Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zubda yawo tace "Zuciyar matar nan duk agurɓace take, da ƙyar idan bata da haɗi da ƴar ta'adda ba" Anuty Zulfa dai bata kula kowa ba, a hankali ta tura handle ɗin Ƙofar tare da shiga ciki, tana shiga suka haɗa Idanu da Sarah da sauri Sarah ta ɗauke kanta, sbd faɗuwar gaba domin a yanzu komai ya dawo mata ta fahimci dalilin kwanciyar ta a hospital, zama Anuty Zulfa tayi tana bin Sarah da kallo kafin tace "Tashi zaune" a hankali ta tashi zaune tana jure zafin da take ji, Anuty Zulfa tace "Yanzu Sarah irin rainon da nayi maki kenan, da har zaki bi namiji ba tare da kin sanar a gida ba?" Bakinta na rawa Hawaye na sakko mata tace "Am sorry Mami, ban sakewa" tsawa ta daka mata wacce ya sanya Sarah saurin matsawa jikinta na rawa tace "Ni kike faɗawa sorry? Sorry for yourself Sarah, da kin san zunubin da kika aikatawa kanki da ba kice haka ba" kasa mgn Sarah tayi kanta a ƙasa, Anuty Zulfa tace "get down" da sauri ta ɗaga kanta ta kalli Anuty Zulfa,a hankali ta sakko da ƙafarta Zuciyarta na bugawa, ganin ta sakko daga bed ɗin ta zauna ba tare data tashi ba, yasa Anuty Zulfa Miƙewa tazo har inda Sarah take hannunta ya sanya ta fisgota tsaye ƙara Sarah ta saki tana riƙe hannun Anuty Zulfa a raunace tace "Ma..Mami" haɗe fuska Anuty Zulfa tayi bayan ta miƙar da Sarah tsaye, zama tayi tace "Walk" a hankali Sarah ta kalli Anuty Zulfa sai kuma ta fara tafiya tana daure dukkan zafin da take ji danma ta fara jin sauƙi, ganin ba taga alamar komai ba yasa Anuty Zulfa sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya tace "Come and site" zama Sarah tayi tana sakin ajjiyar zuciya, a hankali cike da son fahimtar da Sarah everything tace "Sarah wace ni a wajanki?" Kasa Mgn Sarah tayi sai ƙasa da tayi da kanta, Mami tace "Speak up Sarah" Sarah tace "you're my mother,Mami" Mami tace "A good mother never ta zaɓarwa Yarinyar ta bad husband, Sarah I truth Yarima Yisham, yana da hankali nutsuwa, yana da girmama babba yana mutuwar sonki, wlh kika zauna da Yarima Yashim You never cry,sad zai zama miji abinso a gareki Sarah, accepted my choice" Bugawa zuciyar Sarah tayi tsoro da fargaba suka wanzu a Zuciyarta, me Mami ke faɗa haka me take son cewa, a sanyaye Sarah tace "Mami me kike son nayi?" Anuty Zulfa tace "Noting, ina son duk wanda yace ki zauna wajan Yaya Rooma ko kuma ki koma Kano wajan Amma da zama Kice baki so karatu zaki ƙarasa waje na, the best reason kuma Shine" shiru tayi Sarah ta kafe Mami da Idanu, a hankali Anuty Zulfa tace "An ɗaura auren ki da Yarima Yashim, ke matar aure ce yanzu Sarah, kin zama matar Yarima Yashim" kallon Mami kawai Sarah take without blinking, Zuciyarta banda bugawa babu abinda take, Yaya zatai da Jaan ɗinta? Da wanne baki zata faɗa masa ta auri waninsa, tayaya zataiwa Mami bayanin cewa babu son Yarima Yashim a Zuciyarta? Ta yaya zatai zaman aure da wanda Zuciyarta bata so? Zamanta tare da Yarima Yashim zunubi ne, domin tana aurensa amma zuciya da gangar jikinta yana wajan Jaan ɗinta, kasa Mgn tayi domin komai ya daina yi mata daɗi a wannan duniya,ya karya al'ƙawarin da yyi mata sam bai san girma da kimar al'ƙawari