Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da lafiya har kala biyu ta jera musu a ƙaramin dainning ɗin su, kana kuma tayi musu zoɓo me daɗi tare da sauran drinks na kwalba dana Robber duk aka tanadar musu. Ta rigada ta gama komi a lokacin da suka iso, shiyasa suka yi musu tarba suka sauke su a falon nasu, su ma sun sha kwalliya sun yi ankon maroon color ɗin shadda uban-uban su iri ɗaya, yayinda Munira ta cakare ɗauri ta sha kwalliya kowa ya kalle ta ya san Amarya ce don sai tashin ƙamshi take yi tana walwali irin na Amare, ga lallin da ta sha hannu da ƙafa gunun sha'awa sun sake fito da ita.

Bayan sun zauna sun gaisa ne Munira Sarkin tsokana tace, "yau ranan taku ce masoya, babu wanda ya kai ku haɗuwa da dacewa wlh, kun matuƙar dacewa da juna, fatan mu Allah ya nuna mana bikin ku muna da rai da Lafiya."

Afnan wacce take shan drinks a kofi; hararan ta tayi sai dai bata ce komi ba illa kurɓan drinks ɗin da take yi

Munira ta sake cewa, "bar harara na addu'a ce nayi muku me kyau don na san shi ne a zuciyar ku, ba ma kamar ke Afnan, ko ba haka ba Husband?" Ta ƙare maganar da kallon Muhseen wanda suke dariya kaɗai

"Haka ne My wife, ai gaskiya kika faɗa idan kuma sun musa su ƙaryata."

Anwar murmushi yayi da cewa, "kun dai haɗe mana kai ne saboda mun zo gidan ku, kodayake ba ƙarya ku ka yi ba, amma kuma duk soyayyar mu ai bamu kai ku ba domin kuwa a bayan ku muke."

"To ai mu mun rigada mun shiga daga ciki mun wuce zancen nan." Cewar Munira tana dariya, sai kuma tace, "Ni dai fata na kar a yaudarar min ƙawata don na san halin ku Mazan nan kaɗan ne daga aikin ku, kar taje kuma ta saki baki tana jiran ka daga baya ka nuna mata halin ku na Maza don Allah."

"Ohh! Wato kina so ki nuna cewa Maza su ne mayaudara ko Wifey?" Inji Muhseen yana mata wani kallo irin tasu na soyayya

Dariya duk suka yi. inda Anwar yace, "yo ka ji zance, ashe kai ma kasan halin Matan nan; son ɗaurawa Maza laifi kamar a kansu aka ƙirƙiro gaskiya."

"Maganar gaskiya ƙawata gaskiya ta faɗa, ai halin ku kenan." Inji Afnan wacce sai yanzu tayi magana, idanunta a kan Anwar ɗin tana ɗan tura baki

Yayinda ya sakar mata wani kallo ba tare da yace komi ba yana yalwata fuskarsa da murmushi

Duk a idanunsu Munira, su ma sai suka yi murmushin kaɗai suna ɗauke kan su

Inda Munira tace, "wlh ba haka bane, Ni abinda yasa na faɗa haka saboda halin ku ne Maza, bare irin ku masu Mata a gida, sai kuyi ta yiwa ƴan mata daɗin baki kuna hana ta tsayawa da samarin ta, daga ƙarshe kuma ku ƙi auren su ku gudu ku bar su, Ni dai gaskiya a riƙe mana alƙawari ato."

"Wato dai kan mu kike so ki ƙare ko Wifey? Na gano ki wlh zamu haɗu ne?" Muhseen yafaɗa yana tashi tsaye da ballara mata harara, sai kuma yace, "idan ku ka biye ta nata baza ku ci abincin ba, ku tashi mu je mu ci abinci hiran ta isa haka."

"Husband ko dai ba ka so a tono halin ku ba, ai nima na gano ka." Tafaɗa tana dariya. Sai dai yanda ya cillo mata kallo ne yasa ta tashi da gudu tayi hanyar ɗaki

Shi kuma hakan yasa ya shafa ƙeya yana kallon Anwar da cewa, "ina zuwa bari in ɗauko phone ɗina a ɗaki." Sai kuma ya juya be jira cewar su ba yana kwaɗa wa Muniran kira da cewa, "wai baza ki fito ki basu abincin ba me ya kai ki ɗaki kuma? Wifey."

