Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama ba a iya musu ko ya ya ne idan har suna son ƙarin aure babu ruwan su zasu ƙara ne koda ana wadata su da komi a gida, to idan ko haka ne bata ga amfanin ace Anwar ya yiwa Hauwa kishiya ba; Mace kyakykyawa da sanin yakamata ga iya daɗin zama, babu abinda Afnan zata fi ta da shi sai dai hasken fata tunda ita fara ce sol, sai kuma shekaru da Hauwan ta fi ta wanda a ƙalla bazai gaza shekaru biyu zuwa uku ba....



Har Muhseen ya dawo daga aiki suka gaisa har suna ɗan taɓa hira, daga ƙarshe kuma ya wuce ɗaki

Munira bata bi shi ba sabida hira da ya ɗauke mata hankali, suna ta zuba da Sauda wanda dama an haɗu da an haɗe ne, ba ga Muniran ba; ba ga Saudan ba dukkan su iyayen zuba ne

Sai da Hauwa ce tayi mata magana da cewa, "ya kamata ki shiga wajen mijin ki kar yazo yana bukatar wani abu kin bar sa shi kaɗai, kinga idan kika biye wa Sauda zancen ku bazai ƙare ba wlh."

"Ai kuwa dai, gwara ki tafi kar ki biye min." Cewar Sauda tana dariya da buga cinya

Inda ita kuma Muniran tayi murmushi tare da miƙe wa ta wuce ɗakin nasu. Tana shiga ta tarar da shi zaune a bakin gado daga shi zai Singlet da dogon wandon jan shaddar da ya cire, yana latsa wayan da ke hannun sa

"Wato idan har ba ni na kira ki ba Wifey baza ki iya barin mutane ki zo waje na ba? Kin fi son baƙi a kaina ko?"

Tura baki tayi tana isowa wajen sa da cewa, "haba Husband kana da ƙorafi ne kai dai, duka-duka yaushe ka dawo ne? Ka bari ka gani ko bazan zo ɗin ba, sannan ma ai bazai yiwu in bar baƙi in zo wajen ka ba sai su ce na wulaƙanta su."

Jinjina kansa yayi har yanzu idanunsa a kanta yace, "ok Baƙi sun fi Ni hakan kike son faɗa min? To yayi miki kyau; yanzu me ya kawo ki? ki koma wajen su mana." Sai ya tashi yana ajiye wayan sa fuska babu walwala ya nufi hanyar Toilet

Ita kuma sororo tayi a wajen tana bin bayan sa har ya shige, sai ta taɓe baki a ranta tace, "ka cika ƙorafi my Husband, ya za'a yi in bar baƙi saboda kawai in kula da kai bayan muna tare koyaushe? Ni bazan tsaya ba wlh ai kasan inda komi yake a gidan." Sai ta juya kawai ta fice ta koma wajen su Hauwa

Shi kuwa fitowar sa da rashin tarar da ita hakan sai ya ɓata masa rai ainun, ya kula Munira tana da taurin kai sosai a zaman nan nasu, ko kaɗan idan yayi mata magana sai abun da ta ga dama take yi, musamman yanda take son hulɗa da mutane shiyasa har maƙota sun soma zamar mishi da gida wajen zuwa, to abun da ke ba shi haushi yanda take ƙyale shi ba ta ba shi kulawa take fifita baƙin ta a kan shi, sai dai sun tafi ne hankalin ta ke dawowa wajen sa, kuma koda yayi mata magana a kai baza ta gyara ba a ganin ta ita bata yi mishi laifi ba, wai, "ai babu kyau wulaƙanta wanda ya damu da kai, mutane sun taso sun zo wajen su amma ta ƙyale su ta je wajen sa tana kula da shi kamar wani wanda be san komi a gidan ba; dole sai ita ce zata yi masa jagora". To irin waɗannan maganganun nata ne suke ɓata masa rai da ita, sai dai kasancewar sa me haƙuri yana iya bakin ƙoƙarin sa wajen ya ga ya fahimtar da ita but ta kasa gane wa, ita mu'amalar ta me kyau kawai a wajen jama'a ne, idan kuma a wajen sa ne abu mara sa daɗi su suke faruwa. Yanzu ga shi yunwa yake ji but ta bar shi bata san ta kawo mishi abinci ba, dole da ya gaji ya fita falon, a nan ne yake ce mata, "ta kawo mishi abincin sa ɗaki."

