Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take yi, shiyasa itama ta ɓoye nata damuwar tana rarrashinta tare da ce mata, "insha Allahu babu abun da zai faru, saki dai an rigada an yi, amma zata san yanda zata yi har ta koma ba tare da Jamal ya sani ba."
Sosai ta kwantar mata da hankali tana ta bata baki a kan zasu shawo kan komai

Nan fa Fauziyya ta fita ta bar Intisar ɗin tace mata, "zata je ta dawo." Domin bata ga ta zama ba, gwara ta je gidan su Shureim ta neme sa da kanta.
[06/01, 8:55 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*






                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:34*

_____Lokacin da Jamal ya isa gidan; har Mama ta gama shirya wa tana faman jiransa tunda ya faɗa mata, "yanzu zai zo ya ɗauke ta."
Dayake lokacin karfe biyar da rabi ne Hafsah tana Islamiyya, duk da ta san abun da ya sami Intisar ɗin kasancewar a gabanta Jamal ya kira Mama yana sanar mata, tayi tunanin ma zai zo da wuri ne sai su tafi tare, amma har lokacin islamiyya yayi bai zo ba shiyasa ta shirya ta tafi abun ta


Shi kansa koda ya zo sai da ya tambayi Mama ina Hafsah? Don yanzu yana kulawa da ita sosai, duk da kunyarta yasa har yanzu ta kasa sakin jiki dashi, amma a yanzu yana jinta a rai matuƙa, ba ya iya sukuni sai ya zo ya ganta ya ji daɗi,
Ita kanta har ta fahimci irin sintirin da yake yi a gidan su yanzu, da kuma yanda ya canza mu'amalan su a yanzu yana yawan shige mata, ta rasa yanda zata yi, wani lokacin ma shi yake kaita islamiyya

Hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake yi wa Mama ba kasancewar yanda ta ga Jamal na damuwa da Hafsah sosai, tana fatan a ce ta shiga ransa ya ƙaunace ta matuƙa, ko don kar ta shiga gidan shi ta rasa galihu, gwara a ce yana sonta zai iya yin komai sabida ita, sannan zai bata kula wa sosai

Yana zuwa suka wuce da Mama asibitin, a lokacin da suka je ma sun tarar da wasu daga cikin dangin Fauziyyan Maza sun zo gaishe ta, ita kuma Fauziyyan bata dawo ba

Jamal yayi mamakin ganin babu ita, ya tambayi Intisar ɗin inda ta je?

Ita kuma duk ta ruɗe ta rasa me zata ce mishi

Wayansa ya ciro ya fita waje ya soma kiranta, but bata yi peaking ba, har sau biyu ya kira amma bata ɗauka ba, shiyasa ya haƙura ya koma cikin ɗakin; yana mamakin abun da yasa ta fita ta bar Intisar ita kaɗai bayan ta san tana cikin halin rashin lafiya.
***


      Inda ita kuma tana can ta yi wa gidan su Shureim tsinke, part ɗin Intisar ta soma wuce wa ta kwankwasa ƙofan

Mai aikinta ta fito ta buɗe mata, tana ganin ita ce ta zuƙuna har ƙasa tana mata sannu tare da gaishe ta

Fauziyya bata amsa mata ba sai duban ta da tayi tana cewa, "Shureim na ciki?"

"Eh Hajiya, yana ciki."

"Ok." Sai ta wuce yarinyar; ta shiga ciki tare da faɗin, "zo ki kira min shi."

Da sauri yarinyar ta mayar da ƙofan ta rufe before ta wuce da hanzari ta nufi ɗakin Shureim, a bakin ƙofan tayi masa nocking sannan ya fito

Kafin ma tayi magana har ya hangi Fauziyya, hakan ne yasa ya fito yana duban ta, duk da ba ya cikin walwalan sa hakan bai sa ya ƙi sakin fuskarsa ba, yace, "sannu da zuwa Momy."

Bata amsa mishi ba sai ta jeho masa tambayar, "Shureim wai wanne irin saƙo ne ka aiko mana a asibiti? Kanka ɗaya kuwa?"

