Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*P.W.A✍️*











*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*PAGE: 2*

_____"Aslm lailum".

"Wa'alaikumus Salam, sannu da zuwa Mijina".

"Yauwa Matata sannu da gida". Yayi maganar bayan ya shigo yana tsaye riƙe da hulan sa

Hauwa amsar hulan tayi ta ajiye a kan gadon su kana tace, "bari in kawo maka ruwa".

"A'a bar ruwan nan bari in je in Yi sallan isha'i in dawo".

A dawo lafiya tayi masa sannan ya fice, ita kuma ta shimfiɗa tabarma a tsakar ɗakin kana ta ɗauko mishi coolarn tuwon shi, ta ajiye tare da ruwa da Plate, sai ta fice don yin kaye-kayen kayan ta sai tayi alwalan itama.

Sauda na zaune bakin ƙofar ta a saman tabarma ita da yaran ta, sun tasa tuwon da Hauwa ta basu suna ta ci. Ganin fitowar Hauwan sai tace, "don Allah Hauwa ki bani aron Naira ashirin Sulaiman ya siyo min maganin sauro, kafin Baban su ya shigo sai in ba ki ko zuwa gobe".

"To". Kawai tace da ita ta koma ta ɗauko mata, bayan ta kai mata ta wuce ta yi abinda ya kawo ta sannan ta koma ɗakin ta

Tana tayar da Sallah Anwar ya shigo da sallama a bakin sa, ganin tana sallah sai be ce komai ba ya samu wuri ya zauna yana tanƙwashe ƙafafuwan sa, tuwon ya buɗe ya zuba ya soma ci

Tana idar da sallan ta juyo tana kallon shi tana murmushi tace, 'meyasa baka bari na zuba maka ba zaka kwashe min lada na?"

Dariya yayi bayan da ya haɗiye loman tuwon bakin sa, yace, "yi haƙuri da Allah, wlh na kasa jira ne da yunwa na dawo".

Marairaice fuska tayi kafin tace, "Allah Sarki Mijina, meyasa ka zauna da yunwa yau?"

"To ya na iya Matata? ai tunda na san ban bar miki komai ba; to, kuwa nima bazan ci komai ɗin ba, kiyi haƙuri wlh yau gaba ɗaya buga-bugan ne sai a hankali, ban samu kuɗin bane shiyasa ban dawo na ba ki na cefane ba, wlh kina raina na rasa ya zan yi, duk bashi suka ci Abokan harƙallan nawa sai gobe zasu bani".

"Hmmm babu komai ai, ko baka faɗa min ba na san babu Mijina, ba yau muka saba haƙuri ba kuma haka nan zamu ci gaba da yi insha Allahu Allah zai taimake mu, duk sanda aka ce ka sami aikin ka na san komi zai wuce ai na lokaci ƙanƙani ne".

Murmushi yayi Anwar ɗin, cikin so da ƙauna da tausayin matar tashi yace, "haka ne Mata ta na san komi zai wuce, amma ina gani kamar gazawata ce ace Ni na kasa ciyar dake sai ke ce kike ci dani, ga shi yanzu duk na cinye miki ɗan jarin da kike taƙama dashi, yanzu kuma ban san ya aka yi kika samo na yau kika yi mana ba?"

Dariya tayi tace, "kar ka damu Mijina, kai dai kaci abincin ka".

"Baza ki faɗa min ba ko?" Yayi maganar yana tsare ta da idanunsa

Still dariyan tayi tace, "ko na faɗa maka babu abinda zai faru ya Mijina sai dai ya saka ka damuwa, so kabar zancen kawai kaji?"

