Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa

Ƙariso wa yayi ya zauna yana cewa, "don Allah Mama kuyi haƙuri da abin da Fauziyya take muku a gidan nan, na san laifi na ne Ni na bata ƙofan da duk take yin abun da ta ga dama, amma insha Allahu yau zan siyo muku kayan abincin ku ku riƙa dafa wa a nan ba sai Hafsah ta je can ba, daga yau baza ta sake zuwa can tayi mata girki ba ku dafa duk me kuke so a nan. Ke kuma kiyi haƙuri ki dena kukan kinji?"

Ajiyan zuciya Mama ta sauke kafin ta buɗi baki tace, "babu komi Jamalu Allah ya shige mana gaba, Allah ya taimake ka ya sake tsare ka".

"Amin Mama na gode da addu'a". Yafaɗa cike da jin daɗi

Hafsah tashi tayi ta shige ɗaki tana ci gaba da matse hawaye

While su kuma hira suka ɗan taɓa kafin Jamal ɗin yayi mata sallama ya fice

Murya Mama ta ɗaga ta kira Hafsan. "Wai har yanzu kukan kike yi ne baza ki haƙura ba?"

Girgiza kanta tayi cike da sanyin muryan ta tace, "a'a na dena".

"To kiyi haƙuri wata rana sai labari, na san Fauziyya ba son zuwan mu take yi ba, zaman mu a gidan nan kwata-kwata ba a son ranta bane shiyasa ga shi nan duk ta koya wa yaran ta tsanar mu, a matsayi na na Kakar su amma basu damu da su zo waje na ba, amma babu komi Allah ya shirye ta ta gane gaskiya".

Gaba ɗaya sai ta ji tausayin Maman a zuciyarta. Shiyasa tace, "Inna don Allah Kar ki saka damuwa a ranki ba na son ganin ki a cikin damuwa".

Murmushi tayi tace, "idan ina dake ai bazan ji damuwa ba, amma idan kika ce za ki koma ƙauye ki bar Ni ai bazan ji daɗin zama Ni kaɗai ba, domin ke nake zaune a nan saboda kiyi karatu, ba Ni da buri sama da hakan Hafsatu na, tunda Umman ki bata yi ba insha Allahu ke za ki yi har sai kin gaji".

Farin ciki ne ya tabaibaye Hafsan ta kwanto kanta a kafaɗan Maman tana cewa, "na gode Innata, shiyasa nake ƙara son ki, Allah ya cika min buri na in Kai ki Makka da Madina Innata".

Dariya suka yi saboda furucin nata. Daga nan kuma sai suka koma hira cike da nishaɗi har sanda aka kira sallah Maman ta tashi don gabatar wa. Ita kuma Hafsah ta wuce Toilet yin alwala.






✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


Tunda ta fito daga gidan nasu idanuwansu suka faɗa cikin na juna. Murmushi yalwace a fuskarta ta ƙarisa wajen sa itama ta samu wuri a saman dakalin da yake zaune ta zauna bayan da tayi masa sallama

Amsa sallaman nata yayi da cewa, "Gimbiyya sai yanzu? Gaskiya kin shanya Ni".

"Kayi haƙuri don Allah idan ranka ya ɓaci".

Sassanyan murmushi ya saki wanda ya san zai ƙara mishi kyau yace, "Afnan kenan! Ba na tunanin a halin yanzu akwai abin da za ki yi min ya ɓata min rai, domin ke kin kasance wata ɓangare na jikina me sanya Ni nishaɗi a cikin zuciyata. Ina fata kina cikin ƙoshin lafiya?"

"Alhamdulillah. Da fatan kaima haka?" Tayi maganar cike da tsantsan farin ciki itama

"Ai idan kina lafiya nima hakan take a wuri na. Sai dai har yanzu ina mamakin wani abu guda."


Sai da ta ɗago ta kalle sa kafin ta tambaye shi da, "me kenan?"


