Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zancen, ba ƙaramin murna tayi ba, domin burin ta kenan dama Yaran nata suyi aure su samu manema ƴan mutunci inda aka san asalin su, barin ma A'isha da ba ta son zancen aure, gwara Amina tana ɗan tsaya wa da samarin ta, don har tana da wanda take burin aure

Tuni Umma har ta sanar da Muhseen da ya zo hutu ta sanar masa halin da ake ciki

Yace, "shi bai da matsala, in ta ga ya dace a yi musu auren yanzu shikenan, amma shi ya so suyi karatu ne gaskiya."

Umma tace, "ai ba sai lallai an haɗa su dukka su biyun an aurar ba, tunda ita Amina har yanzu bata gama ƙaramar makarantar ba, a bari har ta kammala ta soma itama babban makarantar, tunda hidiman ma zai yi maka yawa."

"To Shikenan Umma, duk yanda kika yanke dai, ya ci gaba da neman ta in sun daidaita sai su turo."

Fannin A'isha kuma sam bata so haka ba, gani take yi ana son yin mata fim ƙarfi, a zahiri Aliyun ma bai yi mata ba, Mutum daga zuwa sau ɗaya bata san halin sa ba bata fahimce sa ba amma har ana neman masa auren ta? Ko dama haka ake yin auren ne lokaci ɗaya sai a sako ka a gaba? Wlh kwata-kwata ba ta farin ciki da auren nan saboda karatu ta fi ƙauna, ga shi Umma ta nace tana ta tusa mata ra'ayin Aliyun tana yabon sa

Haka su ma su Munira da Amina dukka babu wanda bai son auren, duk murna suke yi musamman Amina da ta fi sanin Aliyun sosai, ba abun da suka iya sai yabon shi, duk yanda A'isha tayi da son kushe sa amma sam ba sa gani, shiyasa ta rabu dasu suna tayi tana ganin ikon Allah, da kuma ganin iya gudun ruwan Aliyun; nufin sa a haka zai aure ta babu zuwa bare ta saba dashi? Kuma ma bata amince masa ba haka kawai an kama za a haɗa su, haka ake yi ne?

Shi kuwa Aliyu sai da ya tabbatar an ba shi iznin zuwa sannan ne ya sake dawowa wurin A'ishan, lokacin da ya zo ba ta nan tana school, bai same ta ba, sai a lokacin ne yayi tunanin kiranta saboda tunda ya amshi layin ta bai taɓa kwatanta kiran ta ba, layin ya nemo kamar yanda yayi mata save da sunan ta ya danna mata kira,
Kira biyu yayi mata but bata yi peaking ba, sai ya haƙura ya tura mata saƙo ya rubuta mata

"Aslm alaikum, aminci ya tabbata a gare ki, Aliyu ne, na kira ba ki yi peaking ba kar in katse miki hanzari, na zo gida an ce min kina school, so ina buƙatar ki tura min time na tashin ku zan zo in ɗauke ki."

A time ɗin A'isha tana class bata san ma yana kira ba, cuz wayan a silent ta saka gudun samun matsala. Sai bayan sun gama lecture almost 40 minutes before suka fito, a nan ta ga missed calls din tare da message ɗin sa. Tsaya wa tayi tana ta karanta wa kusan sau uku tana bibiyan message ɗin; before kuma ta ajiye wayan ba tare da ta ba shi amsa ba

Shi kuma Aliyu shiru-shiru yana jiran amsar ta har ya gaji ya koma gida, duk yanda ya so ya haƙura ya cire ta a rai duk da yana bata uzurin maybe bata gani bane, daga ƙarshe dai ya gaza jure wa ya ƙara tura mata message

"Ina jiran ki har yanzu ba ki bani amsa ba, please ki faɗa min zan zo sai mu tattauna."

