Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan a matsayin sa na Aminin Ango, shirye-shiryen da suke yi na biki shiyasa ya fice da duku-duku don su kimtsa tunda ɗaurin auren na safe ne.

Itama kuma Sauda tana gama kimtsa yaranta ta tura su Makarantan Hadda, sai ta shirya itama don ta wuce gidan bikin, sai zumuɗi take yi kamar wani bikin dangin ta

A lokacin Bilal yana zaune yana karin safe da koko, sai bin ta da kallo yake yi yana ganin ikon Allah, ganin dai har ta shirya bata ce mishi komai ba sai yace da ita, "wai ina za ki je ne kika ci uwar wannan kwalliyan? Kin san dai nima zan fita zuwa ɗaurin auren Muhseen amma ba ki sa min ruwan wanka ba kuma kina shirin fita?"

Sai da ta daidaita gyalen dake jikin ta kafin ta juyo tana kallon sa da murmushi a fuskarta, tace, "me kake ci na baka na zuba Baban Haidar? Ai bikin da zaka je nima shi zan je, kuma dama ina son in gama shirya wa ne sai in tambaye ka tunda na ga ba wani waje ka tafi ba; ga ka a gaba na ina kallon ka, ruwan wanka kuma ka duba flaks ɗina yana nan na zuba maka ka ɗiba kayi da shi. Ni zan tafi ka rufe min ɗaki idan ka fita ka ajiye min mukullin a saman kwano".

"Wai daman bikin Muhseen ɗin za ki je amma ba ki tambaye Ni ba har sai da na tambayi inda za ki je? Wannan wane irin wulaƙanci ne Saude? Dama fa kin saba min haka sai idan kin gama shiryawan ki ne kike tambaya na biki tunda kin maishe Ni bani da muhimmanci a wurin ki, ba ki ɗauke Ni Mijinki ba komai yi min kike yi, wlh kiji tsoron Allah, kiji tsoron ranan da Allah zai kama ki..."

"Subhanallah.. subhanallah.. don Allah kar kayi min baki in kasa ganin dai-dai a rayuwata da wannan mugun bakin naka, yanzu meye laifi na don na shirya na tambaye ka? Ai na ga dai na tambaye ka ɗin ba tafiya nayi haka ba? Wasu Matan da suke tafiya babu iznin Mijin nasu sai dai ya dawo ya ga ba sa nan fa? Ka ga Baban Haidar ba maganar ja'inja nake son Yi da kai ba, ina da abin yi yanzu amma idan so kake yi ayi rigiman nan; to, ka jira Ni in dawo sai mu ɗaura daga inda muka tsaya, amma Ni baza ka yi min buƙulun biki ba atoo, don wlh a kan fita bikin nan sai aji mu da kai". Ta ƙare maganar tana ɗaukan jakan ta tayi bakin ƙofa ta zira takalman ta, har ta fita sai ta leƙo tana kallon sa tace, "na san zaka riga Ni dawowa, idan yaran nan sun dawo sai ka kula da su ga raguwan kokon su nan da ɗumamen tuwo na ajiye musu, in kuma na samu dama zan aiko muku da abincin biki, sai dai duk yadda ta yiwu". Daga haka ta saki labulen ta ƙara gaba

Tsaban takaici ya cika Bilal komai bai ce ba; illa danƙwafar da kofin kokon da yayi ya miƙe ya nufi waje don ɗauko bokiti ya ɗibi ruwan wanka shima ya shirya ya tafi.







✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


Da ƙarfe 10:00am. Dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren Muhseen Ya'u da Amaryan sa Munira Shitu Ubaidullahi, inda Abokan Muhseen na school ɗin su suka shirya musu ƙwarya-ƙwaryan liyafa da za'a yi da yammacin ranan a sabon gidan sa, kasancewar gidan da akwai fili sosai, don babba ne gidan sa, sai dai kasancewar be daɗe da fara aiki ba shiyasa ya ɗan ɗiba kaɗan yayi ginin sa dai-dai wanda zasu zauna da Matarsa, ɗakuna biyu ne kaɗai da kichen da Toilet, sai sauran filin da har an soma gini, nan zasu koma idan an gama, inda kuma zasu zauna ya gina ne dama saboda mahaifiyar shi, idan sun tashi sai ta komo nan su zauna tare da ita da ƙannin sa biyu Mata.