Numfashi kawai ya ja yana kallon tuwon a wannan lokacin yana yanko wa zai saka a bakin sa, ya san cewa shi Mutum ne me Sa'a babba da Allah ya haɗa shi da Mata ta gari, a kullum burin sa a yanzu ya sami hanyar da zai riƙa faranta mata yana maida mata da alkhairan da take mishi, da ba don ita ba ba ya jin akwai Macen da zata iya zama dashi a gazawan sa, idan ya bada na yau sai ya kwana biyu be sake bayarwa ba, sai ita ce ko ta halin ƙaƙa sai ta samu tayi musu abinci ko sau ɗaya ne a rana, shiyasa duk wani jarin ta da iyayen ta suka kawo mata sun cinye, kuma koyaushe sai dai ta koma musu su sake bata ta cinye, tun yana tambayarta yanda ake yi take samun kuɗi ko ya ya ne ta sama musu abinda zasu ci tana sanar masa, yanzu kuwa ko me zai ce baza ta taɓa faɗa mishi ba, ta gummaci ta bar abin a ranta ko da bashi ne ta ciyo ko kuma ba da daɗin rai ta samu ba, da dai ace ta sanar mishi gaskiya ranshi ya ɓaci, abinda kullum take gudu kenan ɓacin ran Mijinta, tana iya ƙoƙarin ta wajen ta ga ta dage wajen faranta mishi da iyakan ƙarfin ta domin taga walwala a kan fuskar sa....

Maganarta ce ta katse masa tunanin da ya shiga, sai ya ɗago yana kallon ta

Tace, "ina ta magana kayi shiru sai yawo kake yi da hannun cikin tuwon ka ƙi ci, me ke damun ka ne Mijina? Ko tuwon ne be maka daɗi ba?"

Murmushi yayi idanunsa ƙyam a kanta yace, "a'a tunani kawai nake yi, ina tuna kyawawan halayen ki ne Hauwa ta, a kullum burina in samu hanyar da zan saka miki wannan alkhairin da kike min, taya ya zance abincin ki be min ba Hauwa ta? Wlh ko da kashi kika bani a yanzu a matsayin abinci wlh ci zan yi domin a wuri na ya fi min komai, kar in sake jin ma kin sake zancen nan kinji?"

Sosai tayi farin cikin kalaman sa ba kaɗan ba, don haka ta gyaɗa mishi kai tana sake yalwata fuskar ta da murmushi

"To saka hannu mu ƙarisa ko?"

"A'a na ƙoshi ai, sau biyu ma naci, da na gama na zuba naci yanzu ma naci".

"To shikenan bari in ƙarisa".

Har ta tashi kuma sai tace, "zaka yi wanka ne in ɗumama maka ruwa?"

Ɗago kai yayi ya kalle ta yana cewa, "a'a ki bari zan yi da ruwan sanyi, ki kai min dai kawai".

"To". Ta amsa mishi tana fice wa. Ruwa ta ɗiba a randan ta ta Kai mishi Bayi, sannan ta dawo ta sanar masa

Lokacin ya gama cin tuwon, sai ya tashi ya cire kayan shi ya sanya jallabiya ya fice

Ita kuma ta kawar da komi na wajen, sannan ta nannaɗe tabarman ta mayar ma'ajiyar ta, ta kunna musu maganin sauro tare da sakaya ƙofan.

Tana zaune kan gadon su ya dawo ɗakin. Shirya wa yayi ya sauya wata jallabiyan da yake barci da ita, sannan ya zauna gefen ta yana cewa, "kin san nayi mana ɗinkin bikin Muhseen?"

"Don Allah fa?"

Dariya yayi yace, "wlh kuwa. In miki ta Yara tunda kin maishe Ni Yaro. Ku dai haka kuke Matan nan da zaran an ce muku abu sai kun ce Mutum ya rantse ko kuma dan Allah fa? Ba kwa girma wlh".

Dariyan itama take yi cike da nishaɗi, sai kuma ta soma mishi godiya sosai

Murmushi kawai yayi ya tashi yana rufo musu ƙofan ya dawo yana cewa, "ai Ni ba na son irin wannan godiyar kin sani, mu je dai ki min irin godiyar da na fi so, don akwai ma sauran albishir ɗin da zan miki".

Ita dai dariya kawai take mishi har yazo ya tsallake ta ya haye can ƙarshen gadon, itama kuma sai ta tashi ta sauya kaya zuwa na Barcin ta tazo ta haye tana cewa, "to faɗa min albishir ɗin".

Janyo ta yayi jikin sa yana faɗin, "yanzu kuwa ranki ya daɗe!". Daga nan ya kashe fitilar dake saman gadon a rataye.





