Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannu ya duke ta, to wlh tayi ƙudurin sai ta ƙuntata mishi shima, dole sai ta zubar da cikin nan shima ya ji in da dad'i, tunda ba ya son farin cikin ta itama baza ta taɓa bari ya samu farin cikin ba, da ita yake zancen.
Wuni tayi a ɗaki ta ƙi fitowa, ko abinci ta ƙi ci

Har ɗaki mai aikin ta ta kawo mata abincin amma ta fatattake ta da zagi, dole ta fita da sauri ta kaiwa Shuriem abincin; tunda shi ya saka ta ta je har ɗakin nata ta kai mata, don ya san halin ta baza ta fito ta ci abinci ba in har suna faɗa since ba yau ta saba hakan ba

Amsar abincin yayi ya wuce ɗakin ya kai mata da kansa domin ya rarrashe ta, zama yayi a gefen gadon tare da kiran sunan ta, amma fafur ta ƙi tashi bare ta saurare shi, sai ma ci gaba da gunjin kukan ta take yi. Duk yanda ya so ya rarrashe ta tare da faɗa mata kalamai masu dad'i da sanyaya zuciya amma ta ƙi kula sa. Dole ya haƙura ya tashi ya bar mata abincin a wurin

Yana fita ta tashi tayi fatali da abincin sannan ta shige toilet tayi wanka da alwala ta sauya kayan ta, sallah tayi ta rufe ƙofan ta haye kan gado ta ci gaba da rera sabon kuka

Lokacin ne Shuriem ya shigo mata da akwatin ta, amma ganin ta rufe ƙofa sai ya ajiye mata a wurin yayi tafiyar sa

Tuna wa tayi da wayanta, dole ta tashi ta buɗe ƙofan domin ɗauko Jakarta, ganin Jakar a bakin kofa sai ta ja ta shiga dashi ciki ta datse ƙofan, wayan ta ta ciro ta kira layin Momyn su, ai kuwa ta ci Sa'a ta shiga, tana ɗauka ta fashe mata da kuka tana kiran sunan ta

Cike da tashin hankali Fauziyya tace, "ya buge ki ne Intisar? Yanzun nan muka gama waya da Balaraba take sanar min Dadyn ku ya zo ya tafi da ke, me ya faru ki sanar min abun da yayi miki?"

Tana kuka ta faɗa mata irin marin da yayi mata

Rai a ɓace tace, "ki dena kukan, nima yanzu zan koma gidan, ki kashe wayan zan sake kiran ki daga baya."

Dole ta kashe wayan ta ajiye ta ci gaba da wani sabon kukan, duk da yunwar da take ji amma hakan bai sa ta nemi abinci ba, tunda sosai ta fusata bakin ciki da ƙunci ke nuƙurƙusan ta, wanda tana jin baza ta taɓa huce wa ba sai ta fitar da cikin nan a jikinta. Shuriem da ita yake zancen.
***

             Jamal yana can yana safa da marwa yana jiran Fauziyya ta dawo, tana shigowa falon ya soma sauke mata kwandon bala'in da bata yi zaton samu daga wurin sa ba, don itama a wuya tazo amma sai ta ga nashi masifan ya fi nata, shi kansa daure wa yayi ya nuna mata ɓacin ran nasa, kuma yace, "wlh in har tayi sanadin da ƴarsa ta fito gidan Mijinta; to itama zata fita a nata gidan."

Hankalin Fauziyya ya tashi jin furucin nasa, amma don borin kunya bata ƙyale shi haka nan ba, itama haka ta dinga zuba ruwan masifa tana cewa, "baza ta taɓa barin a tauye mata haƙƙin ƴa ba, tun ba yau ba Shuriem yake wulaƙanta mata yarinya, ya taɓa daukar mataki ne a kan abubuwan da yake yi? Ko ya manta har marin ta ya taɓa yi? Yanzu kuma idan aka bar shi nan gaba dukan ta zai yi, tunda wlh baza ta taɓa yarda ba, don me zai hana ta karatu in ba mugunta irin nasa ba? ai ba a ce dole sai shi zai biya makarantar ba, amma ya ɗaura kishin banza a ransa ya hana yarinya karatu bayan shi ya hure mata kunne a baya ta ƙi makarantar ta zaɓi auren sa, amma yanzu zai jajibo hujjar sa na banza yace baza tayi ba, ai wlh baza ta taɓa bari yarinyar ta ta zauna a gidan babu galihu ba, dole ta taya ta ƙwato haƙƙin ta, abun haushi ne ma a ce kamar shi Mahaifinta amma yana ƙin goyon bayan ƴarsa, ya san cewa dole wata rana ita za a wulaƙanta ƙarshe ya auro mata wata mai ilmin da wayewa, don haka su basu rasa komai ba suna da kuɗin da zasu iya ɗaukar nauyin ƴar su in har shi bazai iya ba."
   