Dariya duk suka fashe da shi Anwar da Afnan

"Ai gidan ba baƙon mu bane zamu yi saving da kan mu." Cewar Afnan tana dariya ta tashi

Kan dainning ɗin suka wuce inda tayi saving ɗin su sannan suka zauna zaman ci

Anwar wanda ke tsakalar abincin yana aika mata da wani irin kallon soyayya yace, "mu ma wata rana haka zamu riƙa yi a gidan mu Baby na, baki ji yanda nake ji ba a zuciyata tamkar ace wannan gidan namu ne sannan kuma mu ne a ciki a matsayin waɗanda suka mallaki juna, uhmmm." Sai yayi shiru yana jan numfashi tare da lumshe idanunsa ya kuma buɗe wa a kanta

Ita kuwa tuni ta sauke kanta ƙasa tana faman doka murmushi, duk kunya ta cika ta don ta kasa kai abincin bakin ta ko sau ɗaya

"Baby ba ki ce komai ba?"

Ɗago kai tayi ta zuba masa kallo me shiga rai tare da kwarkwasa tace, "to me zance dear?"

"Uhmm shiyasa kike burge Ni idan kina min irin wannan yangan, Allah zan faɗa miki gaskiya Baby Ina shiga wani hali duk sa'ilin da aka ce muna tare da juna, ina fama da begen ki tare da tarin ƙaunar ki a zuciya, fata na Allah ya mallaka mana junan mu, Allah ya hore min domin in mallake ki a cikin gida na a kuma ɗaki na."

"Amin Dear." Tafaɗa kanta a ƙasa tana murmushi

Kallon ta kawai yake yi ya kasa cin abincin, sai kuma can ya ɗan leƙa kansa yana son ganin fuskarta

Hakan yasa ta ɗago kai tana kallon shi still tana murmushi

Haɗa idon da suka yi ne yasa suka sakar wa juna murmushi. Sun kasa ɗauke kai daga kallon junan su yayinda suke aika wa junan su saƙon da ba kowa yake iya gane wa ba sai su kansu masoya... Fitowar su Muhseen a tare ne suna dariya da junan su yasa suka kau da kai daga kallon da suke yi

Inda ita Afnan tuni ta mayar da kanta ƙasa ta ci gaba da tsakalar abincin da ke gaban ta

While Anwar kallon su yayi da cewa, "kun gama shanya mu ɗin kun fito? Haka ake yi ne wai muna baƙi ku bar mu babu wani tarba me kyau?"

Muhseen wanda ya jawa Munira ɗaya daga cikin kujeran dainning ɗin ta zauna shima ya ja nashi ya zauna, sai yace, "ai ku ba baƙi bane gidan ku ne, don mun shiga ciki hakan bazai hana kuyi saving ɗin kanku ba, to wai yaushe muka shiga ne idan ba yanzu ba? Ban fa son gulma abunda ban maka ba Ni kace zaka yi min?"

Dariya suka yi

Inda shi Anwar ɗin yace, "maida wuƙan don Allah ayi haƙuri shikenan, idan ma ƙaharu kake min ai akwai ranan rama wa, mu ma zamu rama ne ko Baby na?" Ya ƙare maganar da kallon Afnan yana mata murmushi

Kanta kawai ta ɗaga yayinda take mayar masa da martanin murmushin

Su kuwa Muhseen da Munira dariya suka kwashe da shi suna tafawa, sai kuma suka haɗa goshin su waje ɗaya suna sake tuntsurewa da dariya

"Kai Waɗannan magulmata ne akwai abin da ke ransu wlh." Inji Anwar Wanda suke bin su da kallo fuskar su dauke da mamakin su

Su dai su Muhseen dariya kawai suke tuntsurawa

Duk yanda Anwar yaso suyi musu bayanin abin da yasa suke dariyan sun ƙi. Daga ƙarshe haka suka ci gaba da hiran nasu cike da nishaɗi suna ta tsokanar juna, bini-bini kaɗan sai su Munira su tashi su shige ɗaki can kuma sai su dawo

Anwar yace, "daɗin abun ma nima akwai baby na a gefe bare ku bani haushi." Shiyasa suna tashi su kuma sai su samu sakewa suyi ta hiran soyayyar su.


