Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai ga ta cinye tunda ya bata time sosai, amma koda ya ɗago ya dube ta ya ga bata ci wani da yawa ba, tuni ta tsame hannunta tayi gefe ta ƙi ce mishi ta gama, sai ya miƙe yana cewa, "har kin gama ne wai?"

Ɗaga masa kai tayi

Yace, "ok tashi ki je ki wanke hannunki kar ɓera ya gutsire miki cikin dare; don idan kika kwanta a haka babu ruwana."

Murmushi tayi tana rufe fuskarta, sai ta miƙe a hankali ta nufi toilet ɗin da Hijabin ta a jiki,
Koda ta shiga tsawon lokaci ta ƙi fitowa duk da ta gama abun da zata yi, fargaba da tsoro ya hana ta saƙat, ji take yi kamar ta saka kuka a wannan lokacin, sai yanzu take ƙara jin ta wani iri jikinta sai kerma yake yi

Jin shirunta ta ƙi fitowa shiyasa ya kira sunan ta

Hakan ne yasa dole ta fito daga toilet ɗin

Jamal ya rigada ya san cewa dole hakan zai kasance, shiyasa ya lallaɓa ta yace, "ta hau kan gadon ta kwanta."
Bai takura mata ko ta cire Hijabin ta ba bare ta sauya kaya,
Yana ganin ta hau kan gadon sai ya fita Falo domin ya duba ko su Sumayya sun kwanta, ganin babu kowa sai ya dawo ya rufe nasu ƙofan yana kashe fitilar, da hasken wayansa ya samu ya ƙariso bakin gadon ya zauna, ya ɗan ja lokaci before ya miƙe ya sauya kayansa zuwa jallabiya ya hayo kan gadon ya kwanta, sai da ya matso sosai kusa da ita sannan ya buɗe blanket ɗin da ta rufe jikinta, ya shige ciki yana sanya hannu tare da rungumo ta ya sake matsowa sosai ya manne mata

Lokaci ɗaya Hafsah ta rikice, dama ta kasa ko runtse ido sabida tsoron abun da zai biyo baya, tana jin ya hayo gadon gabanta ya soma buga wa, bata sake rikice wa ba sai da ta ji ya manne mata, tayi sauri da nufin janye jikinta

Amma sai ya sake ƙanƙame ta yana raɗa mata a kunne, "shii! Ki kwantar da hankalin ki, babu abun da zan miki, ki koma ki kwanta Please."

Kasa motsa wa tayi duk da tsoro da fargaban da ke tare da ita ya kasa sakin ta, kamar zata yi kuka shi kansa yana jin yanda jikinta ke faman rawa

Murmushi yayi kawai ya sake ƙanƙame ta idanunsa a rufe yana jin sautin numfashinta da ke haɗe wa da nashi, bai yi motsi ba tsawon lokaci yayi kamar yana barci

Hakan ne yasa Hafsah ta yarda cewan babu abun da zai yi mata, tunda ta ji shiru bai sake kula ta ba, amma fargaba yasa ta kasa runtsa wa tayi muƙus tana faman sauke numfashi da ke fita da ƙarfi sabida halin da take ciki. Tun tana sanya tsammanin wani abu zai biyo baya har ta cire rai ta soma dawowa cikin hayyacinta, daga ƙarshe barci ya sure ta batare da ta san da zuwan sa ba

Sai da ya tabbatar tayi barci sannan ya buɗe idanunsa ya ɗan sake motsa wa yana sake manna ta sosai a jikinsa, idanunsa ya zuba mata duk da ba ya ganin ta, mamaki yake yi wai yau yarinyar da take a matsayin ƴarsa; ita ce yau ta zama mallakin sa kuma har suka kasance a gado ɗaya tare? Allah buwayi kenan; gagara misali, mai sauya rayuwar Bawan sa a duk yanda ya so, abun da basu taɓa tsammanin zai kasance ba, sai ga shi yau Allah ya nuna ikon sa a kansu, lallai Allah shine Allah. Rayuwa kenan!
Bai iya barci ba saboda farin cikin zuwan wannan ranan, ya kasa runtsa wa sai tunane-tunane da yake ta faman yi, dama bai yi ninyar yin mata komai ba shi yasa ko kusa bai yi gigin taɓa ta ba, ya san komai lokaci ne, yanzu Hafsah ta zama tashi ta har abada, babu mai raba su da juna, don haka kamar yanda ta kasance tashi a yau ga su rungume da juna; wata rana yana fatan ace sun zama tsoka guda sun dunƙule sun zama ɗaya,
Ya daɗe a haka before ya samu barci ya ɗauke sa cikin wani irin yanayi mai daɗi tare da mafarkin Hafsah a cikin ransa.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


