Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"zai amince in sha Allahu, ai na san ta yanda zan ɓullo mishi." Sai ya ba shi hannu yana cewa, "Ni bari in je, ina da ayyuka sosai da nake son ƙarƙare wa, When I'm done, I'll come and meet you; and we'll go check out the building."

"Ok ba matsala, ai ina nan nima sai yamman."

Dariya Muhseen yayi yace, "an gama shan Angoncin kenan? Yanzu zamu samu kanka kenan?"

Shima Anwar dariyan yayi yana ba shi hannu suka duki juna, tare da faɗin, "ah sosai ma, ai yanzu komai ya dawo normal kuma, hutu ya ƙare dole in dawo, amma maganar Angonci yanzu ma aka so ma, kai dai kawai ka samu lokaci ka leƙo don bazan huce ba in baka zo ka ci girkin Amarya ba."

"Kar ka damu Abokina, ina nan zuwa a wannan week ɗin, Allah kunyar Hauwa nake ji, amma zan zo."

"Hmm kai da ita ne babu ruwana, Ni dai ka samu dama ka zo ko goben ne Please, tunda ka ga weekend ne ina gida."

Kafaɗa ya ɗage tare da faɗin, "ok no problems, bari in je sai zuwa anjiman in mun haɗu." Ya tashi ya fice bayan sun sake sallama

While Anwar ya ci gaba da aikin da ke gaban sa.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆



               Zeena na ɗaki tana faman kwalliya a gaban mirror, tana sauri ta fita sabida ganin lokacin da suka yi da Sadis yau zasu haɗu, har lokacin ya gota bata gama kimtsa wa ba, dayake ta tsaya yin waya da Aliyu duk ya gama ɓata mata lokaci, shiyasa take ta sauri yanzu. Sai jiyo sallaman mahaifiyar Aliyun tayi tana kwaɗa mata kira. Ajiye lipstick da ta gama shafa wa tayi, tana nufan kan gado tare da ɗaukar ɗankwalin ta ta fice Falo

Inna wacce ta shigo ta izo ƙeyan su Sadiq a gaba

"Inna ke ce ashe?" Zeenan ta furta tana kallon su

Yayinda Innan tace, "eh Ni ce, na dawo miki da waɗannan guntayen ƴaƴan naki ne tunda baza ki ji magana ki dena aiko min su ba, to ba dai a gidana ba ki ƙarata can da su ba na son ganin ƙafafun su a gidana, don nima ba zaman rainon su zan yi ba."

"Yo Inna na ga ai Jikokin ki ne, meye laifi don na ce su zo su zauna kafin in dawo?"

"Kee! Kar kiyi min rashin kunya fa don bazan ɗauki sakarcin nan naki ba, idan ba iskanci da wulaƙanci ba ina za ki je da wannan tsohuwar yammacin? In ke ƴar mutunci ne ai baza ki fita ki bar gidan Mijinki ba, ke kenan yawo baza ki zauna a gidan ki ba sai dai ki tasa Yara suna gantali a titi, to uban wa zai riƙe miki su? Wa kika bari Bawan ki? Can da ke da su kar ki sake turo min su gidana, don wlh zan mummunan saɓa miki tunda baza ki ji maganata ba, ai ke ma kina da Uwar; ki tura su can mana, ko Ni ce marainiyar wayon ki?"

Yatsina fuska tayi, cike da rashin kunya tace, "ai na ga ke ce Uwar Ubansu, dole wurin ki zan tura su tunda ke Kakar su."

"Au rashin kunya za ki yi min?"

"Babu zancen rashin kunya Inna, shi dama babba idan bai ji kunyar hawa Jaki ba; to Jaki bazai ji kunyar ka dashi ba, don na turo Yaran shi ne har da min takakkiya kina taso su? To ina zan tura su in ba wurin ki ba? Kuma da kike faɗin ban tura su wurin Uwata ba ai itama ba ƴar aiki bace, Yara dai Jikokin ki ne, ko ki so su ko kar ki so su ɗanki ya haife su."

Salati Inna ta saka tana cewa, "yanzu ke Zeenatu Ni kike faɗa wa wannan maganar don ba ki da mutunci ba ki da ta ido? Tunda gidan ku ba a koya miki tarbiyya ba ba ki san yanda za ki yi magana da manyan ki ba, wlh ina turr da auren ki da Aliyu yayi, ya rasa wacce zai kwaso mana sai ƴar matsiyata haihuwar titi waɗanda basu san darajar kansu ba."

