Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

but haka ya fice amma ya ƙi zuwa ya bari sai zuwa dare zai je ya ɗauko ta.




✳️✳️✳️✳️

A fannin su Intisar kuwa; har su Sumayya suka dawo makaranta suka tarar da ita kuka take yi a cikin ɗaki

Sumayya da sauri ta isa wajenta tana tambayarta abun da ke faruwa duk ta rikice. But tayi banza da ita don ta kasa yin magana, abinda Shureim yayi mata ya matuƙar ƙona mata rai. Ganin tayi mata shiru ne sai ta wuce ta cire kayan makarantar; ta sauya wasu sannan ta fice ta samu Fauziyya a Parlour da har yanzu tana zaune itama. "Momy wai me aka yiwa Aunty Intisar ne? Me ya faru take kuka?"

Fauziyya kallonta tayi tace, "ɗan Iskan Mijin nan nata ne ya saka hannu ya mare ta."

"Mari?" Sumayya tafaɗa a cikin confused. "Mari Momy? To me tayi mishi?"

Numfashi Fauziyya take ja cike da takaici kafin ta kwashe komai ta sanar mata

"Tab ɗijam.. ashe be da mutunci shima? Duk ƙaunar da yake yi wa Aunty Intisar but yau har da saka hannu ya duke ta?"

"Dama wa yace miki Maza ƴan goyo ne? Ai duk abinda za ki yi musu wlh tallahi sai sun butulce miki, nan yarinyar nan saboda shi babu irin duka da wahalar da bata sha ba duk don saboda tana ƙaunar sa ta dage sai ta aure shi, ta bar karatun ta saboda shi amma kuma yanzu don ta ce tana son ci gaba ya ɗauki ganɗamemen hannun nan nasa ya garƙama mata a fuska, don shi ɗan iska ne mara mutunci wanda be gaji arziƙi ba, to ƴata ba Jaka bace baza ta taɓa komawa gidan sa ba sai ya gane be da wayau."

Shiru kawai Sumayya tayi tana zuba tagumi, gaskiya abun da Shureim yayi be kyauta ba bata taɓa tunanin koda wasa zai iya dukan Intisar ba, ta fi kowa sanin soyayyar su da yanda yake matuƙar ƙaunar ta tamkar ya haɗiye ta, ga shi nan a kan biye masa don ya ji daɗi ta soma fuskantar matsala; tunda har ga shi nan ya fara kiranta da ƴar iska bayan shi ya fara koya mata, tayi imani Intisar bata taɓa yin saurayi bayan Shureim ba; kuma bata taɓa bari wani saurayi ya taɓa mata koda hannu bane bayan shi ba, but yau shi yake kiranta da ƴar iska ko kunya ba ya ji. Shiyasa tsoro ya sake kama Sumayya domin abun ya dame ta, har tana jin a zuciyarta ita kuwa baza ta taɓa yin soyayya ba tunda Mazan duk haka suke basu da kirki, idan ka nuna musu soyayya ƙarshe kai zasu wulaƙanta, zasu yi maka abun da sai ka gummace ba'a haife ka a duniyar ba, to wane amana yayi saura a yanzu? Shureim.. Shureim da kansa shi ne yau da dukan Intisar? Numfashi kawai ta ja tana miƙewa ta wuce ta zuba abincin ta.

Sai dai kuma tunda Jamal ya shigo gidan Fauziyya ta tare shi da zancen; bai ce mata komai ba ya wuce ɗakin sa, sai ga shi ya fito da doguwar bulalar dorina wanda ya siye shi lokacin da ya zane Intisar kafin tayi aure, ai kuwa babu wanda ya kula da fitowar shi har ya shige ɗakin su, sai jin ihun Intisar ɗin suka yi tana ihu da kururuwa sabida dukan da yake mata

Da gudu Fauziyya da Sumayya suka nufi ɗakin har suna gwara kai. Inda shima Jibril ya take musu baya wanda daga ɗakin shi ya fito ya hange su sun yi ɗakin a guje, shima ihun nata ne ya firgita shi har ya fito a sukwane

Suna shiga sai suka ga Jamal ne a kanta yana ta zabgarta tamkar zai ɗaye mata jiki

Da gudu Fauziyya ta isa wurin tana son kare ta but gani take yi idan ta shiga tsakani itama haɗawa da ita zai yi tunda ko saurarawa ba ya yi, hakan yasa tayi wuf ta kama bulalar cikin tashin hankali take cewa, "wai me kake yi haka ne? Kashe min yarinyar zaka yi?"