               Almost 4 months kenan da haihuwar Munira, ta haifi ɗa namiji wanda ya ci sunan Mahaifinsa Muhseen, sun sanya mishi Aaqib *(follower)*

Yanzu haka har an sanya Hanan a makaranta ma

Itama yarinyar Afnan tayi wayau babu inda ba ta taka wa KUBRAH,
Dama aka ce yau da gobe rayuwa takan sauya, musamman idan ka biye wa zuciyarka da kuma zugin mutane, a dai zaman su Afnan babu wata matsala tsakanin ta da Hauwa, amma yau da gobe maganganun mutane da kuma abubuwan da ke faruwa a zamanin nan namu; hakan ne ya sanya ta soma nuna wa Hauwa ba ta son tana ɗaukar mata yarinya, mutane suna faɗa mata kishiya ba abar yarda bace ko ya kuke da ita, komin mutuncin da zata yi miki ki iya takun ki, wasun su suna fake wa ne da soyayya domin su cin ma manufar su a kansu, bare yanda Hauwa ba haihuwar take yi ba, ita kuma daga zuwa ta ajiye ƴa, ba don Allah ya ɗauke ɗaya da tuni sun zama su biyu ne, dole zata ji haushinta har ta iya cutar da ita, abun da ƴan uwa da zigin mutane suke faɗa wa Afnan kenan, tun ba ta ɗaukar maganar nasu tana ganin tamkar Hauwa baza ta taɓa cutar da ƴarta ba, har ta soma yarda tunda suna kawo mata misalai da irin tsananin soyayyar da Hauwa take nuna wa yarinyar, sannan kuma kwanan nan labarin wata mata ya baza gari a cikin rediyo, ta zuba wa ƴar kishiyarta fiya-fiya ta mutu har lahira; sabida tana jin haushin ita bata haihu ba, labarin dai babu dadin ji, shiyasa Afnan ta tsorata da Hauwa ta dena yarda tana ɗaukar mata yarinya, duk da bata fito ƙarara ta nuna mata ba ta so ba, amma a yanda take mata dole mai hankali zai iya fahimta,
Da zaran yarinyar ta je wurin Hauwan; zata amshe ta nan da nan tace mata, "zata yi mata abu kaza," ko "zata je ɗaki ta canza mata kaya." Sai ta ɗauke ta ta tafi da ita,
Duk da dama Hauwan ita take mata komai har wanka da cin kashin ta, ita take kula da ita wuni yarinyar tana hannunta in har ba Anwar bane zai amshe ta, Afnan bata san wahalar yarinyar ba ko kaɗan, sai yanzu da ake zuga ta take ƙoƙarin yakice ƴar, kwata-kwata ba ta son Hauwa ta ɗauke ta domin wlh tsoro take ji,
Abun haushin ma Kubran ta saba da Hauwa sosai, gani take yi kamar ita ce Mamanta shiyasa idan har ba Hauwa ta ɗauke ta ba, ba ta yarda da kowa, already ta saba da ita, ko barci take yi a ɗakin Mamanta, da zaran ta tashi zata sulale ta wuce dakin Hauwa tana kiran ta, Afnan ɗin ma bata san ta je ba sai ta zo neman ta zata ganta a can, abun ya soma ƙular da ita sabida yanda ta dage tana son yakice ƴarta, amma Kubran ta botsare ta dinga kuka tana komawa wurin Hauwa, duk inda Hauwan ta bi wurin ta zata je tana kiran ta da suna Mama, a dole baza a raba su ba,
Hakan ne yasa Afnan ta fusata in ta ɗauke ta ta soma mata kukan; sai ta bubbuge ta sannan zata yi shiru, ba ta barin ta ma tana fita ko falo ne in har batare zasu fita ba ta riƙe ta ko ta ɗauke ta,
Ko Hauwa ta miƙa hannu zata amshe ta sai tayi kamar bata ganta ba ta hana ta, in ta buɗe baki tayi mata maganar ta kawo ta sai tace, "a'a zata yi mata abu kaza ne." Ko kuma ta tsiri dube-dube a jikin yarinyar kamar dai akwai abun da take mata shiyasa bata bata ba,
Ko a gaban Anwar ne sai dai shi ya amshe ta amma baza ta ba Hauwa ba

