Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juya wa jiki na rawa ta shige cikin makarantar

Har ransa ya ji sanyi; take ya lumshe ido a fili ya furta, "ina jinki a raina sosai Hafsah, ina fatan ki kawo sauyi a cikin Rayuwata."
Sai ya tuƙa Motan ya bar wurin,
Kai tsaye gidan su Fauziyya ya wuce, yana tunanin abun da zai yi mata ya huce, tabbas a wannan karon zai nuna mata muhimmancin mahaifiyarsa a gare sa, daga wannan ranan baza ta ƙara marmarin wulaƙanta mishi Uwa ba,
Fita yayi a cikin Motan ya samu mai gadi, after sun gaisa yace mishi, "yayi masa sallama da Mahaifin Fauziyya."

Da sauri ya tafi ciki ya sanar mishi tunda dama yana gida,
Jin wanda aka ce shiyasa yace mishi, "ya je ya ce ya shigo."
Ba ɓata lokaci mai gadi ya je ya sanar mishi sai ga shi ya shigo har cikin falon tunda ba baƙon shi bane gidan

Mamanta da Babanta ne zaune a falon,
Ya shigo suka gaisa cikin mutunta wa suna tambayarsa Yaran?
Ya amsa musu, "alhamdulillah."

Dukkan su sun ji dadin ganin Jamal don a tunanin su ya zo da maganar komar da Fauziyya ne, amma sai suka ji akasin hakan,
Take a nan ya zayyane musu abun da ke faruwa har zuwan da Fauziyya tayi ta ci ma mahaifiyarsa mutunci,
Sannan ya ciro takardan da ya rubuta mata a cikin Mota; na sauran sakin ta, ya miƙa musu

Salati suka yi dukkan su, sun kasa ma furta komai na tsawon lokaci sabida alhinin abun da suka ji, daga baya Mahaifin ya cewa Maman, "ta je ta kira Fauziyyan a daki."

Miƙe wa tayi ta nufi ɗakin Fauziyya wacce take kwana a yanzu; ita da ƙanwarta da ta rage bata yi aure ba, tana kwance tana barci Mamanta ta shirga mata uban duka, sai ga ta ta wartsake ta tashi a firgice


Fuska a ɗaure tace mata, "abun da kika aikata ya dawo kunnen mu Fauziyya, ke ba a isa a gaya miki magana ba ko? To ki taso Babanki yana kira."
Ta juya ta fice ranta a ɓace saboda baƙin cikin abun da Fauziyyan ta aikata

Hankalin Fauziyya ya tashi duk da bata san me ke wakana ba, kuma ko kusa bata yi tunanin abun da ta je ta yi wa Mama ne suka sani ba, since bata kawo hakan a ranta ba, miƙe wa tayi jiki a saɓule sabida barcin da ta sha, ta fito tana ɗaura ɗankwali a kanta,
Sai dai me? Ganin Jamal a zaune a falon ya matuƙar faɗar mata da gaba, amma tsaban kinibibi irin nata sai ta kanne ta ƙi nuna firgicin da ke tare da ita

Baban su da ke jefa mata wani kallo, yake cewa, "dan ubanki za ki ƙariso ko za ki ci gaba da zama a nan ne?"

Jiki a sanyaye ta iso wurin duk da daƙyar take ɗaga ƙafafunta, tsoron ta ɗaya kar a ce Jamal ya zo ƙarisa mata sauran sakin nata ne a kan abun da tayi, wayyo Allah! Sai yanzu ta soma dana-sani,
Bata gama zancen zucin ba ta soma jiyo faɗan mahaifin nata, yana zagin ta da cin mata mutunci


Yace, "tunda abun da kika zaɓa wa kanki kenan, kin nuna mana bamu isa ba, irin tarbiyyar da muka ba ki kenan ko? Ko iyaye sun fi iyaye ne da ba ki da mutunci ba ki san ki raga wa Mahaifiyarsa ba? Anya kina da hankali Fauziyya? Uwar Mijin naki? Ita ce abun wulaƙanta wa ko?"


"Wlh na rantse da Allah..."

