Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gefen gadon ta, kaɗa ƙafafu kawai take yi tana tunanin itama matakin da zata ɗauka, to wlh bazai taɓa yiwuwa ya hana ta mu'amala da mutane ba, kuma fita baza ta fasa ba sai dai idan bata yi ninya ba, zata nuna mishi ba tsoron shi take ji ba idan ta fita sai ya kashe ta ya huta, amma muddin tana numfashi bazai taka ta son ranshi don kawai tana auren shi ya tauye mata haƙƙin ta ba, a kan me? Ai haka ya aure ta don shi kaɗai baza ta dena mu'amala ta hana kanta farin ciki duk sabida shi ba, gani take yi ma son kan shi yayi mishi yawa tunda so yake yi ya hana ta rawan gaban hantsi, ta ƙare a gindin sa bata da aiki sai nashi, bata da wani kataɓus sai na bautar gidan shi

Ƙin fita tayi a ɗakin don tsaban haushin abun da yayi mata, so take yi ta nuna masa itama ɓacin ranta, shiyasa ta tashi ta shige toilet tayi wanka ta zauna gyara jikinta bayan ta saka rigan barci

Yayinda shi kuma Muhseen falon ya koma ya zauna; yana harɗe hannayen sa ya tallabo haɓar sa abun duniya duk ya bi ya ishe shi, jefi-jefi yana kallon fuskar Hanan da ke ta faman barci har da munshari, alamun barcin nata yayi nisa. Tabbas idan ya ci gaba da barin Munira tana aikata abun da ta ga dama a gidan nan, bata ganin mutuncin sa da ƙimar sa a matsayin shi na Mijinta, bai isa ya saka ta abu ta hanu ba, to nan gaba sai ta fi ƙarfin sa, haƙurin sa ya gama ƙare wa, yana yin komai ne domin Umma, amma yanzu ko me zai faru sai dai ya faru wlh ya gaji, tunda babu wanda zai fahimci halin da yake ciki dole ya miƙe tsaye yayi yaƙi iya ƙarfin sa, in ta ga zata zauna dashi a haka ta canza ɗabi'u fine. In kuma baza ta iya ba kowa ya kama hanyar gaban sa. Yana nan zaune amma ya ji shiru Muniran bata fito ba, ga yunwa da ke addabar sa ya san ba fitowa zata yi ba tunda ya ga haka, shiyasa shima ya ƙi tashi ya ci abincin, sai ya ɗauki ledan kayan zaƙin da ya siyo ma Hanan, ya buɗe biscuits ya soma tusa wa a cikin sa ransa na ci gaba da zafi da abubuwan da Munira take mishi a gidan nan, shi ba shi da ikon da zai yi mata faɗa ta ji maganar sa? Ba shi da iko da ita a matsayin shi na Mijinta? Tamkar ita ta haife shi sai abin da take so zata yi? Ai kowanne namiji yana son a girmama shi a matsayin sa na Miji kuma ja-gaba a gidan sa, amma kuma ya rasa wannan damar, ta mayar dashi tamkar Yaronta bai isa ya yanke hukunci ta bi ba, bai da wannan fawan gaba ɗaya ta raina shi, tana ganin kamar kansu ɗaya ne, har yanzu bata san me ake nufi da Miji ba

Miƙe wa yayi ya ɗauko lemon kwali a fridge ya kora da biscuits ɗin. Sai da ya gama ya sha ruwa ya furta alhamdulillah a cikin ransa, sannan ya dauki Hanan ya wuce da ita dakin sa ya kwantar da ita, wanka ya shiga yayi ya sauya kayansa, ya koma Falo ya kashe komai na na'ura daga nan ya shige ya datse ƙofar sa, shima bai da lokacin ta dole ne ya ɗauki mataki a kanta, duk abun da take taƙama dashi shima yana ji, zai nuna mata iyakan ta a wannan karon, dole ne a gobe ya je gidan su ya kai ƙaran ta, idan zata sauya ta sauya, amma duk abun da ya biyo baya kar su kuka da shi tunda already ya gama mata iyaka da fita maƙota, kai ba iya maƙota ba ko'ina ne in har ba da amincewar sa bane, a bakin auren ta ne, don haka dole ya faɗa musu su ja mata kunne, don idan tayi gigin fice wa sai dai su ɗauki ƴar su ya gama auren ta.






    🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


             Kamar yanda Jamal yayi ninyar sauya wa su Mama gida, ai kuwa a cikin sati ɗaya ya gurgurɗa ya samo gidan mai sauƙin kuɗi ya siya. Flat ɗin gida ne, sai dai ƙofa ne ba gate ba, falo ne babba da dakuna guda uku, sai bayi da kichen da wurin dinning. Kuma kowanne daki akwai toilet a ciki, sai tsakar gida madaidaici da bayin tsakar gidan.
Yayi kyau sosai gidan kuma akwai tsada gaskiya, sai dai kasancewar gidan kamar ya ɗan ji jiki ne shiyasa aka yi mishi sauƙi, kuma dayake Abokinsa ne mai gidan duk da haka an mishi sauƙi gaskiya, shiyasa nan da nan ya soma gyaran gidan cikin kwana biyar aka gama ya zama kamar sabo, don har penti sai da ya saka aka canza mishi, aka canza wasu abubuwan da suka gama lalace wa kamar su kayan toilet da kantan kichen, duk sabo aka saka. Sai ya siya kujeru aka zuba a tsakar Falon

To dayake akwai abubuwan da zai siya musu kafin su tare, shiyasa bai sanar da Mama ba ya bari sai wannan watan tayi ya amshi albashi, idan ya gama siyan sauran kayan sai su koma can. Dayake ma a kwanakin ba ya zama sosai tunda aiki sun yi mishi yawa, iyakan ya ɗaura masu aikin a kai ne; shi kuma yana leƙowa idan ya samu dama, ga yawan tafiye-tafiyen shi tunda ba ya zama, shiyasa bai san yanda har yanzu Fauziyya take tafiyar mishi da gida ba, tunda ya san dai yayi mata kashedin saka Hafsah aiki, bai san cewa har yanzu tana cin uƙubar ta ba, don islamiyya ma ta kashe mata sai idan Jamal yana gida sannan take zuwa

Kuma duk wannan abubuwan su Mama ba sa sanar mishi, ita tun daga lokacin ma bata sake mishi zancen Fauziyya ba, tunda dai yanzu an rigada an yi auren shi da Hafsah burin ta ya cika, shiyasa bata sake mishi wani ƙorafi ba, ta barta tayi duk abun da zata yi, duk wanda yayi mai kyau don kansa babu abun da ya shalle ta, da Jikokinta dai ido ne tunda ba sa ƙaunarta, ganin su ma ba ta yi bare su san da zaman ta

Haka ma Intisar ko ta zo gidan ba ta zuwa gaishe da Mama, bata taɓa takowa sashin ta ba tunda aka yi mata auren nan. Sau daya ne ma Maman ta taɓa ganin ta, lokacin ta zo gidan sai Hafsah take faɗa mata, "yanzu da suka dawo school su ka ga Intisar ta zo."

Shi ne Maman tace, "to bari ta tashi ta je su gaisa tunda bata ganta ba tun bayan auren."
Ta ɗebi jiki ta nufi sashin. Ta tarar da su a Falo bayan ta shiga da sallama, amma ko sallaman bata samu arzikin a amsa mata ba, bare a bata iznin zama. Ita da kanta ma ta gaishe da Fauziyyan

Ta amsa mata a daƙile tana yatsina fuska tare da kaɗa ƙafafu cikin izza da taƙama

Mama tace, "dama zuwa nayi mu gaisa da Maryama tunda tun auren bamu haɗu ba, shi ne yanzu Hafsatu take faɗa min ta zo shiyasa nace bari in zo in duba Takwaran nawa." Ta ƙare maganar tana murmushi

Intisar wacce take shan custard, ko ɗago kai ta dubi Maman bata yi ba bare ta saka ran zata yi mata kallon girmama wa

Haka su ma su Sumayya, sai ma haɗa kai da suka yi da Jibril suna duba waya basu san Allah yayi ruwan tsakin ta ba

Fauziyya ce kaɗai ta taɓe baki tace, "Allah Sarki! To ta zo lafiya."

