Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta, "meyasa ta sauya tun sanda ya dawo da su Mama gidan nan?..."

"Dady gani". Cewar Sumayya da ta shigo ɗakin a yanzu ɗin

Sai da ya kalle ta kafin ya sauke ajiyan zuciya yace, "ɗauki kayan nan ki kai wa Mama ta ajiye wa Hafsah na makarantan ta ne, idan gobe ta dawo zuwa jibi zaku soma zuwa school tare".

"To". Tace dashi tana ɗaukan ledan ta fice

Shi kuma ya gyara kwanciyar sa yana ci gaba da tunanin da ya bijiro mishi a kan Matar shi, idan har ya lura Fauziyya ba ta ƙaunar zaman mahaifiyar shi a gidan nan ne? Tirƙashi... Idan ko haka ne ai kuwa zai taka mata birki tun kafin abun yayi yawa, wannan ai shirmen banza ne, mahaifiyar tashi?.






✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️


Hira tayi daɗi a tsakanin su suna ta zuba suna shewa. wayan Munira dake caji sai ringing take yi amma babu me ji a tsakanin su

Har sai da Maman Rahma ta shigo take cewa, "wai Ni kam wayan waye take ta ƙara ana kira amma ba kwa ji tsaban surutu yayi muku yawa?".

Daga Rahma har Afnan dariya suka yi. Inda Rahma tace, "Mama wlh wayan Munira ce".

"To ai sai ku zauna ku yi ta surutun kar ku ɗauka ko?" Tayi maganar tana fice wa

"Ke dai wlh Allah ya shirye ki, duk ke kika cika mana kunne da surutun ki da be ƙare wa". Rahman ta faɗa tana dungure kan Muniran

Ita kuma tashi tayi tana faɗin, "bari dai in zo ina ga Sweety na ne".

Kama haɓa Rahma tayi

Sai Afnan tace, "ai ba ki ga komi ba Ramcy, Munira sai du'a'i wlh".

"Kai kuyi min shiru don Allah shi ne". Tayi maganar da ƙarfi tana ɗaga musu hannu. Sannan ta amsa call ɗin tana kara wa a kunne

A wajen Afnan dai harara ta samu

While Rahma na riƙe da haɓa tana bin ta da kallo, barin ma yanda taga ta kashe murya tana mishi shagwaɓa ai sai ta gyara zama tana sake kasa kunne

Hararan ta Muniran tayi tana zuwa ta zauna kusa da ita tace, "bari dai in dawo gefen ki sai ki fi ji da kyau mara kunya".

Daga can Muhseen ya tambaya, "ke da wace ce haka Wifey?"

"Ni da Rahma ce".

"Ok kina gidan su ne?"

"Eh ba nace maka zamu je rabon chewing gum ba? Muna tare har Afnan ma".

"Ok ki gaishe su dukkan su".

"A'a ba ma amsa wa tunda baza kace ta bamu wayan mu gaisa ba". Inji Afnan tana taɓe baki

Dariya suka yi har Muhseen ɗin dake sauraron ta, sai yace, "ranki ya daɗe! Barka da yammaci, kiyi haƙuri don Allah dama zan ce ta baku mu gaisa ɗin ai".

"Hmm Yaya Muhseen kenan, kai dai ba ka son a katse muku hira kawai".

Dariya yayi yace, "a'a wlh Afnan, kiyi haƙuri to, ta baku wayan mu gaisa shikenan ko?"

"Sweety ƙyale Afnan yau fushi take yi dani, dama neman magana ne Ni bazan bata wayan ba, sai dai ku gaisa da Rahma". Ta ƙare maganar da mata gwalo

Ci je baki kawai Afnan ɗin tayi tana kaɗa kai alamun zata kama ta

Ita dai Rahma dariya kawai take musu. Inda Munira ta miƙa mata wayan. Suka gaisa kafin ta amsa

Muhseen ɗin yace, "kun gama ne in zo in ɗauke ku tunda naga yamma tayi? Kinga sai in ba wa Gimbiyyar tamu haƙuri".

Sai da Munira ta kalli Afnan ɗin suka balla wa junan su harara kafin tace, "a'a ka bari idan har don ita zaka zo ɗaukar mu".