Jamal yace, "Ni dai na faɗa miki, maganata ta ƙarshe kenan, in har kin kashe mata aure to ke ma naki zai mutu, ki ji da kyau."
Ya juya ya fice a gidan, don kwata-kwata ba ya son ci gaba da zaman sa a gidan, yanda yake jin zuciyarsa babu dad'i zaman sa a gidan ƙara masa ɓacin rai zata yi in dai Fauziyya ce. Kai tsaye sai ya wuce gidan Mama

Yayinda Fauziyya kuma itama fitan tayi don bata ga ta zama ba, wlh dole ta kawo ƙarshen matsalar ta da Jamal, ta soma gajiya, idan tayi kamar ta samu bakin zaren; ta soma shawo kansa sai kuma abu ya ƙara jagule mata, ta rasa wanne irin mutum ne shi? Duk kuɗin ta da take kashe wa a banza don mallake sa; daga abu ya fara tasiri a jikinsa sai kuma ya dawo baya, dole ta tashi tsaye, ko me zata yi domin samun mafita, daga ita har ƴarta domin bata ga ta zama ba.
***



           Bayan ya isa; sai ya faka motan sa a bakin ƙofan gidan, tare da zama a ciki ya kasa fitowa illa kwantar da kansa da yayi a sitiyarin motan zuciyarsa tana ta tafarfasa, ya jima a yanayin nan before ya buɗe Motan ya fito ya shiga gidan. Da sallama ya ƙarisa shige wa cikin Falon yana aza idanunsa a kan Hafsah wacce ke zaune ita kaɗai a falon


Da sauri ta sauke ƙafafun ta a ƙasa tana gyara zamanta tare da amsa mishi sallaman, sai tayi saurin ɗauke idanunta ganin nasa sun shige cikin nata,
Sai da ta bari ya shigo ciki ya zauna sannan tayi mishi sannu da zuwa, tana miƙe wa da ninyar ɗauko masa ruwa

"Ina Mama?" Ya tambaye ta cike da sanyin murya yana bin ta da kallo, ganin ta yau babu Hijab tana sanye da riga da wando na fakistan; da suka yi wa ɗan kyakkyawar jikinta cif gunun sha'awa

Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa mishi, "ta shiga maƙota ne."

"Me ake yi a maƙotan?" Ya sake jeho mata tambayar still bai ɗauke idanun a kanta ba, don shi kansa ji yayi yana buƙatar kallon ta don ba ƙaramin kyau tayi masa ba, shi dai bai taɓa ganin ta da MakeUp a fuska ba sai yau, kuma ba ƙaramin ɗaukar fuskarta yayi ba sabida ta iya kwalliyan tana koyo a wurin ƙawarta; since sana'ar ta kenan

Kamar kuwa ta san Mijin nata zai zo, sai ga shi yau ta gwada a fuskarta, abun mamakin kuma hakan ba ƙaramin tafiya da imanin sa yayi ba

Koda ta ba shi amsar, "suna ake yi, shi ne ta shiga tayi musu Barka."

Sai ya kasa yin shiru yace, "wane ne yayi miki wannan kwalliyar Hafsah?"

Ɗago kai tayi tana kallonsa, sai kuma kunya ta kama ta tayi saurin rufe fuskarta tana ƴar dariyan da ya taho mata babu shiri

Lokaci ɗaya shima ya yi murmushin, sabida har zuciyarsa ya ji sanyi, sai yace, "na ba ki dariya ko?"

Saurin girgiza kanta tayi ta kasa ɗauke hannunta a saman face ɗin ta

"Kin yi kyau, na san kin yi ne don Ni."

Jin hakan bata san sanda ta buɗe fuskar nata ba, cike da shagwaɓa kamar zata yi kuka tace, "Allah ba don kai nayi ba Dady."

"Haba da gaske?"