Zeena taso ta ƙyale ta, amma ganin abun da take cewa, shiyasa ta kaɗa jiki tace, "Inna wlh tallahi ina raga miki ne don kawai ɗanki ke aure na, duk abubuwan da kike yi ina ƙyale ki ne kawai amma ba ki san zurum ba, kuma na ga ke ma ɗan naki ai ba tarbiyyan ne dashi ba tunda ya rasa wacce zai aura sai Ni Zeena, tare muka gama tambaɗewar mu don haka dole ya ɗauki saura, kuma wlh babu mai raba mu nan gani nan bari, izuwa yanzu ya ci ace kin haƙura kin zauna da Ni lafiya, amma kullum ba ki da aiki sai muzanta Ni da yin min baki, idan ƴarki ce ai baza ki so a yi mata haka ba, kuma alhamdulillah Yara dai ko ki so ko kar ki so Jikokin ki ne, duk yanda kika kai da ƙin su dole ki zauna da su." Sai ta ja dogon tsaki tana wuce wa cikin daki ta bar Inna da sakakken baki a wurin

Yayinda su Sadiq suna zaune a saman kujera suna ta kallon su. Suhaima mai saurin kuka har ta fara ƙananun kuka

Inna fita tayi a gidan bata sake furta komai ba, sai dai gaba ɗaya zuciyarta ta harzuƙa da abun da Zeena tayi mata, kuma ta ɗauki alwashin in har tana numfashi sai ta raba Aliyu da Zeena, ba ta ƙaunarta kuma baza ta taɓa ƙaunarta ba, sai ta ga bayan auren su ko ta halin ƙa-ƙa ne, tabbas a wannan lokacin zata nuna wa Aliyu ita ta haife shi; ba shi ya haife ta ba, muddin bai rabu da tsohuwar kilakin nan ba, to sai dai su raba Jaha da shi da ita, ya zaɓa ko ita ko Zeena, ta gaji, nan gaba ma bata san me zata yi mata ba, tunda har tana faɗa itama tana faɗa, tana zagin ta da cin mata mutunci, ai kuwa zata nuna mata ita ta haifi Aliyu

Yayinda Zeena itama ranta a ɓace yake, gama shirya wa tayi ta ɗaura ƙaramin gyale a kanta, sannan ta fito Falo tana kallon su Suhaima. Tace, "ku tashi mu je in ajiye ku a gidan Aunty Nadeeya."

Tirje wa Sadiq ya soma yi cike da shagwaɓa yace, "Ni Mamy babu inda zamu je, ki bar mu a nan kawai zamu zauna."

Daƙuwa tayi masa tace, "Ubanka, tashi maza kuna ɓata min lokaci, ke kuma daga saka miki kaya yanzu har kin ɓata ko?" Ta ƙare maganar tana kallon Suhaima wacce take tsotse hannu a yanzu, hancin ta duk ya yi gaja-gaja da majina. Kamo ta tayi ta share mata hancin tare da furta, "tashi nace Sadiq kar in ɓata maka rai."

Dole Sadiq ɗin ya tashi yana mirza idanu hawaye na zuban masa

Sai ta wuce wurin fridge ta dauko musu Bobo ɗai-ɗai ta miƙa musu, tana kallonsu tace, "yanzu zan je in dawo bazan jima ba, zan biyo ta gidan sai in ɗauke ku, kuma zan siyo muku kayan wasa ban son kuna wannan kukan kun ji ko?"

"Mamy ki je da Ni, zan bi ki." Suhaima ta furta tana ƙoƙarin ɓare baki

"Haba Babyna, ai bazan jima ba zan dawo, oya mu je kuna ɓata min lokaci, mu je zan kaiku har gidan ma yanzu."
Ta tasa ƙeyan su suka fice a gidan bayan ta kulle ko'ina

Kai tsaye cikin anguwan suka nausa a ƙafa tana riƙe da hannun Suhaima. Can kusa da gidan Innan suka koma; tunda a nan ƴar uwanta Nadeeya take aure. Koda ta kaisu bata shiga ciki ba kasancewar tana ta samun kiran Sadis yana faman jiran ta, sai ta iza ƙeyan su suka shiga ita kuma ta kamo hanya zata tafi

Bata yi nisa ba Yaran suka fito suna kwaɗa mata kira

"Ha a.. ya haka Sadiq? Wai ina wasa da ku ne? baza ku shiga ciki ba?"