Cike da ƙunan rai ya kalle ta yace, "wlh idan har ba ki sakar min bulalar nan ba sai na haɗa da ke, saka nace."

Tuni Intisar ɗin tayi Parlour aguje tana ta kuka kamar ana yanka ta. Inda su Sumayya suka bi bayanta su ma jikinsu sai rawa yake yi, a yanda suka ga Dadyn nasu sun tabbatar cikin tsananin ɓacin rai yake; ran ƴan Maza ya ɓaci

A cikin ɗakin kuwa nan faɗa ya kaure tsakanin sa da Fauziyya, ta ƙi sakin bulalar tace, "sai dai ya haɗa da ita tunda bai da tausayi bai da imani, kawai yana son ya kashe mata ɗiya ce, Mijinta ya buge ta sannan shima ya zo yana ƙara mata."

Yanda ransa yake a ɓace tabbas idan ya biye mata zai iya mata dukan tsiya itama, shiyasa ya saki bulalar ya fice yana huci. Da fitowar sa ya kalli inda Intisar take a durƙushe a ƙasa tana ta zabga kuka duk jikinta shatan bulala ne, tamkar wata wacce aka sakawa ƙaiƙayi a jikin sai sosawa take yi tana ƙara ɓare baki. "Wlh idan har ba ki tashi kin bar min gida kin koma gidan Mijin ki ba sai na kakkarya ki, ki bari in fito in ganki." Ya ƙare maganar yana nuna ta da yatsa kana ya wuce ɗakin sa da sauri

Cikin tsananin fushi Fauziyya tace, "wlh babu inda ƴata zata koma tunda baka da tausayi, da wanne zata ji ne? To zan gani idan wani ya haifa min ita baza ta koma ba."


Ita Intisar tuni ta tashi da taimakon Sumayya ganin da tayi zata faɗi ta tare ta. Ɗaki ta wuce da sauri ta ɗauki mayafin ta zata fice

Sai ga Fauziyya ta shigo tana kallonta tace, "ke kuma ina za ki je?"


Cikin kuka daƙyar take iya magana tace, "Momy zan koma gida na ne..." Ta ƙare maganar numfashin ta tamkar zai ɗauke tsaban shashsheƙan da take yi

"Babu inda za ki je dan uban ki, wuce dalla ki ajiye gyalen."

"Momy ki barta ta tafi, kin san halin Dady wlh sai ya ƙara mata dukan gwara ki barta ta tafin." Inji Sumayya cike da tausayin ƴar uwanta

"A kan me? Bazai yiwu ba?" Nan fa Fauziyya ta dinga surfa bala'i kuma ta hana Intisar tafiya sai kuka take yi


Ai kuwa sai ga Jamal ya fito ya sake shigowa ɗakin cikin tsananin fushi; don komai yana ji daga ɗakin sa da kuma fitinan da Fauziyyan take yi a kan, "baza ta koma ba." Zai koya mata hankali kuwa, shiyasa ya fito ya zo don ya ci uban su gaba ɗaya.
[10/10, 8:31 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 950
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days



9mobile
500mb. 500
1gb. 530
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days


Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days



Cheap in safety.👌🏼











*PAGE:14*

_____"wlh kin ji na rantse idan har ba ki bar yarinyar nan ta koma gidanta ba; wlh daga ita har ke sai dai ku bar gidan, muddin ba ki barta ta tafi ba auren mu ya ƙare dani da ke, sai ku tarkata ku bar min gida." Yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai yana juyawa ya fice

Sosai kuwa jikin Fauziyya yayi sanyi da jin zancen Jamal ɗin, ta tsorata ta san zai aikata tunda ya rantse, kuma bata shirya rabuwa da shi ba, bata shirya rasa igiyoyin aurenta ba, shiyasa cike da borin kunya take ta faɗa tace wa Intisar ɗin, "ta tafi, amma zata san yanda tayi ta ɗauki mataki a kan Shureim ɗin."