✳️✳️✳️✳️✳️


Ƙarfe huɗu na yamma aka kai Munira gidan Muhseen, sai da aka fara kai ta gidan Umman shi kafin aka wuce da ita, suna zuwa suka soma shirin Partyn da aka shirya za'a yi a gidan, don har ma an gyara wajen an shirya komi mutane sun soma halarta

Cas amarya Munira ta fito cikin English Gown ɗin ta da yayi mata matuƙar kyau, ba ƙarya Munira ba baya ba wajen kyawu. Su Afnan sai tsokanar ta suke yi suna dariya

A lokacin ne Ango Muhseen suka shigo da sauran Abokan sa. Kasancewar tare ake son su isa wajen, Kayan jikin su kala ɗaya ne sosai suka yi kyau gaba ɗayan su

Abokan Ango da ƙwayen amarya fita suka yi suka bar su bayan sun gama tsokanar juna

Muhseen matsowa kusa da Muniran yayi ya riƙo hannayen ta yana bin ta da kallo

Ita kuwa kanta a ƙasa sai zuba murmushi take yi

Sun jima a haka babu wanda ya iya tanka wa, illa shi da yake ta matsa mata hannaye still yana bin ta da kallo. Daƙyar dai ya buɗe baki ya furta mata, "kin yi kyau Baby na".

Sai a lokacin ta samu damar ɗago da kanta ta sauke idanuwanta a kanshi, a tare suka sakar wa juna murmushi a hankali itama ta furta mishi, "kaima kayi kyau sosai Mijina".

"Allah ko?" Ya faɗa yana murmushi me fidda haƙora

Gyaɗa masa kai kawai tayi

Sai ya ɗago hannun ta ɗaya ya sakar mata kiss kafin ya janyo ta jikin sa suka soma tafiya zuwa waje.





A time ɗin gidan ta cika maƙil da mutane, ta kowanne fanni kowa da mutanen sa, musamman ma Munira me mutane, don ita kowa nata ne, duk ƴan anguwan su babu wanda be zo mata murna ba. Su Sauda ana wurin duk inda Hauwa ta saka ƙafa tana biye da ita, ta zama dai tamkar ita ce ma dangin Angon, don yanda ta zage tana taya su aiki har sun saba da ita, komai su ce, "Sauda... Sauda...". Dama haka take so ai a nan ta fi auki, abinci kuwa babu wanda bata loda ta kai gida ba, nan ma da biyu ta zo ko Allah zai bata dama ta samu ko ɗan kaza ne a cewar ta 😂, sai kace bikin wasu ƙusoshi, a irin nan ina za'a ga kaji ban da rashin hankalin Sauda?. 🙄


Bayan MC ya gama surutan sa na koɗa Amarya da Ango; sai aka kira Afnan ta bayar da tarihin Amarya

Nan kuwa ta fito tana karairaya cike da farin ciki ta amshi abun maganar ta soma bayar da tarihin Munira

Kowa yayi tsit ana sauraron ta

A side ɗin Anwar kafe ta yayi da ido kawai yana kallon ta yana murmushi saboda kyan da tayi masa a yau ɗin, ta fita daban a kowane rana da yake ganin ta, tamkar dai yau ya soma tozali da ita haka yake ji a ransa, sai kuma ya faɗa tunani har ta gama bai san ma ta gama ɗin ba. Sai da Ango ya taɓo sa sannan ya dawo hayyacin sa

Ɗaga masa gira yayi yana murmushi yace, "kai mista Love ana fa magana, ko har yanzu baka gama kallon nata bane?"

Murmushi shima yayi yana shafa gefen fuskarsa. A lokacin ya sake jin an kira sunan sa ashe ana ta kiran sa be san ma ana yi ɗin ba. Tashi yayi da sauri ya wuce shima ya bayar da tarihin Ango a matsayin sa na babban Abokin sa.



Ta fannin Hauwa da ta hangi Mijinta itama sai zuba murmushi take yi tana kallon sa; cike da tsantsan soyayyarsa a ranta

While haka ma Afnan, har nuna sa take yi wa sauran friends ɗin su tana cewa, "shi ne wanda take burin ta aura".