ba, Ganin yanayin Sarah yasa Anuty Zulfa kwantar da Murya tace "Don't worry, Zaki zauna dani har ƙarshen last semester na level 2 ɗin da kika ɗaukar wa Yarima zafin nan zamu fara bincikar alhhalinki, I'll teach you yadda zaki kula da Mijinki da everything ba rayuwar aure, kada kiji nauyi da girma na, at this point ki ɗauki ni Matsayin ƙawa Aminiya" gently Sarah ta ɗaga kanta bata da bakin faɗawa Mami bata son zaɓin da tayi mata, zatai accepting auren matsayin nata salon ƙaddarar, tayaya zata gidan wani ba tare da budurci ba? Ajjiyar zuciya ta sauke koda bata auri Jaan ɗinta ba,tabar masa abu mai matuƙar muhimmanci a rayuwarta hakan kuma zai tabbatar masa da irin son da take masa..... Hijab Anuty Zulfa ta bata ta sanya kana ta saka slippers suka fito waje, tunda suka fito idanunta ya sauka akansa yana zaune saman Kujera cikin shigar wata dakakkiyar shadda fara tass ɗinkin half body, sumarsa kwance a bayansa, idanunta takai zuwa ga hannunsa da mmkinta sai taga zanan tattoo kwance a hannunsa, da sauri ta kalli ɗaya gefen suka haɗa Idanu da Zain wanda yake zaune cikin wata Nevy blue ɗin Suit, sai a yanzu ta gasgata zan can Jaan ɗinta Tabbas su biyu ne masu kama ɗaya, juyawa tayi zuwa inda Abeed yake zaune suka haɗa idanu tun daga sama har ƙasa yake binta da kallo
ba tare da yyi Mgn da kowa ba ya miƙe tsaye, walking slowly ya fita zuwa entrance ɗin hospital ɗin rabinsa da cin abinci harya mata jiri har ɗaukansa yake, Naila data saki baki tana kallon Sarah ta tafa hannunta tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w gaskiya da ƙyar Zulfa'u taga Annabi, yarinyar da jikana ya kusan macewa a kanta ashe tana wajanta, to Alkur'anin Ubangiji ƙafata ƙafar Saratu, naga dai bake kika samo yarinyar ba, ba kuma daga cikin ki ta fito ba, da zaki zauna kiyi bake bake a cikin rayuwarta yarinya duk kin ruɓar mata da zuciya, kalli yadda ta fara kallo na kamar taga ƴar iska" Anuty Zulfa ba tace komai ba, Yaya Rooma ta kalli Naila tace "Muje gida sai anyi magana" Naila ta miƙe tana taɓe baki tace "Eh kuma dai kin kawo shawara,bana ta ihu a titi kamar wata ƴar iskar Legas ba" fita sukai baki ɗaya, Anuty Zulfa ta nufi motar Yaya Rooma hannunta riƙe da Sarah, Zain kuma ya shiga motar Abeed, Naila ma gidan baya ta shige kusa da Abeed Zain dai bai kula ta ba, yaja mota suka nufi gidan Yaya Rooma, a hankali Abeed ya zame daga jinginar da yyi ya ɗura kansa saman cinyar Naila, Naila ta shafa sumar kansa tace "Ai lokacin kawai nake jira na rantse idan Za'ai yaƙi ba zan yarda ba, sai na ɗaukar maka fansa, duk an illata min jikin yaro da bugun abu an hana zuciyarka sakat, shima mai Rawanin koni koshi" ta ƙare maganar tana shafa kansa, shiru Abeed yyi yana sauke numfashi yana jin nauyin zuciyarsa na raguwa, rufe idanunsa yyi, har suka isa gidan Yaya Rooma kansa yana cinyar Naila, motar gidan masarautar Zazzau na ƙoƙarin fita daga gate ɗin gidan Yaya Rooma motocin su Zain na shiga, fitowa Yaya Rooma tayi cikin girmamawa Yaya Rooma ta nufi motar tun daga nesa Fulani Bilkisu ta saki kwantaccen Murmushi tana bin Zain Abeed da idanu, kallon sha'awa da birgewa, Yaya Rooma tace "Sannu da zuwa Fulani,irin