Haka Intisar tana kuka Sumayya na taya ta a yanzu ɗin ta bar gidan. Direba ya ɗauke ta suka wuce gidan nata.



Duk abinda ake yi Mama da Hafsah basu sani ba, suna can sashin su suna ta hira abun su.



Drever yana kai Intisar ya juyo ya dawo

Ita kuma ta shiga gidan cikin kuka

A lokacin Shureim na zaune a kan sofa yana kallo, dama yana bari ne ayi sallan isha'i sannan ya tafi ɗauko ta. But sai ga ta ta shigo tana mishi kuka, kallonta kawai yake yi kamar zai yi magana amma ya ƙi furta komai, har yanzu haushinta yake ji don yana son ya koya mata hankali ta dawo tunaninta, yana matuƙar sonta shiyasa yake matuƙar kishin ta, ya san shi kaɗai ya santa a ƴa mace domin da budurcinta ta zo mishi gida, amma kuma ai be da tabbacin shi kaɗai ya taɓa latsa ta, sannan kuma idan ya barta ta ci gaba da zuwa makaranta yana ga kamar zata iya samun waɗanda zasu hure mata kunne irin ƴan iskan Mazan nan har ta biye musu, shi kawai hankalin sa be kwanta ta ci gaba da karatu ba, idan har karatu ne a gidan sa ta gama shi har abada

Ita kanta baƙin ciki da haushin sa ne yake nuƙurƙusan ta shiyasa ta wuce ɗakin ta kanta tsaye bata ko kalli inda yake ba, yayinda take ƙara volume ɗin kukanta sosai sabida takaici ganin ko ta kanta be yi ba

Shi kuwa taɓe baki yayi ya ci gaba da kallon labaran shi cike da nishaɗi a ransa.



A haka suka kwana ranan babu me kula ɗan uwansa, ita ko fitowa bata yi ba yayinda shi kuma ya ƙi zuwa wajenta, duk da a ransa yana son zuwa ɗin domin yana buƙatar ta sosai, amma kuma ya ga idan ya nuna mata ya sauka nan da nan har ya lallaɓa ta shi ne zata ci gaba da yin masa iskancin da ta saba, gwara ya ɗan koya mata Hankali before su shirya, inyaso sai ya bata haƙurin maganganun da ya faɗa mata, amma kuma zai faɗa mata gaskiya baza tayi mishi karatu a gida ba.









✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


"Hello ranki ya daɗe! An gaishe ki ranki ya daɗe uwar Mata, kuma farin wata sha kallo me haske ko ina, kyakykyawa a birnin zuciyar kowanne ɗa namiji me ji da kansa! Ke ce kike zamanin ki ranki ya daɗe!" Cewar Sadis yana kashe murya kamar Mace

Daga can Zeena murmushi tayi cike da so da ƙauna tare da jin kanta a sama tace mishi, "wai ina kake ne tun ɗazu ina ta faman jiranka? Haba My love duk ka bi ka shanya Ni bayan nace maka yau muna tare."

Sake kashe murya yayi cike da salo irin nasa na yaudara har yana wani jan numfashi me tayar da hankali yace, "kiyi haƙuri ranki ya daɗe! kin san bazan iya ɓata miki lokaci ba, yanzun ma akasi aka samu shiyasa ban hallaro ba, amma da ace babu abinda ya tsayar dani ai bazan ƙi zuwa wajen masoyiyata kuma jin daɗin rayuwata ba, ke ce fa me saka min natsuwa a duk sanda nake kasancewa da ke, idan babu ke a rayuwata tamkar babu Sadis ne, Please ki bani cikakkun mintuna goma yanzu za ki ganni, don har na fito bakin titi abin hawa kawai zan tare."

