Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iyayen sa. Dalilin da yasa aka turo kenan aka sanya ranan auren su nan da watanni biyar

Izuwa lokacin kuma Jamal ya hana Intisar fita ko nan da can ne, makarantar ma yace, "ya cire ta, idan ta sake fita be yafe mata ba." Ya ƙuntata mata sosai a gidan wanda ko ruwa idan zata sha sai tayi kuka. Tsatstsauran mataki ya ɗauka a kanta, ga shi ya ƙi dawo da Fauziyya

Sai da Mama ta shiga maganar kafin ya amince ya dawo da ita. Sai dai kuma zaman nasu ya sake taɓarɓarewa tunda yanzu ko sakin fuska ba ya yiwa kowa a gidan, ita kanta Fauziyya tana gwagwatuwa a gidan, kuma yace, "idan baza ta iya ba sai dai ta bar masa gida."

Yanzu ne ta tabbatar Jamal be iya fushi ba, duk tsawon zaman su bata taɓa ganin sa a haka ba sai yanzu, shiyasa yanzu itama ta shiga taitayin ta, duk da a ranta ba ta ƙaunar auren da za'a yiwa ƴar ta amma ta bi yarima ana shan kiɗa da ita. Dole ta tashi tsaye wajen taga ta gyara yarinyan ta

Tunda yanzu gaba ɗaya Intisar ɗin ta fita a hayyacin ta don har baƙin dole tayi, kullum tana ɗaka tana kuka sabida baƙin ciki, har wayanta Jamal duk ya ƙwace ko falo ba ta iya fita koda kuwa babu shi a gidan ne. Ita yanzu burin ta kawai ta ga an yi auren ko zata huta da halin da take ciki, tana ga kamar idan tayi auren shikenan ta fita daga cikin ƙuncin gidan su wanda Dadyn nata ya saka ta, shiyasa a ranta ta ƙosa auren nata yazo.
[22/09, 12:28 pm] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*










*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*PAGE:11*

_____Yau su Hauwa suka wayi gari sun samu Abokiyar zama, an kawo musu wata ƴar hayan, yarinya ce ƙarama don sun girme ta sosai, sunan ta Ruƙayya sai dai ana ce mata Maman Safina kasancewar ta tana da ɗiya guda, auren nasu da Mijin ta Sadis be fi shekara ɗaya ba, domin duka-duka watan Safina ƴar su biyu ne

Kasancewar Sadis Mutum ne me son ƙarya da son rayuwar ƴan gayu, hakan yasa ya zurma Ruƙayya wacce a tunanin su ita da dangin ta me kuɗi ne. Sai da aka yi auren ya kama musu plat ɗin gida a cewar sa, "Gidan shi ne", a lokacin da ya je neman auren ta ya kashe musu kuɗi sosai wanda lokaci ɗaya aka ba shi ita ba tare da wani ƙwaƙƙwaran bincike ba, inda aka yi auren aka gama lafiya. Sai dai kuma tashin farko suka soma samun saɓani da Ruƙayya sabida rashin wadata da ba ta gani a zaman su, abinci ma wannan sai an yi da gaske yake iya kawo musu, daga baya ne suka gane ashe dama ba me kuɗi bane shi yaudaran su yayi tunda ga shi gidan ma da suke ciki haya yake yi, bata gane hakan ba sai da Me gidan ya soma mishi jeka-ka-dawo saboda ya ba shi kuɗin shi, tunda gidan da ya kama hayan ko biya gaba ɗaya be gama yi ba. A nan ne suka soma samun matsala wanda ita Ruƙayya ta tayar da hankalin ta a kan, "sai ya sake ta." But ya ƙi. Daga nan ne ma ya soma nuna mata halin sa na mugunta don har dukan ta yake yi, ga shi ba ya son bata abinci nan da nan Ruƙayya ta soma sauyawa, wahala ta ishe ta har yaji tayi, ƙarshe dai iyayenta su suka dawo da ita tunda me afkuwa ya rigada ya afku ga shi har da rabon ciki. Basu da yanda zasu yi su saka ya sake ta tunda shi ya rantse ya maya, "bazai taɓa sakin ta ba, wahalar da ya sha bazai tafi a banza ba." Dole Ruƙayya ta dawo gidan ta zauna ta ci gaba da zaman haƙuri. Ga shi da biye-biyen Mata har giya yake sha, ta rasa yanda zata yi tun tana iya magana har dai yanzu ya fi ƙarfin ta sai yanda ya juya ta, duk ta gama koɗewa saboda wahala a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Wata tara da kwanaki ta haifi Safina, kuma har a lokacin zaman nasu be sauya zani ba