Bayan ya gama ya koma ya zauna aka ci gaba da shagulgula. Kowanne table an sauke musu kayan motsa baki sai brush suke yi da naman kaza

Hakan kuwa Sauda take so, domin tana a cikin masu rabon ma shiyasa duk ta ƙunshe su a cikin leda ta kai ta ɓoye a cikin gidan, da zummar idan an gama sai ta kwashe ta wuce gida. Dawowar da zata yi wurin taron ne ta haɗu da Afnan da Anwar suna magana, sai murmushi suke yi kai da gani ka san masoya ne sosai

"Kan bu... Wannan ba Mijin Hauwa bane?" Tafaɗa tana sake ware ido a kansu har da mitstsike wa. "Lallai kam Namiji shu'umi! Duk yanda ka kai da kyautata masa sai ya ci amanar ka, ji be yanda ya samu wata ƴar shila yana washe mata baki, kamar a kunnen Hauwa kuwa". Sai ta kaɗa kai tayi gaba zuwa bayan gidan da ake taron. Neman Hauwa ta soma yi don ta sanar mata ta zo ta gani da idanunta domin hakan zai fi mata. Daƙyar ta same ta kuwa babu ɓata lokaci ta janyo ta suka yo wajen da ta ga su Afnan

Hauwan na tambayar ta, "mene ne?"

Amma ce mata take yi, "taho dai mu je ki gani da idanunki tukun sai in miki bayani". Haka ta ja ta har wajen; sai dai wayam babu su a wurin. "Kuttruuu.. wlh a nan na gansu. Ina suka yi to?" Tafaɗa tana kalle-kalle

"Wai su wane ne ki min bayani mana?" Inji Hauwan cike da ƙosawa

"A nan na ga Mijin ki da wata budurwa suna soyayya, al'ƙur'an Hauwa da idanuna na gansu ba ƙarya na miki ba daga gani kin san masoya ne, na so ki gani da idanunki amma kuma babu su a wurin".

Kallon ta kawai Hauwan take yi, sai kuma ta ɗan ja numfashi kaɗan tace, "to Ni Sauda me zance miki?"

"Dama na san ai baza ki yarda ba, amma na rantse da Allah Anwar na gani da wancan yarinyan da aka kira ta bayar da tarihin Amarya, kin gani ko? Maza basu da amana ko kaɗan, duk yanda kika yi da kyautata masa sai ga shi a wurin da kike ma yake son cin amanar ki, wa ya sani ma ita zai aura..."

Hauwa katse ta tayi da cewa, "ya isa don Allah, daga ganin su suna magana sai ki ce soyayya suke yi? Haba Sauda ki riƙa ma Mutane adalci mana, kika sani ma ko wani abun ya haɗa su kina fa gani shi Abokin Ango ne ita kuma ƙawar Amarya ce, to don kin gansu tare ba zai saka ki kawo zargi ba. Idan ma budurwan nasa ne Allah ya sanya alheri iyakan abinda zance kenan". Ta ƙare maganar tana wuce wa ta bar Sauda da sakakken baki

"Kutmar uba! Ni Hauwa za ki watsa wa ƙasa a ido? To shikenan a juri zuwa rafi wlh watarana ai tulun zai fashe, za ki ce na gaya miki ranar da kika gano yana cin amanar ki, ranar kuma da ya nuna miki halin su na Maza". Sai tayi ƙwafa tana wuce wa ciki. Sai da ta sake zuwa ta samo wasu abubuwan na bikin kafin ta je ta ɗauko wanda ta ɓoye tayi gida ko sallama bata yi ma Hauwa ba. A lokacin ma har magriba ta gabato don su ma suna ƙoƙarin tashi ne.



Kowa ya watse sai ƙawayen Amarya da Amaryan da aka bari a cikin gidan, su ma su Ango sun wuce masallaci

Itama Hauwa sai a lokacin ta wuce gida.




