Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take ciki, duk abun da yayi miki Hauwa hakuri za ki yi, can ma a baya kin yi haƙuri bare yanzu? Ban san ki da zafin zuciya ba kinji ko?"
Yayansu ya furta hakan cikin lallami yana kallonta

Ita kuma sai faman hawaye take yi tana furta, "don Allah Hajiya ku bari kar ku kira shi, yanzu Anwar ba ya sona ba ya ƙaunata, tsawon sati biyu ina zaune a gidan sa ina ƙunsan baƙin ciki ba ya kula Ni, me nayi masa da zafi haka da zai ɗauki gaba dani? Ya soma gajiya dani ne tunda har ya iya manta wa dani, don Allah ku ƙyale shi kar ku soma ku kira sa in har ba shi ya neme Ni ba, wlh bazan koma ba na gaji."
Ta ƙare maganar tana fashe wa da wani irin kuka mai cin rai, da alamu abun ya daɗe yana cinta a rai

Dukkan su jikinsu yayi sanyi matuƙa, kuma sun kasa musa mata tunda sun san ba halin ta bane, tunda har Hauwa ta furta hakan; ta fi kowa sanin halin da take ciki, don haka suka taru suka ci gaba da tausan ta

Har Yayan nasu yana cewa, "ta kwantar da hankalinta baza su kira sa ba, Allah ya bata lafiya, idan ma tana so sai ta bi sa Zaria ta zauna wurin sa ko zuciyarta zata samu sukuni."

Duk da Hajiya tayi masa faɗan maganar da yayi

Amma sai ya nuna mata, "bada wata manufa bane, gwara ta koma can ta ɗan samu sukuni sai ta dawo daga baya."

Itama Hauwa ta nuna zata bi shi

Amma Hajiya ta ƙi yarda, tace, "haukan banza kenan, ya za a yi su ba rabuwa suka yi da Mijin ba zata tafi wani wuri da auren ta? Bayan ma ita ta fita gidan tayi yaji ba shi ya kore ta ba? To baza ta amince ba tayi zamanta a gidan tunda bazai yiwu su biye mata ba, ta yarda dai ta zauna tunda hankalin ta a tashe yake yanzu, in ta samu sukuni da sanyin zuciya sai ta koma ɗakin ta, idan ma sun ji shiru wurin Anwar ɗin dole zasu neme sa su ji inda aka kwana."

Dalilin da yasa Hauwa bata bi Yayansu ba kenan, kuma tayi jinya wajen kwanaki tana kwance, duk da a washe gari aka sallame ta amma ta koma gida jikin babu dad'i, sai dai magani take sha

Ƴan uwanta sun tausaya mata sai zuwa duba ta suke yi

Sati ɗaya da tafiyarta Anwar ya kasa haƙura sai ga shi ya zo gidan da kansa,
Hankalinsa ya tashi domin shi kansa bai san Hauwa tana da matukar muhimmanci a rayuwarsa ba sai yanzu da ta guje sa, ya san cewa dole fushi tayi, fushi kuwa ba kaɗan ba tunda har ta iya yaji a gidansa, abun da bata taɓa aikata wa ba, sai yanzu ya gane girman laifinsa da ya rasa ta, sai yanzu yake tuna wace ce Hauwa a gare sa, yayi kuskure tabbas da ya bar shaiɗan yake son tarwatsa musu rayuwarsu; yake son tarwatsa musu farin cikin su, yake son raba tsakanin su,
Hauwa ta wuce wulaƙanci a wurin sa, ita ce duniyarsa, haƙiƙa yayi dana-sani har cikin zuciyarsa,
Kuma koda ya zo ya nuna rashin kyautawar sa wajen su Hajiya, sosai ya basu haƙuri kuma yace, "yana son mayar da ita su tafi tare."

Tunda ya zo Hauwa bata ce masa komai ba, ta ƙi ma kallonsa bare ta saurare sa, sai kuka ta dinga yi suka rasa gane kanta, kuka sosai take yi kamar zata mutu, hankalin su ya tashi sosai; sun rasa yanda zasu yi da ita

Hajiya tace, "tayi haƙuri ta bi Mijinta shi ne rufin asirinta, kuka ba nata bane a yanzu tunda Allah ya kawo sauƙin abun."

