Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"lafiya lau, ya su Fauziyyan?"

"Suna nan lafiya Mama."

"Ai nayi tunanin sai zuwa gobe zaka shigo tunda na ga yammaci tayi, ashe dai zaka zo ɗin?"

Yace, "haba ai tunda na ce zan shigo dole zan shigo Mama, na kwanta nayi barci ne shiyasa ban samu na zo da wuri ba."

"Allah Sarki! Jiki da jini, kai ne ma ba ka jin magana da ka zauna sai zuwa goben ai."

Murmushi kawai Jamal yayi bai ce komai ba, sai kuma ya sauya hiran da faɗin, "ina Hafsah? Ko har ta tafi Islamiyyar ne?"

"Ina fa, tana nan kwance tun ƙarfe ɗaya, ban bata labarin ma zaka dawo ba tunda tana can tana sharan barci, yanzu nake cewa zan idar da Sallah sai in tashe ta."
Sai ta yunkura da nufin mike wa tana cewa, "bari in tashe ta kar lokacin sallah ya ƙure mata."

"A'a Mama, zauna, bari Ni in tashe ta." Sai ya miƙe yana ajiye mukullin Motan sa

Mama tace mishi, "tana nan cikin ɗakin ta a nan ta kwanta."

"Ok." Ya amsa mata yana wuce wa kansa tsaye ɗakin ya shige.




_Ina jin masu ƙorafe-ƙorafe ba a update kullum, a baya ina yin update da yawa amma rashin samun comments yasa na dena, don haka in dai ba a gyara ba nima a haka zan ci gaba da tafiya, sai sanda Allah yayi ku ka ga update._
[03/01, 4:54 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼












            *PAGE:28*

_____Shigan shi ɗakin ya tarar da Hafsah kwance a saman gado, sai sharan barci take yi har da wangale baki, alamun barcin yayi mata nisa sosai, babu ranan ma tashi, tsaya wa kawai yayi yana kallonta tare da ƙare mata kallo, tsab ya tsaya yau ya gama ƙare wa yarinyar kallo, shi gani yake yi kamar ma har da cuta aka yi mata, yarinya ƙanƙanuwa ace wai ita ce Matarsa, to taya zasu yi rayuwar aure? Anya bazai sanar da Mama illan wannan auren ba? numfashi kawai ya ja tare da ƙarisa wa bakin gadon ya soma jan pillown da tayi matashi dashi, but ganin ta ƙi tashi sai ya saka hannu a hankali ya soma taɓa mata cinya yana bubbuga ta, ƙarshe har sai da ya ƙara da kiran sunan ta tukun ta soma motsa wa ta buɗe idanunta

Kamar a mafarki take ganin fuskar nasa, shiyasa tayi saurin wartsake wa tana ƙara zare ido a kansa duk ta daburce

"Ke haka ake yi? Kin kwanta kin saki baki kina ta sharan barci?" Yayi maganar yana mata murmushi

Kunya ne ya kama ta tayi saurin ɗauke kanta a kansa tana neman inda zata ɗauki ɗankwalin ta

"Mama tace in tashe ki kiyi sallah, kuma na shiga haƙƙin ki na ga barcin ya yi miki dad'i, I'm sorry."

Ƙin ɗago wa tayi ta kalle sa sabida ji tayi kamar zata nutse don kunya, ko magana ta kasa yi tsaban yanda take adaburce sabida rigan da ke jikinta

Shi kuma Jamal ya tsaya ya ƙi tafiya yana ci gaba da ƙare wa halittar ta kallo, duk da yayi mamakin ashe tana da ɗan cika da abun kallo a jikinta, fahimtar halin da take ciki ne sai ya taɓe bakin sa ya juya ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba

Kuka ne kawai Hafsah bata saki ba sabida halin da ta shiga, yana fita ta sauke ajiyan zuciya tana kallon jikinta, sai ta ɗaura hannunta ɗaya a saman ƙirjin ta tana jin yanda zuciyarta ke harba wa kamar zata faso ƙirjin ta, wayyo! Bata taɓa tunanin zai dawo yau ba, bare ta saka ran zai iya shigowa ɗakin ta, jikinta sai rawa yake yi ta kasa tashi ma don tsananin kunya da tunanin da wanne idon zata kalle shi, Allah ya gani ta ji kunyarsa. Ganin time na sallah yana ta tafiya dole ta miƙe tayi alwala tayi sallan, amma kuma ƙarshe ta kasa fita Falon sabida jin yana nan har yanzu tana jiyo maganganun su da Mama