Cike da yauƙi itama tace, "to My Love, but kar ka daɗe don Allah ka san ina tsananin buƙatar ka."

"Kar ki damu Gimbiyyata, Ni dai ki adana min kanki sosai don ke kaɗai nake buƙata a halin yanzu."

Murmushi tayi cikin farin ciki tace, "an gama love, kafin ka ƙariso bari in shirya, da zaran ka zo ka shigo kawai don na bar maka ƙofa a bude."

"Ok to." Ya faɗa yana sakar mata kiss daga cikin wayan

Ai kuwa sosai hakan yayi tasiri a wajen Zeena, tuni sha'awarta ta motsa nan da nan ta sake shagwaɓe murya kamar zata yi kuka tace, "Please kayi sauri don Allah."

"Gani nan Gimbiyya saura ƙiris." Yayi maganar yana sake narke murya kamar tsohon kwarto, dama kwarton ne 🙄

A haka suka yi sallama ta ajiye wayan tana tashi da sauri, daga ita sai dogon skirt da guntun under-wear da ya tsaya mata iya saman cibiya. Hijab ta saka ta fita Parlour da sauri. Yaranta ta gani suna wasa ta nufe su da sauri tana cewa, "kai Sadiq. Suhaima ku tashi ku wuce gidan Inna ku ce ina gaishe ta."

"Mamy yanzu fa muka dawo." Inji ƙaramar Suhaima tana shura ƙafafu kamar zata yi kuka

Daƙuwa tayi mata tare da cewa, "ubanki na ce ku tashi ko, yanzu ku ka dawo ɗin ƙaniya; ba nace ku zauna a can ba har sai na zo na ɗauke ku? Yanzu uban me ya dawo da ku?"

"To Mamy ba Innan bace ta kore mu, tace muna mata ɓanna baza ta zauna damu ba, sai zagin mu take yi." Cewar Sadiq kenan yana kallon Uwar

Tsawa ta daka musu tace, "ku tashi nace idan kun je ta kashe ku, ai jikokin ta ne ku idan kun je kar ta bar ku da rai babu ruwana, Dan ubanku ku tashi nace kuna kallo na."

Tashi suka yi tuni Suhaima ta soma kuka

"Kar ku soma ku dawo idan har ta kore ku, ku zauna har in zo, ko kuma ku wuce gidan su Aunty Nadeeya ku zauna. Ka riƙe mata hannu Malam."

Babu musu Sadiq ɗin ya riƙe mata hannu suka fice gaba ɗayan su suna kuka. Shi Sadiq share hawaye yake yi while Suhaima sai ɓarza kuka take yi, sun san suna zuwa gidan Innan nasu zata yi ta hantarar su tana zagin su tana cewa, "basu iya komin su ba sai ɓanna. Aliyu ya haifa mata masifa."