Lokacin da suka cika shekara ɗaya cif me gidan ya zo yayi musu watsi da kaya tunda har yanzu Sadis ya kasa biyan kuɗin shekaran

Dalilin da yasa suka samu haya a gidan da su Hauwa suke haya; saboda yaron Me gidan shi ya nemi alfarma wajen Hajiyar tashi yace, "ta taimaka ta basu ɗaki, daga baya idan Sadis ɗin ya samu sai ya biyata". Saboda shi tausayi suka ba shi kasancewar a gaban shi aka yi musu watsi da kayan. Dalilin da yasa kenan Hajiya me gidan hayan ta basu ɗaki kenan.

Suna zaune su Hauwan suka ga ana ta shigowa da kaya gidan

Yaron Hajiya shi yayi musu jagora zuwa gidan, sannan ya buɗe musu ɗakin ya ƙara gaba

Ruƙayya na goye da ƴar ta Safina suka shigo. Yayinda Mijin ta ke biye da ita a baya. Sannu Ruƙayya tayi musu sannan suka wuce ɗakin nasu

Sauda sarkin tsegumi sai leƙa kai take yi tana bin su da kallo. Bayan sun shige ne ta kalli Hauwa tace, "to fa! mun sami Abokiyar zama kenan? Amma wannan Mijin nata da alamu ba shi da fara'a don Allah ki duba yanda ya wuce ko ci kanku be ce ba, yana wani ɗaure fuska da wani ƙaton bakin sa baƙinƙirin."

Idanu Hauwa ta zaro tana rufe baki da fadin, "ki rufa mana asiri don Allah Sauda kar su ji mu."

"Yo sun daɗe basu jin ba, da akwai abinda zasu iya ne?"

Hauwa jin hakan yasa ta miƙe da faɗin, "to ni kinga tafiya na, baza ki jawo min zance ya ƙare a kaina ba." Bata jira cewar ta ba ta ɗauki waken ta da take rerayewa ta shige ɗaki

Ita kuma Sauda taɓe baki tayi ta ci gaba da surutan ta. Ko damuwa da zasu ji ta bata yi ba. Tana ganin Sadis ɗin ya fice ta tashi ta burma ɗakin Ruƙayyan tana kwaɗa sallama

Ita kuma ta amsa mata tana kallon ta, tana zaune ne a gefen katifan su tana shayar da Safina wacce ta kwanto ta ta ɗaura ta a jikin ta

Washe baki Sauda tayi da faɗin, "sannun ku da zuwa, ashe mun samu abokan zama ne?"

"Eh." Ruƙayya ta amsa mata tana murmushi

"Masha Allah ai haka ake so, Allah yasa mu amfana da juna. Ya sunan yarinyar?" Ta faɗa tana miƙa hannu ta ƙara da cewa, "kawo ta mu ganta."

Miƙa mata tayi tana cewa, "sunan ta Safina."

Rawa ta soma yin mata tana cewa, "tubarakalla yarinyar ga ta kyakykyawa wlh. Kinga Ni sunana Sauda ne, dama mu biyu muke zama a gidan, ita wacce kika gan mu a waje sunan ta Hauwa. Ina da Yara biyu Sulaiman da Haidar, ita kuma Hauwa Allah be bata haihuwa ba."

"Allah Sarki." Cewar Ruƙayyan tana kallon ta, sai dai ta kula Sauda surutu ne da ita shiyasa kawai take bin ta da ido tana mata murmushi, dayake ita ba gwana bace a kan surutu

Daga ƙarshe ita Saudan ta amshi Safinan wai, "zata riƙe mata ta gama gyara ɗakin."

