Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauya mishi kamanni kamar ba shi ba, yanzu ma ya tashi a gidan tunda Ruƙayya ma ta ƙi dawowa,
Jiya da dare Ruƙayyan ta kira Sauda take bata labarin ta amshi takardan sakin ta

Sosai Hauwa ta jajanta mata, kuma ta ji tausayinta ba kaɗan ba, shiyasa tace, "zata kira ta suyi waya in ta koma gida itama."

Ranan suna yarinya ta ci sunan Umman Anwar. Khadija, zasu kira ta da Kubrah, duk da ya so namiji ya haifa domin ya yi wa Muhseen abokinsa takwara, amma hakan bai faru ba, kuma a yanda suka tsara kamar yanda Anwar ya yi wa Afnan alƙawarin in Mace ce sunan Mamanta zai saka, amma sai ga shi ta ji ya sauya, abun ya ɓata mata rai sosai, koda ta tambaye shi sai ya nuna mata, "shi mahaifiyarsa zai saka, sakamakon rashin ganin girmansa da muhimmancin sa da suka yi a matsayin sa na Mijinta, don haka dole ya nuna iko a kan ƴarsa ya canza shawara sunan Ummansa zai saka, tunda ta ƙi bin umarnin sa."

Sai lokacin ta gane sabida haushin zuwan ta gida ne ya huce takaicin sa a nan, shiyasa itama ta share sa a ranta tana taɓe baki tace, "ai akwai wani lokacin kuma, kar Allah yasa kasa sunan".





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


              Yau da gobe gonar Allah; ba mai gama ta sai shi! Yau da gobe mai sa jinjiri ya zama Ango! To ga ranan ta zo, kamar da wasa ga shi har bikin Aliyu da A'isha ya gabato, zuwa wannan lokacin shaƙuwar su tayi tsanani sabida Allah ya dasa mishi ƙaunarta, wani abu da Aliyu yake dashi, in har zai so Mutum yana son shi da dukkan zuciyarsa ne, bai taɓa tunanin zai so wata Mace bayan Zeena ba, sai ga shi a wannan lokacin yana jin soyayyar A'isha fiye da yanda ya ji na Zeena a baya, saboda ba halin su ɗaya ba, kyawun halayen ta su suka fi rinjayen sa fiye da kyawun ta, lokaci guda ya haukace da soyayyarta ga kuma tarin tausayinta da yake ji, tun mutuwar Yayansu shi ya ɗauki nauyin duk wani buƙatun ta, kulawan da yake bata shiyasa A'isha ta haƙura da duk wani abu a ranta itama ta soma ƙaunarsa, dama an ce zuciya ta fi son mai kyautata mata, amma yawanci Samari ba sa gane hakan shiyasa basu san yanda zasu kama zuciyar budurwa ba, idan Mace ta nuna ba ta sonka; to tun farko baka san kan soyayya bane, ga dai shi a ƙanƙanin lokaci Aliyu ya sauya zuciyar A'isha, duk rashin sonta da aure amma yanzu tana jin zata iya zama dashi kuma ta karkata hankalin ta kacokan wurin auren

Har an fara shirye-shiryen biki, wanda a yanzu saura sati ɗaya ya rage, lokacin ma suna tsaka da text ne, koyaushe shi yake zuwa ya kaita ya dauko ta, idan ma ba ya nan Usman yake zuwa ya kaita a machine ɗin Aliyun

Dayake babu wani bidi'a da za a yi a bikin; Walima kaɗai suka shirya tunda A'ishan akwai ustazanci, ranan juma'a aka shirya gagaruman Walima a masallacin anguwan, kasancewar na mata ne zalla kuma sun gayyato Malamar nan da ake ji da ita a yanzu; wacce Mata da yawa suna bukatar ta zo ta yi musu wa'azi don su samu ƙaruwa, Malama Juwairiyya ta zo ta zube musu lectures kala-kala

Kasancewar an fara ƙarfe hudu da mintoci ne; ƙarfe shida aka kammala kowa ya tashi aka watse

Dama su Munira da Amina tare da sauran ƙawayen Aminan, su suka yi ta rabon kayan biki, duk su suka kula da komai,
Zuwa lokacin har cikin Munira ya ɗan tasa yanzu; jikinta alhamdulillah ta fauwala wa Allah, duk da har yanzu idan ta tuna da Mijin nata sai tayi kuka, musamman da bikin nan ya zo tun ana kwana biyu ta zo ta tare a sashin ta, haka suka haɗu da su A'isha suka dinga kuka babu mai rarrashin wani, dukkan su kowa tana tuna wa da Muhseen ne, domin ba kaɗan ba sun yi rashi har yanzu mutuwar sa yana dukan su