Shi ne dalilin da yasa ta tashi ta wuce ta haɗa masa ta kai masa

Hauwa duk sai ta ji babu daɗi a ranta, a ɗan nazartan da tayi da kuma kaifin tunanin ta ta gane Munira irin Matan nan ne da basu bai wa Miji muhimmanci, abun da ke gaban su shi ne me muhimmanci. Shiyasa ta ga ya dace tayi mata magana, sai dai kuma kasancewar ba ita kaɗai bace sai ta kasa mata ɗin sabida tana so tayi mata zancen ne daga ita sai ita. Koda suka tashi tafiya sai ta ce mata, "ta bata Numban wayan ta zasu riƙa gaisawa."

Itama Sauda nan da nan ta kwanto nata a gefen zani tana cewa, "ai nima bani Numban naki mu riƙa gaisawa, ai baza ayi zumuncin babu Ni ba mun rigada mun zama ɗaya."

Haka ta saka musu Numban kafin suka yi mata sallama zasu tafi, inda ta bi su da alkhairai kala-kala don har kayan kwalliya na cikin akwatin ta sai da ta ɗiban musu, kasancewar ta akwai aukin kyauta.



Koda suka tafi ɗaki ta wuce ta tarar da Muhseen zaune yana latsa waya ya tasa abincin a gaba

Duk yunwan da yake ji cokali uku kaɗai ya ci ya mayar da hankalin sa kan wayan sa, Mutum ne shi me son kulawa shiyasa rashin mayar da hankalin Munira a kansa yasa ya ji duk abincin ya gundure sa

"Wai baka ci abincin ba?" Tafaɗa tana kallon sa bayan da ta zauna a gefen sa

Kallo ɗaya kawai yayi mata ya maida hankalin sa a kan wayan ya ci gaba da latsawa

"Husband Ina magana kayi shiru?"

"Me zance miki?" Yafaɗa ba tare da ya kalle ta ba kuma be fasa abin da yake yi ba

Tura baki tayi da saka hannu ta zare wayan tana cewa, "to ya zan kawo maka abinci ka tasa a gaba ka ƙi ci bayan don kai nayi?"

"Really? Don Ni kika yi abincin?"

"Eh mana."

"Oh! ai ban sani ba, nayi tunanin don baƙin ki ne."

Jin hakan yasa ta gane fushi yake yi, sai tayi murmushi kawai tana shige masa jiki

Shi kuma hannu yasa ya janye ta da faɗin, "don Allah ki ƙyale Ni ba na son takura."

Baki ta saki tana kallon sa cike da mamaki, ganin zai tashi sai ta kama mishi hannu da faɗin, "wai don Allah me nayi maka?"

Ido ya tsira mata cike da haushi, har yanzu ita bata san me tayi masa ba saboda ba ta ganin kanta a me laifi. Shiyasa yace mata, "babu komi kawai ina son hutawa ne." Ya ƙwace hannun sa ya wuce kan gado

Ita kuma sai ta kalli abincin kafin ta ɗauka da cewa, "to yanzu ka gama in kawar da abincin?"

"Eh." Ya amsa ta a taƙaice

Haka ta fice da abincin ko a jikin ta. Tana kichen ne ta ji ana mata Nocking, hakan yasa ta wuce ta buɗe

Maƙociyar su ne, wai, "ta zo ta ara mata rariya nata ya ɓarke tana so tayi tankaɗen garin tuwo."

Da fara'a tace mata, "to ta shigo ciki mana."

Ƙarshe da matar suka zauna suna ta surutu kafin ta bata rariyan suka yi sallama. Har an kira magriba haka ta wuce a gurguje ta ɗaura musu girki kafin ta je ɗaki yin Sallah tunda har an kira

Muhseen ma sai a lokacin ya fito ɗaure da alwalan sa, be ce mata komi ba ya fice domin duk zancen nasu da suke yi da maƙociyar tasu yana ji har tafiyan nata.



