Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take ɓoyewa ya sakko mata, Anuty Zulfa tace "Sarah Tashi mu shige" caraf Naila ta riƙe hannun Sarah tace "wlh yau zaki san ƴar bariki ce ni, zaki san yadda ake tsiya idan kin tafi da Saratu Allah ya tsine, bayan nayiwa Junaidu al'ƙawarin komai daɗewa zan aura masa Saratu...


Zain Abeed isn't free contact to subscribe 08119237616 via... 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank******56***Daga Yaya Rooma har Anuty Zulfa kallon Naila suke kafin Anuty tace "Junaid kuma?" Naila tace "A'a, bawai ɗan iska bane naji kina kiran sunansa a wulaƙance, nidai a gsky hukuma zan saka su shiga tsakani na dake, ba wani mutunci ne dani ba Alkur'an sai na zageki ta tass, akwai uwar da wani zai iya ne? Kamar dai ke kika haifi Saratu,gantali fa shalale yaga ta nayi a duniya ya ɗakko ta, banda darajar sa zaki ganta ne? Kiyi hqr kada ki ƙullacan, amma ko zaki zagen ƙafa ta ƙafar Saratu" Naila ta ƙare maganar tana saƙale hannun Sarah a hammata, Anuty Zulfa tace "Amma dai kin san makaranta take ko?" Naila tace "Kaji masifa ko? Har a faɗawa Kano makarantu? Gasu nan kaca kaca kamar ana yaƙi a leges, zanje har makarantar nayi musu bayani kawai a Kaita ajin ƙarshe" rai ɓace Anuty Zulfa ta kalli Sarah tace "Kano kike son zama ko zaki bini?" Shiru Sarah tayi tama kasa Mgn duk akanta ake Wannan tashin hankalin, tsawa Anuty Zulfa ta daka mata tace "mgn nake Sarah" hawaye ya sakkowa Sarah bakinta na rawa tace "Mami zan biki" baki Naila saki da shock kafin ya miƙa hannu ta dungure kan Sarah tace "Algunguma" sai kuma tayi wurgi da hannun Sarah tace "Wlh maƙaryaciya ce" rushewa tayi da kuka idanunta akan Abeed da har yanzu yake tsaye baka gane yanayinsa tace "Ɗazo fa na sakata a ɗaki na gama zugeta ta tass, ta amince zata bini amma kaka wannan makirar matar ta zugata? Kalli yadda yarinyar nan ta tuzarta ni to a gsky ba lallai na amince ma Junaidu ya aureta ba, tunda an gama koya mata rashin kunyar ƴan leges" ta ƙare Mgnar tana sake fasa ihu tace "Huhuhuhu, wlh ta tuzartani" Anuty Zulfa tace "To daman ana aure kan Aure da zaki aurawa Junaid Sarah? Bayan yanzu nace maki an ɗaura mata aure da Yarima Yashim?" Naila ta runtse idanunta tace "Wlh ba dani kike ba, ba zan kula ƴar daba ba, yau na ƙara tabbatarwa ƴar bariki ce ke" juyawa tayi ta kalli Auta tace "Wlh uwarki taja maki,ke zan ƙullata bake ba, itafa baƙin ciki take sbd Mai rawani ya auri Saratu,kuma ita ta yaudaresa ta kwashe masa kuɗi daga ƙarshe tace bata sonsa, ina baki labari bawai tunan asiri ba, na cewa Mai rawani idan har nonona yasha to Tabbas ya auri ƴar uwarta Saratu,tun fa daga lokacin Zulfa'u ta kullace ni" Anuty Zulfa tace "A'a Mgnar Gsky, ba'a aure kan aure ai, kada ma ki sake haɗa Sarah da Junaid" Calmy Abeed yace "Gashi nan ke kinyi ai" da sauri ya juya tare da barin parlon, Anuty Zulfa ta kalli Yaya Rooma Sannan ya kalli Zain tace "Nice Abeed yake faɗawa Mgn? Ni yaron nan zai zaga, wait nema nayi?" Yaya Rooma tace "Kiyi hqr, kin san matsalar Abeed ai" fuuuuu Anuty Zulfa ta fisgi hannun Sarah, Auta da Raudah da kuma Beeba suka bi bayanta, Naila ta tofar da yawo tace "banza ce ba, babu abinda ta iya sai yanka cikin Mutane da wuƙa abinda yasa nayi mata shiru kenan, ban mata gorin kuɗin makkan da Mai rawani ya biya mata ba" Zain dai na zaune yana kallon komai ya