A'isha bata da wasu ƙawaye sai ƴan class din su da ta gayyata, kuma ba kowa ya zo ba tunda basu saba ba, sai waɗanda suka santa suna anguwan; su ne suke ɗan leƙowa ana yin sha'anin da su, Amina ce mai ƙawaye ita ta gayyato nata ga su nan rututu sun zo sun tare a sashin Munira tunda a nan Amaryan take taro, a can suke kwana har ranan bikin

Karfe biyu aka ɗaura auren su da Aliyu, a kan sadaki dubu ɗari da talatin,
Bayan an gama ɗaura auren; Abokan Ango da shi kansa Angon suka zo gidan su A'isha aka soma ɗaukar hotuna,
Tun A'isha tana noƙe wa har ta saki jikinta ana ta ɗaukar su hotuna

Da yawa cikin abokansa sun yaba da kyawun ta, don gani suke yi kamar shi yana da Sa'a ne sabida samun Mata kyawawa tsala-tsala kamar ka latsa jini ya fita, Allah ya basa wlh tunda haka suka yi ta tononsa suna taya sa murna

Shi kuma sai washe baki yake yi yana jin dad'i, musamman idan ya kalle ta sai farin ciki ya ƙara cika sa, a yau yake ƙara tantance irin baiwar kyan da Allah ya yi wa A'isha, tamkar Zahra ce a cikin Wata

A ranan da yamma aka kai mishi Matarsa, gidan sa da ya gyara tamkar ba a taɓa gobara ba, komai ya zuba ya canza sabo, don har ginin ma sai da aka canza mishi fasali, duk wanda ya je sai yayi santin gidan,
Sai mu ce Allah ya sanya alkhairi ya kawo ƙazantar ɗaki.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


       *ONE YEAR AGO*
     Zuwa wannan lokacin har su Hafsah sun kammala makarantar su, tayi WAEC da NECO ɗin ta har results sun fito

Yanzu Jamal duk ya gyara gidan sa komai ya natsa sai dai a kawo masa Matarsa da a yanzu ba shi da burin da ya wuce wannan, yanzu sosai yake son Hafsah har ba ya iya ɓoye soyayyarta saboda mugun kulawar da yake bata

Ita kanta ta san da haka, tun tana ɗar-ɗar dashi da jin kunyarsa; har ta saki jikinta yanzu, da taimakon ƙawarta Naja'atu da take zuga ta kodayaushe, ita ta taimaka mata wajen bata shawarwari har take iya biye wa Jamal tana iya mayar masa da magana, da haka suka saba sai kuma ta saki jikinta, yanzu ita kanta baza ta iya tantance ƙaunarsa take yi ba, amma tana jin sa a rai, yanda suka shaƙu tana jin baza ta taɓa iya rabuwa dashi ba, domin ya iya kula da ita da saka mata shauƙi wanda kodayaushe cikin farin ciki take kasancewa,
Yanzu har ta cire fargaban Fauziyya tunda ta san cewa auren su ya ƙare tuni, kuma basu sake sanya ta a ido ba,
Su Sumayya kaɗai suke zuwa wurin su wani lokacin Dadyn su ya kawo su don su zo su gaishe da Mama,
Su ma yanzu sun ɗan saba da su duk da na ciki na ciki musamman ma ita Sumayyar; sosai take jin haushin su Hafsah don a ganin ta su ne silan mutuwar auren Mahaifiyar su, sannan kuma har yanzu basu san inda ƴar uwansu take ba, har yanzu Jamal ya ƙi dawowa da ita