Ɗan jan numfashi yayi kana yace, "ina mamakin yanda kika sace min zuciya ne a ɗan ƙanƙanin lokaci, ina mamakin yanda a yanzu ba na iya samun sukuni da tunanin ki, musamman ma a jiya da na tabbatar da cewa tabbas ke na daban ce. Afnan ban taɓa sanin haka kike da baiwar kyau ba sai a jiya da na ganki cikin kwalliyan da ban taɓa ganin ki da shi ba, gaskiya ke ɗin ta daban ce, idan da ace za ki riƙa kasance wa da kwalliya kamar na jiya za ki saka na zauce ne matuƙa, na gode Allah da hakan ya kasance ba ɗabi'an ki bane yin kwalliya da ban san ya zan yi da raina ba".

Dariya ne ya suɓuce mata, ta saka hannu tana kare bakin ta zuciyarta na ƙara yalwata da farin ciki

Shi kuma sai yayi murmushi da cewa, "na baki dariya ko? Uhmm baza ki gane bane, baza ki gane a halin da kika saka Ni bane a jiya, gaba ɗaya na kasa runtsa wa, a duk sa'adda na rufe idanuwana ke kaɗai nake hango wa Afnan, wlh Allah ya miki baiwar kyau My Afnan domin ban taɓa tunanin haka kike ba, kinga idan har kika kasance kina irin wannan kwalliyan, to, ina da tabbacin zan iya rasa ki, Ni kuma ban shirya rasa ki ba wlh, domin a yanda nake jin ki a zuciyata idan har na rasa ki a wannan gaɓar tabbas zan iya kamuwa da ciwon zuciya".

"Hmm Anwar kenan! Kana tantaman son da nake maka ne har yanzu?"

Girgiza kansa yayi yana faɗin, "No. Amma ina da yaƙinin idan har kika ci gaba da bayyana irin tsantsan kyan da Allah yayi miki ga mutane tabbas zan iya rasa ki, domin Ni ba kowan kowa bane kinga kuwa wani me halin zai iya zuwa ya ɗauke mini ke alhalin Ni Ko kuɗin da zan iya fitowa in nemi auren ki ba na dashi. Afnan maganar gaskiya ke ba kalar ƙananun Maza bane shiyasa tun farkon haɗuwar mu nake yin baya-baya da ke sabida kar wata rana idan na faɗa soyayyarki yazamana ya zamo ajali na, ina da Mata kuma kin san da haka, abun da zai riƙe mu gagaran mu yake yi bare ace na ƙara da ke, wannan shi ne fargaba na". Ya ƙare maganar da kallon cikin idanunta


Hakan yasa ta ɗan sauke kanta ƙasa tana wasa da kwalliyan ƙasan rigan ta, cikin sanyin murya tace, "Ni ina ga kana tantama da son da nake maka ne shiyasa kake faɗar haka, kar ka manta nima ba daga gidan masu kuɗi na fito ba, ta ya ya zan ɗaura wa kai na burin auren me kuɗi? Ina sam. Kai kaɗai nake ƙauna Anwar, wlh ban taɓa son wani namiji a duniya kamar yanda nake matuƙar ƙaunarka ba, a halin yanzu zuciyata tana kwaɗayin ta zama Matar ka, kuma a ko ina ka ajiye Ni wlh zan zauna da kai, kai ne nake so ba wani abu naka ba, Ina son ka da zuciya ɗaya sannan babu wanda zai zo gare Ni naji zan iya rabuwa da kai a kanshi, har abada."

Murmushi yayi yace, "na yarda da ke My Afnan, insha Allahu kuma nayi miki alƙawarin bazan taɓa rabuwa da ke ba, zan yi iya yi na domin mallakar ki a cikin gida na".

Itama murmushin tayi amma bata ce komi ba

"But kin je gidan ƙawar taki ne yau?"

"A'a ban je ba".

"Why?" Ya tambaye ta da mamaki

Tace, "yau na wuni gidan Yayata ce saboda bata da lafiya, ban daɗe da dawowa ba ka kira Ni zaka zo".

"Ok Nima ban je ba wlh, zuwa gobe dai nake saka ran zuwa tunda yanzu yamma tayi. Ina ga kawai ki shirya gobe sai mu je tare ko?"

Gyaɗa masa kai tayi tana kallon sa

Murmushi ya sakar mata da cewa, "kin san zan fi jin daɗi ace ga ki ga Ni a gidan ko don mu ma mu sha soyayyar mu, Amarya da Ango suna nasu mu ma muna namu ko?"