✳️✳️✳️✳️✳️


Yayinda Sauda a wanann lokacin da ya kasance mahutan bawa, wanda lokaci ne mafi tsada da zaka faranta wa Mijinka kasancewar wunin ranan ba ya gida, amma sai ya zamto da fitinan ta da ba ya ƙare wa ta tare shi, wanda kullum idan basu yi ba ba sa jin daɗi

Yaran su dake kwance har sun yi barci sai da suka tashe su tsaban jaraba irin nasu

Ita Sauda babu haƙuri a ranta, duk abinda kayi mata sai ta rama

Shi kuma Bilal ba ya son raini, duk da ada Mutum ne shi me haƙuri da babu ruwan sa, sai dai fitinan Sauda tuni ya gama tunzura shi ya mayar dashi fitinanne shima. Idan be biye mata bama ba ta ƙyale shi, ta dinga yi kenan baza ta gaji ba, har sai ta kai shi bango Ya kula ta. Kullum a haka suke.

Sai da yaran suka yanka musu kuka kafin suka haƙura da faɗan, kowa ya kwanta yana jin haushin ɗan uwan sa.








✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️



*WASHE GARI*
Shirin ta tayi cikin riga da skert na atamfa da yayi mata kyau matuƙa, ta sanya dogon Hijab har ƙasa blue color, sai ta fito riƙe da Jakar Kwali tana kallon Umman ta dake zaune gaban murhu tana iza wuta. Tace, "Umma bari in tafi na gama shirya wa".

Ɗago wa Umman tayi tana kallon ta tace, "Kai Munira da ƙosa wa kike, ki bari mana ki karya sannan sai ki tafi, kina ganin fa idan kun fita tun safe sai dare kuke dawowa, kuma a hakan ne kike son fita ba ki karya ba?".

"Wlh Umma ba na jin yunwa ko kaɗan, kuma kin san lokaci ya ƙure mana dole mu riƙa fita da wuri, mutanen da ban je wurin su ba suna da yawa wlh; kwanakin nan da ya rage bazai ishe Ni ba, kar ki damu zan siya wani abun a hanya inci insha Allahu".

Gyaɗa kanta Umman tayi tana cewa, "to shikenan ku dawo lafiya. Allah ya tsare hanya".

"Amin Umma". Tafaɗa tana yin gaba da sauri ta fice

Ƙofar gidan su cike take maƙil da Matasa sun fito karin safe, dayake akwai me shagon shayi

Fitowar ta ke da wuya wasu daga cikin Matasan suka soma tsokanar ta da "Amarya... Amarya". Wasu kuma su ce, "Munira Amarya..."

Dariya take yi ta ƙarisa wajen su tana gaishe su kana tace, "ku dai wlh baza ku dena halin nan naku ba, to Ni ina nawa indomin tunda rowa ake min? ko ku ce bari ku aika wa da Munira nata gida babu wanda ya san dani, shiyasa wlh nake kewar My Amadu Allah Sarki".

Dariya dukkan su suka yi

Ɗaya yace, "kiyi haƙuri Amaryan mu ai kin san mu dake ba ta ɓaci, bari a soya miki, na nawa kike so?"

Me shayin dake cikin shagon shi yace, "ai Ni kyauta ma zan soya miki komi Munira tamu, faɗa dai na nawa kike so?"

Dariya tayi tace, "a'a wlh da wasa nake yi, yanzu ma sauri nake yi sai anjiman ku, kar dai ku zauna zaman banza". Ta ƙare maganar tana wuce wa abin ta

Su kuma sai dariya suke yi suna faɗin, "to shikenan Munira tamu, a dawo lafiya Allah ya tsare".

Ɗaga musu hannu tayi tana ci gaba da tafiya ba tare da ta waigo ba. Ta ɗan yi nisa kafin ta shiga wani gida da sallama

Ƙawar ta Afnan dake zaune tana cin tuwo ta amsa mata tana kallon ta, sai kuma ta ɗaga murya tana cewa, "to Mama kin ganta ko. dama nace miki yanzu za ki ga ta bugo min sammako ga shi kuwa".

Janyo kujera Muniran tayi ta kafa shi gaban Afnan tana zama; tare da tsoma hannun ta cikin tuwon tana cewa, "wato gulma ta kika yi ko?"

Hararan ta Afnan tayi tace, "gulman ki? me kike dashi da zan yi gulman ki?"