kasa fahimtar wasu maganganun.... Abeed na fita entrance ɗin gidan yaci karo da Yarima Yashim tsaye yana waya, kallon juna sukai yayinda Abeed yyiwa Yashim kallo guda ya ɗauke kansa gefe, walking slowly ya nufi inda motarsa take yana ƙoƙarin shiga yaji ance "Hey, Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas" Cak Abeed ya tsaya gently kuma ya juya tare da jingina da motarsa ya harɗe hannayensa a ƙirji, frm head to toe yake kallon Yarima Yashim kallon raini, Murmushi Yarima Yashim yyi kafin yace "Zaman tare bai ce haka ba, naga har an ɗaura min aure amma ba kace min congratulations ba, while bana buƙata ba I'm just wanted to say stay away from my wife Sarah, ka cire idanunka daga kan matata, I'm warning you" tunda ya fara mgn Abeed ke kallonsa ba tare da yace komai ba, juyawa yyi zai shiga mota Yarima Yashim yace "Ina Mgn ba kace komai ba, i knw u Love's Sarah, to ka cire ta a rai kafin soyayyar ta, tayi silar baka heart attack, anywhere ng baka damu ba" wani cute smile Abeed yyi yana lumshe fararen idanunsa, kafin a hankali ya taka zuwa inda Yashim yake daidai kunnansa yace "Mene yasa zan damu bayan nasan GANGAR JIKINTA KA AURA" yana faɗin hakan ya juya zuwa cikin mota, Yarima Yashim na ƙoƙarin yin Mgn Anuty Zulfa ta ƙarasu, Abeed ya haɗe rai sosai itama ko inda yake bata kalla ba, bayan Yarima Yashim ya gaisa da Anuty Zulfa yace "Come princess" ya faɗa yana miƙowa Sarah Hannun hakan yasa Abeed ya jingina da jikin motarsa watching all of them, Anuty Zulfa dasu Auta suka shige mota, Murmushi Yarima Yashim yyi yace "Ya jikinki wify?" Ɗagowa tayi suka haɗa idanu da Abeed ya haɗe fuska sosai tare da ɗauke kai, hakan yasa ta kasa bawa Yarima Yashim amsa sai kawai tayi ƙasa da kanta, hannunsa ya miƙa zai kama hannunta tayi saurin harɗe hannun a ƙirji, Yarima Yashim "Oops, na manta nace maki Next week zan shigo New York hutu, I'll spend all my time with you princess" Sarah dai ta kasa cewa komai sai ƙasa take da kanta, Abeed yyi wani irin sakin Murmushi kafin a hankali ya taka kamar zai shige Sarah yana zuwa daidai Inda take tsaye ya ranƙwafa daidai fuskarta, ya sakar nata Peck kiss mai sanyi cikin kasalalliyar Murya yace "Take care, Mamanaaa" yana faɗin hakan ya juya tare da shigewa mota, Suman tsaye Yarima Yashim yyi Sarah kam rawa jikinta ya fara, bata taɓa tunanin Abeed baya da kunya ba sai yau, kafin Yarima Yashim yyi mgn tuni Sarah ta nufi mota jiki na rawa suka barshi tsaye baki a buɗe, tana shiga Raudah tayiwa motar key suka bar gidan, Raudah bata damu da auran Sarah ba, da ace Abeed ta aura shine zata iya yiwa Sarah ko wanne kalar bura'uba.... Zain ya kalli Yaya Rooma yace "Umma batai shawara dake bane?" Yaya Rooma tace "Kasan halin Yaya Zunaiddeen, nayi ƙoƙarin faɗa mata a tambayi ra'ayin yarinyar nan amma tai burus tace, Sarah na son Yarima Yashim kunya ce kawai take hanata nunawa, kuma iya gatan da zata iya yiwa Sarah kenan" Naila tace "huhuhuhu, to a gsky Zulfa'u da ƙyar taga Annabi,sam sam Zuciyarta bata da kyau kamar ruɓar tumatir yasin, za taci ƙwal Ubanta ina na ysin sai na ruguza komai na aurawa Junaidu, nima fa ƴar banza ce" Zain yace "Allah ya kyauta,muma zuwa dare jirgin mu zai tashi" Yaya Rooma tace "Tare Da Abeed?" Naila tace "To Ubanwa zan barwa shi? Bayan an gama lalata masa jiki, tunda idanuna suka gane min abinda ke jikinsa har yanzu kaina juyawa yake kuma ko wanne ɗan banza aniyya bil aniya li'ilafi qurash"........ Kilishi tunda suka koma gida ta kasa zaune ta kasa tsaye, abin duniya yyi mata zafi cin mutuncin da Naila tayi mata har ƙasan Zuciyarta take jinsa, ajjiyar zuciya ta sauke wayarta dake ringing ta ɗauka, tana ɗaga kiran tace "Ya ake ciki?" Daga cikin wayar akace "Ki daina ɗaga hankalin ki, shida gida har abada, ban da kince kada a haukata shi ai da tun tunin mun gama dashi, babu wani wanda zai gaji mulkin Zazzau sai Yarima Yashim, haka kuma babu wanda ya isa ya gano cewa Yarima Yashim ba ɗan Sarki..." Wata tsawa Kilishi ta buga da ƙarfi kafin tace "Ya isa, ba wannan na tambaya ba, kuma...," Motsin da taji a bayanta yasa ta juya da sauri Yarima Yashim ta gani zaune ya kifa kansa jikin kujerar yana shassheƙar kukan abinda Abeed yyi masa ɗazo......... Abeed na kwance daga shi dai 3Quater ƙoƙarin saka kansa Bacci yake ya kasa, kalmar auren Sarah na dawowa kunnansa duk Mgnar da yake faɗa, he just pretend,kamar daga sama yaji Zain yace "Do you love Sarah?" Abeed ya ware idanunsa ba tare da yace komai ba, Zain ya ƙara cewa "Kana sonta?" Mirginawa Abeed yyi zuwa gefe kafin a nutse yace "Wa?" Zain yace "Sarah" taɓe baki Abeed yyi kafin yace "Wace haka?" Zain yace "Ban sani ba, kana Sonta ne?" Shiru kawai Abeed yyi kafin kuma yace "Zaka shiga hurumin Ubangiji,kana haɗa kalmar so da matar aure,ni kaji nace ina son wata ne" Zain yace "That's why I see you are worried about her marriage" shiru kawai Abeed yyi Zain yace "True love cannot be hidden in the heart,no matter how hard you are, love will reveal your weakness,If God makes a division between sai kaga ansha wahala sosai kuma wani ya mutu kai ka aura" Abeed ya haɗe fuska yace "To dawa kke wannan surutun?"...... "I just said it" Zain ya bashi amsa kafin ya zauna kusa dashi yace "Ban san tayaya zan fuskance ka ba, ban san yaushe ka zama haka ba, zuciyata ta kasa ɗauka ace wai kana shaye-shaye, wacce kalar jarrabawa ce?" Shiru Abeed yyi Zain yace "da gaske shaye-shaye kake Biyuni?" Miƙewa Abeed yyi tare da ƙoƙarin fita Zain yyi saurin tare hanya yace "Magana nake maka" a tsawace shima Abeed yace "Kasan dai ni ba kurma bane" Girgiza kai Zain yyi
He was trying to hide his tears, kafin yace "Ni kkewa tsawa sbd na damu dakai Biyuni?" Da sauri Abeed ya nufi wajan Zain yana zuwa ya rungomesa yana sakin ajjiyar zuciya a raunace yace "I have no one, no one is with me, no one asks how I am. no one will ask me whether I have food or not,No matter what you think I did, take it as fate, I have no choice" Yyi mganr a sanyaye yana narkewa jikin Zain, Hawayen da Zain yake ɓoyewa shine ya sakko masa yace "I am sorry Biyuni, Am sorry bana da iko" Abeed ya lumshe idanunta yace "I knw.." sun jima haka kafin a hankali Abeed ya zame Jikinsa daga na Zain bai bari sun haɗa Idanu ba, yyi saurin shigewa bathroom..... Fitowa sukai cikin shiga iri guda cikin haɗaɗɗun wasu suit sai ƙamshi suke, Gaba ɗaya suna baya Khabeer ke driving Naila a gaba sai faɗin take "Inaa,san Katsina ba garin zuwa bane talauci yyiwa ƙasar Ƙasimu mugun kamo haka kurum ka shafi masifa" ta faɗa tana ƙaƙƙabe jikinta kafin ta juya ta kalli Khabeer tace "Kai kam ya naga baƙin ka yyi yawa ne, da ƙyar idan kana wanka sau uku a rana" Khabeer dai yyi Murmushi Naila tace "A'a ba Abin Murmushi bane, wlh