Wannan abubuwan da ke faruwa ne ya soma kawo matsala a tsakanin zamantakewar nasu. Duka-duka auren nasu be fi sati biyu ba amma har sun soma fuskantar matsala. Shi Muhseen me son kulawa ne ga Matar sa, ita kuma ba ta girmama zaman su ba ta ba shi muhimmanci ko kaɗan, ga yawan tara masa jama'a a gida tunda kowa nata ne, ta kance, "ka zama na jama'a shi ne za'a so ka," har ƙannin sa yanda take janyo su a jiki shiyasa koyaushe suna gidan, idan ma basu zo ba ita zata saka Hijab ta je can gidan, abinci kuma duk idan ta yi tana hanyar kai musu, ko kuma ta kira su Amina su zo su amsa, shiyasa suke matuƙar ƙaunarta suna ganin Muhseen yayi Sa'a da dace wajen samun Mata, tuni ta siye zuciyar dangin sa kowa yace, "Munira... Munira". Kowa son ta yake Yi

Muhseen duk haƙurin sa shi dai har ya fara gajiya da halin ta, kullum yana faman mata ƙorafi da nuna mata abun da yake so tayi masa. Shiyasa koyaushe a faɗa suke yi, ga shi ba ta raga masa a matsayin sa na Mijin ta, duk idan ya faɗa sai ta faɗa tunda akwai ta da baki. Ya rasa ya zai yi da ita bare ya canza ta, kuma be son Kai ƙarar ta wajen Umman sa tunda kullum nuna mishi suke yi tana da halin kirki, sannan kuma tana ba shi umarnin, "ya riƙe ta amana kar ya musguna mata ko kaɗan, Munira Macen so ne". Ya rasa ya zai yi shiyasa be faɗa wa kowa ba


Ko Anwar Abokin sa da ya fara ganin ya sanja ya tambaye shi, "me ke faruwa?" but ya kasa sanar mishi



Haka suke zaman ga shi har suna neman zurma wata ɗaya.
[16/09, 7:38 pm] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*










*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*PAGE:10*

_____Yanzu haka Anwar ya samu aiki a wajen aikin su Muhseen, komi yanzu ya soma zama musu dai-dai tunda albashi me tsoka ake ba shi, duniya ta soma zama musu sabuwa, a cikin wata biyu sun wadata kansu da komi babu abinda suke nema su rasa sai ma dai su taimaka ma wasu


Sauda kuwa tuni ta saka wa kanta rigima kullum faɗa suke yi da Bilal wai, "shi ya kasa ya nema sai dai zaman banza, ga su nan kullum a wahale har su Anwar sun fi su samu yanzu, shima idan be tashi tsaye ya nema aiki me kyau ba sai dai su rabu." Rigima kala-kala dai Sauda ta saka wa kanta, tana ganin su Hauwa sun fi su samu bayan kuma ba wai Anwar ɗin ya fi Mijin ta karatu bane

Mamaki sosai Hauwa take yi da halin Sauda ɗin, da kuma yanda take nuna wa a kan ƙaruwar da suka yi da yanda ta tashi hankalin ta duk a kai, shiyasa ta yiwa Anwar magana, "ko za'a dace a samar wa Bilal ɗin aiki shima?"

Tsaki ya ja yace, "ke dai za ki kashe kanki idan kika biye ta wannan Matar, ki bar ta da rigimar ta don Allah."

"A'a Mijina don Allah ka taimaka idan har zasu samu aikin nan, Ni wlh tausayi suke bani bare ka ga suna da yara babu wani aikin kama siyar da shima yake yi, tunda shima yana da kwalin sa a hannu ka shige masa gaba mana koda Muhseen ne ka tambaya shi ya sama mishi, idan ka taimakawa wani shi ne naka."

Numfashi kawai ya ja yana kallon ta, sai kuma yace, "Hauwa'u na, ke dai halin ki daban ne wlh, insha Allahu abun da kika ce za'a yi zan nemi Bilal ɗin da zancen, Allah ya shige mana gaba."

"Amin Mijina, na gode da ka fahimce ni." Tafaɗa tana murmushin farin ciki.