Ita kuwa Zeena ko a jikinta duk da ta san Inna Mahaifiyar Aliyu ba ta ƙaunar yaranta, hakan ya samo asali ne don ta tsani Zeena, kwata-kwata tarbiyyar Zeenan ne be mata ba kasancewar a inda aka auro ta kuma ta san halin ƴan gidan su duk ƴan iska ne. Amma shi Aliyu ya nace sai ita, ga shi kuwa be sani ba har bayan auren nasu tana biye-biyen Maza, shi kansa a wajen iskancin ya haɗu da ita, dalilin da ya aure ta kenan don yana matuƙar ƙaunar Zeena sakamakon irin Matan nan ne kyawawa na gaban kwatance, tamkar irin Matan hurul iin tsaban kyau, ga ta fara sol-sol ba ko ɗigon baƙi a tare da ita, tana da mugun ɗaukar kwalliya don idan tayi sai kace wata zinariya ce aka dasa a wurin tsaban kyanta, da haka take ruɗan Maza suke kawo mata farmaki har silan hakan ya ja ta soma amincewa da su suna bata kuɗi sosai, kyawunta ya ja mata biye-biyen Maza don kowanne namiji ya kalle ta dole ne ta ba shi sha'awa. Haka ƴan gidansu suke gaba ɗaya, kuma su ma duk ba sa ji suna jin su kamar karuwa-karuwai ne, kowa haka yake musu kallo sabida tsaban yangan su da yanda suke juya Maza yau kaga wannan a ƙofar gidan su gobe wancan, sanadin haka itama Zeena ta faɗa tarkon su ta kasa riƙe kanta a yanda suke kawo mata farmaki, inda shi Aliyu shi ne yayi nasaran auren ta saboda yanda yake mugun ƙaunarta bayan sun gama sheƙe ayar su, sai dai kuma tunda ya aure ta ya hana ta mu'amala da kowanne namiji, hatta makaranta ba ya barin ta zuwa duk wani abu da zai jawo hankalin ta waje ya hana ta, a haka har suka yi tsawon shekaru ga su har da Yara biyu, sai dai shi be sani ba Zeena ta saba da Maza baza ta iya bari ba, ba tare da sanin sa ba take bibiyan Mazan, har gida take kawo su suyi sharholiyan su tunda shi matafiyi ne, ya kan yi tafiya na kwana biyu ko zuwa ɗaya, a haka take samun damar kawo Maza har gidan tunda ta ƙi haƙura ta zauna da Mijin ta wanda ya rufa mata Asiri duk da ya san halin ta, ko kaɗan Aliyu be taɓa mata gori don wai ga yanda ya aure ta ba saboda mugun ƙaunar da yake mata, ya yarda da ita ɗari bisa ɗari be taɓa damuwa da rayuwarta na baya ba, a ganinsa yanzu ta shiryu ta riƙe sa shi kaɗai ne, be san cewa tana cin amanar sa ba


A yanzu Sadis shi ne wanda take matuƙar ji dashi saboda ya iya soyayya sosai. Ita take sakar mishi kuɗi don dai kawai ya riƙa zuwa yana biya mata buƙatar ta, kusan koyaushe suna tare idan har Aliyu ba ya nan, sosai ta sake tsulmiya a harkan nan ko kaɗan ba ta tsoron Allah, ko don auren da yake kanta ta ƙi shiryuwa


Yanzu haka tana ganin su Sadiq sun fice sai ta ruga a guje ta shige toilet don yin wanka

A haka Sadis ya zo gidan ya shigo kamar yanda tace mishi. Har ɗakin nata ya shige yana kiran sunan ta

Ita kuwa tana tsaka da wankan ta ne, shiyasa tana jin muryan sa sai ta amsa daga toilet ɗin tana cewa, "my love ka shigo toilet gani nan ina wanka."

Ai tuni ya tanɗe baki yana shafa kai kamar tsohon maye ya nufi toilet ɗin kamar ana ingiza shi

Wa'iyazu billah..! Tun daga cikin toilet ɗin suka soma tanbaɗewa suna aikata masha'an su, babu me tsoron Allah a cikin su, babu me tunanin akwai ranan da Allah zai kama su, duk kansu suna da auren su but suke aikata wannan baɗalar, wa'iyazu billah. Daga ƙarshe sun fito sun yiwa kansu masauki a kan gadonta inda suka ci gaba da tanbaɗewar su na tsawon lokaci