A ranan a gidan suka wuni har goshin magriba kafin suka yi musu sallama suka tafi. Sai da Anwar ya raka Afnan har gida kafin ya hayo Machine ya wuce gida shima.






✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

"Wai ban gane me kake nufi bane Jamal? Idan har ka hana yarinyar nan aiki a gidan nan to waye zai ci gaba da yi ne wai? Har yanzu na kasa fahimtar me kake nufi da Ni? Bazai yiwu in riƙe yarinyar da ba tawa ba tazo tana cin arzikin mu sannan ita bazan more ta ba, to na gaji bazai yiwu ba..."

Katse ta yayi saboda jin maganganun nata ya soma cika masa kunne, cike da fushi irin nasa wanda ba kasafai ne yake nuna wa ba sai idan an kai shi maƙura, ya kalle ta yace, "ke Fauziyya kin fa takura min, kina da hankali kuwa? Ni za ki kalla kina gaya min me nake nufi ko ke ce zan tambayi me kike nufi? To Bari kiji duk abin da ke zuciyar ki na sani kuma na san me kike nufi, na kula tunda Mahaifiyata tazo gidan nan kika sauya gaba ɗaya, ita Hafsan rorota nayi ko me? Ina ce Uwata ce da kuma ɗiyar ƙanwata na kawo su gidan nan? Amma duk kin bi kin tayar da hankalin ki saboda ba kya son zaman su a gidan, kar ki manta ita Uwata ce ba ki isa ki ce za ki yi min katsalandan a gidana ba, sannan zancen girki na ce miki Hafsah baza ta sake miki bauta a gidan nan ba, daga yau babu ke babu saka ta aiki, idan kuma kin ce a'a ki ci gaba da abin da kike ninyar yi kar ki fasa, wlh zan mummunar ɓata miki a gidan nan muddin ba ki shiga taitayin ki ba." Sai ya ja dogon tsaki yana sake faɗin, "zancen banza zancen hofi, abun naki ma naga yana son wuce gona da iri ne." Ya wuce ya buga ƙofan Toilet cike da fushi ya shige

Ita kanta ta shiga taitayin ta sabida ganin tsananin fushin da ya ɗauka, shiyasa bata sake furta komi ba itama ta fice a ɗakin nasa cike da fushi ta wuce nata ɗakin

Yana fito wa daga Toilet ɗin wanda dama alwala ya shiga yi, Parlour ya wuce ya dinga kwaɗa wa Sumayya kira

Da gudu ta fito daga ɗaki tana cewa, "gani Dady."

"Ina Intisar ɗin?" Yafaɗa fuskarsa babu walwala

"Tana ɗaki..." sai kuma maganar nata ta ƙaƙare ta kasa ƙarisawa

"Kira min ita." Yace da ita yana tsayen

Da sauri ta shiga ɗakin inda ta tarar da ita tana waya ta kira ta

A lokacin shima Jibril ya fito daga nasa ɗakin ya zo ya zauna

"Kuna ji na? daga yau duk wacce na sake kama wa a gidan nan bata je ta gaida Mama ba wlh sai nayi mugun saɓa mata, duk ranan duniya ku riƙa zuwa gaishe ta tunda ku baku san abin da yakamata ba, kuna biye wa uwar ku tana ɗaura ku a tirban banza, sai na saɓa wa ko wacce dayan ku wlh ku jini da kyau, sannan duk wacce ta sake saka Hafsah aiki a gidan nan sai na farfasa mata jiki, daga yau idan uwar taku baza ta girka muku ba ku ku shiga kichen ɗin ku girka da kanku kun ji ko?" Ya ƙare maganar da ɗaga muryan sa

Jikin su na rawa suka amsa mishi sabida duk sun tsorata da faɗan nashi

Ya sake kallon Intisar da cewa, "barin ma ke don naga kanki yana hayaki yanzu, ki bari ki shiga hanci na a ranar da zan faco ki Intisar za ki sha mamaki na. Dalla ku ɓace min a nan."

Da gudu suka tashi jiki na ɓari suka yi hanyar ɗakin su; har Jibril

"Kai zo ka wuce ko baka ji ana sallah bane?" Yafaɗa da dakawa Jibril ɗin tsawa

Take a nan ya dawo ya bi hanyar ƙofa zai fice saboda ruɗewa

"Ka yi alwala ne?"