"Mamy babu kowa a ciki wlh."

Tsaki ta ja ta dawo, ta kama hannunsu suka sake shiga gidan. Ai kuwa babu kowa ƙofofin gidan duk a kulle ne, sai zauren gidan da yake a buɗe, sallama ta dinga yi amma babu kowa, dole ta ja hannunsu suka bar gidan suka koma gida, tace musu, "su shiga su zauna baza ta jima ba zata dawo, ban da ɓarna su zauna su jira ta zata siyo musu kayan dad'i."

Dayake babu wutan NEPA, shiyasa ta kunna musu Generator ta saka musu TV don ya ɗauke musu kewa. Ta rufe su a Falon ta tafi ta bar su

Yayinda su kuma suka yi zaman su suna ta kallo, tun suna wasa har Suhaima tayi barci a nan ƙasan kafet. Shi kuma a garin taɓe-taɓen sa ya wuce kichen; har ya je ya kunna gas-kuka kamar yanda ya ga Mamyn sa tana yi, a ƙoƙarin sa na ya ɗaura girki ganin dare yayi, sai murna yake yi yau ya samu damar kunna wa. Sai abun ya zo da tsautsayi a garin ƙure wutan da yake yi yana rage wa yana ƙara wa, kawai ya tashi yayi bombing lokaci guda

Kafin ka ce me, gida ya soma ci har maƙota sun ankare. Allah da ikonsa aka kawo musu agaji amma fa an kasa shiga gidan sabida yanda gidan yake ci fiye da ƙima, duk taimakon da mutane suka bayar daƙyar aka samu aka fasa ƙofan aka shiga ciki, tare da ƙoƙarin kashe wutan don har ƴan kwana-kwana an yi gaggawar kira

Sai dai ba a samu rai ko ɗaya ba don a tunanin jama'ar wurin, babu mutane a ciki, shiyasa aka yi hanzari aka je aka sanar da Mahaifiyar Aliyun domin su zo su ga halin da ake ciki.


                   A daidai wannan lokacin ita kuma Zeena tana can a hotel, sun gama masha'an su da Sadis, domin sai da suka ji kiran sallan magriba sannan suka haƙura da juna haka nan, suka soma haraman tafiya

Sai dai kuma tsautsayi ya rutsa da su, ƴan fashi suka dira a Hotel ɗin, sun biyo wani Alhaji cikin Hotel ɗin. Ɗaya daga cikin ma'aikatan Hotel ɗin ya shiga dakin da Alhajin yake ciki sai ya tarar da ƴan fashin suna ƙoƙarin tilasta shi a kan sai ya fito musu da kuɗi ko su harbe shi. Dalilin da yasa suka harbi ma'aikacin kenan tunda ya rigada ya kama su hand right da bindigu suna bugun Alhajin

Ganin zai gudu ya ɓata musu aiki, sai kawai ɗaya ya harbe shi ba tare da yayi tunanin abun da ya aikata ba. Kafin ka ce me harbin bindigan ya gama tartsawa hotel ɗin. Nan fa mutane suka shiga cikin tashin hankali kowa ya soma ƙoƙarin guduwa

Yayinda nan da nan aka kira jami'an tsaro, lokaci guda suka samu isowa tunda babu nisa da wurin da suke. Shi yasa suka hana kowa fita a cikin hotel ɗin aka rufe tare da fara binciken gaggawa, a tunanin su ƴan fashin suna ciki, sai dai koda suka duba an neme su an rasa, tunda suka yi harbin suka gudu da kuɗin da Alhajin ya miƙa musu saboda halin ruɗe wa, suna fita shima ya sume a wurin bai sake sanin inda kansa yake ba

To wannan ƙaddaran ta rutsa da su Zeena cikin hotel, babu halin fita, don har an tattara su wuri ɗaya sai an gama bincike sannan za a bar su su tafi.
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*




                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼











            *PAGE:24*

_____An ɗauki lokaci mai tsawo kafin a samu a kashe wutan gidan, lokacin komai na gidan ya ƙone ƙurmus,
Ga mutane sun taru a wurin sai jimami da salati ake yi,
Har ƴan uwan Aliyu duk sun taho tare da Inna itama sai kuka take yi tana faɗin, "Allah yasa babu kowa a ciki?"