Ya sake tura mata yana jiran reply

Sai dai ƙiri-ƙiri A'isha ta ƙi ba shi amsa, ba wai don wani abu ba sai don ba ta son zuwan nasa, tunda ba ta bukatar ya biyo ta school

Shi kuma da ya sake jin shiru sai ya wuce neman Usman don ya tambaye sa ko ya san makarantar da take yi, amma bai same sa ba sai dai Habib da ke gida, da ya tambaye sa kuma sai aka yi Sa'a ya sani, shiyasa nan da nan ya sake gyara jikinsa ya feshe da turare ya burga machine ya nufi hanyar makarantar yana fatan ya dace ba a tashi ba,
Canza shawara yayi ya wuce gidan su aka sake mishi sallama da ita

Dalilin da yasa Amina ta fito kenan, tunda two times kenan yana zuwa shiyasa ta fito domin ta sanar mishi har yanzu bata dawo ba

Da farko ma yayi tunanin ita ce, sai daga baya ya tantance su ya gane ba ita bane

Bare Amina ta karɓe shi da fara'a ta gaishe shi har da kiran sunan sa alamun ta san shi sosai, sai tayi masa bayanin, "har yanzu Aunty A'ishan bata dawo ba."

"Ok, to ko za ki faɗa min inda zan same ta zan bi ta school ɗin?"

Babu ɓata lokaci ta sanar mishi har department ɗin da take karatu, sannan suka yi sallama ta shiga gida,
Shi kuma ya wuce makarantar.



Juma'at Mubarakh FAN'S.
[03/01, 4:54 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*






                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼












            *PAGE:33*

_____Bayan Aliyu ya je makarantar ya nemi department ɗin su, ganin kamar ana lectures a wuraren shiyasa ya kafa machine ya zauna yana ta baza ido ta inda zai ganta,
Duk ajin da ya ga an fito sai ya baza ido yana ta famar kallonsu ko zai dace ya ganta, daga ƙarshe ya sake try numban ta still tana ring ba a ɗaga ba, can ya ga wasu class sun fito, yana ƙilla ido ya hango hasken ta tunda ta fita daban a cikin su, ga ta doguwa duk da ta rufe rabin fuskarta da Hijabin da ta zumbula har ƙasa, har wani ajiyan zuciya ya saki yana faman kallonta, bata gansa ba har sai da ta zo giftawa ta wurin sa sannan ya kira Sunanta

Saurin juyawa tayi sabida jin kamar ana kiran ta, ai kuwa karaf suka haɗa ido dashi

Sa'ilin ya tsaya a kan ƙafafunsa ya kafa mata ido yana ɗan mata murmushi

Hakan ne yasa ta taho wurin sa tana mamakin yanda aka yi ya san inda take har ya zo, gaishe shi tayi tana ɗauke ido a kansa sabida kallon da yake mata

Murmushi yayi yace, "ya school ɗin? Ina fatan kun kammala?"

"Eh mun kammala, zan tafi ne."

"Ok ki hau mu je in sauke ki, sai mu tattauna."

Da fari ta nuna masa a'a, but yanda ya nace yace, "ta hau." Dole haka nan ta hau tunda ba ta son ja'inja ana ta kallon su a cikin jama'a

Jan machine ɗin yayi bayan ta hau suka fita a school ɗin. Bai yi mata magana ba har sanda suka isa kofar gidan su, after ta sauka sai shima ya sauka yana ƙoƙarin tsayar da ita sabida har tayi mishi godiya tana son shigewa da sauri, "A'isha ki tsaya mu yi magana mana."

Tsayawa tayi tana ɗan dawowa baya tare da ɗauke kanta gefe

Ɗan numfashi ya ja before yace, "ki yi haƙuri sabida ganin ban sake dawowa ba tun ranan farko, na san yanzu kin gama fahimtar dalilin zuwana wurin ki tunda maganar aure ta shiga tsakanin mu, Iyayena sun zo sun nema min auren ki, to ba na son maganar tayi tsawo sosai tunda kinga ba Yaro bane Ni kamar saurayi; already na taɓa aure, A'isha in kin bani dama ina son mu fahimci juna a ɗan kankanin lokaci don ba na son mu ja tsawon lokaci ba a yi auren ba, me kika ce game da ra'ayina? Ki faɗa min abun da ke ranki don Allah."

Shiru tayi tana juya hannun Jakarta kanta na ƙasa

"Ki yi magana mana ina sauraron ki, ko ba ki da abun cewa?"

Ɗago kai tayi ta kalle sa kaɗan ta sake ɗauke idonta, cikin yanayin muryanta na yanga tace, "Ni bani da abun da zan ce maka a yanzu, amma in so samu ne ka bar Ni in yi karatu na a gida don shi ne a gabana a yanzu, ban shirya aure yanzu ba."