Shi Jamal ma ya manta da ita sai harkan gabansa yake yi, yana zaune yana cin abinci wanda Mama ta ɗibo masa tunda yace yunwa yake ji

Sai da suka ji shiru ne Maman take kwaɗa mata kira

Dole yasa Hafsah ta fito falon, bayan ta saka Hijabin islamiyyarta

"Wai dama ashe za ki je Islamiyyan amma kika zauna tun ɗazu kamar an riƙe ki?"

"Eh Inna zan je." Ta furta kanta a ƙasa, sai kuma ta duƙa tana gaishe da Jamal

Ya amsa ta cike da kula wa yana tambayarta, "ya school ɗin?"

"Alhamdulillah."

"Masha Allah, ba kya buƙatar komai a kan harkan makarantan ko? In dai akwai wata matsalar ki sanar min."

"Babu wata matsala Dady." Tayi maganar kanta a ƙasa tana wasa da yatsun ta

Mama tace, "dauko masa ruwa kafin ki wuce, ki haɗa masa da furan nan dana ajiye wataƙil zai buƙata."

"A'a Mama, ruwan ya isa kawai."

Bayan Hafsah ta kawo mishi sai ta koma cikin daki ta cire Hijabin, cikin sauri ta sauya kayan jikinta ta saka riga da skirt sannan ta zumbula Hijabin, ta ɗauki Jakarta ta fito. Ta yi wa Maman sallama zata wuce

Jamal yace, "ta tsaya ya sauke ta tunda shima gidan zai koma."

Babu yanda Hafsah ta iya dole ta tsaya, duk da rashin son haɗuwar ta da Jamal dole hakan sai ta faru, amma kwata-kwata ta kasa sakin jikanta ko kallon sa ba ta son yi bare su haɗa ido

Shi kansa ya fahimci yanda ta kasa sakin jiki da shi ba kamar baya ba, ga kunyar sa da take ji sai wani nuƙu-nuƙu take yi, shiyasa bayan sun shiga Mota sun tafi yake tambayarta, "ko Mama tayi mata wani magana ne a kansa?" Don shi yana ji a jikinsa dole ta san da zancen auren su yanzu, a yanda ya fahimta kenan

Hafsah duk ta rikice ta kasa ba shi amsa tunda bata san me zata ce ba

"Kin yi shiru, ki sanar min mana? Da alamu an faɗa miki maganar auren mu ne ko?"

Kai ta sunkuyar a ƙasa tayi shiru

Murmushi kawai yayi, sai yayi shiru ya ci gaba da tuƙin sa, can kuma sai ya sake cewa, "Hafsah ina son tambayar ki, ki faɗa min iya gaskiyar ki. Kina so na ko kina ji a ranki za ki iya zama da Ni?"

Da ya san yanda Hafsah take ji a wannan lokacin, da bai yi gigin yin mata wannan tambayar ba, to me yake so tace? Yanda take jin kunyar sa ma baza ta iya buɗe baki tayi magana ba

Shi kansa ya san da haka, musamman yanda ya ga ta ƙara takure wa waje daya ko ɗago kai ta ƙi tayi bare ta amsa mishi tambayar, shiyasa ya furta, "is ok kawai." Bai sake yin magana ba har ya kaita bakin makarantar, sannan ya ciro kuɗi ya bata yace, "ta riƙe a hannunta."
Ta kasa amsa sai da ya kira sunanta babu wasa a tare da shi yace, "karɓa mana, mene ne haka?"

Ɗago kai tayi suka haɗa ido, da sauri ta ɗauke kanta tana amsar kuɗin tare da mishi godiya cikin sanyin murya

"Ki kula da kanki, kuma da zaran an tashi kar ki tsaya wani wasa ki wuce gida."