Kai ta gyaɗa mishi

"Um! Ni ban yarda ba, don Ni aka yi wannan kwalliyar, in kuma ba haka bane a faɗa min wane kika yi wa?"

Shiru tayi tana tura baki kamar zata yi kuka idanunta a ƙasa

Shi kuma sai yayi ƴar dariya cike da nishaɗi yace, "faɗa min mana ina jira?"

"Allah ba don kai nayi ba, wanka nayi shine nayi kwalliyar."

"Ok na yarda, kawo min ruwa in sha, in akwai abinci ma ki zubo min." Ya furta hakan yana bin ta da ido still yana murmusawa

Itama murmushin tayi ta juya tana isa wurin ƙaramin fridge ɗin su, buɗe wa tayi ta ɗauko ruwan pure water tare da ajiye wa a saman fridge ɗin, kana ta nufi kichen ta zubo abinci sannan ta saka spoon, wani plate ɗin ta dauko a hannu sannan ta kawo mishi

Duk bata sani ba yana ta famar kallon ta duk inda tayi, domin duk yanda yaso ya janye idanunsa a kanta ya kasa, yau dai free ya samu ƙare mata kallo; wanda rabon shi da ya ganta a haka babu Hijab ya jima gaskiya

Zuwa tayi ta ɗauki ruwan ta saka a empty plate ɗin da ta ɗauko, sannan ta kawo masa ta ajiye masa. Tana ɗago kai suka sake haɗa ido, sai kunya ya kama ta saboda yanda ta ga yana ta kallonta kamar zai cinye ta, saurin juya wa tayi zata shige ɗaki, sai ya tsayar da ita ya bata umarnin dawowa. Dole ta koma cike da jin kunya ta zauna a ƙasa tana duƙar da kai

Shima sai ya dawo Kasan ya zauna yana cewa, "yau dai da Matata zan ci abincin nan, kunya ta ƙare daga yau; don dole sai na cire miki shi kafin in tafi."

Wani irin sara wa gabanta yayi; musamman yanda ta ji ya kira ta da Matarsa, ba ƙaramin dukan mata zuciya kalman yayi ba, sai ta ɗago tana narai-narai da ido kamar zata yi kuka tace, "wlh na ƙoshi Dady, bazan iya ci ba."

Ɗan waro ido yayi da wasa ya ɗaure fuskarsa yace, "oh! Ni za ki yi wa gardama? Ni fa Mijinki ne, sannan ba na son wannan sunan daga yau, Ni ba Dadyn ki bane, daga yau Ni Mijinki ne, taho mu ci abincin." Ya ƙare maganar yana saka hannu tare da ɗaukar spoon ya soma ci

"Allah na ƙoshi." Tayi maganar tana ƙoƙarin yin kuka
          

"Allah sai kin ci, idan kuma baza ki ci ba na ba ki zaɓi, ko ki bani a baki ko kuma ki zo mu ci tare..." Dole ya ƙumshe baki sabida dariyan dake son kufce masa; ganin yanda ta daburce lokaci ɗaya yanayin ta ya sauya daga tsoratan da tayi, amma ya daure ya cije yana ƙara haɗe fuska babu alamar wasa a tare da shi yace, "Hafsah ki zo mu ci abincin nan; ko ki bani a baki, yau nima ina son ki samu ladan nan; nima in ji dad'i in san ina da wata Matar mai faranta min".




_Happy juma'at Mubarakh ƴan uwana Masoyana, Allah ya bamu albarkatun ranan nan, enjoy your weekend 😘._
[03/01, 4:54 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼











            *PAGE:30*

_____"Hafsah. Kina so mu fara ƴar gardama da ke ne?" Ya furta yana waro idanunsa waje sosai

Hakan ne yasa dole ta soma matsowa wurin sa, yayinda hawaye har sun soma ɗiga a kan kuncin ta, jikinta sai faman rawa yake yi don bata san ya zata yi ba

Shi kuma haka nan ya daure duk da ta ba shi tausayi, amma so yake yi ya tsokane ta don ba ƙaramin nishaɗi yake ji ba, tana gama matsowa sai yace, "oya fara ci, ko kuma a bakin za ki bani?" Ya tsare ta da ido yana jiran amsar ta

Kanta ta sunkuyar ta kasa cewa komai, yayinda take jin zuciyarta na faman buga wa duk ta gama takure wa waje ɗaya, hawayen ta sai ƙara gudu yake yi