Jin zancen nata sai ya kasa yin magana, domin hakan ya tabbatar masa cewan kamar ba ta ra'ayin sa, amma har ga Allah a yanzu yana jin yarinyar ta kwanta masa a rai bazai iya rabuwa da ita ba, don haka ya zama wajibi ya ja ra'ayin ta wajen ganin ta kamu da soyayyarsa har ta amince su yi aure, ba ya son su ɗauki lokaci basu yi aure ba, ashe akwai aiki a gabansa kenan, bai takura mata ba yace, "ta shiga gida zasu yi waya, amma tayi nazari a kan maganarsa, ba shi da wata matsala a kan karatun ta in har ta shiga gidan sa zata ƙarisa; bazai hana ta ba, amma shi yana sonta da aure kuma zai jure duk abun da zai biyo baya."
Daga nan yayi mata sallama ya hau machine ɗin ya tafi

Wanda A'isha kuma ta rasa matsayin da zata saka Aliyu a wurin ta, baza ta ce ba ta sonshi ba, amma kuma takura ne ba ta so tunda ba auren take so ba, ba ta son namiji ya raɓe ta, amma zata ba shi dama tunda ya soma zuwa hakan zai sa su fahimci juna, ita kanta da tunanin sa ta kwana tana ta karanta message ɗin sa da ya tura mata,
Kuma tana ta jiran kiran nasa kamar yanda yace zai kira, amma bata ga kiran ba sai message ɗin sa da yake tambayar lafiyar ta da kuma faɗa mata muhimmancin auren su a yanzu fiye da karatun nata, yana ƙara roƙon ta a kan, "ta amince zata ji daɗi a gidansa, shi bai da wata matsala zata samu farin ciki a tare da shi." Daga ƙarshe ya rubuta mata kalamai masu sanyi da ratsa zuciya,
Wadda hakan ne yasa ta kwana da shi a cikin ranta

Kuma tun daga ranan Aliyu yana zuwa akai-akai wurin ta, ya fi yin mata text message a kan kiran ta, shiyasa A'isha ta saki jikinta tunda bata da yanda zata yi, Umman ta na son auren; tana ji a yanzu tana son Aliyu, amma ba wai don su yi aure a yanzu ba, ba ta son gaggawa, sai dai kuma a ɗan kankanin lokaci wata ɗaya da maganar har sun turo an tsayar da ranan nan da two months

Sai dai kuma kana naka Allah na nashi ne, a wannan lokacin sai Muhseen yayi hatsari a hanyar sa na zuwa Katsina, bai shura ba sai dai gawan sa aka kawo gida,
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Mutuwa mai tonon silili, mutuwar Muhseen da ya girgiza ahalin sa da duk wanda ya san shi, mutuwar farar ɗaya ya tafi ya bar duniyar gaba ɗaya babu dawowa,
Daga Umma har Munira sai da suka yanke jiki suka faɗi, sanadin da har aka kaisu asibiti saboda tashin hankalin da suka shiga sun gaza dawowa hayyacin su

Wani irin kuka su A'isha suka yi; wanda suna jin kamar sun rasa komai nasu, sun fita hayyacin su lokaci guda basu da sana'a sai kuka, ga tashin hankalin halin da Umma take ciki sabida ciwon ta na hawan jini da ya tashi, lokaci guda sun zama abun tausayi, sun girgiza matuƙa kuma sun yi kuka kamar babu gobe

Haka itama Munira, don ita ta fi su shiga tashin hankali, mutuwar yayi matuƙar taɓa ta don ba abun da take tuna wa sai yanda suke rabuwa baram-baram, har wannan lokacin da ya bar duniyar bata sauko sun zauna lafiya ba, kenan da baƙin cikin ta ya tafi ya barta, shiyasa dole mutuwar ta shige ta ta ruɗa ta sosai,
Abun mamakin ma sai da aka kaisu asibiti bayan sun sume, a nan aka gane ashe tana da ƙaramin ciki a jikinta, tayi kuka sosai kamar zata shiɗe, ko magana ta gaza yi bata da aiki sai kuka, lokaci guda ta fita a hayyacin ta tayi firi-firi da ita, sam ta gaza yarda Muhseen ya tafi ya barta, wani lokacin har sambatu take yi a rasa gane kanta,
Sai da tayi jinya kusan sati ɗaya a asibitin sannan aka sallame ta,
Aka mayar da ita ɗakin ta suka ci gaba da kuka tare da ƙanninsa, sabida duk in suka tuna sai sun yi kuka har Umma da ƙoshin lafiya ya ƙi samuwa, itama an sallame ta tun tuni amma sun kasa manta mutuwar Muhseen, tabbas ya buge su kuma manta shi ba yanzu ba