zuwan ba zata" Fulani Bilkisu tai Murmushi kawai Kilishi dake gaba tace "Ance sirikar mu tayi accident shine muka zo dubiya" Yaya Rooma tayi Murmushi tace "Sannunku da zuwa Fulanin Zazzau ku shigo mana" buɗe ƙofa Fulani Bilkisu tayi ta fito, Kilishi ma haka, idanun Fulani Bilkisu ya sauka akan Sarah ta shiga binta da idanu, kallo Guda tayi mata ta gane itace matar Yarima kuma ta amince da ita, yarinyar ta kwanta mata, Sarah kanta a ƙasa a ƙasa ta shige cikin gidan Beeba na ganinta ya kurma ihu tana "wlcm back dear, Mrs Yashim Al'khasim Abubakar Wahab" dam! Zuciyar Sarah ta buga nan da nan hawaye ya shiga sakko mata, da ɗan sauri ta shige part ɗinsu tana shiga ta shige bathroom, warm water ta haɗa mai zafi ta shiga ciki duk azabar da take ji haka ta daure, wanka tayi sosai jikinta ya ware kana tayi Alwala, wata simple Abaya ta sanya a jikinta, komai na duniya baya yi mata daɗi, babu abinda take so irin taga Jaan ɗinta kusa da ita, sallar Zhur tayi ta kwanta saman bed, ji tayi kwanciyar ta isheta hakan yasa ta miƙe a hankali ba tare data ɗauki vail ba, slippers kawai ta sanya ta ɗauki wayarta, wata ƙofa ta buɗe tare da ficewa tana fita ta rufe ƙofar,kai tsaye Garden ɗin gidan Yaya Rooma ta shiga, tana shiga ta tsaya ƙasan bishiyar mango a hankali take shaƙar Ƙamshin fresh air da kuma Ƙamshin nunar Mango ɗin wanda yake mata daɗi, tana tsaye taji an rungometa a hankali ta baya, kafin gently taji ya ɗura kansa saman shoulder ɗinta hannayensa duk biyun ya zago ta cikinta yyi holding nata very tight, ajjiyar zuciya suka sauke a tare duk da bata juya ba amma tasan babu mai mata haka sai shi, sun jima haka zuciyoyinku na harbawa lokaci guda, kafin slowly ya karkatar da fuskarsa zuwa gefen fuskarta, kwantaccen sajansa ya shiga goga mata a saman fatar fuskar ta, numfashi Sarah ta ƙara saukewa sbd yadda taji yana manna mata softness lip's ɗinsa a kumatunta, gently Abeed ya matsar da bakinsa zuwa bayan wuyanta a hankali slowly daidai dugun wuyanta ya ware madaidaicin bakinsa, tare da manna lip's ɗinsa a bayan wuyanta ya shiga sauke mata wani irin fitinan nan kiss mai tsayawa a zuciya, a hankali cike da salo na son manna mata masifaffiyar Soyayyar sa a Zuciyarta ya shiga lashe fatar dugun haɗaɗɗan wuyan nata, rawa jikin Sarah ya fara gashi daman bata da wani ƙarfi ga kuma abinda Abeed ɗin ke mata a yanzu, ƙara shigar da ita jikinsa yyi yana manna bayanta da ƙirjinsa, gangaro da bakinsa yyi zuwa wajan kunnanta wanda babu ear-ring a jiki kama fatar kunnan yyi daidai wajan hudar kunne ya shiga tsotsa gefe guda kuma yana goga mata kwantaccen sajansa wanda sanyin sa ke ratsa zuciyar Sarah... It was kind of gentle romance Abeed yake mata wanda ya gigita duniyar Sarah Salman har bata san lokacin data ɗura hannayenta a saman nasa wanda yyi holding cikinta dasu, ganin yadda duk jikinta ya saki tana neman zubewa a wajan yasa, Abeed juyo da ita zuwa gabansa, idanunta ta ɗaga a hankali suka haɗa idanu, wani irin kallon ƙwayar idanunsu suke without blinking, baya yi kaɗan Ya tsaya hannayensa biyu zube cikin Aljihu, staring at her straight in to her eyes with so much sympathy and pity, har yanzu kallon