"Masha Allah. Haka ake so, Ni na tafi." Mama ta furta tana yin gaba tare da fita sashin jiki a sanyaye, tana sake jinjina irin wannan wulaƙancin da tsanar da suke nuna mata, girgiza kai kawai tayi ta koma ɗakin ta, kuma ta ƙi sanar da Hafsah ma abun da ya faru; ta bar komai a cikin ta

Yayinda su Fauziyyan kuwa sai zagin ta suke yi. Har Intisar ɗin tana cewa, "munafurci kawai ya kawo ta, shegiyar Mata kamar wata salaha bayan kuma duk munafukai ne daga ita har tsinanniyar can."

Duk wannan furucin Fauziyya bata tsawatar musu ba bare ta ga rashin tarbiyyar su, a ganin ta ma sun yi daidai don har da ita ake zagin ta. Tana cewa, "duk yanda zata yi sai ta ga bayan su sun bar mata gida, don basu isa su ci gaba da zama a gidan nan ba, ko suna so; ko ba sa so sai sun bar mata gidan ta wlh."

Haka dai suka ci gaba da maganganun ɓatanci da aibata su Mama. Har suka gaji suka sanja topic ɗin

Wannan abubuwan ke faruwa a gidan Jamal, babu mai hana wa kuma babu damar da Mama zata yi magana a matsayin ta na Uwar mai gidan, bare a kalle ta da ƙima da mutunci, shiyasa ta ƙosa ma Jamal ya samo musu gidan su bar gidan, tunda cin mutuncin da cin kashin yayi musu yawa, ita baƙin cikinta yanda Fauziyyan take azabtar da Hafsah son ranta, abun yayi worse yanzu tunda ba ya sanin komai, kuma tamkar ma yanzu ba ya damuwa da ya duba halin da suke zaune tsakanin iyalan sa da su Mama, ba ya ma maganar tsawatar musu kamar yanda yayi a baya su riƙa zuwa suna gaishe ta

Tunda yanzu Fauziyyan ta dage tana bin hanyar da duk ta san zata mallake shi, domin ya juya wa su Mama baya, kuma tana cin galaba matuƙa tunda yanzu ko faɗan da suke yi a kan abubuwan da take ma su Mama ba sa yi yanzu, a gabansa ma zai ga Hafsan ta je sashin yin aiki amma bazai ce mata komai ba, ba ya magana bare ya ɗaga kai ya kalle su yace don me?

Sai da komai ya kammala na gidan da ya siyan musu, sannan ya je wa Mama da albishir ɗin komawan su gidan a wannan satin

Sosai Mama tayi farin ciki, don ta ƙosa dama su bar ma Fauziyya gidan ta, musamman yanda ta sako Hafsah a gaba ta mayar da ita ƴar Baiwar ta, shiyasa abun ya yi wa Mama dad'i. Haka itama Hafsan sai murna take yi

Jamal kuwa murmushi kawai yake yi yana kallon yanda farin ciki ya cika su, ko ba komai ya ji sanyi a ransa tunda ya gama da wannan matsalar, don shima a ransa yana matuƙar damuwa da wannan matsalar gidan nasa, yana son ya kawo ƙarshen sa domin yana matuƙar ƙaunar Mahaifiyar sa da ƴar ƙanwarsa, amma bai san yanda zai yi ya fahimtar da Fauziyya ta ɗauke su da muhimmanci ba, abun yana mishi ciwo matuƙa, musamman yanzu da yake jin ba ya iya kataɓus a harkan gidan nashi, bare ya saka su a turba, amma dai yanzu tunda sun tashi shikenan sai a zauna lafiya, matsalar sa kuma na gaba tunda bai san yanda zasu kwashe da Fauziyya ba muddin ta san da auren Hafsah a kanshi, amma yana fatan a ce komai ya zo mishi da sauƙi nan gaba, har yanzu ba wai yana kallon yarinyar a matsayin Matar sa ba ce bare ya sanya wani abu a ransa, yana fatan a ce nan gaba idan ita Hafsan ta ji maganar sai ta nemi ya sauwaƙe mata su rabu salin-alin tunda ta san ciwon kanta, ta yiwu ma ta samu wanda take so a lokacin ya san Mama baza ta ƙi son abun da Hafsan ke so ba, tunda tana ƙaunarta sosai, shikenan sai komai ya warware cikin sauki ba tare da an kai ruwa rana ba, domin har ga Allah ba shi da burin ajiye Mata biyu a rayuwarsa, kawai bazai iya yin ma Maman sa musu bane, sannan kuma ya san da cewa duk sabida tsana da hantarar da Fauziyya ta nuna musu ne, shi ne musabbabin komai