To su dai mutane sun tabbatar babu kowa a ciki, tunda ba a ga ɓirɓishin mutane ba, duk yanda aka yi Zeena ta fita a gidan,
Kuma tun farko an rasa numbanta bare a kira, kasancewar a anguwan nasu duk ƙabilu ne, so ba wai saba wa suka yi ba kowa harkan gaban shi yake yi,
Su Inna kuma basu da numban ta sai na Aliyu, shiyasa aka kira sa da gaggawa aka faɗa mishi halin da ake ciki

Matuƙa ya ruɗe da jin abun da ke faruwa, ya kasa ma yin tunanin abun da zai yi daga farko, jikinsa sai faman rawa yake yi zuciyarsa na buga wa, burin sa kawai kar a ce Iyalan sa suna cikin gidan. A lokacin da yayi wannan tunanin nan da nan ya zabura ya soma kiran numban Zeena, sai dai tana ring amma ba a ɗauka ba, kasancewar a silent take. Ya soma jin sanyi-sanyi duba da yanda ya kira wayanta ta shiga, alamu ya nuna duk yanda aka yi ba ta cikin gidan. Shi yasa a daren ya kamo hanya don bazai iya jira ko na misƙala-zarratan bane, dole hankalin sa ya tashi ya nufo gida, duk da tazaran Jigawa da nan Kaduna, amma daren bai sa ya jingirta ya bari sai gobe ba, since a goben ma yake saka ran dawowa.
***


           Su kuma su Zeena suna can cikin halin tashin hankali da ruɗewa su ma, ana ta bincike an ƙi barin su su tafi, ƙarshe ma sai da aka kwashe su zuwa Police station tunda su ne kusa da ɗakin da abin ya faru

Duk dai binciken da aka yi ba a samu komai ba, kasancewar Alhajin ya farka a lokacin ma, kuma shi ya basu evidence na ƴan fashin, shiyasa aka sallami kowa suka nufo gidan. Lokacin kusan ƙarfe tara da rabi na dare ne,
Tun a can hanya ma suka rabu da Sadis, shima yayi gida abun sa hankalin sa a tashe, duk da abun ya zo musu da sauƙi ba a kama su ba, amma dole su shiga wani yanayi

Ita kuma Zeena tashin hankalin yana gaba, ashe bata ga komai ba sai da ta koma gida. Ta je ta tarar da gidan su ƙurmus har yanzu hucin hayaƙi yake yi, ga mutane ƴan anguwan still suna wurin ana ta mayar da zance,
Haka zuciyarta ta buga lokaci guda ta nufi wurin tana tunanin me ke faruwa da gidan nasu da ya koma haka? Take ƴaƴanta suka faɗo mata a rai, ai nan ta saki jakarta ta nufi wurin da gudun ta zata shige gidan

Nan fa mutanen suka ankara da ita, wata jibgegiyar inyamura Maƙociyar ta tace, "yauwa an gode Allah, ga Matar gidan nan, ashe babu su cikin gidan? Mun gode Allah gobaran bata tashi da su ba."

Ƙanin Aliyu wanda yake wurin shima, don shi ya tsaya a wajen; su kuma su Inna suka koma gida tunda dare yayi, sai ya nufo wurin Zeenan yana kallonta ya kira sunan ta

Cak Zeena ta tsaya ta gagara buɗe ƙofan da zafin wutar har yanzu yana jikin ƙofan. Ta juya tana kallon Habib ta kasa haɗiyar yawu sabida irin yanda zuciyarta ke luguden buga wa, jikinta sai faman rawa yake yi ta rasa bakin magana

"Alhamdulillah, ai mun yi tunanin da ku gobaran ya tashi; ashe babu ku? Alhamdulillah mun gode Allah, kin ga yanda Allah yayi abun sa, bamu fitar da komai ba a ciki, yanzu ma su Inna suka koma gida don hankalin mu a matuƙar tashe yake, we assume kuna ciki da ke da Yara?"

