Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen sai in ta ɗauro. Duk nacin da Sauda take mata a kan rashin zama a waje suna hira ta ƙi kula ta

Abun har ya kai Sauda ta ɗauki zafi da ita, har tana cewa, "wai ko don ta ga Mijinta yanzu yayi gida ne shiyasa take son jan baya da su? Dama ta kula yanzu ko magana ba ta son yin musu, Allah Sarki! Ta kwantar da hankalinta su ma wata rana insha Allahu zasu yi gidan kansu, ba sai ta ɗauke musu wuta ba wata rana su ma Allah zai buɗa musu."

Haƙiƙa Hauwa bata ji daɗin zancen Sauda ba, don har hawaye ta zubar take ce mata, "bata taɓa tunanin zata ɗauke ta da wata fuska saɓanin yadda take ɗaukar ta ba. Meyasa zata riƙa mata wannan mummunar fahimtar bayan ta san duk zaman su da ita bata taɓa ƙyamatar ta ba?"

Sauda tace, "yo ai ɗan Adam na sauya wa a kowanne lokaci, ba ga shi ba yanzu kuɗi yana son sauya ki tunda Allah ya hore ma Mijinki? Babu abun da bazan gani ba Hauwa tunda yanzu kun shiga daula, ɗan hiran ma da muke da ke yanzu ƙyashin yi kike yi damu tunda kin fi ƙarfin mu."

Maganar nan fa ta kai har gun Mazajen su, domin tsiya suka yi raga-raga Hauwa sai kuka take yi, a ganin ta don me Sauda zata yi mata wannan fahimtar? Ruƙayya ta raba su amma ta kasa, har sai da Mazajen su suka dawo suka gansu suna sa'insa

Wanda Anwar ya ɗauki zafi sosai yace ma Sauda, "daga yau babu ita babu Matarsa, ta fita a harkan ta tunda ba wata tsiyar take bata ba."

Nan fa Saudan ta dinga fitina tana cewa, "ai dole ya tare ma Matarsa, dole kuma yace haka tunda yanzu suna ganin sun fi ƙarfin su, to sai me? Su ma da yardan Allah zasu yi kuɗin su wuce wulaƙanci."

Bai dai kula ta ba ya ja Hauwa suka shige ɗaki, itama ya dinga mata faɗa domin bai taɓa nuna ɓacin ransa da ita ba sai a ranan, kamar dama jira yake yi haka yayi wa Hauwa kaca-kaca kuma yace, "wlh idan bata fita harkan Matar nan ba duk abun da yayi mata ita ta ja."

Hauwa sai kuka take yi ta tara inda zata saka kanta, bata taɓa tunanin Anwar zai yi mata haka ba, bare tana ganin abun bai kai ya kawo da zai rufe ta da faɗa haka ba. Kuma ƙarshe ya ƙi rarrashinta dole ita tayi shiru don kanta

Inda shima Bilal sai yi wa Sauda faɗan yake yi, yace, "Allah wadaran halin ta, Mace ba kamun kai sai tayar da husuma, kullum ita baza ta yi hankali ta san Annabi ya faku ba? Tana girma tana ƙara taɓarɓare wa wannan wacce irin rayuwa ce? Wlh shima ya soma gajiya zai ɗauki mummunan mataki a kanta tunda bata da hankali."

Sauda ita kanta ta san ta taɓo Bilal domin shima hauka-hauka ya nuna mata wanda bai taɓa nuna mata ba, dole ta haƙura ta yi shiru da nata tsiyan ta shafa wa kanta lafiya

Shi yasa daga ranan sai suka koma babu mai shiga harkan wani ita da Hauwa, domin ita Hauwa Mijinta yayi mata tsakani da Sauda shiyasa ta kasa kula ta gudun ɓacin ransa, ita kuma a lokacin Sauda tana jin haushin Hauwa saboda faɗan da suka yi

Duk Ruƙayya ta ji babu daɗi a wannan lokacin; saboda yanda gidan ya koma, sai dai babu yanda zata yi sabida duk hakurin da ta basu domin su haɗa kansu a koma kamar da abun ya cutura