A wannan lokacin duniyar tayi musu daɗi, inda a dai-dai time ɗin ne Aliyu ya dawo gidan, dama yayi tafiya kwana biyu zai yi but sai ga shi a yau ya dira, sakamakon ya kammala aikin da yake tunanin zai ɗauke shi two days, kasancewar idan zai yi tafiyar ba a Machine ɗinsa yake zuwa ba sai dai ya je a motan haya tunda be da mota sai Machine, to hakan yasa ya shigo na haya aka dawo dashi ya sauka a ƙofar gida, ya biya me keke napep ɗin kuɗin sa ya nufi gidan, yana buɗe ƙofan ta buɗe tunda a buɗe suka bar shi, yau yana son ya yiwa kyakykyawar Matar tasa surprise ne shiyasa yake ta Allah-Allah ya wuce ciki, hakan yasa be kira ta ya sanar mata da dawowar nasa ba, yayinda fuskarsa sai annuri take yi cike da mararin ganin fuskar nata tamkar ya shekara goma be ganta ba, Allah ya ɗaura masa ƙaunarta fiye da tunanin Mutum, duk da tsawon shekarun nan da suka yi da ita tamkar a yau ya santa, kullum sake jin sonta yake yi a zuciya kamar koyaushe idan ya ganta to a lokacin ne ya taɓa ganin ta, sabuwa fill take zama mishi. Ya shiga falon cikin farin ciki tare da yin sallama, inda bai tsaya ba ya kutsa kansa tsaye ɗakin nata ganin babu ita a falo.
[14/10, 9:53 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 950
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days



9mobile
500mb. 500
1gb. 530
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days


Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days



Cheap in safety.👌🏼










*PAGE:15*

_____Har ya kama ƙofan ya murɗa zai shiga sai wayan shi tayi ƙara, dakata wa yayi yana ciro wayan tare da dubawa, ganin sunan Babban Abokin sa tuni ya saki ƙofan yana amsa call ɗin cikin fara'an sa tare da sallama

Maganar nasa ne ya ratsa kunnen Zeena da ke jikin Sadis suna.... Bata san sanda ta fincike bakin ta ba tana mayar da hankalin ta a kan ƙofan, ƙiris ya rage zuciyarta ta fashe saboda arba da tayi da jikin Mijin nata daga bakin ƙofa, yayinda muryan nasa ta ci gaba da ratsa ta a cikin kunnuwan ta, tsaban yanda ta shiga shock bata iya ma motsi ba domin ɗif na'urorin jikinta suka dena aiki na ɗan wasu daƙiƙu sabida tsaban rikicewa

Yayinda Sadis shima tuni ya ankare da Aliyun domin shima muryan nasa har ta ratsa mishi kunne, hakan yasa yayi shiru ya fasa maganar da ya buɗe baki zai yi, nan da nan jikin sa ya soma rawa lokaci ɗaya ya zaro idanu cike da tashin hankali, hankaɗa Zeena yayi yana shirin sauka daga kan gadon jikin sa na wani irin mazari cike da zallan tsoro, kankace me ya soma neman kayan sa sai dai kasancewar yana a cikin ruɗu ne ya rasa inda suke sai wuri-wuri yake yi

Itama Zeena saukowa tayi daga kan gadon da sauri, sai dai sun kasa magana sabida yanda suke hango Aliyu daga bakin ƙofan, yana ƙara buɗe ƙofan kaɗan zai iya hango su a tsakar ɗakin. Da sauri Zeena ta nufi Sadis cikin tsananin ruɗewa inda jikinta ke faman rawa ta riƙo sa, sai dai ta kasa magana sai waige-waige take yi tana fitar da numfashin tsoro, nan da nan sai hawaye suka cika mata idanu zuciyarta na ambaliyan bugawa, tabbas idan Aliyu ya ganta kashin ta ya bushe shikenan auren ta ya ƙare, ta rasa shi. Daƙyar ta samu damar yin magana cikin ruɗu a hankali tace, "wayyo Allah mun shiga uku... Miji na, ya zamu yi?"

Sai a lokacin shima Sadis ya gama dawowa hayyacin sa har ya iya ƙilla idanuwan sa a kan kayan sa, da sauri ya wawura kayan yana shirin ɓoyewa, be san sanda

Please Login or Register in order to submit comment