"Is ok. Tunda baza ki yi ba, ki zauna a wurin har in gama ci, tunda kin san haka ya kamata kowacce Mata ta riƙa yi wa Mijinta, idan yana cin abinci tana zaune a wurin tana taya sa hira har ya gama."
Abincin ya soma ci bai sake ce mata komai ba don itama ta ƙi yin magana, amma yana hankalce da ita, so yake yi yayi dariya but ya daure, can kuma sai ya ajiye cokalin yana ɗan matso da fuskarsa tare da leƙa nata

Da sauri ta ɗago kai sabida jin hucin numfashinsa kusa da ita, nan kuwa suka kusa yin karo da juna, sai tayi saurin matsa wa tana ƙara duƙar da kanta har da runtse ido

Shima matso wa yayi ya saka hannu ya ɗago kanta, tare da ɗaura ɗaya hannun a saman face ɗin ta yana share mata hawayen, yanda ta runtse idanunta sosai tana ɓarin lips; hakan ne yasa ya tsaya yana kallon choco Face ɗin ta gunun sha'awa, yayinda yake jin wani yanayi a jikinsa wanda bai taɓa jin makamancin hakan a tare da ita ba, har wani tsigan jikinsa tashi yake yi, take a nan shima ya rufe idanun yana buɗe wa a kanta, kana ya ci gaba da share mata hawayen a hankali cike da sanyin murya yace, "Sorry My daughter, ban so na saka ki kuka ba, ki yafe min kinji?"

Gyaɗa kanta tayi amma ta kasa buɗe ido bare ta kalle sa, kuma ta kasa janye kanta daga riƙon da yayi mata saboda kwata-kwata ta nemi ƙarfin jikinta ta rasa, tamkar an saka glue an nane ta a wurin haka take ji

"To buɗe idon ki kalle Ni."

Kasa buɗe wa tayi, sai a lokacin ta samu damar saka hannunta ta zare nashi tare da ɓoye kanta a saman cinyoyinta; ta cusa shi ciki tana faman ajiyan zuciya

Shi kuma ya kasa matsa wa a wurin sai faman kallonta yake yi, ya jima yana ɗan tunani a ransa kafin ya sake furta, "please ki ɗago kanki in ci gaba da cin abincin, in ina kallon kwalliyan nan naki na fi jin nishaɗi a raina, zan fi jin daɗin cin abincin, Please My daughter." Ya ƙare maganar cikin wani yanayi tare da dafa mata cinya yana ɗan shafa mata

Sai ga Hafsah ta zabura zata gudu,
Amma kamar ya san abun da take shirin yi yayi saurin cafko mata hannu, ai kuwa sai ta fashe mishi da kuka bil haƙƙi da gaskiyar ta

Waro ido yayi waje yace, "Hafsah za ki tara min mutane ne? Me nayi miki?"

"Don Allah ka bar Ni in tafi." Tayi maganar tana kuka sosai idanunta a kansa duk ta gama fita a hayyacin ta tsaban yanda jikinta ke tsuma da abun da bata saba gani ba

Murmushi yayi mata yace, "Hafsah kenan! To share hawayen, in ba ki share ba Allah bazan bar ki ki tafi ba."

Da sauri ta share tana jan shashsheƙa

"Yauwa ko ke fa, amma kin ɓata kwalliyan, in kin shiga sai ki share."
Sakin hannunta yayi alamun ya bata damar tafiya

Sai ta tashi da sauri ta shige ɗaki tana ci gaba da share wasu hawayen da ke fito mata

Dariya yayi yana ɗan cije laɓɓansa, a ransa yace, "oh! Wannan yarinya, akwai ta da kunya, anya ba'a bani aiki ba?" Sai kuma ya ci gaba da murmusawa tuna abubuwan da ya faru, yana cin abincin yana tunanin Hafsah wacce ta tsaya mishi a rai, har ji yake yi tamkar ta sake dawowa ta zauna kusa da shi, tunanin sa ya tafi gaba ɗaya a kan duk lokacin da aka kawo ta gidan sa ya kenan? Akwai kallo kenan tunda ta kasa sakin jikinta saboda kunya, "ai kuwa zan cire mata kunyar nan tun kafin lokaci yayi, dole zamu saba." Ya furta a fili yana kai wani loman abincin, sai kuma wata zuciyar tace mishi, "kenan ka amince da ita a matsayin Matar ka? Har ka manta hukuncin da ka yanke a baya na rabuwa da ita?"
Take a nan ya dakata da cin abincin, shi kansa bai san cewa wannan ranan zata zo mishi har ya riƙa tunanin Hafsah a matsayin Matarsa da zata tare a nan gaba ba, bayan ya san cewa yayi tunanin sawwake mata, amma kuma a yau baƙon yanayin da ya shige sa yasa yana jin zai iya zama da ita a haka, tabbas har zuciyarsa yana jin hakan, yana son su kasance tare a matsayin Miji da Mata