juna suke yyinda Sarah take tsoran faɗa masa an mata aure ga waninsa, a hankali ya buɗe baki a karo na farko tun bayan fitowarsu daga hospital cikin nutsuwarsa da kamewa kamar babu abinda ya damesa yace “Saaaaa...” saukar muryarsa ke da wuya a cikin kunnanta da gangar jikinta, sai ta ji duk wani rauni na duniya da maraicin duniya ya rufto mata..... “This is indeed a shoulder to lie on” za taso ta kwanta a wannan kafaɗar tayi kukan ta mai isarta a inda ta san za'a lallashe ta, yyi amfanin da sunan da babu wanda ke faɗa mata sai Uncle Twin ɗinta.. A nutse Abeed ya sake buɗe baki yace “Saaaaa.... Come and cry on my shoulder” kamar mai jira da gudu tayi wajansa tana zuwa ta faɗa jikinsa, tsayinta ba zai kai ta ɗura kanta a shoulder ɗinsa ba, a hankali ta manna fuskarta a ƙirjinsa tare da zagaya hannunta a waist ɗinsa ta ƙanƙamesa tare da sakin wani irin raunataccen kuka, kuka take sosai kukan da bata taɓa irinsa ba a rayuwarta ba, kukan da idan ba soyayyya ba da wahala Mutum yyi irinsa sai dai mutuwa. Still holding onto her ya ɗura nasa kan a saman shoulder yana rufe idanunta, cikin ƙasa da murya sosai yana sakar mata nishi a kunne yace "Nine Jaan, kuma nine Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas,kuma nine Uncle, then nine Twin....


Zain Abeed na kuɗi ne, kiji tsoran Allah kada ki karanta min without pay........ It's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank.... Via EVEDANCE 08119237616


SARAUTAR MARUBUTA❤️***55***Maganar Abeed ya daki kunnanta, kukanta ya tsaya Cak a hankali ta zame jikinta daga nasa, ta shiga yin baya tana Girgiza kanta tama kasa magana sai kallon cikin idanunsa take was very confused, she was confirming what he was saying to her, she couldn't understand how he was saying these words,that means Abeed is her Jaan, It was Abeed who raped her not Jaan,kasa Mgn tayi sbd shock da sauri ta juya masa baya tana ɗaga fuskarta sama da sauri take shaƙar iskar dake kaɗawa a wajan, ganin haka yasa gently Abeed ya fara takawa a nutse zuwa inda take, yana ƙoƙarin taɓata tayi saurin juya idanunta rufe tace "don't you dare touch me, don't try to touch anything on my body again" She finished her speech with tears falling from her eyes, tsaye yyi duk da ransa a ɓace yake amma hakan bai yana yyi saurin yin ƙasa da kansa yana sakin wani cute smile , a hankali ya shafa kansa tare da jan sajansa, walking slowly ya Ƙarasa inda take ba tare da yace komai ya leƙa fuskarta tayi saurin juyawa, a nutse cikin Murya mai taushi kana jin Muryar tashi kasan he's serious sick jarumta ne kawai, maganar da zai ya fasa ya shiga Kallonta kamar yadda take binsa da Idanu kafin Calmy ya kame fuskarsa yace "U said wat?" Ta ɗauke fuskarta tana ƙoƙarin shigewa ta gefensa zata tafi yyi saurin saka hannu ya kamota tare da haɗata da side body Nashi, ƙoƙarin kwancewa take yyi saurin jawota zuwa gabansa tare da bata wani very tight hug, ya ɗaure fuska kamar ba zai mgn ba sai kuma yaja hancinta yace "Uhm repeat it" turo baki tayi Zuciyarta sam babu daɗi amma ta kasa jin haushin abinda yyi mata cikin Muryar kuka tace "Nika sakeni, babu kyau abinda kke min" yana zura hannunsa cikin