Itama hararan nata tayi tana kai loman tuwon bakin ta

A lokacin Mama ta fito tana musu dariya

Munira tace, "kema kin san ina da komi na fi ki komi dole ki riƙa gulma ta. Mama ina kwana?" Ta ƙare maganar da mayar da hankalin ta wajen Mama

Mama tace, "lafiya lau Munira ya Ummar taki?"

"Lafiya lau". Ta amsa mata tana tsame hannun ta cikin tuwon ta tashi ta nufi bakin randa

"Mtsww dama gulma ce ta saka ki cin tuwon, ke dai kika sani magulmaciya".

"Ke wlh ki dena ce min magulmaciya idan ba haka ba bakin ki zai yi jini, kina jin ta ko Mama?" Munira ta faɗa hakan tana share ruwan hannun ta a jikin ta

Mama dai dariya take musu tana cewa, "kun fi kusa dai, Ni bazan shiga faɗan ku ba yanzu in ji kunya".

Gwalo Afnan tayi mata

Ita kuma ta ranƙwashe ta a kai tana cewa, "zan kama ki".

"Ban da kama nin da kika yi yanzu? Allah zan rama nima bashi kika ci".

Munira bata ce mata komi ba illa dariya da tayi mata tana cilla Jakar hannun ta sama tana cafke wa

While Afnan taci gaba da cin tuwon ta bata sake kallon ta ba

Ganin tana ɓata mata lokaci sai ta koma ta zauna tana cewa, "ke da Allah kiyi sauri mana, sanin kanki ne kin san wurin zuwar mu yawa ne dashi amma kin zauna kina ɓata mana lokaci, Ni ba ki ga ko abincin ban tsaya naci ba".

"To ina zan san ba ki ci ba? Ki jira Ni har in gama tunda ciki na da naki ba ɗaya ba". Afnan ta maida mata tana hararan ta

"Allah zan tsole idon nan. wai me nayi miki ne kike ta faman harara na da wannan idanun naki masu kama da tsutsa?".

Afnan tace, "kin manta ne wancan Angon naki shi ne me kama da idanun tsutsa, wlh kar ki sa raina ya ɓaci yanzu in CE na fasa raka ki".

"Ahayye da an yi ruwa da ƙanƙara wlh, kin san hali na sarai duk abinda kikai min zan rama".

"Wai baza ku dena wannan shiriritan naku ku zo ku wuce ba?"

"Mama wlh Afnan ce take ɓata min lokaci, kuma bayan nace mata sammako zamu yi amma ta zauna tana min yanga, idan ta bani haushi ma sai in je gidan su Zainab ta raka Ni".

Tsaki Afnan ɗin taja tana tashi tsaye tace, "to kin san da itan ne kika zo wuri na? Wlh Munira kina cin arziƙin me sama ne".

Gwalo Munira tayi mata lokacin da ta juya baya, sai tace, "to naji mu dai je, idan muka fita sai mu ɗaura daga inda muka tsaya don ba ƙyale ki nayi ba".

Ita dai Mama dariya kawai tayi tana bin su da kallo, ta san idan ta biye ta nasu sai suyi ta saka ta magana bakinta yayi tsawo ba gaira ba dalili.




Bayan Afnan ta wanke hannun ta, ɗaki ta shiga ta sanya Hijab irin na Munira sannan ta fito, ta kalli Muniran tace, "dalla tashi mu je ko ki bani haushi in koma".

Dariya Munira tayi tana tashi tace, "na san dai duk fushin na mene ne, aure ne dai sai nayi na barki, kema idan kin yi fushi ki fito da naki a haɗa ayi mana. Mama sai mun dawo".

"To a dawo lafiya, kar dai ayi dare kun ji?".

"To Mama". Munira ta amsa mata tana yin gaba

Afnan na biye da ita a baya

Mama tace, "Afnan babu a dawo lafiya za ki fice?"

Juyo wa tayi tace, "yi haƙuri Mama yarinyan nan ne ta caza min kai. sai mun dawo".

"Allah ya tsare".