"Kamar ya kaina ɗaya?"

"Ina nufin me Intisar tayi maka da har zaka sake ta irin wannan sakin wulaƙancin? Tana halin rashin lafiya amma da sakamakon da zaka saka mata kenan? Har ka iya aiko mata da saki har asibiti sabida baka san muhimmancin ta ba? Yanzu hakan da kayi ya dace?"

Da tsananin mamaki yake kallonta sabida jin furucin ta, sai yace, "Momy ita ba ki tambaye ta abin da ta aikata bane? Ko kuwa Likitan bai yi miki bayanin abun da ya faru bane?"

Nuna wa tayi kamar bata sani ba, sai tace, "a'a Ni Likita bai faɗa mana abun da ke faruwa ba, amma ko ma mene ne meye gamin haɗin bayanin likita da sakin da ka yi wa ƴata? A tunanina duk abun da Intisar zata yi maka ta fi ƙarfin ka yi mata wannan sakin wulaƙancin, ko ka manta yanda aka yi auren nan ne? Yarinyar nan ta bar komai nata at this age nata; ta zaɓe ka, sannan kuma da sakamakon da zaka saka mata kenan ko? Yanzu me kake so muyi kenan?" Ta ƙare maganar a ɗan zafafe tana tsare sa da idanu

Sai yace, "ina ga ba ki san me Intisar ta aikata min bane shiyasa har kike ganin laifi na, cikina gudan jinina ta zubar min fa; kina ganin zan iya ƙyale ta ne in kasa ɗaukar mataki; ko kuma kina ganin zan iya ci gaba da zama da ita ne?"

"Kai ka tabbatar ita ta zubar maka da cikin? Cikin da ya zube da kansa amma zaka laƙaba ma ƴata? Ashe sharrin da zaka yi mata kenan? Kuma ba saki ɗaya ba har saki biyu shi ne sakamakon ta?"

"Momy Ni fa gaskiya ki dena ɗaura min laifi ko ki yi tunanin na zalunci ƴar ki, meyasa baza ki tambaye ta abin da tayi min bane? Likita kuma ai bazai min ƙarya ba, ita da kanta tayi iƙirarin sai ta zubar da cikin, kuma ga shi result ya nuna magani ta sha cikin ya fita, to me kike so in yi mata? Tunda ta nuna ba ta son zama dani ba ta son ɗan da zan haifa, babu amfanin ci gaba da zama da ita, wannan ma nayi mata ne don kawai babu kyau saki Uku lokaci guda, amma wlh da tuni na rubuta mata dukka ukun, domin ba na fatan Intisar ta dawo gidana ta ci gaba da zama, alaƙar mu gaba ɗaya na yanke ta, in fact ma daga yau kar ku sake nuna kun sanni since ba wata alaƙa tsakanin mu."
Sai ya juya ya wuce ya shige daki ya garƙame kofa ransa a ɓace saboda ganin rainin hankalin Matar

Yayinda Fauziyya ta cika da mamakin sa har ta kasa yin magana bare ta tsayar dashi, lallai wannan Yaron, ta ga karfin halin sa da ya zauna yana gaya mata magana, amma kuma tun farko ita ta ja; da ta bi shi da lallama da ba haka ba, ta yiwu ta lallaɓa shi ya dawo da ita, yanzu ya zata yi?
Dole ba don ta so ba ta fita ta koma asibitin,
Lokacin su Mama sun wuce babu kowa sai ita Intisar ɗin tare da Sumayya

Dama kamar jiranta take yi tana shigowa, sai Intisar ɗin ta soma tambayarta inda ta je?

Numfashi ta ja bayan ta zauna, tana kallon Intisar idanunta duk sun sauya kala sun kumbura, ita kanta Fauziyyan zullumin da take ciki nata idanun haka suka koma, ko da gani ka san suna cikin tashin hankali, "ki mayar da hankali ki samu lafiya shi ne kawai burina a yanzu Intisar, ko me zai biyo baya zan ji dashi insha Allahu, matsalar Dadyn ku kuma mai sauƙi ne na san ta hanyar da zan ɓullo mishi, ke ina kika bar Jibril kika taho ke kaɗai?"

