Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya burma cikin toilet ba yana bugo ƙofan

Hakan yasa Aliyu da ke bakin ƙofa shigowa jin ƙaran buga ƙofan. Sai dai yana shigowa idanuwansa suka sauka a kan Zeena da ke tsaye tumɓur haihuwar uwarta tana baza idanu jikin ta sai faman rawa yake yi, yayinda fuskarta kuma ke fitar da gumi cike da zallan tsoro da firgitan da take ciki. Mamaki ne ya cika Aliyu da sauri ya sauke wayan a kan kunnen sa yana kashe wa, "lafiya Honey mene ne haka?" Yayi maganar yana nufo inda take

Ta kasa magana illa zuba mishi idanu da tayi still jikinta yana ta faman mazari

"Wai lafiya Honey mene ne haka kike yi? Me ya same ki?" Ya sake tambayar ta yana riƙo mata hannu

Daƙyar ta iya buɗe bakin ta wanda har hawayen idanuwanta sun soma ɗiga saboda tsaban tsoratan da tayi. Cikin rawan murya tace, "ba... Babu komai..."

Hankalin Aliyu ya soma tashi ganin har da hawaye a kan fuskarta, ga shi kuma duk a firgice take jikin ta sai faman rawa yake yi, mamaki ne ya cika sa matuƙa tuni ya bi ɗakin da kallo, gadon ya ƙurawa idanu sabida ganin yanda aka hargitsa shi tamkar an yi sukuwa a kai

Zeena wacce idanuwanta ke kansa tuni ta sake shiga raɗu yayinda zuciyarta ke wani irin tsallen bugu tamkar zata tsago ƙirjin ta, daƙyar ta iya ɗaurawa kanta jarumta ta soma magana sabida kar ya gano ta, sai dai kuma kallo ɗaya zaka yi mata ka gane bata da gaskiya. Cikin sauri take faɗin, "am.... Dear bincike na gama yi shi ne ... Shi ne na shiga toilet... To...to..." sai kuma ta koma soshe-soshe sabida ta rasa maganar ma daga bakin ta, kallon da Aliyu yake mata ne bata san sanda ta buɗe baki tace, "wlh shi ne naji tsoro saboda motsi naji na fito da gudu, zan yi wanka ne ma shiyasa na cire kaya."

"Haba Zeena motsin da kika ji ne za ki fito da gudu salan ki faɗi? A toilet fa kike yanzu idan kin jiwa kanki ciwo me za ki ce min?"

Jin abun da ya faɗa tuni ta soma jin sanyi a ranta har tana sauke ajiyan zuciya. A jikin sa ta sake lafewa saboda yanda ya haɗa su waje ɗaya yana shafa mata baya

"Ba na son kina irin wannan tsoratan na gaya miki, ba na son wani abu ya same ki." Yafaɗa bayan ya ɗago ta a jikin nasa

Murmushi tayi masa sai dai ta kasa yin magana saboda har yanzu a cikin tsoro take

"Nayi missing ɗin ki wlh. I love You Mata ta, ina su Sadeeq ne?" A yanzu yayi maganar yana shafa mata kyakykyawar fuskarta tare da kai bakin sa ya sumbace ta

Sai dai ita a yanda take ji baza ta iya biye mishi ba, tuni ta janye jikinta tana murmushin yaƙe da faɗin, "sun je gidan Inna, yanzu suka fita ma." Ganin yana liƙe mata sai ta sake cewa. "Dear bari inyi wanka don Allah, kaga duk na gaji nayi aiki na gaji bari inyi wanka."

"Ok." Sai ya sake ta yana juyawa kamar zai shiga toilet ɗin sai ya ja ya tsaya yana laluba aljihun sa da nufin ciro waya

Da sauri ta isa wajen sa cikin tashin hankali, murya na rawa tace, "Wai meyasa ka dawo ne bayan baka faɗa min ba?"

Kallon ta yayi na ɗan wani lokaci., Sai kuma ya saka hannu ɗaya ya shafo fuskarta tare da faɗin, "Ni naga duk kin sauya min ne, kamar kina a tsorace ko dai har yanzu tsoron ne be sake ki ba?"

Yaƙe tayi tana sosa kai, "a'a ai yanzu na dena jin tsoro tunda ka dawo. Ka je dakin ka kayi wanka kaima kafin in fito, sai in shirya maka abinci tunda ban daɗe da gamawa ba."

