Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwanta suna zaune suna bata baki amma sun kasa shawo kanta

Shi yasa Aunty Nadeeya ta daka mata tsawa tana cewa, "wai ke baza ki haƙura ki bar kukan nan bane sai kin jawo wa kanki wani ciwon? Kina dai jin abun da Likitan ya faɗa amma tunda kika tashi kike wannan kukan? Idan ba ki yi haƙuri ba to me za ki yi? Yaran nan dai kin rigada kin rasa su sai ki ɗauki dangana Allah ya mayar miki da wanda ya fi su."

"To da wanne zata ji ke kuma kin tasa ta gaba kina mata wannan ihun? Idan ba ki rarrarshe ta ba ai baza ki tunzura ta haka ba." Cewar Umman nasu da ke duban Nadeeyan, Kana kuma ta mayar da kallonta ga Zeena tana cewa, "Ya isa haka nan Zeena ki yi shiru ki daure ko ruwan tea ɗin ne ki sha, kinga tun jiya ba ki zura komai a cikin ki ba."
Sai ta dubi inda Halira ke zaune tace, "Auta haɗa mata tea ɗin ta sha. Ki zuba mata har dankalin ko zata iya ci."

Zeena wacce ta haɗa majinu kashirɓan, fuskar nan tayi caɓa-caɓa tana zaune saman gadon marasa lafiya, idanun nan sun kaɗa sun yi jazur sai zubar da hawaye take yi, daƙyar ta iya buɗe baki tana sharce hawayen da ke ɗiga har saman laɓɓanta tace, "Umma bazan iya cin komai ba wlh, bazan iya ba, kina ganin tunda abun nan ya faru har yanzu Aliyu bai zo ba, ban san wanne irin mataki zai ɗauka a kaina ba? Na kashe masa Yara shikenan na rasa su."

Dogon tsaki Aunty Nadeeya ta ja tana cewa, "wai kanki farau ne? Tunda asirin ki bai tonu ba ai ya san ƙaddara, kawai ki san abun da za ki ce mishi amma ki dena wannan zancen."

Umma tace, "ya ishe ki Nadeeya, wai meyasa ba ki da tausayi ne? Ki bar yarinyar nan ta huta nace miki in har baza ki yi mata magana da rarrashi ba."

Ƙwafa Aunty Nadeeya ta buga tana miƙe wa tare da furta, "Ni dai bari in wuce gida tunda ina da aikin yi, zuwa anjima zan dawo, in kuma an sallame ki sai dai mu haɗe a gida."
Ta sa kai ta fice ba tare da jiran cewar su ba

Ganin Zeenan ta ƙi amsar tea ɗin ta sha, sai ma sabon kuka da ta ɓarke da shi, Umma sai rarrashinta take yi tana cewa, "haba Zeenatu wai mene ne haka? Ki sha tea ɗin nan kamar yanda Likita yace a ba ki, kinga baza a ci gaba da ba ki magani babu komai a cikin ki ba, idan ba ki ɗauki ƙaddara ba ya kike so ne?"


Shigowar wasu daga cikin ƴan uwansu, shiyasa tayi shiru bata iya furta komai ba, ta amsa tea ɗin tana ƙoƙarin kaiwa bakin ta cikin ɗacin rai still tea's na zuba mata har yanzu,
Duk gaisuwar da mutanen ma suke mata bata amsa musu ba

Umma ce kawai ta amsa tana musu sannu da zuwa,
Su kuma sai jajanta wa suke yi tare da musu ta'aziyyya

Duk sannun da suke wa Zeena ta ƙi amsa wa, sai ma wani sabon kuka da ya kufce mata, haka ta kwanta ta dinga raira shi kamar baza ta dena ba. Kowa ya tausaya mata sabida rashin Yara biyun nan dole ne ta shiga wani hali

Ita yanzu hukuncin da Aliyu zai yanke take tunani, duk da ta san ba lallai ya san inda ta je ba, kawai zata ce mishi tsautsayi ne tunda ita ba ta a cikin gidan abun ya faru