baƙin yyi yawa gsky yara ƙanana sai ka firgita su" har suka isa airport Khabeer bai Mgn ba, Abeed kuma yyi shiru kansa a shoulder ɗin Zain, fitowa sukai lokacin tuni ƙofar jet ɗin ta buɗe, Khabeer yyi musu Allah ya kiyaye jet ɗin ya ɗaga zuwa Kano...... Wasu haɗaɗɗun motoci ne su kazo ɗaukan Zain Abeed, sai a lokacin Abeed ya ɗan ya motsa fuska Zain yace yace "What" ya Girgiza kai ba tare da yace komai ba, Zain yace "Abba baya garin, yaje a duba lafiyar a Russia" Calmy Abeed yace "Liar" duka Zain ya kaiwa Abeed ya goce yana faɗin "Ni yayanka kke faɗawa haka" mota gaba ɗaya suka shiga ta kwashe su zuwa Masarautar Bilhira, komai na Masarautar ya sauya wa Abeed rabonsa da ita shekara kusan guda ke nan, rufe idanunsa yyi yana jin zuciyarsa na tsananta bugawa, gefe guda kuma wani sanyi ya keji zai sanya Amma a idanunsa, gaba ɗaya sai da suka fito bai fito, kafin can ya fito da ƙafarsa a hankali kuma ya Ƙarasa fitowa baki ɗaya, Zain na gaba Naila na biye dashi tana faɗin "Jama'a mun dawo, Allah yyi mana dawowa, fadawa, Barori, Kuyangi,bayi, ƙwarƙwara, gamu mun dawo yanzu jirgin mu ya sauka" ta faɗa tana juyawa, Abeed a hankali yake binsu kamar mai tsoran taka ƙasa, suna shiga Main Parlo wanda ya raba part part na babban shashen suka samu Du'a zaune ita da Riya, baki Naila ta saki kafin da sauri ta juya ta kalli Zain tace "Kaga munafuka, Rariya ce fa a gsky muna ta zaune da mugwaye Allah yyi mana tsari yaushe rabon dana ganta duniya tabi fa, sai yanzu ta kwaso ƙwafa ta dawo sbd shalele,to kiyi hqr amma amfasa Wannan Auren" Zain ya kalli Du'a ga mmkinsa sai yaji tace "Wlcm back Dear, Biyuni sannu da zuwa" Abeed babu wanda ya kalla sbd ganin babu Amma a parlon yyi shigewarsa part ɗin su... Riya kasa motsi tayi she was so surprised da ganin Abeed babu ƙasar da bata zaga ba sbd nemansa yau gashi Allah ya dawo dashi,wani daɗi taji tasan a wannan karan dole Auren su ya tabbata, Zain part ɗin sa ya shiga Du'a tabi bayansa, yana tsaye yana cire kaya yaji ta rungomesa ta baya tace "Am sorry, i knw i made a mistake, amma ba zan sake ba, nayi accepted auren daka ƙara" juyawa yyi yace "Are u sure?" Ta ɗaga masa kai yyi saurin rungometa...... Har gari ya waye Du'a na maƙale jikin Zain cike da kissa ta hanashi fita ko'ina tunanin Sairah ne fal zuciyarsa gashi ba lafiya gareta ba..... Wajan kwana uku kenan da dawowar Abeed har lokacin Amma ta kasa zuwa ganinsa, baya cin abinci ko kaɗan ya sanya a siyo masa Chocolate tafi kala ashirin duk wacce ya gutsira sai yaji salam babu daɗi, ya rasa mene yake buƙata gashi rabonsa da Sarah tun a Katsina, rashin cin abincin kuma yasa ya fara ɗan faɗawa, Yana kwance daga shi sai trousers, fitowarsa daga wanka kenan ruwa na ɗiga daga sumar kansa zuwa bayansa, a hankali yaji an shafa kansa ajjiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanunsa, juyawa yyi kaɗan idanunsa ya sauka akan Amma dake zaune gefen gado, tayi kwalliyya cikin farin lace da golden ɗin Alkyabba, Kallonta yake babu ko ƙiftawa yasan ba lallai tace wani abu ba, hakan yasa ya juyar da kansa yana maida numfashi, a hankali Amma tace "Abeddeen" da sauri ya juya suka sake haɗa Idanu, matsawa tayi kusa dashi sosai gently ta ɗauki kansa ta ɗura saman cinyarta, a nutse ta shiga shafa sumar kansa idanunta na cike da hawaye tace "Kayi hqr...., Kuma ina son faɗa maka cewa niba.....