A lokacin itama Hauwa ta zo sun gaisa cike da mutunta juna

Shiyasa daga ranan ne zaman nasu ya zamana su uku. Kasancewar Ruƙayya bata da matsala shiyasa suke jin dadin zama da ita. Sai dai sun fuskanci halin Mijin nata be da kirki don yana wulaƙanta ta sosai, ga shi ita ba me hayaniya ba shiyasa take shan wahala

Hakan yasa ta soma bai wa Hauwa tausayi, kasancewar ta me kaifin basira da hangen nesa yasa take jan Ruƙayyan a jiki tana bata shawarwarin yanda zata magance matsalar ta. Tabbas Miji irin Sadis akwai babban aiki wajen zama da shi, musamman yanda ta ga Ruƙayyan yarinya ce ƙarama ga shi kuma tana jin tsoron sa sosai

Inda ita Sauda zugata take yi a kan, "ta riƙa cin uban sa, ita bata ga amfanin Miji irin na Ruƙayya ba. Idan da ita ce a cewar ta sai dai su riƙa kwasan ƴan dambe," a cewar ta, "barin shi da Ruƙayyan take yi ne yasa yake mata wannan cin kashin, ita ina zata iya? Shiyasa take zugata ta tashi ta amshi ƴancin kanta."

Hauwa tace, "ai ba ta wannan hanyar ne zata ƙwaci ƴancin ta ba, komai ana bin sa ne a sannu idan shi me shiryuwa ne zai canja wata rana, ta bi komi a hankali da sannu wata rana zai gane amfanin ta a rayuwar shi tunda basu daɗe da auren ba".

To irin waɗannan shawarwarin ne suke bai wa Ruƙayya. Shiyasa itama ta saki jiki sosai da su tunda a ɗan zaman da suka yi duk ta fuskance su, tana kuma iya bakin ƙoƙarin ta wajen ta ga tabi shawaran Hauwa.






Haka rayuwan take tafiya a sannu-sannu, inda yanzu har ginin gidan su Hauwan yayi nisa sosai. Flet biyu yayi da nata da na Afnan da yake shirin aure, yanzu haka har yana shirin kai gaisuwa domin a tsayar da Ranar auren su, sai dai be sanar da Hauwan ba har yanzu yana jira ne idan an tsayar da ranan sai ya faɗa mata, ya san Hauwa bata da matsala shiyasa ko kaɗan be ɗaga hankalin sa ba

Gefe ɗaya kuma suna ta shan soyayyar su shi da Afnan, sai abun da yayi gaba yanzu tunda kowa a familyn ta sun san shi, kuma sun san shi zata aura.






✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

Muhseen shima yanzu ya gama gyaran gidan shi gaba ɗaya. Inda suka koma Part ɗin su yayinda ya dawo da Umman sa da ƙannin sa a inda suka tashi, gida yayi kyau sai son barka, har su Hauwa sun sake zuwa sun yi musu murna tunda yanzu sun zama ƙawaye sosai, kuma suna zumunci don har itama Munira tana zuwa musu

Sai dai zaman su da Muhseen ɗin har yanzu babu daɗi. Abubuwa da yawa sun bi sun yi masa yawa, ya kasa gane kan Munira, ya rasa yanda zai yi ya sauya ta ta koma yanda yake so, ta ƙi ɗaukar auren nasu da muhimmanci ko kaɗan bata ba shi darajar shi a matsayin shi na Mijin ta, bar ta da son zumunci da yiwa mutane hidima amma bata san ta kula da Miji ba. Barin ma yanzu da Umman sa suka dawo gidan sai abun da ya ci gaba, koyaushe tana tare da su don a can part ɗin ma take wuni ta ci abinci a can komi a can take yi, ta zama kamar itama ƴar Umma ce tunda ta mayar da ita kamar mahaifiyar ta. Dayake yanzu tana da ciki shiyasa Umma ke kula da ita tunda tana laulayi me wahala ne, su A'isha suke mata komi ko kuma su haɗu gaba ɗaya su yi

Muhseen duk ya saka damuwa a ransa shiyasa har zurma wa yayi duk ya wani firirice. Tun abun ba ya damun sa yanzu har ya kai da ya sanar wa Anwar

Shi Anwar ɗin ke ba shi shawara da ƙara ba shi haƙuri a kan, "ya ci gaba da haƙuri yana fahimtar da ita, saboda Munira Mace ce me halin ƙwarai."