Cikin kuka Hauwa tace, "Hajiya ku har Ni in yi kuka na domin shi ne kaɗai abun da ke kawo min sauƙi a zuciyata, Hajiya ba na son bin sa bazan iya komawa gidan sa ba, ya rabu dani kawai, idan da hali ma ya bani takardan saki na sabida...."

Saurin katse ta Hajiya tayi ranta a ɓace tace, "subhanallah.. kina da hankali kuwa Hauwa? Ke ce kike neman saki a wurin Mijinki? Kin san kuwa girman laifin abun da kike son aikata wa kuwa?"

Kuka ta sake fashe wa dashi, sai ta miƙe da gudun ta tana shige wa ɗaki

Idan hankalin Anwar yayi dubu to ya tashi, idanunsa sun kaɗa sun yi jazur, ya kasa kataɓus sabida tsananin tashin hankali, gani yake yi kamar ya rigada ya rasa Hauwa tunda har ta buɗe baki tayi wannan furucin,
Kallon Hajiya yayi kamar zai yi kuka tsaban tsananin tashin hankalin da yake ciki, yace, "don Allah Hajiya ki taimaka min ki bata haƙuri, wlh ina sonta ina matuƙar buƙatarta a cikin rayuwata, duk abun bai kai haka ba bazan iya rabuwa da ita ba, ita ce Ni; Ni ce ita. Na san nayi laifi amma zan sauya kuskurena tayi haƙuri ta bi Ni, duk abun da take so zan yi mata."

Ita kanta Hajiya ta kasa cewa komai, sabida bata san me zata ce ba, ga kuma tausayi da Anwar ɗin ya bata, amma tunda ta ga Hauwa ta shiga wannan yanayin to zai yi wuya ta saurare su, an kaita maƙura, yana ɗaya daga cikin halayyarta idan har tayi fushi da abu, ana wuyan tanƙwara ta,
Shiyasa ta ba shi haƙuri tace mishi, "ya je zata shawo kanta, amma ya bi komai a sannu komai zai wuce, dama zaman aure haka ya gada."

Anwar bai so ya tafi ya bar gidan ba, amma ba shi da yanda zai yi tunda Hajiya ta ba shi haƙuri, sauƙin sa ma yanda su basu yi fushi dashi ba, sai yanzu yake ganin bai kyauta wa Hauwa ba, haƙiƙa ya cutar da ita, ya ƙuntata mata a kan abun da ba ita take bama kanta ba, tayi rayuwa dashi da daɗi babu daɗi bata taɓa sauya mishi ba, ya kawo mata maganar aure haka ta amshi zancen hannu bibbiyu bata taɓa nuna masa wani sauyi a fuska ba, koda bak'ar magana ce, sannan ya zo ya soma bambanta su sabida kawai ya samu abun da yake so, yana shirin samun ɗa abun da ya daɗe yana buri, maimakon a lokacin ne ya kamata ya bata kulawa da tarairaya sabida tausayin ta kasancewar ita bata samu haihuwa ba, ya san dole zata shiga damuwa, amma duk bai yi ba, idanunsa sun rufe, haka ya ci gaba da nuna bambanci a tsakanin su har kawo lokacin da Afnan ta haihu, duk abubuwan da Afnan take mishi bai taɓa ganin laifin ta ba sabida ita ce Uwar ƴarsa, sai dai ya ga laifin Hauwa daga kuskure kaɗan, ya manta irin halarcin da tayi mishi, ya muzguna mata tabbas, haƙiƙa ya muzguna mata, bata cancanci haka a gare sa ba, ita ce Macen da ya fara so a rayuwarsa, da ita ya soma sanin daɗin rayuwa,
Ba ya fatan a ce Hauwa ta guje sa a wannan gaɓan, domin bazai taɓa iya rayuwa babu ita ba, ya shirya tsab domin bata farin ciki fiye dana baya, bazai ƙara bambanta su ba ko kusa, bazai ƙara wulaƙanta ta ba insha Allahu

Daga ƙarshe gidan su ya wuce ya sanar da Ummansa halin da ake ciki, har da hawayen sa

Ran Umma ya ɓaci matuƙa, ta dinga surfa mishi bala'i da masifa, kuma tace, "muddin yayi gangancin da ya rabu da Hauwa, wlh zai ga ɓacin ran da bai taɓa ganin ta dashi ba, sai ruwan sha ya gagare shi tunda ya wulakanta ta."

