Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan ƙiman? Abun na damun ta matuƙa, a ce duk Jikokin ta babu mai ganin ta da gashi, kullum ƙyamatar ta suke yi. Shiru tayi kawai lokacin da ta koma daki ta zauna, sai ta yi tagumi tana faman tunani, a ganin ta ya zama dole ta nema wa Jamal wata Matar koda a ƙauyen su ne, tunda bazai yiwu a ce tana zaune da ɗanta bata da shaƙuwa da ƴaƴan sa ba, idan Fauziyya ta hana ƴaƴan ta su so ta, sai ta bar mata su ta ƙarata da su, tunda akwai wasu ƴaƴan ba ita kaɗai ta haifa ba, zata ji dad'i kuma zata yi farin ciki in Jamal ya ƙara aure ta samu wasu Jikokin, zama bai kama ta ba, dole zata je ƙauye don ta gama yanke hukunci.
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼










            *PAGE:18*

_____Kamar yanda Mama ta ƙudura a ranta zata je Ƙauye, bata canza ra'ayin ta ba, Jamal na shigowa ta sanar mishi, "zuwa jibi zata wuce ƙauye, don haka ga Hafsatu nan zata zauna a wurin su har sanda zata dawo, ƙila zata yi sati guda kafin ta dawo."

Sai yace, "Mama wani abun ya faru ne a can?"

"A'a Jamalu, akwai abun da zai kai Ni can ɗin ne, kuma na gaggawa ne, don haka ka kula da Hafsatu don Allah, ka saka ido sosai a kanta tunda ka san yanda take zama a gidan."

Ɗan jan numfashi yayi da faɗin, "insha Allahu Mama, zan kula da ita, sai kin dawo, ina ita Hafsan?"

"Tana ɗaki tana kuka tunda na faɗa mata tafiyan nawa, cewa tayi sai ta bi Ni."

Murmushi yayi da faɗin, "ban da abun Hafsah, tana makaranta taya zata bi ki? Shagwaɓa ne kawai yayi mata yawa."

Dariya Mama tayi tace, "to in ban shagwaɓata ba wa nake dashi da zan shagwaɓa? Ita kenan min fa. Ita kadai nake kallo naji daɗi a yanzu, Yaranka duk sun guje Ni ba sa kallona a matsayin Kakar su, to ya zan yi?"

Yadda tayi maganar ne, yasa Jamal ya sukunyar da kansa yana jin babu daɗi a ransa

Sai tayi murmushi tace, "ka tashi ka je ka ga dare yayi, mu ma zamu kwanta ne."

"To Mama, zuwa gobe sai in saka driver ya yo miki tsaraban da za ki kai musu, insha Allahu da safe in na shigo sai mu lissafa abubuwan da za a siya."

"To shikenan, Allah ya yi albarka, Ubangiji ya ƙara rufa asiri."

"Amin Mama, Nagode." Ya furta cikin jin daɗi yana miƙe wa, tare da sake mata sai da safe ya fita

Itama sai ta tashi ta rufe musu ƙofan, tana shiga uwar ɗaka tare da kiran Hafsah

Hafsah wacce ta zauna a gefen gado riƙe da littafi, tana karatun tana matse hawaye

Sai Mama tace mata, "har yanzu kukan kike ko karatun?"

"Dukka nake yi, Ni Inna gaskiya kar ki tafi ki bar Ni a hannun wannan Matar, Ni wlh sai na bi ki."

"Wai abu ba ya wuce wa ne a wurin ki Hafsatu? Taya ya za ki bi Ni bayan kina makaranta? Kuma ina ce jarabawa kuke yi bare a ce zan tafi da ke?"

Tura baki tayi tana ƙara matso hawayen idanun nata, har da su shashsheƙa

Sai Mama ta zauna a gefen ta tace, "ki yi haƙuri mana Hafsi na, yau da gobe duk ɗaya ne a wurin Allah, yanzu sai ki ga na je na dawo kamar ban je ba, maganar kuma Fauziyya da Yaranta ai nayi ma Jamalu magana bazai bari komai ya faru da ke ba, kuma ke da na sanki da haƙuri, ki ci gaba da hakurin komai mai wuce wa ne, wuya fa ba ta kisa bare a ce zasu kashe ki, ki ci gaba da haƙuri kinji ko?"