Da sauri ta kai hannunta bakinta nan da nan hawaye suka soma sintiri a kan kyakkyawar fuskarta, sai kuma ta kalli gidan sannan ta kalli Habib ɗin, daƙyar ta iya furta maganar nata sabida kyarma da bakin ta yake yi, "wayyo Allah na shiga uku Habib! Akwai... Akwai su Sadiq a cikin gidan fa, kana nufin sun ƙone?"

"Su Sadiq kuma? Akwai su Sadiq?" Shima ya furta cikin sabon wani tashin hankalin

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Na shiga uku na lalace, akwai su Sadiq wlh, a ciki na bar su, a ciki na bar su na rantse da Allah suna ciki, shikenan har da su suka ƙone?" Lokaci ɗaya ta sake ruɗe wa tana furta waɗannan kalaman, yayinda ta tura ƙofan da ƙarfi ta shige ciki tana kwaɗa kiran sunan Yaran

Mutanen wurin fa sai suka sake shiga wani tashin hankalin, duk suka rufa mata baya har Habib yana faman kiran sunan ta da son sake tabbatarwa, "da gaske take yi akwai Yaran a ciki?"

Zeena ta kasa ɗaukar wannan babban tashin hankalin da ya tunkaro ta, lokaci guda ta zube a wurin numfashinta ya rabu da gangar jikinta. Sai dai aka kwashe ta aka wuce da ita asibiti tunda duk taimakon da aka bata a wannan lokacin sun rasa samun numfashinta

Al'amarin da ya ƙara ɗagawa jama'a hankali kenan. Musamman mutanen gidan su Aliyu, sun shiga halin ruɗu tunda aka ce musu har da yaran a ciki, ma'ana dai da su gidan ya ƙone, wannan tashin hankali da me yayi kama?

Ita kanta Inna duk rashin sonta da Yaran, sai da ta koka da dana-sanin abun da ta aikata, tun farko da ta riƙe yaran bata mayar da su ba, da mahaifiyarsu bata kulle su a gidan ta tafi yawon gantalin ta ba. "Kaico na Ni Asabe, na yi sanadin da Yaran da basu ji ba basu gani ba sun mutu, duk a kan sakaci na Ni da Uwar su, wannan wacce irin mummunar ƙaddara ce? Da wanne idon zamu kalli Aliyu? Shikenan bamu san wanne hali zaka shiga ba, Yara har biyu fa?"
Kuka sosai take yi ana bata haƙuri, amma ta ƙi shiru sai kuka

Haka fa gidan su ya kasance jugum babu wanda ya runtsa a wannan daren, kowa yana jimami da tashin hankalin abun da ya same su

Yayinda can asibiti kuma har wannan lokacin Zeenan bata farfaɗo ba, ƙarshe ƴan uwanta ne a wurin ta, domin tunda aka kaita Habib ya bar wurin, sai aka kira su don su zauna da ita.
***

           Aliyu kuma sai washe gari da sassafe ya iso Kaduna, sabida Motan da ya hau dole sai da tayi kwanan hanya, da sassafe suka miƙo hanya suka ƙariso cikin Kaduna tunda baza a barsu su shigo da dare ba, akwai matakan tsaro

Shima zube wa yayi da ya ji labarin abun da ya faru. Koda aka zuba mishi ruwa ya farka kuka kawai yake yi, ya kasa jure jin har da ƴaƴansa a gobaran da ya tashi, shikenan yanzu ya rasa su? Kuka sosai yake yi ya kwanta bai san inda kansa yake ba, duk wanda ya gansa sai ya tausaya masa, babu rarrashin da ba a yi masa ba amma ya ƙi kula kowa sai kuka

Inna nata ba shi baki tana gaya masa abun da ya faru, tare da furta, "itama har da laifin ta, idan da ace ta ajiye Yaran da duk hakan bata faru ba, yanzu sai dai haƙuri, Allah ya ɗauki abun sa, Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi."