Haka ya zauna yana ta famar tunani har Mama ta dawo gidan ta same shi a haka

Kuma har lokacin Hafsah bata fito ba tana ɗaki tayi lamo tana sauraron hiran nasu, yayinda abun da ya faru itama ya tsaya mata a rai; duk ƙwaƙƙwaran motsin da zata yi jin hannun Jamal take yi a jikinta, ta rasa yanda zata yi domin ganin abun take yi kamar a mafarki, har sai da ta sha kuka ta gode wa Allah, sannan ta shiga bayi ta wanke fuskarta. Bata fita ba sai da Jamal ɗin ya bar gidan, don bai jima ba ya tafi,
Amma fa har lokacin Hafsah ta kasa sakin jikinta, ta kasa amsar waɗannan sabbin yanayin da ya shige ta,
A ranan ko runtsa wa ta kasa, da zaran ta rufe ido Jamal take gani, shiyasa dole ta kasa barci, hakan ne yasa da safe ta wuce school da wuri -wuri, lokacin da ta isa babu kowa a class ɗin su, sai tayi zaman ta ta ɗauki littafin English tana duba wa, duk da tunanin Jamal na maƙale a ƙasar zuciyarta ya ƙi fita

Tana nan zaune Sumayya ta soma shigo wa. Tunda suka haɗa ido ta sakar mata wata uwar harara tana jan dogon tsaki tare da zagin ta cikin turanci

Ita kuma Hafsah jikinta ne ya ƙara sanyi, sai ta kawar ta kanta tana ci gaba da duba littafin, amma nan take idanunta suka ciko da hawaye suka canza kala, haka kawai take jin kamar ta fashe da kuka, ita ya zata yi da rayuwarta? Duk ranan da suka san cewa Mahaifin su take aure? Wanne irin ƙalubale zata fuskanta a nan gaba?

Ƙawarta Naja'atu da ta zo wurin, ita ta katse mata tunanin nata tana cewa, "ah! Yau Hafsah an bugo sammako kenan? Kin riga ni zuwa."

Saurin share hawayenta tayi ba tare da ta bari ta fahimta ba, sai ta ɗago kanta tana mata murmushi tare da cewa, "wlh kuwa, yau na bugo sammako. Ykk?"

"Normal ne a waje na, but ke naga kamar kina cikin damuwa don daga ganin idanun nan naki basu samu barci ba? Lafiya?" Ta ƙare maganar tana bin ta da kallo

"Babu komai, gaskiyar ki ne ban samu barci bane shiyasa kika ganni a haka." Itama ta bata amsar tana ɗan sakin fuskarta sosai tare da ƙara yalwata murmushin ta

Hararanta Naja'atu tayi tace, "kar ki raina min wayon? Allah na san da damuwa a ranki don wannan ba rashin barci bane kaɗai, sai dai kuma in Dady ne ya hana ki barcin."

Waro ido Hafsah tayi kamar ta ga abun tsoro

Ita kuma sai ta fashe da dariya har da tafa hannu, sai kuma ta rage murya tana matso da bakin ta kusa da kunnenta tare da raɗa mata, "don Allah faɗa min gaskiya, anya ba Dady bane ya hana ki runtsa wa jiya ba? Don na san babu yanda za a yi ki kasa barci ke ba exams ne da ke ba yau, me ya hana ki barcin?"

Kamar zata yi mata kuka tace, "Allah ki dena ba na so."