"Ai a nan zamu yi wankan tare. Na fi son kulawar ki a yanzu My honey, da kewar ki na dawo." Yayi maganar yana ƙoƙarin cire rigan sa

Tashin hankali.. Zeena duk ta gama ruɗewa ta rasa yanda zata yi, idan ya shiga toilet shikenan asirin ta ya tonu. Shiyasa ta langaɓe kai tare da matsowa kusa dashi sosai tana faɗin, "Ni dai a'a ka je ɗakin ka kayi naka saboda na fi son muyi sauri mu fito, idan zamu yi tare na san halin ka zamu jima kuma ina so mu ci abinci don yunwa nake ji wlh."

Dariya yayi yace, "I swear baza mu ɗau lokaci yanda muke yi ba, yanzu zamu fito."

"A'a Ni dai." Tafaɗa tana ɓata fuska ganin yana son ya tona mata asiri

To dayake shi ba me son ɓacin ranta bane, sai yace, "ok shikenan Honey yanda kike so. Ki fito lafiya bari inje." Daga haka ya sumbace ta yana ficewa

Sai da taga fitan nashi ta sauke ajiyan zuciya. Da sauri kuma ta nufi ƙofan ta leƙa sai da taga babu shi before ta ruga aguje ta shige toilet din

Hakan yasa Sadis da ke zaune a kan dakalin wanka yayi saurin miƙewa cike da tsananin tsoro, duk zufa ya gama wanke mishi fuska saboda tashin hankali da ruɗun da yake ciki. Tuni ya mayar da kayan jikin sa sai dai tsaban ruɗewa rigan ma a juye ya saka. Wani wawan numfashi ya sauke ganin Zeena ce ba wanda yake tunani ba

Da sauri ta iso wajen sa tana zare idanu kamar an kwashe wa karya ya'ya. Murya a ruɗe tace, "mu je yi maza ka bar gidan nan ya shiga ɗakin sa tun kafin ya fito."

Ko jiranta ta ƙarisa zancen be yi ba ya nufi ƙofa zai fice

Da sauri ta bi bayan shi suka fita. Sai da ta leƙa mishi kafin ya fice da sauri jiki na rawa. Tana nan tsaye a bakin ƙofan ɗakin ta tana duba ɗakin Aliyu, sai da ta ga ya fice sannan ta nufi window da mugun saurin ta ta leƙa, tana ganin fitan shi daga gidan gaba ɗaya sai ta sauke ajiyan zuciya da ƙarfi har tana lumshe idanuwa. Sai ta juya da sauri kuma ta wuce ɗakin Aliyun tana jin zuciyarta na sanyi, yau ta samu ta sha daƙyar, Allah ya so ta da bata san ya zata yi ba.







✳️✳️✳️

Shima Sadis be samu sukuni ba sai da ya ganshi a waje, da sauri ya bi hanya yana ta faman bangaza sauri yana faman waige-waige; still har yanzu hankalin sa be dawo jikin sa ba, duk a tsorace yake hakan be taɓa faruwa dashi ba, hasali ma shi be bin wata Mace gida idan har ba Zeena ba, a hotel yake iskancin sa, yau ga shi an kusa cafke shi a banza, ai ɗan ba ƙara gwara su riƙa haɗuwa a hotel ɗin zai fi, ga shi yanzu duk an koro shi wurjan-jan be gama more rayuwarsa ba, tafiya kawai yake yi yana share zufa daga fuskarsa da har yanzu zubar mishi take yi, ya kasa hawa abin hawa saboda rashin natsuwa sai bangaza sauri yake yi kamar zai kifa, sai da ya fita anguwan gaba ɗaya ya shiga titi yana ta tafiya sannan ne ya samu Machine ya haye ya wuce gida. Yana biyan sa kuɗin sa ya shige gida yana faman sauke ajiyan zuciya

Hauwa ce kaɗai a bakin ƙofar ɗakin ta tana zaune tana gyara kayan miya ta jiyo sallaman sa. Sai ta ɗago kai tana kallon sa tare da amsa mishi sallaman, "sannu da zuwa." Tafaɗa tana ɗauke kai

