Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita in ba dai sun fito ba."

"Kawo min nan kawai in ci."

"Ok." Ta amsa tana tashi daƙyar ta fita, bata jima ba ta dawo mishi da abincin a saman tray ta zuba a coolers masu kyau, sai da ta zuba masa a plate sannan ta saka mishi spoon, sai ta koma ta ɗauko mishi ruwa tana kawo mishi, bayan ta zauna take cewa, "wai ya maganar da muka yi da kai ne? Ko yanzu sai da Inna Rakiya ta kira Ni tace in ƙara tuna maka."

Ɗago kai yayi ya kalle ta yace, "wanne maganar kenan?"

Sai ta tura baki kaɗan tana cewa, "wai meyasa kake da mantuwa ne? Ka manta maganar da muka yi da kai jiya ne; na komawa ta gida?"

Fuskarsa ne ta ɗan canza kaɗan, sai da ya gama tauna abincin da ke bakin sa sannan yace, "kinga wannan maganar fa ba na sonta gaskiya, bazan bari ki tafi wani gida yin wanka ba, dama ace ke kaɗai ce; but akwai Hauwa balle ace wata matsalar ce ake gudun ta faru, gaskiya bazan iya jure tun yanzu ki tafi gidan ku and sannan sai bayan kin yi arba'in ki dawo ba."

Cike da shagwaɓa tace, "kai don Allah Mijina, to wai me zan yi maka in na zauna? Ba fa Ni kadai bace a wurin ka bare ka ce zaka damu, kuma na ga ba wata matsalar bace haka, kamar yau ne zaka ga na dawo, wlh in na faɗa ma Inna Rakiya faɗa zata yi min don baza ta amince ba; since wannan al'adar mu ce dole yarinya ta koma gida ta haihu a can, after arba'in ta dawo."

Tsare ta yayi da ido yace, "to Ni ba dani ba, ba na so kuma baza a yi min a gidana ba, ki bar zancen kawai in baza ki iya faɗa mata ba, Ni in ta tare Ni ta sanar min zan faɗa mata gaskiyar abin da ke raina."

Hmm kawai tace tayi shiru sabida har ranta bata ji dad'i ba, tunda wannan al'adar su ne sun saba haka, kuma ta san tabbas akwai matsala in har Anwar bai amince ba, su ma dangin ta baza su bar maganar ba, to yanzu taya ya zata shawo kansa? Dole ne ta san abun yi, dole zata ci gaba da jarabawa ko zai amince mata, don itama zata fi so ta koma gida a yanzu.
***



        Hauwa suna can tare da Sauda cikin ɗakin ta; har sun shantake suna hira, Sauda sai rattafa mata zance take yi, bata san ma Anwar ya dawo ba, sai can daga baya ne Sauda take sanar mata, "ai sun haɗu dashi yana ta mata wani gani-gani har da haɗe fuska, itama ta share shi tayi banza dashi ta shigo ciki."

"Wai kina nufin Anwar ya dawo ne?"

"Eh ya dawo, tare muka shigo ai."

Ɗankwalin ta ta ɗauka tana ɗaura wa a kanta tare da mike wa tace, "bari in zo to."
Fita tayi ta nufi ɗakin sa tunda bata ganshi a falo ba, sallama tayi ta shiga sabida ta ji maganganun su su biyu da Afnan ne, sai da suka amsa mata ta shiga ciki, ta ƙarisa kusa da su tana mishi sannu da zuwa, tare da furta, "wlh ban san ma ka shigo ba, ashe ka dawo?"

Afnan tace, "nima kinga na manta ban sanar miki ba wlh, mun shiga ciki Aunty Sauda ta ɗauke min hankali."

"Haka ne, nima yanzu ta faɗa min." Sai ta samu wuri a saman drowan gadon tana zama

Anwar yace, "wai mene wannan Matar take zuwa yi a gidan nan? Ashe har yanzu ba ki rabu da ita kamar yanda nace miki ba? Kin san ta fa akwai neman rigima, Hauwa na raba ku fa, meyasa har yanzu kike ci gaba da hulɗa da ita?"

