Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sweetheart kuyi addu'a ok" Yusra a sanyaye tace "Bye Mami" kashe wayar tayi gently ta miƙe ta nufi ɗakin hutawar da aka kaisa, yana kwance flat idanunsa rufe sai green riga dake jikinsa kumburin fuskar dana ƙafar ya saɓe, Numfashinsa ya daidaita amma har yanzu oxygen ɗin yana bakinsa, fita tayi ta nufi room ɗin Sara tana zuwa ta samu Dr Haris a wajanta daga inda take bata ƙarasa ba tace "Ya nata jikin?" Yace "Allahamdulillah, amma ta shiga duguwar suma anytime zata iya tashi" kai ta ɗaga masa da sauri tana barin wajan... Ranar Anuty Zulfa a wajan Abeed ta kwana cirr bata runtsa ba, wani irin so da ƙaunar sa take tun ba yanzu ba, balle yanzu data san meke damunsa, da Subhi tayi sallah a nan room ɗin kana ta ɗauki wayarta dake ƙara ta nufi waje tana faɗin "I want to talk to you Abban Yusra.... serious talking" yana daga can ƙasar da yake zai shiga airport yace "Am on my way yau zan dawo" tace "Ok luv Allah ya tsare ya kiyaye sai kazo" Yace "Ok My lady be strong, ko dan ciwon ɗan ki ne Shine zaki zama raguwa" tana ɗan Murmushi tace " Is not like that.... wlh he's critical condition Saratu ba zata jure ba nasan yadda take son Abeed fiye da komai na nan duniya, komai nasu ɗaya ne da Zain amma son da take ma a Zuciyarta special ne" Yace "Owk, ok My lady zan shiga jirgi bye luv u" kashe wayar tayi tasan idan plan ɗinta ya samu shiga har abada ba zatai ladama ba hakan kuma shine daidai ga duk su biyun.....Masarautar Zahel Sairah ce ta kalli Subash tace "Me yasa kuke dake sani ne?" Da mmki yace "Wanne sani? Akwai wanda ya sanar damu wani abu ne?" Kallonsa tayi tace "Baka san Littafin ku ba ke nan? Baibul ko a ciki ba'a faɗa muku cewa Allah ɗaya bane bashi da abokin tarayya bai haifa ba, ba'a haifa masa ba, Sannan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama shine Manzon Allah na gsky, wanda Allah ya turo sa da Littafin Alkur'an kafin kuma Isra'il da mi'iraji su bashi damar zuwa amsar sallah?" Shiru Subash yyi kafin yace "kina nufin Mu ɗin nan yinmu akai?" Was so surprised Sairah ke bin Subash da kallo kafin tace "To waye yyi ku?" Ya ɗaga mata kafaɗa tare da wargatsa hannunsa alamar waya sani, can kuma yace "kawai a haka na ganni, Mabus yace babu abin bautawa sai Abin bauta kabas da dodo, sune suke bamu abinci ruwa, iskar shaƙa da komai?" Miƙewa Sairah tayi tana hange hange tace "Akwai ƙwayar wake kota masara" shiru yyi can kuma yace "Ban sani ba" tace "Addinin Musulunci ya zo ne daga Allah ta hannun Annabi Muhammad(SAW) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, shi ne manzo wanda Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki daya kuma na karshen annabawa a duniya domin ya sake jaddada addinin Allah, a yi imani da Allah wanda Ya halicci kowa da komai. Addinin musulunci na da mabiya a duk fadin Duniya kuma mafiya yawan su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya da yankin Afirka ta Arewa wadanda mafi yawansu Larabawa ne masu bin addinin musulunci, sai dai akwai dunbin mabiya addinin musulunci a ko'ina a fadin Duniyarmu.Ma'anar Addinin Musulunci shi ne " Yarda da Mika wuya ga kwadaituwan Allah Madaukakin Sarki, wato Shaidawa babu abin bautawa da Gaskiya sai Allah kuma Muhammad Manzonsa ne (Ma'aikinsa ne), bayan haka ka yarda da dukkan abubuwan da ya umarci al'umarsa haka kuma da wadanda ya kebanta da su, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai"Allah Madaukakin Sarki shi ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) da Al Kur'ani Mai Girma domin ya zamo shiriya da Rahma ga