A wannan ranan kuwa babu ƙeyan ƴan gidan su Aliyu, babu wanda ya zo duba ta har aka sallame ta suka koma gidan su, babu Aliyu babu labarin sa, ga shi babu wayanta bare ta kira sa, tun ranan da ta saki Jakarta sabida ruɗe wa bata san inda take ba, kuma alamu dai ya nuna an ɗauke Jakar ne ma, ga shi ta kasa kwantar da hankalinta, zullumi da dana-sanin abun da ta aikata ya jefa ta wani hali, tabbas da bata aikata abubuwan da take yi ba; da duk hakan bata faru ba, baza ta rasa ƴaƴanta a kan saɓa wa Mahaliccin ta ba, har ga Allah a wannan lokacin tayi matuƙar nadamar abun da take yi, aikata zina bai ƙare ta da komai ba sai dana-sani. A kwana biyu ma sai da ta zabge ta gama fita a hayyacin ta tsaban firgita da zullumin ƴaƴan nata, ko sukuni bata dashi barci ma ba ta iya yi su kaɗai take iya hango wa

Shi kansa Aliyu ya fita a hayyacin sa, ciwo sosai yayi kuma ya hana kowa ya maida shi asibiti, baƙin ciki da takaicin sa ma yanda ya kasa cire Zeena a cikin ransa, har yanzu soyayyarta yana azabtar da shi, amma kuma ba ya jin shima zai iya ci gaba da zama da ita, tunda ta kasa yarda ta zauna da shi shi kaɗai dole sai ta haɗa shi da wani, babu wani amfanin ci gaba da zama da ita, domin hankalin sa ma yanzu bazai taɓa kwanciya ba, ko ta koma gidansa zai rika kallonta da abun ne, sannan zargi zai shiga tsakani, ga kuma umarnin mahaifiyarsa dole ne ya bi tunda a yanzu ba shi da tsimi bare dabara. Shi yasa ya rubuta mata sakin ta ya aika mata dashi har gida, domin ba ya fatan ya sake ganin fuskarta a yanzu.





_Juma'at Mubarakh Masoyana, Allah ya ƙara mana son Annabi Sallallahu alaihi Wasallam._
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

           *P.W.A✍️*





             *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼











               *PAGE:25*

_____Yau ce ranan da su Mama zasu koma sabon gidan da Jamal ya siya musu, har an kawo mota ana kwasan kayan ana lodawa a ciki

Dayake yau asabar ne Fauziyya na zaune da ita da ƴaƴanta a Falo, ko fita sun ƙi yi bare su fita su ga me ke faruwa

Sai Jamal ne ma ya shigo yana ce mata, "kin zauna kuma ba ki tashi kin shirya ba? Kin ga har an kusa kammala zuba kayan sai mu wuce gaba ɗaya ki ga gida."

Fuska a ɗaure tace, "gaskiya bazan samu zuwa ba, domin Ni yanzu ma jira nake yi ka shigo in faɗa maka zan wuce gidan mu."

Shiru ya ɗan yi yana kallonta ya kasa cewa komai

Ita kuma sai ta ɗauke kanta tana ƙara haɗe fuska don ma kar ya ga hanyar da zai ƙara mata magana

Wuce wa yayi ɗakin sa ya shiga wanka tunda bai samu yayi ba tun safe

While ita kuma ta kalli su Sumayya da hankalin su ke a kan kallo, dukkan su sun kwanta sun lafe kamar babu kowa a wurin, sai tace, "ku tashi ku je ku shirya mu tafi tare, tunda bazan yi wani girki ba, gwara mu wuce gaba ɗaya mu wuni a can."

Jin abun da tace shiyasa suka tashi cike da zumuɗi, Sumayya ta wuce dakin ta shima Jibril da gudun sa ya wuce nasa ɗakin yana farin ciki

Bayan Jamal ya kammala wankan ya shirya tsab, sai ya fito ba tare da yace da Fauziyyan uffan ba ya fice a falon

Ta raka sa da harara tana ƙunƙunai, sai ta miƙe ta wuce itama ɗakin ta don ta shirya

Lokacin komai an zuba a Motan, har su Hafsan sun fito suna jiran Jamal. Yana fitowa ya isa wurin su yana kallon Mama da cewa, "Mama komai an kwashe ko?"