"Dalla rufe mana baki, shegiya wawiya wacce bata san inda kanta ke mata ciwo ba, ai kin haifa kuma za ki ga mai zai faru ranan da za ki girbi abun da kika shuka, ƙatuwa da ke babban banza kin ajiye Yara manya amma ba ki san me ya kamata da ke ba, yau ya sanar mana da komai abun da kike aikatawa."
Inji Mamanta da ke maganar cikin baƙin ciki da ƙunai rai

Ita kuma Fauziyya kuka ta fashe da shi sabida halin da zata shiga, bata kai ga wani magana ba Babanta ya jefo mata takardan sakin nata

"Ga raguwar sakin naki nan tunda haka kika zaɓa ki zo ki ci gaba da zama damu, wlh da na san abun da kika aikata tun farko na kashe ma ƴarki Aure; na rantse da Allah tun a lokacin zan ce ya rubuta miki dukka sakin naki tunda ba ki da mutunci. Kai Jamal tashi ka tafi Allah zai saka maka."

Sai da Jamal ɗin ya kalle ta ya sakar mata wani mugun kallo, ya so a ce sun keɓe domin ta ga nashi haukan rashin mutuncin, amma ya rantse ko ba yau ba sai ya wulaƙanta ta, arzikin ta ɗaya yana jin kunyar Iyayenta, haka ya miƙe yayi musu sallama ya fice zuciyarsa na baƙi da jin tsananin tsanar Fauziyyan,
Bai tsaya ya saurari kukanta da kiran sunan sa da take yi ba, yabar gidan har yanzu yana jin zuciyarsa na zafi, amma daga yau komai ya ƙare, har abada wlh in har yana numfashi; bazai taɓa sake dawo da Fauziyya cikin gidan sa ba, ya haramta ma kansa ita har abada tunda bata san Darajar mahaifiyarsa ba.








🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆



Tunda cikin Afnan ya shiga wata takwas; iyayenta suka dage sai sun tafi da ita gida,
Amma furr Anwar yace musu, "babu inda Matarsa zata je, ba ya son wannan al'adan."
Su kuma sun dage sabida ya zame musu kamar addini ne, dayake irin Fulanin nan ne masu shegen aƙida, idan ka auri yarinya a dangin su, sai ta tafi wankan fari dana biyu, kuma dole ko kana so ko ba ka so sai sun yi wannan al'adan, sai dai ka haƙura ka ƙyale su, don zuwa suke yi har gida su ɗauke yarinya su mayar da ita gaban su; baka da yanda zaka yi, majority ma sun fi yin auren haɗi gaskiya; shiyasa basu cika samun matsala ba, kuma ga nauyin da zasu ɗaura maka da zaran sun ɗauki Matar, komai kai zaka yi musu; a yi ta kawo maka buƙatu kala-kala

Shi ba wannan ya dami Anwar ba, kawai kowa da ra'ayin sa ne, sannan ma yana ganin ba ita kaɗai bace Matarsa bare a ce wani abun zai same ta a gida, akwai Hauwa zata kula da ita, shi kansa ba ya barin ta ita kaɗai, yana ƙoƙarin dawowa da zaran ya ɗan yi wasu awanni a waje domin ya zo ya ga lafiyarta, kulawar da yake bata ya wuce misali sabida farin cikin za a haifa masa ɗa

Idan da wata ce ba Hauwa ba a gidan nan; dole zuciyarta sai ta buga sabida tsaban baƙin cikin da take ƙunsa, ganin yanda komai ya ta'allaka shi a kan Afnan, komai nasa ya koma gare ta, kula wa da duk wani abun da ya kamata ita yake yi wa, ƙarshe ma tunda cikin ya girma sosai; ya koma a dakin ta yake kwana kodayaushe, sai dai ya bama Hauwa haƙuri yana nuna mata irin lalurar da Afnan take fama dashi, idan ya barta bai san me zai faru da ita ba,
Yana nuna mata itama in ita ce a haka dole zai bar komai nasa ya tare a wurin ta yana kula da ita gudun samun matsala,
Sai dai Hauwa ta shige ɗaki tayi kukan ta ma'ishi, bata taɓa nuna masa hakan yana damunta ba, sai dai ta bar abun a zuciyarta yana cin ta sosai, har wani irin rama take yi duk da ga daula babu abun da suka rasa yanzu, ko ada da suke cikin talauci Hauwa bata da rama, amma yanzu duk tayi ƙashin wuya ta rame tayi zuru-zuru, sabida abubuwa da dama suna cin ta a rai ta rasa wanda zata faɗa ma wa, ko an tambaye ta ba ta iya sanar ma kowa, koda mahaifiyarsa ne kuwa, don tana ji da ita sosai

Takan ce, "Hauwa idan wani abun Anwar yake miki don Allah ki sanar min in dauki mataki tun kafin abun yayi nisa, duk kin rame kin canza kamar kina cikin damuwa?"