A ranan itama ya sanar da Fauziyya tashin su Mama da zasu yi, a matsayin ya siya musu gidan da zasu zauna a nan

Duk da haka sai da ta nuna baƙin cikin ta jin maganar da Jamal ya zo mata dashi, har ta kasa shiru tana ce mishi, "maimakon ya mayar da su ƙauye inyaso ya siyan musu gidan a can su zauna, amma ita bata ga amfanin zaman su a nan ba tunda basu saba da zaman birnin ba, shi dai kawai yace ya fifita su a kansu tunda har wani gida yake iya siyan musu ya mayar da su can, su ga su tun yaushe suna fama da wannan gidan bai canza musu ba."

Jamal sai ya saki baki kawai yana kallonta, zahiri baƙin ciki tsagwaron sa yake gani a tattare da Fauziyyan. Bai san meyasa ya kasa bayyana mata irin ɓacin ran da ke ransa ba, amma sai yace mata, "ya rasa mai ƴan uwansa suka tare mata da ta bi ta tsane su haka, gida ne dai ta nuna ba ta son zaman su kuma yanzu ya canza musu gidan, amma kuma don rashin son ci gaban su da Hassada da take musu, ba ta son ma su raɓe ta bare su zauna a birnin gaba ɗaya, ya rasa me take so da su?"

Cikin takaici Fauziyyan tace, "haka zaka ce ai, tunda kana gani baƙin ciki nake musu don kawai na nuna rashin dacewar abun da kayi, ai ba kai kaɗai bane kake da iyayen, ka taɓa cewa zaka siyan ma nawa iyayen gida ko ka canza musu tsarin gidan su? Baka taɓa ba, amma kai ga shi ka siya sabon gida ka saka naka dangin, kuma da an yi magana sai ka ce ba na ƙaunar su ne, ai tun farko na nuna maka ƙin amincewa ta na zaman su a gidan, tunda babu wata Macen da zata yarda ta zauna da Uwar Miji tana saka musu ido a gida, wanne abu ne Mahaifiyar ka bata yi mana ba a nan gidan? Duk sabida rashin ƙauna da kuma ta ƙi jinin mu a gidan, har wannan yarinyar ban isa na saka ta aiki a gidan ba sabida gani take yi kamar kanmu ɗaya, amma ka bi duk ka goyi da bayan su kana ganin tamkar ba na ƙaunar su ne, sabida Ni bazan iya fitowa fili na bayyana maka irin cin kashin da suke min ba, tun shigowar su gidan nan farin ciki yayi ƙaura a gidan namu, ka bi ka canza kana ganin kamar na tsane su ne, bayan sun cusa maka namu tsanar kullum laifi na kake gani, ai wlh abubuwan duk da kayi min na ji ciwon abun sosai, raina ya ɓaci kuma bazan taɓa manta waɗannan abubuwan da suka faru ba, ka nuna dai ka fi son dangin ka a kaina, bamu da matsayin da zaka fifita mu sai dai ka nuna sun fi mu, ai wlh yau dole sai na nuna maka ɓacin ran da na ƙunsa da zuwan su gidan nan."

"Amma Fauziyya ban taɓa tunanin rashin mutuncin naki ya kai intaha haka ba, Mahaifiyata ce fa? Mahaifiyata... Mahaifiyata kike faɗa wa wannan maganar?" Yayi maganar cikin rawan murya yana nuna kansa da yatsa. "Shikenan ki yi duk abun da kike so, abun da kika ga ya dace da ke ki yi kawai." Ya miƙe ya koma nasa ɗakin yana jin zafi da ƙuna a cikin ransa, amma kuma ya kasa ɗaukar mataki bare ya sauke mata irin ɓacin ran da yake ji. Ya yarda Fauziyya bata da hankali, son kai ya rufe mata ido babu ko ɗigon imani a tare da ita, kuma tabbas akwai ranan da zai bata mamaki, zata yi kuka da idanunta, kuma in sha Allahu sai an yi ma nata Uwar haka, ko ba a yi mata ba itama sai wannan baƙin cikin da take ƙunsa wa Uwar shi, sai ta ɗanɗana irin sa, ai duniya budurwan Wawa ce, kuma abun da ka shuka shi zaka girba, tabbas har a ransa yana dana-sanin kasancewar ita Matarsa ce, tunda baza ta iya yaƙi ta taya sa neman Aljannar sa ba, Uwar da ya fito a tsatson ta, amma son rai yasa tana kishi da ita