Kanta ta gyaɗa tana sharce hawayen fuskarta, sai kuma ta janye littafin a gabanta tana kwantar da kanta a saman cinyan Mama, ta ci gaba da tsiyayar da hawayenta

Mama na ci gaba da rarrashinta tana faɗa mata, "komai muƙaddari ne, basu isa su ga bayan ta ba sai Allah ya yi, ta ci gaba da haƙuri wata rana sai labari, zata zama abar kwatance wata rana insha Allahu."

Sai da ta gama tausan ta sannan suka kwanta barci.
****


         Shi kuma Jamal bai sanar da Fauziyya, Mama zata yi tafiya ba, sai a washe gari ya faɗa mata tare da ce mata, "Hafsah zata dawo ɗakin Sumayya su rika kwana kafin Mama ta dawo."

Wani kallon rainin wayon tayi masa, har zata buɗe baki tayi magana sai kuma ta fasa, tana jan ƙwafa ta fice a ɗakin fuuu

Har takai bakin kofa ya kira ta. Dole ta dawo ta tsaya tana faman kallonsa fuska a ɗaure

"Fauziyya ban san meyasa har yanzu kika kasa gane Mama da Hafsah su ɗin dole na bane, meyasa kika kasa haƙura ki zauna da su da zuciya ɗaya a gidan nan? Har yanzu kin kasa sakin jiki da su bare ki bar ƴaƴanki su yi mu'amala da su, why Fauziyya? Me mahaifiyata ta tare miki?"

"Dole ka furta haka mana tunda neman fitina kake ji, ko ta sanar maka da wani abun ake mata da ka zo ka titsiye Ni a nan kana tuhuma na?"

"Ba titsiye ki nayi ba Fauziyya, abun da na sani shine nake tambayar ki, ko Ni makaho ne ai dole zan fahimci yanda kike zaune da su, bare ƙuraratan kike nuna musu tsangwama, sabida ba kya son su, sannan kin hana ƴaƴana su yi mu'amala da mahaifiyata, wai kam Fauziyya kin san ma'anar Uwa da kike wulaƙanta min tawa Uwar?"

A fusace tace, "wato cin mutunci da wulaƙanci yasa ka tsayar da Ni a nan kayi min? Dama ba tun yau ba already na kula da hakan ka sauya Jamal, ka dena kallona da mutunci sabida su, idan sun faɗa maka ƙarya da gaskiya a kaina sai ka zauna a kai..."

"Ki min shiru nace, ba na son jin zancen banzan nan naki, Mamana ne zata yi miki ƙarya a kan abubuwan da kike yi? Tunda nake bata taɓa tara na da zancen ki ba, me ya kawo hakan ba so ba? Wlh ki kula ranan da kika kai Ni bango Fauziyya zan mummunar saɓa miki, yanda kike son taki mahaifiyar haka nima nake son tawa, dangi na sun fi min komai a yanzu, darajar ita wacce kika raina kike zaune har yanzu a gidan nan, ba don haka ba da na nuna miki ainihin wane ne ni, har yanzu kallona kike yi a bai-bai, kuma wlh muddin kika ce za ki muzguna wa Hafsah a gidan nan, zamu game ne." Ya kaɗa mata hannu a kan fuskarta yana wuce wa cikin huci da ɓacin ran da ya taso masa

Ita kuma sai ta juya ta fice batare da ta furta komai ba sabida tsaban haushi da takaicin sa, lallai ta soma gajiya da wannan halin da Jamal yake nuna mata, yanzu gaba ɗaya ya sauya a kan waɗannan banzayen, karkaɗa ƙafa kawai take yi da ta koma Falo ta zauna, tana faman tunanin matakin da zata dauka

Sai ga shi ya fito daga dakin nasa, har ya saka kaya yana faman gyara hulan kansa, ko kallonta bai yi ba ya fice abun sa