Jin zancen nasa sai Afnan ta lallaɓa ta miƙe ta fita ta basu wuri tunda ta ga ba maganar ta bane; musamman yanda ta ga Anwar ɗin yana magana a ɗan zafafe

Hauwa da ke kallonsa cike da damuwa tace, "don Allah ka yi haƙuri, ka san babu yanda za a yi in hana ta zuwa ko in fitar da ita daga rayuwata, mun saba, kuma tunda nake da Sauda bamu taɓa sa'insa da ita ba sai wancan karon, ya kamata ka yi mata uzuri."

"Oh! Wato kina nufin dole dai sai kin ci gaba da alaƙa da ita?"

Shiru tayi tana sauke kanta ƙasa

"Shikenan, Ni dai duk abun da ya biyo baya ke da ita ce, babu ruwana tunda baza a faɗa miki magana ki ji ba, kin fi Ni sanin Matar nan rigimammiya ce, yanzu har nan ta biyo ki don ku ci gaba da hulɗa; daga nan kuma ta shiga tsakanin ku da Afnan ta hana ku zaman lafiya tana muku gulmace-gulmace."

Hauwa kallonsa tayi da mamakin sa, jikinta yayi sanyi sosai, to bata san me zata ce ma Sauda su rabu ba, kuma ta ga kamar Anwar ya dauki zafi da ita; sannan ga irin fassaran da yake mata, duk da ta san Sauda akwai rigima amma sai idan ka taɓo ta ne, kuma gulman da yake magana a kai taya ya zata shiga tsakanin su bayan tana da hankalin ta? "Kayi haƙuri don Allah tunda na ga kamar ka ɗauki zafi, ban san me zan cewa Sauda ta dena bibiyana ba, kuma zata yi min wata fassara daban ne, babu daɗi a ce in tunkare ta in faɗa mata wannan maganar, amma in kai zaka iya shikenan tunda gidan ka ne ai."

Shiru yayi bai ce mata komai ba sai zura abincin sa yake yi, shiyasa ɗakin yayi shiru

While Hauwa sai ta miƙe tace, "bari in je."

Kai ya gyaɗa mata kawai, hakan ne yasa ta fice tana tunanin mafita, don ta ga kamar yana son ɗaukar zafi da ita, ita kuma bata ga abun matsala ba a nan in ba dai neman rigima yake ji ba, in fact ma ita Saudan ta jima rabon da tazo gidan nan, har ga Allah baza ta iya koran ta a jikinta ba, amma tunda gidan sa ne ai yana da right da zai iya tunkaran ta yayi mata iyaka da gidan. Kitchen ta je ta ɗibo mata abinci tare da drink ta kai mata. Tunda ta shiga dakin ma bata fito ba har Anwar ɗin ya tafi, tana can tare da Sauda tana shan labari wurin ta, daga baya Afnan ta shigo suka ɗaura da ita ana ta raha.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


               Duk yanda Fauziyya ta so ta samu galaba a kan Jamal; Allah bai bata iko ba, domin ko a daren ranan da tayi amfani da maganin da Malam ya bata, ƙarshe bata samu biyan buƙata wurin Jamal ba duk yanda ta so. Baƙin ciki kamar ya kashe ta, ta dai samu nasarar zuba mishi maganin a abinci kuma ya ci

Da safe kuma da duku-duku ya bar gidan ko breakfast bai samu yayi ba saboda kiran da aka yi masa na gaggawa. Duk yanda Allah yaso ya kare ka; duk wani sharrin da za a bi ka dashi, insha Allahu Allah bazai taɓa bada damar a ci galaba a kan Mutum ba, to bare Jamal da addu'ar Uwa a tare da shi, babu dare babu rana tana masa addu'ar kariya ga duk mai bin sa da sharri, kuma shima yana yi tunda mutum ne mai yawan zikiri, shiyasa ba komai yake tasiri a jikinsa ba, da zaran magani ya ci sa sai kuma ya sake sa, ba don haka ba da tuni Fauziyya ta jima da cin galaba a kansa a kan magane-maganen da take masa, ko ya ci sa ba ya wani tasiri sosai a jikinsa zai karye

Kwana biyu zai yi a tafiyar nasa, kuma har ya tafi bai san cewa auren ƴarsa ya mutu ba. Sai da ya dawo ya tarar da ita da mamakin zamanta a gidan, kasancewar ya san tun a ranan da ya tafi Fauziyya tace mishi, "an sallame ta."
Shi yasa da ya dawo yake tambayar, "me take masa a gida bata koma gidan Mijinta ba?"