Sai ga Anwar yana kuka kashirɓan sabida jin furucin mahaifiyarsa

Tace, "baka ga komai ba Anwar, wlh ka ji na rantse maka idan har baka yi gaggawan da ka bata haƙuri ta koma dakin ka ba; babu Ni babu kai Anwar, tunda baka san mutunci ba baka san inda ke maka ciwo ba, sai da ka kaita bango kasa tabar gidan wato?"
Sai ta kaɗa kanta ranta a tsananin ɓace, tace masa, "ya tashi ya bar mata gida."

Yana kuka yake bata haƙuri a kan, "bazai sake ba, tayi haƙuri ta je ta bata haƙuri ta koma, bai san ya zai yi ba ta ƙi sauraron sa."

Koron sa tayi a gidan tace mishi, "baza ta je ba, idan shi bazai je ya shawo kanta ba sai da alfarmarta ne; to baza ta taɓa zuwa ba."

Abubuwa fa sun damalmale wa Anwar, yana ganin kamar abun da sauƙi ne but abu yana son fin ƙarfin sa, domin kuwa kowa ya kasa shawo kan Hauwa ta koma ɗakin ta, Iyayenta da ƴan uwanta duk hakurin da suke bata amma ta tubure, sai ma idan sun matsa mata ta dinga kuka kenan ta rufe kanta a daki ta ƙi fitowa,
Ga shi lokaci guda jikinta ya rikice ciwo ta dinga yi har aka wuce da ita asibiti

Umman Anwar ma kanta ta zo har gida domin ta bata haƙuri, saboda yanda Anwar ya sako ta a gaba yana magiya da kukan sa, dole ta canza maganar ta sabida tausayinsa ta tako da kafanta ta bama Hauwa haƙuri

Amma bata ce mata komai ba sai kuka da ta dinga yi, har ta tafi bata amsa mata a kan zata koma dakin ta ba, duk kuwa da rarrashinta da ta dinga yi

Ita kanta bata ji haushin Hauwa ba, domin a ganinta ita ta san me yayi mata ta dauki wannan fushin,
Ga shi abun har ya taɓa lafiyarta yana neman ya kwantar da ita duk ta zabge,
A washe garin ranan da ta zo, aka aiko mata an kwantar da Hauwa a asibiti

Tana cikin wani hali gaskiya, tunda ciwon da take yi ba kaɗan bane, bata san inda kanta yake ba sabida rama da damuwan da ta sanya wa ranta,
Likitocin har sun yi mata gwaje-gwaje har da na ciki don a hasashen su akwai ciki a tare da ita, ilai kuwa ana gwada ta suka tabbatar da tana da shigan ciki har na tsawon watanni ukku da satikai, baya ga haka babu abun da ke damun ta sai damuwar da ta saka wa ranta; wanda yake son taɓa mata zuciyarta.







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


               Tun a washe garin ranan da aka kawo Hafsah; Jamal ya kwashi su Sumayya ya kaisu wurin Mama, domin a ganinsa zasu hana sa jin daɗin rayuwarsa shi da ƴar Hafsansa, sabida kula wa yake son bata babu shamaki bare a samu masu sanya musu ido, zai fi sakin jiki in su kaɗai ne

Ai kuwa tun a ranan ya fara gwangwaje wa ya soma cin Angoncin shi, a haƙiƙa ya so ya bari su yi kwanaki ta yanda zata saba dashi ta fi sakin jikinta sosai, but ya gaza haƙura, haka yayi bidirin sa ya amshi hakkin sa cikin lallami da lallaɓa wa, ai kuwa ya ga taɓara da koke-koke, sai da yayi zaman jinya na tsawon kwanaki, in fact ma ba ya zuwa ko'ina ya ɗauki Hutu na one month sabida more rayuwa,
Haka ya dinga ɓarza gumin sa yana cin duniyarsa da tsinke, sai dai ya koma jinyarta daga baya kuma ya sake sabon aiki