Zain Abeed isn't free contact to subscribe 08119237616****57***Shiru Amma tayi ta kasa faɗin abinda tayi niyya, a hankali take shafa sumar kan Abeed,There is nothing she wants in her heart like Abeed, she doesn't have any desire that goes into his,She is hiding her love for him, for some reason, kamar yadda Abeed ya san ba lallai Amma ta ƙarasa faɗin abinda tayi niyya ba haka ne, domin a hankali ta kallesa tace "why don't you want to eat?" Ya motsa fuska yyi ba tare da yace komai ba, har lokacin kansa yana kan cinyarta ganin yanayinsa tace "Is there any worry in your mind?" Ƙuri yyi mata da idanu a hankali ya buɗe baki kamar zai Mgna sai kuma yayi shiru kawai yana kallonta, "say what's on your mind" ta faɗa a hankali idanunsa ya rufe kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "pray for me" zuciyar Amma ta karye sai kawai ta ɗauki idanunta can gefe, some minutes kuma tace "Meza kaci?" Ya girgiza kai ba tare da yace komai ba, kansa ta ɗauke daga cinyarta kafin ta miƙe tayi waje, a Parlo ta samu Ummi kallo ɗaya tayiwa Ummi ta ɗauke kai, kafin tace "Sannu da zuwa" Ummi tayi Murmushi tace "Ashe Abeed ya dawo, kwana nayi cikin farin ciki, Allah abin gdy na shiga wani hali" Murmushi kawai Amma tayi not looking at her tace "Wlh" Ummi tace "Fatan lafiya yake? Naji ance kamar baya da lafiya" Murmushi Amma ta sakeyi kafin tace "Anya? Ni naka ƙiba ya ƙara kamar dai yana cikin kwanciyar hankali" Ummi tayi dry tace "A to, haka akeso ai, bari naje anjima zan turo Riya ta kawo masa special food" Amma dai ba tace komai ba, Ummi ta tashi ta fita, kitchen Amma ta nufa ta shiga yiwa Abeed fate fate,wanda yasha rama da kifi da kayan lambu, ganin kamar his lost his appetite, not too long ta kama ta haɗa masa kunun gyaɗa mai garɗi bayan ta gama ta jera saman dinnig, a hankali ta nufi part ɗin da yake a tsaye ta samesa Ƙamshin Hugo boss ya cika ko'ina,a karo na farko ta sake ware manyan idanunta irin na Anuty Zulfa, binsa kawai take da kallon ganin yadda yyi mata mugun kyau,yana tsaye sanye da wani farin tattausan voyal ya ɗura milk ɗin Alkyabba mai golden, sai wata half hula ta sarauta daya ɗura, ƙafarsa cikin covet shoe mai gashi gashi, Amma a hankali tace "Ma sha Allah" ta faɗa cikin ranta a fili kuma tace "Abinci" shanyayyun idanunsa ya buɗe yana langwaɓe kai, ba tare da tace komai ba ta juya sai da taje bakin ƙofa tace "Follow me" tana faɗin hakan ta juya, bayanta yabi da kallo kafin a hankali cike da nutsuwa haɗi da kamewa da cikar haiba ya ɗauki Wayarsa yabi bayanta, a saman dinnig ya sameta ita da Zain, Zain yace "Da sauƙi, an sanya mata drip she'll be fine soon" Amma tace "Baka ganin dawowarta nan Zaifi" Zain yace "Hkne, ina jiran Abba ya dawo" Amma ta jinjina kai ba tare da tace komai ba, kujera Abeed yaja tare da zama a time ɗin sai ka rantse shine Abdul-Jabbar Abbas sbd wani irin kyau da kayan sarautar yyi