Gwara-gwara ma Sauda yanzu ta sauko ta koma yi wa Hauwa magana, dama iskanci da kuma halin ta shiyasa take faɗan haka, amma ita kanta shaida ce ta san halin Hauwa, kawai dai ba ta jin daɗin yanda Hauwan ta soma ɗauke musu wuta ne ba ta son shiga cikin su ana hira shiyasa ta faɗa haka, amma kuma a yanzu da take son su dawo dai-dai kuma abun ya faskara tunda Hauwa ta kasa sakin jikinta gudun ɓata wa Mijinta rai, ya rigada ya yanke alaƙar su da Sauda yace, "kar ta ƙara shiga harkan ta." Shi yasa ta kasa bata fuska sai dai gaisuwa da suke yi. Ita kuma Sauda ta ƙi haƙura a haka dai take ta shige mata domin har bata hakuri tayi tace, "zaman tare bai ce haka ba, dama zo mu zauna zo mu saɓa ne, tayi hakuri ta yafe mata tunda zaman su ya kusa ƙarewa, ba ta son ta tafi suna gaba."

Hauwa tace, "ya wuce ai, Ni ban ƙullace ki da komai ba Sauda, sai dai Mijina yayi min tsakani da ke dole in yi taka-tsan-tsan kar in saɓa mishi".







**********

Daga can wajen iyayen Anwar, su suka tilasta shi sai dai ya bar Hauwa ta tare, saboda bazai yiwu ace tana Uwar gida dole sai tare da Amarya zasu tare ba, sun ji shiru-shiru bai da alamar barin ta ta tare shiyasa Mamansa tayi masa tsiya-tsiya a kan tarewan Hauwan

Haka nan ya haƙura ba da son ransa ba aka yi tariyar Hauwan. A lokacin saura sati ɗaya biki

Hauwa da kanta ta zaɓi nata ɗakin aka zuba mata komai nata, duk da ba a canza mata kaya ba amma Anwar ya saka an gyara mata kujeru da abubuwan da suka ɓalle, sai aka canza musu riguna. Ko a haka ma tayi godiya sosai, sai ita kuma ta siya fridge da kuɗin da take samu wurin Anwar ɗin, shi kuma ya saka mata kayan kallo

Har da su Sauda a zuwa kai kayan Hauwa, tare da su aka yi tariyar don su ne kan gaba wajen dafa abinci ita da Ruƙayya

Duk yanda Anwar ya so ya raba su amma ya kasa yana gani Sauda ta zo gidan tana ta hidima, duk da ransa bai so ba amma haka nan ya ƙyale ta da nufin zai ƙara jan ma Hauwa kunne, don bazai juri sakarcin nan ba, tunda Allah ya raba su kowa ya kama gabansa

Ana ta shirye-shiryen biki ta kowanne fanni. Ranan bikin ya fito ranan Juma'a ne, don haka a ranan aka ɗaura auren Muhammadu Anwar da Lubabatu (Afnan)

An yi walima kuma an yi dinner bayan an kawo Amarya

Har da Hauwa sai da ta je tunda har da kujeran ta a wajen dinner. an yi lafiya kuma an gama lafiya

Uwar iyayi Sauda, da su aka hantse domin da ita aka kwana a gidan Anwar ɗin, suna tare da Hauwa tare da ƙanwarta da tsirarun ƴan uwan Hauwa

Haka zalika itama Amarya tana tare da nata tawagar su Munira. Dayake za a kwanar ma Amaryan shiyasa gidan ya cika maƙil

Anwar kuwa sai dai kwana yayi a gidan Muhseen tunda har ɗakin shi an cike da mutane, biki ya yi jama'a, sai mu ce Alhamdulillah tunda an yi an gama, Allah ya bada zaman lafiya.


[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼










            *PAGE:17*

_____A kwana na biyun ne Abokan Anwar suka kai shi ɗakin sa. Daga Hauwa har Afnan ɗin; suka haɗa su suka yi musu nasiha mai ratsa jiki, sannan aka yi barkwanci kafin suka watse suka bar su

Kamar yanda al'ada ta tanadar, haka Anwar ya tafiyar da wannan ranan. Bayan komai ya natsa ya samu keɓe wa da Amaryan sa a cikin wannan daren, kuma ya samu tabbacin cikakkiyar Mace ya samu, wanda hakan ya ƙara mishi armashi da farin cikin gudanar da Angoncin sa cikin kwanciyar hankali