Ya kance, "ba ya tunanin zata sauya tunda ya rigada ya gane halin ta yanzu." Bare yanzu ɗin idan suna faɗa ko raga masa ba ta Yi, takan haƙiƙance tayi ta masa faɗa kamar wacce ta haife shi. Abun na ba shi mamaki sosai. Shiyasa ya ga ya dace ya sanar wa da Umman sa

Koda ya kai ƙarar ta wajen Umma ta ƙi yarda. Sai ma ce masa tayi, "wato yana so ya tada husuma ne a tsakanin su, idan be gode wa Allah ba ai bazai jife ta da sharri ba, duk yanda Allah yayi masa gata ya ba shi Mata ta gari kamar Munira; me son dangin sa amma yace shi tana ƙuntata masa, to dama ai zaman auren haƙuri ake yi, ya je ya ci gaba da haƙuri su zauna lafiya amma kar ya sake kawo mata ƙarar Munira, domin ita bata ga abin da tayi ba, kuma idan ya ce zai muzguna mata zai ga ɓacin ranta ne."

Muhseen jin zancen mahaifiyar sa hankalin sa ya tashi ainun, ya so ya fahimtar da ita but ta kasa fahimta

ƙaunar da take yiwa Munira yasa ba ta ganin laifin ta ko kaɗan, a ganin ta shi Muhseen ɗin ne ya gaza haƙuri, amma bata ga abun da Munira take mishi ba da zai tashi hankalin shi.

Dole ya haƙura ya je ya ci gaba da danne abun da ke ransa tunda be da yanda zai yi, mahaifiyar sa ta kasa fahimtar sa. Shiyasa da ya ga abun yayi yawa sai ya soma ɗaukan mataki wanda har hakan yasa yace mata, "ta tafi gidan su, idan baza ta canja ba shi bazai iya zama da ita ba."

A ranan kuwa ya ga ɓacin ran Umman sa, ce masa tayi, "yayi maza-maza ya je ya dawo da ita ko ta tsine mishi albarka."

Hankalin sa ya tashi da jin zancen ta, dole ba don ya so ba ya wuce gidan nasu. Sai dai koda ya je ya samu iyayen ta da zancen, "su ja mata kunne, kwata-kwata ba ta ganin girman sa, ta dauki auren su tamkar abun wasa, ba ta mishi biyayya yanda ya kamata, kuma idan yana mata faɗa tana ƙoƙarin rama wa, ga mutane da take tara mishi a gida kala-kala. Ya ce mata, ta dena ba ya so. but ta ƙi. Har fita take yi maƙota da duk inda ta so zuwa ba tare da ta tambaye sa ba."

Iyayen sun fahimce sa kuma sun yi mamaki da halin da Munira take yi, domin kasancewar ta me kirki wanda basu taɓa zaton zata watsa musu ƙasa a idanu ba, a inda ya kamata ta samu aljannan ta a nan ne take wasa da shi, ba ta ɗaukar Miji da daraja bayan shi ne zai zamo silan shiga aljannan ta, da ta kyautata wa mutane ta ƙuntata wa Mijin ta ai gwara kyautata mishi domin shi ne aljannar ta. Sun yi mata faɗa sosai inda suka hore ta a kan, "ta gyara halin ta, ta riƙe Mijin ta da muhimmanci ta dena ɓata masa rai, shi ne aljannar ta, idan ta daɗaɗa masa Allah zai bata lada, idan kuwa ta muzguna masa har yayi fushi da ita Allah zai azabtar da ita".