Sai bayan sallan isha'i Abokan Ango suka zo siyan baki, haka suka shantake ana ta hira har da Amarya, dayake akwai ta da surutu ba ta iya ganin ana hira bata saka baki ba, ko irin kunyan nan na Amare bata dashi don bata nuna ba

Sai da suka gama hiran ne suka siyi baki sannan suka musu sallama. Abokan Angon su suka ɗauki su Rahma. Ɗaya daga cikin su kuma ya haɗa da Afnan da Anwar ya wuce da su gida, ita aka fara sauke wa, sai da suka jima suna hira da Anwar ɗin kafin suka tafi, shima aka ƙarisa dashi gida.
[05/09, 4:45 pm] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*










*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*PAGE:6*

_____ *WASHE GARI*
Wajen ƙarfe 12:00pm. Ƙannin Muhseen suka zo gidan, dayake yana Parlour a zaune da ya ji Nocking ɗin su shi ne ya je ya buɗe musu

Gaishe shi suka yi a tare cike da girmamawa

Ya amsa su yana cewa, "ku shigo mana".

Shiga suka yi suka zauna a kan kujera

Shi kuma da ya rufo ƙofan ya dawo ya zauna yana cewa, "Ya Umma fatan tana lafiya?"

"Lafiya lau. Ita tace ma mu zo mu sanar maka su Kawu Shu'aibu zasu tafi kuma sun ƙi biyo wa ta nan, sannan an kira wayan ka a kashe". Cewar Babbar me suna A'isha

"Ok wayata babu caji ne wlh, amma bari in shirya sai mu wuce tare, kodayake ku zauna da Auntyn ku har in dawo before ku tafi tunda na san ba wani abun kuke yi ba ko?" Yayi maganar yana kallon su

Murmushi suka yi suna amsa masa a tare

Tashi yayi shima yace, "bari in Kira muku ita". Ya wuce cikin bedroom ɗin su. Yana shiga wajen gadon ya nufa inda Munira ke kwance ta ƙudundune jikin ta a blanket tana ta sharan barci. Zama yayi a gefen gadon yana ɗaura hannu a saman fuskarta ya soma shafa mata, sai kuma ya matso da fuskarsa yana kiran sunan ta a hankali

Buɗe idanuwanta tayi ta zuba masa su

"Please Wifey ki tashi haka nan, tun ɗazu ina tashin ki but da zaran na fita sai ki koma ba kya gajiya ne?"

Tura baki tayi tana ƙara gyara wa da cewa, "uhm Ni barcin be ishe Ni ba wlh, ka bari in ɗan ƙara kaɗan".

"A'a tashi haka kin san yanzu ƙarfe nawa ne? Twelve twenty fa. Please wake up idan ba so kike yi a sake miki wani daren ba, ga su A'isha can ma sun zo".

Jin hakan yasa ta sake buɗe idanuwanta da ta mayar ta rufe, "da gaske Husband?" Tayi maganar cikin farin ciki

"Ƙwarai kuwa, ki je ki duba ki gani, sun zo kira na ne su Kawu zasu koma ƙauye, zan bar miki su in je in dawo kinji?"

"To".

Shima kuma tashi yayi ya nufi sif ɗin kayan su ya ciro riga da wando na shadda sababbi gau; waɗanda ma ko saka su be yi ba, jallabiyan jikin sa ya kama zai cire

Sai Munira tayi saurin sauko wa daga kan gadon tana shige wa cikin Toilet

Dariya yayi kawai yana cewa, "Wifey kenan". Sauya kayan yayi ya nufi gaban mirror ya fesa turaruka sannan ya ciro takalman sa ya saka. Har ya gama tana ciki bata fito ba sai ya ɗaga murya yana cewa, "Wifey na tafi tunda baza ki fito ba". Daga haka ya juya ya fice da sauri. Koda ya fita parlour'n kallon su A'ishan yayi da suke zaune suna ɗan magana a tsakanin su, yace da su, "ga ta nan fito wa, ta shiga Toilet ne".

"To Yaya".

Daga haka fice wa yayi ya rufo musu ƙofan.




While Munira yana fita ta fito daga Toilet ɗin, wanke fuskarta kawai tayi ta ɗaura dogon Hijab a saman rigan barcin nata sannan ta fice. Da fara'a ta isa wurin su tana zama da cewa, "Aunty Aisha, Amina sannun ku da zuwa, ina kwanan ku?"