"Amin". Daga nan tabi bayan Munira da har ta fice ma.
[31/08, 9:29 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*











*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*PAGE: 3*

_____"Hauwa bari inje gidan Atine. Idan su Sulaiman sun dawo don Allah abincin su na kichen su je su ɗauka".

"To". Hauwa ta amsa mata tana ci gaba da wanke-wanken ta

Ita kuma ta saka kai ta fice, da gidan da suke da gidan Atine me adashi babu nisa, domin gidaje hudu ya raba su, tana shiga da sallama

Atine dake bakin famfo tana matsa ruwa, kasancewar yanzu ruwan Me rusau ya yawaita ko ina, su ma har wajen su ya zo. Amsa mata sallaman tayi tana cin magani ganin Sauda ne, domin ta san idan bata yi haka ba Sauda ba ta da mutunci ko kaɗan, ita kuma yanzu bata da kuɗin bata

"To kuɗi na nazo amsa. Allah yasa kin haɗa min kansu, domin wlh buƙatar su nake yi zan je kasuwa in yo siyayyan kayan siyarwa na".

"Ai ba sai kin faɗa min ba Sauda na san haka, sai dai kiyi haƙuri kamar yanda nace miki jiya, kuɗin nan har yanzu basu haɗu ba, na bi mutanen da nake bi bashi sun hana Ni, sai dai kiyi haƙuri zuwa jibi in ba ki".

"Kan kutumar uba... Wlh Atine kin ci uwar rainin wayau, wato in Yi haƙuri har sai jibi za ki bani?"

"Eh haka nace, tunda ai na ga ba ki fi kowa zane ba, ba ke kaɗai ne me bi na kuɗi ba su ma sauran sun yi haƙuri, tunda na ba ki haƙuri sai ki haƙura zuwa jibin domin ba cinye miki zan yi ba". Atine tace hakan tana kashe famfon, kana ta ɗauki ruwan dake tukunyan ta nufi kichen

Inda Sauda tabi bayan ta tana cewa, "wlh tallahi ban san zancen ba Atine, Ni ban san haƙuri ba kawai ki shiga ki fito min da kuɗi na, idan kuma ba haka ba za ki ga rashin mutunci na".

Tsaki Atine taja tana shige wa kichen ta soma ƙoƙarin aza ruwan a saman murhun dake balbali da wuta

Ganin tayi banza da ita, ita kuma sai ta zuciya ta wuce ɗakin ta ta shige, inda babu jimawa ta fito ɗauke da receiver a hannun ta tana cewa, "Ni na fi ki iya shege wlh, ki jira Ni in je in siyar in kawo miki sauran kuɗin ki".

Jin haka da sauri Atine ta juyo gare ta, tana ganin ta da receiver'n ta ai kuwa ta fito kichen ɗin aguje tayo kanta. "Na rantse ba ki isa ba Saude, babu inda za ki je min da receiver, a Kan dubu huɗun banza za ki kama ki je ki siyar min da receiver har na dubu goma sha biyar? Ke ba ki san haƙuri bane?"

"Ban san shi ba Atine, dama ba ki taɓa taɓo Ni bane shiyasa ban taɓa sauke miki nawa tijaran ba, al'ƙur'an sai na siyar na cire kuɗi na idan har ba ki shiga kin fiddo min kuɗi na ba".

"Ni kuma baza ki fitar min dashi ba wlh, nima duk abinda kike ji dashi na fi ki, rashin mutunci na ya zarce naki".

Kaya-kaya sai suka soma kokawa, inda Atine a dole sai ta ƙwace receiver'n ta, ita kuma Sauda ta ƙwaƙume shi a jikin ta baza ta bata ba, sai bala'i suke yi suna masifa

Masifan nasu ne har ya jawo maƙota aka zo rabon faɗa

Amma sun ƙi rabuwa kowa ya dage a kan bakan shi

Ana haka sai ga Mijin Atine da kayan aikin sa a jikin shi, dayake shi kurtun ɗan sanda ne

Kowa ya san halin shi nan da nan mutane suka dare, wasu kuma na sauya zance suna goyan bayan Atine duk don sabida ganin shi da suka yi

Amma ita Sauda bala'i ya ci ta idanunta sun rufe ko kaɗan bata damu dashi ba bare kakin jikin sa su bata tsoro, sai bala'i take yi tana faɗin, "baza ta saki receiver'n ba sai an bata kuɗin ta".