Fauziyya ta kalailaye shi tana faɗa masa, "Mijin ne yace ta dawo nan tunda jikinta babu daɗi sosai, shiyasa yace ta dawo nan ko za a fi kula wa da ita."

Shiru yayi, sai kuma ya tafi ya ɗauko wayansa yana kiran numban Shureim

Fauziyya fa ta rikice ta rasa yanda zata yi ta tsayar dashi. Amma ina aikin gama ya riga da ya gama, don tsab Shureim ya sanar masa da abun da ke faruwa har sakin da yayi mata

Wani irin yanayi Jamal ya shiga a wannan lokacin, sabida yanda ransa ya ɓaci cikin fushi yake cewa Shureim, "amma ko ma mene ne abun da tayi masa bai kamata ya yi wa ƴarsa wannan sakin ba, ya nuna masa bai da wani mutunci da darajar da ko don shi zai iya yafe mata, tunda har ya iya wulaƙanta masa ƴa yayi mata saki a wannan ƙanƙantar shekarun nata, yayi masa kyau ya gode matuƙa."
Sai ya kashe wayan yana duban Fauziyya da hankalin ta yayi ƙololuwar tashi; zufa duk ya keto mata sai rawan jiki take yi, zata yi magana ya daka mata tsawa yace, "ai kin san me zai biyo baya dama, yanda kika kashe auren ƴarki ke ma naki ya mutu, ki je na sake ki saki ɗaya sai ki haɗa da wancan ɗayan da nayi miki, in kuma a hakan ma ba ki yi hankali ba gobe za ki ƙara aikata abun da kika yi ninya."

Wani irin kururuwa Fauziyya ta saka tare da fashe wa da kuka, ta duƙa ta ƙanƙame mishi riga gam

Idanunsa jazur yake kallonta da nuna ta da yatsa a tsawace yace, "ba dai ba kya jin maganata ba? kina kallona soloɓiyo duk abun da nake faɗa bazan aikata ba kawai furta wa nake yi; wlh kin ji na rantse miki idan ba ki tattara kin bar min gida ba a ƙalilan lokacin nan, wlh sai na datse sauran igiyar da ya rage, in kin je ki samu wani Mijin ki yi aure sabida ƙarshen iyakanki, kin kaini bango Fauziyya, na gaji da halin ki, ke ma kinga sai ki huta da fitinan Uwar Miji, ki je ki auri Mijin da baida Uwa bare a takura miki."
Ya buga rigansa ya wuce ya shige toilet ya rufo ƙofan. Ko kaɗan bai ji tausayin yanda take kuka da magiya ba, taurin kanta yayi mata magani yanzu, gwara ya rabu da ita ya huta kawai tunda baza ta taɓa canza wa ba

Inda Fauziyya kuka ta dinga rusa wa ta ƙi tashi a wurin,
Yaranta suna ji daga Falo amma babu damar shigowa tunda a cikin ɗakin Dadyn su ne,
Sai Intisar ne da ta shiga cikin daki ta rufe kofan tana nata kukan da tunanin dukan da zata sha a wurin Dadyn

Sai da Jamal yayi mata wuta-wuta ya nuna mata zai ɗauki mummunar mataki a kanta in har bata bar mishi gida ba. Daƙyar ta haɗa kayanta a ɗan akwati ta fice zuciyarta na tafarfasa da dana-sani, yanzu ta kashe auren ta; wanda har ga Allah ba ta jin zata iya ci gaba da Rayuwa babu Jamal, komai ta ɗaura a kan Mama ne, sabida gani take yi ita ce silan komai, tun zuwanta gidan su suka soma samun saɓani da Jamal, kuma duk yanda aka yi ita ta shiga tsakanin su, kuma wlh ta ɗauki alwashin baza ta taɓa ƙyale ta ba, sai ta dauki mataki

Su Sumayya sai kuka suke yi ganin yanda Jamal ya yiwa Fauziyya koron kare, tsoro ya hana su bi ta sai shigewa ɗaki suka yi kowa yayi jugum suna alhinin abun da ke faruwa, yau kamar a mafarki mahaifinsu ya rabu da mahaifiyar su