"Haba Wifey ki bari mana mu zo, ai tare da Anwar zamu taho Kinga shi sai ya rarrashe ta".

"To shikenan kazo ka ɗauke mu yanzu zamu fito, dama daga nan gidan zamu wuce".

Daga nan sallama suka yi inda ta cire wayan tana kallon Afnan, sai ta ɗaka mata duka a cinya tana cewa, "ƴar banza kya yi murmushi mana tunda kin ji an ambaci sanyin ran naki, idan ma kika saka wasa sai in Kira shi in CE ya bar shi kawai kar su zo".

Kwaɓe fuska Afnan ɗin tayi kamar zata yi kuka tace, "haba My dear wai ke ba kya jin tausayi na ne? Please kiyi haƙuri mana na dena fushin dake".

Dariya suka kwashe ita da Rahma suna tafa wa

"Wai kema kin yi nisa ashe, wane ne Anwar ɗin nan ne?"

Ita dai Afnan murmushi kawai take yi

Inda Munira kuma ta gyara zama tana cewa, "abokin Muhseen ne, amma kin san Allah Afnan ta mutu a ƙaunar bawan Allan nan ina gaya miki, sai dai shi fa har yanzu ya ƙi bada kai bori ya hau".

"Kina nufin ita kaɗai take haukan ta?" Inji Rahman

"Ba dai zan ce hakan ba, amma gaskiya Afnan ta fi son shi, duk ajin Afnan wai ace a kan wannan gaba ɗaya ta watsar dashi, wlh ba ki ga yanda take ƙaunar bawan Allan nan bane ba ta ɓoye soyayyar shi ko a gaban waye ne, yanzu fa ina gaya miki shi da Muhseen ɗina har sun gano ta, kuma ashe ma yana da Mata shiyasa nake ganin be son amsar tayin Afnan ɗin".

"Cab ɗi.. Afnan ke kuma taki ƙaddaran kenan son me Mata? To wlh daga ganin wannan ba ki da gurbi a wurin shi".

Afnan tace, "a'a kar ki ce haka Rahma, wlh Anwar yana so na, sai dai na kula kamar shi be da hali ne shiyasa yake jan baya dani, Kinga kuwa yana da Mata ga kuma Ni ina zai ajiye Ni be da kuɗin aure na ma?"

Taɓe baki Munira tayi tace, "to tashi mu je ga shi ya kira. Rahma mu Kinga tafiyan mu, don Allah ki roƙi Mama tun ranan Alhamis ki zo don Allah".

"Allah kar ki ji komi zan tambaye ta kuma na san zata bar ni, tunda bikin ki ne ai sai mun hantse".

Dariya Muniran tayi tana ɗaukan Hijab ɗin ta ta sanya sannan tace, "ga shi har zamu tafi Aunty Ikram bata dawo ba?"

"Kuma wlh ban san me ya tsayar da ita ba, ba ta kai wa haka gaskiya, zuwa huɗu ne sun gama lectures". Cewar Rahma tana sake kai idanun ta kan Agogon ɗakin

"To don Allah ki bata nata chewing gum ɗin, wlh na so mu zauna har ta dawo amma kuma an zo ɗaukan mu".

"Kar ki damu Aunty Ikram bata da matsala, ai a gidan nan ban ga wanda bazai zo bikin ki ba har su Yaya Abbas, ko su Aunty Aisha sun ce mana duk sanda bikin ki ya taso in faɗa musu, kuma tuni sun sani, ai Munira ke ta mutane ce, babu wanda zai ƙi zuwa bikin ki, kinga ma nan maƙotan mu duk sun ce in sanar musu idan bikin ya zo".

"Allah Sarki kin ga sai yanzu ma na tuna dasu, wayyo wlh na so idan na zo fa ki raka Ni in Kai musu, har gidan su Hassanan nan na can bakin kasuwa, ko in ba ki ki basu?".

"Eh haka kuwa za'a yi, bani ki gani sai in basu".

"Yauwa Afnan ba ta chewing gum ɗin sai ta kai musu".

Ciro jakan dake kafaɗan ta tayi, ta miƙa wa Rahman tace, "ga shi ke kika san yawan su sai ki ɗiba".