Halittu baki daya, an bayyana musulunci a matsayin addinin dake da saurin karin yawa a duniya a kullum wanda ke da Adadin musulmai na Duniya sun kai kusan kashi 24.1% na dukkan mutanen Duniya, wato fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari takwas (1,800,000,000) a fadin duniya" Miƙewa shima Subash yyi yace "To mu namu mene sunansa? Waye kuma ya halicci duniya da ake ta faɗa?" Sairah ta dubesa cikin nutsuwa tace "Allah shine ya halicci duniya da abinda yake cikinta, yyi sama ya halicci ƙasa, Allati lamshiii alayya....ya bamu rai da lafiya da kuma isar da muke shaƙa, kana da labarin fir'auna da ƙaruna? Kana da Labarin Mutanan Annabi Luɗ? Kasan yadda ƙarshen su ya kasance, kasan dame aka halicce mu aka halicci Mala'iku, komai na nan duniya Allah ya halicce sa, akwai adadin kwanakin ya ɗauka...." Subash dake sauraran Sairah cikin wani irin yanayi yace "Idan Allah ne ya hallice mu yyi duk abinda ya faɗa shi kuma Allah waye ya halicce sa?" Wani ƙyakƙyawan mari Sairah ta masa yana shirin yin mgn ta ƙara zabga masa wani marin, tana sakin kuka tace " brother! It's not a weird question, it's a stupid question.....ALLAH is the creator And no one can create the creator or else he would not be God!" Zubewa Subash yyi a gabanta idanuna jajir kafin ya saki kuka yace "Zaki aure ni Sairah?"....... After 5days Hannunsa ya sanya a kan handle ɗin ƙofar room tare da fitowa a hankali yake tafiya sbd ɗinkin dake jikinsa, yana sanye da wata Armless wacce take da zif hakan ya sanya ya buɗe gaban rigar baki ɗaya faffaɗan ƙirjinsa ya bayyana ga wajan aikin da akai masa rufe, sai kuma 3Qauter jikinsa hannunsa ɗaya cikin aljihunsa, kai tsaye wani room ya nufa yana shiga yaga babu kowa a ciki kai tsaye idanunsa suka sauka akan Sara wacce har lokacin bata farka ba sbd kwanaki wajan 6, shi kansa da yake cikin wani hali gashi harya fara tafiya lallai mutuwa bata san inda ciwo yake ba, rufe ƙofar room ɗin yyi walking slowly yake tafiya ya dawo Abeed ɗinsa sosai kamar ba shi ba, tsaye yyi a kanta kafin yaja Kujera ya zauna kusa da inda kanta yake, ya jima zaune yana kallonta zuciyarsa duk wani irin wacce kalar suma ce haka? Almost 20mnts yaji computer na ɗittttttttt, sai kuma yaga hannunta na motsawa da ɗan sauri ya riƙe hannunta, Sara wacce take jin kamar bacci tayi ta fargaba ta shiga faɗin "Uncle.... Uncle Twin zamu gida ko? Ai ba mutuwa kayi ba ka tashi su gani Uncle kana jina?" Gam Abeed ya matse hannunta dake cikin nasa, kafin ya ɗura ɗaya hannun saman kanta ya shafa sumar kanta yama rasa me zai ce wani irin tausayin ta ya kama shi, duk a sbd dashi ta shiga cikin wannan halin kafin yyi Mgna yaga ta saki kuka tare da zabura tana wani irin kalar ihu tare da faɗin "Wayyooo Uncle baka mutu ba kace kana nan Twin...zan bika zan" yama riga ya mance ciwon jikinsa da wani irin sauri ya hau bed ɗin tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya jawota jikinsa ya ƙanƙame ta yana sakin ajjiyar zuciya murya, fisge fisge ta fara alamar mutanan kanta kuma na son motsawa tana wani kalar ihu tana cewa "Ba zan yarda ba sun kashe min Uncle....Twin kana ka tashi zan bika" gaba ɗaya ya rufe ta da ƙirjinsa yana jin yadda take Dukansa tana cizonsa tare da ihu tana Uncle ka tashi amma ya rungome ta tsam a jikinsa daidai kunnanta ya ɗura bakinsa yace "Shiiiittt..... I'm here just for you Saaaaaaa open your eyes look at me ga Uncle kusa dake..." Anuty Zulfa dake shigowa cikin room ɗin tana waya tare da faɗin "Har an ɗaura? To ma sha Allah Ubangiji ya tabbatar da alkairin naji daɗin auren nan hankali na ya kwanta....