Tsawa Mijin Atine ya daka mata yana cewa, "ke dalla sake ta ko kiyi kwanan cell".

"Kutumar uban Cell ne ba Cell ba, wlh muddin ka ga na saki wannan abun to kuɗi na aka bani, bar ganin kana da jan ido kazo kana wani zare min su, ba tsoron ka nake ji ba Ni kawai kuɗi na na sani".

Jin haka sai yace, "Atine saki receiver'n".

Saka tayi tana huci

Sai ya kalli Sauda yana sake shan mur yace, "wato ke ba ki da mutunci ba ki da raguwar sa? To zan ga ƙaryan iskancin ki zan nuna miki kakin ƴan sanda ba abun wasa bane, bani receiver'n ko in ci kutumar uban ki".

"Ba dai kutumar uba na ba sai dai kutumar uban ka, kai wlh na fi ka iya shege ba na tsoron a kai Ni ko ina ne, sai an bani kuɗi na zan baku receiver'n nan". Sauda tayi maganar tana kaɗa jikin rashin mutunci duk ta haɗa gumi kashirɓan.





Abu fa ya ƙi ya ƙare tsiya raga-raga ake ta yi, inda gidan ya sake cika maƙil, an tara jama'a babu inda labari be kai musu ba, kama daga gidan sirikan Sauda har Hauwa dake gida sai da taji labarin faɗan da ake yi, aikin ta kawai taci gaba da yi ta ƙi taje ta gani

Bilal ma dake bakin kasuwa wajen sana'ar sa labarin har ya je mishi, shima ƙin zuwa yayi yace, "Allah yasa ma ƴan sanda su kaɗa ƙeyan ta yaga ta tsiya tunda bata da mutunci".

Duk yanda mutanen suka so su raba faɗan nan an kasa, Sauda ta zame musu ƙarfen ƙafa domin ta ƙi nuna tsoron ta ko kaɗan, bala'i take yi bilhaƙƙi kamar mahaukaciya sabon hauka

Dole sai da Mijin Atine ya je ya aro kuɗi ya bata kafin ta bar gidan

Haka mutane suka watse ana ta zagin ta, domin fa yau anguwan sun ga tijara, dama babu wanda be san halin Sauda ba, sai dai basu san rashin mutuncin nata ya kai har ɗan sanda bata ƙyale ba. Wasu kuma daɗi suka ji gwara da Allah ya haɗa Atine da Sauda, tunda itama bata da mutunci ko kaɗan, idan aka kwashe adashi daƙyar take bayar da kuɗin, sai tace wai, "tayi amfani dashi amma zata bayar rana kaza". Ka gama bala'in ka har ka gaji kafin ta samu ta bayar da kuɗin.





✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


"Wai ni Jamal ban gane ba? Wancan koɗaɗɗiyar yarinyan ne zaka saka ta a makarantar su Intisar?"

"Eh ita dai wacce kike magana ita nake nufi".

"To wlh bazai yiwu ba, a lokacin da ka saka ta Islamiyyan su ban maka magana ba sai yanzu kazo min da zancen da hankali ma bazai ɗauka ba, sam bazan lamun ta ba tunda ita da su ba ɗaya bane".

"Wai Fauziyya me kike so ki zama ne iye? Idan ba ke ce kika raba su ba ai duk ɗaya suke a wuri na, Hafsah itama tana matsayin ɗiya ta ce tunda mahaifiyar ta ƙanwata ce, duk abinda zan ma ƴaƴana ba laifi bane idan nayi mata, kar in sake jin zancen nan da Allah. Ki kira min ɗaya daga cikin yaran nan su zo su kai wa Mama kayan nan ta ajiye mata".

Tsaki Fauziyyan taja tace, "amma ai akwai makarantu kala-kala na dai-dai ita meyasa baza ka saka ta ba sai nasu Intisar? Ni wlh gaskiya bazan lamunci wannan abun da kake min ba, ka ga fa idan baza ka iya damu bane tun wuri ka sanar min in San madafa na".

"Me kike nufi kenan?" Yayi maganar yana kallon ta da tsananin mamaki

Juya wa tayi kawai ta fice tana surutai a ranta

Shi kuma ya bi ta da sakakken baki cike da mamakin sauyawan

Please Login or Register in order to submit comment