Koda ta dawo gida da farko tayi sanyi tana mishi duk abin da yake so yanzu, kuma tana iya ƙoƙarin ta wajen ta ga ta kyautata mishi ɗin. Sai dai kuma abun be kai ga ko ina ba ta sake komawa yanda ta ke. Ga shi yanzu har cikin ta ya soma tsufa zama dai ya ƙi daɗi

Inda shi kuma yake a cikin matsanancin damuwa tunda Umman shi ta ce, "idan ya sake ƙuntata mata har ya kore ta wlh zai ga ɓacin ranta," ta jaddada mishi, "babu saki a tsakanin su".

Wata tara da kwanaki biyar ta haifi yarinyar ta Mace. An saka wa yarinyar sunan mahaifiyar Muhseen ne, Hannatu suna kiran ta da Hanan.
[29/09, 9:50 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*











*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 160
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700

Verlid for 30 days

Airtel
500MB 180
1gb. 350
2gb. 700
3gb. 1050
4gb. 1400
5gb. 1750
Verlid for 30 days


Cheap in safety.👌🏼











*PAGE:12*

_____Dole yasa Fauziyya ta kwantar da kai ta fuskanci shirin auren ɗiyar ta, to auren fari wadda bata taɓa aurar wa ba shiyasa sosai take hidima a bikin, duk wani abun da ya dace ta yiwa Intisar; duk da har yanzu Jamal fushi yake yi da ita be wani sakar mata fuska, sai dai duk abun da ta tambaya yana bata

Gaskiya bikin Intisar na ƴar gata ne domin komi an wadata ta da shi, su kansu furnitures da aka siyan mata Fauziyya saka Ƙanwarta tayi ta je har Kano ta yo mata siyayyan a can. Yanzu haka har an fara bikin gida ya cika maƙil, sai habaici kuma da ya soma tashi a wajen Dangin Fauziyyan, haka suke ta zage-zage suna yaɓawa Mama magana da ƴan uwanta da suka taho daga ƙauye, har Innan Hafsah itama ta zo, kusan kwana bakwai kenan da zuwan ta.

Ranan Asabar aka ɗaura auren Shureim Usman Batta da Amaryan shi Maryam Jamal (Intisar). An kai ta gidan ta na gani da faɗa

Kasancewar mahaifin Shureim me kuɗi ne sosai domin ɗan siyasa ne sosai, yanzu ma don yayi sanyi ne be cika yi ba amma fitacce ne a Garin Bauchi, sai dai yana harkan kasuwanci sosai domin har ƙaramin Company yake da shi na sarrafa shinkafa. To Shureim shi kaɗai ne ɗan shi, Mahaifiyar shi ta haifi yara kusan uku duk sun rasu domin da girman su ma suka mutu, sai daga baya da ta haifi Shureim ya tsaya, shima sun yi tunanin zai mutu saboda ya sha ciwo sosai shi da Momyn nashi, dalilin da yasa aka juyawa Momy mahaifa kenan kasancewar ta samu matsala a Mahaifar wanda idan har ta ci gaba da haihuwa za'a rasa ranta. Sun ɗauki son duniya sun ɗaurawa Shureim shiyasa ya tashi a cikin gata. Yanzu haka a cikin gidan su aka ɗibi fili me girma aka tsarawa Intisar flat.

Sai mu CE Allah ya bada zaman lafiya tunda an kai Amarya.



✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

Izuwa yanzu Anwar har ya je ya sanar wa iyayen sa da zancen ƙara auren shi da kuma son turawa da yake yi

Baban shi ya saka mishi albarka, inda yace mishi, "zai tuntuɓi Kawunnan sa sai su je suyi bincike idan babu matsala zasu nema mishi yarinyar."

Yayinda Maman shi kuwa maganar kwata-kwata be mata daɗi ba, domin har kasa shiru tayi tace dashi, "yanzu shi me ya rasa a wajen Hauwa da zai ƙara aure? Yarinya me kirki me tsananin kaunar sa da nunawa dangin shi ƙauna amma ita ce zai ƙarawa Kishiya? To meye amfanin Ƙarin auren ko don yana ganin ya samu kuɗi ne yanzu shi ne yake son wulaƙanta ta?"

"Mama wlh ba haka bane, ba zan yi auren nan bane domin in wulaƙanta Hauwa ba, kin San Ina ƙaunar ta sosai wlh bazan taɓa wulaƙanta ta ba, auren nan da zan yi ƙaddarata ce kuma idan da rabo kinga sai in soma samun Yarana nima."