Ta bi sa da ido ranta a mugun ɓace, ƙwafa tayi a fili ta furta, "wlh baka isa ka wulaƙanta Ni a kan wannan Matar ba Jamal, baka isa ba, na fi ƙarfin wulaƙanci, ko mene ne zan iya yi don ganin ta bar mana gida, bata isa ta zo ta ɓata min zamantakewar aure na ba wlh." Sai ta tashi fuuu ta koma ɗaki, gyalenta ta ɗauka da Jakarta ta fito, saboda dama wurin aiki zata je already ta gama shirin ta

Su kuma su Sumayya tuni sun wuce school

Motanta ta hau ta bar gidan a sukwane ranta a ɓace, maimakon ta tafi makarantar kamar yanda tayi ninya, but ɓacin ran da ke nuƙurƙusan ta bai bari ba, sai ta wuce kanta tsaye gidan Yayarta Aunty Salaha, wacce suke kiranta da Ummu Muhseen.
***

            Shima Jamal sashin Mama ya wuce, lissafin kayan da za a siyo suka yi da ita, ya kira driver ya sanar masa abubuwan gaba ɗaya, yace, "ya je ya siyo yanzu."

Bayan ya tafi, shi kuma ya zauna suka ci gaba da taɓa hira a tsakanin su, tunda dama bai da aiki, sai gobe yake saka ran zai yi tafiya na kwana uku before ya dawo.


               Ya so ya kai Mama har ƙauyen, amma bai da time ɗin da zai je ya dawo a lokacin, shiyasa ya saka driver ya kaita, shi kuma ya wuce Kano a ranan

Yayinda Hafsah kuma ta koma sashin Fauziyya da zama. Tun a ranan ma ta soma fuskantar wulaƙanci da tozarci, domin har duka sai da Fauziyya ta naɗa mata, duk ta huce takaici da ɓacin ranta a kanta, kuma tace, "komai ita zata yi musu har wanki da guga."

Ƙarshe a bakin ƙofan kitchen suka watsa mata kayan ta a nan zata riƙa kwana

Ta sha kuka Hafsah sosai, bata taɓa dana-sanin kasancewar ta a gidan nan ba irin na wannan lokacin, zaluncin da suka nuna mata gaba ɗaya ta ji ta tsani karatun ma, gwara ta koma ƙauyen su tayi rayuwarta a can cikin ƴanci, da dai ace ta zauna a nan; wajen waɗanda basu san darajan ɗan Adam ba.
*** *** *** ***



               Tun a ranan da Mama ta sauka a ƙauyen nasu, ta tara Umma Salamatu Mahaifiyar Hafsah, da Mahaifinta ta faɗa musu abin da ke tafe da ita, na son haɗa auren Jamal da Hafsah tunda abun da ya kawo ta kenan, idan sun amince nan da sati ɗaya za a ɗaura auren nasu

Su kansu sun ji maganar ne a bazata duk da ba ƙaramin farin ciki ya bayyana a kan fuskokin su ba

Baban Hafsah yace, "a yi haka Inna? Na ga wannan yarinyar kamar ƴa take a wurin Jamalu. To taya ya zai aure ta?"

"To koda ƴa take a wurin sa addini ya haramta ne? In ce dai ba Ni na haifi Salamatun ba ga ta nan, ƴar uwata ta haife ta, ai ba a ce babu halarcin auren ba duk da Ni na raine ta ban shayar da ita ba, Ni na ga ya dace a haɗa su aure; tunda da ace na nema wata can bare, ga ƴar gida gwara ya aure ta."

"Haka ne Inna, to, mu ai baza mu ce komai ba wlh, duk abun da kika ce shine namu, Hafsah ai taki ce tunda ke kika raine ta, duk hukuncin da kika yanke shi zamu bi wlh.". Cewar Baba yana murmusawa

Mama ta kalli Umma Salame tace, "to ke ba ki ce komai ba?"

Washe baki tayi tace, "Inna Ni farin cikin nawa ne yayi yawa, wlh ba ki ga yanda haɗin nan ya saka Ni farin ciki ba, Allah yasa a ƙulla alkhairi kawai don Ni na amince ma tuni."

"Masha Allah Alhamdulillah, dama yardan ku nake nema, tunda kun amince nan da sati ɗaya sai a ɗaura auren, tunda ina nan har sati, shima Jamalun ban faɗa masa ba, amma zuwa lokacin zan kira sa sai ya zo daga nan in an ɗaura auren mu wuce".








🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


           Abinci suke ci, but hankalin Zeena ba ya jikinta sosai, abun da Aliyu ya fahimta kenan, ya sanya ƙafa ta ƙasan table ɗin ya taɓo ta, hakan yasa ta ɗago kyawawan idanunta masu zubin ƙwai ta zuba mishi

Sai ya ɗage mata gira tare da cewa, "lafiya Honey? Tunanin me kike yi haka?"

Ɗan tsira masa ido tayi, sai kuma ta saki murmushin yaƙe tana girgiza kanta da cewan, "ba komai dear, me ka gani?"


"Haba? Ya za ki ce min ba komai? After all tunani kike yi ga shi nan zahiri?"

Sai ta shagwaɓe fuska cikin kissa irin nata tana narke masa waɗannan idanun nata cikin nasa, tace, "to ba kai ne ba, Ni wlh na gaji da wannan tafiye-tafiyen da kake yi, kuma ka ƙi ka je dani kullum sai dai ka tafi ka bar Ni."

Kujeran sa ya dawo da ita kusa da nata, sai ya kamo hannayen ta yana matso da fuskarsa sosai kusa da nata, cike da ƙaunarta a rai yace, "Oh! Sorry mana Honey, ba na son kina wannan damuwar, wai dama duk don haka ne kike haɗe kyakkyawar fuskarki? Kin san fa sabida makarantar Yara ne ba na son tafiya da ke, amma da zaran sun samu hutu zamu riƙa zuwa tare, Please mana Honey ki dena damuwa, kinga duk abin da kike so ina miki sabida farin cikin ki, just two days zan yi in dawo bazan jima ba."


Ɓata fuska tayi tana cewa, "hakan ne baza ka daɗe ba? Kai kullum haka kake fada bayan ka san yanda nake ji a wannan lokacin da bama tare, tamkar shekara biyu ne ba kwana biyu ba. Na saba da kai dear ina matuƙar shan wahala in baka kusa da Ni, already ka saba min da jin daɗi, Allah ina cutuwa da wannan tafiyar taka, baka ga ƴan uwana ba kullum dariya suke min suna ce min gwauruwa, wai ina da aure amma babu Miji."


Dariya maganar nata ta ba shi, sai ya dara yana kallonta

Ita kuma ta sake kwaɓe fuskar nan nata da yake ganin ya fi mishi kowacce fuska kyawu a duniya, domin har ga Allah komai nata mai kyau ne, kyawun ta yana matuƙar fizgar sa har ya manta wane ne shi. Yanzu ma kamar zata yi kuka take furta, "wai dariya kake min ko? Na zama mahaukaciya?"


"No Honey, I'm sorry bari in wanke laifi na." Sai ya ɗaga ta ya dawo da ita jikinsa yana matse ta sosai tare da raɗa mata magana cikin kunne, "ke ɗin ce jarabar ki tayi yawa, sai ki ce min ga abun da kike ma fushi ba wai ki ce ba kya son tafiyana ba, haba Honey, ɗan kwana biyun kawai baza ki iya jure wa ba?"

Dariya tayi itama tana hararansa, sai kuma ta ƙara turɓune fuska tace, "kana nufin Ni na fi ka Jaraba kenan? Shikenan ka tafi bazan ƙara damuwa da kai ba ma, zaka san Ni Jaruma ce."


"Haba dai? Baza a yi haka ba, mu je na rage miki ƙaiƙayin da kike fama da shi before na tafi, i know yanda zan miki zai ishe ki har in dawo." Yayi maganar yana dariya tare da ɗaga ta ya ɗauke ta

"No ka bar Ni kawai, ba na so fa, please sauke Ni."


"A'a.. a'a. Bazan sauke ki ba." Yayi maganar yana kai mata kissing tako'ina a jikinta. Kai tsaye ɗakin barcin sa ya wuce da ita suka faɗa kan gado

Dama abun da take so kenan Zeena, don ba ta gundura a wannan harkan, shiyasa har yanzu ta kasa dena bin Maza, duk da Aliyu yana iya bakin ƙoƙarin sa wajen biya mata buƙatun ta, but ita bata gani tunda abun ya bi jikinta, in bata bi wasu Mazan ba bata jin daɗi, kamar karya haka ta koma da auren ta

Shi yasa da suka gama suka sake wanka. Shima ya shirya ya gama tsab tunda tafiya zai yi a yau, har bakin kofa ta rako shi tana faman mishi shagwaɓa, ta kasa barin sa ma ya tafi sabida yanda duk ya susuce yana biye mata. Sai da ya biye mata suka sha soyayyar su before ya fice

Murmushi tayi ta koma ciki ta ɗauko wayanta, sai ta soma kiran layin Sadis, har ya ɗauka sai ga Aliyu ya sake dawowa. Da sauri ta kashe wayan duk ta gama daburce wa

Murmushi yayi mata yace, "ah ah... Ke da wa haka kika firgice kuma?"

Cike da yanayin tsorata tana ajiye numfashi tace, "kai ne ka tsorata Ni wlh."

"To sorry my Honey, but ki tashi ki rufe ƙofan mana tunda ba yanzu Yaran nan zasu dawo ba, Please in an tashe su ki je ki ɗauke su cuz ban biya mai keke napep ɗin su ba, dama abun da zan faɗa miki kenan, in na dawo zan biya shi sai ya ci gaba da ɗauko su."


"Ok dear, bari mu je in kulle ƙofan don hankali na zai fi kwanciya."

"Sai ka ce ba ki da gaskiya?" Yayi maganar yana tsira mata ido

Sai ta matse tana yatsina fuska da cewa, "to ba ga shi yanzu ka tsorata Ni ba, Allah nayi tunanin wani ne ma."

Kamo ta yayi ya haɗa bakin su wuri ɗaya, sai da yayi mata hot kissing before ya sake ta yana sake mata sallama, suka narke wa juna kamar baza su rabu ba. Har bakin ƙofan waje ta raka sa tana faman goga masa jikinta

Aliyu ya san ba ƙaramin important abu yake da shi ba, ba don haka ba bazai iya tafiya ba a yanda yake jin tsananin sha'awar Matarsa ta ƙara taso mishi, dole ba don ya so ba yayi mata sallama ya wuce

Ita kuma ta koma ciki tana gode wa Allah gwara da basu fara waya ya shigo ya ji ba. Kiran Sadis ɗin ta soma yi

Yana ɗaga wa yace, "Babbar Mace lafiya dai ko?"

"Uhm ina fa lafiya? Aliyu ne ya sake dawowa shine na kashe wayan."

"Shiyasa kamar na sani na ƙi kiran wayan, gaskiya Zeena kina ganganci fa, kar ki sa wata rana a kama mu, Ni na soma tsorata Allah bazan sake zuwa gidan nan ba."


"Haba kai kuwa, yau muka fara wannan abun ne wai? Please ka cire tsoro ka zo yau tunda kwana biyu zai yi, ka ga muna tare har sai mun gaji da juna." Ta ƙare maganar tana narke masa murya

"Um um fa, gaskiya ina jin tsoro, bazan sake zuwa gidan ki ba in ba kin tabbatar tafiya mai nisa zai yi ba, kawai ki sama mana wurin da zamu haɗu amma ba gidan ki ba."


Zeena tace, "shikenan, bari in shirya sai mu haɗu a nan bakin hanya, mu sama Hotel din da zamu je ko?"

"Yauwa, yanzu na ji batu Babbar Mace, farar Mace alkyabbar Mata, ranki ya daɗe!" Ya ƙare maganar yana dariya. Sai kuma ya rage ganin Ruƙayya ta shigo ɗakin. Ɗauke kansa yayi ya ci gaba da sauraron Zeena, sai kuma can yace, "ok Sai mun haɗu ɗin." Ya katse wayan

Ruƙayya da sauri ta duƙa tana cewa, "dama zan sake tuna maka maganar zuwa gidan Aunty Hauwa ne."

"Yaushe ne tafiyar?"

"Yanzu zamu shirya mu tafi."

Tsaki ya ja yace, "gaskiya babu inda za ki je yanzu, sai dai ki bari sai gobe, sai mu je in kai ki zuwa goben."

Ruƙayya tace, "dama tare da Aunty Sauda zamu tafi ai."

"Ok kin fi so ki je da wata a kan Mijinki?"

Girgiza kanta tayi tana kallonsa


"To ki bari gobe mu je tare tunda nima ina son in je in ƙara ganin gida, tare zamu tafi." Yayi maganar yana mike wa, sai kuma yace, "ki zuba min ruwa ki kai min bayi."


Ganin ya soma cire kayansa shiyasa Ruƙayya ta fita don yin abun da yace mata

Shi kuma yana murmusawa a ransa yana tunanin gobe zai ga Hauwa, don haka bazai bari wannan damar nasa ta kufce ba gwara su tafi tare da Matarsa a zuwan sun zo gaishe su ne, yayi kewarta a kwanakin nan, zai so ya sake ƙara ganin Matar nan saboda ta shiga ransa, matsananciyar sha'awar ta yake fama da ita, but ta ƙi ba shi dama.
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼










            *PAGE:19*

_____Bayan fitan Sadis ne, sai Ruƙayya ta nufi ɗakin Sauda ta sanar mata yanda suka yi dashi, cike da sanyin jiki da tunanin yanda Saudan zata ɗauki abun. amma sai ta ji tace mata

"Au hutaroro waken gizo ya ƙi ƴaƴa, to ai Ni gaba ta kaini na samu sauƙin kuɗin mota, sai mu tafi goben tunda ko banza shi zai biya kuɗin keke napep ɗin, amma bazan je yau ba nima tunda babu amfanin zuwan, abun da zamu je mu yi hira a taru gaba ɗaya; ai sai hiran ya rage armashi, amma ga ki, ga Ni, abun zai fi armashi, ko ba haka ba?"

Ruƙayya tayi murmushin yaƙe tace, "eh haka ne."

"To kin gani, ai ya fi, Allah ya kaimu goben, da yau da gobe duk sammakai, dama ban faɗa ma Baban Haidar ba, don haka goben sai mu je, bari ma ki ga in kira Hauwan kar ta ji mu shiru, a ce kuma zata yi mana girki ta ji bamu zo ba baza ta ji dad'i ba, gwara mu sanar mata." Ta miƙe ta je ta dauko wayanta ta kira Hauwa. Bayan sun gaisa ne take faɗa mata, "to sai gobe zasu taho kar tayi musu komai ma, sun hutashshe ta gobe sai ta shirya musu duk abun da tayi ninya."

Hauwa na dariyan Sauda ɗin, tace, "to shikenan, sai kun zo, Allah ya kawo ku lafiya."

"Amin ya Allah."
Daga nan dai suka yi sallama ta kashe wayan, ta koma inda take zaune, ta ci gaba da yin ma Ruƙayya zancen Hauwan da Amaryanta, duk maganar nata zagin Anwar take yi tunda har yanzu zafin abun da yayi mata take ji, bare yanda ya yi wa Hauwan kishiya, shiyasa take ta zagin shi, tana cewa, "nan gaba ma, haka zai ce zai ƙaro Wata, ai bazai taba samun sukuni ba sai ya cike su sun kai su hudu cib, dama ai ta saba ganin irin waɗannan Mazan, yanzu ma kenan da kuɗi bai zauna mishi ba."

Ruƙayya tace, "to Allah ya kyauta dai."

"Amin ya Allah, don Allah taya Ni sheƙe wannan gyaɗan yanzu in kai markaɗe, don na rantse yau sai na sha kunun nan, na gaji da zama haka, kinga yanda duk na rame fa, ai yanzu dole in tashi neman maganin ƙiba ko don Bilal kar yayi min kishiya."

Dariya Ruƙayya tayi tace, "kai Aunty Sauda, wacce iriyar kishiya ana zaune ƙalau?"

"Ah! To ba ga shi nan ba kina ganin yanda Hauwa ta kasance ba? Ai Maza basu da tabbas Alkur'an, shiyasa gwara in tashi da wuta-wuta na; idan ba haka ba sai kiɗan ta sauya, musamman yanzu da aikin Bilal ya samu, ya samu koyarwan nan a makarantar gaba da primary, ga albashi mai tsoka, gwara in tashi tsaye da

Please Login or Register in order to submit comment