Lokacin Habib da Usman suka shigo ɗakin. Zama suka yi suna kallon Yayan nasu wanda yana kwance yana tsiyayar da hawaye abun duniya duk yayi mishi yawa. Sannu suka yi mishi amma ya kasa buɗe ido ya kalle su bare ya amsa musu

Usman wanda dama shi ya fi jin haushin Zeenan duk gidan, baya ga Innan sai shi a tsanar da suke mata, yau da safen nan Abokinsa yake ba shi labarin abun da ya faru a Hotel, dayake shima ɗan sanda ne, to lokacin da aka kai su Zeena station ya ganta, shiyasa ya bibiyi abun da ya faru har aka kawo su wurin, da zummar gobe idan sun haɗu da Abokinsa Usman sai ya shafa mishi labari, sai kuma ga abun da ya kasance na gobarar da aka samu, har an rasa Yaran Aliyun, shiyasa Abokin Usman ɗin ya ga dacewar faɗa musu komai don gaskiya kamar ya ci amanar su ne, gwara su san inda Zeena ta je a jiya har tsautsayin nan ya kasance. Shi yasa yanzu da suka shigo Usman ɗin yake faɗa musu abun da ya faru, da dalilin da yasa Zeena ta bar gida ashe tana can tare da wani ƙato a hotel, duk laifin nata ne

Jin wannan maganar, ba su kaɗai da suka san halin Zeenan ba, har Aliyu sai da ya ruɗe ya tashi da sauri yana salati a ƙasan ransa, har ga Allah bai san cewa Zeena tana ci gaba da biye-biyen Maza ba, kuma bai taɓa tunanin cewa tun lokacin da suka yi aure bata fasa halin ta ba, a tunanin sa tuni ta dena, sai yanzu da ya soma jin maganganun ƴan uwan nasa suna bayyana mishi irin halin da Matar shi take ciki idan ba ya nan, da kuma jita-jitan da suke samu a kanta, duk yau sai da suka juye mishi tunda suna tsoron faɗa mishi kasancewar bazai taɓa yarda da su ba, musamman yanda yake matuƙar ƙaunarta ko kaɗan ba ya ganin laifin ta, amma yanzu dole ne ya yarda tunda ga abun da ya faru, ta sanadiyyar ta ya rasa ƴaƴansa dukka biyun

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..." Abun da ya iya furta wa kenan yana dafe kansa da yake sara masa kamar zai tsage

Inna tace, "ka ga abun da nake gaya maka kenan ko? Tun farko sai da na gudan maka auren irin waɗannan Yaran, amma ka dage sonta ya rufe maka ido ko kaɗan baka damu da abun da zai biyo baya ba, ka ɗauko wannan sheɗaniyar yarinyar da gidan su ba'a koya musu tarbiyya ba, ka dage ka ce ita zaka aura, kuma ga abun da ya haifar, dama ire-iren su ai sai wanda Allah ya tsare."
Sai ta fashe da kuka tana face majina da cewa, "ka ja mana bala'i kawai Aliyu, ga shi nan ka rasa yaran naka kaima."

Aliyu ya kasa magana sai kuka, kukan baƙin ciki da jin ƙuna a cikin ransa, ga wani irin kishi da ke taso masa daga can ƙasar maƙoshin sa, kuma duk wannan abun jin tsananin ƙaunar Zeenan yake yi a ransa, bai san meyasa tayi masa haka ba, meyasa baza ta iya hakura dashi shi kadai ba har sai ta haɗa shi da wasu? Mene ne bai sauke mata na nauyin sa ba? Me ya rage mata? Amma a haka take cin amanar sa tana haɗa shi da ƙadangarun Bariki,
Ya kasa magana ma don takaici da ɗacin da yake ji a cikin ransa, yayinda maganganun Inna suke ƙara masa wani irin zafi mai raɗaɗi a ƙasan ransa,
Musamman yanda take ta masa faɗan kuskuren da yayi na auren Zeena, kuma tana ba shi umarni a yanzu, "ko yana so ko ba ya so sai ya rabu da ita wlh, dole ta bar musu dangi don baza su iya da Jarabar ta ba, mai hali bazai taɓa fasa wa ba, ba abun kunya bane ma a ce ana nuna sa a gari a kan abun da Matarsa ta aikata?"
***




                   Ita kuma Zeena tana can asibiti, a sa'ilin da ta farka ta tabbatar da cewan ta rasa ƴaƴanta, kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita, tana kaico da dana-sanin abun da ta aikata, ga shi ta rasa Ya'ya har biyu a garin son zuciya da kwaɗayin abun duniya, kuka ta dinga yi ta kasa yin shiru sai sambatu da kururuwa take yi

Umman su da ƴan

Please Login or Register in order to submit comment