Bayan ta cira ɗin ne suka fito waje, sai da suka yi wa Maman Rahama sallama kafin suka fita, inda Rahman ta raka su har wajen motan Muhseen da suke tare da Anwar a tsaye

"An matan Amare". Anwar yayi maganar fuskarsa cike da annuri

Tare suka haɗa baki wajen gaishe su su ma suna dariyan

Suka amsa su cike da fara'a

Inda Muhseen yace, "Gimbiyyar mu an dai dena fushin damu ko?"

Murmushi Afnan tayi idanunta a kan Anwar tace, "ai tunda ka zo min da sanyin idanuna tuni na manta da wannan babin".

Dariya suka yi gaba ɗaya

Rahma ta saka hannu ta mintsine ta tana cewa, "ke dai ko. Idanun ki sun rufe ko?" Sai kuma ta kalle su tace, "to Ni zan tafi sai kuma ranan biki".

Muhseen kuɗi ya ciro a aljihu yana cewa, "ga shi ki siya ma ƙannina biscuit, a gaida su Mama".

Da farko ta ƙi amsa tace mishi, "a'a".

Amma tuni Munira ta amshe kuɗin ta tusa mata ta tura ta hanyar gida

"Ke dai Wifey ba ki ji sai kin ji mata ciwo?".

Hararan sa tayi tana wuce wa ta shige motan

Su ma sai suka bi bayan ta suka shige, inda Afnan da Anwar suka zauna a baya, su kuma suna gaba. A haka suka tafi suna hira ko wacce da tashi.
[02/09, 7:52 pm] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*











*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*PAGE: 4*

_____Koda suka kai su gida sai da suka tsaya suka ɓata lokaci tare, kafin suka yi musu sallama suka tafi

Inda Anwar Yace ma Muhseen ɗin, "ya kai shi shagon me ɗinki ya amshi ɗinkin shi".

Can suka wuce ya amsa, sannan ya kai shi gida ya sauke shi shima ya wuce

Yana shiga gidan, ledan hannun shi ya miƙa wa Hauwa sannan yayi alwala ya fice masallaci, domin a lokacin har an gama kiran sallan magriba.




Sanda ya dawo tana ɗaki itama ta idar da nata sallan, ya shigo da sallama ta amsa mishi

Zama yayi a gefen gadon yana zame hulan shi

Tayi mishi sannu da zuwa kana ta tashi ta ɗauko mishi abincin sa ta shirya mishi a kan tabarman da ta shimfiɗa

Ƙasa ya sauko ya zauna ya soma ci suna ɗan taɓa hira

Bayan ya gama ya fita ya wanke hannun sa da baki sannan ya wuce masallaci yin sallan isha'i

Da ya dawo ne yake faɗa mata "ta ɗauko ledan ta duba ɗinkunan".

Dama tunda ya bata ta ajiye shi bata duba ba, shiyasa yanzu ta ɗauko ta soma buɗe wa fuskarta a washe da murna, kaya ne har kala biyu yayi mata, Masha Allah sun yi kyau matuƙa. Sai ta ɗago kanta ta kalle shi tana cewa, "ya ban ga naka ba?"

"Ai nawa yana tare dana Muhseen, sai ana gobe bikin zamu amso".

Murmushi tayi sannan ta soma mishi godiya

Yayi dariya yace, "babu haka a tsakanin mu, amma yaushe za ki je gidan su Muhseen ɗin? Don ya kamata ki soma zuwa ko aiki ne ki taya Umma tunda kin san ita kaɗai ce ba wani ƴan uwa ne dasu a nan ba, amma kodayake naji yace ƙannin shi biyu zasu dawo nan ɗin da zama tunda yanzu Allah ya hore".

"Haka ne. Ai Muhseen yana da ƙoƙari, wai da na so ko jibi sai in soma leƙa wa".

"To Allah ya kaimu".

"Amin ya Allah".

"Bari in kwanta yau duk na gaji wlh, kuma gobe ina son fita da wuri".

"To wankan fa baza ka yi ba?" Tace dashi tana kallon shi

Sai da ya kishingiɗa kafin yace, "a'a bar shi wankan nan sai zuwa gobe sai in Yi da safe kafin in fita, kema mayar da kayan nan ki zo ki kwanta don na san kin gaji da yawa".