Shi kuwa bai bi ta kan Intisar ba ko sau ɗaya,
Kyale ta yayi bai kula ta ba, har ta fitar da ran zai ɗauki mataki a kanta. Sai a washe gari ya saka ta ta haɗo kayanta dukka a akwati, jiki na rawa tayi abun da yace. Ya saka ta takai kayan Mota yace, "ta shiga ciki."
Babu musu ta shige ya ja Motan sai ƙauyen su Hafsah ya kaita gidan su

Umma Salamatu tayi murnan ganinsa, musamman da ta ga har da Intisar, bayan ta tarbe su da abun sha ta zauna suka sake gaisa wa tare da tambayar su Hafsah da Mama?

Yace, "Alhamdulillah Salamatu, basu san ma na zo ba, sai na koma zan faɗa musu, ga ta nan Intisar na kawo zata zauna a nan, don haka ba wai na kawo ta bane don ta ji daɗi a zaman ta a nan ba, hukuncin da zan iya mata kenan tunda ta kashe auren ta, Salamatu ina son ki hora min ita kowanne aiki ki riƙa saka ta, tunda ta zaɓi bijire min ta bi turban Uwarta; don haka zaman ƙauye ya dace da ke, babu tausayi babu sassauci so nake yi ki gyara min ita ta shiga taitayin ta, duk wani ayyukan gida da kika san ya kamata ɗiya Mace ta koya ki riƙa saka ta, wannan alfarman kawai nake bukata Salma; in har kin min haka kin biya Ni."
Ya ƙare maganar da daka wa Intisar ɗin tsawa ganin ta kure musu kunne da kukan ta

Dole tayi tsit tana kama bakin ta jikinta sai rawa yake yi

Sosai Umma Salamatu ta tausaya mata, ta kalli Jamal tace, "Yaya wannan hukuncin ai yayi tsauri da yawa, taya ya zata iya rayuwa a nan bayan bata taɓa zaman ƙauye ba?"

"Ai yanzu sai ta koya tunda haka ta fi so, babu inda zata koma wlh a nan zata ci gaba da zama, don haka Ni ba zama zan yi ba zan zo in wuce."
Sai ya ciro kuɗi masu yawa ya bata yana miƙe wa tare da yin mata sallama,
Har waje ta raka sa yana tambayar ta sauran Yaran?,
Tace, "sun je makaranta."
Sun ɗan jima kaɗan a waje yana ƙara jaddada mata, "kar tayi mata wasa ko ta ji tausayin ta, don so yake yi ta gyara ta shiga taitayin ta, babu abun da Fauziyya ta koya musu sai banzan ɗabi'a, don haka so yake yi ta shiga taitayin ta ta canza ta horar da ita komai da ake yi na ƙauye ta riƙa sanya ta babu tausaya wa."

Dariya kawai Umma tayi tace, "shikenan, to Allah ya rufa asiri, muna godiya Allah ya ƙara buɗi, in an je a gaishe da su Mama."

Daga nan sallama suka yi ya hau Motan sa ya wuce. Gidan Mama ya zarce kai tsaye daga nan



Hafsah na ɗaki tana jin zuwan sa tayi muƙus ta ƙi fitowa, sai dai ta kasa kunne tana jin abun da suke cewa gabanta sai faɗi yake yi, yanayin da take shiga daban a yanzu in har zata ji muryan Jamal

Kaf Jamal ya sanar da Mama abun da ke faruwa

Cike da rashin jin daɗi tace, "yanzu ita takwaran nawa auren nata ya mutu kenan? Ashsha! Ban ji daɗin wannan al'amarin ba, kuma bai kamata a ce ka kaita can ƙauye ba tunda ka san bata saba da zaman can ba, zai fi a nemi Mijin a ba shi haƙuri tunda akwai sauran igiyar ta koma ɗakin ta."

"Mama ai bata yi hankali ba kenan in ta koma gidan Mijinta, ki barta a can ta girbi abun da ta shuka, dama bata iya komin ta ba ina neman mai gyara min tarbiyyar ta, idan ta ci gaba da zama a nan Fauziyya baza ta barta ba, can kuwa bata san inda take ba bare ta bibiye ta, kuma nayi mata gargaɗin in har ta sake ta dawo nan wlh sai na mugun saɓa mata."