Tana can ƙauye tana cin gwale-gwale, duk da babu wahala bare takura don Umman Hafsah bata biye wa Jamal ba, tana kula da Intisar ɗin sosai, yawanci ma ƴaƴanta suke mata komai ba ta saka Intisar ɗin, amma rashin sabo da zamanta a ƙauyen yasa duk ta tsangwami kanta, tun tana kuka da saka ran wata rana Dadyn ta ko Momyn ta zasu zo su tafi da ita, har ta cire rai, tunda gaba ɗaya ta rame ta fita a hayyacin ta, ko abincin su ba ta iya ci, ba ta kula kowa ko sau ɗari su Umma zasu yi mata magana, sai ta ga damar fitowa tsakar gida ma, ta gama tsangwaman kanta gaba ɗaya,
To yau da gobe kuma dole yasa ta gaji ta soma sakin jikinta tunda ta fitar da ran komawar ta, ta sha kuka ba kaɗan ba, daga ƙarshe ta haƙura ta ci gaba da rayuwarta a gidan, haka nan ta saki jikinta tunda Umma tana da kirki, shiyasa bata iya mata rashin kunya ba bare tace zata yi wani abun, duk ƙyaliya da rashin kula su da ba ta yi; Umma bata taɓa ce mata komai ba kuma bata taɓa kai ƙaran ta wurin mahaifinta ba, since a gabanta tana ji in ya kira yana tambayar intisar ɗin idan tana mata rashin kunya ko tana yin wani abun da bai dace ba, sai Umma tace mishi, "babu komai suna zaune lafiya, babu aikin da bata mata."

Hakan ne yasa intisar ta haƙura ta saki ranta, har ta soma fitowa waje tana ɗan taya Umman ayyuka, a hankali - a hankali ta soma saba wa da rayuwar garin,
Bare akwai Yara a gidan ƙannin Hafsah suna girmama ta sosai, Aunty sama Aunty ƙasa, duk Maza ne sai Autar su ita ce Mace, yarinyar bata gaza shekaru huɗu ba,
Shi yasa Intisar take taya Umman aiki tunda bata da masu taya ta, ita kaɗai take ayyukan ta, Mazan kuma su ɗibo ruwa a rafi ko su je mata aike, sai ya zamana yanzu intisar take musu girki har wanki tana haɗa wa da nata tayi, domin ada Umma da kanta take kwasan kayan intisar ta wanke, amma yanzu tayi hankali zaman gidan ya gyara ta babu hantara babu tsangwama, ta yi wa kanta faɗa tunda bata da madafa, ta gane cewa gwara ta saki jikinta kar ta kashe kanta cikin ƙunci, amma matuƙa tana kewan ƴan uwanta da Iyayenta, uwa uba Mijinta wanda ta rasa, kusan kullum in ta tuna dashi sai ta sha kuka ta godewa Allah, ta san cewa ta rasa Shuriem bazai taɓa dawowa da ita gidan sa ba, kila ma yayi aure yanzu tunda ga shi shekara guda da wasu watanni rabon ta dashi

Rayuwa kenan! Dama komai da lokacin sa.
***

           Tunda an saka ranan tarewan Hafsah shiyasa aka faɗa ma ƴan uwa da abokan arziki

Ƴan ƙauyen su Mama duk sun zo sun ciko Mota sun so garin, kasancewar Umma ban da ita but ta so intisar ta bi su, amma Jamal yace, "a'a, ta zauna a nan bai shirya dawowar ta yanzu ba, don har yanzu bai yarda da hankalin ta ba, tayi zamanta har ta samu Miji."

Hakan yasa intisar ta fashe da kuka duk ta tashi hankalin ta, kwata-kwata bata damu da jin zancen Auren Dadyn su da Hafsah ba, rashin komawar ta ya fi komai ɗaga mata hankali, don yanzu bata da buri sama da ta koma gida, ta gaji da zaman ƙauye

Umma ta tausaya mata sosai, amma haka tayi ta bata baki tana ce mata, "zata shawo kansa zata ba shi haƙuri, baza ta jima ba Insha Allahu zata koma."

Da haka intisar ta samu sassauci a ranta sai dai ta kasa kwantar da hankalin ta sosai, don gani take yi kamar Dadyn ta bazai taɓa dawowa da ita ba, sai dai ta ƙare rayuwarta a ƙauye, kuma tana ganin hakan da wuya wlh don baza ta taɓa auren ɗan ƙauye ba, ko fita ma ba ta yi bare a santa a garin.
  