Inda Hauwa kuma a wannan lokacin, tana can cikin ɗakin ta ta kasa runtsa wa ko kaɗan, kowacce Mace tana tsintan kanta a irin wannan mummunan yanayin idan har Mijinta ya keɓe da wata ɗiya Mace, haƙiƙa so ke janyo haka, so ke sa wa kayi kishin Mijinka idan ya kasance da wata, sai dai ba kowacce Mace bace mai iya juriyar halin da ta shiga makamancin wannan, sai Mace mai imani. To zan iya cewa itama Hauwa tana ɗaya daga cikin irin waɗannan Matan masu juriya da tawali'u, haƙiƙa ta miƙa komai nata ga rabbil izzati, wanda shi ya ƙago dukkan wata ƙaddaran ɗan Adam, bata da tsimi ko dabaran da zata iya hana yiwuwar hakan, duk da taso ta jure tayi barcin ta kamar kowacce mai farin ciki take gudanar wa, amma hakan ya gagara, zuciyarta tana cinkushe da baƙin ciki da damuwa gami da zallan kishi, sai dai kasancewar ta Macen da take iya sarrafa zuciyarta, bata bari zuciyarta ta fi ƙarfin ta har ta aikata ba dai-dai ba, wannan daren ta raya shi ne cikin ibadan Allah domin hana zuciyarta ci gaba da zama cikin ƙunci. Har garin Allah ya waye bata runtsa ba ko kaɗan, tana zaune a kan darduma tana lazimi har sai da ta ga kusan ƙarfe bakwai a agogon ta, kana ta mike ta ninke darduman; ta mayar ma'adanar ta, fita tayi ta shiga kichen ta soma haɗa musu breakfast, sai da ta gama tsab sannan ta wuce ɗaki tayi wanka ta shirya cikin riga da zani na atamfa sababbi gau, wanda ɗinkin yana ɗaya daga cikin wanda Anwar yayi mata na fitan kishiya. Ganin yanda fuskarta tayi duk ta kumbura; musamman ma idanunta da suka yi luhu-luhu sun yi jazur, na rashin barcin da bata yi ba, shiyasa ta zauna tayi kwalliya gudun kar a gane halin da take ciki, sai ta ɗan kakkaɓe ɗakin nata ta gyara gadon, sannan ta saka turaren tsinke a ko'ina har falo

Lokacin ƙarfe 09:40am. But har yanzu basu tashi ba, shiyasa tayi zaman ta a falo tana jiran fitowar su

Har goma da rabi basu fito ba, shiyasa ita ta tashi ta je tayi nata breakfast ɗin, before ta koma daki ta kwanta tana faman tunani a ranta

A lokacin ne suka fito a tare sun ci ado iri ɗaya cikin bugaggiyar shadda, sai dariya suke yi da alamu maganar da suke yi ne ya basu dariya

Ganin falon neet, ga kuma coololi a kan ɗan ƙaramin dinning din su, sai yace da ita, "ina zuwa, bari in duba Uwar gida." Sai ya sakar mata hannu ya wuce ɗakin Hauwa. A saman gado ya same ta a kwance

Itama sai shigowar sa ne yasa ta motsa, ganin shine sai ta tashi da sauri tana murmusawa tare da ƙoƙarin gaishe shi cikin girmamawa

Ya amsa ta bayan ya zauna a gefen ta yana cewa, "ashe har kin tashi?"

Murmushi tayi tace, "wlh kuwa, tun ɗazu na tashi har nayi muku abun kari, to na ji shiru ne shiyasa na ci nawa."

Cikin jin dad'i yace, "kin kyauta mana wlh, dama kamar kin san da yunwa na fito." Sai ya ɗan shafa cikinsa before kuma yace, "taso mu je sai ku gaisa da Amaryan, ki taya mu hira."

Bata iya masa musu ba tunda ba ta son ta nuna wani abun na damun ta. Shi yasa ta mike ta biyo bayansa suka fita a tare

Lokacin Afnan na zaune a saman sofa ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai ta ga fitowar su, ta bi su da idanu har suka ƙariso

Hauwa ta soma mata magana cike da fara'an ta tace, "Amaryan mu, an tashi lafiya?"

"Lafiya lau Aunty." Afnan ta amsa tana yafa wa fuskarta murmushin a sa'ilin

"To kinga Aunty Hauwa har tayi mana break ashe, gwara mu tashi mu ci kar yayi sanyi."

Yanda yayi maganar yasa su dariya

"Ke ma mu je sai ki zauna ki taya mu hira, hakan zai fi, amma ban yarda ki sake yin wani break babu mu ba, gaba ɗaya zamu riƙa yi."