Dariya kawai tayi tana kwashe kayan ta mayar a ledan, sannan taje ta ajiye a cikin kayan ta na wardrobe, ta kulle musu ƙofan tabi lafiyan gado.







*******

Ranan Laraba kamar yanda tayi alƙawarin leƙa gidan bikin, tana gama aikace-aikacen ta ta yiwa Sauda sallama a kan "zata je gidan su Muhseen ne"

Sauda tace, "kinga ai da ba na komi da na bi ki mun tafi tare ko?"

Dariya tayi kawai tace, "Ni dai sai na dawo, ina tunanin zuwa magriba zan shigo idan har da aiki da yawa".

"To adawo lafiya. Idan an samu dai a rago min, kin san gidan sha'ani ba a rasa abun taɓa wa".

Murmushi kawai Hauwa tayi tana girgiza kanta, ta san halin Sauda idan ta biye mata, shiyasa tayi ficewar ta ba tare da ta tanka ta ba

Ita kuma ta ci gaba da wanke-wanken da take yi tana rera waƙa

Lokacin ne Bilal ya shigo gidan da sallama

Amsa mishi tayi tana kallon hannun sa, ganin wayam babu leda a hannun nasa; kuma yana ƙoƙarin wuce ta ya shiga ɗaki, sai ta ce, "ah ah Baban Haidar ina kuma zaka shige ban ganka da komi ba a hannu? Ka san dai tun safe nake jiran ka ka dawo ka bamu na cefane, ga shi har yaran nan sun kusa shigowa ban ɗaura abinci ba, ya kake so in Yi idan suka dawo?"

"To Saude nima ya kike so inyi? Tunda na fita na kasa kayan nan babu wanda ya zo ya siya sai kace anyi min baki, tun safe ina cikin rana ina ƙwallan ta. Yanzu ma nan da kika ganni na dawo ne in kama ruwa tunda bayin wajen mu ya rushe, yanzu abinda za ki yi kawai ki ranta min kiyi, sai duk ki haɗa lissafi duk sanda na samu zan biya ki".

Dogon tsaki taja tana bin shi da harara sama da ƙasa, kana cike da hassala take faɗin, "Bilal wlh tallahi ka fara kai Ni bango, bazai yiwu ace ina zaune a ƙarƙashin ka ina bautar aure ba amma kuma ace Ni ce wacce zan riƙa ci da kaina, sannan inci da ƴaƴanka, kai ga ka ƙato majiyin ƙarfi baka san ka je ka nemo ba, sai dai Ni Matarka Ni ce wacce zan baka ka ci, Al'ƙur'an Bilal na fara gajiya da halin ka, gani nake yi ka ƙi ka sauya, duk haƙuri na ka fara kai Ni bango Bilal, tun auren mu haka nake fama da kai amma har yanzu bata sauya zani ba". Sai ta ɗago yatsun ta tana faɗin, "babu cima me kyau, babu suturan arziƙi, sannan babu muhallin kanka, kai kenan a kanka talauci ya ƙare iyee?"

Idanun sa kawai ya rufe yana buɗe wa a lokaci ɗaya, kana kuma ya juya da ninyan tafiya bayin ba tare da ya ce mata komi ba, gani yake yi idan ya biye mata Sauda zata iya haukata shi, gaba ɗaya ya zare a kanta ta gama sauya masa ɗabi'a, shikenan kullum murya a sama yana biye mata a kan masifa

"Au magana ma nake maka amma kayi banza dani ko? Je ka fito ka same Ni yau ko Ni Ko kai. Lusari kawai, Mutum dai tamkar Mace be san ya fita yayi ƙwadugo ya nema ba, nan kake ganin Anwar yana fita komi zafi da rana sai ya nemo yake dawowa, ko shi baza kayi koyi da shi ba, ina amfanin zama da irin ku?"

Har ya fito sababi take yi ta ƙi tayi shiru, tana ganin ya fito ɗin ma sai ta ɗaura daga inda ta tsaya, har tana miƙe wa tsaye tana cewa, "to ina zaka je yanzu kake shirin fita? Kasan da sani fa wlh bazan ranta maka ko sisi ba domin ba kai kake bani jari ba, sai dai yau a zauna da yunwa kaji na rantse maka".