"Eh, bamu bar komai ba a ciki."

"To Shikenan mu je cikin mota na sai mu wuce, ku je ku shiga bari in zo."
Ya sa kai ya wuce wurin masu Motan da suke rufe bayan motan,
Magana yayi musu sannan ya koma ya shiga nasa Motan,
Mama ne a gaba sai Hafsah a baya. Bayan ya shiga sai ya ja zuwa bakin gate yana danna horn, ana buɗe mishi ya harba motan waje, while motan kayan su ma suka take mishi baya

Kai tsaye anguwan da gidan yake suka wuce. Aka kai aka dire kayan a waje, masu Motan suka soma shiga dashi,
While su Mama suna a ciki suna zagaye gidan bakin su ya ƙi rufuwa don farin ciki, gida yayi musu kyau musamman da suka ga an zuba kujeru a falon har da kayan kallo

Suna nan tsaye Jamal ya shigo yana ƙarisa wa wurin su tare da cewa, "Mama sai ki zaɓi ɗakin da kike so a cikin ukun nan, tunda dakuna uku ne, itama Hafsah sai ta dauki ɗaya, yanzu zasu shigo da kayan sai ki nuna musu ɗakin."
    

"To, ai Ni kowanne ka zaɓa min yayi Jamalu, ai ba sai na tsaya ruwan ido ba kowanne ina so, gaskiya gida yayi kyau Masha Allah tubarakalla, Allah ya buɗa ya ƙara buɗa wa, wlh kayi kokari sosai Jamalu, Allah yayi albarka, Ubangiji ya ƙara tsare ka a duk inda kake, ya yalwata maka hanyar samun ka."

Daga shi har Hafsah suka amsa da Amin dukkan su suna murmusawa,
Farin cikin Hafsah ma ba a magana, don ko magana ba tayi sai ware idanunta take yi tana kallon zubi da tsarin gidan, ga sanyin teyes da ke huda musu ƙafafu, haka ma iskar da ke shigowa ta kafofin window da ƙofan da aka buɗe

    

Bayan an kammala shigo da kayan, har cikin ɗakin da Mama ta zaɓa; masu Motan suka shiga da kayan, dayake akwai gado da sif a ciki, tunda har da su Jamal ya siya sabo fil, kuma ba a haɗa gadon ba yana ajiye, sabida yana jiran Mama ta zaɓa ɗakin da take so ne sai a haɗa mata, bayan ta zaba shine masu Motan suka hada mata, sannan aka saka tsohon gadon a cikin wanda Hafsah zata zauna a ciki, duk da Maman da kanta tace, "ai tare zasu kwana babu mai raba su, wannan gida yayi musu girma."

Jamal yace, "haka ne Mama, nima na so in siya gadon biyu ne a zuba, amma hakan bai samu ba, ko daga baya ne zan siya sai a canza mata na ɗakin nata, duk dai yanda ku ka yi babu matsala in ma kun kwana tare." Sai kuma ya sake cewa, "tunda yanzu an gama komai, sai mu je in nuna muku kitchen ɗin da komai da komai, yanzu idan na fita sai in siyo kayan abinci a ajiye."

Mama da farin ciki ya hana ta rufe baki, har ƙwallan murna take fitar wa tana furta, "Allah kaɗai zai biya ka abun da kayi mana Jamalu, Allah ya saka maka ya biya ka da mafificin alkhairi."

"Haba Mama, sai ka ce ba ɗanki ba kike min wannan godiyar? Ai ya zama dole na in yi muku, bani da buri da ya wuce in sanya ku farin ciki, kullum cikin damuwa nake da tunanin hanyar da zan saka miki Mama, abubuwan da kika yi min a rayuwa, da ba don kin saka Ni a makaranta nayi karatu har nayi yaƙi da jahilci ba; ai bazan kai wannan matsayin ba."

Girgiza kanta tayi tana ɗan jan majina da furta, "duk da haka Jamaluddin yau ina farin ciki matuƙa, ka siya mana wannan gidan duk saboda farin cikin mu, dole in gode maka, ai zuciya tana son mai kyautata mata, yanda ka faranta mana dole mu faranta maka da nuna godiyar mu."