[24/01, 6:59 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:39*

_____Sai ranan tariyan ne labari ya je wa Fauziyya, dama har lokacin bata cire rai wata rana zata koma gidan Jamal ba, tunda ta kasa cire sa a rai ko ta halin ƙa-ƙa so take yi ta koma gidan auren ta; duk da ta san saki Uku ne a tsakanin su, amma yadda ta dage tana biye-biyen Malamai don ta samu ta shawo kansa, har auren kisan wuta ta shirya zata yi sabida ta samu ta koma gidan sa, amma sai ga wannan mummunar labarin ya iso gare ta, kiɗima da tashin hankali gami da girgizan da tayi; lokaci guda sai ta zube a sume tsaban tashin hankali,
Sai dai Iyayenta suka kwashe ta aka yi da ita asibiti sabida halin da take ciki.
***

       Can kuwa gida ana ta shagulgulan biki basu san ma me ke wakana ba, shi kansa Jamal bai san halin da Fauziyya take ciki ba, don ba a kira sa an sanar masa ba, dama shi ya yanke alaƙar su, ko Yaransa ba ya bari su je sai idan an ɗauki lokaci, don yace, "baza su ci gaba da zuwa tana ɓata musu tarbiyya ba."
Basu da lokacin kansu ma wuni suna school, har hadda ya mayar da su, dama weekends ne suke samun Hutu to yanzu babu hutun

Babu abun da ba a yi wa Hafsah ba, har gyaran jiki an yi mata an yi mata lalli hannu da ƙafa ta fito sak a Amaryanta,
Ƙawarta Naja'atu ita tayi mata MakeUp a ranan,
Kayan da aka yi mata a cikin sabbin akwatunan ta da aka kawo mata a daren jiya, tunda akwai ɗinkakku su ta dinga saka wa tana fita wannan ta shiga wannan,
Duk da kunyar Hafsah haka nan ta jure tana cikin ƴan uwa ana ta tsokanar ta, bata je ko'ina ba suna tare da su Mama, ko ƙawayenta sai dai a gidan aka zuba musu abinci, suna cikin dakin ta a nan suka zauna suna ta mata tsiya ana raha,
Wasu sai lokacin suka san cewa Mahaifin Sumayya; Hafsah take aure,
domin Naja'atu sai basu labari take yi tana faɗa musu, "ai auren ya jima ma."

Ƙawayen sai mamaki suke yi suna jinjina maganar, abun akwai ɗaure kai sabida in suka tuna Sumayyar da yanda ake ƴar tsama da ita da Hafsan, basu mance irin zagi da cin mutuncin da take mata ba, ashe Auntyn ta ne tunda Mahaifinta take aure, yanzu kuma ai Hafsah ta fi ƙarfin ta don ba sa tunanin zata yi mata irin wannan cin kashin, kowa so yake yi ya ga yanda Sumayya zata yi, har wasu suna gulman sai sun je gidan in har aka kai Hafsah sun ga ƙwaƙwaf

Babu wanda ya kai Mama farin ciki a wannan ranan, yau ga shi za a kai Hafsah ɗakin Mijinta, lokacin da take fatan zuwan sa kuma ga shi ya zo da cikan burika da dama, musamman yanda Allah ya haɗa kansu sai fatan a zauna lafiya kuma, tana da yaƙinin Insha Allahu wannan auren an ƙulla alkhairi kenan har abada,
Sosai ta zaunar da Hafsah tayi mata faɗa tayi mata nasiha mai ratsa zuciya, da yanda zata kula da gidan da duk abun da ya kamata, sun jima suna magana don ɗakin gaba ɗaya aka bar musu suna ta magana Hafsah na kuka,
Daga ƙarshe ta rarrashe ta har ta samu tayi shiru, ita kanta tana jin kamar ta zubar da hawaye tunda yau ga shi zasu rabu bayan sun saba da juna, yanzu ita kadai zata ci gaba da zama a wannan gidan babu Hafsah Abokiyar zamanta da suka saba tun a ƙauye, ita ta raini Hafsah tun gama yaye ta da Umma tayi, ta san ta ciki da bai babu abinda suke ɓoye wa juna, dole rabuwan su zai taɓa zuciyarsu

Musamman ma ita Hafsan lokacin da ta tabbatar za a tafi da ita, ta dinga kuka tana kiran sunan Mama, daƙyar aka iya ɓanɓare ta a jikinta suka wuce da ƴan uwa, tunda zasu je su gyara mata ɗaki daga baya sai su dawo nan gidan su kwana, washe gari kuma su wuce

Ita kanta Mama ta kasa jure wa sai da tayi hawaye, zata so su zauna wuri ɗaya da Hafsah, amma aure ba wasa ba kuma shine ya raba su, baza ta so ta koma can gidan da zama ba don kar ta takura musu, shiyasa ma tun farko da Jamal yayi mata maganar komawar ta asalin ɗakin da ta zauna; tace masa, "a'a, ya barta a nan kawai, baza ta je ta takura musu ba, ita yanzu ta saba da nan ɗin."