Sumayya tace, "yanzu suka fita da Dady, ya bi su sun tafi gidan Mama."

Kanta ta gyaɗa tana sake mayar da idanunta a kan Intisar da ke hawaye, "wai kukan na mene ne Intisar? Ba na ce kiyi hakuri ba? Ai aikin gama ya gama tunda har matsiyacin ya sake ki, dama bai gaji arziki ba; ba shi da kirki bare mutunci, bai san darajar ki ba, wannan ma ko nan gaba wlh baza ki koma gidansa ba, kuskuren da nayi kawai shi ne yanzu ya mayar min da ke ƙaramar bazawara, don haka ba na son kukan nan naki tun kafin raina yayi ƙololuwar ɓaci in ɗauki mataki a kanki, baza ki kasa min hankali biyu ba."
Sai ta ja dogon tsaki tana miƙe wa cike da masifa ta ci gaba da sababin nata duk ranta a ɓace, toilet ta shiga ta fito sannan ta kalle su tace, "bari in koma gida in yi girki, ke kuma Sumayya ki zauna da ita, in Dadyn ku ya sake biyo wa ta nan ku faɗa masa na koma gida yin abinci."
Gyalenta ta yafa bata bi ta kansu ba koda suka amsa mata, ta fice a dakin da sauri tana lissafin mataki da hanyar da zata bi domin samun mafita,
A tunanin ta hanya ɗaya ne shi ne; rufe bakin Jamal kar shima ya ɗauki mataki a kansu, shiyasa ta bazama kanta tsaye gidan Yayarta Aunty Salaha, don ita take amso mata duk wani magani da take amfani dashi domin ganin ta mallake Jamal, tunda Aunty Salahan tana da Malamin da yake mata aiki, iyakan Fauziyya sai dai ta bata kuɗi ta faɗa abun da take so; ita kuma Aunty Salaha sai ta je da kanta

Amma yanzu da ta isa gidan Aunty Salahan, bayan ta kora mata bayanin abun da ke faruwa, tace mata, "gwara a yau su tafi tare ta yi wa Malamin bayani da kanta, don idan har Jamal ya san abun da ke faruwa kashin ta ya bushe, tunda ya ce muddin auren ƴarsa ya mutu tamkar nata ne ya mutu, don haka ta taimaka mata su je tare tayi masa bayani."

Ba ɓata lokaci Ummu Muhseen ta canza kaya ta figa gyale suka wuce wurin Malamin

Burin Fauziyya kawai ta samu hanyar da zata rufe bakin Jamal, shiyasa bata damu ta koma gida ba bare tayi girkin kamar yanda tace, ga nisan wurin sai da suka kai bayan magriba sannan suka isa ƙauyen, haka Fauziyya ta zayyane mishi duk abun da ke faruwa da kuma matakin da take so a ɗauka a kansa. Na farko a rufe mishi bakin sa gam ko da ya san da sakin ƴarsa kar ya ɗauki mataki, sai kuma na mallaka da take so ta mallake shi ya dena mata faɗa ya dawo a tafin hannunta; har yanzu ta kasa samun damar mallakar sa. Duk da wannan halin da take ciki bai hana ta saka an yi mata aiki a kan Mama ba, don itama sai da ta sanya a yi musu farraƙu ya zamana ya dena damuwa da su bare ya basu kula wa, ƙarshe ma a saka wa Maman rashin son ɗanta ta ji ta tsane shi ta koma ƙauyen su

Duk wannan aikin sai da Malamin yace mata, "zai yiwu, amma sai ta jure tunda aiki ne mai wahala, ta ba shi nan da kwana uku zai tashi mata aiki ba dare ba rana, a cikin kwana uku zata ga sauyi." Sannan ya bata wasu magungunan da zata je ta zuba mishi a abinci, ta tabbatar ya ci kuma tayi tsarki da wasu ya kusance ta a daren ranan, kai ba ma mahaifiyarsa kaɗai ba kowacece bazai taɓa ganin ta a Mace ba sai ita kaɗai, sai yanda ta juya sa son ranta, ko me take so zai yi mata in har tayi abun da yace, har da wanda zata zuba wa Mama a abinci sai da ya bata maganin,
Yayinda Fauziyya ta biya sa kudin sa suka taho, ba tare da tunanin cewa aikin zai yi mata wahala ba, don gani take yi in har burin ta zai cika to ko mene ne zata iya yi.