Shi kuma tuni ya aza murmushi a kan fuskarsa yana amsa mata yayinda idanuwansa ko ƙyafta su ba ya yi a kanta. Wanda ita bata san ma yanayi ba, haɗiye yawu yayi yana lanɗe baki tare da kama wandon sa yayi hanyar ɗaki, har a lokacin kuma ya kasa ɗauke ido a kan Hauwa sabida yanda yaga wuyan rigan ta ya zazzago yana kallon boobs ɗin ta, shi dai a rayuwa Hauwa tana matuƙar burge shi ba ƙaramin sha'awar ta yake ji ba, da zai samu dama da tuni ya dama, sai dai matsalar ya lura tana da kamun kai bazai taɓa samun haɗin kanta ba, ko kaɗan ma be ga fuskar bayyana mata abun da ke cikin ransa ba. Ɗaki ya shige ko sallama be yi ba

Inda Ruƙayya da ke bakin gado a kwance a gefen ƴarta, tuni ta ɗago ta kai duban ta gare shi, a inda tana ƙoƙarin tashi zaune take mishi sannu da zuwa cikin girmamawa

Kallon ta yayi yana wani ɗaure fuska ba tare da ya amsa ba, sai yace, "tashi ki zuba min ruwa a buta ki kai min bayi, ki zuba min ruwan wanka na shima ki kai min."

"To." Tace dashi tana miƙewa before kuma tace, "Amma ruwan babu me zafi sabida flaks ɗin ɗazu ya fashe, yanzu ma na gama girki shi ne na zuba maka tunda na san zaka..."

Tsawa ya daka mata da cewa, "dalla yi min shiru sai afkin iyayi sai kace wata me kirkin ƙwarai. Wawuya jaka ba ki iya koman ki ba, kuma flaks ɗin da kika fasa zan ga uban da zai biya za ki ci uban ki ne yanzu. Je ki zuba min ruwa ki dawo dan uwar ki."

Hawaye ne suka soma zuba daga kan kuncin ta sabida cin mutuncin da yake mata. Sai dai bata iya cewa komai ba ta wuce jiki na ɓari ta fita, ruwan ta zuba mishi daga bakin ƙofa sannan ta wuce ta kai mishi bayin. Ko kaɗan bata bari Hauwa ta hangi fuskar nata ba har ta je ta dawo ta shiga ɗakin

Sai jin saukar duka da ihun Ruƙayya Hauwa ta soma yi, bata san sanda ta hantsalar da wuƙar hannun nata ba tana miƙewa ta nufi ɗakin cikin tashin hankali da damuwa, domin ba yau suka saba ganin Sadis yana dukan Ruƙayya ba, su ke zuwa wani lokacin su cece ta musamman ma Sauda, wani lokacin kuma cikin dare yake dukan ta bayan sun kulle kofa, duk yanda suka so cecen ta su Anwar da Bilal bazai taɓa buɗewa ba, shiyasa idan har suka kulle ƙofa ma ba sa zuwa yanzu tunda ko sun je bazai buɗe ba


Hauwa na shiga ta ga yanda yake kimanta da belt ɗin wandon sa. Bata san sanda ta isa wajen ta riƙe mishi hannu tana cewa, "haba don Allah Sadis mene ne haka? Wannan wacce irin Rayuwa ce?"

Shi kuwa jin hannun Hauwa a kan nashi hannun tuni ya dakata da dukan Ruƙayyan, sai ya saka ɗaya hannun nasa ya damƙe nata irin yana son cire mata hannun nan, sai dai ya ƙi saki cike da wani irin shauƙi yake aika mata saƙon salon sa yanda zata fahimce sa, har wani lanɗe baki yake yi yana kafa mata idanu


A lokacin hankalin Hauwa na kan Ruƙayya da ke faman rusa kuka, tana shirin ƙwace hannun ta ta duƙa a gaban ta; sai jinta tayi an jawo ta ta afka jikin Sadis wanda yayi aika-aikan ba tare da shima ya san ya aikata mata hakan ba.


[23/10, 8:50 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days


9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days


Cheap in safety.👌🏼











*PAGE:16*

_____Hauwa jinta a jikin Sadis tuni ta furta, "A'uzu billahi minash shaiɗanir rajim!" Tana yunƙurawa da sauri ta miƙe jikinta na faman rawa

Sadis kuwa ganin sun haɗa idanu tuni ya narke fuska kamar me gaskiya ya soma bata haƙuri da faɗin, "don Allah kiyi haƙuri wlh ban sani ba, don Allah kiyi haƙuri kinji?"