Tun Hafsah tana jin jiki tana noƙewa da kukan taɓara, har ta soma saba wa da sabuwar rayuwarta, tsab ta ɗauke Dadyn ta tayi juriya ba kaɗan ba,
Daga ƙarshe rayuwa ta soma sauya musu

Wani irin kulawa yake bata tamkar ya mayar da ita cikin sa, babu irin soyayyar da ba ya nuna mata komai shi yake mata sabida gatanci da yake nuna mata, tamkar ƙwai a cikin ƙaya ya mayar da ita, kai tamkar tsoka ɗaya cikin miya haka Hafsah ta koma wurin Jamal, ita kanta ta san cewa tayi dacen Miji, sabida ba kowa bane zai kasance kamar Dadyn ta ba, a yanzu tana farin ciki da samun sa matsayin Abokin rayuwa, idanunta sun soma buɗe wa ta soma saba wa dashi da kuma soyayyarsa,
Tun tana jin kunyarsa har itama ta soma sakin jiki tana basa kula wa yanda ya kamata; tare da nuna juriyan ta babu raki a zaman su, komai tana iya bakin ƙoƙarin ta

Shi yasa nan da nan Jamal ya soma sauya wa, sai ya ɗan yi ƙiba har da ajiye tumbi, abun da tun soma samun kudin sa bai taɓa yi ba, amma yanzu sauyin rayuwa da samun ƴar shila ya soma manta kansa 😜😂

Sumayya kuwa sai gani sai hange, Hafsah tayi mata rata, babu yanda za a yi ma ta ɗauki mataki a kanta, ƙiri-ƙiri Jamal ya ƙi dawowa dasu gidan, yace, "su yi zaman su a wurin Mama."
Sai dai ya ɗauko Hafsah su zo su gaishe su amma ya hana su zuwa gidan

Itama Hafsan kamar jira take yi nan da nan ta kile a ɗan ƙanƙanin lokaci, sai ga shi ta soma cike ɗan ƙasusuwan wuyanta; tare da dirke wa tana zama Mace, ɗan ƙaramin jikin nan ya soma buɗe wa yana zama jikin manya, abu kamar wasa Hafsah ta soma canza wa. Ko kusa bata taɓa biye wa Sumayya ba bare ta san Allah ya kwaɓa ta, bata da lokacin ta ma bare ta san me take yi, iyakan in ta ganta tace mata sannu, idan ma akwai Jamal dole Sumayyar ita take gaishe ta, Hafsah kuwa ta fuske ta amsa tana ɗauke kanta

Mama sai murna da jin dad'i, farin ciki da godiya ga Allah kawai take yi, yanda ta ga rayuwar ɗanta ya sauya, har yanzu kuma bata fasa musu addu'o'i ba a rayuwarsu, Allah yasa su ɗaure a haka

Yau da gobe kuma komai ya soma tafiya rayuwa ta miƙa, basu ƙara jin labarin Fauziyya ba ko a bakin ƴaƴanta, tunda su kansu ba sa zuwa, Sumayya ce kawai wata rana take sulale wa ta je idan zata je Islamiyya

Ana haka Jamal ya je ƙauye ya taho da intisar. Intisar ta ga rayuwa, domin ta sauya ba kaɗan ba, ta zama tamkar ƴar ƙauye tsaban sauyawan da tayi, shekara daya da kusan rabi kenan da kaita can ƙauye, ta sauya tabbas, sai kuka take yi da ta ga ƴan uwanta, haka su ma. Sun sha kuka ba kaɗan ba domin sun yi kewar juna

Sai da Jamal ya ja mata kunne sosai, ya kuma gargaɗe ta a kan, "muddin bata natsu ta fuskanci rayuwa ba, nan gaba abun da zai yi mata sai ya fi haka, amma yanzu zai bata dama ta biyu ta sauya rayuwarta, zai mayar da ita makaranta har ta samu wani Mijin tayi aure."