Yau da gobe tunda ita ba wawiya bace; ta soma fahimtar me Afnan take nufi, amma kuma wani abu irin na Hauwa, tana ma Mutum uzuri sosai, ta ƙi saka abun a ranta bare ta yarda cewan Afnan tana ƙoƙarin hana ta ɗaukar ƴarta ne, tana son yarinyar sosai shiyasa ta kasa janye jikinta, ko me zata yi mata bata da zuciya haka zata sake ce mata ta bata yarinyar, idan ma ta kawo mata wani uzurin sai ta zauna zaman jiran sai ta gama sannan ta bata yarinyar ta ɗauke ta

Hakan na ƙara ƙular da Afnan, ta soma gajiya wlh,
Shi yasa yau ma da zasu tafi asibiti tare da Anwar, dayake Afnan ɗin tana fama da ciwon ciki ya matsa mata a kwana biyun nan, sun shirya zasu tafi ta je ta amso ƴarta a wurin Hauwa tace mata, "zasu je asibiti."

Hauwa tace, "ta bar mata ita a wurin ta zata riƙe ta tunda ba rigima zata yi ba har ta je ta dawo."

Sai ta haɗe rai tace, "a'a gaskiya, ki bani ita mu tafi tare don zan fi samun sukuni gaskiya, kuma kinga nonuwa na sun yi min nauyi na fi son in je da ita; ko zan samu in shayar da ita in samu sassauci."

"To." Hauwa tace tana miƙa mata yarinyar; fuskarta da ɗan Murmushi ko damuwa bata yi ba

Ita kuma ta amshe ta ta wuce daki ta canza mata kayan jikinta,
Yarinyar sai fitina take yi amma bata saurare ta ba, after ta sauya mata kayan ta fito ta samu Anwar ɗin yana zaune a falo shi da Hauwa

Shima ganin da Kubra za a je, sai yace, "ta bar ma Hauwa ita mana tunda ba lafiya ta cika ba, ba wani jima wa zasu yi ba."

Amma furr ta nuna a'a, tace, "su tafi kawai da ita zai fi."

Bayan sun fita ne Anwar yake ce mata, "ya ga alamun kamar ba ta son barin yarinyar ne kamar wani abun za a yi mata? Bayan ga Hauwa nan baza ta ji dad'i ba ta ɗauki yarinyar, kuma ta saba barin mata amma yau ta dage a'a."

Afnan tace, "baza ka gane bane, amma Ni na fi so Yarinyata ta riƙa zama kusa dani zai fi gaskiya, ba na son ana daukar min ita bazan yarda da kowa ba."


Da mamaki yake duban ta yace, "me kike nufi ne wai? Hauwa fa nace ki bama ƴar; ba wai wata ba."

"To ita ɗin mana, Ni fa wlh tunda na ji labarin nan a rediyo hankalina ya soma tashi, duk wani so da kulawa da mutum zai nuna wa ƴarka baya ga na Uwa ce, don haka a bar min abata in dai fita zan yi da ita zan je ko'ina wlh, duniya babu yarda."

Shiru yayi yana sake mamakin maganar nata, abun da ya fahimta wato so take yi tace bata yarda da Hauwa ba, anya Afnan tana da hankali kuwa? "Afnan kin san abun da kike furta wa kuwa? Hauwa ce fa, kuma koda wani zai cutar da ƴarki ai ba na tunanin za ki sako Hauwa a cikin wannan zancen, ture batun ma zata cutar miki da ƴa, a yanda na san Hauwa take so na na tabbata baza ta taɓa cutar da abun da na haifa ba koda ba ita ta zuƙuna ta haifar min ba, wlh raina ya ɓaci saboda wannan maganar naki, ya kamata ki san abun da za ki riƙa furta wa a kanta don bazan lamunta ba, ita Matana ce tana da right da zata ɗauki abun da na haifa, ba na son irin wannan shirmen kar ki soma gigin sake aikata wa; kina jina?"