"Ayyo yanzu ka fito da zance, kace kana son ƙara auren ne sabida baka haihu ba, yanzu kai Anwar duka-duka yaushe ne kayi auren da zaka fara tunanin wani haihuwa? Ai haihuwa na Allah ne kuma idan lokaci yayi zaka haihu, Ni kai na ban damu da rashin haihuwar ka ba tunda na san ka samu Macen kirki, kuma a kullum ina muku fatan samun zuri'a ɗayyiba, amma yanzu ita wacce zaka aura baka san halinta ba ya zaku zauna da ita? Duk baka sani ba, zaka ɗauko ta ka ɓatawa kanku zaman ku alhalin kuna zaune lafiya, duk da nasan halin Hauwa sai dai idan kai ne da ita wancan ɗin zaku muzguna mata. Anwar ka guji ranan da Hauwa zata kawo min ƙaran ka wlh zaka ga ɓacin raina tunda duk abin da zai faru a gaba kai ne sila."

Duk jikin sa yayi sanyi saboda jin kalaman Maman nasa, har ya kasa magana illa kallon ta da yake yi

Sai tace, "ka tashi ka wuce Allah ya taimaka ya bada Sa'a, tunda haka ka zaɓa ko? Ƙaddaran ka ce."

"Mama idan ba kya so wlh zan fasa, bazai yiwu inyi aure babu albarkan ki ba."

"Ni rufa min Asiri, taya zan hana ka abin da kayi ninya? Bayan ma har ka sanar da Mahaifinka ya amince to Ni meye nawa? Kaje nace Allah ya bada Sa'a ya sanya albarka."

"Amin." Yafaɗa duk da har yanzu jikin sa a sanyaye yake. Tashi yayi ya mata sallama ya fice, Machine ɗin sa da ya siya sabuwa fill ya hau ya wuce sabon gidan shi kai tsaye, dama can yake son zuwa daga nan ya ga aikin da ake mishi. Koda ya je ya sauko ya saka keey ya buɗe Gate ɗin; tunda idan suna aikin masu aikin suna rufewa kasancewar anguwan sabuwar anguwa ce, idan ya zo shi kuma zai shiga sai ya buɗe ya shiga. Koda ya shiga yanzu ya same su a ciki suna ta aikin nasu, suka gaisa cike da girmamawa kana ya soma bi yana duba ko ina, idan da wani abu kuma yana tambayar su ko akwai matsala?

Gidan yayi kyau sosai duk da ba wani fili ne me yawa ba, sai dai anyi flat biyu ne mu haɗu a Parlour. Kowacce da bedroom ɗinta me yalwa da Toilet a ciki, sai kichen ɗin su da wani Toilet ɗin a parlour. Parlour'n yana da girma don zai iya cin kujeru set uku sannan daga parlour'n zuwa ɗakunan su akwai ɗan tazara da corridor a wajen. Nasu na kallon juna ɗakunan sai nashi daban shima bedroom ɗin. Filin gaba ɗaya an cinye shi a ginin ne sai haraban gidan be da girma, ɗan kaɗan ne wanda zai wadata su suyi aikace-aikace a wajen, sai kuma inda za'a ajiye mota ɗan tsukut guda ɗaya. Yanzu haka penti ne ya rage da wasu kayan Toilet da ba'a saka ba

Ya jima a gidan kafin ya wuce gida.

Kwana biyu da yin maganar aka je aka yi magana da iyayen Afnan aka saka musu rana wata huɗu masu zuwa

Anwar har a lokacin be sanar da Hauwa ba saboda duk ya rasa ta inda zai fara ma. Sai da aka saka ranan ne sannan ya samu ya daure ya sanar mata a lokacin suna kwance da daddare sun yi shirin barci. Ya tashe ta yace, "ta tashi akwai maganar da zasu yi". Koda ta tashi sai ya soma sanar mata da zancen a cikin sanyin murya ta yanda zata fahimce shi

Ita kuwa kallon sa

Please Login or Register in order to submit comment