Yanda jikin Munira ya ƙi daɗi; ga zafin mutuwar Mijinta ga ciwon laulayi, shiyasa aka mayar da ita gidan Iyayenta ana ci gaba da kula da ita, amma duk da haka ta kasa cire damuwa bare ta dangana, musamman in ta tuna rashin mutunci da abubuwan da ta dinga yin masa tana ɓata masa rai; sai ga shi ya bar mata duniyar ita kaɗai; wanda bata taɓa tunanin hakan ba, tayi kuka tayi nadama tsantsa, a yanzu bata da aiki sai kuka tunda shi ne samun salamanta a zuciya, duk rarrashi da ban bakin da Mamanta take mata amma ina; ta kasa dena wa, kuka baza ta taɓa bari ba tunda har Muhseen ya tafi da fushi da ɓacin ranta, ina zata saka kanta? Tabbas tayi dana-sani, tayi dana-sanin aikata masa duk abubuwan da tayi masa, da tana da dama a ce zai dawo duniyar; da ta zame mishi Macen da yake so, da ta gyara duk kuskuren ta na baya. Kaicon ta! Ta ji ta tsani kanta, baza ta taɓa yafe wa kanta ba muddin ba Muhseen ya dawo duniyar ya ce ya yafe mata ba, wuni tana zaune tana kuka tare da neman gafarar Allah da yin mishi addu'a kala-kala

Sai dai kuma lokaci ya ƙure Munira kin makaro, Muhseen ya tafi ya bar miki duniyar sai kuma wani ba shi ba. Rayuwa juyi-juyi.

Inda Aliyu shima ya tausaya wa A'isha ba kaɗan, musamman yanda ta koma mutuwar ya shige ta, ta sake zama shiru -shiru ta dena fitowa wurin sa, sai da suka jima sannan ta soma sakin jikinta dashi har tana fitowa suna gaisa wa, sai dai bata da walwala ko kaɗan ba ta wani fara'a, gaskiya ya tausaya mata tunda rashin ɗan uwa kamar Muhseen akwai ciwo, shiyasa ya dage wajen kwantar mata da hankali tare da cire mata damuwa, duk wani abu da zai saka ta cikin farin ciki yana yi duk da shima ba mazauni bane sosai, amma yana ƙoƙarin faranta mata,
Dole aka ɗaga bikin nasu aka ƙara wata biyu a kai. Yanzu saura wata uku tunda an ci one month.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


          Gefe ɗaya kuma kamar yanda Intisar ta dauki alƙawarin zubar da cikin, sabida wauta irin nata ta manta abun da zai biyo baya; bata huta ba sai da ta zubar sannan ta samu salama,
Ai kuwa ta sha wahala domin yanda jini yayi ta zuban mata dole aka kaita asibiti,
A can ne ma Shuriem ya san cewa zubar mishi da ciki tayi, tabbas ransa yayi ƙololuwar ɓaci, idanunsa sun kaɗa sun yi jazur, haka ya fito a wurin likitan ya wuce gida, ya kasa jure wa sai da ya zubar da hawaye, lallai ya yarda Intisar bata da hankali kuma baza ta taɓa jin maganar sa ba, shi kuma bazai iya ci gaba da zama da ita ba, dama ta cika sa, dole ya kawo ƙarshen auren su, bai san me ya tsinta a auren ta ba sai tarin dana-sani, yayi dana-sanin auren ta wlh, Mace dai irin Intisar bazai taɓa iya zama da ita ba. Dole ne ya rabu da ita