"A'a."

"To wuce ka je kayi."

Tsayawa yayi har sai da ya fito kafin ya tasa shi suka fice.

Fauziyya duk tana jin hayaniyar nasa but ko motsi ta ƙi yi bare ta fito, tana kwance a saman gadon ta sai kaɗa ƙafafu take yi cike da fushi. Ita har ga Allah ta gaji baza ta iya ba, bazai yiwu ta zauna yana mata abun da ya ga dama ba, dole ne sai ta ɗauki mataki, ba haƙuri take yi ba ma da zaman ta da uwar Mijin? Amma shi duk be gani kullum laifin ta yake gani, bazai yiwu ya riƙa juyata kamar waina ba, baza ta zauna tayi masa bauta sannan ta yiwa uwar sa da dangin sa ba, ita kawai duk abin da zai faru baza ta bar Maman shi ta zauna ba, zaman ta ne a gidan ba ta so dole ya tarkata ya bar gidan da su. Tana ji ana kiran sallah but tsaban rigima ya ci ranta ko tashi ta kasa yi, sai da taji wasu masallatan sun tayar da Sallah kafin ta miƙe ta faɗa Toilet, tana yin alwala ta fito ta saka hijab ta gabatar da sallan, bayan ta idar ko ishashshen azkar bata yi ba ta wuce falo. Babu kowa sai ta zauna a kan sofa tana faman karkaɗa ƙafafu. Intisar ta soma kira kafin kuma ta haɗa da Sumayyan tana kwaɗa musu kira. Suna fito wa ta kalle su da cewa, "tun wuri ku nemi abinda zaku ci don bazan yi girki ba, kar kuma anjima tayi ku dame ni da yunwa kuke ji, idan wancan yarinyar baza ta girka ba wlh nima bazan girka ba sai dai kowa ya kwana da yunwa."

Intisar tace, "haba Momy ke ma kin san bamu wani iya girki ba, ya za'a yi muyi bayan bazai ciwu ba koda mun girka?"

"To ki zauna uban ki ya zo ya girka miki kinji ko? Yau yanda raina ke ɓace wlh babu wanda zai saka Ni abun da ban yi ninya ba."

"Yau dai duk kun sauke fushin ku a kanmu, Allah ya baku haƙuri." Inji Sumayya tana wuce wa hanyar kichen ta shige

Ita kuma Intisar tashi tayi tana tura baki, dayake wayanta ne a gaban ta tuni ta mayar da hankalin ta a kai ta ci gaba da chatting ɗinta ta wuce ɗaki


Tsaki taja ita kuma ta ci gaba da zama a wajen. Tana nan har aka kira sallan isha'i aka idar su Jamal suka shigo gidan

Koda suka shigo shi ɗakin sa ya wuce don ko bi ta kanta be yi ba

"Aikin banza harara a duhu, kayi ka gama da Ni kake zancen wlh, yanzu muka soma idan har baza kabi abinda nake so ba." Tafaɗa tana raka sa da harara wanda shi tuni ya shige ma be san tana yi ba

Jibril zama yayi kusa da ita yana shigewa jikin ta tare da faɗin, "Momy kinga Dady sai da ya mangare Ni a masallaci wai ban iya Sallah ba har yanzu, kuma Momy yunwa nake ji."

Sai da ta kalle sa kafin ta kawar da kai da faɗin, "kaga Jibril nima ta kaina nake yi ka tashi min nan kar in zane ka."

"To Momy yunwa." Yafaɗa yana soma dirza ƙafa a ƙasa alamun shagwaɓa

"Ka wuce ka je idan su Sumayya sun girka su baka, Ni yau babu me saka Ni girki a gidan nan, bazan zauna kullum ina wahala babu me gani bare godiya ba, yau idan ina da rana za'a ga amfani na."

"To Momy kin san fa basu iya abinci me daɗi ba, Ni dai ki tashi ki girka min indomie."

Tsawa ta daka masa da cewa, "uban ka da kai da indomien, zaka tashi min a jiki ko sai na faffalle ka da mari?"

Kuka ya saka mata yana janye jikin sa tare da kwanciya a tsakiyar wurin, sai birgima yake yi. Da ya ga ta yo kanshi sai ya tashi a guje ya wuce yana sake fashe wa da wani sabon kukan.