Kanta kawai ta gyaɗa mishi tana juyawa ta fice don baza ta iya tsayuwa ba, gwara ta gudu kar ta jawa kanta matsala, daga rabon faɗa sai ta faɗa kan wani? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Duk ta rikice sabida abun da be taɓa faruwa da ita bane ganin ta a jikin wani ba Mijinta ba, shiyasa duk ta rasa sukunin ta tsoro ya cika mata zuciya

Shi kuwa Sadis da kallo ya bi ta kamar zai haɗiye ta, domin ba ƙamarin mugun daɗi ya ji ba sabida jin albarkatun jikinta a saman nashi, kamar kar ya sake ta wlh. Tana fita sai ya mayar da idanuwansa a kan Ruƙayya da tayi gefe tun ɗazu tana ta kuka domin ko rarrashin Safina ta kasa, tunda taji kukan Maman nata ta farka take ta tsala kuka. Mugun kallo ya sakar mata yana cewa, "baza ki rufe wa Mutane baki ba sai na ƙara miki mafiyin shi? Kuma ki rarrashi yarinyar nan tun kafin in zo kanki, sha-sha-shan yarinya kawai."

Da sauri jikinta na rawa ta ɗauki Safina tana rarrashin ta, yayinda hawaye ke kwaranya a kan fuskarta sai dai babu halin kuka

Tsaki ya ja yana ficewa. Sai dai ya so ganin Hauwa a waje but ganin babu ita sai ya wuce bayi. Da ya dawo ya shiga ɗakin yana ɓata fuska kamar zai kaiwa Ruƙayya duka saboda tsaban mugunta irin nasa, gaba ɗaya haushin da ya dawo dashi da takaicin sa a kanta yake son juyewa, shiyasa yake ta wani cin magani yana ɗaure fuska, tsawa ya daka mata yace, "ta je ta sake mishi ruwan ta kai mishi bayin."

Da sauri ta ajiye Safina tana shirin tashi

Ya daka mata tsawa da cewa, "zo ki ɗauke ta wa kika bar wa ita?"

Babu musu ta dawo ta ɗauke ta ɗin, duk a tsorace take sabida kar ya sake dukan ta, har yanzu zubar da hawaye take yi tana sosa bayan ta sabida azaba. Ɗaukar ta tayi ta haɗa da zanin goyo sannan ta fice. Sai da ta goya Safinan before ta sake ruwan daga murhu ta sirka mishi ta kai mishi, tana shirin shiga ɗakin ta sanar mishi; shi kuma ya fito. Harara ya sakar mata yana ɗauke kai, ita kuma tuni ta sauke kai ƙasa tana matsa mishi a hanya har ya wuce sannan ta shige ɗakin ta tana sharan hawaye.


A inda Hauwa kuwa tana ɗaki ta ƙi fitowa don har yanzu damuwar abun da ya faru da ita ya ƙi sakin ta, kwata-kwata ba ta ƙaunar ma su sake haɗa idanu dashi gaba ɗaya haushin kanta take ji, tana nan zaune har sai da taji alamun fitansa sannan ta fito ta zauna tana ci gaba da gyaran kayan miyanta, ta kasa ma leƙa Ruƙayyan taga wanne hali take ciki? daga baya kuma sai ta kwaɗa mata kira ta fito

Har a lokacin kuka take yi

Cike da tausayin ta Hauwa tace, "kiyi haƙuri don Allah wata rana sai labari, abun da yake miki tabbas ba ya kyautawa amma jarabawa ne Allah ya ɗaura miki, haka nan za ki ci gaba da haƙuri ko don rayuwar ƴarki Safina."