Zain Abeed isn't free kiji tsoran Allah wlh bana bacci sbd rubutu...... Contact to subscribe 08119237616



Sarautar marubuta
[08-15 08:45] +234 703 831 1110: *_25 Nimcyluv_*
Juyawa waje Anuty Zulfa tayi hannunta riƙe da key car tace "U have know idea how happy d nke ciki" shiru tayi tana tafiya zuwa office ɗin ta tace "Sure...Ita yarinyar zata samu nutsuwa, kuma Rahila ai bata da wani mugun abu, kawai cutar ta yaso yi" shiru ta sake yi tace "You're right, tunda an ɗaura auren shima Bilyamin hankalinsa zai kwanta bye" kashe wayar tayi lokacin da take shiga office ɗin nata, zama tayi saman kujerar looking directly zuwa kan matar dake jiranta tace "Kika ce me?" Matar tace "An gama Mgnar auren, sai bayan anyi Genotype aka samu saurayin da As, I really love him, i decided to marry him" Zulfa na kallon ta tana girgiza ƙafa tace "So where are you here? Tunda U alrdy make a decision na auren nasa" Matar wacce ba zata shige shekaru 25 tace "Sorry Maah" shiru Anuty Zulfa ta yi can tace "Can AA Genotype marry AA?" Gently Budurwar tace "Eh" Zulfa tace "What's AA Genotype?" Budurwar tace "The term “homozygous” is used to describe the pairs “AA” and “aa” because the alleles in the pair are the same, i.e. both dominant or both recessive. In contrast, the term “heterozygous” is used to describe the allelic pair, “Aa”... Da mmki Anuty Zulfa tace "Menene jinin AA, AS,SS...?" Budurwar mai suna Noha tace "Typically, there are five (5) distinct types of blood genotype. They are AA, AS, AC, SS, and SC. While the first 2 pairs (AA & AS) are normal, AC is rare and the latter two (SS, SC) are irregular and anomalous, commonly causing sickle cell disease, and kowa yasan As da Ss Sikila ne" Tsaki Anuty Zulfa taja domin bata son rainin hankali yarinyar tasan all this take tunanin auren As bayan ita Ss ce tace "Can As marry As?" Calmly Noha tace "A'a" Anuty Zulfa tace "Why, i mean mene ya sanya they can't marry?" Shiru Noha tayi Anuty Zulfa ta gyara zama tana zare glass ɗin idanunta tace "Look at into my eyes Noha, A wannan rayuwar abinda kke so ba shine kke samu ba, U love him ba matsala, U can love him till the end of your life, amma kin fara tunanin halin da zaki shiga when you'll marry him har kuka haihuwa, AS ya auri AS double sickle ya samu, wani kariya wani zallar Sickle, Subuhanallahi bare kuma aure tsakanin AS da SS, dan me ake Aure Noha tell me? Badan samun farin ciki da kwanciyar hankali da samun ƙyakkyawar zuri'a ba, akwai Sickle mai shan jini, akwai mai karya mutum, akwai mai taɓa ɓargo ke kanki ina tunanin Mamanki ke kula da lamarinki, idan kikai aure ke ciwo yaro ciwo miji ciwo, waye zai kula da wani? U hve to think very carefully, kina Sickle is does means baki da ƴan cin samun mijin da kike so ko kike fata ba, kiyi hqr ki rabu dashi ki jira rabonki yana nan zuwa let him go.... Wlh Noha you deceive yourself Allah" Noha zatai mgn Anuty Zulfa a tsawace tace "Get out please.... U hve nothing nothing to say" fita Noha tayi tana goge hawaye, tace baki ƙofa Anuty Zulfa tace "U can marry him b ruwana, Am just advice you ne. Shiru kawai Noha tayi har ta fice