Murmushi yayi kawai, sai kuma ya mayar da kallonsa wurin Hafsah da ke tsaye kanta a ƙasa tana sauraron su, kamar bazai yi magana ba kuma sai yace, "ƴata Allah yasa gidan yayi miki? Ke naji ba ki ce komai ba?"


Ɗago ido tayi ta zuba mishi, ganin yanda suka shige cikin nasa kai tsaye sai ta ɗauke su da sauri tana murmusawa tare da furta, "ayya Dady, wlh farin cikin nawa ne ya ƙi bari na in yi magana, ban san me zan ce ba?"

Dariya yayi, yace, "ba ki san me za ki ce ba kuma? Ai ko Addu'a kika yi min zan ji daɗi da shirun nan naki."

Cike da sanyin murya tace, "mun gode  Dady Allah ya saka da alkhairi, yanda ka sanya mu a cikin wannan farin cikin; ka share mana damuwarmu, Allah Ubangiji ya sanya ka a farin cikin da ya ninka namu, Allah ya buɗa maka arziki mai albarka."

Ba shi kaɗai ba, hatta Mama ta ji daɗin addu'ar da Hafsah tayi mishi. Shi yasa dukkan su suke ta murmusawa tare da amsa mata da Amin cike da farin ciki

Tare suka wuce kitchen ɗin ya nuna musu komai, ya sake musu bayanin wasu abubuwan sannan yayi musu sallama a kan zai dawo zuwa anjima



Zama suka yi a Falon suna ƙara kallon tsarin komai, duk da ba komai aka saka a Falon ba, kujerun ne kawai da kayan kallo, sai ƙamshin sabunta da penti a falon yake tashi

"Allah mun gode maka, yau mu ne a wannan daular gidan namu na kanmu? duk da gidan ko rabin kyan nashi bai kai ba amma muna farin ciki da hakan, tunda a yanzu babu wani matsa wa da zamu samu, zamu yi rayuwar mu cikin farin ciki, dama fata na ace kin samu ƴanci da walwala a cikin rayuwar ki Hafsatu, yanzu babu takurar Fauziyya bare ta matsa miki da ayyukan ta, nan daga mu sai mu." Mama ta ƙare maganar tana ci gaba da murmusawa

Ita kuma Hafsah wacce take washe baki tace, "Inna wlh ba ki ji farin cikin da nake ji ba, nayi murna matuƙa da barin mu can, ko ba komai baza mu sake fuskantar wulaƙanci da tozarci ba, Ni Inna wlh yanda suke nuna miki ne ya fi damu na, amma ba aikin da suke saka Ni ba, yanda suke wulaƙanta ki sun dauke ki ba a bakin komai ba; kuma kin kasa ɗaukar mataki, shi ya fi komai ci min tuwo a ƙwarya." Ta ƙare maganar cikin ɗacin rai tare da gusar da murmushin da ke saman fuskarta sabida tuna abun da ya faru a baya

Mama tayi murmushi tace, "ai komai ya wuce Hafsatu, mu bar ma tuna baya kar farin cikin mu ya gushe, abun da tayi ai ta yi wa kanta ne, duk wanda ya yi da kyau zai ga da kyau, fatan mu dai Allah ya shirya su in masu shiryuwan ne, dama Jamalun na fi ji, amma yanzu komai ya wuce."
Sai ta ɗan yi shiru tana tunani, dole ne yau ta sanar da Hafsah auren da ke kanta ko don ta san matsayin ta a wurin Jamal yanzu, kuma tana son a ce tun yanzu Hafsah ta saka a ranta Jamal Mijinta ne kafin lokacin da zata tare a matsayin Matarsa, don haka ya kamata ta sanar mata tun yanzu tunda barin maganar ma a ciki bai da amfani,
Shi yasa tace mata, "su tashi su je suyi sallah tukunn, akwai maganar da zasu tattauna."

Hafsah bata kawo komai a ranta ba, don haka ta miƙe ta wuce ɗakin da yake a matsayin nata, ta shiga toilet ɗin, sai dai babu ruwa a ciki fomfon a rufe suke alamun kamar bai fara amfani ba, hakan ne yasa ta koma ta fita falon tana nufin shiga na Mama, a nan suka ci karo bata kai ga shiga ba, sai tace, "Inna babu ruwa fa."