masa, kansa a ƙasa yana danna Wayarsa Danish yake ƙoƙarin kira amma baya son dugun surutu, yana danna wayar yaji Amma tace "Haaa" ware idanu yyi ganin yadda ta ɗebo wani wanda bai ma san sunansa ba, kwaɓe fuska yyi yace "Mom plea..." Kafin ya Ƙarasa tayi saurin saka masa spoon a cikin bakinsa, hakan ya tilasta masa yin shiru a hankali yaja faten zuwa bakinsa ya fara taunawa a nutse, ɗan tsamin ramar yasa yaji bakinsa yyi ya daɗi, bai wani sha da yawa ba ya ɗauke bakinsa, kunun gyaɗar ta kafa masa abaki ya fara sha, tass ya shanye cup ɗin kunun yana yatsuna fuska, Zain yace "Ɗan gatan Amma, ni ko ayi min Bisimillah, gsky nima yau a baki za'a ban abinci" a kunya ce Amma ta ɗauke kanta tana sakin Murmushi kafin ta kalli Zain tace "Tare zaku fita ne?" Zain ya Girgiza kai yace "wani wajan zashi? Ni daga nan court zan shiga ina da meeting ne" Har lokacin dai Abeed bai ce komai ba, Zain yace "Ina zaka?" Abeed ya ware idanu kafin ya kalli Diamond Rolex ɗinsa hannunsa yace "By 2 jirgi na zai tashi" da mmki Zain yace "To where?" Ya ɗauke kai yana miƙewa tsaye yace "Canada" Zain yace "To babu inda zaka" Abeed nayin gaba Abinsa yace "To Abdul-Jabbar Abbas" Zain yyi Murmushi, Abeed na ƙoƙarin fita Riya na shigowa, Murmushi tayi tace "Wlcm back Sweetheart" ko inuwar ta bai kalla ba ya nufi part ɗin Naila hakan yasa gaba ɗaya fadawa suka rufa masa baya suna kirari, a lokacin na farko Abeed ya fara wata kalar tafiya ta ƙasaita cike da taƙama da izza...... Sarah na zaune fitowarsu kenan daga lecture, shiru tayi sam Zuciyarta babu daɗi akwai abinda take so amma ta rasa mene shi, Auta ta ƙarasu wajan ita da Nadiya, Nadiya tace "Are You Okay Mrs Yashim Al'khasim Abubakar Wahab?" Sarah ta haɗe fuska ba tare da tace komai ba, Auta tayi dry sosai tace "gamo dai a semester ta farko na level 2" tsaki Sarah tayi tare da miƙe ta ɗauki wayarta da hand bag ɗin na Gucci, A hankali take tafiya jikinta waist ɗinta daya ƙara buɗewa sosai yana juyawa cikin palazzo trousers, da Riga Gucci Brown sai Cardigan da ƙaramin scraf sbd sanyi, ƙafarta cikin Regal hill shoe, Duk littafan ta na wajan Auta, a hankali take tafiya tare da nufar wajan hutar Makarantar nasu, Tun daga nesa ya ƙafeta da fararen idanunsa yana gyara tsaiwar sa da zaman Alkyabba ɗinsa, tana zuwa dab dashi yace "Princess" da sauri Sarah ta juya ganinsa yasa taji damuwarta ya ƙaro, Murmushi Yarima Yashim yyi kafin yace "Are You Okay? U looks so learn" ba tare data amsa masa ba tace "Ina yini?" Binta yake da kallo yace "Mene yasa baki ɗaga wayata? Baki reply all message why Sarah?" Sarah ta ɗauke kai tace "Nayi busy karatu ne, bana using phone sosai".... "Karatu zai hanaki ɗaga waya? Anywhere kamar yanzu ne last semester na level 2 ɗin" ɗaga kai Sarah tayi taga wasu mutane na kallonta dake cikin mota a hankali ta murguɗa musu baki, ganin hakan yasa Yarima Yashim juyawa, kafin ya gansu sunyi