Jamal wanda ya shige ɗaki wanka yayi ya fito. Ya saka jallabiya tare da gajeren wando ya fita Parlour. Babu kowa a time ɗin, tunda ya kalli kan dainning ya ga babu coololi sai yayi ficewar sa zuwa Part ɗin su Mama zuciyarsa na tafarfasa, dole ne ya ɗau tsatstsauran mataki a kan ta, bazai yiwu ta riƙa juya sa a gidan nan ba, abin da yake so shi za'a yi, ya kula bata da kirki ko kaɗan, be gane hakan ba sai da ya kawo Mahaifiyarsa gidan, nufin ta kenan ba ta son zaman ta a gidan? Ai kuwa bazai lamunta ba duk wani iskanci da ke kanta zai sauke mata, ta ga yana ƙyale ta ne shiyasa take son fin ƙarfin sa, amma yanzu ya dawo daga rakiyar ta.
[14/09, 9:30 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*










*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*PAGE:9*

_____Washe gari tun ƙarfe goma har Sauda ta gama shirin ta. A lokacin ko Anwar be bar gidan ba duk ta ishi Hauwa da nacin, "ita fa ta gama shirin ta ita kaɗai take jira."

Anwar wanda ke zaune sa'ilin da Saudan ta bar bakin ƙofan ya kalli Hauwa yace, "wai da wannan Matar zaku je gidan Amaryan?"

"Eh, ita tace zata bi Ni mu je tare."

Tsaki ya ja yana miƙe wa da faɗin, "gaskiya matar nan tana takura min, ko kaɗan ba na son hulɗar ki da ita, Ni fa kwata-kwata ba na son kuna alaƙa ta koya miki halin nan nata, yanzu idan kun fita tare ta je ta janyo rigima ƙarshe har da ke a ciki, tunda kowa zai kalle ku tare ne."

Hauwa wacce take bin shi da kallo, murmushi kaɗai tayi da cewa, "to ya na iya? tunda zaman tare ta haɗa mu sai haƙuri."

"Babu wani zancen sai haƙuri, ke ya kamata ki riƙa janye jikin ki a tattare da ita, matar nan bata da hankali wlh." Sai ya kuma jan tsaki yana ɗaukar hulan sa tare da faɗin, "Ni kinga tafiya na, ki duba rigan can da na cire za ki ga kuɗi na ajiye miki." Daga haka ya fice bayan ya shura takalman sa ya saka ya bar gidan. Tana masa a dawo lafiya ma Ko bi ta kanta be yi ba

Numfashi ta ja cike da rashin jin daɗi, duk da ba yau ya saba da halin Sauda ba amma ita bata ga abun ɗaukar zafi ba, Sauda fitinanniya ce ba kowa yake iya zama da ita ba, sai dai kasancewar ita me haƙuri ne da kau da kai ba ta bari ma wani abu yana shiga a tsakanin su, don dai mutunci Sauda tana dashi matsalan ta kawai rigima da yawan fitina da mutane, ita kuma a yanzu har sun saba ma sabida tsawon shekarun da suka ɗauka, ga shi yanzu kusan shekaru uku kenan suna a tare babu abun da ke haɗa su tunda ta rigada ta laƙanci halin ta... Shigowar Saudan a wannan karo na uku kenan hakan yasa Hauwan tashi tana bata amsar maganar nata da cewa, "to kin dai koran min Miji kinji daɗi Sauda, gani nan yanzu zan yi wanka sai mu tafi, amma fa dole za ki jira in sauke dafen farar shinkafar can tunda bazan bar Mijina da yunwa ba, na san anjima zai dawo kuma ba na nan, tunda ina da miya na dole zan mishi kafin in fita."

Shewa Saudan ta saki tana sake hankaɗa labulen da cewa, "to Hauwa me Miji ai ba sai kin faɗa min kina da Miji ba, daɗin abun nima fa ina da shi bare ki ce za ki yi min gori, tun ɗazu me ya hana shi fita bayan ga shi har rana ta take ai ba haka yake yi ba? sai yau da zamu je anguwa ne zai wani maƙale a ɗaki, ba ga shi tun ɗazu Bilal ya fice ba shi yana zaune ya dirke a ɗaka. Ni wlh ba na son rana ne tayi bamu tafi ba, na fi son a gan mu da sassafe a san da zuwar mu."