Dariya tayi da ɓoye fuskarta tace, "haka ne."

"Yauwa ko ke fa, Allah ya kaimu goben lafiya".

"Amin ya Allah".

Daga nan hiran kaɗan suka taɓa sannan yace mata, "zai tafi". Suka yi sallama ya wuce.


Machine ya hau daga nan ya ƙarisa da shi anguwan su, yana sauka ana kiran sallan magriba shiyasa ya dakata a masallacin bakin titin yayi sallan kafin ya wuce gida. A lokacin da ya shiga gidan nasu mata ne da yawa ana ta hayaniya; da alamu faɗa ake yi domin mutane har ta katanga suke leƙa wa.




*Whatsapp number only*
07065334256
[08/09, 9:43 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*











*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*PAGE:7*

_____Ba komai ne ya ja taron jama'ar a gidan ba illa faɗan da ake yi da Sauda da wata Mata. Sanadin Sauda tana bin ta Naira ɗari biyu ta je har gida bin bashin ta, ita kuma Matar tace mata, "bata da shi yanzu". Shi ne ita kuma ta ɗauko mata ƙaton gas-kuka ta nufo da shi gida, Matar ta biyo ta har gida tace, "baza ta yarda ba sai ta bata". Shi ne faɗa ya kaure a tsakanin su, duk yanda aka so a raba su an kasa sai cacan baki suke yi suna dambe. Sauda ta shigar da gas-kukan cikin ɗaki ta hana matar shiga sai kokawa suke yi, hakan yasa mutane suka cika gidan ana ta son raba su amma an kasa

Hauwa dake cikin taron jama'ar har da ita ake rabon faɗan, tana hango Anwar ya shigo gidan ta lallaɓa ta wuce ɗaki, sallama tayi ta shiga

Anwar da har ya samu wuri ya zauna a gefen gadon su ya amsa mata yana cewa, "wai me ake yi a gidan nan ne aka tara mana mutane?"

Murmushi tayi tana taho wa ta zauna a gefen sa da cewa, "kai ma ka san bazai wuce fitinan da Sauda ta saba tara mana mutane ba, faɗa suke yi da wata Mata ta ɗauko mata Gas-kuka a kan Naira ɗari biyu, Bilal ma yayi rabon ya kasa ya ficewar sa tunda ba ta jin rarrashi, wlh ta hana Gas-kukan nan sai an bata kuɗin ta".

Ajiyan zuciya ya sauke yace, "to Allah ya kyauta, Ni fa gaskiya lamarin gidan nan sai a hankali, ni da zan samu wani gidan me sauƙin kuɗi tashi zamu yi a nan tunda ban ga amfanin zaman mu ba, kullum gida ana tara mana jama'a ana fitina har kaina ya soma ciwo wlh." Sai ya ja tsaki yana cewa, "kin ga kawo min ruwa da abinci na in ci kafin a Kira Sallah".

Tashi tayi ta fita, bata jima ba ta dawo da kwano me murfi a hannun ta ta ajiye masa, sannan ta ɗibo masa ruwan daga cikin randan ta dake bayan ƙofar ɗakin. Ta ajiye masa tana zama a inda ta tashi

Kallon ta yayi yace, "baza ki koma rabon faɗan bane?"

Dariya tayi tace, "a'a kai ma ka san bazan koma ba tunda kana gida ka dawo. Ni akwai maganar ma da nake so mu yi da kai idan ka gama."

"Ok kiyi magana ai ina jin ki". Yafaɗa yana saka tuwon a bikin sa

Ita kuma gyara zaman ta tayi ta soma magana da faɗin, "dama gobe nake son in leƙa gidan mu; daga nan sai in wuce gidan Muhseen mu gaisa da Amarya".

Kallon ta yayi yace, "a'a ki bari zuwa jibi ki je hakan zai fi, zuwa lokacin na san na samu kuɗin da zan ba ki ko tsaraba ne ki yiwa su Hajiya. Ɗazu yaro ya kawo miki kayan miya ko?"