daga office ɗin, Anuty Zulfa ta bita da kallon tausayi.... Gently Abeed ya zame Sara daga jikinsa idanunsa ya buɗe a kanta ganin yadda take kallonsa ya ɗan kame fuska Murya can ciki yace "U are sick,daina kuka" kai ta ɗaga masa kafin tace "Promise me Uncle" Kallonta yyi bai dai ce komai ba tace "U never sick again, ka daina kwanciya hk" kai ya ɗaga mata yn mmkin yadda ta damu da ciwon nasa, Sara ta marairaice fuska tace "To mu ƙulla mn" fuska a kame Murya can ƙasa yace "Stop acting like a baby Saaaaaa" turo baki tayi ba tare da tace komai ba ta ɗauke kanta zuwa gefe guda, wani ɗan cute smile yyi yana ya motsa fuska a lokaci ɗaya yace "Ok i promise" juyowa tayi ta kallesa tana washe bakinta kamar yarinya har manyan dimples ɗinta na lomawa tace "Thanks" idanunsa ya ɗauke ya mayar zuwa kan ƙofa kallo guda yyi musu ya ɗauke kansa tare da rufe idanunsa ya shiga kaɗa ƙafa kaɗan kaɗan Dr Haris dake biye da Anuty Zulfa da kuma Autar ta yace "Sai dai yana zuwa scanning time to time" Anuty Zulfa idanunta akan Sara tace "bbu matsala, zamu shige dashi ne ng jikin allahamdulillah" Dr Haris yace "Allah ya ƙara lfy bari na koma" kujera Anuty Zulfa taja ta zauna tana faɗin "Ya jikin Sara?" Kanta ƙasa ba tare data ɗago ba tace "Ai lou nake" Zulfa tace "I see" direction ɗinta ta juya kan Abeed da bai ma kalleta ba gudun masifa tace "Ka shirya zamu shige" da sauri ya buɗe idanuna ya kalli Anuty Zulfa tana haɗe fuska bbu alamun wasa tace "Mene ka tsare ni da ido ko zuwa ne ba zakai ba" ya motsa fuska yyi kamar ba zai mgn ba sai yace "Ina za'a Mami...." Kai tsaye tace "My house" yace "Ohh! zan shige nawa gidan" ba tare data kallesa ba tace "To ƙaruna nasan da gidan naka nace nawa, kana iya ƙin zuwa idan kaga ban isa ba" shiru kawai yyi tare da Miƙewa zai fita da sauri Sara ta sakko daga kan bed ɗin tana riƙesa tace "Twin zani" bai tsaya ba ya nufi waje Sara na biye dashi, Anuty Zulfa dai ƙafa take kaɗawa idanunta akan wayarta, ganin da gske Sara binsa zatai yasa tace "Sara come back" maƙale ka faɗa tayi tace "Zani Twin" a tsawace ce Anuty Zulfa tace "I said come back.." jikin Sara har wani rawa yake sbd firgita, da wani irin sauri kuma ya fice domin ba zai jure jin tsawar ba, yana fita Sara ta saka kuka ƙasa ƙasa, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru Anuty Zulfa dai ba tace komai ba, Autar ta tace "she's cry Mami" harara Anuty Zulfa ta cillawa Autar ta, sai da ta gama duba abinda zatai a waya kafin gently ta kalli Sara tace "Zonan, ƙanwata" maƙale kafaɗa tayi Anuty Zulfa ta miƙe tare da kama hannunta suka zauna tace "Yi Shiru Kinji" Sara tace "Ya tafi" tace "zai dawo,kina jina Sara?" Kallonta kawai Sara tayi tace "Ina Mamanki?" Hannunta ta watsa mata alamar bata sani ba, Murmushi Anuty Zulfa tayi tace "Am your mother Sara, i was looking for you since, ban ganki fa zaki farin ciki da zama tare da Mamanki ki zama big and classes beb, Zaki daina wannan shirman ki koma University and start your study, Zaki zama babbar mace did you like it?" Sara tace "Zaki bani mota?" Zulfa Kallonta tayi kawai wato Yarinyar nan kassarata aljanun suka suyi, su sukai