Wannan wacce duniya muke ciki? Wai Mata ta riƙa kishi da Uwar Mijinta? Ko kuma Uwa ta riƙa kishi da Matar ɗanta? Duk don Hassada da ƙyashin a ƙaru da shi.
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

         *RAYUWAR CIKIN AURE*
             _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

          *P.W.A✍️*





            *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼










            *PAGE:23*

_____Alhamdulillah zaman Hauwa da Afnan sai son Barka, babu wani abun da za a ce Allah wadai a ciki, tunda Afnan ɗin wayayyiya ce shiyasa ta iya zaman kissa, bare itama Hauwa bata da wata matsala, Mace ce mai sauƙin kai, shiyasa suke zaman su cikin girmama juna babu nuna Hassada bare baƙin ciki a tsakanin su, kowa tana ƙoƙarin iya takunta

Shi yasa shima Anwar yake jin daɗin zama da su, don har wani ƙiba yayi tsaban farin ciki da samun kwanciyar hankali, kowanne fanni ba shi da matsala ana kula da shi, gefe ɗaya kuma sai gurzan Angoncin shi yake yi yana mulka ƙiba kamar ba shi ba

Dalilin da yasa Muhseen ya ji sha'awar shima ya ƙara auren ko Allah zai sa ya dace da Matar da zata kula da shi, amma ba irin Munira wacce Mijinta kullum sai dai ya kwana da baƙin cikin ta; hakan bai shafe ta ba, ta ƙuntata ma Mijinta; ta faranta wa mutanen da ke tare da ita. Ga shi nan matsalar su sai gaba take yi yanzu, tun sanda Muhseen ya gindaya mata sharaɗin fita, to tun daga ranan suke faɗa da masifa a gidan, ta dena mishi komai ko abinci sai dai ta girka iya cikin ta, kullum cikin faɗa suke yi, da dare ma ba sa barci da masifa ake kwana, tace, "muddin bai janye ƙudirin sa ba, to wlh tallahi shi da zaman lafiya har abada, sai dai a ci gaba da zama a haka, ita baza ta fita ba, amma bazai taɓa jin daɗin ta ba."

Ga shi ita faɗan ta sai sun shiga ciki sun kulle ƙofa sannan take tayar da fitinan nata, duk zaman su Umma basu taɓa fahimtar irin zaman su na samun saɓani ba, baza ta taɓa buɗe baki a gaban mutane tayi faɗa ba, sai ita da shi

Shi yasa ko Muhseen ɗin ya kai ƙaranta, sai Umma ta ƙi yarda, tunda gani take yi har da rashin haƙuri na Muhseen ɗin yana zafafa wa, amma Munira ai yarinyar kirki ce, in bai yi haƙuri da ita ba kowacce Mace ma bazai iya zama da ita ba, basu san shi kaɗai ya san me yake ƙunsa na baƙin cikin ta ba, gaba ɗaya ba shi da sukuni da kwanciyar hankali, don har faɗa wa yake yi, ya rame kamar ba shi ba, duk wanda ya san shi shekarun baya kafin yayi aure, bazai ce shi ne yanzu ba

Da farko da ya kawo wa Anwar maganar zancen sake auren nasa, sai yayi dariya yace, "Ni ina ga wannan ba shi ne maslaha ba Abokina, kamata yayi a ce ka zauna ka fahimtar da Munira a kan abubuwan da kake so da wanda ba ka so, amma ba wai ka ɗauki wannan matakin ba, duka-duka yaushe ne ka yi auren da zaka sake wani? Ka yi haƙuri ka sake haƙuri kamar yanda Umma ta ce maka babu saki a tsakanin ku, kuma na tabbata ko maganar ƙara aure ka je mata dashi baza ta taɓa amince maka ba, ka san yanda take son Munira dai."