"Eh ya kawo min"

"To na san zai ishe mu kwana biyu idan kika yi, goben idan na samu kuɗin da nake jira sai in siyo mana shinkafa, idan kuma ban samu ba sai jibin kamar yanda muka yi da wanda zai bani kudin shikenan."

"To Allah ya kaimu. ɗazu Jalila ta shigo gidan nan muke magana a kan neman aiki da na sanya ta ta samo min, shi ne nace idan ka dawo sai in sanar maka na san hakan zai taimaka mana sosai".

Tsayar da cin tuwon yayi yana ɗago wa ya kalle ta, "ban fahimta ba kamar ya neman aiki?"

"Dama nace mata ta nemo min aikatau a gidajen masa kuɗi sai in riƙa zuwa ina yi muna samun abinda zamu ci, tunda ka ga abubuwa suna gagaran mu yanzu".

"Ya isa Hauwa'u, kina nufin in bar ki zuwa wani gida aikatau? To Ni bazan iya ba, ki dena ma zancen nan kina jina?" Zata yi magana ya dakatar da ita yana tashi tsaye ya fice

Ita kuma shiru tayi ta kasa motsa wa a wurin illa tunani da ta afka, duk da har yanzu hayaniya ake yi a gidan amma be sa ta fita ba har sanda ya sake dawowa. Lokacin an yi sallan isha'i shiyasa ta tashi ta gabatar tunda tana da alwala, ta ɗauko tuwon ta ta tasa a gaba tana ci

Shi kuma yana zaune a kan gado yana ta latse-latsen waya. Can ya ɗago ya kalle ta ganin kamar hankalin ta ba a jikin ta yake ba sai ya kirayi sunan ta

Hakan yasa ta ɗago ta kalle sa tana amsa wa

"Ki dena saka damuwa a ran ki ba na so, idan ma za ki yi wannan aikin ne don taimako na Ni ba na so don bazan bar ki kiyi wani aikatau ba, Ni da ke ne kaɗai bamu da wasu ƴaƴa da suka yi mana nauyi, don haka a haka zamu lallaɓa rayuwar mu har sanda zan samu aikin yi komi ya wuce tunda na san ba komai zai dauwama ba, Allah ma ba ya haɗa wa bawan sa zafi biyu shiyasa har yanzu be bamu haihuwa ba saboda bamu da halin riƙe su, kiyi haƙuri ki zauna a haka wata rana sai labari, amma batun aiki ba na tunanin zan amince, insha Allahu idan an bani kuɗi na zan ba ki wani abun a ciki ki ci gaba da sana'ar taki".

"To". Tace da shi tana ci gaba da cin tuwon ta. Ba su sake magana ba har sanda ta gama ta mayar da kwanon kichen ta dawo

Yace da ita, "ki zuba min ruwa in ɗan watsa".

Amsa mishi tayi tana fita ta zuba mishi ruwan a bucket. Bayan ya je yayi itama tayi nata sannan ta rufe musu ƙofan.




Washe gari wajen ƙarfe Goma da rabi Hauwa na zaune a bakin ƙofan ta, a lokacin ta gama wanke-wanken ta tayi shara ta zauna suna ɗan hira da Sauda da ke wanke kayan fitsarin Haidar

Yaro ya shigo da baƙin leda a hannun sa yace, "wai an ce in ba wa Hauwa inji Anwar."

Hauwa tace, "kawo min gani nan". Amsa tayi tayi masa godiya tana leƙa cikin ledan. Shinkafa ne ƴar tsinta tiya ɗaya a ciki

Sauda da ke ta leƙe tun daga inda take tace, "wai daga fitan shi ne har ya yo miki aike?"

"Eh dama ya ce kuɗin kawai zai amsa ya siyo".

"Lallai.. ai Ni wlh ina rasa wane irin Miji ne da Ni wlh, ko koyi da naki be yi kullum shi a babu yake kamar a kanshi fatara ta ƙare, yanzu Ni da inga ƙafafun shi sai yamma ya zo min yana maganar be samu ba, Ni kuma wlh na gaji yanzu gaba ɗaya idan har be kawo ba bazan sake dafa wa da shi ba daga Ni sai yara na Al'ƙur'an".