To daga ranan ne Anwar ya yiwa Bilal magana don ya ba shi takardun sa ko za'a dace. Ana dai ta neman masa but ba'a dace ba har yanzu

Da sannu rayuwa ta ci gaba da gudana ga shi har Anwar ya siya fili ya soma gini

Murna a wajen Hauwa ba'a magana, ga shi burin su zai cika Allah ya wadata su har zasu mallaki gidan kan su, yanzu sun fi ƙarfin wasu abubuwan buƙata komi suna da shi, haihuwa ce dai har yanzu Allah be basu ba kuma suna ta roƙon Allah. Ita Hauwa ta soma tada hankalin ta kasancewar taji shiru babu zancen haihuwar, tunda ga shi sun samu wadata shiyasa ta dami Anwar ɗin, "su je asibiti a duba su."

Shi kuwa ko kaɗan ba ya damuwa tunda a ganin sa Allah ne be basu ba, idan ma ita ce me matsalar ai yana da shirin sake aure Allah zai ba shi ko ta wajen Afnan ne. Yanda ya ƙi ɗaukar maganar nata da muhimmanci ne yasa ta tayar da hankali. Dole ya ɗauke ta suka soma zuwa asibiti. Sai dai an bincika babu me matsala a cikin su

Dalilin da yasa Hauwa ta samu nutsuwa kenan. Amma dai tana a cikin damuwa domin gani take yi wata rana dole Anwar zai nuna damuwar sa a kan maganar, duk da dai har yanzu dangin sa basu sako ta a gaba ba tunda suna ƙaunar ta, ko kaɗan basu sanja mata ba har yanzu. Amma tana gudun wata rana a lokacin da Anwar zai juya mata baya ko yace mata, "zai yo mata kishiya." Ba wai kishiyar take gudu ba amma ba ta son wata matsala ta shiga tsakanin su, ta sanadiyar haka kuma wata tazo ta raba su.










✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


Fannin su Jamal kuwa babu zaman lafiya yanzu tsakanin sa da Fauziyya, tunda ya gane ba ta ƙaunar zaman mahaifiyarsa a gidan shima ya dena sakin mata fuska. Zuwa yanzu har yaji tayi sabida fitinan da suke yi a kodayaushe, ga shi ya hana Hafsah yin musu bauta shiyasa duk ta ɗaga hankalin ta. Koda ta tafi ɗin be je yayi bikon ta ba a cewar sa, "ita zata gaji ta dawo da kanta."

Sai dai Mama ta saka shi dole ya je ya dawo da ita ba a son ransa ba

Amma hakan ita ko a jikinta be sa tana jin zata iya barin Mama ta zauna mata a gida ba. Dawowar ta sai ta tsurfo abubuwa kala-kala tunda ta je gida an zigo ta, babu irin shawaran da ƴan uwanta da ƙawayen ta basu bata ba, a cewar su, "idan tayi sake da uwar Miji ƙarshe ita ce zata yi kuka a nan gaba, Uwar Miji ba abar so bane, duk yanda za'a yi ta tayar da husuma dole idan yana son ta zai bi abun da take so." Shiyasa kullum rigima ya ƙi ci ya ƙi cinye wa

Tun Jamal yana biye mata yayi fushi sosai da ita, har dai ya haƙura ya zura mata idanu duk da rarrashin da Mama take mishi a kan, "ya bi komi a sannu, wata rana sai labari, yanzu suna da Yara a gaban su be kamata ace wani abu ya haɗa su da zai saka su rabu ba." Hakan yasa yake ƙyale ta take yin duk abin da ta ga dama

Idan ba ya nan sai ta je har Part ɗin su Maman ta kira Hafsan ta saka ta aiki. Shiyasa yanzu Hafsan ita take musu komi sabida rashin idon Jamal

Mama takan ce, "ta je tayi musu tunda ba raguwa tayi ba," kuma ita take hana ta faɗan ma Jamal ɗin ko da ya tambaye ta, "idan Akwai abun da suke mata mara daɗi."