saurin barin wajan da motar su.... Bayan motarsa ya buɗe mata yace "Enter" bata son damuwa kuma komai tayi a yanzu zata iya ɗaukan zunubi, hakan yasa dole ta shiga, shima baya ya shiga driver yaja su, shiru babu wanda yyi Mgn Ƙamshin Valentino na jikinta na ratsa zuciyar Yarima Yashim ga kuma gyaran da Anuty Zulfa ta fara yiwa Sarah hakan yasa jikinta ya murje da ƙara wata cika da ƙima, babu abinda Sarah take sai shan Madara da fruits, gently Yarima Yashim ya miƙa hannunsa ya kama na Sarah, abinda ya keji idan Abeed ya taɓa ta, sam bata jinsa a tare da Yarima Yashim, hannunsu ya harɗe waje guda kafin yace "Kina sani damuwa, bana son sabon yanayin nan naki" hannunta ta zare duk ta san ba Haram ya taɓa ba, amma Zuciyarta ta kasa yarda da hakan, a haka suka ƙarasa har gida suna zuwa kafin yace komai ta buɗe ƙofa ta fita Zuciyarta nayi mata zafi, har kukan rashin sanin mafita take game da rayuwarta...... Misalin 10 na safiya bayan jet ɗin Abeed ya sauka a Canada, kai tsaye wani haɗaɗɗan gida driver ya ɗauke sa, tunda suka nufi gidan zuciyar Abeed tayi sanyi nutsuwa ta fara saukar masa, yanayin sassaucin fuskarsa ya tabbatar da farin cikin da yake ciki, a babban entrance gidan driver yayi parking, da sauri wani guard ya buɗewa Abeed ƙofa, fitowa yyi yana sanye cikin Single Breasted Suit, dark blue sumar kansa da taji Ginger Geminal Oil-hair tai kwance sosai, sbd ko ribbon bai ɗaura ba, a hankali yake tafiya yana lumshe fararen idanunsa kamar mai jin bacci, yana zuwa bakin ƙofar akace “Wlcm back Yarima Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas" ƙofar tayi amfani da sahun ƙafar Abeed ta buɗe, shiga ciki yyi yana shiga idanunsa ya sauka akansa yana zaune sanye da farar jallabiya mai taushi da santsi, ajjiyar zuciya Abeed ya sauke sbd kwantaccen Murmushi daya sakar masa, da sassarfa ya nufi wajansa ganin hakan yasa gently Mai martaba ya miƙe tsaye yana ware hannayensa, Abeed na zuwa ya shigewa jikin Abba yana kwantar da kansa tare da sakin Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, Abba ya rungome Abeed yana bubbuga bayansa, cikin murya mai sanyi Abba yace "Ka tashi hankali na Magaji, ka sanya na haɗa tafiyar ƙarya Because of you" Abeed ya ƙanƙame Abba yace "Na gaji, I'm so tired Abbi, how long Wannan plan ɗin zai ƙare?" Mai martaba yyi Murmushi yana zame Abeed daga jikinsa a hankali ya sumbaci goshinsa yace "Soon Magaji" ya faɗi hakan yana zama shima Zama Abeed yyi yana kwantar da kansa jikin Abba ba tare da yace komai ba....... Sarah na kwance saman bed Anuty Zulfa ta shigo hannunta riƙe da waya, Sarah zatai Mgn Anuty Zulfa tace "Mijinki" dam! Sarah taji ƙirjinta ya buga bata ƙaunar ana haɗa sunanta da kalmar aure, amsa tayi tana amsa Anuty Zulfa ta fita, a hankali tace "Uhm" Yashim yace "Me kike?" Tai shiru ya kuma cewa "Kinyi shiru" ta haɗe rai

Please Login or Register in order to submit comment