Hauwa kallon ta tayi tace, "ki gode wa Allah Sauda, Bilal yana iya ƙoƙarin sa wajen nemo wa, ku ke nan da kuke da yara ma ina ga mu da babu, wlh duk neman Anwar Bilal ya fi shi ƙoƙari, ke dai ba kya ganin hakan ne saboda kina raina ƙoƙarin sa, ban taɓa ganin kun kwana biyu baku ci abinci a gidan nan ba, ko bashi ne yana zuwa yana ci amma ba kya ganin ƙoƙarin sa, ki dai riƙa haƙuri don Allah".

Taɓe baki Sauda tayi tana tashi da zanin da ta ɗauraye ta shanya shi a jikin igiyar shanya, sai da ta dawo wajen ruwan wankin ta ɗauka zata zubar kafin ta ce, "wai Ni kam yaushe ne za ki je gidan Amarya ne?"

"Yau na so zuwa amma Anwar ya ce sai gobe zan je".

"To nima zan bi ki muje tare wlh, don nima ina son koma wa inga Amarya ko don mu ƙulla zumunci, ai yanzu mun zama ɗaya tunda Abokin Mazajen mu ne".

Murmushi Hauwa tayi tace, "haka ne. Amma fa zan biya ta gidan mu."

"Ai babu damuwa sai mu je." Cewar Saudan

Hauwa tashi tayi ta ɗauko faranti a ɗakin ta ta soma zuba shinkafan a ciki, dayake ƴar tsinta ce shiyasa take son ta rage

Bayan Sauda ta gama shanyan ɗaki ta wuce ta ɗauko mayafi tana faɗin, "Ni bari in je gidan Hansa'u ta bani kuɗi na, tunda jiya na haƙura na bar mata Gas ɗin yanzu zan je in amso kuɗi na wlh, idan kuma bata samu ba yau zata ga ruwan bala'i na rantse da Allah, duk uban da zai bani haƙuri bazan taɓa haƙura ba. Ga ɗaki na nan na bar miki idan su Sulaiman sun dawo makaranta ban shigo ba ki ce musu ɗumamen tuwon su na nan a kichen su ɗauka."

Girgiza kanta Hauwan tayi cike da takaici tace, "wai kina nufin ba yanzu za ki je ki dawo ba? Yanzu nan da gidan Hansa'un ne har sai kin je kin zauna?".

"Ba fa can kaɗai zan je ba; zan wuce gidan Jummai zamu yi maganar kayan t.v na da nace zan sayar mata".

"To Allah ya kiyaye." Abin da Hauwan tace kenan ta ci gaba da tsince shinkafan ta.




Fitan ta babu daɗe wa Anwar ya shigo gidan

Amsa sallaman sa Hauwa tayi tana mishi sannu da zuwa bayan ta tashi ta amsa ledan hannun sa

Ya amsa ta yana cewa, "ashe yaron ya kawo miki?".

"Eh ya kawo min be daɗe ba ai".

"To Ni dama sanja kaya nazo yi zan fita anguwa, sa min ruwa a buta in ɗauraye jiki na".

"To". Ta amsa mishi tana nufan ɗaki ta ɗauko butan. Ta zuba masa ruwan a ciki

Shi kuma ya ɗauka ya zagaya bayi. Bayan ya fito ya ɗauraye jikin sa ya wuce ɗaki, be fi mintuna sha biyar da shigan sa ba ya fito sanye da farar shadda wanda suka ɗinka shi da Muhseen a bikin sa. Kasancewar kayan sabo ne sai ƙyalli take yi, bare yana da hasken skin shiyasa tayi masa mugun kyau tamkar dai wani Ango sai tashin ƙamshi yake yi, ga shi ya buga uban hula a karkace wanda ta dace da aikin kayan, sai cover shoes da ya saka fari ƙal

Sakin baki Hauwa tayi saboda kyan da yayi mata, dayake bata ga kwalliyan sa da kayan ba tunda a can wajen Muhseen ya shirya suka je ɗaurin aure, zuwa yamma kuma ya cire ya saka wani jan yadi shiyasa bata ganshi da su ba. Sosai yayi mata kyau tamkar ranan auren su haka take ganin sa. Yanda ta faɗa tunani sai da ya saka hannu ya shafa mata fuska kafin ta dawo hayyacin sa. Ta kalle sa da murmushi ta kasa cewa komi

Shima murmushin yayi yace, "nayi miki kyau ne?"