Sai dai tayi murmushi tace mata, "wlh babu komai Umma, babu abun da ke damu na babu abun da Anwar yayi min."

Daga nan sai tayi ta mata nasiha tana nuna mata haihuwa da rashin sa duk na Allah ne, a ganin ta Hauwa tana damuwa da rashin haihuwa ne tunda ga shi Abokiyar Zaman ta har ta zo ta samu ciki; ita kuma shiru. Da haka take zaunar da ita tayi ta mata nasiha,
Kuma idan Anwar ya zo wurin ta haka shima take zaunar dashi tayi ta masa nasiha tana nuna masa muhimmancin Hauwa a wurin sa, da kuma muhimmancin yin adalci a tsakanin su


Tun Anwar na jin haushi, don a tunanin sa Hauwan ce take zuwa take kai ƙaransa wurin Mahaifiyar sa, ranan farko sai da ya ci mata mutunci yayi mata faɗa kaca-kaca, yake cewa, "ku Mata kuna da son kanku wlh, idan da ace ke ce a cikin wannan laluran baza ki taɓa tunanin a yi wa wancan adalci ba; bare ki tuna an tauye mata haƙƙin ta, amma ke kin zo kina yaɗa Ni a gari ba tare da nayi miki komai ba, Hauwa ki faɗa min me na rage ki dashi da har kike son haɗa Ni da mahaifiyata? Kin ko san girman gobaran da kike shirin kunna wa tsakanin Uwa da ɗan ta?"


Wani irin kuka Hauwa take yi, ta durƙushe a gabansa tana faɗa masa, "wlh tallahi bata taɓa faɗa mata komai a kansa ba, bata taɓa ce mata komai ba."


Yanda ya ga tana kuka sosai ga kuma rantse-rantsen da take yi, tabbas ya san Hauwa ya kuma san me zata iya aikata wa, shiyasa ya yarda har zuciyarsa da gaskiyar ta bata faɗa mata komai ba, amma kuma bai nuna mata ba sai ya nuna kamar yana fushi da ita don ta koki gaba, ba ya son ko kusa ta soma kai ƙaransa wurin Mahaifiyar sa

A ranar Hauwa ta sha kuka, kukan da bata taɓa yi ba tun auren su da Anwar, ta kasa danne abun da ke ranta sabida irin wulaƙancin da bata taɓa tsammanin ganinsa a wurin Mijinta ba, gani take yi kamar ya dena sonta, tana jin idan ta ci gaba da barin ƙuncin da ke ranta kamar zata iya haɗiyar zuciya ta mutu ne, tana buƙatar mai rarrashinta. Shi yasa ta kira Hajiyarta ta zayyane mata komai tana kuka mai cin rai

Ita kanta Hajiyar ta tausaya mata, sai dai kuma ta san dole dama wata rana zata iya fuskantar irin wannan ƙalubalen, shi dama aure ɗan haƙuri ne, ba kullum ne zaka kasance a cikin farin ciki ba, dole akwai lokacin da Allah zai jarabce ka domin ya gwada imanin ka, idan ma baka yarda da ƙaddara ba kamar baka yi imani da Allah bane,
Nan ta zauna tayi mata nasiha mai ratsa zuciya, ta kuma kawo mata misalai ga Matan Annabawa da suka gabata, waɗanda suka yi haƙuri daga ƙarshe suka ci riba, don haka ta ci gaba da haƙuri komai zai wuce kamar ba a yi ba, rashin fahimta ne amma wata rana bazai yi mata haka ba,
Sannan ta gargaɗe ta sosai ta cire komai a ranta sabida gudun shiga wata matsala ko ta janyo wa kanta ciwo,
Ita kanta tana mamakin wannan rama nata, kuma ta sha tambayarta, "ko akwai wani abun da yake mata ne?"
Amma Hauwa bata taɓa buɗe baki ta sanar mata ba, a matsayin ta na Uwa gare ta wanda ko wani abun ne yake damun ta; baza ta iya ɓoye mata ba, tana jinjina haƙuri irin na Hauwa, kuma tana jinjina girman hankalin ta, duk a cikin ƴaƴanta ita ce na daban wlh, kuma ko a gaban waye tana furta hakan, "Hauwa halin ta daban ne a cikin ƴaƴanta, ko ita baza ta nuna mata yawan haƙuri ba."