Haka nan ya haƙura duk da ba a son ransa ba, amma ko ba yanzu ba yasa a ransa zai dawo da ita gwara ta koma can hankalin sa zai fi kwanciya, tunda ita kaɗai ne a nan babu mataimaki.
***

    Bayan an kai Hafsah ɗakinta, sun ɗan yi mata gyare-gyare har zuwa Magriba sannan suka soma haraman komawa gidan Mama

Su Sumayya suna cikin daki sun ƙule ita da Jibril, shi Jibril ma bai wani damu ba sai ita Sumayyar, don ita kuka ta dinga yi tunda ta ji maganar auren, zuciyarta kamar ta fashe don baƙin ciki da taya Momyn su kishi, bare tana tunanin mutane zasu yi musu dariya wai a rasa wacce zata zama Matar Dadyn su sai wannan Bagidajiyar baƙauyiyar wacce ta zauna a karkashin su? Abun yayi mata ciwo, har lokacin ta ƙi sakin jikinta idanunta sun kumbura ta sha kuka, suna jin mutane an kawo Hafsah ta ja hannun Jibril suka shige ɗakin ta, ita kaɗai take ta sintiri tana leƙen mutanen tana jiran su bar musu gida

Jin an kira sallah sai Jibril yayi alwala a toilet ɗin ya fita zuwa sallah, tunda ya san gargaɗin Dadyn su yanzu sallah ba ya wuce sa har ya saba sabida yanda ya sauya musu alƙibla, sosai suke tsoron sa a yanzu

Ita kuma Sumayya tana zaune ta kasa kataɓus har sai da ta ji gidan shiru tukunna ta fito Falon, sai waige-waige take yi tana duba wa ko akwai mutane, sai kuma ta wuce ɗakin Hafsah kanta tsaye ta shige ciki

Hafsah na kwance a kan gado ko tashi ta ƙi yi, ta ƙudundune da gyalen da aka yafa mata, motsin da ta jiyo ne yasa ta ɗago kanta tana kallon Sumayyar

Ita kuma tana tsaye a bakin ƙofan tana aika mata da wani mugun kallo, ganin sun haɗa ido yasa tace, "shegiya muna-fuka annamimiya, burin ku ya cika kun raba mu da Uwarmu kin zo kin aurar mana Mahaifi, wlh sai ruwan gidan nan ya gagare ki sha don bazan taɓa ƙyale ki ba, sai na ɗauki fansa a kanki."

Yanda ka san an dasa Hafsah haka tayi tana kallon Sumayya ta ƙi cewa komai, sai dai jikinta yayi tsananin sanyi sabida jin yanda Sumayyar take zagin ta ranta a ɓace

"Wlh ki sani sai na wulaƙanta rayuwarki tunda kika yi gangancin aurar mana Uba, ƴar iska ashe dama abun da kuke kitsa wa kenan sai da ku ka cika burin ku ko? To Ni ce dai-dai dake a gidan nan, mu zuba wlh."
Sai tayi shiru sabida jin kamar sallaman Dadyn su, da sauri ta juya zata fita suka yi arangama

Bin ta da kallo yayi sabida ganin yanda duk ta daburce tana muzurai, sai ya kira sunan ta yace, "Sumayya, mai kika zo yi nan?"

"Babu komai Dady." Ta furta cikin rashin gaskiya

"Ina Jibril ɗin?"

"Ya je masallaci."

"Ok." Sai ya miƙa mata leda ɗaya da ke hannunsa yace, "ku je dashi ku ci."

Hannu biyu ta sanya ta amsa tana wuce wa ta fita

Shi kuma ya shigo ɗakin yana sake yin sallama idanunsa suka sauka a kan Hafsah; wacce ta mayar da kanta ta sake ƙudundune wa, lokaci ɗaya hawaye suka soma tsiyayo mata sabida jin abun da Sumayya tace, dama ta san za a rina, bata san wanne irin zama zasu yi ba,
Tahowa yayi wurin gadon yana kallonta ko dauke ido ba ya yi, ajiye ledan hannunsa yayi yana kiran sunanta

Bata ɗago ba sai da ya sake kiranta sannan ta ɗaga kai amma ta ɓoye fuskarta a cikin gyale

Murmushi yayi yana kallonta, yana tsaye a wurin ba tare da ya zauna ba yace, "daughter fito a cikin gyalen mana ki sha iska."