Shiyasa itama Hafsan ta ƙi sanar da shi komi tunda Mama ta ja mata kunne sosai. Idan yana nan ne kawai take samun salama a gidan, ga wulaƙancin da su Intisar suke mata kala-kala na cin kashi, amma haka take shanye wa tunda bata da yanda zata yi, tana son tayi karatu shiyasa take son zaman ta a birni, ba don haka ba da tuni ta saka Mama ta mayar da ita ƙauyen su tunda a nan wahala take sha


Bare yanzu da Jamal ɗin yana yawan tafiye-tafiye shiyasa Fauziyya take rashin mutuncin ta yanda ranta ke so, ƙiri-ƙiri take zuwa har wajen Maman ta karta mata rashin mutunci, zagin ta ne kaɗai ba ta yi duk da zigin ƴan uwa, wanda a ceWar su, "idan tana mata haka dole ita zata ji haushi da ƙafafuwanta zata nemi Jamal ya mayar da ita ƙauye."

Sai dai ita Mama me haƙuri ne tana shanye duk abun da Fauziyya zata yi mata, a ganin ta baza ta shiga tsakanin ɗanta da Matar sa ba, duk da abun na mata ciwo matuƙa, sai dai kuma tana yiwa Fauziyya uzuri duk a dalilin ta na cewa, "wata rana zata sauya, zata gane gaskiya."

Ta kai ta kawo har Hafsah kuka take yi saboda abun da Fauziyya take yiwa Mama da cin kashin da take mata, tamkar ba uwar Mijin ta ba, takan ce, "meyasa Inna baza ki sanar wa Dady ya ɗauki mataki ba? Idan ke baza ki iya ba ki bar ni in faɗa mishi, abun da take miki yana yawa sai kace ita bata da Uwa? Don Allah Inna idan har hakan zata ci gaba da miki Ni na haƙura da karatun mu koma ƙauye tunda duk sabida Ni kike zaune a nan ɗin."

Murmushi Mama tayi da cewa, "har yanzu ke yarinya ce Hafsah, Ni na ɗauki Fauziyya tamkar mahaifiyarki ce, basu da bambanci shiyasa ba na son na shiga tsakanin ta da Mijin ta, idan abun da take yi na gari ne zata gani a ƙwaryan ta, amma Ni zama na a nan ba yana nufin zan shiga tsakanin su bane, akwai yara a tsakani ba na son ace yaran su sun tashi babu Uwa, na san wata rana komi zai wuce."

Idan Hafsah ta ji wannnan zancen na Mama sai ta koma ɗaka tayi ta kuka tana tur da halin Fauziyya, sam bata da kirki bata da mutunci, duk yanda Mama ta kai da son zaman lafiya amma ita ta kasa gane wa. Ta koya wa yaran ta rashin kunya kala-kala ko kaɗan ba sa ganin girman Mama

Duk da Jamal ya ja musu kunne, "su riƙa zuwa suna gaishe ta." But sun ƙi, sai idan yana nan ne suke zuwa su gaishe ta ba don ransu ya so ba.



To haka zaman nasu yake ta ci gaba a haka. Izuwa yanzu Intisar soyayyarta da saurayin ta Shureim yayi tsamari, yanzu har gida take kawo shi suke yin zancen su tunda Jamal ba ya zama sosai, ya kan yi tafiya yayi kwana biyar zuwa sama. Shiyasa yanzu take cin karen ta babu babbaka tunda da ɗaurin gindin uwar ta, har ma Parlour ake ware musu idan ya zo su sha soyayyarsu