Sanadin wannan abun ne Hauwa ta sake zabge wa ta rame sosai, duk yanda ta so ta fitar da komai a cikin ranta amma ta kasa, duk da a yanzu komai ya dawo musu normal suna zaune lafiya, amma canje-canjen da Anwar yake nuna mata abun yana cin ta a rai, amma baza ta taɓa iya magana ba, ta san komai lokaci ne, zata ci gaba da haƙuri kamar yanda ta saba, wata rana itama zata samu nata ɗan, wanda zata riƙa kallo tana jin farin ciki a ranta, wanda zata riƙa bayyana masa damuwarta koda ba ya jin ta,
Rashin haihuwar ma ya ƙara saka ta a cikin wani yanayi sosai, tana fatan a ce itama Allah ya bata nata rabon.
***




Ba tare da sanin Anwar ba, yan uwan Baban Afnan suka zo har gida suka haɗa mata kan kayanta suka ɗauke ta,
Sai a waya Afnan ta kira sa tana sanar masa abun da ke faruwa


Tun daga lokacin ma ya katse mata wayan sabida tsananin ɓacin rai da hakan ya jawo masa,
Ta kira ta kira but ya ƙi ɗauka, sai ma tura mata message da yayi a kan, "idan har tana son zaman lafiya wlh kafin ya koma gida ta koma dakin ta, if not kuma duk matakin da ya dauka ita ta ja."


Koda tayi arba da saƙon sa bata wani damu ba, tunda ba yau ta saba ganin haka ba, sannan ma a ganin ta Anwar yana da son kansa da yawa, idan bata koma gida ta haihu ta gyara kanta ba; shi da kansa wata rana zai kore ta a gidan, ya ɗauke ta mara muhimmanci tunda bata da wata daraja a idanunsa, balle ita da take da kishiya, dole ta tafi ta gyara kanta ta kankaro wa kanta mutunci, ai ba ita kaɗai bace Matarsa ba; akwai wata, ko me yake nema zai samu a wurin wancan, don haka baza ta taɓa koma wa ba sai dai yayi fushin ya gama, dole zai sauko ne


A tunanin Anwar zai koma gida ya tarar da Afnan ta dawo, amma sai bai ganta ba, ransa yayi ƙololuwar ɓaci, ya shaƙa ba kaɗan ba, amma ya danne abun a ransa kuma ya saka a ransa wlh bazai taɓa zuwa neman ta ba, su je suyi duk abun da zasu yi tunda basu ɗauke sa da daraja ba, haka ya tafi gidan su yana zayyane wa Umman sa duk abun da ke faruwa

Tace, "yayi haƙuri tunda shi ya ɗauko ta a inda suka saba da nasu Al'adan, dole ya girmama abun da suke so tunda shi ya gani yace yana son irin su, haƙuri kawai zai yi, tsuntsun da ya jawo ruwa shi ruwa kan duka."


Shi da ya zo ya samu sassauci a wurin ta, amma sai ya ga kamar tana gaya masa magana ne, shiyasa ya kakkaɓe mazaunan sa ya tafi gida gwiwa a sacce

Hauwa duk da irin sauyin da ta gani a kan fuskarsa, ko kusa bata tambaye shi ba tunda bai sanar mata da kansa ba, don haka itama ta share sa ta mayar da hankali a kan abun da ya shafe ta

Ganin yanda ta nuna ko'in kula da damuwarsa, shiyasa ya kasa haƙura ya sanar mata abun da ke damun sa, ko don ya samu ta ba shi haƙuri ko ya samu sassauci

Murmushi kawai Hauwa tayi tace, "to Allah ya dawo dasu lafiya ya raba lafiya, ai ta faɗa min kafin su tafi, nayi tunanin da sanin ka?"