Kallonsa tayi ranta a ɓace, sai dai ta ƙi yin magana sabida rashin jin daɗin jikinta a lokacin, amma tuni hawaye sun soma zubo mata a kan kunci

Bai yi mata magana ba duk da ya ga yanda take hawayen, har ga Allah bai ji daɗin irin halin da take ƙoƙarin laƙaba wa Hauwan sa ba, don ba ya tunanin koda wasa a halin Hauwa da kirkin ta zata iya aikata wani abu makamancin haka, su ma waɗanda suke aikata wa rashin imani ne da kuma jahilci ke damun su, suna manta akwai Allah shiyasa har suke makance wa suke wannan mummunar aikin duk kawai a kan kishi, tabbas Afnan bata da laifi in ta dauki wannan matakin tunda yanzu duniya ta ɓaci, Mata suna yin komai a kan kishi, ki ji wata ta kashe wata sabida kishi, Kishiya ta kashe ƴaƴan kishiya saboda kishi, wannan duk ba kishi bane Hassada ne da kuma jahilci da rashin imani, shi kansa a kwanakin nan ya sha jin labarai makamancin irin wannan abubuwan da ke ta faruwa a gari, amma koda wasa bazai taɓa kawo Hauwa a irin wannan Matan ba, kuma bazai lamunta Afnan ta hana ta ɗaukar ƴarta haka kawai a kan tunanin ta na banza da hofi ba.



         Basu sake yin maganar ba har suka je suka dawo, don tuni ma shi ya manta sai dai ita Afnan ɗin da abun ke ranta, tunda har ga Allah baza ta canza daga ƙudurin ta ba,
Kuma bata sauya ɗin ba, yau da gobe har Hauwa ta soma fahimtar me Afnan take nufi da ita,
Shi yasa abun yayi mata ciwo matuƙa, bata san dalilin hana ta ɗaukar mata ƴa ba, amma ko ma mene ne ta san kamar tana son cin mata fuska ne ko yin mata gori don kawai ita bata haihu ba,
Bare dama tana cikin wani hali da ƙuncin rashin haihuwa, kowacce Mace idan tana jin wannan ciwon; in har aka hana ta ɗaukar Yara to tana ganin kamar gori ake mata don ita bata haihu ba, shiyasa abun ya yi wa Hauwa zafi ta dinga kuka ta kasa faɗa ma kowa, sai dai ta shiga ɗaki ta sha kukan ta babu mai gani bare yayi tunanin halin da take ciki, kuma tun daga lokacin ta rage daukar Kubra duk da ita yarinyar ta saba da ita koyaushe sai ta je wurin ta in ta samu sake, amma tana ƙoƙarin danne sonta ta ƙi ɗaukar ta bare ma wani abun ya biyo baya

Anwar bai fahimci komai ba tunda Hauwa bata sanar mishi ba, ita kuma Afnan bata yi yanda zai gane ba, in fact ma ba ta nuna komai in a gabansa ne, kuma in ma suna tare dukkan su shi yake ɗaukar ta ba ya bari kowa ya ɗauke ta sabida SOYAYYA da yake nuna mata

Ana haka Sauda ta haihu ta samu ɗa namiji wannan karon ma, lokacin ma har sun yi kusan wata ɗaya da tarewan su a sabon gidan su

Dayake Hauwa bata samu zuwa ba tana ta yi wa Anwar maganar zata je, but ya ƙi barin ta, ita kuma ta dena zuwa ne tunda tun barin su gidan hayan nan bata ƙara zuwa ba, sai dai Sauda ta zo wurin ta, tun Sauda na yin fushi tace, "baza ta ƙara zuwa wurin ta ba tunda itama bata damu da ita ba."
Sai ta dauki tsawon lokaci ba ta kiran Hauwa kuma ba ta zuwa gidan ta, daga baya kuma sai ka ganta ta zo bata yi zuciya ba, tayi ta mitan Hauwa ta zo wurin ta but amma ina har lokacin Hauwa ta ƙi zuwa sai dai ta kawo mata uzuri kala-kala

Sauda tace, "ko bata faɗa mata ba ta san Mijinta ne ya hana ta, amma shikenan itama baza ta ƙara zuwa ba, dama rashin zuciya ce irin nata shiyasa har yanzu bata yi fushi da ita ba."