"Insha Allah." Cewar Hauwan tana murmushin ta

Dukka suka wuce kan dinning din suka zauna suka karya. Ita dai Hauwa bata sake cin komai ba tunda ta ƙoshi, duk da yayi mata tayin ta sake ci, but ta ƙi. Shi yasa bayan sun gama suka dawo falo suka zauna, ya haɗa su gaba ɗaya yayi musu nasiha mai ratsa zuciya, ya kuma ba wa kowacce matsayin ta a gidan, sannan ya faɗa abubuwan da ba ya so da wanda zasu kiyaye mishi, kuma ya basu damar su ma su faɗa abun da ke ransu

Dukkan su ba wacce tayi magana a cikin su, kowa tace, "babu komai."

Shi yasa ya ƙyale su kawai ya ci gaba da jan su da hira cikin barkwanci don ya ga dukkan su suna walwala. Bai bar wurin ba sai da ya ji baƙi ƴan ganin Amarya sun soma ƙoƙarin shigowa, sai ya shiga ɗakin sa ya rufe ƙofa

Itama Hauwa tunda ta gaisa da baƙin, da alamu ƴan uwan Afnan ne na jini, shiyasa bayan sun gaisa sai ta basu wuri ta koma nata ɗakin itama.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


         "Intisar, wai meyasa kike min haka ne? Magana ba ta wucewa a wurin ki ne? Ni na gaji fa da irin wannan abubuwan da kike min."

Intisar da ke zaune a saman sofa ta harɗe ƙafafu, ta ci kwalliya ta cakare cikin ƙananun kaya tsukakku, sai taunan chewing gum take yi tana latsa wayanta, duk maganar da Shureim yake yi bata ɗago ta kalle sa ba bare ya sa ran zata tanka shi, saboda tun abun nan da aka yi ta fita harkan sa, har ya gaji ya bata hakuri amma ta ƙi kula sa, mugun fushi tayi masa sabida Momyn ta tace, "muddin bai amince ya barta ta koma makaranta ba, kar ta ƙara sakin masa fuska, kuma kar ta ƙara yarda dashi." Shi yasa take gwada hakan tunda har yanzu bata ji ya sake mata magana ba, ta tabbata idan ya gaji dole da maganar zai tunkare ta tunda ya san me ya sauya ta

Shureim da ya dawo daga bakin aiki, gaba ɗaya gajiya da buƙatar Matarsa ce ta dawo dashi, ya kasa jure wa shiyasa ya dawo don a buƙace yake, amma kuma ya zo ya zauna yana mata magana ta ƙi kula sa kamar kullum yanda ta saba, shima kwata-kwata ba ya son yana nuna mata ɓacin ransa bare ya amshi haƙƙin sa da ƙarfi, ya fi son ya lallaɓa ta tunda ya san muhimmancin soyayya ga ma'aurata. Dayake yana kan kujerar da ke kallon nata ne, sai ya miƙe ya dawo kusa da ita yana leƙa wayan hannunta, Game kawai take yi a ciki, shiyasa ya ɗan ja numfashi yana sauke tagwayen ajiyan zuciya akai-akai, tare da sanya hannu ya zame wayan yana faman kallonta

Ɗago ido tayi itama ta zuba mishi, ganin sun haɗa ido sai ta haɗe rai tana mai kumbura fuskar nata, cike da hassala ta miƙa masa hannu tace, "bani wayata Malam."

"Ban bayarwa." Ya furta yana sake sakin nimfarfashi

Cike da tsiwa ta kalle sa ido cikin ido tace, "wlh idan baka bani ba zaka ga abun da zan maka, tunda ba kai ka siyan min ba ka bani wayata nace."

"Ni kike faɗa ma haka Intisar? kuma har da gori za ki yi min? Amma ai na siyan miki abun da ya fi wannan ko?"

Dogon tsaki ta ja tana shirin mike wa, sai ya kamo ta ya zaunar da ita a jikinsa tare da ajiye wayan, ya kama ta sosai kasancewar tana kokarin ƙwace wa, "haba ƴan matana, wai me nayi miki ne? Meyasa kike da riƙo haka? Tun yaushe komai ya wuce but kin kasa sakin jiki dani, Ni fa Mijin ki ne kuma kin san illar gaba da Miji, haba babyna don Allah ki yafe min mu koma kamar da. I swear I will give you everything you want in har za ki sauko."