ta zama kamar ƙaramar yarinya dole ta nema mata mgn, sbd duk zurfin cikin Abeed sai ta takura masa ya faɗi komai itama ya ɓoye mata cewa ita ta caka masa wuƙa, kanta Zulfa ta shafa tace "Zan baki mota babba latest car in new York" Sara cikin ƙaramar muryarta tace "To Zani, shima Twin zashi?" ikon Allah kawai Anuty Zulfa tace a ranta kai kawai ta ɗaga mata, kafin ta kalli Auta tace "Raka ta bathroom tai wanka tai brush taci abinci mu tafi" Bathroom suka nufa Anuty Zulfa mmki da girman Sara take amma gata nan sai a hankali, tana zaune ta fito daga wanka a bathroom ta sauya kaya zuwa white-collared t.shirts da Cropped trousers sai Ƙamshin shower gel take, Zama tayi skin ɗinta na wani glowing sosai, breakfast aka bata taci kaɗan tana faraci ta ajjiye tana riƙe ciki, Anuty Zulfa ta fahimci abinda yake damunta tace "Ina zuwa" fita tayi zuwa office ɗin ta, not too long ta dawo ɗauke da injection zatai mata, wani irin zare idanu Sara tayi nan da nan idanunta ya kawo ruwa tace "Mami banso" Mami tace "Zaki daina jin ciwo" girgiza kai tayi tana yarfe hannu..A hankali Abeed ya turo ƙofar ya shigo ƙamshin Thierry mungler ne ya fara musu sallama, yana sanye cikin Modern Fit Suit sai ƙafarsa dake cikin Chalsea-style Boots, hannunsa ɗaya zube cikin Aljihun suit ɗin, sumar kannan nasa sai ƙyalli yake da alama ba a nan ya shirya ba, Cak ya tsaya daga inda yake tsigar jikinsa na tashi sbd ganin allurar nan take hankalinsa ya tashi, juya yyi zai fita Anuty Zulfa tace "jira ni" kansa ya sunkuyar ya shiga danna Wayarsa ba tare daya san abinda yake ba, wani ihu Sara tayi lokacin da Zulfa tayi mata allurar tana kiran sunan Abeed, Abeed runtse idanunsa yana wani irin taune bakinsa, Murmushi Zulfa tayi tace "Sorry Sara, muje" ƙin motsawa Sara tayi kanta a ƙasa jikinta na rawa nan da nan idanunta sukai jajir, Zulfa tace "Saraaa" amma bata motsa ba ta juya taga Abeed waya kawai yake dannawa tace "Is she alright?" Idanunsa ya ɗaga irin bai gane ba tace "Kalli Saraa" ya jima da fahimtar bata ita kaɗai bace a yanzu sai kawai yace "Ban sani ba" yana faɗin hakan ya fita daga room ɗin, Anuty Zulfa ta kalli Auta tace "kwashe kayan ki kai mota" ta faɗi hakan tana kama hannun Sara ta ɗura mata kinomo a saman kayan kana ta jata zuwa waje, suna tafe tana turjewa a haka suka isa wajan motar, a entrance ɗin asibitin ta samu Abeed waya manne a kunnansa da alama mgn yake, Sara ta saka a baya ita da Auta ita kuma ta nufi wajan driver ta zauna, tana jiran Abeed ya gama, Abeed ba wata waya da yake, baya son binta ne ba zai jure yawan surutu ba, Horn ta danna masa hakan yasa ya nufi wajan motar yana tafiya a hankali, yana ƙarasa wa ya kalli Zulfa yace "Zan amshi abu" kallonsa tayi kafin tace "Abeddeen yaushe na fara wasa dakai?" Ya shafa kansa idanunsa a ƙasa yace "Zan zo Mami" motar ta rufe ba tare data ƙara ce masa komai ba, ya saci kallon Sara dake zaune a baya jikinta duk rawa yake juyawa yyi zuwa cikin ward ɗin yana kiran Khabeer.. Anuty Zulfa taja motar ta wani irin gudu tabar hospital ɗin, tana fita wata mota ƙirar Chevrolet Silverado wacce bata da baya nan ta manyan yara ta