Gyaɗa masa kai tayi kana tace, "sosai da sosai, tamkar ranan auren mu".

Dariya yayi yace, "ko Hauwa'u na? Anya ranan auren mu ban fi haka kyau ba? Ni ina ji a jiki na na fi haka kyau saboda ranan na daban ne kasancewar ta babban rana wacce na fi kowa sa'ar samun Mata me tsananin ƙaunata da tarairaya ta".

Dariya itama tayi jin furucin sa tace, "haka ne. Sai nake jin tamkar ka zauna nayi ta kallon ka saboda shauƙi da tsananin begen ka".

"Oh kar ki damu Mata ta insha Allah zan dawo a kan lokaci saboda ke, ba don ina da inda zan je me muhimmanci ba babu abun da zai hana Ni zama a gida ko don mu tuna baya". Sai ya saka hannu ya shafa fuskarta yana me riƙe mata hannaye, ido cikin ido yake kallon ta da murmushi a fuskarsa yace, "gaba ɗaya yau babu abinda nake tuna wa sai sanda na mallake ki a matsayin Matata, sanya fararen kayan nan ya tuna min da abubuwa da dama masu muhimmanci a rayuwar mu. Uhmm ina jin farin ciki matuƙa."

Murmushi tayi har jerin fararen haƙoran ta da suka kasance da hushirya a tsakiya suka bayyana, tace, "nima haka farin ciki na ya zarce naka Mijina, domin ganin ka a haka ya tuna min rayuwar mu ta baya. Allah ya kiyaye hanya Mijina, Allah ya tsare ka ya dawo min da kai lafiya. Allah ya tsole idon maƙiya da mahassada a kan ka". Sai ta duƙar da kanta saboda jin hawaye sun cika mata idanu

Hannun sa ya mayar ya kamo mata fuskarta yana ɗago wa suka haɗa ido

Hawayen ciki suka zubo hakan yasa ta sakar masa murmushi

Share mata hawayen yayi yace, "mene ne kuma na kuka? Me ya faru?"

"Babu komi Mijina. Kawai ina jin tsananin kishin ka ne a zuciya, haka kawai yau nake ji tamkar kar ka fita wata Mace ta gane min kai, amma kuma babu yadda zan yi".

Shiru yayi yana kallon ta

Hakan yasa tace, "kar lokaci ya ƙure maka ka tafi. Allah ya tsare".

"Amin". Yace da ita cike da sanyin murya yana mata murmushi. Sannan ya fice yana ɗaga mata hannu

Ita kuma zama tayi ta ci gaba da tsintan ta sai dai kuma duk ranta babu daɗi, haka kawai take jin zuciyarta na nauyi, shiyasa daga baya ta koma addu'a a zuciyarta jin Abubuwa da dama suna bijiro mata a rai wadda suke son hana ta walwalan ta. Da haka har ta samu sukuni ta ci gaba da aikin ta.







✳️✳️✳️✳️


Anwar na fita daga gidan machine ya tare ya wuce gidan Muhseen, a waje ya tsaya kasancewar sun yi waya da Afnan itama tana kan hanya

Keke napep ta hayo ya kawo ta har bakin Gate ɗin gidan

Yana ganin ta cikin napep ɗin ya nufi wajen yana mata murmushi, yace, "barka da zuwa Gimbiyyata."

Murmushi tayi masa tana shirin miƙa wa me napep ɗin kuɗin sa ta amsa mishi

Hakan yasa yace, "a'a bar kuɗin ki Ni zan biya." Ya zaro kuɗin sa a cikin aljihu ya miƙa masa kana ya kalle ta yace, "mu je ranki ya daɗe!"

Tare suka jera har zuwa cikin gidan suna taɓa hira cike da farin ciki da walwala irin ta masoya.
[11/09, 9:54 pm] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*










*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*PAGE:8*

_____Already dama su Muhseen sun san da zuwan su, shiyasa Munira tayi musu girki me rai

Please Login or Register in order to submit comment