"To ka fi son in zauna in ci gaba da ƙunsan baƙin cikin ta kenan? In da Munira zata sauya ai da tuni ta sauya, Munira halin ta ne baza ta taɓa canza wa ba, wlh ka ji na rantse maka na soma dana-sanin auren yarinyar nan, nayi dana-sani matuƙa, kuma bazai yiwu a ce in ci gaba da zama a haka babu farin ciki ba, kullum ina ƙunsan azaba da baƙin cikin ta, ta ƙi ta sauya, Munira tana da taurin kai matuƙa, dole ne in auri wacce zan samu sauƙi a gare ta, wacce ta san darajar Miji kuma zata ɗauke Ni da ƙima da mutunci ta bani girmana. Kai ba ga shi kana zaune da naka Matan ba dukka cikin kwanciyar hankali? Allah ya ba ka kayi dacen Mata na gari, to me ya fi wannan Abokina? Ji be yanda kake mulka ƙiba kana jin daɗin ka fa, duk sabida ba sa raina ka ne suna yin abun da kake so; shiyasa kuke zaune lafiya da su. to me ake da irin Munira?"

Dariya Anwar yayi yana ɗaura hannunsa a saman kafaɗan shi, tare da cewa, "I feel the pain of what you are feeling my friend. Ka bi komai a sannu, kar zafin abun da take maka ka ce zaka ɗauki mataki."

Murmushi mai ciwo Muhseen yayi, tare da faɗin, "to ai idan zan ɗauki mataki tun farko da tuni na ɗauka, sai dai an fi ƙarfi na Anwar, auren Munira tamkar ƙaddara ce a cikin rayuwata, zan ci gaba da haƙuri har zuwa lokacin da zan samu wacce ta dace da tsarin rayuwata. Sai dai akwai hukuncin da na yanke." Sai yayi shiru yana shafa gefen kumatun sa tare da jan numfashi a hankali

Yayinda Anwar ya bi sa da kallo bai ce komai ba; yana jiran ya ji mai zai faɗa mishi

Ɗago kai yayi ya kalle shi yana faɗin, "dole zan ajiye aikina gaskiya, ina son in nemi aiki a wata Jahar, sabida nisanta kaina da Munira shi ne zai kawo min kwanciyar hankali, kwata-kwata ba na son faɗan nan da muke yawan yi. I am so tired of this happening, don na ga kamar hakan zai fi samun daidaito a tsakanin mu."

"Haba dai? Taya zaka ajiye aikin ka ka koma wani wajen? Gaskiya bazan ji dadin hakan ba, tamkar mun yi nesa da juna ne fa?"

"To ya zan yi Abokina? Ina buƙatar hutu da farin ciki ko ɗan ya ya ne a cikin rayuwata, ina ga don tana gani na kullum ne take min irin wannan abubuwan, amma ka ga in na matsa gefe sai jefi-jefi zan dawo ina duba su, zaman mu zai fi daɗi." Ya ƙare maganar yana murmusawa

Anwar yace, "shikenan, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi, amma taya zaka fara? Kuma wanne state kake son koma wa?"

Ɗan shiru yayi yana ci je leɓen ƙasan bakin sa, sai kuma yace, "I will write a letter and send it to the president, if I am lucky, he can change my place of work to Kano or Katsina. Since a can muke da reshe, ka ga ba sai na ajiye aikin ba ma."

"Haba dai har waɗannan garuruwan? Ina laifin ko nan Zaria ne ka koma."
    
        
"Yo ai babu amfanin canza wurin aikin kenan in har zan koma Zaria da aiki, ka san Umma ma baza ta bari in riƙa kwana ba, zata ce in riƙa dawowa kullum, Ni kuma ba haka nake so ba, gwara dai in yi nesa sosai zai fi."

"Well. Allah yasa a dace to, ka san shima Ogan akwai tashi matsalar. It can cause problems since you know he prefers you here."

Murmushi yayi yace,

Please Login or Register in order to submit comment