Hauwa hakuri tayi ta bata amma a wannan time ɗin Sauda tayi fushi ba kaɗan ba, abun haushin ma har suka tare Hauwa bata je gidan ta ba, hakan ne ya ƙara fusata ta; ga ciwon da ta dinga yi sabida cikin nan da ya zo mata da matsala, amma babu Hauwa babu labarin ta, sai dai ta kira ta a waya ta bata haƙuri tana ce mata, "Anwar ya hana ta zuwa."
Itama sai ta yanke alaƙar su tace, "shikenan tunda ya nuna ba ya son su ci gaba da hurɗa itama baza ta sake neman ta ba, domin abun da tayi mata taji zafi baza ta ɓoye mata ba, a wannan karon ta barta har abada in har ba ita ta neme ta ba."

Koda ta haihu ma sai dai Ruƙayya ta kira Hauwa ta sanar mata, "Sauda tana asibiti kwanan ta biyu bata san inda kanta yake ba." saboda haihuwar ta zo mata da matsala ba kaɗan ba, tun da cikin ma take faman shan wahala har kawo yanzu da ta haifa

Hauwa tayi nacin Anwar ya bar su su je; koda ita kaɗai ce ya barta, but amma ya ƙi,
Shi yasa da aka faɗa mata haihuwar nan hankalinta ya tashi ta sake samun sa da maganar har da kukan ta, saboda matuƙa ta shiga damuwa da halin da Sauda take ciki, ita bata ga mai Sauda ta yi wa Anwar ba da yake nuna tsanarta ƙarara yanzu, kuma idan ma ya yanke alaƙar su ai wannan ciwo ne yana wuyan kowa, baza ta so Sauda tayi fushi da ita a kan hakan ba

Shi kuma nacin da take masa ne abun ya fusata shi yace mata, "wlh baza ta taɓa zuwa ba, ko ita mayya ce sai dai ta haƙura ta ƙyale shi, mai Saudan take bata da dole sai ta nace sun yi alaƙa? Ya raba su amma ita kamar Mayya bata da zuciya ta bi ta ishe sa da zancen ta, to in har ta sake mishi maganar sai ranta ya ɓaci wlh."

Ita kuma Hauwa kalman mayyan da ya ambata mata yayi mata zafi, tana kuka ta kalle sa tace, "tabbas ina da zuciya ba rashin ta bane yasa nake maka maganar koyaushe ba, idan kuma Ni Mayya ce zaka fi kowa sani tunda kai kake tare dani a gidan, bazan sake maka magana ba in Allah ya yarda daga yau, kayi haƙuri."
Daga haka ta fice a ɗakin ta koma nata ɗakin tana faman zubar da hawaye, haka kawai ta ji ciwon maganar da yayi mata shiyasa ta wuce ɗakinta ta ƙi koma wa nashi duk da ita ne dashi, ta fi son ta zauna ta samu sassaucin halin da take ciki sabida ba ta son ranta ya ɓaci a banza a hofi, bata iya fushi ba kuma ba ta iya jure wa yanayin sabida yana cutar da ita, in har tayi fushi tana shan wahala matuƙa, bata saba ba Mace ce mara ɗaukar komai da zafi, amma duk randa ranta ya soma ɓaci tana cutuwa sosai, domin fushin da take yi kowa sai ransa ya ɓaci in ta hau dokin fushi,
Shi yasa ta janye jikinta tayi kwanciyarta a ɗaki bata koma nasa ɗakin ba

Wannan abun da tayi ne; a wurin Anwar don me? Har ita a kan wata banza can zata yi fushi da shi? Gani yake yi kamar ta fifita Sauda fiye dashi Mijinta, tunda tun farko ya raba su amma ta nuna mishi bai isa ba, yau har ita take mishi yaji a ɗaki duk saboda Sauda; abun da bata taɓa yin masa ba tsawon wannan lokutan?