rigarta try to touch her breast yace "Idan naƙi fa?" Kuka ta sanya masa tana narkewa jikinsa tace "Allah zan maka ihu,kasan ba kyau abinda kke ka daina taɓa jikina banso" ya ware idanunsa sosai ba tare da yyi niyya ba, ya murza hannunsa akan breast ɗin ta, jikinta ya fara rawa tace "Innalillahi mene haka, Mami tace Am married woman now, what are you trying to do, please stop it I don't like anymore" ta faɗa gaba ɗaya a tsorace take sai juya idanu take da tsoran kada wani ya gansu a haka, bakinsa ya ɗura a kunnanta yace "Mene ba kyau?" A fusace tace "Taɓa jikina da kake mana Uncle, kasan abinda kke yanzu haramun ne, zunubi kake son ɗaukar mana bana son ka ɗauki zunubi" ta ƙare maganar tana buɗe baki zata saki kuka yyi saurin rufe mata baki da hannu, gently ya ƙara haɗata da jikin sa, kafin a hankali Muryar mai sanyi yace "To ina son zunubin ni" shiru sarah tayi sai ɗauke fuska take Abeed ya juyo da fuskarta baki ɗaya yace "Do you think ina shiga haƙƙin ki ko?" Sarah na ƙara sakin kuka tace "Mene yasa haka Uncle, na kasa fahimta mene yasa kayiwa zuciyata haka? Mene yasa kaƙi faɗa min you're the one daya bani kidney, Why didn't you tell me that you are the one who helped my life?,Why didn't you tell me the truth that I am in love with you? Mene ba zaka tausaya min ba, zuciyata ta kasa ɗauka kana so nane ka ɓoye ko mene?" Ta faɗa tana sakin wani kukan tare da ƙoƙarin Zamewa daga jikinsa, kasa magana Abeed yyi sai ƙirjinsa daya buɗe ya bata damar kwantar da kanta tayi kukan daya isheta, kuka take sosai cikin kuka tace "You raped me Uncle, me zan cewa mijin da aka zaɓa min? Tunda ba'a barni na zaɓi muradin raina ba, kace kaine Abbana, kai ne Ammina, kai ne sister brother friends, mene yasa zaka zaɓi akaita min haka? Kayi min fyaɗe a lokacin da igiyar auren wani ya hau kai na, me zance da da Yaa Ya..." Kafin ta Ƙarasa faɗar sunan Yaa Yashim Abeed ya sanya yatsarsa ya buge mata bakinta, ta ƙara sautin kukanta, zata saka hannunta ta shafa lip's ɗinta wanda daya daka yyi saurin riƙe Hannun, da ƙarfi ya kuma sanya yatsarsa ya buge lip's ɗinta wanda ya sanya Sarah runtse idanunta ta ƙara sautin kukanta, haɗe fuska yyi wacce tayi jajir yana fesa mata numfashi yace "Da zafi?" Kai ta ɗaga masa tace "Let go of me,ka sakeni banso bafii" ya jinjina kai yace "Good, take this as punishment, Duk sanda kika sake faɗin sunnan wani" yana faɗin hakan ya ɗura bakinsa daidai inda ya bugeta, slowly ya shiga busa mata iska kafin gently ya cafke lip's ɗin ya shiga mata wata sahihiyar sumbata wacce ta sanya Sarah ƙoƙarin zube masa numfashinta na yin sama, sai da ya tabbata all zafin da take ji daɗi ya maye gurbinsa ya saketa, bayanta ya juya ya haɗa da ƙirjinsa sosai yana kwantar da kansa a wuyanta yace "Look!" Ya faɗa yana nuna mata wasu fararen tsuntsaye guda biyu, cikin ƙasa da Murya da kuma tilatawa kansa Mgn yace "kallesu mata da miji ne, ko kuma uwa da ɗa" shiru yyi yana sauke numfashi a hankali kafin yace "A good father never hurts his own daughter,If you believe that, then believe that I will never hurt you, Sarah" shiru tayi tana sauke numfashi bai ƙara cewa komai yadai rungome ta, tare da ɗan durƙosawa