"Ina fa, bayan nace mata kar ta je babu inda zata tafi tabar min gida tunda ga ki in ma haihuwar ne, amma saboda ban isa ba ta ƙetare ta zaɓi dangin ta a kaina."

"To ai na ga Ni kaina ban san haihuwar ba bare in san yanda zan kula da ita, tafiyan nata ina ga zai fi alkhairi ai."
Tayi maganar tare da miƙe wa ta nufi kichen ba tare da ta sake bi ta kansa ba,
Koda ta dawo ta ƙi yarda su ci gaba da maganar duk da yanda yake son su yi maganar, sai ta jawo wani zancen sabida gani take yi bai shafe ta ba, kuma idan ya ci gaba da zancen yana saka mata ɓacin rai ne sabida kishi, gwara ta janye maganar shine samun kwanciyar hankalin ta


Shi yasa tun daga ranan Anwar bai sake taka gidan su Afnan ba, duk kiran da suke masa da kuɗin da suke bukata a wurin sa; ya ƙi kula su bare ma ya basu,
Sai da suka kai ƙaransa wajen Mahaifinsa sannan ya kira sa yayi masa fata-fata

Yace, "haka ake yi ne? Ya za a yi Matarka tana gida ana kula da ita amma baza ka iya zuwa ka je ka duba ta ba? Sannan ma ka san dole zasu buƙaci abubuwa tunda ba ɗauke maka nauyin da ke kanka aka yi ba, amma ka ƙi zuwa kuma sun yi maka magana ka ƙi basu abun da suke buƙata, haka ake yi ne?"


"Baba Ni fa bada amincewa na suka tafi da ita ba, su suka yi gaban kansu don haka babu inda zan je sai dai su dawo min da Matata."


"Ka ga naka, nace ka ga naka Muhammadu, idan basu tafi da ita ba so kake yi ta mutu babu mai kula da ita? Ka san kuwa halin da mai ciki take shiga a irin wannan gaɓar? To ba na son haka wlh, idan sun tafi da ita wani aibun ne? Ko kai zaka iya kula da ita ne kai da baka a gidan?"
Yayi shiru yana jiran jin amsar sa

Sai yace, "Baba amma akwai Hauwa a gidan ba ita kaɗai bace, zata kula da ita ko haihuwa ya zo zata samu taimakon ta, sannan zata kira Ni sai mu tafi asibiti."

"To Ni ban ga abun tayar da hankali
a nan ba don Allah Muhammadu, ai sun san da kishiyar nata suka ɗauke ta, sannan ita kanta Hauwan bata taɓa haihuwa ba bare ta san yanda zata kula da ita, komawan ta gaban iyayenta shine a'ala, don haka kayi hakuri kayi duk abun da suke so komai ya wuce, fatan mu kawai ta haihu lafiya shine; ba wai a riƙa gutsiri tsoma ba, mu ji da laluran da ke kanta."


Ba shi da yanda zai yi haka ya haƙura ya koma gida, but duk da haka bai taɓa zuwa ba sai dai ya tura musu kuɗi, duk abun da suke buƙata zai basu amma ya dena zuwa, kuma ko wayan Afnan ɗin ya dena ɗauka


Wasa-wasa sai ga cikin ya wuce watanni tara amma har yanzu Afnan bata haihu ba, yanzu watan cikin goma cif babu labarin haihuwar ta


Dole Anwar hankalin sa ya fara tashi, sabida jin shiru - shiru har yanzu ba a ce mishi ta haihu ba, hakan ne yasa ya ajiye duk wani fushin sa ya miƙa ƙafa ya tafi gidan.
[21/01, 7:16 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:38*

_____Koda ya je gidan su Afnan, ya tarar an tafi da ita asibiti, ashe tun jiya take ciwon naƙuda, yau da sassafe suka tafi da ita asibitin, kuma ba a samu an kira sa an faɗa masa ba sai yanzu da ya je can ake sanar mishi, shiyasa ya kama hanyar asibiti, a hanya ma ya kira Iyayensa ya sanar musu, sannan ya kira Hauwa ya faɗa mata itama

A tare suka isa asibitin da Hauwa da su Umma,
Lokacin hankula ya tashi har yanzu Afnan tana can tana naƙuda babu labarin haihuwa, tun suna tsammanin fitowar ta yanzu har sun gama fidda rai, musamman yanda suka ga ana ta sintiri a ɗakin da aka shigar da ita