Ƙara ƙudundune kanta tayi ta ɓoye a tsakanin ƙafafunta

Shi kansa ya san zai yi fama da Hafsah, amma kuma ya shirya wa zaman su cikin jin dad'i da kwanciyar hankali, da kuma yanda zai shawo kanta har ta saba dashi cikin ruwan sanyi,
Kiran sunan ta yayi ya bata umarnin, "ta sauko su yi alwala."

Sai ta faɗa masa, "tana da alwalan ta."

Bai ce komai ba ya fita daga ɗakin bayan ya tuɓe malin-malin ɗin jikinsa, ya fita Falo ya tarar da su Sumayya zaune; Jibril ya tasa kazar da ya basu yana yaga yana korawa da yoghurt, ita kuma Sumayya tana zaune ta buga tagumi idanun nan sun kada sun yi ja tana kallon ɗakin da Hafsah take,
Ganin su a haka yace, "ke Sumayya ya aka yi kika zuba tagumi; baza ki ci kazar bane?"

Hannunta ta sauke tana girgiza kanta da faɗin, "zan ci Dady."

"Kuma shine kika zauna kika bar sa a haka yana ci; ba ki san ki ɗauko plate ki sake muku ki yanka bane?"

Miƙe wa tayi bata ce komai ba, ta bi hanyar kichen ta wuce

Shima Jibril ya tsame hannunsa ya dena ci, sai taunan na bakin sa yake yi yana wulla ido

Ba tare da Jamal ya sake magana ba sai ya wuce bakin ƙofan ya kulle sannan ya koma kichen ɗin, ya sanya Sumayya ta ɗauko masa plate da spoon tare da cups; ta zuba mishi a tray, sannan ya amsa ya fito ta biyo bayansa, sai da ya gargaɗe su, "su yi sauri su gama su wuce daki su kwanta."

Suka amsa mishi da to a tare

Shi kuma ya wuce ɗakin Hafsah ya shiga,
Bayan ya ajiye tray ya shiga toilet ya ɗaura alwala, sannan ya fito ya bata umarnin tashi su yi sallah

Babu musu Hafsah ta miƙe ta bi umarnin sa tunda bata saba mishi gardama ba, bare tana ganin girman sa ga kuma irin gargaɗin da aka yi mata

Bayan sun gama ya dafa kanta yayi musu addu'o'i mai tsayi sannan ya jawo tray ya buɗe ledan duk ya fitar da kayan ciki

Hafsah na zaune kanta a ƙasa tana jin moments ɗin sa

Bayan ya gama gyara komai, ya dube ta yace, "daughter ɗago mu ci abinci, don na san yanzu haka kina jin yunwa ba ki ci komai ba."

Ƙin motsi tayi; tayi shiru ta ƙi magana

"Daughter, kina jina kuwa? Ko dai barci kika soma?" Yayi maganar yana ɗan Murmushi

"Ba na jin yunwa." Ta furta tana ƙara tusa kanta cikin ƙafafunta

"Ba na son gardama ta so ki ci, idan kuma ba ki ci da kanki ba Ni zan ba ki, bazan bar ki da yunwa ba, za ki ci shi dole."

Jin maganar da yace ne dole ba don ta so ba ta ɗago kanta, amma ta kasa kallonsa

Ya tura mata plate ɗin kusa da ita yace, "ta ci."
Sannan ya ɗauko Holandia yana tsiyaya mata a cup, ajiye mata yayi kusa da ita yana sake tanƙwashe ƙafafunsa, ya tsira mata ido tare da furta, "maza ki cinye ki dena cakala hannu, duk naki ne."

Noƙe kai tayi tana rufe idanunta

Sai yayi murmushi ya dauki cup ya tsiyaya nashi yana sha a hankali, wayansa ya ɗauka ya soma duba wa yayi kamar ya manta da ita

Hakan ne yasa Hafsah ta ɗan saki jikinta tana cin abincin ganin kamar hankalin sa ba ya tare da ita, dama akwai yunwa a tare da ita, bare kayan ƙwalama ne shiyasa ta saki ciki tana ci tana ta zare ido; ciki fal tsoro,
Tana ganin kamar zai kallo ta sai ta dena ci ta koma nuƙu-nuƙu

Daga ƙarshe ma tashi yayi a wurin ya koma bakin gadon sa ya ci gaba da harkan gabansa a waya,
Tsawon lokaci suna a haka a tunanin sa

Please Login or Register in order to submit comment