Dariya suka yi

A'isha tana cewa, "haba Auntyn mu don Allah ki dena ce min Auntyn nan Ni na bar miki girman wlh, ba ki ga ke Matar Yaya bane don Allah ki dena".

"A'a Ni dai bazan dena ba, taya zan iya kallon ki in Kira ki da sunan ki bayan kin girme ni? ai be dace ba kiyi hakuri kawai".

Ita kuma A'ishan tace, "Ni kuma bazan amsa ba wlh, Ni dai ba na so ke ce Aunty na".

Amina na dariya tace, "to Ni bari in raba muku gardaman, tunda kowa be yarda ba sai kuna kiran junan ku da Auntyn zai fi".

"Yauwa ƴar gari hakan zai fi kam". Inji Muniran itama tana dariya

A'isha tace, "Ni dai ba ruwana idan Yaya ya ji".

Still Munira na dariya ta tashi ta wuce wajen Fridge tana cewa, "ai babu abinda zai ce ma tunda ya san hakan nake ce miki". Drinks ta ɗauko ta kawo musu ta cika musu gaba da shi, sannan ta wuce ɗaki ta ɗibo musu alkaki da aka haɗo mata da shi tun jiya, ta ajiye musu tana zama tare da cewa, "to Bismillan ku, idan kun gama sai ku sanar min abun da kuke son ci in shiga in girka muku".

Amina tace, "kai Auntyn mu wannan ma ya isa, ina mu ina saka ki girki daga kawo ki?"

"To mene ne a ciki? Idan ban muku ba waye zan yi ma?"

"A'a mun gode wlh, wannan ma ya isa". Suka haɗa baki wajen faɗi

Dariya tayi kawai tana cewa, "to ku ɗauka ku ci kun bar shi, ya Umma na?"

"Lafiya lau tana gaishe ki sosai wlh".

Daga haka dai hira suka ci gaba da yi Munira sai jan su take yi a jiki, dama ita gwana ce wajen magana da son mutane, dole ne idan ka zauna da ita a ɗan ƙanƙanin lokaci ko baka santa ba sai ka saba da halin ta, tana da yawan faram-faram da jama'a kowa nata ne, ga ta da son kyauta komi ta samu na mutane ne, shiyasa ko ba ka wa Allah Idan ka zauna da ita sai ka so ta saboda Halin kirkin ta.







✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


Saukar marin da Hafsah ta ji a kan kuncin ta yasa ta saki ƙara tana duƙe wa ƙasa tsaban gigita

"Dan kutumar uban ki ban faɗa miki ba na son yaji ba? uban meyasa kika saka min? So kike yi ki kashe Ni Ko?" Intisar tafaɗa cikin hayagaga da ihu

Dalilin da yasa Sumayya da Jibril dake parlour zaune suka rugo a guje don ganin meke faruwa

"Lafiya Aunty Intisar me tayi miki?" Cewar Sumayya kenan

"Wannan banzan yarinyan ce ta saka min yaji a indomie, na fara ci kawai naji yaji a ciki, ba ki ji yanda baki na yake zafi ba ina ga har da mugunta ta so tayi min, useless kawai, kuma ki sake min wani tun kafin in ci uwar ki a nan wlh".

Sumayya tace, "ai ba haka za ki yi ba, ki saka ta ta cinye wannan ɗin tunda ita muguwa ce sai ya ƙare mata. Ɗauka ki cinye shi yanzu nan ko muyi miki dukan tsiya". Ta ƙare maganar da daka mata tsawa

Tuni Hafsan ta sanya hannu jiki na rawa yayinda hawaye ke zubar mata saboda azaban marin da ta sha, haka ta soma kaiwa baki zuciyarta na ƙuna hawayen idanunta na ƙara gudu har da su majinu; saboda zafin indomien da zafin yajin da ke ciki

Shi Jibril tuni ya juya ya fice don be cika shiga shirgin su ba

While su kuma sun tasa ta gaba sai zagin ta suke yi suna tsinanta. Babu wanda ya ji tausayin ta har sai da suka ga ta cinye tass kafin Intisar tace da ita, "kinga gobe sai ki sake maimaita min abinda kika min don Allah, kar ki fasa haka nake so, na ba ki mintuna goma ki girka min wani ki kawo min ɗaki tun kafin in ci uban ki, ƴar ƙauye kawai".