Ta ji dad'i matuƙa domin bata taɓa tunanin haka daga gare sa ba, ta natsu sosai kuma ta saka a ranta yanzu karatu zata yi baza ta taɓa kula kowanne namiji ba, in har Dadynta zai biya mata karatu har illa Masha Allah, to babu ita babu aure a nan kusa,
Duk da bata sakar wa Hafsah fuska ba tunda babu shaƙuwa a tare dasu, amma babu ruwan ta da ita, ko ta zo gidan tana gaishe ta baza ta sake ce mata komai ba, babu kallon banza bare harara, halin da take ciki ma ya ishe ta, burin ta kawai ta soma zuwa makaranta

Ana haka Dady ya mayar da ita school, tunda dama daga S.S 2 ta fita, sai aka yi mata jumping zuwa S.S 3 zata zana jarabawar fita, ita kuma Sumayya ya sama mata gurbin karatu zata ci gaba, tunda har yanzu babu mashinshini; ba ta kula kowa sabida babu soyayya a ranta, abun da ya faru da Intisar ya zame mata izna kwata-kwata soyayya ba ta burge ta, itama ta fi son karatu, wala'Allah a nan gaba tayi sha'awar abun a ranta, tunda baza ta dauwama haka nan babu aure ba

Abun mamakin har da Hafsah ya nema musu gurbin karatun, ai kuwa ba ƙaramin farin ciki tayi ba, har da kukan ta tunda bata taɓa tunanin nan kusa zata ci gaba da karatu ba, sai ga shi ya basu mamaki

Ita kanta Mama tayi murna tunda ta cire ran Jamal zai bar Hafsah ta ci gaba da karatu; since yanzu rayuwa ta sauya tayi Aure, dama a baya ne ta ci mata burin yin karatun, amma ko yanzu da ya saka ta tayi murna tana ta sanya mishi albarka

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci suka soma karatun su hankali a kwance. Rayuwa Kenan.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


           Anwar yayi murna da kasancewar samun cikin Hauwa, kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, sai rawan jiki yake yi kamar ba a taɓa haihuwar masa ba

Sai Afnan ta raina kanta sabida yanda Anwar kwata-kwata ya sauya mata a wannan lokacin, abun ya ɗaure mata kai matuƙa, tun tana mishi fitina da irin sauyin da yake mata, har dai ta gaji ta ƙyale sa don ba shi da lokacin da zai zauna yana biye mata ma

Kullum yana kan hanyar zuwa asibiti duba Hauwa ko baza ta je ba, idan yace, "ta zo su je."
In ta nuna baza ta je ba sai dai ya tafi shi kaɗai, da kansa zai shiga kichen ya haɗa abinci ya zuba a kwando ya tafi musu dashi asibiti,
Barin ma yanzu da ya samu Hauwa tana kula sa, don yanzu ta sauko ba kamar baya ba, amma bata cika yin masa magana ba sai idan ya dame ta, shi ko a hakan ma farin ciki ne a tare dashi, gani yake yi don cikin nan ne ya sauya Hauwa, amma zata sauko da zaran ta haihu komai zai daidaita, babu irin kulawar da ba ya bata har aka sallame su ta koma gidan su, domin ta ƙi yarda ta bi shi har yanzu, shima ɗin gudun ɓacin ranta yace, "ta zauna a nan babu damuwa zata fi samun kula wa ai, in har hakan zai fi mata."

Afnan dai sai haƙuri don hankalin Mijinta ya karkace sai du'a'i, bata da yanda zata yi tunda tare tazo ta tarar da su, bata isa ma ta nuna wani ɓacin rai ba since ba ya kula ta, sai dai ya barta tayi tayi ita kaɗai tana haushin kare.
***

