro nake kada Dodo ya buƙaci jininta a yanzu, domin ina jin ta a ƙoƙon zuciyata, wai ashe daman haka ake jin Soyayyar, fuskarta kaɗai ta isa tasa na samu nutsuwa, kamar Abin bauta yay min zalunci daya sanya naji ina son wata ƙabilar ba ƙabilar Zahel ba, maza jeka tawo min da ita" dogarin ya koma wani sashe inda a nan ne aka ajjiye Sara, tana zaune kan wata kujera an dasa mata madubi a gabanta, wani irin kayan ado ake sanya mata na gwala-gwalai, idanunta sunyi jajir kuma sam ba kuka tayi ba, kawai jarumta ce, fuskarta babu walwala sam, tunda tazo ƙala bata ce ba da idanu kawai take kallon kowa, matar dake shirya ta tace "Abin bauta ya saka maki jarumta yake Sarauniyar Zahel ta gobe tashi muje" ta faɗa tana kama hannunta, miƙewa tayi tsaye suka fita waje, kamar Mabus zai hauka haka yaji, gaba ɗaya wajan Dodo sukai, suna zuwa wajan ya ɗauki wata girgiza da ƙara can suka ji ance "Kada a bari ta ƙara yin Sallah.....
[08-15 08:41] +234 703 831 1110: *🌈ZAIN_ABEED🌈*


_By Nimcyluv sarauta_

Page 6....

http://wa.me/+2348119237616
_Domin yiwa writer ɗin mgn👆🏾_



“Kada a bari ta sake yin sallah, a cikin Masarautar Zahel” shine abinda boka yake faɗa, wanda a tunaninsu Dodo ne da kansa yake faɗin hakan, Sara shock! da abinda taji ana faɗa, tana matsayin musulma za'a ce kada ta sake yin Sallah? What does that means? Ka furta ta za suyi or what? Sarki Mabus yace "Akwai illa gayin dunguran nasu a cikin wannan masarauta ta Zahel ne?" Boka yace "Na rantse da Abin bauta kabas, duk sanda ta sake yin Sallah, Tabbas dubban mutane zasu halaka, a kullum tai sallah Abin bauta girgiza yake" Jinjina Kai Mabus ya yi kafin yace "Mene mafita, Wlh ina sonta kamar na lasheta hakan nan na keji, bana son a cutar da ita" Boka yace "Da acutar da ita, da kuma mulkin daka ƙafa bisa tsari da adalci ya wargatse fa?" Da mmki Mabus yace "kamarya?" Boka yace "Ina nufin, dukiyar ka zata halaka, kujerar mulkin ka zata zama bakai bane akai, gumaka zasu ƙone, garin Zahel zai shiga uku" cikin girgiza da tashin hankali Mabus yace "kutumar uba, na rantse da abin bauta, har gobe nine Sarkin Zahel, babu mutuwa a zanan lissafin ƙaddarata" ya faɗa idanunsa na juyawa, kafin a hankali ya juya wajan da Sara take tsaye kanta ƙasa, ƙirjinta na bugawa, tashin hankali tsoro ya bayyana saman fuskarta, bata son sha rauninta wannan dalilin ya sanya gaba ɗaya tayi ƙasa da kanta, wacce kalar masifa ko ƙaddara ce ke bibiyar Rayuwar su, Ina Twin take, mene makomarta...tana tsaka da tunani taji ance "Ke kice kin rantse da abin bauta kabas" shiru tayi deep down na Zuciyarta tana kiran sunan Allah akan ya kawo mata ɗauki, jin tayi shiru yasa Boka ya ƙara cewa "kic kin rantse da abin bauta kabas, kin daina sallah kin kafurta kin koma ƙabilar Zahel?" A karo na farko ta ɗago jajayen idanunta wanda launinsu yay masifar sauya kala, kallon baku da hankali tayi musu, kafin a hankali ta kalli Sarki Mabus ta tofa masa yawo, cikin nutsuwa da kuma kakkausar murya mai kama da gargaɗi da kuma fansa tace. "Allah ya tsinewa Abin bautar daku, In sha Allah Ubangijin al'arshi wanda ya halicci ne, ya halicci ku, sai ya kawo ƙarshen ku, zuciyata cike take da soayyar Manzon Allah, wanda ake duniya domin da lahira, kuma albarkacin Baban faɗimatul-Zahrah sai na kuɓuta daga hannunku" Sarki Mabus ji ya yi kansa yana sarawa, babu abinda yake kalla a jikin irin ƙaramin bakinta, da yadda take magana a nutse, shi dai yana ganin soyayyarta itace rauninsa, cikin gargaɗi yace "kafin ke mun samu wasu, kuma ƙarshe mun aika ka su lahira, ta hanyar yanka wuyansu, ina gargaɗinki da ki gaggauta amsar addinin Zahel, wanda shine yake daidai ba naku addinin na Musulunci ba, idan addinin Musulunci shine daidai, mene ya sanya kuke zuwa wajan bokaye da mutunan tsubbu bayan kun san su ɗin ɓatattu ne?" Tafiya Sara ta dinga yi har zuwa gaban Mabus kamar ba zatai magana ba, sai kuma tace "Wacce buƙata wancan gunkin ya taɓa biya maka? Ubangiji na halittar Mutane da ƙyakkyawar zuciya, sharrin shaidan da kuma sharrin irinku wanda har yanzu ko kasa ajjiye Littafin Injila ko ɗauki Alqur'ani, shine yake sanya wasu nagartattun ɓata, na Aminci koda yanzu shine rayuwata ta ƙarshe ka bani dama nayi alwala nayi sallah na roƙi Ubangiji ya kare ni daga sharrin ku, kai ma kaje gaban gunkin naku wanda baya tsinana maku komai ka roƙesa akan ya kareka daga masifar da zata iya samunka, idan har wani abu bai sameka ba, ni kuma ban kuɓuta ba, zan tabbatar cewa nayi maku mubaya'a" girgiza kai Boka ya yi yace "wannan tatsuniya kike, musulmai nawa ne suke zuwa waje na, akan samun mulki, ko ɗaukaka, ko kuma kashe kishiya, sun san cewa ni ba musulmi bane, amma suna bina muna shirka tare,su da kansu sun tabbatar abinda nake gsky ne, kuma bisa sahalewar abin bauta kabas nake hakan..." Sara tace "Ohh really! Let's see,who win between i and you...,zan tabbatar maku cewa addinin musulunci shine addinin gaskiya, kuma Shine aka aiko Manzon Allah Sallallahu alaihi dashi bayan zuwan Annabi Isa Alaihissalam, ɗan Nana Maryama da yazo da Littafin Injila,idan duk kun amince a bani ruwa..." Sarki Mabus yace "a bata ruwa" boka ya girgiza kai yace "kada ka biye mata, akwai hanya mai sauƙi wacce zamu iya wajan ganin tayi mana mubaya'a" Mabus yace "barta, bana son ta raina min addini na, da kuma ƙarfin mulkin da Zahel take dashi na san me zanyi akai" Ruwa aka bawa Sara, mutunan wajan duk suka bita da kallo,ta shiga yin alwala a nutse, tana juya fararan yatsunta masu kyau da tsari, bayan ta kammala alwalar ne ta buƙaci abu mai kyau da kuma tsafta,tayi nesa

Please Login or Register in order to submit comment