"Yanzu shikenan Aunty haka zan dauwama cikin uƙuban rayuwa? Shikenan Ni bani da gata? Wlh na gaji gida zan tafi bazan iya ba." Ruƙayya tayi maganar tana sake fashewa da wani sabon kukan

Inda Hauwa ta saka hannu ta dafa ta da cewa, "don Allah ki sake haƙuri gaggawa ba naki bane, kiyi ta roƙan masa Allah idan me shiryuwa ne zai sanja wata rana, dama aure ai akwai ƙalubale kala-kala, kowa yana fuskantar tasa matsalar ba ke kaɗai bace, idan kika ji na wasu za ki ce naki me sauƙi ne, kiyi haƙuri ki sake yin haƙuri Abun da zance miki kenan, sannan kuma be kamata ki zauna haka nan ba; dole ki tashi tsaye wajen nemawa Mijin ki shiriya, Mijin ki ne, idan kika tashi tsaye a kan shi ba faɗuwa kika yi ba, ki nemi taimako wajen Allah shi kaɗai a yanzu zai taimaka miki, sallan daren nan da roƙo wajen Allah Subhanahu wata'ala shi zai yaye miki matsalar ki, kinji ko? Ki riƙa yawaita karanta "Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faƙir" a duk sanda kike neman biyan buƙata wurin Allah kinji?"

Gyaɗa kanta tayi ba tare da ta iya cewa komai ba illa shashsheƙan kukan da take yi

"Yauwa to; ki share hawayen ki tun kafin Sauda ta shigo gidan ta ganki a haka kuma ta ɗaga miki hankali, kin san halin ta."

Hannu ta saka ta share hawayen

Ai kuwa sai ga Saudan ta shigo gidan da sallama tana yaye hijabin jikin ta. "Kuna nan a zaune Mutanen gidan ga?"

"Eh. Har kin dawo?" Inji Hauwa tana kallon ta bayan da ta amsa mata sallaman nata

Sai da ta samu waje ta zauna a kan kujeran zuƙuno kafin tace, "wlh kuwa. Ai mun sha yawo, Ni ce har wajen gidan ku na rantse da Allah." Sai ta yarfa hannu tana kama haɓa da cewa, "waii! Haka gidan naku ya zama? An gama komai fa, wlh gida tubarakalla, to me kuke jira har yanzu ba ki koma ba ga biki yana ta ƙaratowa?"

Murmushi Hauwa tayi tana cewa, "to ban da abun ki be ce in koma ba, har yanzu da sauran fa aiki."

"O'o O'o wlh; babu wani sauran aiki, har ciki fa na shiga, ciki dai komai an gama sai waje da ba'a gama filastan farandan ba, ina ga ma kamar tayes zasu saka, sai penti da ya rage, bayan haka babu wani abu sai komawa, shi kuwa wannan ko kina ciki za ki iya komawa wlh sai dai idan ba son komawar ki yake yi ba, sai ya bari aure ya zo ya haɗa ki da Amarya ku koma tare, wannan kuma abun da bazai taɓa yiwuwa bane wlh don idan ma kika yarda kin so ne, tashi tsaye za ki yi ki sanar mishi kawai ku koma kafin aure idan ba haka ba ke ruwa zai sha, yo ina za ki yarda ai matsayin ku ma ba ɗaya bane."

Girgiza kai Hauwa tayi tana cewa, "to ya kike so inyi Sauda? Shi da gidan sa kike son in tsara mishi yanda zai yi?"


"To ai wannan ba maganar gidan sa ake yi ko akasin haka ba, ana maganar ƴanci ne a nan, ke ce Matarsa na farko, ko kin fi so dole sai idan Amarya zata tare sannan zaku tare? Ai ba haka ake yi ba, Maman Safina gane min hanya don Allah." Ta ƙare maganar tana kallon Ruƙayya wacce ta miƙe tsaye tana ta rarrashin Safina da ke bayan ta

Murmushi kaɗai Ruƙayyan tayi ba tare da tace komai ba

Inda ita kuma Hauwa tace, "Ni dai a waje na Sauda bani da wata matsala wlh, duk sanda yace mu koma ko bayan ya kai Amaryan ne falillahil hamdu..."

"Wlh Ni kam ina rasa irin ki Hauwa, kina bani haushi kina bani takaici na rantse da Allah, ki dena irin haka ba na so, don Allah kiyi masa magana gaskiya kinga biki yana zuwa."

"Shikenan Sauda, Allah dai ya nuna mana wannan ranan, kinga rana tayi har yanzu ban yi aikin da ke gaba na ba, bari in kai markaɗen kayan miyan nan ina zuwa." Tafaɗa tana miƙewa tare da shiga ɗaki ta dauko Hijab. Sakawa tayi sannan tayi musu sallama ta fice

Ita kuma Ruƙayya tace, "bari in ɗauko miki abincin ki tun ɗazu nima na gama."