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


               Yau kwana biyu kenan da aka kama Sadis gidan wani Soja ya je kwartanci, dama Matar customern sa ne tunda sun saba harƙalla tare, kuma Mijinta yana yin irin five to six months ba ya gari yana can an tura su aiki, hakan ne yasa take kawo masa Maza kala-kala gidan shi su kwana da ita, in taƙaice muku zance Yaranta biyar kuma duk babu nasa a ciki na kwartayen ta ne; amma bai sani ba tunda bai taɓa tunanin Matarsa tana cin amanar sa ba, kuma Mutanen gari suna tsoron su tunkare sa da maganar tunda kowa ya san me take aikata wa a anguwan nasu, ga shi shi kuma irin Mazan nan ne masu zafi abu kaɗan zai iya kulle ka sai igiya tayi rara, to taya ya zasu faɗa mishi karshe reshe ya juye da mujiya? Bakin su gum alaikum. To ga tsautsayi ya afka a kan Sadis, domin kusan sati ɗaya yana gidan ya tare suna masha'an su tunda sun san babu ranan dawowar Mijin, kasancewar bai jima da yin wannan tafiyar ba, in fact ma sati guda kenan, kwana ne kaɗai Sadis ba ya yi a gidan, amma wuni yana gidan.
Sai ga shi tsautsayi yasa Mijin ya dawo ɗaukar wasu muhimman takardun sa da ya manta, hand right ya kama su ra'ayil ainu suna aikata masha'a kuma a ɗakin sa a kan gadon sa

Hohoho! Kun san Soja, abu bai shafe sa ba ma ya shiga; bare wannan gonan sa aka shiga. Tunda ya cafke Sadis ya dinga duka babu kaya a jikinsa sai da ya sumar dashi ko numfashi ba ya yi, sai zubar da jini yake yi; yayi masa jina-jina, take ya saka waya ya kira folisawa suka tafi dashi caji office; daƙyar ya bari aka saka mishi wando, don da yace, "a haka za a fitar dashi gidan, domin shi ne hukuncin duk wani kwarto ya tafi a tsirara mutanen gari su gansa."
Ai ya ga tijara Sadis ba kaɗan ba, tashin hankalin da ba a saka mishi rana, yana ji yana gani bayan an farfaɗo dashi aka jasa kamar kayan wanki aka wuce dashi,
Ita kuma Matar nasa yayi mata shegen duka ya rufe ta a ɗaki ya tafi police station ɗin,
A can ya saka aka kulle sa bayan an ƙara jibgar sa kamar za a fitar masa da ransa, iya lugui-guituwa ya yi gaba ɗaya ya fita a hayyacin sa, don sai da suka saka shi yayi dana-sanin zuwan sa duniya ma baki ɗaya, domin azabtarwan da suka yi mishi ba na wasa bane, kuma yasa aka kulle sa babu belin har sai ya sake dawowa ya waiwaye sa.
🔆🔆🔆


        Allah Sarki! Ruƙayya, tana can a tashin hankali, yau kwana biyu bata saka Mijinta a ido ba, tunda komin dare sai ya dawo duk inda ya je, amma shiru kake ji babu shi babu alamar sa, abun ya soma damun ta ga babu abinci bare ta san me zata saka a cikinta

Yau ma tun tashin ta ta buga tagumi tana kallon Yarinyarta da ke ta faman barci ko tashi bata yi ba, damuwarta ma idan ta tashi bata san me zata bata ba tunda babu ko ƙwayar abinci a ɗakin

Tana nan zaune ta juyo bugun ƙofan Sauda tana kiran sunan ta. Hakan ne yasa ta tashi da hanzari ta buɗe ƙofan tana kallonta, tun kafin tayi magana ta ƙaƙalo murmushi tare da cewa, "Ina kwana Aunty Sauda?"