"To."
Ta amsa mishi tana buɗe ƙofan ta fice

Shi kuma ya ja motan ya bar wajen

Yayinda Hafsah daƙyar take iya ɗaga ƙafafunta ta wuce cikin makarantar, yayinda komai da ya faru ya tsaya mata a rai, tun daga tashin ta daga barci da yayi har izuwa yanzu maganar sa na ƙarshe, tana ganin abun ne tamkar a mafarki har yanzu, shikenan kuma ita haka zata ci gaba da tafiya cikin wannan halin? Komai nata zai sauya baza ta taɓa sakin jiki da shi ba, wani ƙarin kunyar sa ne sosai ya ƙaru mata a zuciya, musamman yanzu da ya fahimci ta san da zancen auren, wai Dady shi ne Mijinta?
Wannan tunanin yasa ko fahimtar abinda ya kaita makaranta bata yi ba, sukuku ta wuni tare da fargaba a ranta har aka tashi, ta koma gida a haka babu wata walwala a ranta, tunda ko da second ɗaya bata saurara wa kanta da tunanin da ke ranta ba, ita dai baza tace ba ta ƙaunar Jamal ba, yana da matuƙar girma da ƙima a a idanunta, amma taya ya zata iya sauya kallon da take mishi a zuciyarta? Taya ya zata iya sakin jikinta da wannan maganar a ranta? Wayyo Allah! Ji take yi kamar ta gudu ta bar gidan; ta koma ƙauyen su, tunda ta san cewa in har tana nan zata riƙa haɗuwa da shi, kullum suna haɗuwa suna ganin juna, bata san ya zata yi ba.







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


           *SOME MONTHS AGO*
         Yau da gobe kayan Allah, rayuwa ta ci gaba da gudana cikin farin ciki da akasin sa, wasu ta zo musu a fari, wasu kuma ta zo musu a baƙi, kai wasu ma har ja take zuwan musu, kowa da tashi ƙaddarar

A gidan Anwar dai farin ciki ke tafiya har wannan lokacin, babu abun da ke shiga tsakanin Hauwa da Afnan face mutunci da mutunta juna kamar yanda suka saba, wanda a ƙanƙanin lokaci sai Afnan ta soma laulayin ciki, abun da Anwar ya jima yana bukata sai ga shi Allah ya ba shi a wurin Afnan, matuƙa yayi farin ciki ji yayi tamkar ya goya Afnan tsaban murna da tsananin zumuɗi, shiyasa wani soyayya da kula wa ya ƙara bata, babu irin abun da ba ya mata sabida kyautar da ya samu a gare ta, don gaskiya ba ya iya ɓoye farin cikin sa da kulawan da yake bata, musamman in ya kalle ta ya hangi cikin ɗan sa a jikinta, kwata-kwata ba ya iya control ɗin kansa ko a gaban Hauwa haka yake bata kula wa yana tarairayan ta kamar ƙwai, aiki ma wannan ba ya so tayi in har yana gida shi yake yin mata, ba ya barin ta tayi da kanta yana manne da ita yace, "dole shi zai yi."

Hakan ne yasa Hauwa take yin wasu abubuwan da kanta tunda ita baza ta iya zura ido tana ganin Mijinsu yana ayyukan gida da kansa ba, wani lokacin ma kashe ayyukan sa yake yi, kwata-kwata Hauwa bata taɓa saka abun a ranta ba bare ya dame ta, duk da dole akwai kishi tana ganin yanda Afnan ke shan tarairaya a wurin sa, amma ta san cewa duk sabida abun da ke cikin ta ne, itama da Allah ya bata hakan zai iya faruwa a kanta, bata taɓa ɗaura wa kanta damuwar hakan ba, da zuciya ɗaya take yin komai nata, kuma yanzu tuni ta cire rai da samun nata ɗan tunda tana ganin cewa kamar ita ce da matsalar, since ga shi Afnan daga zuwa ta samu ciki.





🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆



        Yayinda wasu suke farin ciki da ƙaruwar da suka samu, wasu kuma akasin hakan ne. Tunda a wannan lokacin fitina ne ta kunno gidan Shureim tsakanin sa da Intisar, tunda suka je asibiti aka yi mata gwaji aka tabbatar da tana da shigan ciki, shikenan ta tayar da hankalin ta a kan, "baza ta iya haihuwa yanzu ba, ita bata shirya haihuwa yanzu ba, tana da burin ci gaba da karatun ta har sai tayi nisa sannan zata soma tunanin wani haihuwa."