ya ɗaura kanta a shoulder ɗinsa, a hankali yake patting bayanta, trying to calm her down, Zuciyarta ce ta fara saki kafin tace "Mami tace anyi min aure" shiru yyi mata ba tare da yace komai ba tayi ƙasa da kanta tace "Bai dace kana taɓa ni ba, sbd babu kyau" sai a yanzu ya ware idanunsa sosai breathing nasa yana sauka Calmy yace "A wajanki,da wajanta ne ba kyau?" Da rashin fahimta dake kallonsa sai kuma ta ɗauke kai tana ƙoƙarin zame jikinta ya riƙeta, ta kwaɓe fuska tace "Allah ka sakeni, bacci na keji" ya langwaɓar da kansa gefe tare da kallon sama some minutes yace "So you want to go?" Ta ɗaga masa kai a kame yace "Ok, but" tace "Me?" Ya juya mata fuskarsa yace "Peck me" ta waro Idanunta ita a yanzu kunyarsa ma take ji wlh, har Zuciyarta ta kasa jin haushin abinda yyi mata, idan ta tuna auren dake kanta sai taji tausayin rayuwarsu ita dashi ya kamata, kafin ta motsa ta jiyo Muryar Beeba na cewa "Sarah, Sarah where are you" a gigice tana Kallonsa tace "Dan girman Allah ka sakeni, Beeba fa" ƙara matseta yyi a jikinsa yana ta Kallonta without blinking ba tare da yace komai ba, ganin da gaske ba zai saketa ba ta kwantar da murya tana son sakar masa kuka tace "please Uncle ka sakeni" a taushashe yana tsareta da fararen idanunsa yana kuma ɓoye damuwar ransa yace "Kiss me, Sarah Maamanaaaaa" ya faɗa yana jan sunan sai a lokacin ta tuna sunan Amma Saratu, ita kuma Sarah that's means d same name suke dashi, idanunta yyi rau rau, Beeba ta kuma ƙwala mata kira, ai bata san lokacin data manna jajayen laɓɓanta masu sanyi da taushi a saman kumatunsa ba.. "Mu'ahh" ta sakar masa wani light Peck a kumatunsa, sakinta yyi jikinta na rawa ta nufi ƙofa tana goge bakinta, baya kaɗan Abeed yyi yana maida numfashi kafin gently ya zauna saman kujerar dake wajan a hankali yaja numfashi tare da rufe idanunsa yana jin sanyin lip's ɗinta har ƙasan Zuciyarsa...... Fulani Bilkisu da Kilishi da kuma Anuty Zulfa na zaune a Main Parlo sai Yaya Rooma dake ajjiye drinks, Sarah ta biyo bayan Beeba jiki a sanyaye gaba ɗaya a firgice take gani take tamkar za'a gane abinda tayi, sulalewa tayi tare da zama saman carpet daidai ƙafar Fulani Bilkisu kanta a ƙasa cikin siririyar muryarta tace "Ina yini" Kilishi dai kallon Sarah kawai take, Fulani Bilkisu tayi Murmushi a hankali ta ɗura kanta saman kan Sarah da sauri Sarah ta sauke ajjiyar zuciya "Lafiya, ya ƙarfin jiki?" Fulani Bilkisu ta amsa tana ƙara shafa kan Sarah tare da yabawa da nutsuwar Sarah, Murmushi kawai Sarah tayi sai kuma ta washe fararen white teeths ɗinta, a hankali ta ɗaga kanta suka haɗa Idanu da Fulani Bilkisu tace "Ina ƙalau" hancinta Fulani Bilkisu taja tace "Da sauƙi dai, Princess" sai a lokacin Kilishi tace "Kenan itace wacce Yarima zai aura kuma ba'a san iyayenta ba right?" Dum! Zuciyar Sarah ta buga da sauri ta ɗaga kanta suka haɗa Idanu da Anuty Zulfa, Naila dake zaune ta ɗura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta doka uban salati tana runtse idanunta tace "Muhammadur Rasulullah s.a.w, inji wanne Annamimin yace bata da iyaye? Kamar wacce tayi tashin leges, ƴan iskan Legas ne fa zaka samu ɗaiɗaiko da iyaye wallahi duk ƴan