Tura baki ta soma yi tana mutsu-mutsun ƙwace wa, tare da furta, "Ni fa don Allah ka sake Ni Malam, ai wlh bazan sake yarda da kai ba, tunda har Ni zaka iya cire hannu ka mare Ni." Sai ga hawaye a kwarmin idon ta tana ci gaba da faɗin, "duk soyayyar da kake nuna min ashe a banza, akwai ranan da zaka iya duka na Shureim, to me ya rage? Wlh gwara ka sauwaƙe min in koma gidan mu tunda..."

Saurin rufe mata bakinta yayi da nasa bakin, haka ya manne ta sosai a jikinsa ta yanda baza ta iya ƙwace wa ba

Ai kuwa duk yanda ta so ta tirje mishi ta kasa, sai da ya gaji don kansa sannan ya zare bakin nasa yana kallonta

"Ba na son kina tuna wannan mana babyna, nayi miki alƙawari bazan sake dukan ki ba, wannan ma kuskure ne don Allah ki yi hakuri, i need you ki taimaka min, kinga ina son mu ji dad'i tare ba na son in sake cutar da ke."

"Ni bazan yarda ba wlh, tunda kaima ba ka son abun da nake so, nima bazan amince ba."

Shiru yayi saboda a ɗan zaman nan nasu, ya gane Intisar akwai taurin kai, har da kuma rashin tarbiyya da sangarta da suka samu. sai kuma ya ɗauke ta zuwa ɗakin sa yana cewa, "to mu je in nuna miki wani abu da na kawo miki kyauta, mu je sai ki faɗa min abun da kike so, na yarda zan miki ko mene ne."

Jin haka yasa ta dena ƙoƙarin ƙwace wa, shiyasa ta yarda suka shiga ɗakin tunda a ganin ta zai amince da komawar ta makaranta since ya faɗa haka.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


         "Wai kin yi sallah kuwa da kika zauna kika tasa littafi a gaba?" Cewar Mama da ta fito daga ɗaki ta tarar da Hafsah zaune a bakin ƙofa tana duba littafi

Ɗago kai tayi tana duban Maman tare da cewa, "nayi mana Inna."

"To ki je ki ci Abinci hakan zai fi miki tunda baza ki zauna haka nan ba, kin dawo kuma kin ƙufe a kan littafi; ai karatun ma sai ya ƙi shiga."

Kamar zata yi kuka Hafsan tace, "wlh kuwa kamar kin sani Inna, Allah gaba ɗaya ba na gane Maths ɗin nan, kuma ga shi gobe shi zamu yi jarabawa a kai, har pepper biyu ma, shiyasa duk na ruɗe."

"To maza ki je ki ci abincin sai ki zauna ki ci gaba, Allah ya bada Sa'a, ai Insha Allah za ki haye komai zai zo miki da sauƙi."

"To Allah yasa Innata." Sai kuma tace, "amma Inna da zaran mun yi jarabawar nan; zan je hutu ƙauye ko?"

Kafin Inna ta bata amsa sai ga Jibril ya zo wurin, babu ko gaisuwa yace, "ke ki je Momy na kiran ki." Daga haka ya juya ya tafi wayansa a hannu yana sana'ar da ya saba, wato Game

"Innalillahi... Na shiga uku Ni kam, wlh Inna in na je baza ta bar Ni in dawo yanzu ba, kuma kinga bani da lokacin karatun nan in har ban yi yanzu ba, ga shi ban yi sallah ba."

Da damuwa Mama itama tace, "to ya za ki yi? Kin san halin Jarabar matar nan, amma tashi ki je ki yi sallah tunda shi ne ya zama wajibin ki, inyaso zuwa dare sai ki yi karatun kin ji ko? Ki dena damuwa haka."

Miƙewa Hafsan tayi tana gyaɗa mata kai don ta kasa ma magana, ta shiga ɗakin ta ajiye littafin don tayi alwala.
***




        "Ina yarinyar? ka kira ta ne?" Cewar Fauziyya da ke ƙoƙarin gyara ɗankwalin ta, ta cakare cikin shigan ta na Swiss less

Tura baki Jibril yayi yana zama a gefen Sumayya, tare da cewa, "na kira ta."

"Ok." Ta furta tana yin gaba zuwa nata ɗakin. Bata jima ba ta fito riƙe da waya tana miƙa wa Sumayya tace, "kira min Ummun Muhseen."