            Bayan wasu watanni sannan Hauwa ta koma gidan Mijinta, lokacin cikinta ya girma, komai ya zama normal ta haƙura ta yafe masa sun koma kamar baya,
Shima ya sauya ba ya bambanta su a haƙiƙanin gaskiya, yana kamanta adalci tunda dukka matansa ne kuma kowacce soyayya yasa ya auro ta, farin cikin sa ma yanda suka haɗa kansu don har yanzu babu wata matsala a tsakaninsu,
Dama matsalar Afnan ce, yanzu kuwa sai borin kunya tunda itama Hauwan ga ta nan ta samu nata cikin zata haife nan da lokaci kaɗan, a baya an yi mata gori amma yanzu komai ya wuce, kuma Hauwa bata taɓa tayar da zancen ba bare ta nuna mata abun da ya faru a baya ta ji zafin ta

Anwar da kansa ya ɗauki Hauwa ya kaita har gidan Sauda tayi mata wuni a can, duk da Saudan tayi fushi sosai amma ta sauko ganin Hauwan a gidan ta. Sun yi hira kamar baza su rabu ba har dare sannan Anwar ya je ya ɗauke ta,
Har gaisawa suka yi da Sauda kamar babu abun da ya taɓa haɗa su,
Amma Sauda tunda bata barin kashi a ciki sai da tayi masa tsiya da wayon ta gaggaya masa magana

Shi dama yayi don Hauwa ne; don haka bai wani damu da ita ba bare ya kula ta, sai dai ya saki fuska sun yi magana faram-faram, har suka ɗan jima da Bilal a ƙofar gida suna ta labaran duniya,
Daga nan ya ɗauke ta suka koma gida

Sati biyu tsakani Hauwa ta haihu lafiya a gida, ta haifi ɗa namiji kyakkyawa mai kama da ita sak, Allah kenan! Ga shi yanzu komai ya wuce, dama ba a taɓa ganin mai haƙuri ya gaza ba wata rana dole zai dafa dutse har ya sha roman sa, yau ga shi komai ya wuce tamkar ba Hauwa bace tayi rayuwar ƙunci sabida rashin haihuwa, ga shi itama ta zama ɗaya da waɗanda suka taɓa haihuwar, Allah ya bata nata rabon ta samu ɗanta na cikin ta, dama komai lokaci ne kuma da sannu komai yake zama labari

Ranan suna aka sanya sunan Muhseen; kamar yanda Anwar yayi alƙawari, kuma bai fasa ba haka Yaro ya ci sunan, suna kiran sa da Barraq *(shining. Haske)*

Itama Munira ta samu Miji zata yi aure, sai dai mai Mata ne wanda zata aura a cikin dangin su

Yanzu haka A'isha ta haihu ɗiya Mace; sunan ta Alia,
Itama Amina wannan banan aka saka mata rana, bai wuce few months ba

Side ɗin su Hafsah; su ma komai alhamdulillah. Sai da tayi two years before ta haihu ɗa namiji ya zo babu rai, ta ɗan yi jinya sannan ta samu lafiya suka fauwala wa Allah ta ci gaba da zuwa makarantar ta,
Allah da ikonsa har ta gama school bata ƙara samun wani ciki ba,
Kasancewar tana son karatun shiyasa Jamal ya barta ta ɗaura degree ɗin ta, shekara na huɗu da auren su Allah ya ƙara bata wani cikin, ta sake haihuwar namiji. Yaro ya ci sunan Mahaifinsa Jamaluddin, suka sanya mishi Aahil *(Prince).*




_Alhamdulillah...! Komai yayi farko zai yi ƙarshe, ba don na gaji ba zan dakatar da rubutu na a nan; face saƙon da nake son bayyanawa na rigada na isar dashi. Allah yasa ya amfana al'umma kamar yanda nayi labarin domin gyara, kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min ba don hali na ba, ina ma Masoyana fatan alkhairi a duk inda suke, Allah ya bar mu tare. Amin ya Allah._

*Ku nemi new book ɗina, SHAREEF, yanzu haka ina rubuta shi. Labarin soyayya ce mai cike da ban tausayi gami da taɓa zuciya, son maso wani ne wanda yake faruwa a cikin rayuwar wata yarinya, soyayya jarabta ce; wanda ya zama cuta gare ta. Ku nemi naku kawai ku sha labari. Love you FAN'S.😊💕😘.*
07065334256.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment