Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara in koma Mace tunda abinci ya samu."

Murmushi kawai Ruƙayya take yi, tana sheƙe gyaɗar da Sauda da bata

Itama kuma Saudan tana fere doya da zata dafa musu da rana, tana yi tana zuba zance ra-ra-ra ko gajiya ba ta yi, gaba ɗaya yanzu maganar nata ya koma kan kishiya ne

Sai da suka gama sannan ta fita kai niƙan, sai ta bar Ruƙayya tana duba mata doyan da aka ɗaura a wuta.
***



               Washe gari Sadis ya samo Keke napep ya zo ya ɗauke su dukkan su har Sauda, sabida tunda Ruƙayya ta faɗa mishi har da Sauda zasu je, bai ce komai ba tunda ya san Matar jarababbiya ce, yanzu in yace baza a je da ita ba ta dinga magana kenan, ƙarshe ma har taran shi zata yi ta gaya mishi duk abun da ke ranta, ai yana ganin yanda ake faɗa da ita koyaushe a gidan, kullum cikin hayaniya take da mutanen gari

Har da su Suleiman aka tafi tunda yau asabar ne basu je makaranta ba, ta shirya su suka tafi tare

Bilal dai bai ce komai ba, saboda ko yayi magana baza ta ji maganar sa ba, amma kwata -kwata bai ji daɗin tafiyar su da Sadis ba, don mutumin haushi yake ba shi tunda zaman su a gidan duk sun fahimci halin sa, musamman shaye-shayen sa da bin Mata labari har ya kai musu sun san wane ne shi, in aka zauna zaman majalisa har yi dashi ake yi ana ce wa, "Matan aure yake bi ma."
Shi yasa duk hankalin sa bai kwanta dashi ba yanzu, duk da ya yarda da Matarsa, ya san halin Sauda, idan ma ya ce zai neme ta ƙila watan tonon asirin sa ne yayi,
Amma shima yana fatan Allah ya hore mishi ya siya ko kwatan fegi ne ya soma gina wa tunda yanzu Allah ya ba shi aikin koyarwa, kuma ga saye da sayarwa da yake yi ba ya zama haka nan, don har ya soma ganin sauyi wajen Sauda. Hmm Mata kenan, su dai in har zasu samu yanda suke so to yanzu zaka ga sun sauya, tsit kake ji babu mai jin kansu tunda yana bata wadatacce, ga jari da ya ƙara mata duk ya biya ta kuɗaɗen ta da take bin shi. Yanzu zaman lafiya ta samu a tsakanin su, sai dai ka ji ta da maƙota a kan kuɗin ta


Bayan sun kai ƙofar gidan su Hauwa, suka sauka Sadis ya biya kuɗin gaba ɗaya, sannan sai suka shiga gidan

Shi kuma Sadis ya tsaya a haraban gidan, yace ma Ruƙayya, "idan ta shiga sai tayi masa sallama da Anwar ɗin."

Duk da babu Motan sa a haraban gidan, alamun ya fice ne, amma hakan bai sa Sadis ya canza daga ƙudurin sa ba, don ko babu Anwar bazai koma ba sai ya shiga ciki wlh

Ai kuwa sai ga Ruƙayya ta fito, tana goye da Safina; hannunta kuma riƙe dana Haidar, tace mishi, "babu Anwar ɗin ya fita wai."

Sai yace, "to mu je ciki mu gaisa da Matan nasa, daga nan inga Amarya, ai bazai yiwu in tafi bamu gaisa ba." Yayi gaba ba tare da ya jira cewar ta ba, yana yi yana share fuskarsa yana ƙara gyagygyara jikin sa

Ruƙayya dai bata ce komai ba saboda tsoron tayi magana ya ɗauki mataki a kanta, amma ta san hakan bai dace ba. Bin bayansa tayi suka shiga ciki


Su Hauwa suna zaune a falon ita da Sauda. Yayinda Afnan ta tafi dauko musu diblan da cin-cin, don har ta fito sun gaisa ma

Sauda ta ɗan ranƙwafo da kanta tana gulman Afnan ɗin

Hauwa har ta buɗe baki zata yi mata magana a kan, "gwara ta dena kar ta fito ta ji ta."

Sai suka ji sallaman Sadis da shigowar sa

Sai da gaban Hauwa ya faɗi haka kawai, don bata yi tsammanin ganin sa a ciki ba tunda babu Anwar, da sauri ta miƙe tana shirin wuce wa daki sabida babu Hijab a jikinta, tana sanye da riga da skirt na atamfa, kuma sun kama ta sosai don har breasts ɗin ta sun bayyana, shiyasa duk ta daburce musamman yanda ta ga idanunsa a kanta suke

Washe baki yayi nan da nan ya soma mata magana yana cewa, "Uwar gida ran gida."

Hauwa tace, "sannu da zuwa, bari in zo zan saka mayafi ne sai na zo mu gaisa."

"To to, Shikenan." Yayi maganar yana ƙara ɓashe baki idanunsa kamar zasu faɗo ƙasa don kallon ta

Ruƙayya ce kaɗai ta kula da yanayin kallon da yake mata, shiyasa sai bata ji dad'i ba ta zauna a gefen Sauda; yayinda ta faɗa tunanin halin Mijin nata, da yanda yake yi wa Hauwan kallo kamar zai haɗiye ta har ta shige

Afnan ta soma fito wa riƙe da faranti mai faɗi, ta zubo musu cin-cin din, itama tayi shigan ta na atamfa ne ta cakare cikin ɗinkin ta mai kyau, sai shining da take yi ga MakeUp da ya ɗauke farar fuskarta

Itama tana fitowa Sadis ya bi ta da kallo, yana mai mamakin yanda Anwar duk ya tara kyawawan Mata a gidan sa, Allah ya basa domin duk ba na yarwa a cikin su, Mata iya Mata. Ya kasa ma amsa gaisuwar nata sabida yanda ya shagaltu da kallon nata

Sai da Suleiman ya taɓa sa yana faɗa masa, "ana gaishe shi."

Sannan ne ya dawo hayyacin sa, yana amsa wa tare da ce mata, "ya Amarci?"

Bata iya amsa wa ba illa murmusawa da tayi, dayake ba ta kallonsa bata san ma me yake yi ba, zama tayi a gefe tana ce ma su Sauda, "ga cin-cin nan su taɓa." Sai kuma ta miƙe tana wuce wa ciki don ɗibo ma Sadis nasa

Ita kuma Sauda har ta ɗauki farantin ta ajiye a jikinta tana afawa, while Haidar da ya zo ya manne a kusa da ita, ta dumbizo tana zuba mishi a hannu kuma take faɗin, "shiyasa ba na son zuwa da ku anguwa, tunda baza ku jira a baku ba sai ku zo kuna tsira wa Mutane na mujiya, dalla riƙe, kaima zo ka amsa naka."
Duk ta cika musu hannu itama tana afawa a bakin ta, sai da ta ci ta ƙara ɗiba ta kai bakin ta tukun tace, "kai bari in ajiye kar kuma mu cinye mu da zamu raba."

Ruƙayya murmushi tayi bata ce komai ba ita kam

Hauwa ta fito a lokacin ta saka Hijab dinta har ƙasa, bata bari sun haɗa ido da Sadis ba ta zauna tana mishi sannu da zuwa. Daga nan suka gaisa idanunta yana a kan Haidar da take mishi wasa, don ta kasa haɗa ido da Sadis sabida har ranta take jin ita yake kallo, baƙin ciki da tsanarsa ne kawai a ranta, don wlh sosai take mugun jin haushin mutumin tunda ya nuna mata halin sa, da alamu bazai barta ba tunda ga shi ya biyo ta har gida. Sai magana yake yi amma tayi banza da shi, tana jin su suna hira gaba ɗayan su bata ce komai ba, sai ma daga baya tace ma Ruƙayya, "ta ɗauko musu ruwa su sha."

Itama Afnan koda ta fito ta saka gyale a jikinta, tunda ta ga akwai namiji a wurin bai kamata ta fito a haka ba. ta zauna ana ɗan taɓa hiran da ita, duk da duk ƙarfin surutun Sauda ne

Shi kuma Sadis ya ƙi tafiya, a nan ya gyara zama yana ta cin diblan da cin-cin, har sai da ya cinye sannan ya tafi, shima don ya ga wasu baƙin sun shigo ne, shiyasa yayi musu sallama ya fice

Sai a lokacin Hauwa ta saki jikinta sosai, sai ta cire Hijabin tana sauke ajiyan zuciya, bata san wanne irin mayen Mutum bane wannan, idanunsa a kan Mata, sai dai ya ci kansa kuwa, dole ne ma ta taka masa burgi da shigo musu gida, don ba ta ƙaunar sake ganin fuskarsa ma, Allah ya yi sun bar gidan ma, da yanzu bata san yanda zata yi ba da wannan matsiyacin mutumin.








🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


               Kwana uku Jamal yayi ya dawo daga tafiyar sa. Dawowar sa ya ga yanda Hafsah duk ta fige ta lalace kamar wacce ta shekara a ciwo, shi kansa ya sha mamakin ganin ta a haka, shiyasa ita ya soma tambaya yana cewa, "ko dai ciwo tayi duk ta rame haka?"

Tsoro yasa tace mishi, "eh ciwo tayi."


"Subhanallah... Shi ne kuma ba a yi min magana ko asibiti an kai ki ba?"

Ita dai bata ce komai ba, illa zuba masa ruwan da tayi tana miƙe wa tsaye ta nufi hanyar kichen, ya bi bayanta da kallo cike da tausayin ta

Fauziyya tana fitowa yace mata, "wai dama Hafsah tana ciwo ne ba ki sanar min ba? And kuma ba a kaita asibiti ba?"

"Ciwo kuma? Ita tace maka tana ciwon?"

"Ai ko ba a tambaya ba kin san ba haka take ba ko? Ji be yanda duk tayi baƙi ta rame fa."


Yatsina fuska tayi tana zama tare da harɗe kafanta, cikin yanayin ko in kula tace, "to Ni gaskiya ban sani ba, ai ita ba yarinya bace da baza ta iya sanar min bata da lafiya ba, sai Ni ce zan tambaye ta tunda Ni na ajiye ta."

Jin haka sai Jamal ɗin bai ce mata komai ba, illa ɗaukar ruwan da yayi ya kurɓa kaɗan yana cire wa, alhamdulillah ya furta a fili before yace, "kin tara min ruwan ne?"

"Eh." Ta amsa a taƙaice idanunta a kan wayanta


"Ok, ban ji motsin yaran nan ba, ina suke?"

"Suna gidan Intisar, but yanzu zaka ga sun shigo since sun san da dawowar ka."


Miƙe wa yayi bai ce komai ba ya wuce cikin dakin sa

Ita kuma ta mayar da hankalin ta a kan kallo ba tare da ta damu da yanayin da yake ciki ba


Wanka ya soma yi da ya shiga ciki, bayan ya fito ne ya samu kira daga Mama, gaisa wa suka yi tana mishi sannu da zuwa. Ya amsa yana cewa, "alhamdulillah Mama, ya wurin su Salamatu?"

"Suna nan lafiya, sun ce a gaishe ka, yanzu ma ta fita zuwa gidan ta. Na so kiran ka tun ɗazu amma wayan ta ƙi shiga, sai yanzu na ce bari in ƙara gwada wa, ka ga kuwa ta shiga." Ta ƙare maganar tana murmusawa

Shima murmushin yayi yace, "ai dama Mama ana fama da matsalar network kwanan nan, ba ma iya nan ba har nan wlh, don nima na so kiran ki tun ina kan Mota amma ban samu ba."


"Allah Sarki! Ya su Hafsatu na, suna nan lafiya ko?"

Dariya yayi yace, "kina ji da Hafsatun nan naki dai Mama, suna nan lafiya, yanzu ma ta kawo min ruwa ta tafi zuwa kichen."


"To alhamdulillah." Sai ta ɗan yi jim, daga bisani kuma tace, "yauwa dama nace sai idan ka dawo zamu yi magana, in Allah ya yarda zuwa Juma'a nake saka ran dawowa, to ina son ganin ka ranan sai ka zo ka ɗauke Ni."


"Allah yasa lafiya Mama?"

"A'a lafiya ƙalau wlh, zan fi so dai ka zo ka ɗauke Ni ne, sai mu koma tare tunda ka jima baka zo ba ai."


"To Shikenan Mama, Insha Allahu zan zo, ko in taho da Hafsah ne?"

"A'a, ina kai ina taho wa da Hafsah? Ba akwai makaranta ba?"

"Eh akwai, tunda kinga jaraba wa suke yi, ba jima wa suke yi a can ba, shiyasa sai in jira ta su tashi mu taho tare."

"A'a ka barta kawai, mu ma ai a ranan zamu taho, kar ma ka sanar mata kaji ko?"

Yace, "to Mama, Allah ya kaimu."


"Amin ya Allah, bari in bar ka haka nan kar in cika ka da surutu, ka gaishe da Yaran."

Daga nan suka yi sallama ta kashe wayan. Shi kuma ya tashi ya saka jallabiya a jikinsa yana fice wa Falo.
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼











            *PAGE:20*

_____Ranan juma'a kamar yanda Mama tace Jamal ya je ƙauye ya same ta, haka kuwa ya yi, ƙarfe goma ya isa can. Bayan sun gaisa da mutane da ƴan uwa, har ya ci abinci suna ta hira da Maman

Daga baya ne ta tayar mishi da zancen abun da yasa ta kira shi, maganar auren su da Hafsah da za a ɗaura a yau ɗin

Matuƙa ya girgiza da jin zancen nata, shiyasa ya saki baki ya kasa cewa komai har ta kai aya a maganar ta, sannan yace, "wai Mama kina nufin Hafsah ƴata, ƴar ƙanwata Salamatu za a yi mana aure?"

"Ƙwarai kuwa, domin yanzu Ni har na nema maka auren ta, Jamaluddin ba na son ka ce komai don Allah ka amince da auren nan, domin Ni na ga dacewar hakan shiyasa na nema maka auren nan, bazan yi abun da zai cutar da kai ba, haka itama, Hafsatu yarinya ce mai tarbiyya don kaima ka shaida hakan tunda Ni na raine ta, abun da yayi ka itama shi yayi ta. Abun nan nayi min ciwo a ce kamar Ni bani da iko da kuma girman da ƴaƴan ka zasu kalle Ni a matsayin Kakar su, kai kaɗai ke gare Ni fa Jamalu, kai kaɗai na haifa a cikin cikina, amma ƴaƴan ka suna gudu na." Sai ta sharce hawayen da suka zubo mata batare da sanin ta ba, tana ci gaba da faɗin, "shiyasa na ga dacewar kayi aure ko don ka ƙara samun wasu ƴaƴan tunda Allah bai albarkace ka da su da yawa ba, kuma ban ga wacce ta dace irin Hafsatu ba, ina gudun mu sake yin kuskuren baya shiyasa na zaɓa maka ƴar uwanka wacce na tabbata baza ta taɓa wulaƙanta Ni a nan gaba ba, domin ko ba kai ta aura ba; ƴaƴanta nawa ne, bare kuma a ce kai zata aura, zan yi farin ciki da wannan auren."

Sosai maganganun Mama suka sagar mishi da gwiwa, suka saka mishi sanyin jikin da ya kasa ɗago kai bare ya kalle ta, illa mirza yatsun sa da yake yi a hankali yana sake jinjina maganar tamkar a mafarki

"Baka ce komai ba Jamaluddin? Kai nake saurare, dama nayi haka ne don ina ganin baza ka taɓa watsa min ƙasa a ido ba, na san na shiga haƙƙin ka haka kawai na jajibo maka aure ba tare da izinin ka ba, amma ina gyara maka goben ka ne Jamalu, ita kanta Fauziyyan wata rana zata gane kuskurenta ta gyara halayyar ta; tunda turban da ta ɗauka ba mai ɓulle wa bane."

Ɗago kai Jamal yayi, fuskarsa ɗauke da murmushin da ake kira da ka fi kuka ciwo, a nufin ya ɓoye tsantsan damuwar da ke tattare da shi, ya washe baki yana cewa, "Haba Mama, wlh ko ba ki nemi shawarata ba bazan taɓa bijire miki a kan wannan auren da za ki yi min ba, ke fa Uwata ce, kina da ikon da za ki zaɓa min abun da kika ga ya dace da Ni, don haka bani da wani haufi a kan hukuncin da kika yanke a kaina, duk da haka ina ba ki haƙuri sabida na san duk abubuwan da Fauziyya take miki ne ya janyo hakan, ki yi haƙuri na gaza ba ki farin ciki a matsayina na ɗanki ɗaya tilo..." Sai yayi shiru yana lumshe idanunsa sabida jin muryansa ya soma rawa, muddin ya ci gaba da magana kukan da yake ƙoƙarin kufce mishi ne zai fito fili

Mama da ke kallonsa cike da tausaya wa tace, "babu komai Jamaluddin, wannan ma biyayyan idan ka yi min ka gama min komai wlh, na tabbata wata rana zaka yi alfahari da haɗin ko ba na raye zaka ce na faɗa maka, ka riƙe Hafsah tsakani da Allah har mutuwa babu saki, Allah zai sanya muku albarka a auren nan naku, kuma zaku yi alfahari da juna."

Jinjina kansa kawai yayi bai iya cewa komai ba. Yana zaune yana ta sauraron ta har ta gama mishi huɗuba da nasiha.
***

                Zuwa ƙarfe ɗaya bayan an sauko masallacin juma'a, aka ɗaura musu aure a kan sadaki Naira dubu ɗari cif

Bayan an ɗaura ne, kusan ƙarfe uku da rabi suka kamo hanyan Bauchi. Biyar da rabi suka iso gidan.
Jamal da kansa ya ɗauko ma Maman kayanta daga cikin akwati suka wuce sashin ta

A lokacin Hafsah na kichen ɗin Fauziyya tana faman girka musu abincin dare, har ta ɗaura ruwan zafi ya soma tausa, tana shirin wanke shinkafar da zata zuba, ta ji ƙaran buɗe gate, sai ta leƙa ta window, ai kuwa nan idanunta suka faɗa a kan su Mama suna ƙoƙarin fitowa. Da sauri jikinta na rawa ta nufi gass ɗin ta kashe, ta fice da gudun ta tsaban murna da zumudin ganin Maman ta dawo, tunda ta san da tafiyan Jamal da safe da ya faɗa mata, "yau zai je dauko Mama."
Shi yasa gaba ɗaya a wunin yau zumuɗi ne ya cika ta, tana jin an taɓa gate zata duba window

Yanzu ma babu Fauziyya ta fice a motar ta, sai su Sumayya da suke Falo zaune suna Game sai iface-iface suke yi

Koda Hafsah ta zo fita, bata kalli inda suke ba duk da kiran da Sumayyar take mata. Haka ta fice ta gudunta ta nufi part ɗin su,
Ganin ta kawai suka yi ta faɗa kan Maman da ta nemi wuri ta zauna a kan kujera. Tana jin ta jikin Mama kuma sai ta fashe da kuka tana sake rungume ta

"Ah ah.. ah ah.. ikon Allah! Hafsatu har da kuka kuma? Ko duk murnan ne?" Cewar Mama cike da walwala tana ɗago kan Hafsan

Shi kuma Jamal da ke tsaye, kallonta kawai yake yi, a hankali ya samu wuri ya zauna bayan ya ajiye Jakar hannun nasa, yana sauraron abun da take cewa

Ita kuma Mama sai gaba ɗaya hankalin ta ya tashi sabida ganin yanda Hafsan ta koma, tace, "ko dai ciwo kika yi Hafsatu? Ya aka yi kika rame haka?"

Kamar ta kunna ta, sai ta ƙara ɓare baki tana cewa, "Ni wlh Mama bazan sake zama a gidan nan ba, kawai ki mayar da Ni ƙauye na fasa karatun, bazan sake zama ba." Ta ƙare maganar tana murje ido

Sai Mama ta kama mata hannun tare da cewa, "ya haƙuri haka nan yi shiru, ba ga shi yanzu na dawo ba, ai bazan sake tafiya in bar ki ba, ki yi shiru haka nan don Allah kukan nan naki yana tayar min da hankali."

Dole Hafsan ta shanye kukan, amma hawayen ta sun kasa tsayuwa wuri ɗaya, sai sharce su take yi da hannu

Sai a lokacin Jamal ya ja numfashi idanunsa ƙyar a kan Hafsan, a ransa yana ƙara mamakin wai yau shi ne aka ɗaura mishi aure da sa'ar ƴar shi? Ba ma Intisar ba; Sumayya fa. To ya zai yi kenan? Taya ma zai fara kallonta a matsayin Matarsa har ya iya sauke mata dukkan nauyin ta da ya rataya a kansa? Har ga Allah ya san yana jin tausayin ta amma bai taɓa kallonta da wata manufa ba, idan zai kalle ta da wata manufa kenan zai iya kallon ƴaƴan sa haka? Sosai ya ƙara nitsa wa a cikin tunani yana ƙara ƙare wa Hafsan kallo, wai wannan tatsitsiyar ce Matarsa? Yarinyar da ko girma bata dashi, yanzu ne ma take ƙirgan dangi, duk da tana sa'ar Sumayya, amma ita Sumayyar ta fita girma sosai tunda tana da gaɓa-gaɓan jiki irin na Mahaifiyarta, amma ita Hafsah kamar ka tatse ta ka saka a aljihu tsaban ƙanƙantar jiki. To ba a nan ma gizo ke saƙan ba, taya zai fuskanci Fauziyya da zancen auren nan nasa?
Duk da Mama ta faɗa masa, "ya bi komai a sannu, duk sanda ya ga dacewar sanar da Fauziyya sai ya faɗa mata kodayaushe don kar a shiga haƙƙin ta, amma ita Hafsah baza ta tare ba sai ta gama karatun nan na secondary." Shi yasa ya ɗan ji sanyi a cikin ransa, ya san yana da lokacin da zai samu damar faɗa wa Fauziyya, amma ba yanzu ba gaskiya, don ba ya son wata fitina ta kunno kai kuma...