Amsar wayan tayi ta kira mata, tana mayar mata da wayan da cewa, "wai Momy to sai yaushe zaku dawo? Kinga yamma ta fara yi fa?"

Bata bata amsa ba, ta kara wayan a kunne saboda an amsa wayan, "Hello. Wai kina ina ne har yanzu ba ki ƙariso ba? Kina ganin har na shirya but kin gagara zuwa?" Sai tayi shiru tana sauraron ta, daga baya kuma tace, "ok sai kin zo." Ta kashe wayan

"Momy Ni fa wlh yunwa nake ji, zan mutu." Jibril ya furta yana shura ƙafa

"Ni fa Jibril bani da lokacin sauraron ku, ka jira yarinyar nan ta zo ta yi muku girkin." Sai kuma cike da ɓacin rai tace, "Sumayya je ki kira min ƴar iskan yarinyar nan, idan bata zo ba na biyo ta wlh jikinta zai yi tsami a gidan nan."
    


Tsaki ta ja Sumayyan tana faman zumɓura baki tare da ƙunƙunai ta tashi. Sashin Mama ta nufa ta shige dakin ko sallama, a nan ta tarar da Hafsah tana sallan bata idar ba, sai tace, "ke Jaka ƴar ƙauye, Momy na kiran ki shine don munafurci za ki kama alayen sallah? To wlh muddin ba ki katse shi kin taho kiran ta ba sai kin ci kutmar uban ki."


Mama da ta ji hayaniyar Sumayyar daga uwar ɗaka, sai ta fito tana cewa, "ah ah, Sumayya, ba ki ga sallah take yi ba? Kuyi haƙuri yanzu zata zo."



"Babu wani sallah munafurci ne dai, don an kira ta shine zata fara sallah saboda ta raina Momyn wato?" Sai ta ja ƙwafa tana cewa, "ki jira za ki gani." Ta juya ta fice da sauri.
Tana isa part ɗin su ta sanar da Fauziyya cewan, "Hafsah bata da ninyar zuwa, don wulaƙanci da munafurci irin nasu sallah ma take yi don kar ta zo, da alamu ma Mama take zuga ta shiyasa ita ta ɗaure mata gindi."


Tashi Fauziyya tayi ta fita ranta a ɓace, tana zuwa suka haɗu da Hafsan a hanya, bata yi wata-wata ba ta tsinka mata mari tana cewa, "ke dan uban ki har kin kai matsayin da zan kira ki; ki ƙi zuwa a gidan nan? Wane ne uban ki a garin nan da har in ce a kira ki but sabida ban isa ba baza ki taho sanda nake so ba? Shegiya ƴar ƙauye ballagaza."



"Haba Fauziyya, me yarinyar nan tayi miki da kike cin mata mutunci haka? Kuma tunda kika kira ta ai kin san zata zo baza ta ƙi kiran ki ba." Cewar Mama da ta fito sabida jin kukan Hafsan


Cikin rashin mutunci irin na Fauziyyan tace, "taya ya na kira ta almost 10 minutes but a ce ta ƙi zuwa? In Uwarta ce zata ƙara minti ɗaya bata zo bane? Muna ciyar da ita mu shayar da ita amma tsaban iskanci irin na baƙauye sai ya nuna jahilcin sa, to Ni bazan saurara mata ba don ba na ɗaukar raini, dalla tashi mu je ko in tattaka ki a wurin nan, stupid Nonsense, common Get up and let's go." Ta daka ma Hafsan tsawa, wacce ke durƙushe a ƙasa tana kuka kashirɓan sabida gigitan marin da tayi mata



Ran Mama ya ɓaci sosai, amma ta kasa magana tunda bata cika magana a kan abubuwan da Fauziyya take yi ko ƴaƴan ta ba, amma yau sosai ranta ya sosu tunda ba ta son ko kusa wani abu ya taɓa Hafsah. Hafsah amana ce a wurin ta baza ta zuba ido ana mata irin wannan wulaƙancin ba tamkar bata da gata, lokaci yayi da zata taka wa Fauziyya birki a kan duk abubuwan da take yi, ta soma gajiya, a ce kamar ita tana matsayin Mahaifiyar Mijinta amma bata da ƙima da mutunci a idanunta, bare kan Jikokin ta, to har yaushe zata samu

Please Login or Register in order to submit comment