Momyn shi tana can asibiti tana jiran ya dawo amma ta ji shiru, shiyasa ta kira wayansa but ya ƙi ɗaga wa, haka nan ta ci gaba da zama da Intisar ɗin har sanda Fauziyya ta zo ita da ƴan uwanta, shiyasa ta tafi ta bar su. Kuma ta koma gida ta tarar da tashin hankalin da Shureim ya sanar mata, ita kanta ta san cewa ɗanta bai yi dacen Mata ba, tunda Intisar ko kusa bata da tarbiyya bata da ɗabi'a, duk da halin da take nuna mata ba ta ganin girman ta; bata taɓa damuwa a kan hakan ba, tana ganin kamar yarinya ce zata canza hali, amma ga abun da ta aikata. Koda ya sanar mata da sakin da yayi mata bata hana sa ba, tunda a ganin ta babu amfanin zama da Intisar tunda har ta iya aikata wannan ɗanyen aikin, nan gaba ma zata yi abun da ya fi haka, yarinya kamar ita kaɗai ce ƴa a duniya? Duk gatan da ɗanta ya nuna mata ƙarshe abun da zata yi masa kenan? Gidansa gaba ɗaya ta ɓata masa tunda bata isa ta gyara ba sai dai mai aiki tayi, ga rashin tsabta ga rashin yin abinci, babu kula da Miji komai bata iya ba an sangarta ta sai abun da ta so zata yi, haka Shureim ya jure wannan tsawon lokacin da suka yi bai taɓa mata ƙorafi ba, wanne namiji ne zai iya zama da Mace a haka tamkar ba aure yayi ba? Uwa Uba ba ta girmama mahaifiyarsa da dangin sa, duk haƙuri da shanyewar da yayi sai da ta kaishi bango, a wannan lokacin kuma bazai iya jure wa ba yana ganin zaman su ya zo ƙarshe. Daga ƙarshe rubuta mata saki biyu yayi ya aika musu dashi har asibitin.



            Tirƙashi! Tashin hankalin da ba a saka mishi rana, a cikin Intisar da Fauziyya babu wanda yayi tunanin Shureim zai iya wannan sakin, musamman ma Intisar da ta san cewa yana matuƙar ƙaunarta; a wautar ta bazai taɓa iya rabuwa da ita ba ko me tayi mishi, wanda son zuciya da rashin hankali irin nata ta aikata hakan ba tare da sanin kowa ba don a tunanin ta bazai san ita ta zubar ba, sai dai yayi tunanin ɓarewa yayi, ashe Likitoci zasu iya gane wa

Ita kanta Fauziyya bata san Intisar ɗin zata zubar da cikin ba tunda bata faɗa mata ba, bare cikin ya rigada ya soma girma hakan babban hatsari ne zata iya rasa ranta, ashe abun yana a ran Intisar ɗin, har sai da ta zubar ta samu salama, yanzu kuma ga shi tana dana-sani, tunda kuka ta dinga yi tana kiran sunan Shureim a kan, "baza ta iya rayuwa babu shi ba."

Fauziyya ta fusata ta dinga ƙunduma mata zagi tana cewa, "meyasa tun farko bata faɗa mata ba; bayan ta san abun da Mahaifinta ya faɗa zai ɗauki mummunar mataki? Yanzu shikenan ta ja ya sake ta sai kuma abun da zai biyo baya in Jamal ya sani, domin ta san muddin ya sani kashin su ya bushe."

"To Momy ba ke kika ce za a zubar ba? Meyasa kike ganin laifi na yanzu?"
Tayi maganar tana kuka sosai

Wani kallo Fauziyya ta sakar mata tace, "dan ubanki tun yaushe aka yi wannan maganar? Tunda kika ga ban ɗauki mataki ba ai maganar ta fi ƙarfi na ne; musamman yanda Ubanki ya sako Ni a gaba, muddin nayi wani yunƙuri a kaina zai fanshe, tunda yayi min barazanar sakina na haƙura, duk wannan abun da kika ga ina yi; ina yi ne kawai a fatar baki ba wai don in aikata ba; ina tauna Aya ne don tsakuwa ta ji tsoro, amma don ba ki da hankali cikin da ya girma ko tsoron ki rasa ranki ba kya yi za ki zubar? To don ubanki Aina kika samu maganin? Ya aka yi kika samu za ki faɗa min ko kuwa?"