Shureim a tunanin sa wasa take yi, amma ganin a haƙiƙanin gaskiyar ta take maganar, hakan ne yasa yace, "to ban da hauka ita tana ganin har yanzu shi zai iya barin ta tayi karatu ne? Maganar da ya faɗa mata tun farko har yanzu ita ce, in har yana auren ta wlh gwara ta cire ranta a maganar ci gaba da karatu, kuma shi yana son cikinsa ya shirya haihuwa bata isa ta hana hakan ba."

Ita kuma Intisar ta dire a kan, "ta rantse da Allah bai isa ya tauye mata haƙƙin ta ba, ko ya barta tayi karatun nan ta yarda zata raini cikin ta haife shi, ko kuma ta zubar dashi."

Dubanta yayi zuciyarsa na ƙuna yace, "wlh Intisar ban taɓa tunanin ke Jahilar yarinya bace sai yanzu, to kina nufin zubar min da cikin za ki yi?"

"Eh wlh, sai na zubar, zan nuna maka ni babbar Jahila ce in har ka ƙi yarda da sharuɗa na, kana ganin har yanzu ina bibiyan ka ta lallama a kan ka bar Ni in koma makaranta amma sai min wasa da hankali kake yi, to wlh baka isa ba bazan zauna a haka ka tauye min haƙƙi na ba, ai tun farko kai ka cuce Ni ka hure min kunne; amma yanzu na aure ka ka ci amanata, na rantse da Allah sai nayi karatu na."
Ta ƙare maganar da kuka sosai

Wani irin dariyar takaici Shureim ya saki, tare da kallonta idanunsa jawur ya furta, "wlh tallahi, in har kika yi gigin zubar min da gudan jini na, sai kin yi babbar nadamar da ba ki taɓa yin sa ba a rayuwar ki, kuma zamu gani in ke kike aure na ko Ni nake auren ki."

Tsiya fa ya ƙi ƙare wa a wurin Intisar da Shureim, ƙarshe ma yaji Intisar tayi ta koma gida da kukanta ta sanar da Mahaifiyarta

Fauziyya tace, "ai wannan zancen banza ne zancen hofi, wai mai yake so ya mayar da ke ne wannan mutumin? To muddin kuwa yana ƙaunarki dole sai yayi abun da muke so, a kan me zai hana ki karatu bayan mu ba jahilai bane mun san daɗin karatun? Ki bar Ni dashi wlh zan ɗauki mummunan mataki a kansa, kuma cikin baza ki haife shi ba in ga ta tsiya, tunda abun da yace kenan dole a wannan lokacin yayi mana biyayya, zamu yi amfani da cikin nan ko ya bar ki ki ci gaba da karatun ki, ko kuma baza ki haife shi ba, tunda ba Jaka aka kawo mishi ba, karshe ma haka zai ci moriyar ki ya yasar da ke tunda ya samu abun da yake so, amma idan kina da ilmin ki kin fi ƙarfin wulaƙanci a wurin ɗa namiji, so yake yi kiyi ta hayayyafar Yara su kenan aikin ki; ƴar ƙaramar ki da ke? Ni na kula Yaron nan baƙin ciki yake miki tunda dai shima ya san daɗin karatun balle a ce Jahili ne kansa bai waye ba, amma zan dauki mataki, zama a gidan nan bai kama ki ba ko don mahaifin ki, yanzu zan ɗauke ki in kai ki wurin ƙawata gwara ki zauna a can zai fi."

Haka Fauziyya ta tattara Intisar suka fice a gidan ta kaita gidan ƙawarta ba tare da sanin kowa ba. Wanda kusan kwana biyu kenan Jamal bai san da zancen ba

Haka shima Shuriem bai kira ya neme ta ba, tunda ya sa a ransa in har sai ya je ya dauko ta ne sai dai ta dauwama a can, in sun gaji iyayenta da kansu zasu dawo da ita

Momyn shi tace, "gwara dai ya je ya neme ta ya dawo da ita gida zai fi, kar ya barta a can kuma ƙarshe abun da yake gudu ya afku, a zubar masa da cikin tunda tana ganin yarinyar kanta yana rawa, ga kuma ɗaurin gindin mahaifiyar ta tsab zasu cire masa cikin."