shigo cikin asibitin, Parking Khabeer yyi Abeed na tsaye yaga kiran Khabeer ɗaga ba walking slowly ya nufi motar da sauri Khabeer ya buɗe masa motar yana zuwa ya shiga ya rufe, key yyiwa motar ya fita suna kan hanyar zuwa Khabeer ya saci kallon Abeed yace "Sir ya jiki?" Idanun Abeed a rufe yana sauke numfashi a hankali ya ɗan ɗaga kansa, Khabeer yace "Ma sha Allah, Allah ya ƙara afuwa" nan ma kai kawai ya ɗaga masa, har suka isa babban gidan nasa idanunsa rufe, ƙofa Khabeer ya buɗe masa, ya fito a hankali cike da nutsuwa da kamala yana fitowa ya zare jacket ɗin Suit tare da riƙewa a hannunsa, kallon Khabeer kawai yyi Khabeer yace "Ok zan faɗawa Danish" ciki ya shige yana dafe kansa, yana zuwa part ɗinsa an gyara komai direct bathroom ya shiga yana zare kayan jikinsa, shower ya sakarwa kansa yana
fidda numfashi, ya san dole Anuty Zulfa ta nemesa sbd Sara dan kanta za tace yazo ya tafi da ita, kamar ita ta Kawo ta ƙasar, kashe showern yyi ya sanya bathrube jikinsa sai ƙamshin MUD BEGIN Natural Shower Gel yake, wajan mirror ya nufa ya ɗauki SFT's peppermint coated fennel seeds ya saka a bakinsa, Remote ya ɗauka ya ƙure gudun ac kafin ya kwanta kan bed tare da jan duvet ya rufe jikinsa, ya jima idanunsa a buɗe kafin can ya rufe idanunsa bacci ya ɗauke sa. har bayan sallar asr yana bacci, slowly ya shiga buɗe idanunsa da sukai masa nauyi, da sauri ya runtse idanunsa sbd wani irin abu ya zaki tsakiyar kansa, ga wani abu da yazo mararsa ya tokare, can ƙasan ransa yake cewa "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ya jima kafin ya miƙe tsaye kansa tuni yyi masa nauyi, shower yyi ya ɗaura alwala kafin ya Sanya jallabiya, a nan yyi sallar tare da istigifari na makarar da yyi, yana zaune Wayarsa tayi ƙara ganin sunan Anuty Zulfa yasa yaƙi ɗaga kiran, ya jima zaune gently ya miƙe ya sauya kaya zuwa wata red ɗin Armless mai babbar hula da zif, sai wando 3Qauter sai ƙamshin Bois elite yake, sumar kansa data fuskarsa suna wani sheƙi, Main Parlo ya fito bayan ya zuge gaban rigar nasa ƙirjinsa duk a waje, zama yyi a Main Parlo bayan ya ɗauki madara da cup sai chocolate, haka nan ya samu kansa cikin damuwa da son manta wani abu wanda yake da tsananin muhimmanci a gunsa, a hankali yake shan Madarar ya nayi yana danna system ɗin sa, G-mail ɗinsa ya shiga nan ya fara ganin saƙwanni ana haka wani saƙon Abba ya shigo, fararan idanunsa ya lumshe yana jan numfashi kafin ya buɗe idanun tare da shiga cikin message wata ƙyakkyawar bugawa zuciyarsa tayi abinda ya gani ba ƙaramin girgiza sa yyi, al'amarin daya saya sarawar kansa, abinda ya zama tubalin ruguza dukkan wani farin ciki da jin daɗi haɗi da kwanciyar hankalin da Abeed yake ciki, saƙon Abba ya zama silar faɗawarsa dukkan wani abu bai taɓa tsammani a rayuwa ba..... Rufe system ɗin yyi domin baya fata ya sake ganin koda kalma guda na saƙon, yana zaune shiru kamar wani zautacce har aka kira magrib ƙin tashi yyi maimakon ya gabatar da sallar sai kawai ya kwanta kan kujerar nan take bacci ya ɗauke sa, baccin da bai san dalilin faruwar sa ba, yana jin yana gab da barin wani muhimmin abu a cikin rayuwarsa.