Sumayya har da dungure mata kai kafin suka juya suka fice. Intisar ɗaki ta shiga ita kuma Sumayya ta zauna a Parlour tana ci gaba da kallon ta

Fitowar Fauziyya daga ɗaki take tambayar, "ina Hafsan ta gama girkin?"

"Ina fa bata gama ba, yanzu ma Aunty Intisar ta sanya ta ta girka mata indomie ta je ta cika mata yaji a ciki".

"What...! Yaji? Zata kashe min yarinya ce? Ina take dan uban ta?" Sai kuma ta juya da sauri ta wuce kichen ɗin tana kwaɗa mata kira

Hafsah dake ta matsan hawaye; jiyo muryan Fauziyya ai sai jikin ta ya soma rawa duk ta takure waje ɗaya

Tana zuwa kuwa ta wanka mata mari da cewa, "za ki kashe min yarinya ce ke jahilan ina ce? Kina hauka za ki kashe min ƴarinya?" Duk ta karaɗe kichen ɗin da ihun ta tana zagin Hafsan da a yanzu sai kuka take yi sosai

Hayaniyan ta ne ya fito da Jamal dake kwance a ɗaki daga shi sai Singlet da gajeren wando, kichen ɗin ya nufa ba tare da ya kula da su Sumayyan ba ya nufi can jin a can ne yake jin hayaniyan. Da shigan shi ya ga Fauziyya ta rufe Hafsah da Duka, da sauri ya ƙarisa hankali a tashe ya riƙo ta yana faɗin, "Fauziyya meye haka me kike yi ne? Lafiya me tayi miki?"

Cike da bala'i tace, "ba ka gani kashe min yarinya zata yi. Intisar ta saka ta tayi mata indomie kuma ta san ba ta son yaji amma ta zuba mata; tunda so take yi taga bayan ta, to Ni kafin ta kashe ta gwara Ni in kashe ta".

"Fauziyya ban son hauka kinji ko? Idan ta zuba mata yaji meyasa ta saka ta girkin bata da hannu ne ita? Kullum yarinya tana muku bauta amma kullum sai kun ci zalun ta haka ake yi ne? Daga yau tunda bata iya muku abinda kuke so ba ku dena saka ta amma ba na son na sake gani kin dake ta a gidan nan tunda ba baiwar ki bace".

Cike da ɓacin rai tace, "kana so ka nuna min cewa abun da tayi laifin mu ne wato? Idan ta kashe min yarinya baka da asara ko? To wlh bazai yiwu ba dole ne sai dai ta bar min gida tunda baza ta yi mana amfani ba".

Guntun tsaki ya ja yana kallon Hafsan da cewa, "ke taso ki wuce, ba na son kukan nan haka ya isa kiyi haƙuri. Daga yau kin ga sai ki ci gaba da girkin ki tunda ita ba baiwa bace". Ya tasa ƙeyar Hafsan kamar wata yarinya suka fice. Har waje ya raka ta yana shirin bin bayan ta sai ya tuna babu kaya a jikin sa. Dakata wa yayi yana kiran sunan ta

Kanta a ƙasa ta amsa mishi tana me ci gaba da shashsheƙan kukan ta

"Ki dena kuka kinji insha Allahu daga yau baza ki sake mata bauta a gidan nan ba, zan yi maganin abun ki je ina zuwa sashin".

Gyaɗa masa kai tayi tana wuce wa can sashin su

Tana shiga Mama da ke kan dadduma tana lazimi tana jiran a kira sallan azahar ta gabatar, tana kallon ta sai ta hau tambayar ta, "lafiya Hafsah me ya faru? Ko wani abun suka yi miki?"

Kuka ta saka tana durƙushe wa a gaban ta tare da ɗaura kanta a saman cinyoyin ta tace, "Inna wlh Ni na gaji ƙauye zan koma." Ta ƙare maganar tana sake fashe wa da wani sabon kukan

Ɗago kanta tayi Maman duk a rikice take cewa, "wai me suka yi miki faɗa min don Allah?"

Bata kai ga magana ba Jamal ya shigo da Sallama

Mama ta amsa mishi tana kallon

Please Login or Register in order to submit comment