Hakan ne yasa Shuriem ya shirya ya tafi gidan, ai kuwa ya tarar da Jamal time ɗin Fauziyya ta tafi wurin aikin ta, sai su Sumayya da su ma dawowar su kenan. A nan ya sanar mishi bayanin abun da ya kawo shi zuwa ɗaukar Intisar

Jamal yayi mamaki, yace, "ai Intisar bata zo gidan nan ba yau."

"Dady ai Intisar kwanan ta biyar kenan tana nan gidan, tunda tayi yaji a kan hatsaniyar da muka yi ta taho, har yanzu bata dawo ba."
Nan ya sanar mishi da abun da ke faruwa kaf ya kwashe ya faɗa masa; tunda ya kula alamun bai san komai ba

Jamal fa ya ƙara rikice wa da al'amarin, hankalin sa ya tashi kuma ransa yayi mugun ɓaci, take ya kira Sumayya ya tambaye ta inda Intisar take? Don yana da yaƙinin dole ta sani

Ai kuwa jiki na rawa ta sanar mishi inda Fauziyya ta kai Intisar
     

Jinjina kansa yayi tare da miƙe wa yace ma Shuriem, "yana zuwa."
Ɗaki ya je ya saka riga sannan ya fito da key ɗin mota, yace mishi, "ya taso su je."

A tare suka fita, Shuriem na motan sa; shima yana nashi suka wuce kansu tsaye gidan ƙawar Fauziyya.
[03/01, 4:54 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:29*

_____Zuwan su gidan, Jamal yasa mai gadi ya kira mishi Intisar a ciki

Dayake shi bai gane wace ce Intisar ɗin ba, shiyasa kawai ya shiga ya sanar wa Matar gidan

Hakan yasa Hajiya Balaraba ta fito domin ta duba wane ne, ai kuwa nan ta ga Jamal da Shuriem tsaye a haraban gidan, ƙarisa wa tayi wurin su tana aza murmushin yaƙe tare da furta, "Au ashe Dadyn Intisar ɗin ne da kansa? Mu shiga ciki to."

Fuskarsa ba walwala yace, "ba zama ya kawo mu ba, ina Intisar ɗin?"

Ta so ta ɓoye mishi tace babu intisar a gidan ta, amma kuma ganin yanayin fuskarsa sai hakan ya ɗan bata tsoro tare da cewa, "tana ciki, bari in kira ta."
Ta juya zuwa ciki, tana shiga jiki na rawa ta soma neman layin Fauziyya, amma kuma ta ƙi shiga, shiyasa kanta tsaye ta haura upstairs inda ɗakin ƴaƴanta suke, ta shiga ciki ta tarar da Intisar ɗin ita kaɗai tana ta sharan barci, dayake cikin nata ba abun da yake saka ta sai barci, wuni tana kwance tunda ta zo ba ta tsinana uban komai. Tashin ta tayi tana cewa, "intisar tashi mana, Dadyn ki ne a waje yanzu ya zo ɗaukar ki, maza ki tashi."

Ai tuni Intisar ta wartsake tunda ta ji an ambaci Dadyn ta, salati ta saka tana kallon Hajiya Balaraban tare da waro ido waje, baki na rawa tace, "don Allah da gaske Dadyna ne?"

"Ƙwarai kuwa, yana nan a waje tare da Mijin naki, da alamu dai ya san komai shiyasa ya zo tarkata ki, gwara ki tashi ki fita kar ki ja wa kanki wata matsalar, kuma na kira wayan Momyn naki amma ba service."


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... Na shiga Uku! Ya zan yi? Wlh duka na zai yi."
Ta furta tana yarfe hannu cikin tashin hankali

"To ai kuma zaman naki ma matsala ne, dama wannan ranan nake gudu amma ba kya jin magana daga ke har Momyn naki ai, kun san zai ɗauki mataki in ya san abun da ke faruwa, gwara dai ki tashi ki fita tunda in ya ji shiru ƙarin laifi ne."