"Nima abun da na gani kenan na fito in duba a nan, wataƙil famfon ma bai fara amfani bane tunda sabo ne na ga alama."

"Eh mana, amma bari in dudduba gidan ko zamu samu ruwa."
Hafsan ta ambaci hakan tana juya wa tare da duba toile ɗin falon, nan ma babu ruwan, har Kitchen ta shiga bata ga alamun wurin ruwa ba, sai ta fita haraban gidan, a nan ta samu famfo ɗaya yana yi, shiyasa ta koma ta dauko musu buta ta zuba musu ruwan a ciki

Bayan sun yi alwala sai suka jeru a falon suka tayar da Sallah,
Suna cikin yi ne, Jamal ya shigo gidan da niƙi-niƙin kaya, kai tsaye kitchen ya nufa da su ya dinga ajiye wa yana koma wa yana kwaso sauran,
Sai da ya gama sannan ya dawo ciki a lokacin Mama ta idar

Sai ta kalle shi cike da tausayin sa a ranta tace, "sannu Jamalu."

"Yauwa Mama, har kin idar ne?" Yayi maganar yana zama a kan sofa wanda yake gefen su

"Na idar, kana ta ɗawainiya maimakon ka bari sai anjima?"

Murmushi yayi yace, "nima na so zuwa dare zan dawo, sai kuma na tuna in ban kawo kayan abincin ba babu abun da zaku dafa, shiyasa kawai na wuce kai tsaye kasuwa nayo siyayyan."

"Masha Allah, Allah yayi albarka."

Amin ya amsa mata yana ɗan jujjuya mukullin motan sa, kansa a ƙasa yana ɗan kallon yatsun ƙafafunsa

Shiru ne ya ratsa Falon. Inda Mama ta ci gaba da addu'o'i hannayen ta a sama,
Ita kuma Hafsah tana duke itama kanta a ƙasa tana ɗan motsa bakin ta alamun azkar take yi

Dalilin da yasa Jamal bai sake cewa komai ba tunda ya ɗago yayi musu duba ɗaya, sai ya mayar da kansa kasa yana dulmiya wa tunanin da ya tsaya mishi a rai

Sai can da Mama ta shafa addu'ar sannan ta ɗago tana duban sa da cewan, "sai ka hanzarta ka tafi kar iyalan ka su ji ka shiru ko?"

Murmushi yayi bayan ya ji saukar muryanta a kunnen sa, wanda ya dawo da shi ɗan guntun tunanin da ya afka, satan kallon Hafsah yayi har yanzu kanta a ƙasa tana motsa yatsunta

Mama tace, "yauwa famfon gidan ma mun ga ba sa aiki, mun zo yin alwala dakyar muka samu a waje Allah yasa Hafsatu ta fita haraban gidan, a nan ta ga famfon da yake yi."

Yace, "eh dayake da wuta famfunan suke yi, kuma an yi wearing amma babu wutan lantarkin a sauran ɗakunan, gobe sun ce zasu zo su ƙarisa ruwan zai riƙa zuwa Insha Allahu, in na fita ma sai in siyo muku pure water ku fara amfani dashi."

"A'a kayi tafiyar ka kawai, Hafsatu sai ta fita ta je ta siyo ba sai ka sha wahalar dawowa ba."

Mike wa yayi da furta, "a'a Mama, bari in je kawai, don shagunan anguwan suna da ɗan tazara, bari in je Ni in siyo." Ya nufi hanyar fita ba tare da ya jira cewar ta ba

Hakan ne yasa ta amsa mishi da to kawai, yayinda dukkan su suka bi shi da kallo har ya fice

Murmushi Hafsah tayi tana sake mayar da kanta a ƙasa, yau matuƙa tana farin ciki, Jamal ya sanya su a farin ciki, shiyasa ta ji har zuciyarta tana buƙatar yin masa addu'a, shima Allah ya faranta masa. Bata yi magana ba har sai da ta gama zikirorin ta, sannan ta ɗaga hannu ta soma yin addu'ar daga cikin zuciyarta, wanda gaba ɗaya addu'ar ta yi wa Jamal ne