"To damo Sarkin haƙuri, na ji kina da haƙuri Saude kici gaba da haƙurin, Ni yanzu bazan iya biye miki ba, amma idan na fita ko bashi ne zan ci a waje in aiko miki". Yayi maganar yana bin hanyar fita ya ficewar sa

Sai da ya fitan ne kuma taga kamar yaɓa mata magana yayi, ai kuwa sai ta soma surfa bala'i tana faɗin, "meyasa be fito fili ya faɗa abinda ke ransa ba? Ai tsoro ya ji tunda yayi mata shaguɗe, kuma haƙuri ne ai tana dashi tunda har ta iya zama dashi tsawon wannan shekarun a wannan ƙaddararren talaucin nasa". Haka dai ta gaji ta gama don kanta taci gaba da wanke-wanken nata.






✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️




*THURSDAY MORNING*
Cikin sauri take shirin nata kasancewar yanda suka ƙwazzabe ta ta fito zasu tafi

Mama na zaune a gefen ta tana ce mata, "Hafsatu kiyi a hankali don Allah duk kin ƙwazzabi kanki, ga kokon naki nan sai ki sha".

Ɗago wa tayi tana kallon Maman tace, "Inna wlh bazan iya sha ba zamu yi latti kinga suna ta jira na, yanzu za ki ga sun sake shigo wa".

"To yanzu haka za ki tafi ba ki karya ba?"

"Eh ai ina da raguwar kuɗin da Dady ya bani, zan siya wani abun in ci, sai na dawo". Ta ƙare maganar tana ɗaukan jakan makarantarta tabi hanya zata fice

"To a dawo lafiya Allah ya tsare, Allah ya bada sa'ar abinda aka je nema".

"Amin Inna". Ta amsa ta tana ƙarisa fice wa

Wajen motan da su Intisar ke ciki ta nufa, da sauri ta buɗe gidan baya ta shige kusa da Sumayya dake zaune ita da Jibril, yayinda Intisar kuma ke gaba tana faman latsa wayan ta da ya zame mata jiki, inda driver ke mazaunin sa yana shirin tayar da motan ganin Hafsan ta shige

Harara ta soma samu wajen Sumayya da tafi jin haushin ta a yanzu, kasancewar haɗa su aji ɗaya da aka yi, duk da ita Hafsan primary kawai ta gama, shi kuma Jamal ya dage sai da aka sanya ta ajin su Sumayya ita da take S.S 1, sai Intisar kuma tana S.S 2 ne, sai kuma Jibril dake J.l.S 1, to, ganin tayi girma kuma ita sa'ar Sumayyan ce shi ne Jamal ya dage sai da aka saka ta ajin su, ita abinda yake bata haushi kenan don me za'a saka ta a ajin su salon ta ja mata raini tana ƴar ƙauye da ita?.

Hafsah dai sake manne wa tayi da ƙofan tayi gum da bakin ta, don ta san halin su yanzu sai su gaya mata ba daɗi, ko kuma su mangare ta, shiyasa ta natsu wuri ɗaya tana kallon titi har suka ƙarisa makarantan babu wanda ya ce mata ci kanki

Ana tsayar da motan suka fice ko wacce tayi hanyar class ɗin ta, Hafsah na biye da Sumayya a baya har suka shige, sun ci Sa'a teacher ɗin su be shigo ba, sai duk suka sami wuri suka zauna. Sumayya kujeran ta na layin gaba ne, inda ita kuma Hafsah tana layi na huɗu gefen dama, ajin ba wasu mutane ne da yawa ba tunda basu fi su ashirin ba, kasancewar makarantan kuɗi ne shiyasa babu ɗalibai da yawa.





Da aka tashi suna fita suka ga driver'n su yana jiran su, shiga suka yi yaja motan suka yi gaba

Sun yi tafiya me ɗan nisa Intisar tace mishi, "ya tsaya".

Dole yaja ya tsaya tunda hakan ba sabon shi bane, yanzu haka da saurayin ta zasu haɗu tunda sun saba hakan

Ilai kuwa shi ne, sai ga shi shima ya faka motar shi a kusa da nasu

Sai ta fito ta wuce nashi motan, buɗe wa tayi kawai ta shige

Saurayin nata me suna Shureim yace da ita, "Hy Babe kin yi kyau".