"Duk da haka Jamaluddin akwai cutar wa a gare ta, amma to su su Sumayyar ya saka yi da su; gida babu kowa? Ko zaka kawo su nan ne su zauna da mu?"

Girgiza kansa yayi yace, "a'a Mama, a can zasu zauna, itama Sumayyar so nake yi ta san abin da ya kamata, ita zata riƙa kula da gidan tana yin girki tunda Mace ce ai; gidan wani zata je, ba sai an kaita ta kasa taɓuka komai ba, ba fa abun da suka iya sai dai su ci su kwanta, yanzu ko dole in canza musu rayuwa tunda na fitar da ita a rayuwata na huta; idan ta samu Miji tayi auren ta wlh ta kaini maƙura."

Mama tace, "Allah ya kyauta gaba, amma insha Allahu za a daidaita ai; tunda akwai Yara a tsakani, Ni dai yanzu bazan tilasta maka ba tunda kai kaɗai ka san halin da kake ciki, amma kuma zaman ka babu Mace bazai yiwu ba ka sani ko? Sumayya baza ta iya kula da gidan nan ita kaɗai ba, ga kuma Jibril duk baza ta iya kula da ku ba, sai dai in baza ka daɗe ba zaka dawo da ita Fauziyyan?"


"Mama Fauziyya fa ta tafi baza ta taɓa dawowa ba, ko zan dawo da ita ba yanzu ba wlh tunda baza ta taɓa hankali ba; baza ta taɓa sauya wa ba."

Jinjina kanta tayi tunda itama shaida ce, amma ya zama dole ta taushe shi ya mayar da ita tunda babu daɗi a ce sun ɗauki tsawon lokaci; rana tsaka Uwar ya'yansa su rabu, itama baza ta so haka ba, don haka sai tace, "to ko Hafsatu zata tare ne? Inyaso abubuwan zasu yi maka sauƙi; da dai ka zauna babu Mata haka nan Jamal."

Daram gaban Hafsah da ke maƙe tana sauraron su ya buga, nan da nan jikinta ya soma rawa tana ƙara kasa kunne don ta ji me zai ce; har gumi ya soma keto mata sai ta ji maganar Jamal ɗin da ya soma dawowa da ita hayyacinta

Yana faɗin, "a'a Mama, ai Hafsah yarinya ce har yanzu, ki barta kawai ta karisa karatunta a tsanake zai fi."

"To ban da abun ka; ai yanzu saura ya rage, tunda ga shi hutun nan zasu shiga ajin ƙarshe, nima abun da na so kenan, amma ka ga bazai yiwu ka yi zama babu Mata ba ko?"

"Mama don Allah a barta ta ƙarisa ɗin zai fi, kar mu shiga haƙƙin ta; in ta ƙarisa sai ta tare Ni zan iya jira koyaushe ne."

"Shikenan tunda ka ce haka, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi."

"Amin ya Allah, tunda na zo ban ji motsin ta ba; ina take?"
      


"Tana ɗaki, tunda ta shiga yin sallan isha'i bata fito ba, ko barci ya ɗauke ta ne ƙila."

Duk da har a ransa yana son ganin ta, amma kuma babu yanda zai yi, sai ya miƙe ya yi wa Maman sallama kasancewar dare ya soma yi,
Tare suka fita da Maman ta rufe Kofar gidan tana dawowa ciki.
[13/01, 9:05 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*






                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:36*

_____Sauda bata fito gidan su Hauwa ba; sai da ta ga an kusa kiran Magriba, sannan suka fito tare da Hauwan har haraban gidan ta rako ta, nan ma sai da Sauda tayi kamar baza ta tafi ba sai rattafa zance take yi, har sun yi sallama kuma ta sake dawowa tana bata labarin sabon gidan su da aka kusa gama wa, har tana cewa, "ai wlh Bilal yayi ƙoƙari, sai kin ga gidan, mu ma Insha Allahu mun kusa barin gidan haya, ke ba ki ga gidan bane, har da ɗakunan Yara daban, komai fa a wadace, kin san ina son Falo babba, ai kuwa ya gwangwaje Ni da Falo ba kaɗan ba, don Ni dai a fahimta ta zai iya kai girman naku."