Suna zaune a wurin sai ga shi ya dawo da ruwan ledan. Mama ne kaɗai ta tashi ta zauna a kan sofa tana ci gaba da lazimi tunda ta ga Hafsah itama abun da take yi kenan, shiyasa bata ce komai ba ta mayar da hankalin ta a kan nata, sai ga Jamal ɗin ya shigo da ledan ruwan har huɗu. Zuba musu yayi a can gefe sannan ya dawo kusa da su yana cewa Maman zai tafi

Sai da ta sake mishi addu'a tare da godiya sannan suka yi sallama ya fice

Sa'ilin har lokacin Hafsah kanta a ƙasa bata ɗago ta dube shi ba har ya fice. Bayan ya fita ne Mama ta kira sunan ta, hakan ne yasa ta ɗago kanta tana duban ta tare da amsa mata

"Ba ki idar da azkar ɗin bane?"

"Na idar Inna." Tayi maganar tana tuɓe Hijabin daga jikinta


Sai Mama tace, "maganar da nake so muyi da ke mai muhimmanci ne Hafsatu, don haka ki natsu ki saurari mai zan faɗa miki".
[03/01, 4:52 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*




*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼











*PAGE:26*

_____Tsoro da firgici ne ya bayyana a kan fuskar Hafsah, yayinda ta zaro ido waje tana kallon Maman tamkar bata fahimci me take cewa ba, don ta kore tantama baki na rawa tace, "Inna, wai Ni... Ni kike nufin na zama Matar Dady?"

Murmushi Mama tayi tana kallonta cikin ido, tace, "ƙwarai kuwa, ke nake nufi, shiyasa ma na ƙi faɗa miki sabida na san dole za ki shiga firgici, amma tun ranan da na je ƙauye na nema mishi auren ki, a ranan da zamu baro aka ɗaura muku aure, don haka abun da nake so da ke ki kwantar da hankalinki ki natsu wuri ɗaya, duk da ban so na faɗa miki ba kasancewar ba yanzu nake so ki tare ba, har sai Allah yasa kin gama wannan karatun naki, inyaso lokacin da za ki shiga babban makaranta sai ki tare, amma kuma shigowar mu gidan nan yasa nace bari in faɗa miki ki san da sani gudun samun matsala, na san Hafsi na baza ki taɓa bijire min ba shi yasa nayi abun nan ba tare da sanin ki ba, ina fata kin amince da wannan hukuncin da na yanke babu sanin ki?"

Shiru Hafsah tayi, saboda har yanzu gani take yi tamkar a mafarki, wai ita ce ta auri Dady wanda take ganin tamkar mahaifi; shi ya zuƙuna ya haife ta, amma yau shi ne ake kiran wanda ya aure ta, anya ba mafarki take yi ba?
Sai da ta ji kiran da Mama take mata, sannan ta ƙifta ido ta bi ta da kallo kamar ta samu TV

"Hafsatu, ko dai ba ki ji me nace miki bane? Kiyi magana mana."

"Inna, anya ba mafarki nake yi ba? Taya hakan zai kasance?" Tayi maganar cikin rawan murya

Kallonta Mama take yi cike da tausayi, sai tace, "ki yi hakuri Hafsatu, ki ɗauki wannan auren tamkar ƙaddaran ki ne, na san ban kyauta miki ba, amma ke kaɗai na ji a raina kin fi dacewa da Jamalu, sabida gudun samun wata matsalar a nan gaba, kin san dai yanda muka yi rayuwa a gidan Jamalu; da kuma irin ƙalubalen da na fuskanta, a matsayina na Uwa amma na rasa farin cikin da ya kamata, na rasa soyayyar Jikokina a tare da Ni." Sai ta ja numfashi tayi shiru sabida yanda takaicin abun ya zo mata iya wuya

Har yanzu Hafsah kallonta take yi ta kasa cewa komai

"Hafsatu na duba miki goben ki ne, na san ko ba na raye Jamalu mai riƙe ki ne, Ƙaunar da nake miki yasa na yanke wannan hukuncin domin samun farin cikin ki a nan

Please Login or Register in order to submit comment