Cikin kuka ta sanar mata Ƙawarta ce ta bata shawaran inda zata samo maganin, shi ne ta kaita wani Chemist a can aka bata ta zo gida ta sha over lode

"Kinga ai shikenan kin ja mana tsiya, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Ban san wanne mataki Dadyn ku zai ɗauka ba?"
Kamar Fauziyya zata yi kuka don takaici da tashin hankalin da ke tattare da ita,
Ganin Intisar ta cika ta da kuka sai ta daka mata tsawa tana cewa, "za ki yi min shiru ko kuma sai na ci kutmar Ubanki? Yanzu in wani ya zo ya ganki kina wannan kukan fa? Banza kawai, dalla miƙo min wayar ki in kira Shureim, ai dole in san yanda za a yi ki koma gidan sa tun kafin asiri na ya tonu."
Haka ta fizge wayan Intisar ɗin tana latso numban Shureim, amma tunda ya shiga daga farko sai ya dena shiga alamun an kashe wayan ne,
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"
Salati kawai take yi da tunanin abun da zai biyo baya in har Jamal ya sani, kar dai a ce itama zata rasa nata auren tunda ya rigada yayi iƙirarin hakan?
Ai kuwa ya zama dole ta san abun yi don baza ta taɓa sanar mishi ba,
"Ki share hawayen nan ki dena kukan kar ya zo ya ganki a haka, don tsab za ki iya ganin sa yanzu..."

Ai kuwa kamar yana jin su, bata rufe baki ba ya shigo ɗakin yana sallama

Hakan ne yasa da sauri Intisar ta share hawayen nata tana kokarin ɓoye fuskarta

Shi kuma tuni ya hangi hawayen nata, kuma ga Fauziyya duk ta ruɗe tana baza idanu da fitar da gumi, "wai lafiya? Me ke faruwa ne? Ko wani abun kuma aka kuma cewa?"

Cikin sauri da ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin ta Fauziyya tace, "a'a, babu abun da aka ce, Intisar ɗin ne dai har yanzu ta ƙi saduda ta hakura tunda Likitan ya sanar mana cikin ya zube."

Kallon Intisar yayi, tare da matso wa inda take yace, "Mamana wai ba ki san halin da kike ciki bane amma kike tayar da hankalin ki haka? Idan wani abun ya same ki fa? Allah ne ya ba ki kuma shi zai sake ba ki wani; ki yi shiru ba na son ki sake zubar da hawayen ki kina jina?"

"Eh Dady." Ta amsa mishi tana ƙoƙarin share hawayen fuskarta jikinta sai faman rawa yake yi

"Yanzu mai Likitan yace ne? Kuma ina Mijin nata?" Yayi maganar yana kallon Fauziyya

"Eh tun safe dai da ya tafi bai dawo ba, kuma likita yanzu ya fita yace tunda jinin ya tsaya ko zuwa anjima da dare za a iya sallaman ta."

Jinjina kansa yayi yana ɗan jan numfashi kaɗan, sai yayi shiru kuma yana kallon Intisar da ke faman kokuwa da hawayenta da suka ƙi tsaya wa. "Dama yanzu zan wuce in ɗauko Mama ne mu taho tare, kuma sai na ga ya dace in fara zuwa tunda ban zo ba na kira wayanki ba ki yi peaking ba?" Ya ƙare maganar yana kallon Fauziyya

Ita kuma ta ɗan yi yaƙe tana ɗago wayan nata tare da duba wa, sai tace, "wlh ban gani ba, hankalina duk a tashe yake ina nan Intisar na ƙara min damuwa da kukan ta, ban san ka kira ba."

"Ok bari in wuce in ɗauko Maman, sai na dawo." Sai ya shafa kan Intisar yana ƙara bata haƙuri tare da kwantar mata da hankali

Yana fita Fauziyya ta sauke ajiyan zuciya

Ita kuma Intisar wani sabon kukan ta fashe da shi tana yarfe hannu, don ta san muddin Dadyn ta ya san abun da ta aikata da kuma mutuwar auren ta tabbas kashin ta ya bushe, wlh sai yanzu take dana-sani, zuciya ta kaita ta baro, bata yi zaton zai sake ta ba, "wayyo Momy don Allah ki taimaka min kar Dady ya sani, kashe Ni zai yi."

Ganin yanda ta shiga tashin hankali sai ɓarza kuka

Please Login or Register in order to submit comment