Murmushi tayi tana fari da ido tace, "thanks dear. Ya kake to?"

"Uhm I'm not feeling well, gaskiya nayi missing ɗin ki da yawa, yaushe rabon da naga kyakykyawar fuskar nan taki? Kuma kin ƙi yarda na zo gida na ganki, i miss You so Much wlh".

"Me too dear. Ka san dai nima ina damuwa da son koyaushe mu kasance tare, amma hakan bazai yiwu ba sabida Dad, amma na san very soon komi zai wuce".

Ɗan hararan ta yayi yace, "kamar da gaske, bayan ba aure na za ki yi ba yanzu".

Dariya tayi tace, "wlh da gaske Dear zan aure ka, Ni kaina ba na son karatun nan na fi son AURE, kuma insha Allahu daga secondary School zan nuna wa Dad kai, ka ga shikenan sai dai muyi aure".

"Allah ko Baby na?"

Sai da tayi masa kallon love kafin tace, "I'm sure My Dear".

"Ok Kar in cika ki da surutu ƴan uwan ki suna jiran ki, bari muyi sallama a nan, tunda yanzu na dawo koyaushe zamu riƙa haɗuwa ko?"

Gyaɗa masa kai tayi

"Yauwa. To babu ɗan kiss na ba-bye?"

Rufe idon ta tayi tana cewa, "Allah kunya nake ji Dear, Ni dai ka dena ce min in maka".

"Common Babe sai kace ba ki waye ba, ba fa wani abun nace kiyi min ba, just kiss ne fa. Ok Ina jira na rufe ido na ma idan kunya na kike ji. Common common Babe".

Matsowa tayi a hankali tayi kissing ɗin shi a baki

"Wow babe. Thank you, I love you so much". Yayi maganar yana riƙe hannun ta idanun shi a kanta

Ita dai tuni ta sauke nata idon a ƙasa

"Kin cika kunya Babe, but very soon zan cire miki ita".

Dariya tayi tana ɗago wa ta kalle shi

"Yauwa ko ke fa. Bye ki kula min da kanki sai mun yi waya".

"ok". Tace dashi tana buɗe motan ta fice, sai da ta ɗaga mishi hannu kafin ta ƙarisa wajen tasu motan ta shige

Shi kuma driver yaja suka wuce

Hafsah dai har suka bar wajen sai kallon motan Shureim take yi. Sai da Sumayya ta bugar mata kai kafin ta juyo tana kallon ta

Ita kuma ta balla mata harara kana tace, "Aunty Intisar wlh gwara ki jawa yarinyan nan kunne, kinga dai yau ta ganki da Yaya Shureim, idan ta koma gida zata iya faɗa wa Dad tunda kinga yana janta da hira, ta yiwu ta sanar mishi".

"Kan bu... Da ko bata sake ba, wlh muddin kika sake kika yi taɗin abinda kika gani a nan, wlh sai na lahira ya fi ki jin daɗi, Dan sai na miki mugun duka, shegiya ƴar iska". Cewar Intisar ɗin da ta juyo da kanta tana kallon Hafsan

Ita kuma Sumayya hannu tasa ta sake dungure ta tana faɗin, "muna-fuka, ayi mutum sai sumui-sumui da kai yake yi, wlh saura ko Mama ki sanar ma wa ki ga yanda zamu yi biji-biji dake. Jakar ƙauye".

Ita dai Hafsah kanta na ƙasa ta kasa ɗago wa, har idanunta sun soma tara ruwan hawaye

While driver na sauraron su shi dai be ce komi ba tunda ya san halin yaran basu da kunya, yanzu sai su haɗa dashi

Shi kuma Jibril hankalin sa na kan waya yana Game shiyasa be saka musu baki ba

A haka har suka kai gida, inda suka sauka suka wuce nasu Part ɗin

Itama Hafsah sashin su ta wuce jakan ta a hannu, sai da ta isa bakin ƙofan su kafin ta share hawayenta tana daidaita fuskarta ta shige.
[04/09, 1:13 pm] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*











*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*PAGE: 5*

_____ *SATURDAY*
Tun sassafe Hauwa tayi shirin ta tayi ma Sauda sallama ta tafi gidan bikin, tunda dama Anwar shi da asuba ma ya bar

Please Login or Register in order to submit comment