Mama ta dawo dashi hayyacin sa tana cewa, "Jamalu, ka je kayi Sallah ko? Sai ka huta, Allah ya yi albarka."

Murmushi yayi yace, "Amin Mama. Amma na yanke shawara sabida ganin halin da Hafsah take ciki, da kuma abubuwan da suka faru yau, na san duk saboda kuna zama a gidan nan ne hakan ke faruwa, i know Fauziyya ba ta ƙaunar zaman ku a nan gidan, insha Allahu zan nema wani gidan sai ku koma can da zama, zan siya wani sabo sai ku zauna ke da Hafsah a can."

Cikin ɓashe baki Mama tace, "a yi haka kuma? Kar kuma nauyin yayi maka yawa Jamalu? Ka bar mu kawai a nan tunda dai mun soma saba wa da komai."

Murmushi yayi yana kallon Hafsah wacce ta ɗago kai itama ta zuba mishi ido. Ba tare da ya ɗauke idanun nasa ba yace, "ai ko don Hafsah zan yi haka, tunda ga shi tana shirin guduwa ƙauye ta bar ki ke kaɗai, gwara ku koma sabon gida inda babu matsa wa, zata fi sakin jiki a can tayi karatun ta ko Hafsah?"

Saurin ɗauke kanta tayi a kanshi, sai a lokacin ma ta ji kunyar zuba mishi ido da take yi ko ƙyafta su ba ta yi tana ta kallon bakin sa, ɓoye fuskarta tayi a jikin Mama tana ƴar ƙaramar dariya

Mama da Jamal su kuma suka yi murmushi gaba ɗaya. Inda Mama sai sanya mishi albarka take yi tana masa godiya

Sai ya tashi yace, "babu komai Mama, bari in je zuwa anjima sai in sake dawowa."

"To Shikenan, ka gaishe da mutanen gidan."

Yana fita Hafsah tace, "Inna ba ki ga yanda nake ta shan wahala a gidan nan ba, kullum sai Aunty Fauziyya ta duke Ni, kullum cikin hantara na suke yi, ko makarantar islamiyya na dena zuwa ba ta bari na in je sai dai in ta musu aiki." Sai ta matso hawaye tana cewa, "ƙila ma jarabawar nan bazan ci ba tunda ba na yin karatu, haka nan nake rubuta wa idan na je makaranta sai in zauna in duba."

Mama tace, "ai kuka ya ƙare yanzu ko? Tunda zamu tashi mu bar mata gidan ta. Ki share hawayen nan naki babu ke babu sake kuka kinji ko?"

Murmushi Hafsan tayi tana jin dad'i, sai kuma ta soma tambayar iyayenta da ƙannin ta?

Mama tace, "suna nan lafiya, sun bani saƙo ma in ba ki, ki duba kaya na Ni bari in yi sallah tunda bamu samu mun yi ba."

Da sauri Hafsah ta amsa mata tana miƙe wa ta koma gaban kayan

Ita kuma Mama ta shiga toilet ɗauro alwala

Sai daga baya Hafsah ta tuna girki take yi fa, ta san in har bata gama ba babu mai raba ta da Fauziyya, shiyasa ta tashi tace ma Mama, "zata je ta ƙarisa aikin ta sai ta dawo."

Da saurin ta ta koma sashin. Sai dai tana shiga ta samu harara daga Sumayya, kasancewar Sumayyar ta san akwai Dadyn su shiyasa bata ce ma Hafsan komai ba, sai tayi ƙwafa tana dauke kanta. Itama kuma Hafsah ta wuce kanta tsaye kichen ta sake kunna gass ɗin. Yana tausa ta zuba shinkafar; ta ci gaba da sauran aikace-aikacen ta

Jamal ne ya shigo kichen ɗin, lokacin har ya watsa ruwa ya

Please Login or Register in order to submit comment