To da haka ne fa aka soma samun matsala, kasancewar Shureim Mutum ne me son aji daɗi, wayayye ne shi sosai ya san kan harkan duniya. Da sannu-sannu ya soma jan ra'ayin ta ta soma biye masa suna irin soyayyar nan na shan minti irin na zamani da ƴan mata da samari suke yi; wanda suke ganin shi ne wayewa a halin yanzu. Idan ya zo gidan koyaushe sai sun gama sheƙe ayan su kafin yake tafiya, shiyasa kodayaushe yana kan hanyar zuwa ne wai, "ya zo taɗi." Kuɗi kuwa ko me take so kashe mata yake yi, ya bata kuɗi ya bai wa ƴan uwanta, ya siyan musu duk abin da suke so, har Fauziyya itama tana samu daga wurin sa shiyasa take ƙara zuga Intisar ɗin a kan, "ta kama shi ta riƙe shi gam domin Shureim irin Mazan nan ne da ake so a halin yanzu, idan tayi wasa ta biye wa Dadyn su a kan, "ba yanzu zai musu aure ba" zata rasa shi ne a banza a hofi. Idan yaso idan ta riƙe shi duk sanda suka tashi aure tana da dahir ɗin ta". Wannan yasa Intisar ta sake sakin jiki sosai dashi duk abin da yake so tana mishi, ga zigin mahaifiyarta ga daɗin bakin Shureim ɗin. Shiyasa yanzu har Party take raka shi, babu abun da ba sa yi a halin yanzu illa kawai kusantan juna ne da be taɓa yi da ita ba, shima yana da burin yi tunda a ganin sa ai shi zai aure ta. Yana matuƙar son ta kuma ba ya son ya rasa ta, a ganin sa kafin lokacin auren nasu ai zasu rage zafi ne, ya san Intisar yarinya ce kuma ya san mahaifinta bazai taɓa mata aure yanzu ba, ita kanta Intisar ɗin tana yawan faɗa masa, "burin mahaifin su suyi karatu me zurfi." Shiyasa da ya hure mata kunne a cewar sa, "wannan hanyar ne kaɗai wanda zai saka su ji daɗi har su manta da yawan shekarun da ke gaban su na jiran ranan da zasu mallaki juna, idan suna rage zafi da haka ranan da zasu yi aure zai zo musu da sauri".


Sai dai sanda asirin nasu zai tonu basu taɓa tunani ba. Kwatsam Jamal ya dawo daga tafiyan da yayi na kwana biyu wanda shi ya tafi ne a kan, "zai yi five days". Sai ga shi baka-tatan ya diro gida, kuma a motan haya ya dawo sabida yana sauri ya ɗauki documents ɗin da ya manta da su ya koma. Sai ya shigo parlour'n ya tarar da su a wannan halin suna romance ɗin junan su. Intisar na jikin Shureim bakunan su a haɗe sai matsa ta yake yi, ga kayan jikinta dasu da babu duk ɗaya

A lokacin babu Fauziyya domin ta tafi gantalin ta da ta saba zuwa gidajen ƙawayen ta

Su kuma su Sumayya suna school kasancewar ranan talata ne

But ita Intisar ta ƙi zuwa domin dama ba ƙaunar makarantar take yi ba. Shiyasa Fauziyya ba ta takura mata muddin tace, "baza taje ba."

Mugun ganin da Jamal yayi musu yasa shi tashin hankali ba kaɗan ba. Ya kasa yarda ƴar shi ita ce take wannan baɗalan a kuma gidan shi. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Bazan iya misalta muku a halin da ya tsinci kansa ba. Har kuka sai da yayi sabida baƙin ciki, yayinda a ranan sai da ya yiwa Intisar mugun dukan da sai da aka kwantar da ita a asibiti, kwana biyu curr bata iya farfaɗo wa ba, sabida dukan da yayi mata ko maƙiyin ta sai ya tausaya mata, ya sauya mata kamanni ta yanda idan aka ganta baza a iya shaida ta ba

Tsiya raga-raga aka yi a wannan gidan. Inda har sai da ya kai ga ya saki Fauziyya saboda abun da ya faru, yayi tur da ita kasancewar ta Matar shi kuma uwar ƴaƴan shi wacce ta ɓata masa tarbiyyar Yara. Yanda ya ɗauki fushi ba don akwai Mama a tsakani ba da abun bazai yi kyau ba. Ita take ta tausan shi har ya sauko, tace mishi, "ya ɗau haƙuri ya fauwalawa Allah, tunda Allah ya nuna masa halin da ɗiyar sa take ciki yayi mata aure domin guje wa wannan baɗalan". Dalilin da yasa Jamal ya yarda kenan ya saka Intisar ɗin ta kira mishi Shureim


Shureim ya zo gidan a cikin tashin hankali tare da kunyar haɗa ido da Jamal

Sai dai shi Jamal be ce mishi komi a kan zancen ba illa ba shi umarni da yayi a kan, "ya turo iyayen sa."

Shi kansa Shureim be yi zaton hakan ba, amma kuma ya ji daɗi sosai hakan yasa ya koma gida jiki na rawa ya sanar wa

Please Login or Register in order to submit comment