Maimakon ta amsa mata sai ta soma mata ƙorafi, "wai dama kina nan ido buɗe kika shiga ɗaka kika kulle kanki? Duk wannan uwar ranan da ta fallatso ke barcin bai ishe ki ba ashe?"

"A'a Aunty Sauda, na tashi tun ɗazu wlh, sakaya ƙofan nayi."

"Ohio! Ai nayi zaton wani daren za a sake muku, na ce wannan baiwar Allan lafiya kuwa har sha ɗayan safe babu labarin ta? Bari dai in duba ta in gani, ashe dai kin tashi?"

"Wlh na tashi. Ina zaune ma."

"Ina Safina ban ji kwaranniyar ta ba?"
Tayi maganar har tana leƙa ɗakin

Ruƙayya tace, "bata farka ba, tana barci."

"To kinga dama sanar miki zan yi yau zan je gidan Hauwa, tunda an kwana biyu ba a haɗu ba, shiyasa nace bari in sanar miki ko za ki shirya mu tafi tare?"

Shiru Ruƙayya tayi, sai kuma tace, "to Aunty Sauda ai Sadis bai dawo ba, kuma kinga ba yanda zan yi in tafi ban sanar mishi ba."

"Wai kina nufin har yanzu bai dawo ba? Kwana biyu kenan fa?"

"Eh har yanzu, kuma na kira wayansa ba ta shiga." Tayi maganar cikin sanyin murya

Sauda tace, "to anya lafiya? Kar dai ace wani abun ne ya faru dashi? Ai wannan abun duba wa ne."

"Nima haka nake ji a jikina wlh kamar akwai abun da yake faruwa, tunda bai taɓa yin haka ba."

"To ai zama bai kamace ki ba, sai ki bazama ki shiga gidajen Abokansa inda kika san za a iya juyo labarin sa ki cigiya ki ji, har gidan su ki je ki duba, nima don ina da ayyuka a gabana ga kuma tafiya gidan Hauwa da zan yi; da sai mu tafi tare."

"To shikenan zan je, amma bari ko zuwa anjima ne in na ga bai shigo ba sai in je gidan su."

"Ai kuwa dai; gwara hakan, nima zan bar miki sallahun Kokon su Haidar ki ajiye musu tunda ba zan yi girki ba, sai ki zuba wa Safina itama ta sha, yanzu bari in ƙarisa shanyan nan in yi wanka in wuce."
Tayi maganar tana juya wa zuwa wurin kayan fitsarin Haidar da ta zuba

Itama Ruƙayya fitowa tayi ta ɗauki buta ta shiga bayi; sabida dama maranta ta cika fam da fitsari.



          Bayan Sauda ta gama tayi wanka ta shirya, sannan ta ba wa Ruƙayya kokon Yaranta da ɗan raguwar ɗumamen shinkafa, tayi mata sallama ta wuce sai gidan Hauwa

Lokacin da mai machine ya sauke ta a wurin, shima Anwar ya dawo gidan; ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga da motansa, yana ganin ta ya haɗe rai tunda har yanzu ya ƙi sauko wa a kan Matar, har yanzu ba ya son mu'amalan su da Matarsa, bai ma san cewa tana zuwa mishi gida ba sai yau da ya ganta, kuma tabbas zai ɗauki mataki sai ya ji dalilin da yasa Hauwa ta ƙetare maganarsa ta ci gaba da mu'amala da ita