Amma ina Intisar ta kasa tashi ta fita sai ma hawaye da ta soma tana roƙon Hajiya Balaraba, "ta sake kiran Momynta ta ji ko zata zo ta cece ta."

Ganin yanda ta ruɗe sai tace, "Intisar mahaifin ki bazai buge ki ba tunda yanzu kin wuce duka a wurin sa, bare kina da ciki babu abun da zai yi miki, amma zaman ki ƙara wa kanki laifi kike yi, kinga dai ga shi ina ta faman kiran ta bai shiga ba, bari in haɗa miki kayan ki ki zo ki wuce."

Haka ta haɗa mata kayan daƙyar ta rarrashe ta suka fito waje, sai maƙe wa take yi a bayanta don ta san halin Dadyn nata tsab zai zane ta wlh, musamman da suka fita ta ga yanda fuskarsa take sai ta ƙara tsure wa

Shi kuma nuna mata hanya yayi yace, "zo ki wuce."

Babu musu ta nufi ƙofan fita gidan a ɗar-ɗar ta fice,
Su kuma suka take mata baya ko sauraron Hajiya Balaraba da ke yi wa Jamal sallama basu yi ba

Juya wa tayi ta shige gida tana sake gwada layin Fauziyyan

Yayinda suna fita Jamal ya cafko Intisar ɗin; ya sauke mata maruka har biyu a saman kuncin ta, domin so yayi yay mata dukan tsiya, but ganin ɗan cikinta yasa ya dakata da hukuncin, ransa a ɓace ya daka mata tsawa yace, "tayi masa shiru."

Da sauri ta kama bakin ta tana hawaye jikinta sai faman rawa yake yi

"Ke wato ba ki da hankali ba ki da tunani ko? Abun da mahaifiyarki take saka ki shi kike yi? To daga yau ga Mijin naki a gaban shi zan faɗa, babu ke babu zancen karatun nan, kar in sake jin kin ƙara tayar mishi da hankali a kan wani karatu, idan kuma ba ki natsu kin zauna a dakin ki ba; ranan da kika shiga hannu na Intisar baza ki ji da dad'i ba, wuce ki shiga Motan nasa." Ya sake daka mata tsawan kamar zai make ta

Da gudu ta wuce cikin Motan ko ɗaukar Jakarta bata yi ba

Sai Shuriem ɗin ne da kansa ya ja Jakar ya saka a Motan; sannan ya yi wa Jamal sallama ya shiga Motan suka wuce

Shima nasa Motan ya shiga ya wuce gida ransa a mugun ɓace, tare da tunanin matakin da zai ɗauka a kan Fauziyya, so take yi ta kashe wa ƴarsa aure sabida ya san cewa duk ita take ɗaura ta a turban banza, to wlh zai ɗauki mummunar mataki a kanta, ya fara gajiya

Shi kansa Shuriem ya san cewa mahaifin Intisar mutumin kirki ne, kawai yana tuna yanda aka yi auren ne da kuma soyayyar da yake yi mata; ba don haka da tuni ya saki Intisar, don yanzu kwata-kwata ya gundura da yarinyar, bata da tarbiyya ko kaɗan, bata iya komin ta ba sai tsiya da fitsara, rashin kunyar ta yayi yawa, shi zai iya cewa ba abun da ya tsinta a auren Intisar sai dana-sani, tunda ta gagara ba shi farin ciki, Allah don yana kai zuciya nesa ne da tuni ya sake ta, ya gaji matuƙa, yana jin yanda take kuka kamar ranta zai fita amma ya ƙi kula ta, a haka suka ƙarisa gidan ta fita a Motan ta shige gida, shi kuma ya wuce kansa tsaye sashin Iyayensa domin ya sanar wa Momy ya ɗauko ta

Inda ita kuma Intisar ta wuce ɗakin ta ta faɗa kan gado sai riskar kuka take yi kamar ranta zai fita, yayinda zuciyarta sai tafarfasa take yi tana ƙara jin haushin Shuriem, tunda gani take yi shi ne duk Ummul aba'isin abun da ya faru, duk a sanadin sa Dadynta yake ɗaga

Please Login or Register in order to submit comment