Murmushi Hauwa tayi sabida halin Saudan, shiyasa bata ce mata komai ba ta wuce ta ta fice a ɗakin

Take mata baya tayi da faɗin, "kinga bari in duba miki shinkafar kafin ki fito daga bayin." Ta wuce kanta tsaye wajen murhun inda Hauwa ta ɗaura girkin nata.





A taƙaice ba su suka bar gidan ba sai da ɗaya saura tayi. Suna zuwa gidan su Hauwan sallah suka soma gabatar wa Bayan sun gaisa da Hajiyar ta

Mahaifiyarta Mace me fara'a da son mutane. Su huɗu ne Allah ya bata yaran, daga babban yayan su sai Hauwan sai kuma ƙannin ta biyu Mata, ɗaya tayi aure har da yaron ta ɗaya; tunda shekara ɗaya kenan da auren nata, sai kuma autar nasu wacce a yanzu bata fi shekaru 15 ba a duniya. Kasancewar babban yayan nasu shi ne me rufin asiri a gidan Don haka shi ke riƙe su sakamakon mahaifin su ya jima da rasuwa, kuma shi ne ya yiwa su Hauwa aure sannan shi ke basu jari tunda duk a mazajen nasu babu me shi, gwara-gwara ma na Mijin ƙanwar Hauwan be kai rashi da babun Anwar ba, amma a haka suke haƙuri tunda sun kasance masu tarbiyya ƴan gidan su, kuma sun biyo Mahaifiyar su sosai a haƙuri. Ita Hajiyar tasu ita ke taimakon su a kodayaushe tunda itama tana sana'a, idan bata dashi kuma sai ta saka Babban yayan su yayi musu, shiyasa sau dubu aka bai wa Hauwa jari idan ta cinye a laluran gida Hajiyar ba ta gajiya wajen ta ga ta sake bata wani, ta kance, "Hauwa duk idan kin cinye ki zo gida ki amsa tunda mu Allah ya buɗa mana, idan ma bani da shi sai in saka Yayan ku ya ba ki, amma ku dena zama a babu don Allah." Wannan shi ne zancen Hajiyar su a kodayaushe, tana tsananin tausayin Hauwa tunda ita ce kullum a wahale. Har yanzu suna nan a hakan su babu ci gaba tun auren su, don ma Allah be basu haihuwa ba da tuni abun ya sake musu yawa

Duk da a yanzu Anwar ɗin yana saka ran samun aiki a wajen aikin su Muhseen, dayake tunda Muhseen ɗin ya samu aiki shima ya amsa takardun shi ya kai Companin su domin a ɗauke shi, to sun amsa takardun amma har yanzu shiru kake ji basu ce musu komi ba, basu da tabbacin zai samu ko bazai samu ba amma dai suna saka rai.





Daga gidan su Hauwan bayan sun yi sallan, basu wani jima ba suka wuce gidan Munira

Tayi murna da ganin su kuma tayi musu tarba me kyau kasancewar ta me son jama'a me faram-faram da iya daɗin zama

Hakan yasa su ma suka saki jikin su sosai

Har Sauda tana cewa, "ai kam mun ga wajen zuwa wlh, ai inda aka amshe ka hannu bibbiyu aka mutunta ka nan ne wajen zuwa. Kinga Mijin ki da Mijin Hauwa Abokai ne, sannan Mijina da Mijin Hauwa su ma Abokai ne, gamu mu kuma ƙawaye, kinga mu ma mun zama ɗaya gaba ɗayan mu kenan."

Dariya kaɗai Munira tayi bata ce komai ba domin babu abun da take tuna wa illa ranar da Hauwa zata gane ƙawarta tana soyayya da Mijin ta, sai kawai ta ji sam babu daɗi sabida yanda ta ga Hauwan me tsananin kirki, ita bata ga abun da yasa Anwar zai je yayi soyayya da wata har ya ƙaro aure ba, duk abun da namiji yake nema a wajen Mace Hauwa tana da shi kuma ta kai a zauna da ita ita kaɗai, amma kuma idan ta tuna Maza

Please Login or Register in order to submit comment