Hauwa ta nemi ta ba shi haƙuri zafin da ya dauka safiyar ranan da ya bi ta ɗaki ya dinga surfa mata bala'i, amma bai saurare ta ba sai ma fita da yayi ya bata wuri,
Daga lokacin ya ɗauke mata gaba ɗaya ya dena kula ta, ko abincin ta ba ya ci bare ya shiga ɗakin ta

Dama idan sheɗan ya gilma a tsakani komai yana iya yi, bare in ya ga ma'aurata suna zaman lafiyar su, to a wannan lokacin yayi tasiri a kan su domin ita kanta Hauwa ta shaƙa da abun da Anwar yayi mata, a ganinta bata yi masa komai ba tunda ta ba shi hakuri tun farko amma ya dauki wannan gaban da ita yana haɗe mata rai, sai ta fita harkansa bata sake bi ta kansa ba bare ta ƙara ba shi wani haƙurin

Shi kuma jira yake yi ta zo ta same shi ta kwantar da kai kamar yanda ta saba mishi; tana bin shi tana ba shi haƙuri

Amma furr Hauwa ta ƙi zuwa, ta ci gaba da rayuwarta a haka a gidan suna zaune zaman doya da manja,
Har Afnan ita kanta sai da ta fahimci zaman nasu, amma babu ruwan ta tunda bai shafe ta ba, abun ma farin ciki da murna ne a wurin ta shiyasa ta ƙara kama Mijinta gam tana basa duk wata kula wa,
Don Anwar ya ƙular da Hauwa ya biye mata ya canza takun soyayyarsu babu irin kulawa da tarairayan da ba ya bata ita da ƴarta tamkar ya haɗiye su

Basu farga ba sai dai suka nemi Hauwa suka rasa a gidan ta gudu, kusan kwanan ta biyu da tafiya basu san cewa ba ta gidan ba sai daga baya.
[26/01, 9:57 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:40*

_____Da farko Anwar yayi nufin bazai nemi Hauwa ba tunda bada iznin sa tabar gidan sa ba, tabbas ya nuna bazai damu da ita ba tunda kusan sati ɗaya kenan da tafiyar ta amma bai neme ta a waya ba, yace, "idan ta gaji da zaman gidan zata dawo, tunda nan ne rufin asirin ta."
Kuma iyayenta basu neme sa ba; haka shima Iyayansa basu yi masa maganar ta ba, tunda basu san da cewan Hauwa ta bar gidan sa ba, hakan yasa shima bai basu labari ba ya bar abun a ransa

Can kuma tunda Hauwa ta koma gida ta kwanta ciwo rigigim,
A lokacin hankalin Hajiya yayi matukar tashi, ta rikice ta shiga tashin hankali da ta ga Hauwa ta dawo mata a wannan yanayin a firgice duk ta rame, ga kayanta da ta zubo a Jaka; wadda hakan yasa tayi tunanin Anwar ne ya sake ta,
Amma koda ta bincika sai Hauwa ta sanar mata da halin da take ciki

Tace, "ta gaji ne baza ta ci gaba da zama a haka tana ƙunsan baƙin ciki ba, zuciyarta zata iya buga wa ta mutu sabida yanda take ji a wannan lokacin."

Tabbas Hajiya ta yarda cewa an kai Hauwa maƙura, har zuciyarta gaskiya take faɗi, ta tausaya mata matuƙa musamman yanda ta ga ta kwanta jikinta ya rikice sai zazzaɓi,
Shi yasa ta kira Yayansu ta faɗa mishi halin da ake ciki

Duk da ba ya garin yana zaune a Zaria ne tare da Iyalansa, amma haka a ranan ya taho suka ɗauke ta zuwa asibiti,
Sun yi tunanin kiran Anwar amma kuma basu samu dama ba har a washe gari

A ranan jikin Hauwa da ɗan sauƙi tunda zazzaɓin ya sauka mata, har tana iya zama, sai dai babu walwala a tare da ita ko kaɗan tana cikin tsananin damuwa,
Koda ta ji suna maganar zasu kira Anwar su sanar mishi halin da ake ciki, amma ita ta nuna ba ta bukatar haka, kar su kira sa

Hajiya tace, "ai dole ne Hauwa tunda har yanzu Mijinki ne, kuma da rashin sanin sa kika fito gidansa kika dawo gida, dole mu kira sa mu faɗa masa halin da kike ciki ko bazai zo ba."

"Gaskiya ne Hajiya, ya kamata a kira sa a sanar mishi don ya san halin

Please Login or Register in order to submit comment