"Ke fa banza ce Hafsah, ban san meyasa Allah ya ba ki dama a hannun ki kike wasa da ita ba, na rantse da Allah da Ni ce nake auren Dadyn wata a class ɗin nan, da an ga bura'uba, don wlh sai yarinya ta raina kanta, sai na nuna mata Ni ba Sa'ar wasan ta bane sai dai tsohon ta."
Tayi maganar cikin ƙarfi sabida so take yi Sumayya ta ji

Kuma da alamun ta ji ɗin, domin har ɗago kai tayi tana kallon Naja'atun, duk da kwata-kwata bata gane me take nufi ba,
Kuma yawancin ƴan ajin ma sun ji abun da take furta wa kowa ya mayar da hankalin sa a kanta saboda su fahimci mai ake faɗa

Amma sai Hafsah ta rufe mata baki kamar zata yi kuka tace, "don Allah ki yi shiru, mene ne haka? Wlh na soma dana-sanin faɗa miki sirrina tunda baza ki iya riƙe min ba."

"Ki yi haƙuri Hafsah, ba wai na kasa riƙe miki sirrin ki bane, amma gani nayi kwata-kwata ba ki da wayon, wai meyasa baza ki yi amfani da damar ki wurin ƙwace Mijin nan naki ba? Me kika rasa? Amma har yanzu kin zauna da auren wani a kanki bai shafe ki ba, sai lokacin da aka kaiki ɗakin shi sannan za ki soma jawo hankalin sa ko? To wlh ki san me kike yi tun wuri ki farka daga shegen mafarkin nan naki da kike tunanin koyaushe shi yake faruwa da ke, ki kama Mijinki a tafin hannun ki, ke kinji dad'i ma auren gata aka yi miki, babu abun da za ki nema a wurin namiji kamar Dady ki kasa samu, ya kai namijin da kowacce Mace zata so shi, amma kin zauna har yanzu kanki a tukunya a rufe kina nuƙu-nuƙu kin kasa sakin jikin ki, wata rana kina..."
Shigowar Teacher cikin ajin shiyasa Naja'atu tayi shiru daga zuban da take yi ko haɗiyar yawu ba ta yi. Amma ta dauki alwashin wlh in dai suna raye sai ta tusa wa Hafsah ra'ayin Dady ko ta halin ƙa-ƙa, don ita so take yi ta ga yanda draman zai kasance lokacin da Sumayya ta san cewa mahaifin ta yana auren Hafsah, hmm akwai kallo kenan, ai da sannu sai ta ci galaba a kan Hafsah dole ne sai ta dawo da ita kan hanya, don gani take yi wawiya ce ita har yanzu ƙauyanci na damun ta, amma mene ne abun kunya da ƙin sakin jiki ta samo soyayyar Mijinta? Tunda an rigada an yi auren, magana kuma ta ƙare.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


          Jin ƙaran buɗe ƙofan yasa ta miƙe da sauri; domin a tunanin ta Aliyu ne kamar yanda ta aiki Yaro ya kira mata shi, amma saɓanin haka sai ta ga ƙaninsa Usman ne ya fito fuska a turɓune

Wani kallo ya watsa mata; har ya buɗe baki da ninyar yin mata tijara, sai ya ji muryan Aliyun daga bayan sa yana cewa

"Usman zo ka wuce."

"Amma Yaya."

"Shut up! Ka zo ka wuce nace." Ya basa umarni cikin daka tsawa

Kwafa yayi yana karkaɗa kansa, tare da juya wa ya shige gidan yana faman huci

Shi kuma sai ya taho wurin ta yana kallonta cike da baƙin cikin sake ganin fuskarta yace, "Zeena mai kika zo yi a nan? Ban ce kar in ƙara ganin fuskar ki a kofar gidan mu ba?"

Tuni hawaye sun zubo mata a kan kunci, sai tayi saurin duƙa wa a gaban sa cikin rawan murya ta soma magana da faɗin, "don Allah kayi haƙuri Aliyu ka tsaya ka fahimce Ni, ban zo nan don wata manufa ba face in baka haƙuri a kan abubuwan da suka faru, wlh tallahi na kasa jure wa ne ina cikin tsananin tashin hankali da damuwa, idan baka yafe min ba ina zan saka raina? Kullum bani da sukuni ba na iya barci mai daɗi saboda abubuwan da suka faru, bani da aiki sai tunanin su Sadiq ko barci idan ina yi su nake gani, ban san ya zan yi da rayuwata ba ka taimaka min ka yafe min ko zan samu sassauci

Please Login or Register in order to submit comment