Zain Abeed isn't free contact to subscribe dan darajar Allah👏🏻........08119237616*26 Nimcyluv*
Ya manta when last daya daɗe bai bacci kamar haka ba, idanunsa ya buɗe kaɗan yana dafe kansa da hannayensa duk biyun, kafin gently ya miƙe yana tafiya kamar mai irga foot steps ɗinsa, bedroom ya nufa cikin tariyar nan nashi a nutse mai cike da ƙasaita da tarin haiba, yana shiga bathroom ɗin ya zame Armless ɗin jikinsa tare da sakarwa kansa shower wata ƙyakkyawar ajjiyar zuciya ya sauke lokacin da ruwan ya sauka a tsakiyar kansa ya daɗe ruwa na Dukansa kafin ya kashe showern wani irin ƙamshin Nivea men active clean shower gel na tashi a jikinsa, yana fitowa ya shafa wani body oil sama sama kafin ya ɗauki Double Breasted Suit ya saka a jikinsa, bayan ya gama shiryawa yyi sallah ya ɗauki key car time ɗin wajan 10 na dare, entrance ɗin gidan nasa ya nufa, Khabeer na ganinsa ya tashi da sauri yana faɗin "Sir fita zakai ne? Da wacce motar" shiru Abeed yyi har ya nufi wajan wata Toyota Rav 4, ganin Khabeer na biye dashi yasa fuska a kame cike da kwarjini ya juya tare da kallon Khabeer ɗin, bai ce komai ba ya buɗe murfin motar tare da shiga mazaunin driver ko addu'ar daya saba ya nayi ne zamu zarafin yi ba, key yyiwa motar ya fita da wani irin sauri kamar zai tashi sama, wata waƙarsa ya sanya cikin motar yana tafe yana ji yana ɗan lumshe idanunsa, har ya isa wani da alama peach ne, parking yyi ta cikin motar yake hango Mutane ka ɗan kaɗan kowa yana harkar gabansa, kashe motar yyi tare da fitowa a hankali yana kame fuska, gaba ɗaya idanun matan wajan suka dawo kansa, they can't believe cewa Singer ɗin nan suke gani a gabansu, domin ba kowa ke ganinsa face to face ba, taɓe baki yyi gently ya nufi wajan wata ƴar ƙaramar rumfa mai ɗauke da tsuntsaye ga ruwa na sauka a hankali a wajan wasu different colours na sauyawa, kan Kujera yaje ya zauna tare da ɗura ƙafarsa ɗaya akan ɗaya ya fara danna Wayarsa, daga can ɓangaren wasu ƴan mata ne zaune su biyu gaba ɗaya hankalinsu yana kan Abeed ɗaya tace "He's so handsome and extra ordinary, see the way everyone is looking at him, i just like his style" ta faɗa tana

Please Login or Register in order to submit comment