ta zubar ne, ina zaka samu wankakkiyyar yarinya kamar Saratu a Legas hatta sarkin leges ɗin fa ɗan iska ne billahil lazi, abinda acan mukai wayo muna kallon Uban kowa ban san adadin yaƙin da akai akan idanuna ba, duk iskanci mutum idan bai je leges yasin buge ne, to a gsky ba zan biye maki ba muyi ta ihu a gidan jama'a, kuma wannan maganar shegenta Sarah da kikai ko mijinki mai rawani bai isa yyi mana sulhu sai hisba Alkur'an" Naila ta faɗa tana ƙifta idanu, Kilishi kowa idan ranta yyi dubu ya ɓaci tace "A'a yaushe na shegenta ta? Daga Mgnar Iyaye kuma ai maganar aure ake bata wasan yara ba ko kuma gigin tsofa" zabura Naila tayi har tana hantsilawa tsaye tayi gaban Kilishi tace "Ubanki dake ɗaure a kurkukun Leges shine mai gingin tsofan, nafa san komai wlh kibi a hankali kafin na tuna asirin dake ɓoye, ko wanne watsattse kallonsa kawai nake, wani Shegen ne bai iya ta'addanci ba, ana kasss ɗin pamili meye naki a ciki" A hankali Fulani Bilkisu tace "Kiyi hqr Naila" Naila ta kalli Fulani Bilkisu tace "Ji banza? To a gsky imaninki yyi yawa da zan tuna asiri wlh ba zaki ban hqr ba da ƙyar daga nan baki shige leges ko ofis ɗin ƴan hisba Kinyi hayar ƴab ta'adda ba" Anuty Zulfa dai na zaune tana duba time lokacin zuwa lokacin, domin 5 daidai jirginta zai tashi, Yaya Rooma kasa mgn tayi Fulani Bilkisu ta miƙe tsaye tace "Bari muje, Allah ya nuna mana lokacin bikin" Yaya Rooma tace "Amin, Allah ya ƙara lafiya" sai a lokacin Anuty Zulfa ta kalli Fulani Bilkisu tace "Ko gaida gida" fuuuuu Kilishi ta fice daga cikin parlon, Naila ta ɗaga Murya tace "Ohhu dai" sai kuma tayi ƙasa da murya tace "Banza ce, ba naji labarin ko haihuwa bata taɓa yi ba ai mantawa nayi ban mata gorin haihuwar ba Wlh" Yaya Rooma tace "Gsky Naila baki kyauta ba, kuma Yarima Yashim ɗan waye ba nata ba? manyan Mutane matan Sarki guda kiyi musu haka" Naila tace "Dan Allah? Matan Sarki ne?" Yaya Rooma tace "Wacce kikaiwa itace matarsa ta farko Kilishi, kuma sirikan kune fa"
Naila tace "Allah?" Yaya Rooma dai tayi shiru kafin ta juya ta kalli Anuty Zulfa tace "Anuty ga abinci fa" Girgiza kai Anuty Zulfa tayi tace "Bana jin zanci abincin nan Rooma, ƙarfe biyar jirgin mu zai tashi" kafin su yi magana Zain yyi sallama ya shigo hannunsa zube cikin Aljihu, ƙamshin Hugo boss da Sarah taji ya tabbatar mata cewa hadda shi, zama Zain yyi Yaya Rooma ta kalli Abeed tace "Ya jikin?" Kallo ɗaya yyi mata ya ɗauke kai ba tare da yace komai ba, Anuty Zulfa ta buɗe hand bag ɗin ta, ta ciro kuɗi ƴan 1k bandir 20 ta ajjiye kujerar da Abeed yake tsaye tace "Sadakin Sarah, naga kamar kaine matsayin Uba a wajanta, an ɗaura aurenta da Yarima Yashim last semester na level 2 za'ai bikin ta tare" baki Naila ta saki kafin ta fasa ihu tace "Wanne Algungumin ne ya aurar da ita, uban waye kuma wani abu shisham?" Abeed dai na tsaye Sarah kuma kanta a ƙasa, Miƙewa Anuty Zulfa tayi tace "Rooma zamu shige, Raudah zo kiyi dropping namu a airport" Auta ta miƙe tare da jan trolly bag ɗin su, Sarah kasa Miƙewa tsaye tayi a hankali ta ɗaga idanunta suka haɗa Idanu da Abeed kenan ita dashi har abada? Hawayen

Please Login or Register in order to submit comment