Dariya Hauwa tayi tace, "oh! Yau wacce rana Sauda tana yabon Bilal?"

"Uhm ke dai bari, ai yayi abun yabon ne, amma kin san me? Ni gani nake yi kamar ɗakunan sun yi yawa, anya ba nan gaba zai ce min aure zai ƙara ba?"

"To ke mene ne abun damuwa in ya ƙara auren? Ai kowa wurin ta daban ba a kanki zata zauna ba in ta zo."

"Billahil lazi Ni bazan yi haƙuri kamar ki ba ke ma kin sani, idan kuwa yace zai kawo min wata gidan nan uhm zai ga ba dai-dai ba, dama ai halin su kenan, ke aka yi wa kishiya bare Ni? Take-taken sa da nake gani kenan; amma sai ya ƙaryata Ni yace min, "yayi daƙunan ne don su ishe mu a wadace, ba ya son ƙuntacaccen gida." Bai san cewa kallonsa nake yi kar ba."

Dariya kawai Hauwa take yi, sai tace, "kinga kar in riƙe ki kiyi dare a hanya, zamu yi magana a waya ki gaishe min da Ruƙayya da su Sulaiman da kyau da kyau."

"To zasu ji, dama anguwan naku abun haushin ba zuwa bane; sai ka fita can bakin titi sannan zaka samu abun hawa, don haka Ni na tafi, sai kuma wani lokacin, amma ya kamata ki kawo mana ziyara har yanzu ba ki ƙara takowa gidan mu ba, su Maman Abashe kullum ƙorafin su kenan har yanzu ba ki ƙara zuwa ba bare a ci gaba da zumunci."

Hauwa numfashi ta ja tana furta, "ke ma kin san halin Anwar, gidan namu ma sau ɗaya na taɓa zuwa, da dare muka je Ni dashi, amma kin san Ni da na zo anguwan babu abun da zai hana Ni zuwa."

"To ai sun ce ba kya son a ci gaba da zumunci ne, zuwan su gidan nan sau biyu, tarewan ki da kawo miki kishiya; ke kuma ba ki je kin musu ban-gajiya ba, kin san su da riƙe abu a rai ga nacin tsiya suyi ta gutsiri tsoma."

Ganin dai hiran Sauda ba ƙare wa zai yi ba, sai tayi mata sallama tana sake jaddada mata, "muddin ta shigo anguwan zata zo; ta basu haƙuri don Allah."
Daga nan suka yi sallama Hauwa ta wuce ciki

While Sauda ta fita gidan tare da ƙunshin leda wacce Hauwan ta bata tsaraban Yara; har da na Ruƙayya itama a kaiwa Safina.
Haka ta dinga bangaza sauri kamar zata tashi sama, sai surutu take yi tana sambatun rashin samun abin hawa, ita kaɗai take masifar ta kamar wani ne yace takai dare har haka, ga shi ta sha wahala sai da tayi tattaki har bakin titi ga nisan tsiya, daƙyar ta samu abun hawa shima sai da suka tsaya suka yi tsada, ta ƙi yarda a kan farashin da yayi mata, haka ta ɓata lokaci wurin ta ga ya yarda da abun da zata ba shi,
Ga shi shima kamar maye; tana ja yana ja sun ƙi daidaitawa, daƙyar dai ya amince mata don ita ta ƙi hawa dole sai yanda tace zata ba shi,
Bayan ta hau ta dinga surutu tana cewa, "haka kawai tsaban fitina irin naku; baku san rayuwa tayi tsada bane? Yanzu mene ne bambancin ɗazu da yanzu da zaka zuƙa kuɗi haka don kawai dare yayi? Wlh ku riƙa yi kuna tsoron Allah wannan zalunci ne tsantsa, a ce har hamsin zaku ƙara don dai baku san halin da mutane suke ciki ba."

"To Hajiya ai mu ma baku san halin da muke ciki ba, kuma in kina maganar mutane har da mu kenan a ciki, Sabida Allah ke ma tsoron Allan ne da ke? Ai kin san abun da ya kamata ya za a yi a ce ki bani tamanin har zuwa nan da sha-tale-tale? Abun Naira ɗari ko da ranan ne ma. Don kawai kin ƙara ashirin shi ne kike kumfar baki?

Please Login or Register in order to submit comment