Anwar ya kasa tsaye ya kasa zaune, ko masallaci bai iya zuwa ba, sai daga baya ne da aka kira sallan Asar sannan ya je ya haɗa

Su ma su Umma tun suna zaune cikin daɗin rai har sun gaji, ga babu halin tafiya gida tunda har yanzu basu san halin da take ciki ba

Ƴan uwanta sai tururuwan zuwa suke yi duk da an ce musu bata haihu ba, suna ta zuwa su ga halin da take ciki

Bata haihu ba sai gab da magriba asalin naƙudan ya zo mata gadan-gadan, dama sun ƙi mata aiki ne don sun ga alamun zata iya haihuwa da kanta, lokaci ne bai gama yi ba,
Ilai kuwa sai ga ƴaƴa ta sako su har su biyu, abun mamakin basu taɓa tunanin ya'ya biyu zata haifa ba tunda ba a taɓa sanar musu ba, in fact ma ba a taɓa duba mata ba, su dai a hasashen likitoci sun ce ɗaya ne,
Sai ga shi ta sako yara biyu Mata tubarakallah Masha Allah kyawawa da su, sai dai basu da girma ne sosai

Zo ku ga murna wurin Anwar, kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha don daɗi da farin ciki, bakin nan ya ƙi rufuwa

Bama shi kaɗai ba; jama'a duk sun yi farin ciki ba kaɗan ba, sai taya su murna ake yi,
Sai lokacin hankula ya kwanta wasu suka tafi gida aka bar dangi na kusa,
Daga Hauwa sai su Maman Afnan ɗin,
Ita kuma Umma tunda ta ga ta haihu sai ta tafi da nufin ta turo ƴar uwanta

Haka aka yi ta zuwa tururuwan ganin jarirai Masha Allah. Anwar har ya fita ya siyo musu kayan da za a saka musu iri ɗaya sak tunda ba a san ƴan biyu za a haifa ba, shiyasa ya fita da sauri ya siyo guda biyu komai kala ɗaya, aka yi musu wanka aka sanya musu,
Ɗaya dai bata yi kuka ba har yanzu duk da alamun tana da rai

Likitoci sun duba ta sun ce, "a dena jagula ta da yawa."
Sannan suka ce, "su fita waje a bar Uwar ta huta sosai sabida tana buƙatar hutu a yanzu."

Har dare su Anwar suna asibitin sun ƙi tafiya, Hauwa na zaune itama tana jiran in zai tafi sai su wuce tare, sosai ta taya Afnan murnan zuwan yaran, musamman yanda ta ga yaran suna kama da Mijinsu, shiyasa suka shiga ranta kamar ta bata ɗaya haka take ji, har ƙwalla sai da ta share tana fatan a ranta Allah ya nuna mata nata itama

Ba a sallame su ba sai a washe gari kusan ƙarfe ɗaya na rana, sannan aka basu sallama suka koma gida

Anwar ya ji haushi da aka ƙi ba shi Matarsa kamar ya kurma ihu haka yake ji, sai dai ba shi da yanda zai yi amma sai tukuburci yake yi, bai so aka raba shi da ƴaƴan shi ba wlh amma ba shi da yanda zai yi, amma ransa a jagule yake

Har suka tafi gida ɗaya yarinyar bata yi kuka ba, ashe ma abun zai zo da ƙaran kwana ne baza tayi wani tsawon rai ba, a ranan aka gane ta mutu tunda ba ta motsi

Ba kaɗan ba sun ji mutuwar yarinyar, musamman da aka sanar da Ubanta kamar yayi hauka, Afnan kuwa har da share hawayen ta don ji tayi kamar kar a tafi mata da ƴarta, shikenan ta rasa ta?
Koda aka rufe ta sai dai ta koma kallon hotunan su da aka yi musu a waya basu da yanda zasu yi

Haka dai rayuwa ta ci gaba kullum Hauwa tana kan hanyar zuwa gidan, idan ta zo tun safe sai dare take koma wa gida,
Har Sauda ta zo mata Barka har can gidan,
Sai lokacin ne ma take bama Hauwa labarin fitowar Sadis da aka sake shi, sai kwanan nan aka sake shi tun ɗaure shi da Sojan ya saka ayi, duk sun

Please Login or Register in order to submit comment