Ita kuma Sauda tunda ta gansa, ta ga yanda ya haɗe fuska, shiyasa itama ta riƙe gaisuwarta ta ƙi ce masa komai tunda itama tana cike dashi, sai ma taɓe baki tayi a ranta tana ayyana muddin ba shi ya tare ta da cewan ta dena zuwa mishi gida ba, wani haɗe fuska da hararan sa bazai mata komai ba, sai dai ya gaji ya bari wlh, nan gani nan bari gida baza ta fasa zuwa ba, in ya isa ya tare ta da zancen da kansa, wlh sai ta shuka masa rashin mutunci don baza ta jure rainin hankali ba, ƙiris take jira ya tanka ta ya ga ruwan bala'i, iskancin banza kawai shi har ya isa ya hana ta zuwa gidan sa? Duk wani fushe-fushen sa sai dai ya ga Sauda ya ƙyale bai isa ya tare ta da zancen ba, kuma jira take yi yayi mata wata magana tunda ta ga alamun sa tun ba yanzu; ba ya son alaƙar su da Hauwa, kuma Hauwan ma ta sanar mata da komai,
Yanzu ma har da buga ƙwafan ta tana shige wa cikin Falon da kuzarin ta; ta buga musu sallama.
[10/01, 9:30 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*






                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼














            *PAGE:35*

_____Koda ya shiga ɗakin sa; toilet ya wuce kai tsaye yayi uzurinsa before ya fito ya samu wuri a gefen gadon sa ya zauna, ya ɗan ɗauki lokaci kafin Afnan ta shigo ɗakin tana doka sallama. Sai da ya ɗago ya kalle ta sannan ya amsa sallaman nata, "uhm ai nayi tunanin baza ki zo bane za ki shanya Ni, sai in tashi in koma, since kin san saboda ke na zo in ga babyna."

Murmushi tayi tana isowa wurin sa tare da zama a hankali sabida girman cikin nata, tana furta, "haba dai Honey, taya ya zan shanya ka bayan na san da shigowar ka? Na tsaya mun gaisa da Aunty Sauda ne; shi ne na shiga na tado mata Aunty Hauwa ashe barci take yi ma."

Ba tare da ya bi ta kan zancen nata ba ya soma shafa cikin nata yana ɗan lumahe ido cike da tsananin farin ciki, "kin san me My dear?"

"No sai ka faɗa?"

Sai ya ja numfashi a hankali yana ɗago kansa, yayinda murmushin kan fuskarsa ya gushe yake faɗin, "insha Allahu namiji zamu samu domin na yi wa Muhseen takwara, zan fi son haka, nayi matuƙar rashin Abokina, har yanzu gani nake yi tamkar bai mutu ba; zuciyata ta kasa yarda cewa na rasa shi..." Shiru yayi sabida jin muryansa ta soma rawa; while idanunsa har sun soma canza kala alamun kamar zai yi hawaye

Itama Afnan shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta saka hannunta ta ɗaura a kan nasa da ke saman cikinta tana cewa, "don Allah ka dena fadin haka, addu'ar ka kaɗai yake buƙata a yanzu, nima ina son zuwa gaishe da Munira in duba jikinta; sabida Mama ta kira Ni tana faɗa min sun je sun duba ta; jikin babu daɗi har yanzu, tana nan a kwance, zan so ka kaini ko ka bani damar zuwa ko Ni da Aunty Hauwa ne mu je mu duba ta, ka ga mun daɗe bamu je ba."

"Ok shikenan, amma ba yanzu ba, ke ma fa ba ƙoshin lafiyar nan kika cika ba, shiyasa akai-akai nake yawan dawowa duba ki duk da tarin aikin da ke gabana, hankalina ba ya kwanciya har sai na zo na duba ki."

Dariya tayi tace, "na sani Mijina, soyayyarka tana burge Ni ina matuƙar cin alfarman ɗan babyn mu, ko in ce little Muhseen da yardan Allah."

Dukkan su suka yi dariyan, while yana lakuce mata hanci before yace, "yunwa fa nake ji, ina son in saka wani abu a cikina before in wuce don ba daɗe wa zan yi ba."

"Ok, nan zan kawo maka abincin?"

Yana bata amsa yake zare hulan kansa yace, "eh kawo min nan, don ba na son ganin wancan Matar da ta zo."

"Wai Aunty Sauda?" Tafaɗa da ɗan mamakin ta

Ɗauke kansa yayi ba tare da ya amsa mata ba yana ɓalle bottle na wurin wuyan sa

"To bari in kawo maka nan ɗin, amma ta shiga ɗakin Aunty Hauwa don na san bata zauna a Falo ba, tare ma muka shiga da

Please Login or Register in order to submit comment