Idanu Sauda ta waro waje tace, "wai daga fita na har kin gama?"


"Wlh kuwa. Kinga yau da icce nayi amfani shiyasa yayi min sauri, bari in ɗauko miki." Ta wuce ɗakin tana ɗauko mata ta kawo mata

Hannu tasa Sauda ta amsa tana mata godiya da faɗin, "nima bari ki ga in tashi in zo in ɗaura nawa tun kafin yaran nan su dawo su fitine Ni." Sai kuma ta gyara zama tana buɗe abincin ta soma afawa tana ci gaba da surutun ta. Ƙarshe dai har Hauwa ta dawo ta ɗaura nata miyan but Sauda tana nan zaune tana ta zuba labari. Sai da ta ga yaran sun shigo sannan ta miƙe tana faɗin, "oh Ni Saude, ga shi hira ta ɗauke min hankali har yaran nan sun dawo ban yi komai ba, kai Allah ya kyauta... Kai Sulaiman je ka cire muku kayan ku zo ga wannan abincin ku ci kafin in gama."

"To Mama." Sulaiman ɗin yafaɗa cikin zumuɗi yana yin hanyar ɗakin su da gudu

Shima Haidar sai ya bi bayan shi yana ƙoƙarin cire rigan sa but ya kasa, sai ya zare wandon kawai ya yasar a wajen ya shiga ɗakin yana kiran sunan Sulaiman da cewa, "Yaya cire min rigan".







✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


Kamar yanda Sauda ta faɗa ne; domin maganar nata ya tsaya wa Hauwa a rai, shiyasa itama ganin shiru-shiru basu da alamun tare wa ga shi har biki ya gabato, saura sati Uku yanzu, kuma komai na gidan an gama, shiyasa ta yi wa Anwar maganar tarewan su tunda ta ji shiru bai ce mata komai ba, kuma itama ta zuba ido domin ta ji yayi magana, ga shi ta saka rai ƴan uwa sai yin mata maganar tarewan su suke yi, wai, "yaushe zasu tare?" Sai dai ta ce musu, "da saura ai." Yanzu kuma shiyasa ta tambaye shi domin ta ji daga bakin sa

Amma kuma abun da Anwar ɗin yace mata, wai, "sai dai ta bari biki ya zo ana gobe sai ta tare, hakan zai fi domin ba ya son gidan ya soma ɓaci da wuri."

Duk da haƙurin Hauwa; sai da ranta ya ɓaci sabida jin furucin sa, tsaban yadda take ji a cikin ranta shiyasa ta kasa mishi magana tayi shiru kanta a ƙasa

Sai ya sanya hannu ya ɗago mata kan yana cewa, "ah ah! Ya naji kin yi shiru kuma? Ko ba ki ji me nace bane?"

"Na ji." Ta furta tana sake kawar da kanta domin ta kasa ɓoye halin da take ciki, tuni hawaye sun soma ciko mata ido, Allah da ikonsa kuma bai samu damar gani ba, a lokacin wayansa ta soma ƙara, shiyasa ta samu damar share wa har da su shashsheƙa sabida ganin ya matsa yana duba kayan da zai saka

Dama fita zai yi shine ya zauna cin abinci, ita kuma ta samu damar faɗa mishi. Bai sake zama ba ya saka kayan ya fice bayan yayi mata sallama, ko sake bi ta kan abincin bai yi ba duk da a yanzu ya saka hannu ya soma ci

Hakan ne yasa Hauwa ta samu damar yin kukanta ma'ishi, Allah ya gani tana son Mijinta kuma tana tsananin kishin sa, ya Allah ya bata damar jure wannan jarabawar da ya tunkare ta, baza ta iya ɗaga masa hankali ba abun da yace shima ita zata bi

Shi yasa tun daga ranan bata sake bi ta kan Sauda da take zuga ta ba, ta yi kunnen uwar shegu da ita sai dai ta bi ta da idanu idan tana zancen. Yanzu matsalarta ma Sadis ne da ya sako ta a gaba, take-taken shi ta gama kula da abun da yake nema a wajen ta, shiyasa yanzu kwata-kwata ba ta sakar mishi fuska, ko gaisuwa ta dena mishi, ta ma dena zama a

Please Login or Register in order to submit comment